Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*_INAYAH_*

_(Riba Biyu)_



_Mamuhgee_



1

_*please masu daukamun Sunayen books da Labarai suna sauyawa suyi nasu lamarin ina ganinku dan Allah ku daina ba kyau, kuma masu copying nagani allah ya kyauta ngd duk cikin Qaunace allah yaqaro kauna🥰*_





_BismillahirRahmanirRaheem_

Tasowa tayi ahankali tana takowa zuwa tsakar gidansu datake jiyo maganar mahaifiyarta da yayyunta maza tareda kishiyar mahaifiyartata suna magana duk a jujjuye sbd hankalinsa daya tashi lokaci daya cikin mummanan yanayi da tashin hankalin mugun labarin dayazo musu yanzu yanzun.



Ita kanta hankalinta baa kwance yakeba dama can sbd halinda take ciki na jinyar mijinta dake kwance asibiti Yana jinyar accident dasukai kwana biyu dasuka wuce a hanyarsa ta dawowa daga gurin daurin auren qaninsa dasuke uwa daya uba daya,



Kaman a fizge kunnuwanta suka jiyo mata abinda babban yayanta Umar ke fada saidai Sam takasa fahimtar abinda yafada din zahirance Dan haka tana buqatan jinsa da kyau,



Ta qaraso jikin kofar ta yaye labule ta fito tana kallonsu daya bayan daya fararen idanuwanta dasuka jima da shigewa ciki ciki sbd damuwar datake ciki kwanakin,



Suma ita suke kallo Kaman yanda take binsu da kallo kowannensu fuskarsa cike dauke da alhini dakuma tausayinta Dan kuwa Rashin miji a irin shekarunta abin tausayi

Ga Kuma 'da da ciki dake jikinta.



Kallon mahaifiyarta tayi taga yanda tayi qasa da Kai cikin yanayi na hawayen dasuke Neman saukar mata takasa kallon Yar Tata



Dan haka ta kalli kishiyar mahaifiyarta kai tsaye tace"



Inna Menene duk kukai wani iri haka?

Lafiya kuwa?

Wani abin yakuma faruwa ne?



Maida kallonta tayi kan yayyunta dake tsaye suna kallonta tace"



Yaya Umar,Yaya kabiru?

Lafiya duk kukai shiru haka?

Jikin Abban Abdul ya tashi ne?



Ajiyar zuciya Yaya kabirun ya sauke tareda gyara tsayuwarsa ya kalleta da Dan alhininsa irin na maza masu taurin zuciya Kai tsaye yace"



Khadija bayan barowarki asibiti yanzu Allah yayiwa Salisu cikawa........



Bai qarasa ba ta waiwayo gefensa tana kallonsa cikeda zallan mamaki da faduwar gaba muryarta na gwamutsuwa tace"



Yanzu fa na Barosa Yana barci,

Wanka fa kawai zanyi nakoma asibitin shine zaace ya rasu????

Yanzu yanzu fa?



Da sauri innar ta riqota cikin tausayawa tace"



Hadiza karkiyiwa ubangijin haka,

Tawakkali zakiyi tunda kinsan dai baa wasan mutuwa...



Idonta na sauya zuwa ja da hawayen dake kokarin cikowa saidai taurin zuciyarta ya hanasu fitowa

ta katse innar da cewa"



Inna bacci nabarosa yanayi fa,

Yaji sauki sosai yau,

Rasuwa fa akace,

Mutuwa fa kenan, ya tafi ba dawowa har abada,

Ta Yaya zanyi.......



Cikin Dan daga murya Yaya kabirun yace"



Ke Khadija Menene hakan?

Rasuwa fa akace Miki salisun yayi,

Ki nutsu ki fahimci ita rasuwa babu ruwanta da yanzu yanzun dakike fada,

Kiyi gaggawar bude hankalinki ki fahimci abinda yafaru dake,

Salisu ya rasu bazai taba tashiba......



Bakinsa take kalla kanta na juyawa

Zuciyarta na harbawa da mugun qarfi Kaman zata faso kirjinta,



Mamarta ta kalla idanuwanta na qafewa taga alamar gskiyar zancensa akan fuskan mamar,



Ta waiwaya ta kalli Yaya kabiru Shima hakan tagani.



Wani busasshen yawu ta hadiye wanda har yankan maqoshinta yake

Ta juya kai tsaye Takoma dakin mama ta dauki doguwar hijabinta data cire bayan shigowarta gidan ta zira ko waya da kudin adaidaita Bata daukaba ta fito ta zira slippers din mamarta daya Da nata takalmun daya batareda ta luraba ta nufi kofa tana jefa ka kawai dan bata cikin hayyacin kallon gaban nata

asibitin take buqatan isa kawai.



Inna ce tayi saurin janyo nata hijabin tabi bayanta tana Kiran sunanta,



Mamarta kuwa kallon Yaya Umar tayi tana cewa"



Bisu kabasu kudin adaidata ban Saka ran kowannensu ya daukaba.



Juyawa yayi ya bisu

A titi yayi saurin taddasu ya ciro 1000 ya miqawa Inna Yana cewa"



Ga kudin adaidata Inna

Ki lura da ita Inna kartaje asibiti tayita wainnan maganganun

Tawakkali akeyi kifada mata Inna.



Da sauri innar ta qarasa gurin hadizar daketa zuba sauri tana tafiya ta riqota ta riqe hannunta gam tana kokarin Kiran sunanta saiga adaidata gabansu ba Bata lokaci suka fada ciki

innarce tafada masa asibitin da zasu

Khadijan kuwa Banda rawa babu abinda qafafunta da hannuwanta keyi.



Isarsu asibitin ko Gama tsayuwa baiyiba Khadija ta sauka tareda wucewa da sauri ta nufi hanyar Emergency ward da har lokacin Salisu anan yake.,



Tun daga nesa Yan uwan Salisu din maza da mata suka hangota tana tahowa a gigice ko ganin gabanta batayi

Hankalinsu yakuma tashi da tsananin tausayinta dan haka da yawansu suka qara fashewa da sabon kukan Rashin Dan uwansu.



Tana qarasowa da kallo tabisu daya baya daya taga yanda mahaifiyar salisun ke rusa kuka take taji Rabin jikinta na neman mutuwa ta qarasa dakin tashige da gudu ta nufi gadonsa da gawarsa kawai ta tadda a rufe da zanin gadon data zo masa dashi yau da safen.



Tsawonsa ta kalla tareda hannuwansa da aka miqar,



Kasa gasgatawa tayi Saida takai hannu ta yaye zanin tayi arba da kyakkawar fuskarsa ta asalin fulanin Yola....



Mummanan bugawa zuciyarta tayi ba tsammani idonta yarufe tana kokarin zubewa Inna tayi saurin tarota tana Kiran sunanta Amma Sam batajinta sai neman somewa takeyi.



Da sauri hajiyarsu salisun ta qaraso tana cewa"



Ku koma gida da ita karta shiga wani Mummanan halin ga juna biyu a jikinta.



Qwacewa takeson yi Dan Bata tunanin zata bar gawar salisun ta tafi koina Amma batada qarfin motsawa bare magana Dan bakinta take ya manne Kaman an Saka mata glue.



Tana kallon gawar mijinta Salisu aka jata aka fice da ita har waje aka kuma sakata napep tareda Inna da qanwar salisun suka nufi can gidan iyayen salisun.



Suna isa ko tsakar gidan Bata qarasa shigaba ta yanke jiki ta fadi jini nabin qafafunta.



Hankali tashe sukai kanta tareda ciccibarta zuwa dakin hajiyarsu salisun Inna na Kiran sunanta hankali tashe.



Jini sosai take zubarwa Wanda ya tabbar musu da cikin zubewa ne yayi babu tantama Dan haka basuyi wani yunqurin maidata asibiti ba haka Inna da dattijuwar gidan qanwar mahaifinsu suka taimaka mata gurin ganin jinin yagama zuba ta Dan gyara.



Kururuwar koke koken da gidan ya dauka ne ya tabbatar musu da isowar gawar Salisu gida

Tana jin hakan ta rintse idonta cikin tsananin azaba sauran abin dake cikin nata ya qarasa zubowa sai alokacin wani irin gunjin kuka Mai tafe da radadin zuciya ya kufce mata.



Inna dake kanta ta qara matsowa tana dafata cikin tausayawa jin irin girman kukan datake,



Kuka takeyi sosai zuciyarta na radadin Rashin mijinta uban 'danta dakuma wannan cikin daya qwallafa ransa akansa,

Ashe tareda cikin zasu bar duniya Rana daya shiyasa Allah ya saka masa tsananin kaunar cikin abokin tafiyarsa ne kenan.



Bata damu da yanayin datake ciki ba

Haka ta dafa ta miqe tsaye tareda qarasawa tsakiyar bayin dakin hajiyar ta wanke jikinta daqyar sbd tsananin rawar da hannuwanta da qafafunta keyi.



Fitowa tayi Kai tsaye ta karba zanin da inna ke miqo mata ta daura wani irin tsananin jiri da ciwon mara Mai tsananin gaske Yana nukurkusarta Amma taqi yarda tazauna Kai tsaye ta fito tsakar gidan sanyeda hijabinta tanajin yanda tako ina gidan ke amsa amon kukan Yan uwan Salisu.



Gawarsa dake shimfide a dakin da zaai masa wanka ta nufa ta zube gabansa tafara rero wani irin gunjin kuka tana Kiran sunansa.



Duk yanda akaso janyeta kasawa akai sbd kuka takeyi sosai zuciyarta na tsananin qunar Rashin mijinta datake tsananin so da kauna yau gashi ya tafi yabarta cikin duniyar da kowa babu abinda yasani sai kansa,



Ina zata da 'danta Abdul Wanda tasan babu Wanda zai daki kirji a cikin danginta Kona salisun ya tallafi rayuwarsu.



Lokacinda za ai masa wanka da sirita aka samu aka janyeta daga dakin musamman da itama wani irin gagarumin zazzabi ya rufeta lokaci daya dakuma sabon jinin daya Kuma balle mata sai alokacinma kowa ya San da Bari tayi.



Baa kaita asibiti ba a dakinta dake gidan aka kwantar da ita kasancewar a gidan suke zaune tareda iyayen salisun tunda dagasu har iyayen ba masu hali ban Dan hakan nema sukeda daki daya tal da Dan qaramin palo da bandaki acikin palon,

Tana daki ana fama da ita har aka tafi da gawar makwancinsa,



Iya fatu aka kirawo makociyarsu Mai karban haihuwa ita tazo ta duba hadizan ta tabbar musu da cikin yagama zubewa

Nan aka shiga wani jimamin aka fara kulawa da hadizan.



Sbd yanayin jikinta dakuma zaman gaisuwar da ake gidan yasa dole Inna ta zauna tareda ita tadawo da kwana gidan tunda maman hadizan bazatazo ta zauna ba.



Sosai take fama da jinyar kanta bayan kwana biyu da rasuwar sbd takasa daina kukan mutuwar Salisu,



Salisu mijine ma gari Kuma uba nagari hakama 'da na gari gun iyayensa.



Cikin kwana biyu duk tabi ta yamutse da tsananin damuwa dakuma ciwo dake damunta na tsananin ciwon mara na barin datai.



Angama zaman gaisuwar har anyi sati biyu babu wani Abu daya sauya daga gareta saima sabon ciwon damuwa daya kamata Sam takasa fita daga halin damuwar Rashin mijinta,



Inna na tareda ita har lokacin Kuma dai ita zata zauna da itan har tsawon watannin dazata Gama takabarta kafin sukoma gida tare.



Abdul Yana gurin mama dama tun tana zaman jinyar abbansa asibitin kafin rasuwar tasa Dan haka kullum a daki suke wuni daga ita sai Inna,



Abincinta Wanda yake kicin dinsu tun Wanda salisun ya siya shi Inna ke dafa musu yana qarewa babu Wanda yakawo musu wani saidai aka ringa Basu daga cikin gidan Idan an dafa,



Wanda ake basun baya wani isarsu itada innar dan haka so da yawa innar Idan taci na safe yafe mata na ranar take ita taci,



Itakuma Idan anbasu na daren saitace ta koshi saita barwa innar taci.



Tun daga Nan yanayin yafara kulle musu

Da innar dai taga daga ita har hadizan sunfara dogayen wuyan yunwa Kamar Yan gudun hijira dole taje gida ta sanarwa mamar hadizan sukai shawara akaiwa Umar da kabiru magana akan su taimakawa hadizan da abinci

shine suka Dan fara taimakawar duk bayan kwana biyu suna Bata dubu daddaya ko dari Biyar Biyar.



Tun suna Bata tana samun na siyan abinci da Kamar su sabulun wanki hardai Suma ana Jan lokaci suka daina sbd Suma da nauyin nasu iyalan akansu dan haka suka koma Yar gidan jiya.



Watan salisun uku da satittika da rasuwa gabaki daya rayuwarta ta juya mata upside down sbd hajiyarsa itama ta kanta takeyi Dan dama shine kawai Mai tausayi da tallafa mata acikin yayanta shiyasa itama bazata iya daukan nauyin hadizarba Dan haka kowa tasa ta fisshesa akeyi a gidan.



Hadizar ta rame ta hargitse ta sauya kamanni sosai bayan dogon wuya da dogon hanci sai ido dasuka fito kaman me Neman allura a duhu haka Takoma dama ita Inna sun saba da talaucinsu Dan haka masifar quncin Rashin ba wani damunta tayiba Kaman dai yanda tausayin rayuwar hadizan tafi damunta sbd tasan wani sabon gararin ne zata tadda gida koda tagama zaman takabar sunkoma.



Ta bangare daya tunda tayi barin cikinta lokacin rasuwar Salisu har yanzu takasa ganewa lafiyaarta sbd ciwon mararta yi yakeyi Yana tasan mata,

Wani lokacin idan yatasar mata Kaman zata rasa ranta haka take fama dashi Amma Bata taba zuwa asibiti ba Dan babu hali,



Ko innar dasuke tare Bata sanarwaba Dan karta daga mata hankali bayan daga ita har mamarta tada hankali kawai zasuyi basuda wata mafitar.



Cikin wani irin tsanani da matsuwar Rashi da tarin damuwa tagama zaman takabarta suka fara Shirin tattarawarta komawarta gidansu.



Hajiyar Salisu tayi sabon kukan mutuwarsa lokacinda hadizan zata tafi,

Tanajin inama tanada halin cigaba da kulawa da matar salisunta da 'dansa data riqesu

Amma batada Wannan halin,

Ko Abdul dinma tana tsananin kaunarsa saidai bazata iya riqonsaba shiyasa batamayi maganar karbarsaba,

Da mahaifinsu salisun Shima Yana raye tasan bazai taba barin hadiza da Abdul din su tafi ba.



Ita kanta hadizan ta San cewa Rashin halin ne yasa hajiyar batai yunkurin cewa a bar mata abdul ba Dan tunda salisun ya rasu itama yanzu abincinta neman gagarta yake

Gwara tabarwa hadizar 'danta tasan duk tsanani zata nema ta kula dashi.

##MAMUH#

#ZAFAFABIYAR#





_ZAFAFA BIYAR_



*_INAYAH_*

_MamuhGee_



*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_



*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_



*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_



*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_





_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*





_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK_



_4 BOOKS 4500_

_3 BOOKS : 3500_

_2 BOOKS : 2500_

_1 BOOK: 1500_





YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾



ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070



SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


2
Dawowarta gidansu dole dakin Inna ta tare tareda innar tunda babu wani extra daki dazata zauna a gidan bayan  nan,

Duka duka dakuna biyu ne gidan sai bandaki dake tsakar gida,
Daki daya na mama daya na innar,

Ko acan dah da mahaifinsu na raye zagayen dakuna yake,
Ita Kuma Idan Yana kwana dakin mama saita kwana a dakin Inna,

Idan a dakin Inna zai kwana saita kwana a dakin mama
Ahaka ta girma harya rasu itama akai mata aure.

Dawowarta gida wata sabuwar rayuwar zullumin kullum tashiga acikinta,

Daga Inna har mama babu Mai wata qwaqwarar sana'a,
Mamace ke Saida lallen hausa
Inna Kuma tana saida su kanwa da borkono
To tundama ta tafi taya hadizan zaman takaba sana'ar ta tafi sbd jarin ba wani Mai yawa bane dakuma hardashi suka hada duk suka cinye a can gurin zaman tunda sun shiga tsanani,
Dan haka sana'ar innace kawai yanzu take Dan taimakawa ta wani bangaren Amma kam suna cikin gararin yanayi sbd Suma dama can salisun ne yake dauke da nauyin nasu tunda nasu yayan basa taimakonsu kansu da matayensu da yayansu kawai suka sani.

Ita Inna Bata taba haihuwaba shiyasa tun take riqon hadiza tun tana yarinya gashi Kuma hadizar ce kawai mace acikin yayan mama dukansu mazane su uku,
Malam Nafi'u Wanda Allah yayi rasuwa watannin baya,
Sai Kabiru da Umar dasu kuma ayanzu kownanensu yakeda mata daddaya da yara kusan Biyar biyar,

Sai ita autarsu Khadija wadda Rashin tsayayyan manemi yasa batai auren wuriba sai data dan girma a gida sosai takai kusan shekara ashirin da takwas  kafin tasamu salisunta dasuke tsananin so da kaunar juna sukai aure ya dauke nauyin tallafawa su Inna daidai gwargwadonsa.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda  ya dauke lalaurar kula dasu mama,
Saidai idan an kwana biyu su samu Kamar dubu daddaya su Basu ko 500 Wanda sukam suke ganin kokarinsu a hakan suyita saka musu albarka duk da innar tasan basa kyautawa suna kallo Salisu ke ciyar dasu bayan Shima ba wani karfin yake dashiba kawai zuciyar alkhairi yafisu.

Yya Kabiru koyarwa yakeyi a secondary school din gwamnati dake kusa da anguwar dayake da iyalinsa
Kusan shekara goma kenan Yana aikin koyarwar Amma babu wani cigaba kullum Yana Nan a yanda yake.

Yaya Umar kuwa sanaa kowacce yi yakeyi baida tsayayya guda daya Amma dai yafi yin ta dillancin harkar Saida filaye da gidaje Dan Yana samu sosai acikinta shiyasa yafi yya Kabiru rufin asiri,
Qarshema dai fadawa yayi siyasa sbd uban gidansa dayasashi fitowa Dan samun kudin jam'iyyar da zasu fito ta karkashinta tunda sunsan dai ba ci zasuyiba Amma sunsan jam'iyyar zata Basu kudi sosai Dan haka gadan gadan yafada siyasa baji ba gani,

Yaya kabiru daya fahimci akwai samu sosai a harkar take ya marawa Umar din Baya Dan Shima ya samma masa Idan ta 'bulle.

Itakam hadiza ganin zaman baida wata mafita
Ga Abdul ya isa sakawa makaranta tuni
Sbd abbansa koda ya rasu yanada burin sakasa makaranta alokacin,

Yanzu komai ya juye musu Kuma tanada burin bawa Abdul din ilimi Dan ya anfana rayuwarsa,

Gasu Inna da mama kullum cikin dubaru ake
Yau aci kwadon kwaki,
Gobe aci kwadon qanzo,

sai ankwana hudu ko Biyar Daqyar ake hada cinikin da zaai musu tuwon gari da miya.

Dole hadiza ta tashi ta Saida katifarta da ita kadai ta dawo da ita sai tarkacen kayan kitchen ta kwashesu takai kasuwar Yan kayan hannu ta saida ta tattaro kan kudin taraba biyu ta siyo musu abinci da kayan abincin tadawo gida.

Sana'ar kosan safe dakuma awarar Rana tafara da sauran kudin yafara juyuwa.

Kasancewar ita Inna da sauran karfinta sai tana taya hadizar aikin sana'ar musamman awarar datafi wuyar sha'ani.

Cikin ikon Allah lokaci qanqani saigashi sana'ar ta samu karbuwa sosai duk da farko taci tsananin wuyar wuta da Rashin jamaa masu siya tunda baa saniba,

Babu ranarda Bata konewa shiyasa kusan koina tagama kokkonewa hannuwa da qafafu
Har fuska ma wani lokacin idan Mai yayi watsi.

Ba laifi yanzu basa neman komai a gurin kowa Wanda dai zasuci saidai Dan abinda baa rasaba.

Inna ma tuni dole suke komai tare sbd aikin yanawa hadizan yawa ga koko dasuke hadawa dashi yanzu da safe,
Da Rana ma yanzu ba awarar kawai sukeba harda dankalin hausa da wainar rogo.

Dole dai yanzu innace take aikin kosai da kokon safe ita Kuma tana awarar da sauransu da Rana sbd dukkaninsu aikin yayi mutsu tsananin wuya musamman tunda aikin wuta ne,

Mama ba cikakkiyar lafiyayyaceba shiyasa Basu taba barin ta shiga sana'ar ba,

Tunda mahaifinsu ya rasu haka take yau lafiya gobe ciwo,
Hawan jini da ciwon sugar ke tsananin damunta Dan haka lallabawa kawai takeyi tana rayuwar.

Ahaka hadiza ta samu ta sanya Abdul a makarantar gwamnati yafara zuwa
Kullum ita ke rakasa da qafa tadawo
Idan antashi haka take komawa ta dawo dashi sbd akwai Dan nisa sosai.

Hutun farko na makarantar tabi taqarasa hargitsewa sbd yanda kullum saita kaisa ta daukosa ga lattin fara sanaarta datakeyi Idan taje daukosa,

Dole Inna ce take fara yimata kafin ta dawo daukosa ganin mutane sun fara janyewa ansamu wata Yar baqin cikin ta fara sana'ar a makwaftansu.

Ganin Inna ma wahalar duniya tafara sakota gaba sbd ayyukan sun mata yawa ko baccin arziki bata samu sosai dole mama ta ringa karba tanayi sbd Suma su ringa samun sassaauci tunda Allah yasa yanzu da aikin suka dogara kacokam.

Tsawon lokaci rayuwar tana yanda take garesu ba wani dogon sauyi saima ciwo daya kwantar da mama Dan haka suka sake zagewa da Sanaa ga Inna itama karfinta yayi qasa,
Ga Abdul yanzu karatun nasa yafara nisa tunda Yana aji biyu yanzu.

Ita kanta lafiyarta wani lokacin qaranci take mata sbd ciwon mararta har lokacin Yana taso mata akai akai gashi wani babban ikon Allah dayake kamata shine tunda tayi Bari lokacin rasuwar Salisu har yau Bata taba yin wani al'adar ba,

Tayiwa Inna maganar innar tace mata wasu matan na hakan musamman Idan suntaba samun matsala ta Bari Dan haka ko jinin Al'adar zai koma ya ringa zuwa daidai sai tayi wani auren kilan.

Da Wannan zancen ta tattara maganar Rashin zuwan Al'adar ta watsar tafara neman wata sana'ar sbd wannan din ta daina tafiya sosai sbd kusan anguwar ganin ana samu duk sun fara sana'ar shiyasa yanzu ba mutane sosai.

Ganin wata sana'ar taki samuwane
Duk Wanda tafara Bata karbuwa gashi jarin nata tafiya gurin hidimar gidan yasa dole tafara zuwa aiki wani gida acan GRA da mama Indo qanwar Inna ta Samar mata.

Fara aikinta sai rayuwa kuwa ta sauya musu Dan yanzu da albashin suke komai.

Bata wani jimaba da fara aikin saigashi hajiyar suka tattara suka bar qasar itada 'yayanta dole tadawo zaman gida ba wani aikin.

Jin bazata iya zaman ba aikin komaiba yasa takuma zuwa tasamu mama inda dake shirye shiryen tafiya Lagos itama aikin Sanaa tace takuma samar mata wani aikin.

"Babu wani gidan aiki Idan ba Lagos Zaki shirya ki bini ba kya ringa musu aike daga can kokuma abaki Aron kudi ki bar musu Idan munje can kya ringa biyana da kudin aikinki??"

Haka mama indo ta sanar mata Dan haka batada wani sauran zabi bayan amincewarta sbd suna cikin tsananin halin nema gskia.

Ko data sanar dasu Inna farko sunso hanawa Amma ganin yanda mama Indo tai musu bayanin aikine kawai a wani babban restaurant na masu kudi da aka bude Kuma sunada masauki Mai kyau da restaurant din suka tanadarwa ma'aikatansu a tsaftace cikin kwanciyar hankali.

Hakan yasa suka amince tareda bawa mama Indon Amanar kula da hadizar duk da ba yarinya bace.

Kudi sosai hadiza ta karba gurin mama Indo ta siyawa su mama abinci Mai Dan yawa tareda dinkawa Abdul uniforms har kala biyu da sabbin takarman zuwa makaranta da slippers harma da sababbin litattafai.

Sauran kudin taje takuma siyo musu sabulan wanka da omon wanki dasu lalle da kanwar dazasu ringa saidawa daga zaune cikin gida ta damqawa Inna sauran kudaden a hannunta.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda yayi yunqurin hanata tafiya sbd su yanzu siyasar gabansu ta ishesu shi Yaya kabiru harda tattara  aikinsa yayi ya ajiye sbd ganin sun fara samu ba laifi.

_LAGOS_
Da farko tafara Shan wuyar rayuwar garin data aikin dasukeyi sbd wani sabon hotel ne da aka bude aka daukesu aikin Dan haka wainda basajin turanci bangaren restaurant aka ajesu gurin harkar abinci.,

Farko ganin baa bacci kwana akeyi aiki yasa tafarajin zuciyarta tayi sanyi da rayuwar,
Amma ana Bata albashin farko taga irin yawan kudin sai kawai ta tattara kyuya da damuwar komai ta watsar ta zage da aiki gadan gadan.

Kasancewarta mai tsananin kokarin aiki da Amana da ladabi yasa cikin wainda aka daukesu tare watansu biyu aka qara mata matsayi tareda dauketa daga kitchen aka maida bangaren tsafta,
Ma'ana bangaren masu Kai abinci dakunan manyan Idan sunyi odar abinci Dan haka kusan yanzu hutawa takeyi sosai sai anyi odar abinci taje takai.

Gidan dasuke cikin kudinsu na albashi ake Dan tsakura duk wata ana biyan haya Dan haka hankalinta ya kwanta sosai gashi ahakan duk wata take turawa su Inna Yan canji ta hanyar Mai pos din kusada gidan nasu data baro.

Kwanciyar hankali da hutu da Kuma nutsuwar datake samu yasa tafara sauyawa sosai sbd abinci Mai kyau na hotel din sukeci,
Nama da kayan Dadi kala kala haka suke ci dan haka tafara sauyawa sosai,

Mama indo dai ita a bangaren abinci take har lokacin Kuma babu ranar sauyata daga gurin sbd yanda ta iya wata irin lallausan sakwara da Amala,Eba,semo
duka dai kalolin swallow babu Wanda mama Indo Bata qwareba shiyasa saka barta agurin Kuma itama ahakan ba qananun kudi take samuba sbd yanda suke tsananin son aikinta.

Hutu da nutsuwar da kwanciyar hankalin data samu tareda abinci mai kyau yasa tafara sauyawa jikinta yafara budewa da wata irin kiba,

Hasken fatarta daya jima da dafewa saigashi yafara washewa Yana dawowa,

Da farko tayi mamakin hakan Amma ganin rayuwar nutsuwar datake yasa Bata damuba saima Jin dadin hakan datai sbd tasan inshallah yanzu zata iya samun miji tayi aure tunda tayi kyan gani.

Ba laifi cikin qanqanin

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

1 year ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

1 year ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment