Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

BOOKS  4500_
_3 BOOKS : 3500_
_2 BOOKS : 2500_
_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_14_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Farko Inayah tayi mamaki sosai da maganganun Zaid din sbd Bata dauka Yana fada da gaske bane kawai dai yanason daga Mata hankaline sai kawai Bata dauki zancen da wani mahimmanciba tadaiyi mamakin Inda yasamu guts na iya fada Mata hakan.

Shima Zaid din ganin ta watsar da maganar yasan Bata dauka maganan bane Dan haka ya tattara Shima ya watsar Yafara Dan kula tsohuwar budurwarsa data maqale tanason su dawo tare dama friend din Sufian ce.


Tunda dad din yazo yasamu Abbi sukai magana da yanda sukai da me ake ciki babu abinda Abbi ya sanar masu daga ita har umma yaganah,

Maganar dakatar da zuwan Zaid ma shine da kansa ya kirasa ya sanar Masa Dan haka Inayah Bata saniba Shikuwa Zaid din tuni hakan yasa ya sake watsar da zancen Inayah yanzu yakama Amal suka bude shafin soyayya duk da ba wani jinta yakeba Inayah ce kawai a ransa har koda yaushe.

Illar Abokai masu aikita barna Dana Amal yasa tuni yafara samun cikakkiyar nutsuwar samun mace atareda Amal dan haka yanzu yasamu nutsuwa sosai hankali kwance yake jin dadinsa da Amal.

Ahankali jin Dadi da samun cikakkiyar macen data iya biya Masa buqatarsa yasa ya daina kiran Inayah gabaki daya idanma ta Kira komai basayi yanzu sai hayaniyar fada sbd haryanzu fushi yakeyi akan yanda ta zabi hakura dashi har sai bayan shekara.

Itama haushi takeji na yanda ya daina zuwa gurinta kwata kwata wayarma Neman gagarsu takeyi.

Tun tana jin haushi hankalinta haryazo ya tashi sosai tafara shiga damuwa.

Umma yaganah ma saida tashiga damuwar yanda Inayar kwana biyu ta daga hankalinta akan matsalarta da Zaid,ta kirasa da kanta Dan taji menene matsalar suketa fada yanzu koda yaushe Amma Bai dagaba Kuma daga baya Bai biyo kiranba Dan haka itama tasan da wuya idan ba babbar matsala bace gashi basuda ikon fadawa Abbi kokuma tambayarsa.

Ahakan har sukai exams suka kammala suka samu qaramin break na sati biyu sbd daga wannan sai final exams Dinsu.

Karatu takeyi sosai kaman zata rasa Zaid takeji idan Bata maida hankali sosai tayi karatun taci exams ta wuce gurinba,

Har wata irin Rama ta ringa yi sbd tsananin karatu da Kuma matsalarta da Zaid sbd yanzu kam sosai tasan suna gab da rabuwa tunda sukanyi sati ma basuyi wayaba,

Ta bangare daya Abbinta ya maida hankali sosai Shima akanta sbd ganin tayi karatu sosai duk da yasan kanta na ja sosai akan karatu Amma dai wannan kaman wani burinsa ne akan yarsa.

Ta bangare daya Shima ramarta da damuwarta tafara sakashi damuwa Sam Baya buqatan abinda zai sakata muguwar damuwa irin hakan,

Dan haka da kansa ya janye maganar Hana zuwan Zaid yabasa damar zuwa akai akai gurinta yanzu tunda ana gab da Gama karatun.

Sosai Inayah taji dadin ganin Zaid ranarda yazo Dan dama sbd dokar abbin yasa ya janye kansa daga gareta dakuma Amal data Gama kamesa tako Ina yanzu.

Ranar da farin ciki ta wuni Wanda yabawa Abbinta mamaki duk da yanzu bayajin Zaid din da yarsa sbd yana lure da kaman ya sauya sabon halaye, barinsa yayi kawai yaga yanda Al'amarin zai kasance.

Yanzu hankalin Inayah ya kwanta tunda Zaid yadawo Mata yanda suke farko Amma har lokacin Batasan da wata Amal a rayuwarsa ba,

Shima yanzu sosai yake jin Inayar tunda sun kusa dai cika sharuddan mahaifinta suyi auren Dan haka saiya fara tsananin kiyaye alaqarsa da Amal sbd koda tsautsayi bayason Inayah tasan da Amal bare mahaifinta dazai iya hadawa harshi hai dad dinsa yayi dealing Dinsu idan suka tarwatsa rayuwar 'yarsa.


*****Maganar aure dole Abbinta ya aminta da ita aka tsaida lokacin auren wata biyar masu zuwa Wanda sukai daidai da kammala karatunta da wata daya kenan,
Dan haka tuni aka fara shirye shiryen Auren ta bangaren mata kenan suda sukeda hidimar yi ta shagalin biki.

Inayah tunda aka tsaida lokacin auren ta Zaid daga ita har Zaid din suke cikin wani irin tsananin farin ciki,

Iyayensama kaman zasu janyo lokacin sukeje musamman dad dinsa,

Umma yaganah ma kam fadar farin cikin datake kwana dashi tana tashi dashi bazai yiyuba,

Babban burinta a dah shine ganin ranarda MAJEED zaiyi aure ya ajiye mace da sunan matarsa kafin Auren Inayah yazo daga baya saigashi na Inayah dinne a gaba duk da hakan tana farin ciki,
Bare tunda auren Inayah Yana hanya Inshallah Shima nasa Yana hanya din.

A Nigeria Abbinta keson sukoma ayi auren acan kafin sudawo daga baya,
Aikuwa Murna kan Murna agurin Umma yaganah sbd tanason zuwa Nigeria dama sbd sada zumunta da jama'ar arziki da aka zazzauna tare acan baya.


Neesah da Inayah duk da irin yanda suka maida hankali sosai akan karatun yanzu hakan Bai hanasu tsananin Shirin gaske ba akan yawon shoppings da gyaran jiki duk da Abbin baisan tana zuwaba tunda ya hanata zuwa spa's.

Amal kuwa daga hankalinta tayi akan auren Zaid Dan haka tafara kokarin tona asirin alaqarta da Zaid gurin Inayah Amma tana shakka sosai na mahaifin Inayah sbd ita batama da kowa qasar karatu kawai takeyi da watsewarta Dan haka take shakkar taba Inayah,Amma badan mahaifin Inayar ba da tuni ta yaga Mata rigar mutunci tasa anyi Mata kaca kaca da ita.


****Saura wata daya sufara exams Neesah ta aje Inayah gida da mota ta nufo hanyar gidansu taci Karo da motar Zaid a gabanta tareda Amal zaune gaban motar suna wani irin tuqi a hankali.

Sake kallon motar tayi da kyau ta tabbarda motar Zaid ce Kuma da mace aciki.

Bata kawo tunanin komaiba tayi over taking dinsa ta wuce motarsa tana Masa horn alamar gaisuwa.

Bai lura da motartaba sbd hankalinsa na kan Amal dake Masa wani shegen Wasa Yana dariya.

Amal din taga Neesah Dan haka take sake Matsoda fuskarta tayi kissing bakinsa tana lasar kumatunsa.

Wani shegen burki Neesah taja tana neman gefen hanya ta saukar da motarta sbd kokarin kufce Mata datake.

Kutttt....."tafada cikeda mamaki da faduwar gaba sbd kasa yarda da abinda tagani,

Zaid?da wata macen Kuma?
Har suna irin haka?
Anya kuwa Zaid ne?
Zaid din Inayah da babu wata bayan Inayah agunsa.

"Oh my God, this is unbelievable" tafada zufa na Dan karyo Mata na tashin hankali,

"I can't tell this to Inayah,
Bazata yardaba,Nima nakasa yarda da abinda nagani gskia.

Sosai takejin firgici da tsoron abinda tagani din,

Tun baayi aurenba Zaid ya iya cin amanan Inayah duk yanda take tsananin sonsa da kaunarsa,

Tabawa rayuwar aure datakeson yi Amana da yarda da burirrika
Tun yanzu hakan yafara faruwa to me Zata tadda idan taje gidan nasa?

Inayah nada tsananin zafin kishi na gaske ga zuciyarta nada rauni wlh bazata iya daukan hakan ba,

She is too weak to take this,

Tayaya Zata iya daukan wannan?

Daqyar Neesah ta iya tattara kanta ta tada motar ta nufi hanyar gida jikinta amace Dan Jin take Kamar itace akewa wannan cin amanar tunda aminiyarta akewa,

Ta yanke shawarar bazata fadawa kowaba Amma Zata saka Ido sosai tasan Gaskiar Zaid din tun kafin ayi auren.


Tun daga ranar Neesah tasaka ido sosai akan Zaid da Amal saigashi kuwa dai ta tabbatar da wata irin qazamar soyayya sukeyi Mai zurfi.,

Hankalinta ya tashi sosai saidai Kuma batason fadawa Inayah sbd ga karatu Mai nauyi agabansu ga tsoron halinda Zata shiga,

Gashi Abbi ma ba abun wasaba bare ta fada Masa.

Haka tanaji tana kallo Zaid nata yaudarar mata Inayah.

Ana cikin hakan suka fara exams dole ta tattarasa ta watsar suka maida hankali akan karatunsu.


Suna cikin exams Dr farhat taci gaba da Taya umma yaganah shirye shiryen biki da tafiyarsu Nigeria wadda zasuyi bayan Gama exams din Inayah.

Ta dayan bangaren Zaid yakasa rabuwa da Amal duk da kwata kwata ko Rabin matsayi Inayah aransa Bata kaiba Amma sbd mumunar jarabta yakasa rabuwa da ita.



****Ranarda su Inayah suka kammala jarabawa kwana sukayi farin ciki itada Abbinta da umma yaganah.

Kwana biyu tsakani suka wuce umrah,
Sati biyu acan suka dawo aka fara shirye shiryen zuwansu Nigeria sbd Saura sati uku bikin.

Koda suka dawo dayake tareda Neesah da Abbin da umma sukeje,

Tanata kiran Zaid Bata samu gashi baisan sun isoba,

Batada karyar dazataiwa Abbi ta fita ranar Dan haka tace itace Zata Kai Neesah gida.

Kai tsaye yace umma yaganah ce Zata kaita gida sbd yiwa iyayenta godia.

Bata damuba tace bakomai sbd tasan umma bazata hanata biyawa gidan Zaid dinba.

Sai yamma suka fito shiye take cikin riga da wando na Nike black da sneakers farare ta saka face mask da hular rigar kayan sbd batason kowa ya ganeta lokacinda Zata shiga gidan Zaid Dan kada afadawa Abbinta da Kaman duk motsinta Yana sane dashi.

Da farko umma yaganah qin yarda tayi abiya din suka ringa rokonta,

Musamman Neesah datakeson abiya din ko Allah zaisa yau kowa yasan mummunan rayuwar dayakeyi tun baayi aurenba Allah yaraba Inayah da rayuwar damuwa.

Cikin saa kuwa suna Isa motar Zaid na gida Dan haka Kai tsaye suka shiga itada Neesah Banda umma data zauna a mota.

Door bell suka ringa dannawa babu Wanda yazo ya bude Dan haka Inayah datasan password din kofar ta saka kawai ta bude suka shiga.

Da gudunta ta nufa kofar dakinsa tana Kiran sunansa.

Bakin kofar dakin ta tsaya batareda tashigaba sbd sanin Bai kamata tafara Kiran sunansa ahankali cikin shagwaba da soyayya.

Yana kitchen tareda Amal suna cin pizza dasukai order yagama ci yaje gidansu Inayah sbd yasan sun jima da isowa yanzu.

Neesah ce ta ringa Jin dariyarsu ta nufa kofar ta leqa ahankali aikuwa tagansu suna cin pizza kowanne babu wani kayan kirki jikinsu sai wasanni sukeyi hannuwansa na cikin fingilalliyar rigar baccin jikinta dake nuni da tun safe suna daki suna Abu daya.

Da sauri Neesah ta Isa kofar bedroom dinsa da Inayah take ta kamo hannunta tana cewa"

Yana kitchen.

Ha yar kitchen din suka nufa Inayah na Kiran sunansa da cewa"

Baby,
Baby where are you?
Bab.......

Cak ta tsaya kafin ta qarasa kitchen din ganin abinda takasa ganewa.

Da gudu ta qaraso cikin gurin tana kallon yanda yake kokarin ture Amal daga jikinsa hankali tashe Yana cewa"

Baby?
Me kikeyi anan?
Abbinki yasan kinzo kuwa?
Bakya tsoron yasan kin zo?

Amal ya kalla da sauri Yana cewa"

Inayah ba abinda kike tunani bane ki.....

Tsayawa gabansa Neesah tayi Rai abace tace"

Karma kayi wahalar bayanin komai,
Ni nasan wannan qazamar rayuwar da kakeyi bada sanin kowaba tuntuni yanzu Kuma Inayah tagani da idonta.

Jan hannun Inayah tayi suka juya suka fice.

Har mota Inayah kasa cewa komai tayi sbd cak kanta da tunaninta ya tsaya.

Umma yaganah sai tambayar abinda yafaru takeyi sunqi cewa komai sai ajiyar zuciya da Inayah ke jerowa cikin fita hayyaci.

Suna tsayuwa kofar gidansu Neesah
Sai alokacin Inayah ta juyo ta kalli Neesah murya a sarke tace"

Neesah Zaid nagani da mace right?

Numfashi Neesah tasake tareda kallon umma data gwalo Ido ta gyada Kai.

Wait wait wait,
Ina nufin mace Naga zaid da ita cikin yanayi na aikata wani Abu fa?

Kai tsaye tace"

Yes Inayah zai kika gani Kuma ba qarya idonki yamikiba,
Gskia ne,Kuma ba tun yanzu bane sun jima atare,
Zaid ba yanda kikasansaba yake yanzu.

Numfashinta taji Yana Neman hardewa Dan haka da sauri umma da itama tashiga shock ta fincike Mata mask din hancinta tana Kiran sunanta.
##MAMUH#
#INAYAH
#MAJEEDs LOVE




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_15_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Cikin damuwa umma yaganah tace"

Ga irinta Nan ai Nima Dana biyewa roqonku aka biyo din Kuma wlh sbd MAJEED yasan zaku biyo din yasa yace nice zan maida Neesan gida gashi nawa zuwanma baiyi amfanin abinda yaso yayi ba,

Yanzu Ina amfanin wannan mugun ji da mugun ganin ana zaune kalau buki saura kwanaki,
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun.

ACn motar suka qara umma na Kiran sunan Inayah cikin Dan sauti Mai tashi tace"

Karki saka wannan aranki kijawa mahaifinki Inayah tunda zuwan qaddarane koma yayane,

Kuma dai Ni nakasa yarda da abinda kuke cewan kungani,Zaid dinne Kuma yake Neman Mata?
Kun kuwa tabbata?
Idan har bawai kamasu kukayi tirmi da tabaryaba karku zartar da hukunci sbd ana maganar Zina ne anan fa....

Cikin wani irin tsananin fushi da kukan gaske da tunda take arayuwarta Bata taba yinsaba sai yau akan wani namiji
Tace"

Umma yaganah kiyi shiru kawai sbd bakisan abinda idanuwana suka ganiba,
Wallahi tallahi tare yake da wannan dai dana gansu ayau nasan tare suke akwai abinda suke aikatawa,
Hannunsa fa acikin rigarta Yana matsa nonuwarta Kuma......

A kidime umman ta katseta da cewa"

Innalillahi Inayah banason ji daina fada,
Kuma karma nakuma Jin wannan zancen banzan,
kema daina fadan wannan maganar a bakinki batada dadin ji kadama koda tsautsayi mubari MAJEED yasan mun biya gidansa da wannan mugun labarin.

Da zallar mamaki Neesah ke kallonta tace"

Umma yaganah idan Abbi baijiba shiru zaayi Inayah ta aura mazinaci?

Kinga Neesah ku Yara ne,
Wannan bawai maganace da Kai tsaye zaa fito afada cewa zaid ga abinda yakeyiba sbd akwai maganar manya ta aure acikin lamarin Dan haka komai a sannu zaa bisa,
Kuma idan ance arusa auren atake sbd haka shi Wanda Zata samu agaba ansan nasa boyayyan halin?

Da yawa akwai mazinata a mazan aure Amma baka taba sani,
Itama Dan Allah yayi Zata sanine kafin Auren,
Idan anzauna an duba komai a tsare zaa iya samun mafitar komai a natse.,
Muje na rakaki ciki na gaisa da haj Salma da dadynki idan Yana gidan nazo mu wuce kafin qawarki ta some Mana anan asirinmu yagama tonuwa.

Daqyar Inayah ta iya danne halinda take ciki suka shiga su dukansu aka ringa Murna da musu sannu da zuwa.

Momyn Neesah murnar ganinsu takeyi sosai itada qanwarta dadyn Neesah din musamman ganin dattijuwa umma yaganah da kanta a gidan Dan kallon mahaifiyar MAJEED suke Mata.

Angama gaishe gaishe da firar dawowarsu lafiya dama firar bikin Inayah dake gabansu Kuma yanzu,

Sai kame kame umman da Neesah keyi sbd kowannensu har lokacin cikin shock din abinda yafaru suke da Inayah dasuketa Allah Allah agama atafi gida kafin ta ringa rusa musu kuka agurin Dan Zata iya gashi Allah yasa tasamu jarumtar dannewa din kada su momy sugane.

Basu wani jimaba suka fito sbd cewar datayi kanta na ciwo su koma gida.

Har mota dukkaninsu suka rakosu har momy.

Shahada kawai umma yaganah tayi tabari Inayah taja motar suka nufo hanyar gida.

Suna fitowa gidansu Neesah hawayen datake riqewa suka fara gangaro Mata zuciyarta na wani irin tafasa.

Tunda take rayuwarta Bata taba Jin 'daci da qunci ba irin yau din,

Dukkanin rayuwarta quncinta biyu ne zuwa uku,
'Bacin ran mahaifinta,
Rashin uwa,
Saikuma 'yar damuwar yau da gobe da bazaa rasaba Amma ita ko zafin rashi da talauci Bata saniba tunda koda mahaifinta yayi talauci da gwagwarmayar rayuwa batada wayo Tana qarama Kuma ko a wancan lokacin baitaba barinta ta nema Abu ta rasaba.

Sbd tana tuqi yasa umma yaganah batai Mata maganaba Dan tasan tana buqatan kukan ko zataji sassauci shiyasa taja bakinta tayi shiru tana kallo Inayan na wani irin gudu dasu.

Zuciyan Inayah wani 'daci da zafi take Mata Mai tsanani,
Tayaya Zaid har zai iya taba jikin wata macen ba itaba?
Tayaya zaid zai iya hakan?

Tsigar jikintane yafara tashi sbd tsananin qyanqyami da baqin cikin abin,

Meyasa bazai kasa hakurin sauran kwanakin daya rage aurensuba zaije ya iya hada jiki da wata,
Harma ya iya hada shimfida da ita,

Kuka sosai takeyi har suka Isa gidan,

Parking din motar ma a juye tayisa ta fito tayi ciki da gudu tana share hawayenta Dan batasaniba ko Abbinta na gida.

Dakinta ta nufa ta zauna kan sofa tana kokarin tsaida hawayenta da hannuwanta dake tawa.,

Umma yaganah ce tashigo dakin tareda rufe kofar jikinta a mace ta qaraso gurin Inayan ta zauna gefenta tareda diban tissue dake gaban mirror tafara sharewa Inayah hawayen cikin tsananin kulawa da nutsuwa Dan Inayah ta fahimta abinda Zata fada Mata din,

"Inayah karki daga hankalinki kishiga tashin hankali akan wannan mugun tsautsayin,
Kinga na farko mahaifinki shine babban fargabar yasan kinje gidan saurayi,
Na biyu nima nasan ba qaramin qona ransa zanyiba idan yaji na biye Miki nabada damar zuwan gidan nasa,

Hakama Kinga abinda kika gani bawai kinada tabbacin ya aikata wani mummunan abin bane duk da ba mutunci ko kamun kan dazaisa yakai mace gidansa harma ki samesu a ayanda Bai kamataba,
Dan hakan kiyi hkr karki daga hankalinki da kaina Nima zan fadawa Abbinki idan har ta tabbata Zaid din yagama 'bata rayuwarsa da neme nemen matan banza,
Sbd yanzu MAJEED najin wannan zancen kinsan kome zai faru bazai basu aurenba kuma so gwara afara tabbatarwa Kuma ko an tabbatar akwai tsautsayi akwai qaddara kilan sune suka ritsa dashi kawai bawai halinsa bane,
Kinga idan yayi alqawarin gyarawa ai shikenan ba komai bane sai muyita adduar Allah yasa ya gane din ya daina.

Kasa magana tayi sai kuka datake faman rusawa umman tana share Mata hawaye.

Daqyar umma yaganah ta rarrasheta sukabar maganar akan Abbinta bazaijiba tukuna sai sun tabbarda abin bamai gyaruwa bane Dan kuwa Inayah tayi rantsuwar bazata auresaba matuqar tagane takuma tabbatarda Neman matan yake da gaske Kuma Yana kwanciya dasu sbd ta wani fannin ta gado halin mahaifinta sosai da sosai gurin tsananin qyanqyamin gaske shiyasa take ganin bazata iya hada miji da wata macenba.

Kashe wayarta tayi sbd yanda Zaid din keta faman Kira Kuma batajin Zata iya daga wayarsa shiyasa ta kashe duk da Bata kashe wayarta duk tsanani sbd Abbinta kada yakira yaji kashe Sam ya hanata kashe waya bayan shi Yana shigowa gida yake kashe wayoyinsa sai Kuma idan zai fita kokuma ya saka silent sbd rashin son damuwa.

Da daddare cikin qarfin hali umma yaganah ta sakata fitowa cin abinci suka Dan ringa kamewa sbd kada Abbin yagane.

Kallo daya yayiwa Inayah lokacinda take qarasowa gurin cin abincin sanye cikin Riga da wandon Prada farare masu kauri sosai kaman na sanyi da qaramar hula gabaki daya saita fito kaman qaramar baby.

Yanayin shigarta da fuskarta datake fresh ba komai da alama wanka tayi Kuma Bata shafa komaiba sai turarenta da qamshinsa ke tashi ahankali.

Shine yafi kowa sanin Inayah sbd shine mahaifinta Dan haka fuskarta da yanayin shigarta ya bayyanar Masa da 'yarsa na cikin damuwa...

Sake kallon yanayinta yayi yanda take cin abinci jikinta amatuqar sanyaye bakuma wai Dan tana jin yunwa ko dadin abincin ba,
Cusawa kawai takeyi.

Gun umma yaganah ya 'dan maida kallonsa yaga yanda ita Kuma take Dan hada kokarin share guminta akai akai duk da tsananin sanyin Aircon da babu Inda babusa a cikin gidan...

Maida kallonsa yayi a natse kan Inayah da hankalinta Baya kan kowa saina abincin datake ci Shima bawai hankalinta na kan abincin bane.

Jin yayi kwata kwata abincin dayake gabansa fita ransa sbd yasan akwai abinda suke boye Masa Dan daga umma yaganah har Inayar babu Wanda Bai San halayensa ciki da wajeba,hakama kallo daya yake musu kowannensu ya gane halinda suke ciki sbd Sam Baya Wasa da kulawa dakuma tarbiyar gidansa Wanda umma yaganah ta jima da Zama cikin ahalinsa Dan haka itama duk da tana matsayin uwa shine Mai lurarda ita lokuta da dama.

Ruwan sanyi da aka Dan zubawa lemon ya dauka ahankali yakai bakinsa yasha tareda ajiyewa ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe yabar dining din.

Daga umma yaganah har Inayah babu Wanda yayi Magana daya miqe din sbd hankalinsu Baya Kai Kuma hakan yasake tabbatar Masa da zarginsa akansu na akwai abinda suke boyewa basason ya sanin Dan Bai taba miqewa daga dining batareda dayansu ya ringa maimaita Masa ko ya qoshi da abincinba Dan sun San rashin zamansa yasa Baya wani samun damar cin abinci yanda ya kamata shiyasa daya miqe zasu fara tambayar ya koshi kokuwa ya zauna yaqara ci.

Yana barin dining din Umma yaganah ta kalli Inayah cikin qosawa tace"

Inayah kinason sakawa Abbinki tunanin akwai wata matsalar ne?

Ba nace Miki da kaina zan sanar Masa ba idan aka bada lokaci akasan Gaskiar lamarin¿

Kallon umman tayi tana jin damuwa sosai,
Ita sbd batada uwa batama San uwartaba shiyasa Abbinta takejin idan Abu ya sameta Bata sanar masaba kaman zuciyarta Zata buga.

Ahankali ta gyada Kai tana cewa"

Abbi fa kinsani kwana biyu cikakki bazamuyiba muna wannan boyon zai gano mu.

"Nasani shiyasa nakeson kiyi kokarin cire damuwar komai aranki.

Bata iya cewa komaiba ta miqe tana daukan tissue tace"

Zan kwanta da wuri umma,
Goodnight.

Daqyar ta iya tattara kanta ta nutsu yanda Abbinta bazai gano kamaiba ta qarasa palonsa cikin sanyi da shagwaba ta nuna Masa bacci takeji Zata kwanta da wuri tai Masa goodnight Shima ta fice.

Bai bi bayanta da kalloba sbd Baya buqatan qari fahimta yasan for sure akwai wani abu,

Idan irin hakan tafaru bayace musu komai sharesu yake sbd cikin kwana biyu yasan zai Gama sanin meke faruwa.

Tana barin palon Abbi taji idanuwanta na cikowa da hawayen rashin sanar dashi damuwarta sbd Abbinta shine maganin kowacce damuwarta Wanda Allah ne ya tsaya musu duka akan hakan.
#MAMUH#
#LOVE#
#MARRIAGE


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/16, 8:20 PM] Mariyamah: *16*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Tana Isa bedroom dinta ta kwanta ko kallon Inda wayarta take bataiba.

Bata wani qin samun bacci ba,
Sosai tayi bacci kaman yanda ta saba saidai tana farkawa damuwar dake dabaibaye cikin ranta ta dawo Mata sabuwa fil harma wani 'dacin maqoshi takeji sbd tsananin damuwa da fargabar abinda zaije yadawo,

Tanajin wani irin tsananin bacin Rai da zafin abinda Zaid din yayi Mata da har takejin bazata taba iya mantawaba Amma ta wani bangaren tana cikin tsananin fargaba da tsoron rasashi sbd girman son datake Masa.

Tayi lattin sallah Dan haka alwala tafara yowa tazo tayi sallar asuba tukuna tayi adhkar.

Tana gamawa ta koma kan gadonta tashige bargo tana son komawa bacci.

Rufe idanuwanta tayi tana sake gyara kwanciyarta Amma takasa Jin dadin kwanciyar,

Sake juyawa tayi dayan banagren tana Dan yamutsa fuska cikin yanayi na qosawa.

Jin duk batajin dadin kwanciyar yasata yaye bargon datake rufe dashi tareda tashi zaune ta kalli wayarta dake kan bedside, takuma dauke Kai tana Dan sake yamutsa fuska.

Mintuna biyu ahakan kafin ta qarasa yaye bargon tayi gefe dashi tareda ziro qafafuwanta qasa tana daukar wayarta ta kunna ko duba wayar bataiba daga kunnawan darai ta ajiyeta Nan Inda ta dauka ta miqe tsaye tareda nufar Inda tarin jerin takalmanta suke jere Kaya guda,kusan babu designer shoe brand dinda batada masu zallar tsada.

Time ta kalla taga yanzuma 6:30 tayi Dan haka tasan har yanxu dadynta Yana geam,

Riga da wandon Nike ta saka black da Triple S Balenciaga sneakers farare ta fito ta nufi gym Dinsu dake gidan Wanda saika ratsa palon daya raba palonsu Dana Abbinta zaka Isa watadaccen gym din Mai girma da tsari.

Tana Isa knocking daya tayi ta tura kofar da kusan tafi karfinta sbd qarfin kifar tashiga tana gyara qaramar Vandanar dake kanta.

Sanye yake da black Lululemon wears na exercise,
Bench press yakeyi da nannauyan qarfe a hannayensa Yana dagawa da dawowa,

Shigowarta baisa ya dakataba Kuma Bai waiwayo ya kalli Wanda ta shigoba Dan yasan babu Mai shigowa Nan din kaf idan ba 'yarsaba.,

Cikin kauna da kulawa ta qaraso gurinsa tana cewa"

Good morning Abbi"

A natse ya qarasa abinda yakeyi ya ajiye qarfen tareda tashi zaune wasu qananun zufa abinda ya Gama suna gangara kan lafiyayyar fresh fatarsa ya kalleta lokacinda take daukan ruwa tana basa takuma cewa"

Abbi ka tashi lfy?

Idonta yafara kalla baiga alamar rashin bacci atareda itaba Dan haka Kai tsaye cikin nutsuwa da kulawa yace"

Morning Inayah,
Lfy kalau alhmdllh,
Me zakiyi da gymin yanzu?
kinason ki rage keda kike amarya?
Ko Kin manta kin daina zumudin auren ne tun yanzu?" ya qarasa cikin yanayi na Wasa da 'yar tasa tilo.

'yar qaramar dariya tayi tana hawa kan leg press machine tafara ahankali tana cewa"

Abbi naji banason auren Kuma yanzu
Banason tafiya nabar gida,
Abbi kullum zanyi missing naka,
Gskia Zaid zai ajeni a Inda zanna ganinka.

Murmushi kawai yasake ahankali Yana goge qananun zufansa da wata farar towel qarama yace"

Zaki Saba ahankali musamman idan kika Zama uwa,
And kafin can ma you will be busy with your work bazaki samu lokacin tunanin kewan gidaba.

Abbi duk da hakan nasan kullum sainayi kewanka,Dan Allah Abbi kace musu anan zasu ajiyeni.

Girgiza Mata Kai yayi Yana murmushin wautarta da har take cewa ta girma yanzu idan Yana Mata fadan wani abun,

Haryanzu jinjira ce shi agabansa Dan ko wannan auren Dan kawai ta nace tanaso ne yanzu yasa zaiyi Mata Amma tabbas da saita sake wayo da girma sosai
Aqalla saita fara aiki tasan ciwon kanta Dana rayuwama Dan kuwa haryanzu Batasan komai na rayuwaba,
Babu abinda tasani daga mahaifinta sai mahaifinta tukuna sauran abubuwan.

Tare suka qarasa gymin din suka fito itace mai surutu Yana saurarenta hankali kwance daga shi har ita skin Dinsu glowing kawai suke gasa ta tsantsar hutu da wadata kasancewar shi rigarsa armless sai dogon wando,
Itama rigarta qaramin hannu me da ita sai dogon wando.

Kowannensu hanyar dakinsa ya nufa,
Wanka tafara tubewa tayo ta fito kenan wayarta tahau ringing ta qarasa tana dubawa

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

1 year ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

1 year ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment