Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanuwanta tayi ahankali tana Jin nauyin Kirjin nata na tsananta
Ta miqe tsaye ahankali tareda aje jaririyarta a gefe ta matsa gurin inna dake qudundune gefe tana Nishin azababben zazzabi takai hannu ta tada ita tareda Kiran sunanta ahankali cikin sanyi tace"

Inna ki tashi Allah ya karbi ran mama...

Wani mugun yunquri Inna tayi tana tashi zaune idanuwanta a waje ta kalli inda mamar take tana qara hasken fitilarta tace"

Aishatu ta rasu kikace hadiza?

Yanzu nabarta akwance fa tana numfashi.

Miqewa tsaye tayi ta nufi maman hankali tashe tana cewa"

Ya akai kikasan ta rasu ne tunda ba ganewa zakiyiba.

Gaban gawar maman ta tsaya tana Kiran sunanta muryarta na rawa cikin firgici.

Data tabbatarda Aishatun ta rasu ficewa tayi daga dakin ta zauna tsakar gida tana rusa wani irin kuka Mai rauni.

Tun tanada shekara goma Sha uku Malam ya aurota daga qauyensu kasancewarta marainiya itada qanwarta Indo yazo ya kawosu Mama lokacin itama batafi shekara goma Sha biyarba ya hadasu suka zauna lafiya harya aurar da Indo itama.

Lafiya kalau sukai rayuwa da mama tamkar yaya da qanwa haka suka zauna harsukai wayo mamar ta hayayyafa su kabiru har manyanci da tsufa yakamasu suna zaune lafiya,

Basu qara kaunar juna na mutunta junaba saida malam ya rasu ya barsu
Ita Inna Batada kowa sai mama da 'yayan mamar da itace tayi renon kowannensu harya girma.

Yau aishatu ta tafi tabarta da tsananin kewa da kadaici adaidai lokacinda 'yayanta suke tsaka da rikicin da zai rabasu har abada Idan ba Allah ne ya kawo dauki ba.

Koda aka fito sallar asuba tuni su Yaya Umar da malam kabiru suka iso sbd Inna ta buga musu da 'yar qaramar wayarsu da hadiza ta siya musu tun kafin zuwanta Lagos wadda da ita take waya dasu.

Hadiza na zaune gefe cikin dakin da jaririyarta a dunqule suka shigo babu Wanda ya kalla inda take sukaiwa gawar mahaifiyarsu Addua suka fice Dan fara shirye shiryen jana'izarta da sauransu.

Jaririyarta data Kira da sunan AYSHATUH daidai bayan rasuwar mahaifiyarta sai baccinta takeyi sanyeda kayan sanyi farare tas data zakulo daga kayanta data Bari Nan gida tun kafin tafiyarta,
Kayan tun na Abdul ne Dan haka sun Mata yawa sosai amma tunda babu wani kayan haka ta Sanya Mata su.

Jamaar anguwa da koina sunji labarin rasuwar Mama Dan haka mutane sukaita shigowa cikeda alhini.

Tana dakin itadai Bata fitoba da jaririyarta sbd mutane zasu iya zunde duk da rasuwar da akai mata tasani

Dan haka ta kame kanta a daki Bata fitoba har akaiwa mamar wanka da sitira ta matso tayi Mata Addua aka
Dauketa aka tafi da ita.

Duk yanda taso kuka takasa zuciyarta ta bushe ta kafe da tsagwaron qunci da baqin ciki.

Saida Yan gaisuwa suka rage tana daki tafito taje tayi wanka da tafasasshen ruwan da Inna ta Dora Mata tana gurin wankan jaririyarta tayita kuka
Nan take Yan zaman gaisuwar suka fara yi da ita.

Haka tafito bandaki Takoma daki Bata Kuma fitowaba,
Wankanba itace tayiwa jaririyar da kanta sbd inna na cikin Yan gaisuwa.

Har dare Bata fitoba tana daki
Saidai taci abinci data fidda kudi tabawa innar aka siyo musu sukaci da daddare.

Washe gari take anguwa da jamaa suka dauka cewar haihuwar cikin shegen datai shine ya kashe mama da baqin ciki
Dan haka Take masifar gidan takuma tashi da daddare harta kwanta su malam kabiru suka shiga shida Yaya Umar sukace wlh saita bar gidan da 'yarta bazata rena 'yar datai sanadin mutuwar mahaifiyarsuba adakin mahaifiyar tasu.

Tunda mama ta rasu zuciyarta ta kafe Dan haka ta tashi ta hau tattara kayanta.

Kallonta Inna tayi tana cewa

"Ina Zaki ki barni hadiza?

Wasu siraren hawayen tsananin tausayin Inna ne suka gangaro Mata.

Inna abar tausayice tako Ina sbd barinta tamkar watsar da itane ga duniya Dan kuwa su Yaya Umar Basu tallafi mahaifiyarsu data kawosu duniyaba tanada Rai tayaya zasu iya tallafar rayuwar Inna da batada kowa batada komai...

To Amma ya zatai tunda ankoreta ita kanta,
Kuma ita kanta zataso tafiyar sbd yanda ake zundenta da qyamatarta da yarta tareda jifanta da alkaba'i daban daban akan itace tayi sanadin mutuwar mahaifiyarta.

Tana kuka ta tattara kayanta tabar gidan cikeda baqin ciki da quncin Rashin ganinta Abdul daya koma hannun hajiyarsu Salisu sbd jinyar da mama keyi Inna Batada lokacin kulawa dashi.

Inna kam itama kukanta daukewa yayi bayan tafiyar hadizar da sunaji suna gani su malam Umar ana gaman zaman gaisuwa ya Roshe dakin mama ya hade da wanda yafara ginawa cikin gidan ya fake da sunan zai kawowa Inna abokiyar zamane sbd kadaici.

Barin Hadiza gida ya rusa rayuwar Inna da ita kanta hadizar wadda batasan Ina ta nufaba.
ALLAH YA ZAMA GATAN MARAYA A DUK INDA YAKE..AMIN

**************
_March 2002_
_7:26am_

Kokarin saka Mata pink safa a qananun qafafunta yakeyi Yana dan sake waiwayawa yana kallon wajen dakin nasu dan duba yanayin garin dakeda hadari sosai Wanda tun bayan sallar asuba yaketa haduwa.

Ganin yanda duk tabi ta lafe masa tamkar Mara lfy yasashi dagowa ya kalli kyakkawar qaramar fuskarta dake kallonsa da idanuwanta dako yaushe zai kaita makarantar raino sai tayi wannna qyuyar wadda tun batai wayo hakaba takeda ita.

Batasan kowaba bayan mahaifin nata da a duniya batada kowa bayanshi Kuma Bata yarda da kowa sai shi din  sai uwar renonta yagana wadda take kira da Ummey.

Cikin idanuwanta dasuka Dan Yi Kaman zatai hawaye ya kalla ya saki ajiyar zuciya ahankali Yana janyota jikinsa cikin lallausan muryarsa me zallan nutsuwa ya furta

_"INAYA.._

Hawayene suka fara gangaro Mata ta girgiza kai ahankali cikin Rashin budewar harshenta sosai tace"

_ABBI..._

cikin kulawa ya hanata fadar abinda yasan rigimace kawai zatayi sbd batason zuwa
Kuma ya saba da hakan tunda yafara kaita kullum saitai masa wannna rigimar.

Share Mata hawayenta yayi tareda miqewa tsaye ya dauki Yar jakar takardar dayake saka Mata robar ruwan pure daya dayake juye Mata a empty robar Coke sai fanke da kosan matar kofar gidansu daake soyawa na siyarwa.

Daukarta yayi ya riqe jakar a dayan hannunsa suka fito ya janyo kofar dakin tareda Sanya padlock dinsa ya rufe kofar dakin nasa ya juya ya nufi hanyar kofar ficewa.

Dukkanin jamaar gidan hayar dasuke gidan kusan kowa yafito Yana hada hadarsa a qatoton tsakar.

Da damarsu dasukaci karo da fitowarsa da mugun kallo suka bisa
Wasu Kuma dai tabe Baki sukai suka dauke Kai Suma.

Maman habiba ce dai da Bata gajiya da cusa kai tana ganinsa ta taso tana washe baki da cewa"

Aa su INAYAN Abbinta ce anfito zaa tafi makaranta?
Zo mu gaisa kinji?

Hannu ta miqa Dan karbanta
Inayar ta sake maqalewa Mahaifinta tana lafewa tareda rintse ido batamason kallon maman habiba din.

Yar dariya tasake tana cewa

"Inaya haryanzu dai qyuya ko?
To adawo lfy.

Amin kawai ya iya bude bakinsa ya furta ahankali kafin ya ra6a maman habiban ya wuce tana bin bayansa da kallo.

Mijintane ya qaraso ta bayanta Yana kallon Wanda takebin da kallo yace"

Zuwaira bazaki daina shiga sha'anin Wannan Mai shegen girman kan da miskilanciba ko?
Sam Dan iskan yaro a naqushe cikin talauci Amma baya ganin girman kowa
Baya daraja kowa
a duniyarsa babu abinda yasani sai wannan aljanar 'yar tasa Mai kama da   'yar Rake,

Kullum Yana tafe Yana kame kansa Kaman dan kwalisar daya sauko daga jirgi.,
Ke Kuma sai naci da shishigi kike masa akan yabaki renon Yar tasa kina samun 'yan kudin da yagana ke samu gurinsa.

Juyowa tayi tana fuskantar mijin nata tace"

Baban habiba laifine Dan na nace masa akan yaban renon Nima naringa samun Yan qananun canjin da yagana ke samu?
Inace Idan nasamu kudin Kai zan rufawa asiri na ringa Dan samun ciyar da yarana tunda Kai zuciyarka ta jima da mutuwa bazaka iya fita kayi ko aikin wahalar dashi yakeyi Dan ya kula da 'yarsa kasamoba...

Cikin masifa Yana jefanta da mugun kallo yace"

Idan zuciyata mutuwa tayi ke taki konewa tayi ko?
Sbd Naga alamar son abin duniyarki Neman yake ya rufe Miki ido yaro Dan qarami Wanda kikai qani dashi Zaki zauna Yana wulaqantaki tunda ko kallonki bantaba ganin yayiba duk wannna shishigin da kike masa akan 'yarsa dako qafarta baya barin ta taka tsakar gidan Nan Kamar akansa aka fara haihuwa
mu duka 'yayanmu ba 'Yaya bane sai tasa 'yar ce kawai 'ya,

Yasan Yana tsananin jinta kamar ransa ubanwa yace ya rabu da uwarta?

Cikin takaici maman habiba tace

"Ina ruwanka da Idan sakin uwarta yayi idanma mutuwa tayi,meye naka?

Bbn habiba ka fita fa idona na rufe kabarni nasamu nacusa kaina a gurin nasa nasamu abinda nakeso.

Inaya dai inshallah sai ka ganni Ina renonta
Ina laifin dari Biyar duk sati?wlh zanyi kokari nasamu tunda Kai din ba nemowa kakeyiba sai shegen gulma da sa ido.

Qaramin tsaki ta sake tana juyawa ta wucewarta tabarsa tsaye Yana binta da hararar mugun rainin datai masa Bata kunyar fada masa magana kowace iri tunda taga ita ke nomowa ta ciyar dashi.

Suna fitowa gida Kai tsaye hanyar titi ya nufa Bai Kuma sauketaba har lokacin sbd karta Bata qafafunta da takarminta da daudar hanya tunda lokacin damuna ne.
Barema koba lokacin damuna bane baya ajeta koyaushe daukarta yakeyi daga cikin gida har inda yake kaita,
Bai cika barin ta fitoba tayi tafiyaba koyaushe daukar 'yarsa yakeyi shiyasa tayi wani irin mugun sabo da abbin nata Bata yarda da kowa saishi Bata iya zama da kowa sai shi,

Wani irin qawa zucin Mahaifinta Allah ya dasa Mata acikin ranta sbd tunda tafara wayo shine halitta mafi soyuwa a zuciya da idanuwanta,

Yagana farkoma data fara wayo qin yarda takeyi yabarta gurinta yaje gurin nema sai ahankali tadan fara sabawa da ita Amma harya dawo daukanta Bata sakewa duk da qananun shekarunta tasan Mahaifinta ta yanda ko sallamarsa taji daga nesa tana gane shine.

Wata qaramar private school ya nufa da ita Kai tsaye dake anguwar.

Yana Isa dayake maigadin makarantar ya sanshi sosai sbd yanda kullum yake zuwa kawo 'yarsa tun tana jinjira har tayi shekaru hudu yanzu.

Da sakewar fuskar ya miqe tsaye Yana cewa"

*_Haji ABDUL-MAJEED_* baban Inaya sannu da qarasowa,

Inayar ya kalla yana dariya yace"

Inayar Abbi sauko to na kaiki gurin yagana.

Kallon Abbin nata tayi tana sake riqesa idanuwanta na kokarin cikowa da hawaye Kaman yanda tasaba kullum aka kawota.

Wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta cikin kulawa tareda zareta daga jikinsa ya miqawa yagana data iso gurinsu tana Kiran sunanta cikin kulawa da kauna.

A natse da kamilalliyar murya yace"

Barka da safiya yagana,
Mun tashi lfy?

Lfy kalau Baban Inaya,
Ya Inaya?antashi lfy?

Alhmdlh" ya furta a taqaice Yana maida kallonsa kan inayar datake kallonsa ya sakar Mata wani taqaitaccen murmushin da duk duniya ita kadaice yakewa murmushi da tattausan lafazi ya furta

"INAYA"
Karkiyi kuka zandawo da wuri inshallah kinji??

Gyada Kai tayi ahankali tana cewa"

Abbi...

Kallon yagana yayi yana ciro 500 ya miqa Mata tareda jakar inayar Yana cewa"

Ku shige zan koma daga Nan.

Juyawa sukai yaganar tayi ciki da ita tana Mata wasa.

200 yaciro ya miqawa Jamilu Mai gadin Shima kafin ya juya ya wuce yanajin yanda yake jero godiya Yana adduar Allah ya Raya musu Inaya.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR
#AYSHATOUH INAYA#
#A MAJEED#
#LOVE/ROMANCE#
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_Mamuhgee 6_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Yagana aiki takeyi a qaramar private school din dake kusa da anguwar tasu amatsayin nanny Mai kula da yara Amma gidansu na haya 'daya da ABDULMAJEED din da yarsa Inayah,

Tun 'yarsa na jaririya shi kadai ke dawainiya da lalurar kulawa da ita sai yaganar wadda Rana daya suka tare gidan hayar itama tazo tareda mijinta da kusan yake kwance ba lafiyayyeba,

Da farko sbd babu yanda zaiyi ne yasa ya amince yaganar datai masa tayin taimaka masa da rainon 'yar tasa da Kai tsaye ya sanar Mata da ya rabu da mahaifiyarta.

Yagana itace tayi rainon Inaya hartai wayo ta girma tasan Mahaifinta har takewa yaganar qyuya akansa shiyasa daga baya Takoma gurin Mahaifinta gabaki daya saidai idan zai fita takaita gurin yaganar Amma daya dawo yake zuwa ya taho da ita
Da haka harsuka koma rayuwarsu su kadai,
a dakinsa yake Mata wanka cikin qatuwar robar wankanta daya siyo
Zata tsaya aciki kokuma ta zauna aciki yayi Mata wankanta tas ya shiryata.

Rayuwarsa da 'yarsa wata irin rayuwace dasuke abarsu su kadai dagashi sai ita sai yagana data Dan shigo ciki,

Duk duniyarsa babu wani buri ko abinda yake gabansa bayan 'yarsa INAYA dayake iyayin komai dabai sabawa shariah ba Dan inganta rayuwarta da Bata wadatacciyar tarbiya da nutsuwar rayuwa,

Bayan INAYA babu wani Abu dayake so da kauna a duniyarsa,
Ita kadaice abinda yakeda,
Ita kadaice Nutsuwarsa da abinda yake kalla yaji qwarin gwiwar cigaba da yaqi da gwagwarmaya Dan inganta rayuwarsu musamman ganin yanda takeda tsananin qawa zucinsa kasancewarsa Mahaifinta Kuma mahaifiyarta.

Kafin tayi wayon datake dashi yanzu yasha wata irin gwagwarmayar wahalalliyar rayuwa Dan samarda abinda zai rainar masa ita.,

Karatun jamia yake alokacin hakama bayada aikin komai face kalolin aikin wahalar daya ringa yi Yana samarda abubuwan da kowane baby zai buqata.

Cikin wani irin tsananin hali yasamu ya kammala karatunsa yayi service yafara zuwa yan ayyukan da zasu ringa taimaka masa Dan lalurarsa data 'yarsa.

Sana'ar gadin wani gida yafarayi tsawon watanni kafin Mai gidan yabar qasar Dole ya nema wata aikin.

Daqyar yakuma samun aikin security a wata private hospital.

Da Wannan aikin yake rayuwa kafin raga baya yasamu aikin wankin mota yana hadawa dashi.

Shekarar inaya uku yafara tunanin aure badan Jin dadinsaba ko Dan yanajin buqatar hakan
Kawai dai zaiyi auren ne Dan ya samarwa 'yarsa kwanciyar hankalin samun mutum ataredasu ko zata sake tayi rayuwa Kamar kowanne yaro,
Amma badan wai ya Samar Mata uwaba,
Har abada shine uba Kuma uwar INAYArsa,
Har abada babu mace data Isa ta zamto uwa ga INAYA,
Shine uwa Kuma uba
Ita kanta Inayah duk da qarancin shekarunta tariga ta Dan San halayen Mahaifinta Dan haka ta daina ambatar sunan mahaifiya tuni sbd Hani da yayi mata da hakan aduk lokacinda bakinta ya furta Mama.

Alokacinda yayi neman auren farko ga 'yar Mai Basu sallah a masallacin anguwar da farko lafiya kalau yafara zuwa fira bawai danma yasan Mai zaiyita fadaba sbd shi miskilin mutum ne shiyasa Bai cika shiga mutaneba,

Iyakacinsa da 'yan anguwar da mutanen gidan hayarsu gaisuwa
Itama gaisuwar sbd sanin mahimmancinta a addini ne.

Da yawa mutanen anguwar da mutanen gidansu na haya kallon me girman Kai da Rashin mutunta mutane suke masa saidai Kuma basa iya fada gaban idanuwansa sbd kwarjinsa da kamewar mutuncin kansa duk da kasancewarsa qaramin matashi.

ABDULMAJEED ABBI kamar yanda yarsa ke kiransa kusan hakan kowa ya sansa,
Wani irin baudadden mutum ne da babu Wanda yake iya gane inda ya dosa,
Meye ne acikin ransa?,
Meye abinda yake tunani?,
Waye shi?

Sam babu Wanda yace yataba ganin koda murmushinsa bare dariyarsa sbd
Bayan 'yarsa babu Wanda ya taba yiwa koda murmushin bare dariyar
Dan haka kusan kowa baya masa dogon shishigi
ciki kuwa harda yan saka idon anguwa da munafukan anguwa kowa ya kama kansa dashi
Zagi dai ne Idan anzauna dattijawan anguwa da Basu San su kama girmansuba sai sunyi saka idon kullum cikin zaginsa sukeyi sunayi dashi a fakaice
Idan yawuce ta gabansu yayi musu sallama ya gaishesu haka zasu ringa washe Baki suna amsawa suna yabonsa da yabon 'yarsa
Daya wuce zasu fara zundensa.

Aurensa da Hafsat yar liman ya lalace ne bayanda aka zuga mahaifin nata da cewar ana zargin zafin zuciyarsa da baqar zuciya kamar kuturu ya ringa azabtarda matarsa da duka da yunwa da wahala da baqin talauci ta gudu ta barsa da jinjirar 'ya bayan ta haihu,

Wasu Kuma suka ringa fadar bada aure ya Haifa yarsaba Dan haka hafsatu renon 'yar gaba da fatiha kawai zata tayi.

Wannan zugar ta lalata maganar aurensa da Hafsat wadda take tsananin sonsa Kuma shi kansa har cikin ransa ya yaba da nutsuwarta yayi shaawar auranta ta zauna da Inayah.

Bayan an hana masa auren hafsa bai cire raiba sbd yanzu sosai yakeda shaawar samarwa Inayah Mai zama da ita Dan haka tunanin yin auren yashigesa sosai bawai Dan har lokacin tunaninsa ya sauya akan Mata bane dakuma Wai Jin Yana son aure ko mace ba,
Sam Mata bayada shaawarsu ko kadan,
Baya Kuma Jin tunaninsa da tsananin yanayinsu zai sauya a zuciyarsa har abada.

Fatima yakuma nema aure a bayan layinsu
bayan ya Dan kwana biyu Yana zuwa fira gunta daganan ya aika Mijin Yagana da Daman shine kawai yake tsananin ganin girmansa da mutuncinsa ya nema masa aurenta.

Kamar yanda tafaru farko hakance takuma faruwa
Har anbasa auren daga baya aka fasa sbd wasu maganganun da aka Kuma kaiwa mahaifanta itama.

Cikin qanqanin lokaci Saida ya nema aure so hudu ana hanasa daga Nan Mata suka Kuma ficewa a Ransa kwata kwata
Musamman sbd yanda aka dauki hanyar aibata masa 'ya sai hakan yakuma tsananta qamewar zuciyarsa akan Mata da mutane,
Bai Kuma shaawar neman kowace macen ba,
Yacire maganar aure daga ransa kwata kwata har abada bayajin zai Kuma kallon kowace mace da sunan wani abu face sunansu na mace.

Daga Wannan lokacin burinsa ya sauyu ya karkata ga ilmantar da 'yarsa yakuma dage ba dare ba Rana da Neman aiki da mafita dama Kuma karatu dayakeson qarawa sbd babban burinsane Dana mahaifinsa tun Yana raye.

Aikin wahalarsa dayakeyi ya matuqar tsananta Dan kuwa bayan security na asibiti da aikin wankin mota yanzu harda sana'ar 'dan acaba yanayi Idan yasamu abokin aikinsa na gurin aikin security ya basa Aron mashin dinsa yayi.

Rayuwa Mai tsanani da wahalar gaske yake gudanarwa,
Baya samun cin abincin dazai kosar da cikinsa,
Duk Rana da dukan ruwan dayake Sha na fafatawar ayyukan wahalar dayake duk na inganta rayuwar Inayah ne,
Ita yake siyawa Yar sitirar sakawa sbd ko sitirar arziki basudashi,
Abincinta da Shanta sune yake iya kokarin samarwa,

So da dama haka yake wuni da yunwa  saidai yasha ruwa da Dan biredi haka ya kwanta amma Inayah baya taba Bari ta nema abinci ko abin buqata ta rasa.
Ahaka yake gudanar da rayuwarsa acikin wani irin tsananin hali.

Yagana tana samun aiki a private school ta primary ya dage yayo wahalarsa yasamu ya saka Inaya duk da kusan shekarunta sunyi qanqanci Amma haka ya sakata sbd a gida yagana ta dena zama aikin take zuwa
Shima gashi yanzu ya sake dagewa da ayyukan wahala iri iri da yawon Neman aiki
Dan haka kullum yake kaita makarantar idan yadawo da wuri ya biya ya daukota Idan baidawoba anan take zama tareda yagana har sai antada Yan primary kowa ya tafi sai sudawo gida ta zauna gurin yagana harya dawo,

Yana dawowa yake tsayawa gurin yagana ya dauketa su shige Bata qara fitowa dakinsu sai washe gari Idan zaije sallah wani lokacin yakan kaita gurin yagana yaje yadawo
Wani lokacin Kuma rufeta yake a dakin yaje yadawo sbd itama Kaman tayi gadon mahaifin nata miskilace ta gaske batason zuwa koina tafison ta zauna gurin Abbin nata.
Musamman sun saba rayuwarsu daga ita sai shi.

*****
Wani tsautsayi daya samesu shine dakinsu daya fara zubar ruwa ta sama Idan ana ruwa yasa tunda damunar ta tsayu sosai yadaina baccin dare,

Zaune yake kwana yayi gadin Inayah tayi bacci sbd gudin yanayi na tsautsayi ko zai riskesu,

Da safe kafin su fita zai kwashe ruwan daya taru a dakin ya goge musu ya gyare dakin dako ledar qasa babu sai Rabin dakin ne kawai keda Leda Shima gurin katifar Inayah sbd kada sanyi ya kamata.

Sauyin aiki akai masa daga security na asibiti zuwa na wani super market.

Ranar farko daya fara aiki a super market din yahadu da wani class mate dinsa a gurin.

Da farko Nuradden ya bayyanarda mamakinsa sosai ganin A MAJEED a matsayin security sbd sanin tsananin ilimi da kyakkawar takardun da MAJEED din yake dasu Dan haka Bai wani boyeba ya bayyanarda mamakinsa tareda yimasa tayin wani aikin wanda yafi Wannan.

Da farko MAJEED yaso kaucewa tayin Amma Nuradden din ya dage tareda tabbar masa ba daga garesa bane taimakon dagaske maikatan ake nema.

Amincewa yayi washe gari ya Isa makekiyar maaikatar kasuwancin mahaifin Nuradden din cikin saa yasamu aikin cashier na daya daga cikin manyan malls dinsu sbd sunason fara jarabta aikinsa kafin su basa wani aikin daya kamata shima sbd Nuradden yayita zuzuta musu ilimi da MAJEED din yakedashi
Dan hkaa ahankali cikin yardar Allah yafara aikinsa na cashier a gurin.

********
Tunda yasamu aikin cashier a taqon mall din rayuwar tafara yi masa sauki shida yarsa harma da yagana da mijin yaganar sbd shi din mutum ne Mai alkhairi musamman ga mutanenda suke tsananin kaunar Inayah,

Duk Mai kaunar Inayah to tabbas matsayinsa a cikin ransa Mai girma ne,
Yanda yake tsananin kaunar 'yarsa Jin yake komai zai iyayiwa duk namijin daya aurawa ita duk ranarda ya cutatar masa da ita,

Wasu lokutan har fargabar yanda zai fara fuskantar bayar da ita aure zuwa wani gurin yake Dan haka alqawarine Mai girma acikin ransa na zai wadatar da ita da ilimin Mai zurfi sbd rayuwa a gidan wani tayi Mata sauki.

Majeed sam Bai damu da abun hannunsaba duk lokacinda yasamu 'yan kudade baya qyashi haka zai kashewa Inaya sauran Kuma ya bawa su yaganah Suma tunda ba laifi suna cikin yanayin rayuwa suma,

Basu taba haihuwaba itada mijinta wanda yake zaune baya iya fita nema sbd yanayin Rashin lafiya dayake ciki na sugar gashi anyanke duka qafafun nasa biyu duk sbd lalurar a keke yake rayuwa,
Dan haka shigowar Inaya da Abbin nata rayuwarsu ba qaramin taimakawa rayuwarsu yakeyiba
Hakannema yasa duk yanda ake gulmar da zindensa babu ruwansu basa shiga sbd sukam majeed kusan shine rufin asirinsu yanzu
Suma qarshe aka ringa binsu da zagin makwadaita Dan sungansa kalar 'yayan masu arziki dama Kuma a wani bangaren da yawansu suna masa kallon Wanda yafito daga zuriar masu hannu da shuni Kuma duk iya gulma da bin diddiqi ankasa sanin asalinsa dakuma inda yafito.


***Ahankali Lokaci yaja sosai har INAYA ta kammala nursery tashiga primary hartayi nisa tana primary 4.

Har lokacin a mall yake aiki saidai ba laifi yasamu qarin girma sosai harya zama assistant manager,

Alhmdlh komai Yana tafiyar musu a daidai dan kuwa babu kalar Jin dadin da Inayah Bata samu gurin mahaifinta sai Wanda baa rasaba daidai gwargwadonsa.

Yanason tashi yabar gidan ya kama haya wani gurin sbd 'yarsa datake girma gashi gidan gidan tarone mutane iri daban daban
amma Kuma sbd rayuwar kadaici da zata iya wargaza Mata walwalarta data fara samu sakamon girma data fara shiyasa Bai tashiba gidan har lokacin Amma zuwa lokacin yanada halin sauyawa din tunda sunfara samun rufin asiri.

Inaya na gaf da kammala primary 4 yasamu hayar wani gidan acan hanyar gurin aikin nasa Dan haka yafara musu shirye shiryen tashi duk da ba wani kayan suke dashiba bayan katifar baccin Inayah sabuwa Mai dakan mutum daya,
Sai qaton bargon dayake shimfidawa qasa ya kwanta sai jakar kayansu da 'yan abubuwan amfanin cin abinci.

yasamu su yagana da maganar tashin nasa dakuma tayin dayakeda niyar yimusu ko Allah zaisa su amince.

A zaune ya samu malam Aminu Mijin yaganar a kofar dakinsu kan tabarma Yana Dan sauraron radio dayake dare yayi Dan har qarfe tara takusa bugawa.

Inayah batai bacciba sbd assignment datake dashi dazai koya Mata Kaman yanda yasaba yimata tishin karatunta na bokon Dana addini kowanne dare kafin tayi bacci Dan haka tareda ita yaqaraso shimfidar malam Aminun Yana riqeda hannunta jikinta sanyeda doguwar rigar bacci Mai kauri da har qasa sai qaramar hular sanyi akanta,
Hatta qafafunta suna sanye cikin safa Mara nauyi sbd Sam baya Wasa da duk abinda zai taba masa lafiyarta shiyasa ko Yaya yaji Alamar sanyi to baya Wasa ko bacci zatai saida socks.

A natse Kaman yanda yake koda yaushe ya zauna gefen tabarmar Yana bude Baki cikin kamilalliyar muryarsa Mai nutsuwa yace"

Barka da dare Malam,
Yaya lafiyar jikin?
Allah yaqaro afuwa da nisan kwana.

Sosai cikin kulawa malam din ya amsa Yana kallon Inayah data zauna gefen mahaifin nata yace"

Inayah yau bakiyi bacci da wuriba Kika biyo Abbin naki cikin sanyin Nan.

Ahankali ta kallesa tana sake Dan guntun murmushinta da qaramar muryarta tace"

Ina wuni malam?

Sake Yar dariyar kulawa da shaawar nutsuwarta data abbinta yayi Yana amsawa kafin yace"

Ki shiga ciki gurin ummen taki yagana tana sallah ne.

Sake riqe hannun abbinta tayi tana sauke Kai Dan
Saida Abbin ya Dan kalleta da fararen idanuwansa yayi Mata alamar taje din tukuna ta miqe ta nufi kofar dakin da sallamarta a Baki ta shige.

Cikin nutsuwa yayiwa malam din tayin zama dasu a sabon gidan hayar daya kama Mai daukeda dakuna uku zuwa.,

Baya boye boye shi mutum ne Mai magana kai tsaye Dan haka Kai tsaye ya sanarwa da malam din sbd yanda Inayah tayi sabo fa yagana dakuma yanda INAYArsa zata cigaba da walwalarta cikin mutane Idan taga Basu kadaineba a gidan.

Da farko malam shiru yayi Yana nazarin al'amarin
sbd Kai tsaye suje su qarawa Abdulmajeed din nauyi Kaman Bai kamata ba tunda Shima yanzunema ya 'dan damu walwala ta abin yi.

Amma Kuma ata wani fannin kaman yanda Abdulmajeed din yafada rayuwar Inayah kam Idan babu mutane zata iya rasa walwalarta Duk da idan tana ganin Mahaifinta Bata buqatan kowa Amma ai shi mutum rahama ne,
Kuma itama yaganarsa Yana so tasamu mutanenda koba

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

1 year ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

1 year ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment