Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma na isowa da 'yar qaramar motarsa.

Ganin Alhaji MAJEED dinne dakansa yakawo Inayah yasa Dr Abdul qarasowa cikin nutsuwa da tsananin girmamawa ya gaida Abbin Yana cewa"

Barka da zuwa Sir.

Kallon Abdul din yayi da kyau cikin sake karantar nutsuwarsa ya gyada Kai shima a natse ya amsa da cewa"

Thank you Dr,
Ya aiki?
Ya fama patients da Inayah?

Murmushi yayi Yana Dan sake kallon Inayah dake kallonsa fuska asake
Ya kasa maida kallonsa sosai akan AA MAJEED din sbd tsananin kwarjini da cika Masa idon da yayi uwa uba ga wata irin nutsuwa da kamewa atare dashi,

Shima Adidas dinne a jikinsa black masu hade da hula yayi fresh acikinsu sosai tamkar sabon saurayi Mai tashen samartaka Dan kuwa shi Yama kasa yarda da shine ya Haifa zuqeqiyar budurwar 'ya kaman Inayah.

A hankali yace"

Lfy kalau alhmdllh Sir.

Ok Tom Allah ya taimaka
Thank you ko.

U're welcome Sir.

Jan motar Abbi yayi yabar gurin
Suma suka dunguma zuwa ciki.

Washe gari qarfe 8 tadawo gida wanka kawai tayi ta shige bargo sai bacci.

Bata farkaba sai 1 na Rana shima Kiran Anty Hafsat ne ya tadada.

Saidatai wanka tayi sallah taci abinci kafin ta Kira anty Hafsat din wadda tuni takira umma yaganah ta sanar mata 'dan Yar uwarta yaga Inayah din ya rikice musu tun jiya.

Umma yaganah Bata wani dauki zancen da mahimmanci ba saidai tace musu ya nema Inayah din da kansa idan sun daidaita ai shikenan haka akeso.

Kasancewar Inayah din batada wani saurayi ko daya yasa bata wani damuba tabawa anty Hafsat damar gabatar dashi din.

Ranar farko daya fara zuwa gidan Abbinta bayanan yayi tafiya zuwa Kano da CM Dan haka basu wani samu damuwaba ko fargaba daga ita har umma yaganah.


Faruk Ismail kyakkyawa ne ba laifi Kuma Dan boko da gayun gaske,
Ya waye sbd Yana ganin yayi karatu a Malaysia saidai Kuma daya Gama sanin cikakkiyar waye Inayah da mahaifinta sai ya Dan sassauto daga 'dagawar dayake Yi na shi baa Nigeria yayi karatu ba,

Shi karatun kawai yaje yayo yadawo ita kuwa acan taqarasa girma acan tayi karatu.

Ranar Ashe Bai yiwa Inayahn kallon tsaf ba sai yau din daya Gama kallonta a natse
Yaga irin kyan siffa data fuska dama sanyin halaye so innocent take yaji ya mutu akanta.

Cikin sanyi da sakewa irinta wayayyu take komai uwa uba ga shagwaba data Zama kamar halinta sbd tasowarta a shagwaben Dan haka tasaba komai Kai tsaye da gaskiyarta take yinsa.


At first Bata tsaya ta karanta Faruk ba sai daga baya daya Gama karantar shikam ya dauki duk wata hanyar mallakar zuciyarta,

Tsananin kulawa da kauna Mai girma yake nuna Mata tareda wata irin soyayya.

Shikansa yayi mamakin daya iya soyayya lokaci kankani sbd Bai taba soyayyar ba.

Halayensa na kulawa da zallar soyayya yasa tuni itama tafada soyayyarsa Mai qarfi taqarasa mantawa da Zaid gabaki daya da babinsa.

Soyayya Mai qarfin gaske sukewa junansa cikin watanni kadan
Ga Dr Abdul dayake fama da tsananin Sonta Amma haka yabawa kansa hakuri ya danne tunda anriga ansha gabansa.

Abbinta Bai damuba sbd tako Ina ya bincika iyaye da familynsu faruk din basuda illa Kuma tunda tagama karatu yanzu baida damuwa da aurenta koba komai auren ne next dama Dan haka yabawa faruk din Daman neman Inayah din.
##MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
#MAJEED/INAYAH/MARRIAGE



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[10/24, 5:32 PM] Mariyamah: *_22_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Lokaci ya tafi sosai dan tuni maganar aurenta da Faruk ta Gama kammaluwa aka saka lokacin biki hankalinta Dana faruk din ya kwanta sbd wata irin soyayya ce sukeyi Mai zurfi da qulafucin juna.

Shi kansa Abbin hankalinsa yafi kwantawa sosai da aurenta da Faruk akan can baya da Zaid.

Ba maganar komawarsu Australia saidai idan sunje hutu saikuma Abbin da shikam zai ringa zuwa akai akai sbd huldodinsa wasu dasuke can.

Daga Nan gidansu har familynsu Anty Hafsat da dangin CM Babu Wanda baya cikin farin ciki da murnar wannan biki sai Mimi wadda baqin cikin datake ciki ya hanata sukuni sbd bazata iya kallo Hafsat tasamu shiga jikin zuriar AA MAJEED ba fiyeda ita Dan kuwa ko yanzu akan wannan auren ba qananan arziki taketa samuba daga AA MAJEED harma da umma yaganah datake Jin Hafsat tagama Mata komai tunda tayi sanadinda Inayarsu tasamu kamilallan miji dayake sonta sosai.

Safnah kuwa Bata wani damu da damuwar da Mimin take cikiba sbd tadauka kishi ne irin Wanda Allah ya halitta a zuciyar Mata shine takeyiwa Anty Hafsat na ganin tasamu shiga a Inda itace taso tasamu shigar.

Neesah kam Dole da qarfi da yaji tazo Nigeria tareda momy Dan haka Murna a gidan takuma Zama sabuwa.

Ta bangaren Dr Abdul son Inayah Bai taba raguwa acikin ransaba saima Jin dayake kaman zuciyarsa bazata iya daukaba ganin Inayah ta aura wani tabarsa,

Amma iliminsa na addini Dana bokon daya kedashi Bai barsa ya qullata komaiba saima nesa nesa daya Dan farayi da Inayah sbd zuciyarsa bazata iya cigaba da daukan kishinta Mai tsananin gaske dayake ji Amma Inayah Bata iya nesa dashi sbd yariga yazama tamkar wani babban bangare na rayuwarta a Nigeria,

Tayi sabo da shaquwa Mai tsananin gaske dashi da har kaunarsa ta ginu a ranta amatsayin aboki Kuma Dan uwan Dan haka idan yaqi kiranta itace da kanta take kiransa.


*****Bikinta Saura sati uku Dr Abdul yabar Lagos yakoma Adamawa
Farko hankalin Inayah din yatashi sosai da barinsa Amma hidima da shaanin biki yaqi barinta maida hankali sosai kan tafiyar tasa
Sai kawai tabarshi akan idan angama bikin Zatai magana dashi.

Anfara gyaran Amarya INAYAH tako Ina,
Umma yaganah baji ba gani ta dauko masu gyara daga maiduguri ana gyaran Inayah ta ciki da waje.

Anty Hafsat ma ba Zama kusan kullum saitaxo gidan da nata kayan gyaran.

Neesah dai kam tana gidan sbd suna sauka Abuja can gidan iyayen momy kwana biyu kawai tayi ta biyo jirgi zuwa Lagos Dan haka duk sauran shirye shiryensu tare suke yinsu
Ko Safnah ma kusan kullum gidan take wuni.

Umma yaganah taje maiduguri kusan kwananta biyar acan daqyar daqyar ta iya samun wasu daga cikin 'yan uwanta Amma sauran kam duk sun rasu wasu Kuma ba'a San Inda sukeba kaman ita.

Wainda ta sama cikin Yan uwan nata bama irin Yan uwan kusa bane
Kawun malam mijinta ne da iyalansa ta samu sunkoma kauyensu da aka watse sai wasu daga cikin amininan iyayenta saikuma kishiyar mahaifiyarta da itama ta tsufa sosai.

Tayi musu Sha Tara ta arziki tabaro tadawo maiduguri tasake kwana daya tabi jirgi Takoma Lagos.


*****A daren da zaa saka amarya lalle saqon wani mugun labarin ya isowa umma yaganah ta hanyar Mimi.

Rigimace ta barke a gidansu faruk da iyayensa da shi harma da mahaifin dadynsa..

Wannan wata babbar maganace data girgiza umma da ita kanta Inayah sbd basu taba tsintar wannan mumunar kalmarba sai ranar.

AA MAJEED ya Haifa Inayah bada aureba,
'yar gaba da fatiha ce...

Tashin hankali Mai girman gaske umma yaganah da Neesah suka Shiga sbd kalmar tayi Muni da yawa.

Inayah kuwa zuciyarta ce taji tana harbawa da sauri da qarfi
Wani irin zufane masu dumi suka ringa tsatsafo Mata.

Dafa kujera tayi ahankali ta zauna tana Jan numfashi da sauri sauri.

Ruwa zubbi taje da gudu takawo tabawa Neesah dake Kiran sunanta da Dan qarfi tana cewa"

Inayah karki daga hankalinki please
Wannan labari ne fa kawai aka kawo.

Karban ruwan tayi takai bakinta da Dan sauri ta kwankwada ta miqawa zubbi cup din tana miqewa tsaye tace"

Faruk yasan wannan zancen shirme ne,
Ina ruwansu data yanda mahaifina ya haifeni,
Idanma Ni shigeyarce an haramta auren shegu ne?
Tunda Ina tareda mahaifi ai banajin zan karba suna kokuma bin layin shegu..

Umma yaganah ma cikin damuwa da tashin hankalin datake dannewa tace"

Menene Kuma na wannan zancen ma Kuma yanzu?
Yarinya da ubanta Dan Allah bamason janye janye da wulaqanci,
Waye yafara kawo wannan zancen?
Wane Mara hankalin ne zai kawo Mana fitina muna shaaninmu cikin Jin Dadi da farin ciki?

Kuka sosai anty Hafsat keyi agaban Umma yaganah din sbd batama San Mimi tafara kawo musu zancen basu yardaba sai yanzu datazo da kanta sbd Al'amarin ya tsananta acan familyn Anata rigima da tashin hankali,

Mahaifiyar faruk da mahaifiyar dadynsa sunyi rantsuwar bazaai aurenba Dan faruk bazai aura Inayah ba sai mahaifinta ya sanar dasu Gaskiar wannan zancen da aka kawo musu.

Dadyn Faruk yasan saidai afasa auren har abada Amma AA MAJEED bazai zauna yiwa kowa bayaniba Dan a aura 'yarsa
Kai tsayema za'a samu babbar matsala dashi Dan kuwa suna shegenta Masa 'ya ne Kai tsaye da kalamansu.

Shi kansa Alhaji baba kakan faruk din Bai wani goyi bayan faruk da mahaifinsaba sbd ganin kaman harda kwadayin suna da arzikin AA MAJEED sukeson rufe Ido su hada zuria dashi koda da gaske Inayah din 'yar gaban fatiha ce.

Dayake maganar a tsakanin mata tafara har lokacin Abbi baisan abinda yake faruwaba dagashi har CM Dan haka su sun Riga sun Gama rabawa jama'arsu katikan daurin aure da invitations na special lunch da zaai bayan daurin auren sbd abokanan huldodinsu Christians da turawan dake Nan tunda su ba daurin aure suke zuwaba.

Wasa Wasa saiga zance dai yazama Babba Dan kuwa Dadyn Faruk yasamu CM da zancen har gida sbd bazai iya tunkarar AA MAJEED ba,
Ko daya girma MAJEED sosai yanajin kunya da nauyinsa yaje Masa da maganar Dan haka yasamu CM da zancen.

Sosai cm ya girgiza da wannan mugun sakon, dan haka baiyi saurin isarda sakonba saiya samu Alhaji baba dasu hajiyar yayi kokarin fahimtar dasu illar abinda zaayi din Dan tamkar tozarcine Kuma wulaqanci ga AA MAJEED da 'yarsa ace zaa tambayesa yanda ya Haifa yarsa.

Sam kasa fahimtar juna sukai dasu dashi Dan haka baida wani zabi sai sanarda AA MAJEED halinda ake ciki.

Shiru yayi bayan yagama sauraron bayanin CM cikin nutsuwa.

Bai bayyanarda bacin Rai ko fushiba saidai kam idanuwansa wannan karon sun bayyanarda tsananin 'dacin daya Kama zuciyarsa.

Ba'a taba cin fuska ko cin mutuncin Martabarsaba sai wannan karon,

Ko alokacinda yake talakansa baida girma ko qima a idon mutane tunda shi talakane baa ci zarafin mutuncinsa kaman wannan lokacinba.

Idanuwansa ya Dan juyo ahankali ya dauki wayarsa dake gefensa ajiye ya Nemo numbern umma yaganah ya saka Kira.

Zaune suke gabaki daya gidan yanzu Murna na Neman komawa ciki tunda wannan muguwar magana ta bayyana.

Tashin hankalin da Faruk yake cikine ya tabbatarwa dasu Inayah Al'amarin ya girmama,
Babban tsoro da fargaba tareda tashin hankalinsu shine idan zancen yaje gaban Abbi yanda zai karbesa.

Sbd farin cikin Inayah sunsan zai iya komai hakama sunsan bazai taba bawa Wainda suka shegantata suka alqantata da 'yar gaban fatiha aurentaba,
Zancen na zuwa gabansa sunsan maganar bawa su faruk aurenta Kuma ta mutu saidai wani ikon na ubangiji.

Hakan yasa Kiran abbin na shigowa wayar umma yaganah duk jikinsu yakuma sanyi sbd sunsan cm na gidan tun dazu suna magana.

A natse ta dauka tareda sallama a sanyaye tace'"

Naam ABDULMAJEED.

Umma kuzo Palo akwai sako.
Ina Inayah?

Gatanan kwance tana fama da Dan ciwon Kai ne.

Kizo harda ita din.


Yana fadar hakan ya kashe wayar a natse tareda ajiyewa Yana cigaba da sauraren amininsa CM dake fadar rashin dattakon dasu Alhaji suka nuna akan wannan Al'amarin
Magana dai gatanan irinta mata Amma sun biyewa zancen banzan.


Shidai Bai iya cewa komaiba sbd zancen yazo Masa ne a bazata,
Bai taba tunani ko sanin wani zai iya samun guts na aibata 'yarsaba.

Kuma aibatawa mafi muni bafi tozarci Dan kuwa Saida suka kammala komai na ya'da maganar aure ace an fasa.

Ta wani bangaren Inayah din yakeji,
Tanada rauni sosai
Bata iya saka damuwa ka shiga baqin ciki ba sbd sosai take shiga damuwa,
Da qarancin shekarunta ace itama wannan shine Karo na biyu ana neman aurenta ana fasawa.

Tabbas su Alhaji baba sun tozartasa
Tozarta mafi muni.

Sallamar umma yaganah ce tasashi Dan rufe Ido ya bude batareda ya juyo ya kallesuba Dan yasan dukansu Babu Wanda yake cikin yanayi Mai kyau sbd daga Inayah din har umma yaganah baisan Wanda yafi wani qulafucin aurenba,
Ya rasa meyasa suke tsananin son auren tunda komai lokaci ne dashi.

Inayah na ganin yanayin Abbinta tasan maganar fasa aurence zaai Dan haka ta fashe da kuka ahankali tana kwantawa jikin umma yaganah da itama nata idanuwan sukai jajir.

Har lokacin Bai waiwayo ya kallesuba saidai cm ne yafara bayani cikin damuwa da rashin Jin Dadi yace"

Umma nasan dai kinji bayanin abinda yake faruwa daga bakin Hafsat,

Iyayen faruk dai basu amince da auren faruk din da Inayah ba akan wasu dalilansu da Babu amfanin ambatarsu yanzu,
Dan haka ayi hakuri maganar auren dai yanzu abarta babuta saidai bamusan abinda Allah zaiyi agaba ba,
Faruk idan mijinta ne Inshallah duk wainnan tashin hankalin da maganganun zasu wuce.


Inayah ya kalla cikeda tausayi da kulawa yace"

Kiyi hakuri kinji Inayah
Inshallah Zaki samu mijinda yafi Zaid da Faruk,
Wannan fashin auren wata jarabawace da ubangiji ne kadai yasan tanadin da yayi Miki a gaba.

Kallonta Abbi yayi da idanuwansa dasuka sauya cikin nutsuwa da Jin zafin abinda akaiwa 'yarsa yace"

Karkiyi kuka ki dauka hakan amatsayin wani gwaji daga Allah.

Umma yaganah ki kula da ita sosai kada ta saka Al'amarin aranta tajawa kanta damuwa ko wani ciwon.
Allah ya zaba Mana abinda yafi Zama Alkhairi.

Amin" suka furta CM da umma yaganah
Inayah kam kuka takeyi sosai Wanda kusan Bata taba irinsaba.

Daqyar ta iya Isa dakin umma ta zube jikin umman Yana Jan numfashi zuciyarta na harbawa da qarfi.

Neman yankewa numfashinta keyi da gudu Neesah taje takawo ruwa suka Bata suna Mata firfita duk da sanyin AC daya cika dakin zufa takeyi sosai tana Jan numfashi ga hawaye nabin fuskarta.

Hankalin umma yaganah da Neesah harma da Anty Hafsat da Safnah da mimi dake gidan tashi yayi ganin yanda Inayah take cikin yanayin ban tausayi ga hawayen idonta dasuka qi tsayawa.

Mimi datai wannan mummunan qullin Saida jikinta yayi sanyi tashiga damuwar tausayin Inayah duk da batai Dan cutatar da Inayah ba tayine Dan lalata Hafsat.

Jiki amace suka watse suka koma gida aka bar ssu umman da Inayah suna fama da ita.

Abbinta dayasan hakan Zata kasance da ita da wuri ya Kira likita akazo gida aka dubata
Harda drip akai Mata qari sbd tashiga tension sosai na Al'amarin.
##MAMUH#
#RIBA BIYU#
#AYSHATOUH INAYAH#




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
0913484810
*_23_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da zazzabi ta kwana sosai a daren Dan haka a dakin umma yaganah ma ta kwana sbd tasamu kulawa da ita yanda yakamata Neesah ma kasa kwana tayi daki ita daya ba Inayah tadawo dakin umman suka kwana.

Washe gari ba laifi ta tashi da lafiyar jiki saidai rashin ta zuciyata,

A sanyaye take gabaki dayanta,
Damuwa da 'dacin zuciya harma da baqin ciki sune takeji mamaye da zuciyarta tako Ina,

Ga faruk tun jiya sai kiranta yake hankalinsa ya tashi dajin batada lafiya Amma bazata iya daga kiransaba ayanzu Dan kukane kawai zatai tamasa,

Sun shirya tareda tsara yanda zasu gudanarda rayuwarsa da tsantsar so da kaunar juna,
Daga ita har faruk suna tsananin son juna sbd tako Ina suna ganin sun dace da rayuwarda suke so da burin gudanarwa a rayuwar aure.

To menene yasa iyayensa zasu datse musu buri da kaunar junansu?

Meyesa zasu aibatata Rana tsaka Dan kawai cin zarafi ga mahaifinta
Dan kuwa wannan da gani ba ita sukeson tozartawa da wulaqantawaba sai mahaifinta...sai dai kuma duk abinda zaa tozarta ko cin zarafin mahaifinta fita ranta yake.

Tana son faruk kusan ma fiyeda yanda taso Zaid Kuma cire sonsa aranta zaiyi Mata wuya sosai amma Kuma Dole Zata dauki dangana kodan kada acigaba da cin mutuncin Abbinta da maganar yanda ya haifeta,

Itadai koma Yaya mahaifinta ya haifeta tunda Bai yar da itaba kokuma ya gudu yabarta kokuma yamayi denying zamansa mahaifinta to tanason abunta ahakan,

Idanma bada aure ya haifetaba Bata buqatan sani tunda barna ce to Riga ta afku ba gyara acikinta,
Hakama dawo da zancen kokuma tambayarsa akan Gaskiar zancen kaman cin mutuncin mahaifintane zatai bayan Babu ta Inda ya gaza a matsayinsa na uba Wanda ya maye gurbin uwa.

Ko danginsu da kakanninta Bata sake tambayaba sbd tsananin dokar daya kafa Mata akan hakan shiyasa Bata sake shaawa ko marmarin tambayaba.
Abu daya tasani takuma tabbatar shin,
Koma menene ya Raba mahaifinta da mahaifiyarta harma da danginsu ba abune Mai dadiba,tashin hankaline.




****Bayan kwana biyu da fashin auren jama'ar da suka sani sunyita yawo da zancen Wanda har gurin abokan aiki da huldarsa zancen yaje na cewa bada aure ya Haifa yarsaba,

Da yawa basu wani damuba sbd harkace data shafesa bawai aikinsaba
Haka zalika dukiyarsa da matsayinsa ya hana kowama daga zancen saidai mamaki da la shakka mutane sunyita fada.
Inda ma zancen yayi sauki bai wani shiga media ba sbd a Nigeria din ba kowane ya sansaba tunda baa qasar yake zauneba,

Manyan mutane abokanan huldodinsa ne kawai suka Sansa sosai sai jama'ar da baa rasaba.

AA MAJEED mutum ne da Baya damuwa da Al'amarin kowa sai Wanda ya shafesa,
Kuma Sam Baya damuwa da abinda kowa zai fada akansa Dan Bai taba damuwaba sbd yasan iya bayan fage ne bazaa iya zuwa afada a gabansaba sbd iskancinma gurin yinsa ake samu
Ko su Alhaji baba duk wannan abin daya faru basu iya zuwa sun fada a gabansa ba sbd kwarjini da cika idon da Allah yayi Masa akan mutane Dan haka shima baiga amfanin nemansuba ko ji daga garesu tunda sun Kai sakon gurin Aminsa CM Kuma ya isar musu da sakonsu ga AA din,

Sun dauka zaizo ya rokesu akan janye maganar tunda sunsan Babu abinda bazai iyaba akan farin cikin 'yarsa saigashi sunga sabanin hakan,

Abinda basu saniba da akan wani dalilin ne suka soke auren zai iya nemansu a sulhunta Amma Kuma har abada bazai iya bawa Wanda ya sheganta asalin 'yarsa aurenta ba Dan hakan take ya toshe duk wata sauran hanyar dazata ma tunatar da Inayah wannan Al'amarin.

Private hospital din da aketa kokarin budewa da sunanta aka sake bada himma sbd ko aikin tafara sosai yanda hankalinta bazai zauna akan damuwar matsalar da aka samuba.


Dole ta sakawa kanta dangana da tawakkali sbd ganin Abbinta daya tattara maganarsu faruk ya watsar duk da tasan abin Yana damunsa tunda shi ubane da aka fasa auren yarsa Rana tsaka saidai Kuma bayyanarda damuwar batada wani amfani shiyasa basa gane Inda yanayinsa yake dosa.

Umma yaganah ma haka suka hakura suka dauki dangana suka cigaba da adduar Allah yakawo Mata wani mijin yasa hakan shine yafi Zama Alkhairi.

Yanzu Bata wani fita asibiti sbd baa kammala tasu asibitin ba gashi Dr Abdul ma Dole yanzu zai dawo yaci gaba da aiki a asibitin tasu idan angama tare.

Da labarin lalacewar auren ya samesa baiji dadiba sosai sbd tunanin halinda Inayah Zata shiga Dan haka Saida ya matse ayyukansa yazo Lagos din hankalinsa ya kwanta.

Da farko Inayah na ganinsa daya iso gidan nasu Batasan lokacinda ta fashe Masa da kuka ba tana sake maimaita Masa abinda yafaru.

Hankalinsa Bai tashi da abinda ya faru dinba kaman yanda hankalinsa yatashi da kukan datakeyi Wanda taketa riqewa da dannewa cikin ranta sbd gudun daga hankalin umma yaganah da Abbinta,

Amma tsakani da Allah har cikin ranta tanajin tsananin quncin rashin faruk Wanda gabaki daya yanzu idanma yakira bayan kuka Babu abinda take Masa harya daina kiranta sbd kukanta ba qaramin daga hankalinsa yakeyiba,

Kukanta zai iya sakasa bijirewa iyayensa ya dauketa suje suyi aurensu wani gurin Amma Kuma hakan ba qaramar fitina zai tadaba dan kuwa Yana shakkar mahaifin Inayah din sosai tako ina.,
Bayason ya jawa iyayensa 'daurin da zai taba tsufa da mutuncinsu Amma badan hakanba Babu abinda zai hanasa guduwa da Inayah wani gurin a daura musu aure.

Hankalin Dr Abdul ya matuqar dimauta da kukan Inayah wadda yakewa wani irin boyayyan son da yafara fin qarfin qarfinsa,

Shi mutum ne Mai tsananin zurfin ciki da iya danne Abu shiyasa son nata yake boye cikin ciki da zuciyarsa Amma irin son dayakejin yanai Mata a yanzu bazai iya barin wani ya auretaba koda zaaita saka ranar auren nata ana warwarewa har sai ranarda ya sameta.

Ita kanta tanajin Dr Abdul cikin ranta sosai Amma ba amatsayin masoyiba sai matsayin aboki wanda batada tamkarsa bayan Neesah.

A gidan ya qarasa wuninsa Yana rarrashin Inayah shida umma yaganah daketa qara gode Masa kan damuwarsa dayake nunawa sosai akan Inayah din.

Yana gidan Abbi yadawo Dan hakama Dole atare dasu yaci abincin dare dukkaninsu a dining.

Dr Abdulsamad yasamu shiga sosai agurin Abbi Wanda da farko harsu Inayah din sunyi mamaki sosai tunda sunsan shi mutum ne Mai wuyar sabo da mutane,
Bakowa yake yarda yashiga jikinsaba sosai
Amma Dr Abdul lokaci qanqani yashiga ran abbin ya kwanta Masa sbd sanin kansa dakuma qaunar Inayah Mai girman gaske daya hanga atareda Dr Abdul din.

Ya jima Yana fira agurin abbin kusanma duk akan aikin asibitin ne nasu da ake gab da kammalawa,
Sai dare yabar gidan yatafi lokacin INAYAH ta jima da yin bacci sbd yanzu Bata wani jimawa take bacci.

Neesah Takoma Abuja gurin momy datazo ta jajanta musu suka koma tareda Neesah din Abuja.



******Ahankali Dr Abdul ya Dage sosai gurin mantar da ita faruk dukda da Kamar wuya
Amma Kuma dagewar tasa da tsananin kulawarsa akanta yafara cin nasarar hakan Dan yanzu ba laifi tacirewa ranta faruk din ta hakura saima hankalinta data maida sosai akan Dr Abdul din kan aikinsu.

Faruk yakoma Malaysia qaro karatu Dan haka yanzu wayar tasu ma kusan kwata kwata sun daina saidai idan sunga juna a social network.



***Lokaci ya 'dan sake ja son da Dr Abdul ke Mata yafara juyewa zuwa wani Al'amarin daban,
Yanzu gabaki daya ya sauya akanta yakoma kaman ba Natsatsen Dr Abdul din dakowa ya saniba,

Wani irin so Mai zafin gaske yake Mata Wanda harya fara bawa umma yaganah tsoro gashi dai Bai fito yafada Mata Sonta yakeba Amma dai kowa ya kallesa yasan yagama zautiwa a Sonta Dan ko kallonta idan yanayi mantawa yakeyi da kowa.

Ita kanta Inayah lokuta da dama tsananin kulawarsa da abubuwan dayake Mata na kauna tsoro da shakka suke Bata Amma har lokacin batajin tana Masa son soyayya saina aboki,yanzuma ya wuce abokinta ya Zama wani bari na rayuwarta.

Abbinta ma ya lurada halinda Dr Abdul yake ciki akan Inayah,

Baida matsala akan bawa Dr Abdul aurenta Amma Kuma Yana shakkar irin son dayake Mata zai iya cutatar da ita akan kishi kokuma cutatar da duk wanda zai shiga tsakaninsa da ita Dan haka son shima yake sakasa shakku,
Ta wani bangaren Kuma tausayinsa yakeji Mai tsanani sbd son mace irin haka kaman ba so bane ciwo ne.

Anty Hafsat koda aka fasa auren Inayah da Faruk Bai taba alaqarsuba saima sake shaquwa dasukai Dan haka yanzu tazama antyn Inayah tamkar wata qanwar uwa ko qanwar ubanta
Komai na Inayah tasani da ita suke shawara so da dama
Hakama Umma yaganah ta zamar musu tamkar uwa a gurinta suke wasu shawarwarin.

Anty Hafsat din batai qasa a gwiwa ba takuma hada wani qaninta dasuke uba daya da Inayah.

Sadeeq qanin anty Hafsat yayi karatun likita shima anan Lagos yatashi Kuma sosai yakeda abun kansa saidai yayi irin wayewar datai qazanta shima Neman Mata yakeyi sosai Amma Kuma bazaka kallesa kace yanayi dinba Dan kuwa a kamile yake a zahirinsa.

Ba laifi ya Dan fara shiga ran Inayah saidai Bata wani zura da yawaba sbd tafara Jin shakkar Al'amarin maza da aure.

Shima dagewa yayi da soyayyarsa da kulawarsa harma da alqawuransa yasamu yashiga zuciyar Inayah din.

Wannan karonma ba Bata lokaci ya aiko iyayensa da maganar aure.

Abbin yaso su saurara Kar ayi rushing din Al'amarin Amma Dr sadeeq din ya dage da iyayensa har abbin ya yarda.

Dr Abdulsamad kusan zaucewa yayi da wannan maganar auren Kuma Saida kusan kowa yakusa gane halinda yashiga,

Kasa hakuri yayi sbd zuciyarsa bazata iya daukaba yabi ta qarqashin qasa ya lalata auren ta hanyar tona asalin waye Dr Sadeeq Kuma can ma gidansu anty Hafsat akai fitinar ta hada 'dan uwanta da 'yar gaban fatiha tunda ba uwarsu dayaba.

Wannan karon har asibiti Inayah ta kwanta ciwo sosai sbd zuciyarta tafara kasa dauka
Abubuwan sun fara tabata sosai.

Hankalin umma yaganah da mahaifinta ya tashi sosai sbd Saida suka dangana da zuwa Australia taga likita acan tayi jinya
Ta huta kanta ya Dan sake kafin suka dawo.

Ciwonta ba ita kadai ya taba ba harda Dr Abdul Wanda shima hankalin mahaifiyarsa yafara tashi da wannan mummunan masifar dake tunkarota 'dan ta namiji guda datake alfahari dashi Yana Neman samun tabin qaqwalwa akan son mace.
##MAMUH#
#AA MAJEED#
#AYSHATOUH INAYAH#
#DR ABDUL SALEES/HADIZA



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
*_24_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Alaqarta da Anty Hafsat Bata taba girgiza ba sbd fashin auren da aka samu akaro na biyu saima tausayin juna dasuke,

Su suna ganin qoqarinta da tausayinta akan yanda taketa kokarin hada Alkhairi Amma Alamuran na lalacewa,

Itama tausayin Inayah takeji sosai

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

1 year ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

1 year ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment