Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokaci tasan mutane dakuma Yan tsirarrakun areas da streets sbd tana fita Yar siyayyarta
Yanzu har maganin gargajiya take siya daga nan ta aikawa mama da koyaushe take fama da jiki duk da ana cemata taji sauki din saidai yanayin muryar maman yasa ta fahimci suna fadane kawai Dan kwantar mata da hankali.
Hakama Abdul tana Dan yimasa siyayya idan zatai Aiken ta aika musu.

Tana gab da cike shekara a sabuwar rayuwarta ta Lagos ta fahimci wani babban alamari Mai tsananin ban tsoro da firgitarwa a tareda ita.

Bata tabbatarba Dan haka ta saka lokacin zuwa wani qaramin asibiti dake kusada anguwar dasuke,

Ana albashi da kwana biyu ta kwasa ta nufi asibiti a dubata sbd tabbas Idan tanaji Kuma tana fahimtar daidai motsin ciki takeji a cikinta Wanda girman daya fara yasa ta dauka kibar datayi ce Kuma hakan Wainda take taredasu suke fada tayi qiba tayi tumbi.

To me take Shirin ji ne?
Tsakanin kwanaki Biyar zuwa yanzu take Jin motsin sosai da juyi Wanda ta tabbarda cikin haihuwane kawai yake Wannan motsin.
#MAMUH#
#LOVE#
#ROMANCE#
#ZAFAFABIYAR#
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


3
InnalillahiWainna ilayhirrajiun"

Shine abinda zuciyarta tafada lokacinda take zaune cikin jerin layin ganin likita data buga sammakon zuwa.

Gyara zamanta tayi a karo na Bata lissafi sbd gabaki daya takasa nutsuwa ta aje jikinta guri daya,

A tsananin matse take datasan asalin Menene ajikinta,

Shin wani ciwon ne yasameta?
kokuwa wata lalurarce Wannan da batasan da itaba?

Itadai a yanzu koma menene gata agaban dakin ganin likita Allah yasa taji abinda zuciyarta zata iya dauka sbd koma wane irin ciwone atareda ita Bata tunanin Mai saukine sbd girman motsin datake ji.

Dago Kai tayi ta Dan bude manyan fararen idanuwanta dasukai jajir da tsantsar damuwa da fargabar fake gamutse cikin ranta da kanta
Ta kalla inyamurar data fito daga ganin likitar wadda daga ita mutum biyune ya rage layin yazo kanta.

Bin bayan wadda ta shiga tayi harta shige kafin ta dauke kanta tana sunkuyar da kanta gefe tareda rufe idanuwanta tana sake Jin motsin da akeyi acikin cikin nata.

Haka ta muskuta tana cigaba da zaman jira zuciyarta na cigaba da cika ta koina da damuwa da fargabar abinda zaije yadawo har tsawon mintuna ashirin kafin aka kirata ta miqe tareda gyara zaman qaramar Jakarta dake rataye kafadarta ta nufi kofar dakin ganin likitan tashige tana kokarin samarwa kanta nutsuwa sbd tayiwa likita bayanin yanayinta a matse.

Dr Adebayo A Aziz tagani rubuce a gaban farar Lab coat din dake jikinsa

Ta qaraso ta zauna jiki a sanyaye sbd taso tasamu likita Mai Jin hausa koda Yar kadan ce sbd tasamu ya fahimci zancenta dakyau hakama itama ta fahimci abinda zai sanar da ita da kyau.

Tanajin dan pidgin dinta data koya a zaman garin Lagos din saidai bazai isheta suyi magana da kyauba Dan haka sai kawai jikinta yakuma sanyi ta gyara zamanta ahankali tana dagowa ta kallesa lokacinda ya bude Baki Yana kallonta Kai tsaye yace"

Yes, what's the problem madam?

Dan rage kallonta akansa tayi cikin sanyin jiki ta bude Baki tana Kai hannu kan cikinta da yayi tauri cikin kwanakin ta nuna masa tana harhada turancin da qyar cikin gwamutsawa tace"

Something is moving inside my here" ta qarasa fada tana nuna masa cikinta da hannuwanta biyu.

Is moving very very much,
But no pains,
No fever,
No anything only the movement inside here.

Idanuwansa ya Dan zuba mata tareda sakin murmushin bayanin nata.

Ya kalli cikin dakyau Yana cewa ta janye hannunta ya gani.

You said no any pains or fever?

Gyada Kai tayi tana kallon fuskarsa.

Rubuce rubuce yayi cikin file dinta kafin ya aje ya miqe tsaye.

Gadon dake dakin ya nuna mata Yana cewa tahau ta janye rigarta ya duba cikin.

Ajiye Jakarta tayi gefe tareda moqewa ta nufi gadon tahau zuciyarta na cigaba da tsalle cikin rudani da fargaba.

Tana janye rigarta tun kafin yakai hannunsa kan cikin idanuwansa suka tabbatar masa da cikine a jikinta Kuma tabbas inshallah zai Kai wata Biyar zuwa shida haka.

Hannu yakai yafara Danna cikin da Dan qarfi Yana examining nata aikuwa saiga cikin Yana sake motsawa.

Kallonta yayi Yana zare Safar hannunsa yace"

Madam ciki wata nawa???

Kallonsa tayi da sauri tana kokarin Jan rigarta ta rufe cikin ta tashi zaune tana Kuma kallonsa Kaman Bata gama fahimtar abinda yafadaba tace"

Eh??

Komawa yayi ya zauna gurin daya tashi Yana kallonta bayan itama tadawo ta zauna yace"

Madma ciki naka wata nawa??

Girgiza Kai tayi tana kokarin Hana kanta shiga firgici sbd zancen nasa buga kirjinta yake.

Ganin halinda take ciki take ya fahimci batasan da cikinba kokuma cikin Bata shirya daukarsaba kokuma ma batada tabbacin na waye acikin mazan datake taredasu dan haka rubuce rubucensa yayi yagama ya kalleta tareda miqa mata takarda yace"

Madam you are pregnant,
I mean kanada ciki zai Kai like 5mnth
Take this kaje kayi scanning ka kawo.

Wata takardar yakuma miqa mata yace"

And this one,test ne go lab zasu dauka blood naka ayi test na ciki da shauransu, then you'll come back on Monday and bring the results to me.

Hannuwanta dake tsananin rawa takai ta karba takardun tareda miqewa tsaye ta fice zuciyarta na wani irin azabar bugawa da nauyin gaske.

Kasa barin asibitin tayi Kai tsaye ta nufi bangaren da ake scanning ta biya ta shiga akayo mata cikin mintuna qalilan saigata da result din ciki a hannu.

Rufewa idanuwanta sukai da wani irin tsananin duhu,

da daddafawa ta samu wata kujerar plastic dake hanyar fita asibitin ta securities ta zube zaune hannuwanta da qafafunta sosai suka dauki wata Mummanan rawa zuciyarta na qafewa da zallar tashin hankalin da Bata taba shigaba ko alokacin mutuwar Salisu.

Takardar dake damqe hannunta ta Kuma dagowa ta kalla kafin takuma budewa hannuwanta na rawa tafara bin rubutun dake ciki daki daki da idanuwanta dake mata zallar yajin radadin Neman hawaye Amma Sam babu alamar zuwansu.

Daya bayan daya take bin kalmomin tana karantawa da 'Dan ilimin bokon datake dashi na iya secondary.

Hawaye ne taji suna ciko idanuwanta take data Gama duba takardar,

Ko ba Dan ta karanta ba Wannan takardar da abinda ke cikinta ya tabbatar mata da zancen likitan sbd Zak irinta wannan bayanin ne na ciki ajikin takardar dasukai scanning tareda Salisu wancan lokacin cikin Abdul.,

Kenan da gaske ta tabbata cikine ajikinta?

Tayaya?

A Ina ya fito tunda tasani Kuma Allahn da yayita shine mafi sanin Bata taba aikata komaiba a duniya da wani da namijin bayan salisunta.

Dama Ace shekarar data gabata ne da saitace cikintane da Salisu ya barta dashi Bai bare ba.... InnalillahiWainna ilayhirrajiun,,

Ni hadiza wane irin Mummanan haline Wannan nashiga Wanda bansan meyake faruwaba.

Sai alokacin tafashe da wani irin Mummanan kukan mawuyacin halin datake ciki
Ga cikin sai sake motsawa yakeyi alamar Yana cikin cikakkiyar koshin lafiyarsa data sanyashi kwanci tsawon shekara biyu sai yanzu daya samu tashi.

Kukan fitar hankali tayi tsawon lokacinda Bata saniba agurin har Saida taji idanuwanta da fuskarta sun kumbura kafin ta iya miqewa ta kama hanyar komawa gida.

Isarta gida Bata Bari kowa ya gantaba ta shige daki ta aje Jakarta ta fito tayi alwala Takoma dakin sallah kawai tayi ta fara rokon Allah mafita tana hawaye
Ahaka ta Gama ta miqe Takoma ta kwanta Bata Kuma fitowaba sai washer gari.

Gurin aikima datazo nokewa kawai taketa faman yi tana kame kame sbd ganin Kamar kowa zai fahimci cikin jikinta Dan haka duk tabi tayita Jin kanta a muzance.

Tana tashi aiki Bata koma gidaba Kai tsaye gurin wani gurin scanning din daban ta nufa takuma yi,
Shima result daya tasamu na akwai ciki.

Wani gurin takuma zuwa Shima duk daya,

Haka tayita yawon guraren scanning ana Bata result daya
Ta tattara tadawo gida hankalinta zuwa lokacin yagama barin jikinta,

Tashin hankali da tsananin tsoro takeji yanzu sbd ta tabbata takuma shaidar kanta Idan har Wannan cikin na haihuwane bana aljanuba to wlh cikin Salisu ne ajikinta Wanda yabarta dashi tunda tasan Bata taba ko tunanin 'da namiji ba bayan rasuwar salisunta.

A daren kwana tayi wani irin kuka da quncin zuciya mai nauyin gaske.

Tayaya zata fuskanci duniya da ciki a jikinta?
Cikin da bai tashi fitowa ya bayyana kansaba sai data baro gaban iyayenta tazo Lagos,
To tace me akan cikin?
Zaa yarda da itane?

Cikin qanqanin lokaci damuwa da kunci  sukaiwa rayuwarta mugun baibayi,
Sam tarasa walwala da kwanciyar hankali da nutsuwarta,

Kullum cikin zullumi da tashin hankali take tashi takuma wuni acikinsa sbd ciki dai yanzu gadan gadan fitowa yakeyi Yana girma ahankali Kaman yanda kowanne lafiyayyan cikin keyi.

Lokaci na Ja tadain shiga mutune Sam yanzu Takoma tamkar mujiya sbd yanda cikin yagama fitowa kowa ya ganta Kai tsaye zai shaida cikine a jikinta,

Hankalin mama Indo yayi Mummanan tashi da girman mamakin ganin Wannan alamari,

Tashin farko Bata yardaba da anata gulmar cikin Hadizar sai data tinkareta ta ganarwa idonta ta tabbatar musamman yanda hadizar takasa hada ido da ita sai hawayen baiqin ciki takeyi.

Babu kalar diban albarka da Rashin mutuncin da mama Indo batai mata tareda gori da zagi kala kala karshe ma haka ta tara mata jamaa agabansu tai mata Mummanan wulaqanci har Wanda baima Gama sanin halinda take cikiba yasani,
Take gurin aikin dama gidansu aka fara zundenta,
Masu zaginta da masu tausayinta dama wainda suke ganin ba komai bane Dan tayi cikin,

Haka aka ringa yi da ita tun tana daurewa zuciyarta harta fara gazawa sbd babu inda take Jin Dadi ko sassaunci alamarin duniya yataru yayi duhu,

Babbar fargabarta da tashin hankalinta Kar mama inda ta sanarwa su mama da Inna halinda take ciki
Dan haka duk tabi ta daga hankalinta wata sabuwar damuwar da tashin hankali yakuma shigarta.

Ahankali Ahankali lokaci yakuma tafiya Amma a rayuwar hadiza kullum da'da zurfafa take cikin tashin hankali da damuwa da qunci take sbd rayuwa tayi mata tsanani sosai sbd ciki kam ya tsufa sosai kowanne lokaci zata iya haihuwa,

Kullum adduarta Allah yasa ta Haifa abunda yake cikin yazo ba rai ta huta ta tattara Takoma gida sbd bazata iya zuwa gaban iyayenta da Wannan cikin ko abinda zata haifa barema yayyunta data San basuda imanin karbanta da abinda zataje dashi,
barinma yanzu dasuke siyasa bazasu yarda da abinda zai taba qimarsu dasuke tunanin sunada ita a manyansu.

Wani sabon tashin hankalin ta shiga Rana tsaka da gurin aikin suka sallameta bataredama sun jira watan yaqare anbata albashintaba.

Lokacinda taringa roqar Manager tana basa hakurin yabarta zata iya aikinta koda cikin Amma ya rufe ido ya sallameta tareda Bata awanni akan ta tattara tabar gidan kamfani tunda gurin aikinne suke Basu gurin zaman Dan haka Kai tsaye gida Takoma bayan tagama ganin tonan asiri da tozarci iri iri daga gurin abokan aikinta da jamaar hotel din.

Kuka zuwa Wannan lokacin ya 'dauke mata zuciyarta bayan radadi da tsananin qunci babu abinda take Mata
Dan haka ta tattara kayanta da duka abubuwanta ta fito Kai tsaye ta nufi inda zata shiga motar dazata kaita tashar da zata siya ticket din motar komawa Adamawa.

Tunda tashiga mota zuciyarta tai Mata nauyinda Bata ko iya kuka sbd dole dai Takoma gida ta fuskanci Wannan sabuwar qaddarar data zo Mata.
Har motarsu tayi wuni guda a Tasha tana zaune guri daya sallah kawai ke tada ita har dare yayi suna tashar Basu tashiba sai tsakiyar dare motocinsu suka tashi aka dauki hanya.

A hanya asuba tai musu,Rana tayi musu,yamma tayi sunata Dukan hanya har wani daren yakuma yi suka kwana ahanya sai ana gabanin asuba suka iso cikin garin Adamawa kowa ya sauka.

Lokacin har anfara Kiran sallar asuba a masallatai da dama Dan haka dole da yawansu suka tsaya anan tashar sukai sallar asuba ciki harda ita sbd batasan abinda zata tadda a gidan ba gwara tayi sallar ta nema sassauci daga ubangiji dayake jarabtarta da Wannan rayuwar.

Qarfe 5:24 mashin ya sauketa bakin kofar gidansu datai mamakin ganinsa bude lokacin ta sauka daga kan mashin din tana miqa masa kudin data fidda daga jaka tun a hanya sbd daga ta saka ya miqa masa ta shige gida batareda ta tsaya jamaar anguwa  sun gantaba.

babu kowa tsit anguwar sbd garin da Bai Gama haske ba
ta kinkimi qatuwar Jakarta da akwatinta harma da wasu ledojin ta nufi cikin gidan zuciyarta na tsananta bugu duk da tayi imanin da iyayenta bazasuyi Mata zargin Zina ba tunda sune suke tarbiyanceta Kuma sunsan halinta da abinda zata iya dama wanda bazata iyaba koda kuwa inda yafi Lagos taje.

Ganin Sabon mashin fil a soron gidan yasata kallon kofar cikin gidan zuciyarta na neman karaya sbd fahimtar tabbas kodai Yaya kabiru kokuma Yaya Umar ne acikin gidan.

Siririyar shaqurarriyar sallama ta saki lokacinda ta shigo tsakiyar gidan daukeda kayanta kamar sabuwar bokanyar datayo gudun hijira.
##MAMUH#
#LOVE#
#ROMANCE#
##INAYA A MAJEED ABBI#



IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇

09134848107
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


4
Inna ce dake kokarin fitowa bandaki riqeda mama ta amsa sallamar Kai tsaye batareda ta Gama tantance waye me sallamar sbd hankalinta gaba daya dake kan Mama data riqo wadda ko tsayuwa Bata iya yi Dan jikinta matuqar sosai yayi tsanani a kwanakin.

Sai data fito tsakar gidan da kyau ta dago tana sake amsa sallamar da hadizar takuma tana kallon mahaifiyarta data sauya kamanni gabaki daya sbd tsanani da azabar ciwo.

Hawayene suka ciko idanuwanta da sukai zurfin Rama da irin kukan rayuwar datake ciki ta dago qafafuwanta dasukai Mata sanyi da nauyi ta tunkarosu tana Dan kasa kallon cikin idanuwansu da suka zuba Mata dukkaninsu.

Inna da qafafunta suka kusa sakewa sbd tsananin mamaki da faduwar gaba
A 'dan rude muryarta na gwamutsuwa tace"

Hadiza kece Wannan a tsaye???

Jin hakan yasa mama da Bata gane kowa sosai ta Dan sake riqe hannun innar tana bude idanuwanta ko zata sake ganinta da kyau

Sai idanuwanta suka sauka kan tsohon cikin gaban hadizar
Ta Dan motsa kadan tana bude Baki cikin sanyin ciwo tace"

Lami?

Kasa amsawa Inna tayi sbd idanuwanta data kasa daukewa kan tsohon cikin Hadizar.

Lami?
Wace hadizar Kika ambata?
Hadizata ce tadawo?
Itace Wannan a tsaye?

wani busasshen yawu Inna ta hadiye tareda sake riqo mamar da kyau sbd hannuwanta dataji suna sanyi da daukar rawar tashin hankali mugun ganin datai safiyar fari.

Dakyar ta qarasa da maman kofar dakinta tana kokarin kwantarwa kan shimfidar datai Mata a wajen
Maman ta Dan janye tana waiwayowa ta kalli hadiza da har lokacin take tsaye a inda take cikin mutuwar jiki da qamewar zuciya.

Hadiza?
Hadiza kece agurin tsaye?

Sai alokacin ta daqo qafafunta ta janyo jiki ta qaraso gaban mamar ta zube tareda fashewa da wani irin kuka dukkanin zuciyarta na Mata wani irin radadin qunci da damuwa da baqin ciki.

Kukanta ya tabbatarwa da maman tabbas hadiza ce kuma cikine ajikinta ta samo ta dawo dashi.

Cikin rawar murya ta firgici Inna tace"

Hadiza cikine ajikinki?

Ba musu ba Jan dogon yanayi ta dago jajayen idanuwanta ta kasa kallon innar ta bude Baki murya a shaqe tace"

Eh.

Hadiza Ina nufin ciki fa na haihuwa?

Kuma amsawa tayi da "eh..

Hadiza daga Lagos fa kikaxo da Wannan cikin.,

Aure kikai acan bamu saniba?

Girgiza kai tayi ahankali tareda cewa"

Aa inna,Amma wallahi tallahi......

Zubewar innace da sautin salatin Yaya Umar Mai qarfine yasa maganarta yankewa hankali tashe ta dago tana kallonsa idanuwanta jajir.

Inna gurin mama ta nufa tana Kiran sunanta,

Aishatu?
Aishatu? Aishatu Dan Allah karki kashe kanki sbd wannan mugun abun kunyar da hadiza tadauko,

Innalillahi Aishatu Dan Allah karki tafi ki barni banida kowa,
Malam ya tafi ya barmu ke kadai Kika rage karki tafi ki barni.

Kuka Inna ta fashe dashi tana Kiran sunan inna data jima da somewa.

Sabon tashin hankali hadiza tasamu kanta aciki
Da sauri tayi kan maman itama tana kiran sunanta cikin mummunan mawuyacin hali sbd ita kanta tanaji batada lafiya.

Wani Mummanan Marin Rashin Imani da baqin ciki Umar ya sauke Mata lokaci daya Yana kallonta a qazance ransa a matuqar bace yace"

Karki kuskura ki tabata,
Shekara kusan biyu kena bakya gida
Bakizo musu da kudin dakikaje nemaba sai tsohon cikin banza¿

Gashinan Zaki kasheta lokaci daya da baqin ciki,

Tashi na daina ganinki wlh kafin na illataki daga ke har abin banzan da kike dauke dashi.

Yanda yayi maganar a tsananin fushi da bacin Rai har Yana sake yowa Kanta yasata Jan jiki tayi can gefe tana wani irin kukan zuci Mara sauti.

Kwasar mamar sukayi sukai cikin daki da ita sai firfita Inna ke Mata tana kuka Wanda yake na firgici da tsoron halinda Aishatun zata shiga dakuma zallar baqin cikin al'amarin da hadizar take tafe dashi.

Duk dubarunsu da ruwa dasuka ringa shafa Mata Bai saka ta farfafo saima qarasa rikicewa sosai da jikin yayi gabaki daya.

Hankalinsu duka yatashi Dan haka dole Yaya Umar din ya fidda waya yakira Yaya kabiru,
Shima rabon zaai gabansa ne yasashi zuwa gidan tunda asuba sbd ruwan da aka kwana ana zubawa yasashi tunanin gininsa da akeyi acikin gidan da baa kammalaba Wanda yasa ai masa daki daya da bandaki
amarya yakeson yi to anan zai kawota ya gwamutsa cikinsu innar.

Koda Yaya kabirun ya iso tuni innar tayi nisa Amma basuyi yunqurin kaita asibiti ba saima wani sabon tashin hankalin daya barke tsakaninsu sbd ganin hadiza ce silar koma meya samu mamar.

Kabiru buga rantsuwa yayi akan wallahi saita bar gidan da cikin,
Bazasu taba barinta ta zaunaba a gidan baqin cikin rainon ciki da goyon shege ya kashesu mama
hakama bazasu yarda ta Bata musu sunan dasukai gwagwarmayar samarwa kansuba lokacinda take Lagos tana zubarda mutuncinta da qimartaba.

Yaya Umar dinma bayan kabirun yabi akan Takoma inda tafito da cikin.

Rokonsu takeyi tana wani irin kukan tausayi da tsananin quncin datake ciki akan su yarda da ita Bata taba aikata Zina ba Amma Sam babu Wanda ya saurareta saima qara harzuqa dasukeyi da tsananin fushi da bacin rai,Yaya Umar Dukan mutuwa yakeson yi Mata Amma Inna dake kuka sosai ta Hana ta riqesa tana bayyanarda nata fishin itama.

Riqonsu tadawo yi akan su fito da mama akaita asibiti
Nan ne Umar yabi takan qafafuwanta ynaa neman tattakawa a fusace yace"

Uban waye Zaki fadawa akai mama asibiti? Lokacinda kike zubarda mutuncinki kinyi tunanin halinda zata shiga Idan taganki da wanna abun.

Kukanta qafewa yayi alokacin sbd a yanzu mahaifiyarta kawai takeson yiwa bayanin gaskiyarta,
Mahaifiyarta dake cikin mawuyacin hali takeson tabbatarwa Bata lalaceba Kaman ynada suke tunani.

Gurin Inna ta rarrafa tana roqonta akan subarta taga mama Dan Allah.,

Wallahi tallahi Inna ban taba aikata abinda kuke tunaniba,
Inna ku yarda Dani Dan Allah,
Wlh Inna cikina kwanci yayi sai yanzu yatashi,

Inna wlh cikin Salisu ne,Dan Allah inna ke ki yarda Dani.......kuka ta fashe dashi Mai tsananin ciwo tana sauke kanta sbd babu sassauci ko alamar yarda da ita atareda kowa.

Tashin hankalin data samu kanta dawowarta bata dauka zata tadda hakanba.

Duk wani sauki da rahama Bata samu daga yayyunta har innar ba qarshema haka ciwo ya tasar Mata Wanda tabbatar naqudace Amma tashin hankali yakasa barinta tanema guri ta nutsu ko haihuwarce zatazo.

Irin wulaqanci da tozarcin da yayunta sukai Mata bazai taba barin tasamu sassaucin nauyin zuciyarta ba har abada,
Sunkuma tabbatar Mata da wallahi bazata taba rainon cikinba a gidan bare haihuwarsa,
Idanma ta haifesa koko zasusa abasa yasha ya mutu su sun huta itama ta huta da renon 'dan da babu uba hakama shi kansa Dan ya huta da girma a duniya yatashi cikin gori da wulaqanci.

Masiface da tozarci Wanda ya haddasawa maqota sanin abinda tadawo dashi daga Lagos din suka ringa zuba Mata cikin fushi da bacin Rai,

Da yawa wasu sunshigo da sunan duba Inna Dan su tabbatarwa da idonsu cikin shege tayo daga zuwa Lagos....

Bata taba kukan Rashin mahaifintaba da Rashin Salisu kamar ayau datai wunin tsananin baqin ciki da danasanin tafiyarta Lagos sbd da agaban iyayenta cikin ya farfado da babu Wanda zaiyi Mata Wannan yankan qaunar.

Idanuwanta sunyi wani irin kumburi da Bata iya gani sosai.

Daddafawa tayi bayan tasamu dare yayi su Yaya Umar sunbar gidan ta shigo dakin da mahaifiyarta take ta zube gabanta Daqyar sbd tsananin azabar naquda.

Hawaye ne suka gangaro Mata takai hanunta dake rawa ahankali ta dafa na mahaifiyarta tareda rintse ido wasu hawayen na tsananta Mata gudu.

Kuka takeson yi ganin yanda mahaifiyarta ke numfashi ahankali alamar samun sauki saidai bazata kukanba Dan naqudarta tagama zuwa kusa,ta gyara zamanta da qyar tana hada wani irin zufan gaske tako Ina jikinta azababbiyar azaba takeji Dan haka ta damqe hannun mahaifiyarta da qarfi tana sake wani irin gurnanin Nishi tana Kiran sunayen Allah a azabance.

Inna na dakinta kwance zazzabi Mai tsananin gske ya kwantar da ita da wannan babbar masifar data kunno musu Kai Dan haka batasan meyake faruwa da hadizan ba.

Naquda Mai tsananin wuya da azaba takeyi gadan gadan
Tagama jiqewa sharkaf da zufa
hakama mama tuni tafara bude idanuwanta cikin tsananin ciwo,

Tanajin 'yarta na nakuda Kuma Mai wuya da azaba Amma babu abinda zata iya yimata hakama babu Wanda zai taimaka Mata...

Hawaye da 'dacin tausayin 'yartane ya gangaro gefen idonta
ta Dan motsa hanunta dana hadizan yake Kai ta kama hannun hadizar ahankali idanuwanta na zubowa da wasu hawayen masu zafin gaske.

Hadiza taji mamar Amma bazata iya magana ba ko juyowa takalleta saima wani wahalllen Nishin datake fitarwa tana fidda Rai ga rayuwa,.

Jin take da zata mutu agurin wannan naqudar data godewa Allah ta huta da Wannan rayuwar da babu komai acikinta sai qunci da damuwa.

Wani qaqqarfan Nishi ne yafara zuwar Mata Idanuwanta sukai jajir gumin na sake jiqota tako Ina...

Cikin dauriya da azaba tafara Addua sbd sanin adduar mace Mai naquda karbabbiyace inshallah.

"Ya Allah kaine masanin gaskiyata nida abinda zan Haifa,

Ya Allah ka albarki rayuwarsa ko rayuwarta Idan mace ce,

Allah ka tallafi rayuwar abinda zan Haifa ka datar dashi kyakkawar rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwa.

Mahaifiyarta da 'danta Abdul take kokarin yiwa Addua Amma Ina mamar kawai tasamu damar rokarwa Allah sauki jariri ya kunno Kai Kuma adaidai lokacin mama Allah yabata ikon riqe hannunta kyau Dan sassauta Mata radadin datake ciki na kutsowar 'da ya fito ta jikinka.

Gabaki daya jaririn ya fado tareda sake lafiyayyan kukan jarirai ba kakkautawa.

Wani irin numfashi take saukewa da a wahalce tana Kai hannu inda jaririn yake ta dauko ta Dora jikinta.

Daqyar ta bude idonta dakyau ta Dan daga kafar jaririn taga 'ya mace ce
Take wasu hawayen suka gangaro Mata masu dumi,

Duk da hakan ta godewa Allah daya Bata abinda ta haifar Amma taso namijine sbd zaifi samun qwarin zuciyar fuskantar zunde da qalubalan maganar da zaa ringa binsa dasu na Kalmar 'da Mara uba.

Kukan jaririyar ne ya karade gida tako Ina
A gigice Inna ta taso ta fado dakin tana Kiran sunan hadiza.

Da mamaki da tausayi take kallon hadizar tana cewa"

Hadiza ke kadai Kika haihu acikin wannan halin?

Komawa tayi da hanzari ta dauko sabuwar Reza a dakinta tazo ta yanke cibin jaririyar tana kallon fuskar Yar da fitilar hannunta.

Bata iya cewa komaiba sbd batasan Mai zata fada ba,
Rayuwarsu cikin Rana daya Allah ya juya musu akalarta inda yaso dan haka take fatar Allah yabasu ikon cinye Wannan jarabawar.

Ruwan zafi ta Dora acikin tsakar dare tazo ta karba karba Yar ta wanke tas
Ta juyewa hadizar sauran ruwan itama ta lallaba taje tayo wanka tadawo.

Sauran tafasasshen ruwan hadiza ta karba Tasha sosai sbd babu abinci babu komai.

Komawa sukayi suka zauna jigum jigum babu Mai cewa qala.

Hadizar zaune take bakin shimfidar mama Idanuwanta dake kumbure ta zubawa jaririyar tana kallo duk da acikin duhune Bata ganin komai.

Hannu mahaifiyarta taji akan kafadarta
Ta juyo ahankali idanuwanta na Mata nauyi da radadi ta kalla maman cikin duhu ta bude Baki jikinta matuqar sanyaye muryarta a shaqe tace"

Mama 'ya mace ce na Haifa.

Wani sanyayyan numfashin da Baya fita sosai maman tasaki tareda janye hannunta kan hadizar ta bude Baki daqyar cikin yanayi na majinyaci Mai tsananin Jin jiki ta Kira sunan Hadizar.
##MAMUH#
#ZAFAFABIYAR#
#LOVE#
#ROMANCE#
#INAYA A MAJEED#
#AYSHATOUH#
[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


5
Daqyar ta iya furta

"Hadiza Allah zai zama gatanki,
Allah zai raya Miki 'yarki cikin Aminci inshallah.

Allah ya Raya zuriarki ya sanyawa zuriarki albarka kinji¿

Hakama halima ki kula da ita tamkar uwar data dauki cikinki ta haifeki sbd dagani harku har abada bamuda abinda zamu saka Mata dashi akan halacci da kaunarta garemu,
Batada kowa saiku ku sauke nauyin uwa mahaifiya akanta kinji hadiza.

kasa kuka tayi sbd yanda zuciyarta taso tsayawa cak daga bugawa da sanyin kalaman mahaifiyarta,

Tunda mutuwa ta dauki mijinta Bata taba samun kyakkawar kalamiba daya taba zuciyarta sai yau da mahaifiyarta ta furta matasu adaidai lokacinda duniya da kowa ya juya Mata baya ana gudunta akan abinda daya sameta.

Cikin rawar murya dake son bayyanarda kukan dake kokarin yiwa kansa iso tace"

Mama kin yarda da bazan taba aikata abinda ake zargina dashiba???

Mamar Bata iya mgna ba saidai gyara kanta tayi ahankali tana rufe Idanuwanta dake lumshewa da kansu...

Kalmar shahada take kokarin furtawa a kakkarye
Hadizar naji ta tabbatarwa da kanta rasuwa mamar zatayi
Cikin sanyi da qarfin zuciya ta Bata sauran Kalmar shahadar
Cikin saa maman ta karba ta qarasa daqyar sbd Rai dayazo gangar fita.

Wata masifar a rayuwa fin karfin wata masifar take,

Idanuwanta da zuciyarta ne suka bushe Mata alokaci daya
Saidai wani irin gagarumin nauyi daya tokale zuciyarta ya tsaya a maqoshinta.

Hannnunta na cikin na mahaifiyarta ta cika,
Rintse

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

1 year ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

1 year ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment