Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baida laifi kiyayyar ki ta tsaya kaina kar ta shafi abinda ke jikinki,
ase Allah ya mana kyauta ke kuma ki butul ce harda kukan ki toh yanzu gaya min me kike so".

Cikin kukan ta matsa tare da zubda k'ollah tace.

"Dan Allah kayi hak'uri kar ka gayawa kowa plss Na tuba kasa ya zubar min da cikin ni banson haihuwa wlh ni dai a zubar da cikin tun ba wanda ya sani ma".

Ido ya zare a tsorice a hankali ya kuma jawota jikinshi cikin lallashi ya had'a bakinshi da nata kissing d'inta yayi da kyau sannan ya tsare ta da ido murya a raunane yace.

" Kin san sanda cikin ya shiga ne? kinsan me zaki haifa ne? kinsan rayuwar da zaiyi?
Ko kyau tar da rabbi ya mana kika raina ki nitsu Khadija cikina fa kike cewa wai ince a zubar ciki na nefa d'ana nefa kinsan wahalar dana sha kafin na sameshi a ranar muka samu cikin kin manta a sume na wuni a wannan ranar d'an nanefa na halal kike cewa a zubar me zaki gayawa mahalliccin mu?".

Ita dai kauda kai tayi tare da cewa.

"Bana so wlh ko zan Haihu ba da kai ba kam na haihu da kai nace k'anina ne mijina ko nace kaninah ne uban yarana".

Sosai zantu kanta suka bata mai rai cikin tsura mata ido ya nunata da yatsa jikin shi har rawa yake yana fidda numfashi da k'arfi yace.

" Ina binki ne ina lallab'a kine dan ke macece kuma macce mai rauni ce da tawayan tunani Ku mata akan biku a hankali dan a fahimtar daku amman na lura abin naki rainine,
dan haka ya zama dole na gyara miki tunanin ki,
kiji da bakina wlh kar bakin ki ya kuma furta Kalmar zubda cika in kuwa kikayi gagganci furtawa wlh zaki gane kuren ki,
cikina dai yana jikin ki wlh ko kallon banza kikayi wa cikina zaki gane kuren ki wlh kar ki k'ureni zan miki abin da bakya zato".

Baki ta tura da kame jikin ta dan ganin yadda yake bala,i kamar zai doketa har jikin shi na rawa har cikin ranta taji tsoron shi ya rufeta cikin sanyi ta bud'e baki a hankali tace.

"Dan Allah kayi hak'uri a zubar da wannan in yaso gaba".

Bakinta tarufe tare da rumtse ido tasa hannu ta tare fuskar ta jin wani tsawa daya watsa mata ga hannushi da ya daga zai yarfa mata mari cikin rawan baki tace.
" wayyo Allah na wayyo Anty na".

Dai-dai lkcin kuma Anty da Sulaiman da Anty Ray da suka had'u da ita a k'ofar gida suka taho tare,
suka shiga ga ninsu yasa ya sauk'e hannushi.

Suna shiga suka tsaya kanta suna mata sannu cikin kula Anty ta kalleshi a hankali tace.
"wai meke damun ta?".

Da sauri ta kalleshi cikin yanayin dan Allah kar ka fad'a sannan ta juya gun Anty a hankali tace.
" a a fa kawai murace yanzu ma tare zamu koma in ruwan nan ya k'are".

Ita dai Anty shi take sauraron ganin haka yasa yace.

" Anty ciki ne take dashi Amman ba wani matsala".

Cikin mmki Anty Ray da su Anty suka zuba mata ido ikon Allah ciki Allah mai iko.

Ita kam sake kifa kai tayi cikin kunya da takaici sai kuka ta saki cikin sanyi,
bata sake dago kanta ba har ruwan ya k'are Dr yazo ya cire aka sallah mesu suka koma.

Suna komawa Rayhana ta shiga gun Mamin su cikin farin ciki da dariya ta kalli Mamin dake konce gefen ta tace.

" kai Mami gsky Mahmoud dinki sai Allah wlh kinga gwara da akayi mishi Auren nan yanzu da ba,ayiba ta ina cikin nan zai zo,
gashi tun basu tareba sai ciki wlh Abba yayi tunani dan ya toshe hanyar b'arna da ya yarda yamishi auren".

Cikin mmki Mamin ta mik'e zaune tana kallon 'yar tata
tace .

"Ke wai tsaya mana waye mai cikin?".

dariya tayi cikin sanyi tace .

" Mami matar Mahmoudu kinda ke da ciki".

A kufule tace.
"Wacce d'aya a cikin su?".

Ido ta tsura mata ganin yadda ta sauya a hankali tace.

"Khadija ce,
Amman Mami ya naga kamar abin bakin ciki na gaya miki?".

Aiko Mami kam a take sai zufa da rawan jiki cikin bala,i tace.

" Toh dama wanne bakin cikin ne ya wuce wannan da Abida ne da cikin ai nanne abin farin ciki tab lallai
wato ita har ta samu gun haihuwa tun yanzu har ta rarumi ciki wlh wannan cikin kam badai ta haife shi ba,
Sai na bada cikin ai bazata ma sabu ba".

Ita kam Rayhana dafe kirki tayi tana kallon uwar tasu cikin tsoro da ker ta bud'e baki da nufin yi mata nasiha aiko tai kanta da bala,i
harda cewa ta bace bata maza ta tafi gidan ta mgnar ba tata bace.

Haka ta tafi tana mai jin tsoron uwar tasu daga baya ta kira k'aninta ta shaida mai k'udurin mahaifi yarsun.

Shi kam Mahmoud abu ya had'e mai tunda itama mai abin bata sonshi sannan ga Mamin shi ma bata son cikin ga fiti nan Abida tunda taji Khadija nada ciki take mita ai ita kam tunda yana sonta gashi har ta samu ciki watoh ita kuma ko oho haka yasa take nace mai tai tace mai itama cikin take so.

Haka Abu yayi ta juyawa Khadija dai ya sa mata takun kumi ya kuma hanata ko motsi mai k'arfi Mami kuma ba wanda yasan shirin ta sai Allah sai Abida da Adda Asabe.

Yauma kamar kullum da safe Mahmoud ne konce yana baccin gajiyar da Abida ta tara mai,
cikin baccin yaji ta ta konta bayan shi a hankali tasa hannu ta shafa fuskar shi cikin rad'a tace.

"Hamma ka tashi Baby nake so".

Mik'a yayi tare da juyowa gareta cikin baccin ya jawota jikinshi a hankali yace.

" ke bakya gajiya ne shifa cikin nan ba zafin nema ke kamo samu ba kiyi ta Addu,a zaki samu kinji ko".

Mak'aleshi ta kuma cikin kirsa tace.
"Ko ban samu baby ba ni dai na isarwa mijina na kawar mai da buk'a tarsa".

Kara janta jikinshi yayi cikin ranshi yake cewa.
" inama Khadija ce mai jarum tar nan da yaji dad'in rayuwa amman sai sab'a nin haka ita wannan ko zai shekara gareta baijin gamsuwa sai dai kawai yana rege zafi,
yayin da ita kuma Khadija cikin dare daya take k'anwar mai da duk wani k'ishin sa ga ciki ammam ita bata so,
mai son kuma bata samu ba,
ita kuwa Abida ako da yaushe hamdalah take da Allah ya bata gwaranzon namiji ".

A haka ya jawota suka shigewa juna shima rashin Khadija yasa dole ya saduda da ita,
da ker suka sahirta wa juna sannan ya shirya ya nufi gida.


Yana na shiga gidan Khadija na jinshi ta koma cikin d'aki ta konta ta had'e fuska,
Anty dake lura da rashin kula da take nunawa mijin nata cekin
juya kai ta zauna gefen ta cikin fad'a da nasiha tace.

" Khadija anya kinsan me kikayi kuwa shin kinsan cewa shi namiji tamkar yaro yake yadda ka horeshi a haka zai tafi
shifa namiji dan son a nuna mai kula ne yanzu ke kinga gudun shi da kike alherine a gareki,
wlh duk sonki da yake kina dab da rasa zuciya sa dan waccar yarin yar ta gama gane logon sa ta kuma bishi a yadda Allah ya halicce shi domin ko dole ne ga duk wata ya mace taga tayi iya yinta ta samarwa mijinta gamsuwa Khadija ki kula ki gyara tun kafin lkci ya kure miki,
sam bakya bawa mijinki kula sai raki da mita da kike nuna mishi dole yana sonki zaiyi nesa dake tunda bakya bashi kulan da yake bukata daga gareki kinga ko dole yaje inda za,a kula dashi".

Haka tai ta mata fad'a da nasiha ita kuwa sai shiru tayi tana rufe da ido jin yayi sallamah a parlon ta fice ta tafi d'akin ta ita kuma Khadijan dama a d'akin su ita da Nabila take.

Bayan sun gaida da Antynne tace.
" ka isa tana d'akin su"

Toh yace tare da wucewa cikin d'akin a hankali ya taka har zuwa.........

By Garkuwan FulaniπŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 4⃣4⃣to4⃣7⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Pure moment of life writters
p.m.l.w


hankalinsa kwance ya kutsa cikin d'akin kwance ya hangeta kan 3siter kanta asama idonta alumshe fuskar ta tayi fayau lip d'inta ya kara ja a nutsu ya kalli k'irjinta ya cicciko sosai ajiyar xuciya ya sauke had'e da lasar leb'ensa cikin xuciyarsa ya furta
"ina sonki khadeeja!"

cikin takun isa da kai ya tunkareta
jin tafiya da shak'ar k'amshin datake matuk'ar so yasa ta mik'e xumbur tana kallonsa tafiyar da yakeyi ce ta k'ara k'ular da ita

yaro k'arami yaita abin manya taja d'an k'aramin tsaki ta kauda kai murmushi yai ya xauna kan kujerar had'e da janyota jikinsa lumshe ido tayi tana shak'ar k'amshin jikinsa hannunsa yasa a hankl yana shafar gashin kanta xuciyar shi fess khadeeja na d'auke da cikinsa lumshe idon yai shima cikin kuxari yasa hannunsa yana shafar cikin yana jin tsananin sonsa

cikin kasalalliyar murya ya furta
"babyna hop kina kular min da kanki da kuma babyna na jikinki?"

haushi kalamansa suka bata tayi shiru dan batasan kalan amsar da xata bashi ba tarasa yarda da wannan lamarin ita ce wai Khadeeja d'auke da cikin k'aninta Mahmoud
takaici taji ta ko ina kamar xatayi me ta cije muryar ta na rawa ranta ab'ace musamman jin hannunsa datayi yana shafar cikinta shafa ta lallashi da kiyayewa
a k'ufele ta so yin mgn da kyar ta daure ta saita kanta cikin wahalalliyar murya ta takaici tace

"Mahmoud plx bana son cikin nan axubar dashi in yaso gaba sai.....!"

cikin wata raxananniyar tsawa ya tunkud'eta jikinsa ya mik'e idonsa ya firfito
"enough khadeeja !"
yana huci makar wanda yai dambe da xaki ya k'ara xare mata manyan idanuwansa da b'acin rai yasa suka fara rinewa jaja jaja
"abinna ki yayi yawa k'iyayyar ta kai ki kyamaci d'ana !? wanda yake jikinki
meyasa baxaki gane bane kin san haka xata faru ? idan aka xubar kina da tabbacin sake samun wani !? ke kika bawa kanki shi ? ya isa ! ya isa ! bazan yarda da wannan tsarinba wallahi ! wallahi ! zan iya jure komai banda tab'a cikin jikinki ! "
takaicine yasashi kakarewa bai k'arasa maganar ba illa yarfe hannuwa daya dink'a takaici yasa ya kaiwa kujera naushi

itakam tunda ya fara fad'an taga ya juye mata kamar bashiba ilahirin jikinta kyarma yake kanta ak'asa tana xubda k'walla gefe guda na ranta kuwa suya yake k'aninta na surfa mata fad'a irin wannan kamar wani ubanta d'aya gefen kuma cike yake da matuk'ar tsoranshi dan batayi tunanin Mahmoud na rikid'ewa ya koma haka ba

tsura mata ido yai xuciyar a k'untace lallai Khadeeja bata k'aunarsa tunda har bata son cikinsa wanda yake jikinta gabansa ya fad'i ya lumshe ido harga Allah yana sonta amma baya jin xai jure wannan yanayin yaushe xata soshi har taso d'ansa dayake jikinta ??

yana girgixa kai yai mata magana a hasale
" kina jina !? "
kai ta d'aga a tsorace
"naga take takenki akan cikin nan yau xuwa gobe xaki tare a gidana ni xan kula da abina inyaso duk randa kika saukemin shi ki kama gabanki ! sannan ki sani bake kad'ai bace mace da xan xauna kina min sakarcin da kika ga dama !"

fuuu ! ya fice hawayen daya mak'ale ya gangaro mata ta fashe da kukan maganarsa wai xata tare a gidansa itakam taga ta kanta daga wannan sai wannan abu iri iri xuciyar tak'i tahuta.

yana fita b'angaren Abba yayi xuciyarsa a hasale lallai rainin khadeeja yai yawa xai saita ta kam dan baxai jure tab'a masa gudan tsokansa gudan jininsa datake shirinyi

sallama yayi Abba ya amsa ya shiga falon kansa akatsa d'ago Abba yayi yana kallonsa dan ya fuskanci yana tare da damuwa xama Mahmoud yayi kusa da mafhaifin nasa ya gaisheshi cikin kulawa ya amsa yana son karantar damuwar d'annasa suna gama gaisawa ya fara sosa kansa yana son yiwa Abba maganar yarasa ta ina xai fara
d'an k'aramin murmushi Abba yayi ya fuskanceshi
"yadai Mahmoud?"

cikin in ina ya tattaro nutsuwarsa ya fara magana
"Abba ina .. ganin.. tunda ... me xai.. hana khadeeja ta tare tunda itama Abida ta dad'e da tarewa ?"

murmushi Abba ya kumayi ya girgixa kai dan ya dad'e da tunanin haka dama ya gaji da xirga xirgan Mahmoud d'in kwara abashi matarsa suje cen suk'arata

"hakane Mahmoud nadade ina wannan tunanin cikin wannan satin nake son ta tare"

ajiyar xuciya Mahmoud d'in yayi ya mik'e har yanxun xuciyarsa turiri kawai take bak'in cikin abinda Khadeeja takeson aikatawa gudan jininsa ransa b'ace ya bar gidan ranan kam duk jarabar Abida sai da ta kyaleshi dan Rasa gane kansa tayi.


cikin satin kam ta tare ranan da y'anuwa suka rakota Anty ta dad'e tana mata nasiha akan ta bi mijinta kada tabiye xuciyarta haka suka barta tana rusa kuka tunani kala kala ga babban takaicinta wai ankawo ta gidan Mahmoud k'aninta ! ta k'ara rusa kuka tun tanayi har muryar ta dishe tana kukan har bacci ya kwasheta cikin dare ta farka sbd batayi shafa'i da wutr ba a hnkl cikin nutsuwa ta mik'e ta kunna wayarta taga agogo 2:40 ta mik'e ta shiga toilet ta d'aure auwala tana mmkin rashin xuwan Mahmoud tada sanshi kamar maye yau gata a gidanshi bai xo ba ? tab'e baki tayi tace "shiya sani na ma huta da jaraba" tai sallarta ta sauya kaya tai addu'a ta kwanta bacci mai nauyi yai awan gaba da ita


k'aran kiran sallah ne ya tasheta ta mik'e bayan tayi addu'a ta shiga toilet ta d'auro alwala tai raka'atainil fijr sannan tai sallan asuba tana gama azkar bacci ya kuma surarta

wajen 11:00 taji maganar Abida sama sama a hnkl ta bud'e ido had'e da addu'a ta mik'e daga kwancen da take tana kallon Abidan tsaye akanta tana murmushi
"Anty Khadeeja ina kwana ? ga breakfast d'inki nan yakamata ki tashi kici kinga bake ka d'ai bace"

kallon mmk Khadeeja tai mata ya akayi Abida ta xama haka ? yarinyar da ko kallan arxik'i bata mata
d'aga mata kai khadeeaj tayi Abidan ta fice mik'ewa tayi akasalance ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta xauna ta fara breakfast d'in har ta gama kwanciya ta k'arayi a hnkl taji kwanciyar ta isheta
d'an k'aramin tsaki taja ta mik'e ta koma falonta k'amshin data ke so taji a hnkl ta lumshe ido tana bin wajen da take jin k'amshin na fitowa har babban falon gidan muryar Mahmoud taji da Abida suna kyalkyala dariya gabanta taji yayi mummunan fad'uwa labulen falon ya d'aga hangosu tayi cikin wani yanayi na jin dad'i

wani irin xugi taji xuciyar ta nayi ta juya tana k'ok'arin barin wajen sbd bak'on yanayin data tsinci kanta ciki wanda tarasa na menene ga uban jiri data ji lokaci d'aya ta juya kenan taja k'afarta da tai mata nauyi gum ta bige gefan goshinta
k'aran buguwar sukaji suka fito dukansu shida Abida.


plc plc kuyi hakuri da wannan kad'an ne dai gobe inshaa Allah xan cigaba da gashi nagode sosai fans da soyayyar ku


By
Garkuwan fulani
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ *NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 4⃣8⃣to5⃣1⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

pure moment of life writters
p.m.l.w

*K'aunar ki a raina bata da adadi har kullum ina alfahari dake Ummee Garkuwa ke tawace ni takice rabbi ya sadamu a jannatul Firdausi*

```Bazan manta da k'iba kun zamo ni Na zamo Ku ina alfahari daku Khaleesat haydar
Anty Fauzo Ummu Khamal Dr Ruk'ayyat Aysha A Muhammad Rufaida Yusuf Jannart lamido```

sannu kawai suke jera mata shida Abida runtse idonta tayi sbd kayan dake jikin Abida na nuna ilahirin siffarta kanta kawai ta d'aga musu ta ja k'afarta ta bar wajen xuciyar na mata wani irin tuk'ik'i data rasa na menene
tana xuwa kan gadon ta tafad'a a wahale tana mmkin sauyawarta
wani uban tsaki taja had'e da runtse idanuwanta hangosu tayi a yanayin data gansu da sauri ta bud'e ido tan jijjiga kanta sam tarasa wanne kalan tunani xatayi ta samu sauk'in wannan yanayin data fad'a wanda tarasa gane kansa ga uban xogi da gefen goshinta ke mata.



washegari jikinta asanyaye ta tashi tarasa gane yanayin data ke ciki rabonta da Mahmoud tun jiya data bige sukai mata sannu kanta ta dafe tana kallon breakfast d'in da Abida ta kawo mata tun d'axu da safe.
jikinta ba kwari ta tashi daga xaunen da take ta shiga toilet tai wanka ranta ajagule.


tunda Khadeeja ta tare Mamy ranta ke suya abin na matuk'ar damunta tarasa gane inda wannan k'addararren aure xaije uwa uba cikin da akace khadeejan nadashi sam ko kad'an bata k'aunar wannan cikin hnklinta tashe take kai komo tarasa hanyar da xatabi ta warware wannan d'aurin gwammon na auren Khadeeja da d'anta Mahmoud anty Ray ce tai sallama da kyar Mamy ta amsa tana kallom fuskar ta hannunta tasa ta d'auki hijab ta kalli anty Ray tai mata alama da ido na sutafi ba musu anty Ray tabi bayanta har suk fito haraban gidan inda motocin su suke kai tsaye mota mamy ta shiga anty Ray ta shiga driver yaja su suka tafi gidan Mahmoud d'in dan xuciyar mamy takasa nutsuwa sai taje daga kalan xaman da sukeyi babban burinta taciwa baxawarar yarinyar nan mutunci ta hkr ta bar mata d'anta dan tasha alwashin yau yau d'in nan sai Mahmoud yasaketa tagaji da tafasan da xuciyar ta ke mata

akan hanya Anty Ray taiwa Mahmoud test akan lallai ya fice ya bar gidan kafin mamy tak'araso.

yana ganin test d'in ya maxa ya bar gidan hankalin sa atashe yarasa gane kan mahaifiyar sa tak'i hak'ura da wannan lamarin na aurensa da Khadeeja.

driver na tsayawa afusace ta bud'e k'ofar motar ta fito tun kan tashiga gidan ta fara kiran sunan Mahmoud a k'ufule Anty Ray cikin sanyi da mmkin sauyawar mamy lokaci d'aya akan auren Khadeeja da Mahmoud da tayi
kai tsaye b'angaren khadeeja ta nufa tana kwalawa Mahmoud kira dan tasan mayen ta ne xuciyarta na bata yana cen d'akinta yana maitar tashi

kamar daga sama Khadeeja taji kiran tana barci dan har cikin d'akin mamy ta shigo tana surfa masifa tana kwalawa Mahmoud kira
a hankali Khadeeja ta bud'e idonta dayayi ja alamun bacci ne sosai acikinsa
wani wawan mari mamy ta d'auketa dashi wanda yasa Khadeejan wartsakewa daga nannauyan baccinta a gigice ta mik'e had'e da sakin wani bahagon kuka me ban tausayi Anty ray ma da Abida mmkin marin sukai fuskokin su alamun tsoro suka k'ura musu ido cike da tausayin Khadeeja
nuna mami tayi da d'an yatsanta cikin k'araji da masifa tace
"uwarki xatai sallama ki kasa amsa mata ?? tabbacin baki da tarbiyya ko ? tun yaushe nake kwalawa d'ana kira kina ji kinyi biris dani, to ni ce uwar Mahmoud ayau kuma sai ya rabu dake tambad'ad'd'iya tarasa wa xata aura sai k'aninta har da d'aukan ciki dan tsabar tambad'ewa,
na tsani wannan k'addararren auren naku kuma ayau xaa warwaresa dan bazan iya cigaba da xama dake a matsayin matar d'ana ba wllh !"

tak'ara tana fidda huci naban takaici babu abinda ke tashi sai sautin kukan khadeeja mai ban tausayi.
waiwayowa mami tayi tana kallonsu Abida da suka tsura mata ido
"ina yake shima shanyayyen?"
girgixa mata kai Abida tayi tana jin ba dad'i aranta dan tasan muddin aka tab'a Khadeeja tofa bata tab'a gane kan mijinta shiyasa ko kad'an batasan wannan hayaniyar yanxu
"mami ya fita cen gida wajen Abba kuma bana jin xai dawo da wuri"
wata wawar ajiyan xuciya mami tayi "sai ya dawo yau yasame ni shima dan ubansa yau sai ya rabu da tsohuwar guxumar nan !" tana cikin masifar Khadeeja na fidda kukan takaici kuka na fidda sauti na ban tausayi ga duk mai sauraronta

wayar mami ce tayi k'ara number Abba tagani a k'ufule ta d'aga itafa ayanxu batak'i aurenta ya mutu akan raba auren Khadeeja da Mahmoud abinda taji abban na fad'ane yass jikinta ya sanyaya ta kashe wayan tana fidda huci da kuma mmkin abinda Abban yace mik'ewa tayi ta watsawa Khadeeja mugun kallo "kisani tsohuwar bazawara kik'a tunanin wani xawarcin nan gaba zanje na dawo duk dare yau sai dai ki kwana gidan ubanki yarinya sai kace mayya !?"

fuuu ta wuce anty ray da Abida suka bi bayanta mota ta fad'a tana takaicin rashin samun Mahmoud d'in a gida girgixa kai Anty ray tayi tace "mami yakamata ki fuskanci yarannan ki duba damuwarsu, auren nan daga Allah ne kina kallon rabo har ya ratsa..."
katseta mami tayi
"rabon banza me ake da rabo irin wannan idan ina raye baxata haife wannan rabon ba"
shiru anty Ray tayi dan abin yafi k'arfin ta suna komawa gida lbrn da Mamy taji ya gigita sosai Abba ne ya sa ta ta xauna ya fara mata jawabi
"kinga abinda akaiwa Amira ko ? baxan yarda ba sai na d'au mataki UWAR MIJINTA tai mata dukan tsiya har cikin jikinta ya xube sannan ga gociyar k'ashi a hannunta duka na fitan hankali kamar ba mutun ba kalleta fa !"

wani irin masifaffen yanayi mami ta shiga lokaci d'aya tana kallon amira da fuskarka tasha bandage tana fidda kwalla ilahirin kamanninta sun sauya baxakace Amira y'ar gayu ce akai mata wannan mummunan dukan kuma ma wai uwar mijinta wani kuka mai k'una ya kufcewa mami kasa jure kallonta tayi gaba d'aya jikinta amace yake xuciyarta na harbawa da mugun sauri takaici da bak'in cikin dataji yanxu bata tab'a tunanin akwai irinshi ba,

jikin Abba a mace ya mik'e ya fice daga falon yana ayyana shi kad'ai yasan irin matakin da xai d'auka kan mutanen nan

wani bahagon kallo anty ray takewa mami tana girgixa kai kwalla na fitar mata
" mamy kin gani ko ? ishara ce wannan kome ? kin daki y'ar mutane anyiwa taki dukan tsiya kina k'ok'arin xubar da cikin y'ar wani an xubar dana taki y'ar,
duniya kenan yanxu sakayya nan danan take xuwan wa mutun kanayi xa ai maka ninkin ba ninki wanda Allah keso yake nunawa ishara"
ta mik'e kwalla na xubar mata tana kallon Amira da itama kwallan takeyi jikin mami asanyaye take sauraron Anty ray xuciyar ta asanyaye.

yana kallon sun fice daga gidan ya shigo hnklinsa atashe kai komo ya fara yi yana son sanin halin da Khadeejan sa ke ciki ya na matuk'ar k'aunarta da kyar ya iya jurewa rashin ta na kwana biyu kasa jurewa yayi jikinsa na rawa yai b'angaren ta sautin kukanta ya hautsina masa xuciya wani irin yanayi na b'acin rai ya xiyarceshi kai tsaye wajenta yayi yana jin takaicin fitar kukan nata dayake tab'a masa xuciya.


by
Garkuwan fulani[5/14, 5:15 PM] Miwasmiti Author: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg
5⃣2⃣to5⃣5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

pure moment of life writters
p.m.l.w

*Wannan shafi nakine ke kadai Aminiyar kirki Fiddausi Sodangi Allah ya bar zumunci*

cikin wani irin taku na k'asaita ya shigo cikin d'akin ganinta a takure cen k'arshen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta kukan ta na fita cikin wani sauti me hautsina masa xuciya
kai tsaye kusa da ita ya k'arasa ya xauna gefenta had'e da janyo ta jikinsa k'amshin turarenaa data ke so ta shak'a shiya hana ta hankad'esa dan mugun haushin sa
take shi akanshi akai mata marin data hango taurari
duk da haka sai da tayi yunk'urin kwace kanta ta kasa
dan ba k'aramin ruk'o yai mata a k'urjinsa va hannunsa ya sa ya xuge xif d'inta
ya cusa hannunsa cikin jikinta yana shafa gadon bayanta
had'e da shafar fatan jikinta mai laushi da tsantsi kasa mata magana yayi sbd
kukan ta na sa jin xafi
musamman yasan dalilin faruwan kukan
yasan mami ce cikin jarumta da dauriya had'e da jin dad'in shafar da yakewa fatarta data fara sashi cikin wani yanayi ya fara magana cikin muryar lallashi
" kiyi hkr babyna ki dink'a kallon komai kamar bai faru ba, laifi nane ni na janyo miki amma kiyi hkr komai xai wuce inshaa Allah,
ki d'auki komai amatsayin k'addara wacce xata xame miki alheri nan gaba ko ma ince ta xama musammaan dan babyn dake jikinki da kuma aurenmu shi kad'ai ya isa yasa ki gane ko mai muk'addari ne daga Allah,
khadeeja babu wani bawa da ya isa ya kaucewa k'addarar sa
tabbasa ikon Allah yafi k'arfin komai Allah ya k'addara ke tawa ce babu wanda ya isa ya rayu dake saini babu wanda ya isa ya dasa miki d'a sai ni babu wanda ya isa ya

2 Comments On NAMIJI BAYA KADAN
avatar
yarima-ummi

12 months ago

Reply

Why won't I download it?

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to yarima-ummi

You have to subscribe for our package before downloading

Please Login or Register in order to submit comment