Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai k'unci
ase bai isa a barta ba sannan wayema mai cewa yana sonta dan naci da mayta ai naga sai a barta ta huta ko"?

Ido kawai ya Auwal da Salma suka zuba mai abin har tsoro ya bawa Ya Auwal din dan ganin kishi k'arara a fuskar k'anin nashi.

Ita kuwa cikin jin dad'i zancen tace ni kamma ba Aure zanyi ba .
ganin zasu raina mai wayyo yasa cikin had'e fuska ya ce
"Ke tashi kike yana parlor na jiranki,
ji yarinya da shirme ke a zatonki barinki zamuyi ki zauna ba Aure "

Mik'e tayi cikin sanyi ta nufi parlon nashi,

Shi kuwa Mahmoud tuk'uru ya rink'a fad'a kamar shine baba kan Auwal d'in,
Abin ya basu mmk ganin haka yasa yace
"Kai Mahmud ko dai sonta kake ne"?

Cikin wata iriyar murya yace
" ehh sonta nake ya Auwal kuma sonta da Aure nake ni zan Aureta wlh itace burin raina".

Cikin mmk Auwal ya bishi da ido itako Salma ba mmk a fuskar ta dan ta dad'e da gane Mahmoud son Khadija yake.

Cikin had'e fuska ya kalleshi yace lallai baka da hankali Mahmoud na yarda yarinta ke cika inaba hakaba ina kai ina Aure Wai shin yaushema ka gama rik'a"?

Mik'ewa yayi cikin murtuk'e fuska Wai shi sai aitacemai yarinta yarinta
Fuska a had'e yace
"Wlh ni dai nasan ni ba yaro bane kuma nasan zan iya rik'e ko mata 4 zan kuma iya wodatar musu sannan da kuke cewa yarinta
Ina dai
Amira k'anwar tace?
Shekara nawa nake bata?
Kuma ina yanzu saura 9 days Aurenta wato ita ba yirinya bace saini"?

A harzuk'e yace,
"can matsa daga nan ita mace kai namiji".

Mik'ewa yayi yana
" sai kuma akace namiji bai da rai ko ba zuciya ne daniba"?

Ganin fad'an zai nisa yasa ya matsoshi cikin dariya yace
"Haba Mahmoud ka bari ko digiri d'inka ka had'a mana tukun
yanzu kai kama san yadda zaka iya kula da mace ne"?

dariya yayi ta irin kumma rainani
Cikin ko in kula yace.
" tsaf zan iya kula da ita har nai mata ciki ta Haihu "

Toh mgnar fa ta girmama ganin haka Auwal ya bishi da ido shiko
Phone d'inshi ya zaro ya kirata
tana d'agawa yace
Khady ki fito mu tafi ina da abin yi".
fita yayi batare daya sallah mesu ba,

Ita kuwa tana samun haka ta dan juyo ta kalleshi cikin sanyi tace

"Kai hak'ura zamu tafi Mahmoud na jirana kuma Azumi yakeyi".

ajiyar zuciya ya sauk'e tare da jin dad'i voice nata yace.
"Ba matsala
gimbiya sai kuma nazo gida ko"

Hmm kawai tace ta mik'e ta fita shima binta yayi suka fito tare shi sai ya tsaya tare da Auwal ita kuma hannun Nabila takama suka yi musu sallah ma suka fita.

Suna shiga mota ya figi motar a guje
suna fita ya juyo cikin had'e fuska yace.

"Kina sonshi ne"?

Tab'e fuska tayi cikin gyatsine tace
" me zanyi dashi ina zan kaishi ai ni ko aurenma zanyi ba irin shi zan Auraba dan yamin k'ank'anta yamin kad'an nifa nafisin namiji mai haiba"?
Shiru yayi bai sake mgn ba Dan ji yake kamar da ganggan take gaya mai kuma dashi take.

Ita kuwa ta dage sai cewa take yara k'anana dason tara mata yanafa da mata yake son k'ara Aure ina zai kaimu ".

Ba tare daya kalleta ba yace

" Wlh ki dena raina namiji ni Na tabbata duk k'ank'antar namiji zai dai cika miki mararki"

Cikin tsoro da kunyar mgnarsa ita har ga Allah ba haka take nufiba shi kuma
Daga nan bai kuma mgn ba dan ya mata daya tamkar da 1000 suna isa gida d'akinshi ya shige yana ta nemawa kanshi mafita tun kafin aimai shigar sauri.


Ita ma Azumin take
5 dai-dai ta shiga kitchen ta had'a musu abin bud'a baki kamar kullum,

Bai shigo ba sai da akayi sallah sannan ya shigo a parlon Anty suka zauna,
Fruit salad ta samai a Cup ta mik'a mai tana
"Gashi kaci Sa,a na regema wlh da shanyewa zanyi,
shi kuwa
Ido ya d'an tsura mata tare da cewa
" ai duk d'aya ne inma kin shanye ni kikewa tanadi gaba,
Cikin rashin gane mgnar da ya nad'e mata tace
"ai yayi dad'i ne shiyasa bazan hanaka ba"

Wani irin kallo ya bita dashi
A ranshi yace Na tabbata kinfi haka dad'i
A zahiri kuwa cewa yayi
"Ngd baby"
Jin haka yasa ta had'e fuska ta bud'e baki da nufin cewa yaro
Shiko gane Abinda take son fad'a yasa cikin sauri ya had'e bakinta da.......

By Garkuwan Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 4⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w


_Dedicated 2 Anty Na Ummi Aysha RUWAN KASHE GOBARA INA sonki a raina_


Manna mata cup d'in yayi a bakinta,
Sanyin cup d'in ya ratsata cikin jin sanyin ta d'an kad'a mai ido alamar zan shanye fa ka rasa,
Shi kuwa ido ya tsurawa fuskarta tare da kafesu kan pink lips d'in ta idonshi yana ganin yadda take motsasu alamar zata shad'in.

Ido ya lumshe tare da sauk'e ayijar hrt ya d'aga mata giransa d'aya cikin alamun kisha,

aiko ta k'ara manne lips d'inta kan Cup d'in shiko ya d'an tura mata yana mai kashe mata ido d'aya,

gaba d'aya ya mace da kallonta shiyasa har baisan sanda ya tura mata shi har ya haura sanan lips d'in ta na saman cup d'in

Da sauri ta janye kanta cikin Sa hannu ta ture nashi hannun ido ta zare mai cikin had'e fuska tace

"Jifa zaka tura min har cikin hanci dan mugunta ai kai ka nuna bai dameka ba".

Murmushi ya d'anyi dan ganin ya cika mata lips d'inta da fruit salad d'in
cikin lumshe ido a ranshi yake ina ma da Aure a tsaka ninsu wlh da da harshensa zai tsotse na kan lips d'in nata sai dai kuma ba dama.

sai kuma ya d'an sun kuyo yasa hannu saitin kan lips d'in nata a nufunshi in ta barshi da tafin hannu shi zai goge mata.
Ita kuwa ganin hakan yasa ta mike tana
" Allah ko Mahmoud ka rainani"

Shi kam murmushi yayi a ranshi ko cewa yake
"Ai da sauran raini tunda har yanzu ban zamo shugaba a gareki ba"

Cup d'in ya d'auke ya sa harshensa yana lasar ta inda ta shad'in
Ita kuwa wonke jikinta tayi sannan ta wuce d'akin
Mami ganin shuru bata shigoba ya sashi mik'ewa ya fito rik'e da pilet d'in abinci
d'akin Mamin ya lek'a cikin kauda kai yace
"Khadija ana kiranki a phone"
juyowa tayi tare da cemai "waye ne"?

Kafad'a ya d'aga tare da tab'e baki yace
" Na sani? ke da buhun samarinki tarukuce zallah daga masu k'aton ciki sai masu bak'in fuska".

Mik'ewa tayi ta fito tana
"Wlh fad'i kake kaima kasan wlh ba Na kushewa a cikin
ni suma bawai suna gabana bane a a kaiwa banson wula k'anta mutun ne".

Tsaki yaja tare da binta a baya yana tsurawa k'ugunta ido ganin yadda yake rausaya kamar da gangan take mai abin ma yake gani.

a parlon Anty cikin kauda kai yace
" kije ki kwanta ki huta dan dare yayi"

hara ta cilla mai tare da cewa to
Hamma Mahmoud ai dole kai guda ai dole na kwanta ko banjin bacci"

K'arisa shigawa yayi yana shafa sajen fuskarsa da dan cika izza yace
"Ai na kaine dan girma ne dai Allah ya bani tunda yayini NAMIJI".

Tab'e fuska tayi tare da cewa "Hmmm ni ina da abin yi Dan wonka nake son yima"

Juyawa yayi ya fita tare da cewa
"Toh sai kin gama kimin flashing akwai mgn"

yana tafiya d'akin su Abincin ya danci sannan ya watsa ruwa ya dawo parlon ya kwanta kan 3 str
shiru yana jiran yaji kiranta amma shiru har zuwa kusan 9 sannan ya kirata yana mai tunanin ko wani mayenne ya tsareta da surutu,

aiko yana kira bata d'aga ba har saida ya kuma na 3 sannan ta d'aga
yana jinta
rai a bace yace
"Dawa kike mgn tun d'azu?
Kuma me yake gaya miki?
Sannan ba nace in kin gama kimin flashing ba"?

tsaki ta ja sannan tace " Dan Allah mlm kar ka k'ara min zafi kan zafi"

shiru yayi cikin had'e fuska yace
"zafin me kuma?"

Tsaki ta kuma ja cikin sanyi da rawar murya kamar zatayi kuka tace.

"Ba ya Auwal bane ya kirani wai gobe Nazir zai zo sannan kuma jibi zai turo iyayenshi gunsu Abba"

Mgnar ta sonki zuciyarsa har baisan sanda ya mik'e zaune ba
Cikin Neman k'arin bayani yace
"Ubban me zaizo ya miki? sannan me iyayenshi zasu zo yi mana a gida"?

Cikin sanyi tace
" Wai Auren yake so ayi da wuri kuma shi ya Auwal yace ai shi Dan mutun cine".

a kufule yace
"Zancen banza ai kowa ma nason Auren da wuri ko an gaya musu kin resa masoya ne shi wayafi buk'atar Aure zancen banza wlh bazai yiwuba insha Allah zan d'auki mata ki".

Ita har ga Allah gani take yana guje mata shiga wani haline bare da taji yana cewa
" toh shi kuma a wurin d'aurin Auren zaice ya sake ki ko"?

A sanyaye tace
"Ni banson zancen wani aurema yanzu wlh ya Auwal ne ke son jaza min".

Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da cewa
" Khady ki dena cewa bakya son Auren shin kin manta shi Aurennan sunnace baba shin bakya fatan ki zama uwa ta gari ga y'ay'ayenki Ke a zaton ki a shekara run kin nan za,a barki bakiyi Aure bane
Sannan ai ke da kankima muddin kina da lfy toh dole zaki buk'aci Auren
Ko so kike ai ta zagin iyayenmu ace sun zuba miki ido"?

Shiru tayi cikin sanyi jin zantu kanshi Na ratsata Dan ta tabbar gsky yake gaya mata.

A haka yai ta mata jirwaye mai kama da wonka Wanda itako bata gane ba
Har dai ta fara jin bacci cikin jin baccin da raunin murya tace.

"Mahmoudu bacci nakeji fa".

dariya ya danyi cikin jin dad'i
Yace
" Yau kuma Mahmoudu na zama ne Nana"?

"ehh mana ba ka fiye son girma ba"

" A a fa bani ke son girma ba Allah ne ya bani girman"

Mik'a tayi cikin sanyi tayi hamma alamun baccin sosai,
Shima mik'ar yayi tare da cewa.

"Kiyi Addu,a toh".

"Toh" tace tare da katse kiran
Shiko gaba d'aya daran ranan ya kasa samun nitsuwa tunani yake da gske fa ya Auwal gani yake bazan iya Aureba ko kuma mugunta ce shi yana can da matarsa Niko yana had'a min zafi.
A haka ya tashi ya sake watsa ruwa tare dayin alwala yazo yai nafila tare da Addu,ar Neman zab'in Allah
Daga nan kuma yayi ta karatu k'ur,ani
A haka bai samu yayi baccin kirkiba saida akayi sallan Asuba sannan ya dawo ya konta yasamu ya fara baccin.

Shine bai tashiba sai 11 dai-dai
yana tashi wonka yayi ya sa manyan kaya ya fito ras sai k'amshi yake sumar kana sai shek'i yake ya fito ras dashi.

Cikin gida ya shiga kai tsaye d'akin Mami ya shiga kan gado ya sameta tana konce cikin sanyi ya zauna kan carpet ya kalleta a nitse yace.

"Mami barka da safiya"
Cikin son d'an nata tai murmushi tace "babana antashi lfy"

Kai ya Dan Sosa cikin sanyi yace
"Toh lfy zance" ido ta tsura mai tare da cewa
"Akwai matsala ne"?

Kai ya gyad'a alamun a,a dan baisan ta yadda zata d'auki matsalan tashi ba.

K'anwarsa Amira dake gefe ne ta kalleshi cikin raha tace "Hamma Mahmoud ni har yanzu baka bani gudumawar ka bafa gashi Aure saura 1 week"
Mami ya tsurawa ido cikin yana yin ji yarinyar nanfa Amman ni in an tashi sai ace kar nayi mgn

dariya mami tayi tare da cewa
Zai baki ai Amira"

Shiko baki ya tab'e tare da cewa "jeki kira min Khadija ta kawo min breakfast na"

Mami ce tace "a a ita Amiran ta kawo ma dan Khadija tayi bak'in suna parlon baki"
Zubbur ya mik'e tare da zare ido yana waya zo gun ta kuma Wai su mayune kam"?

yana kaiwa nan kuma ya juya ya fita
Ita kuwa Mami zare ido tayi da bud'e baki Cikin tsoro tace
"Amira kar dai mgnar yayanku gsky ne Na shiga uku Mahmoud son yarin yar nan yake Yaro k'ara mi da bazawara ina bazai yiwuba"

Ita ko Amira cikin sanyi tace
Toh Mami mene dan yazo Anty Khadija ai naga ba haramun bane ko"?

Cikin had'e fuska tace
Ke baki da hankali Mahmoud ai bai kai Aureba sannan inzai Auren ma ya nemi dedanshi mana Amman ya sunk'umo matar da tafi shi kuma sai Na kama cewa mutane Mahmoud d'ana d'an kwalisan nan ya buge da son bazawara wlh bazata sabu ba"
Haka dai tayi ta kumfar baki.
Shiko yana fita parlon ya wuce yana shiga tare da slm
bai ko kalli inda Nazir yakeba yace
"Wallahi yunwa nakeji kuma gashi ina son shiga school"

Nazir dinne yace
" Mahmoud kana gida kenan"?
Ehh yace ba tare daya kalleshi ba sannan ya juya gunta yana kizo ki ban in yaso ki dawo
cikin girma Nazir yace "a a
Mahmoud kaje dai ka jira".

Tuka rinnan ya fad'a a ranshi tare da murtuk'e fuska ya juya zai mgn kenan ya Auwal ya shigo Wanda dama yana Parlon Anty ne suna tattaunawa kan Nazir d'in cikin had'e fuska yace
" kai Mahmoud me kakeyi a nan kaje Mami Na nemanka.

Fuska ya k'ara murtuk'ewa sannan ya fice yana
Hmmm
yana fita gidan Goggo Zahra ya wuce
yana zuwa ko yayi sa,a malam Abubakar nanan mijin Goggo Zahra kuma abokin Abbanshi suna gaisawa da Gaggo Zahra yace
Goggo gun baba fa nazo.
Toh tace dashi tare da cewa "to tashi muje tun kan bak'in su fara ta ruwa"

Suna shiga parlon shi yaje gaban shi cinkin girmamawa ya gaidashi
Ya amsa cikin son yaron dan yana da nitsuwa da cikar haiba cikin halin girma yace
"Mahmoudu ya karatu ya su Abban ka"?

Kai ya dan sunkuyar tare da cewa "Alhamdulillah"
Daga nan kuma sai yayi shiru tare da sunkuyar da kai
Lkci d'aya shiko mlm ya gane da mgn a tare dashi
Shiyasa cikin kula yace
"Mahmoudu meke tafe da kaine ka gaya min kar kaji komai kaji ko".

Shiko cikin jin k'arfin guiwa yace.
"Baba dama......


By Garkuwan Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w

_Dedicated Khaleesat Haydar_

Sai kuma ya dan dago ya kalli mlm da yana yin nitsuwa,
shi kuwa sei
Gyad'a mai kai yayi cikin yanayin
fad'i ina jinka.

Cikin nitsuwa yace
" Baba dama ina son a taimaka a gayawa Abba abinda nake sone"
Ajiyar zuciya ya sauk'e cikin sanyi yace "gaya min mene kake son"?

A nitsa ya korowa mlm jawabin buk'a tarsa cikin hikima da shiga zuciyar mai sauraro ya kareshi zancen da cewa
" Ni ko yau a shirye nake da Aurenta "

Shi kuwa mlm Abubakar ido ya tsura mai a ranshi kuwa Allah ya godewa da ya tsare musu imanin yaron nasu ya samai tunanin gwara yayi Aure dan badan Allah ya tare shi ba zai iya aikata komai tunda har yakai matsayin da zai fito kai tsaye ya bayya na buk'a tarshi ga Auren.

Cikin kula yace.

"Mahmoudu Aure dai ina Aure kake so toh wannan ba wani matsala shi Aure nufin Allah ne kuma insha Allah gobe zanje muyi mgn da Abban naku
Sannan ka dena damuwa da batun masu zuwa gareta in dai rebonka ce ba makawa zaka samu".

Shi kuwa kai ya sunkuyar cikin jin dad'i da k'arfin guiwa yace
"Baba Amman da yau za,ayiwa Abba mgn dan fa su iyayen Nazir d'in sunce goben zasuzo ai kuma gwara mu rigasu".

murmushi yayi tare da kallon yaron yana tunani shiko wanne irin hallitta Allah ya mishi
Cikin dan fara,a yace
" toh yau zanzo da dare"
Toh yace cikin jin dad'i tare da mik'ewa zai fita
Adam da yanzu ya shigo kuma yaji mgnar tasu kad'an cikin mmk yabi Mahmoud d'in da ido shiko hannu ya mik'a mai suka gaisa sannan ya juya gun
Goggo Zahra ya kalleta a dan sokane
ya karya wuya cikin sanyi yace
"Ayyah Goggo Zahra baki yi Allah sanya Alkhairi cikin Auren ba "
dariya sukayi baki d'aya Adam yace
"Tab har anyi Auren kenan har kuna Neman sanya Alkhairi mijin bazawara manya"

Juyawa yayi gun Adam d'in cikin shafa kanshi yace
"Sunnah ce babba Annabinmu ma da bazawara ya fara".

Mlm ne da Goggo Zahra sukace
" wannan haka yake
Allah baka ladan raya sunnar"

Amin yace tare da yi musu slm ya tafi.


A wunin ranar Mahmoud ya wuni cikin farin ciki sai dai kuma yakanji far gaba bai San ya iyayenshi zasu d'auki zancen ba sannan uwa uba Khadijan,

Cikin wunin ya kuma gano yadda zai boye zancen gareta in yaso sai taji abin daga baya,


Da dare bayan anyi sallan inshah
Malam Abubakar ya fito cikin kamala bai zame ko ina ba sai
gidan Alhj Ibrahim.

cikin mutun ta juna suka isa parlon shi

Bayan sun gaggaisa malam ya gyara zama tare da gyaran murya cikin nitsuwa yace.

"Ibrahim wata mgn ce mai mahinmanci ke tafe dani fatan zamu samu fahimtar juna"
Shima zaman ya gyara tare da juyowa gareshi cikin kula yace.

"Insha Allah zamu fahimci juna".

Kai ya jinjina sannan cikin hikima ya koro mai jawabin da Mahmoud din yaje ya fad'a mai,

Shiru Abban yayi tare da jinjina kai sannan ya kalli
Mlma Abubakar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.

" Abubakar yanzu kai me ka fahimta a zancen Yaron nan,?
Yanzu ina Mahmoud ina Aure?
yanzu anyama Mahmoud yasan me ake cewa Aure?
Abubakar Yanzu nefa Mahmoud d'in ya jona University anya yaro nan yasan me ake cewa Aure ai ko yayunshi mata ban tab'a Aurar dasuba har sai sun gama secondary sun fara zuwa F,C,E kafin suke Aure"

Tunda ya fara mgnar Malam Abubakar ke binshi da ido har saida yazo k'arshe sannan yace.

"Amman nayi mmkin jin zantu kan nan daga bakinka shin
A sheri,a ace akece sai yaro yayi digiri zaiyi Aure?
Shin Wanne matsayin da sharad'u musulunci ya gindayar in NAMIJI ko mace sun kai za,a basu damar suyi Auren?
Shin a cikin su wanne Mahmoud ya gaza bai kaiba?
Ibrahim ase baza ka marawa Mahmoudu baya ba ko dan a kauda shi daga sharrin zina, shin baka tsoro yaron fa ya fito fili yace Aure yake so in mun hanashi zai iya aikata komai
shin kana tunanin bazai san ya zai zauna da maceba?
Ko ka manta Mahmoudu yaro ne mai ilimin Addini duk abin da kake tunani bai saniba K'ur,ani da hadisai sun sanar dashi,
Haba Ibrahim ase kaima kana da tuaninnan Na tauye rayuwar yaro ko yarinya Wai da sunan sai Sunyi karatu mai zurfi kuma kana sane da illan da hakan ke jazawa yaran mu shin kasan irin halittar da Allah ya masane? kana da yakinin zai iya danne buk'a tarsa har yayi shekarun da kake tunani? Kuma kana da dukiyar da damar da zaka warewa rayuwarsa da matarsa komai cikin wadata haba Ibrahim kayi tunani mu a shekara nawa iyayenmu suka Aura mana mata"?

Tun da ya fara jero mai tabb'ayoyi sai shiru yayi mgnganusa Na ratsashi cikin sanyi ya rink'a gyad'a kai,
alamar a,a a,a.

Shi kuwa mlm cikin sanyi yace.

"Toh matuk'ar dai ba so kake muyi sanadin yaduwar barna da fasadiba to ayi mishi abinda yake buk'atar dan wlh illace baba iyaye su kafe kan yayansu bazasu yi Aureba har sai sunkai wani mataki a karatu boko hakan Na jawo yawan barna da fasadi ".

Kai ya kinji yace.
"Tohhh"
ganin kamar har yanzu bai nitsuba da abin gaba yasa
Mlm Abubakar ciro woyarsa
Mahmoud d'in ya kira yana d'agawa yace.

"Kazo gani a Parlon Abban ka".

Toh ya amsa tare da tasowa cikin happy ya iso parlon,

Yana shiga gaban su ya zauna a kasa kan carpet cinkin girmamawa yace.

" Baba gani"

Abba kam ido ya tsura mai cikin mmk
Shiko kai ya sad'a k'asa.

A hankali Baba yace.

"Yana da kyau Abban ka yaji buk'a tarka daga bakinka"

Kai ya kuma shafawa sannan a hankali yace.

"Abba dama eh ni dama Abba ni Aure nake sonyi kuma Khadija ce nake so sannan mun gama mgn da ita ni nafi son ayi Auren nan kusa".

Abba kam tunda ya fara mgnar ya bud'e baki da mmk yana binshi da ido shi har tsoro Yaron ya bashi (wai Aure nake so)

Mlm Abubakar ne yace.
"Toh Ibrahim kaji ko"?
Ehh yace cikin sanyi sannan ya kalleshi cikin kura mai ido yace.

" Mahmoud Aure kake so ko"?
Kai ya gyad'a tare da cewa "ehh"

Abin yanzu dariya ya bawa Abba shiyasa cikin sanyi yace.

"Wato kun gama shirya zancenku kai da Khadijan. ita Khadijan ta yarda da Auren"?

_Kai Mahmoud ya isa dan duniyar domain ta kar karewa yayi ya rink'a tsara zance yadda abin zai tafin mai dai-dai_

Gyara zama yayi cikin sanyi yace.
"Yauwa Abba daman mun gama mgnar da ita ita tace duk abinda za,ayi kar a kirata Dan kunya yakeji ta kuma amince dani shiyasa ma tak'i komawa gidan Sulaiman"

Ido Abban ya tsura mai cikin son gane gskyar zance sai kuma yace "Khadijan ko ta amince"?

Ehh yace cikin k'arfin hali
Baba ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
" toh tashi ka tafi"
toh yace tare da mik'ewa ya fice abin shi.

Mlm Abubakar ya juyo gunshi cikin mgn irin ta manya yace.

"Toh ka ga da idon ka dai tunda sun dai-daita Kansu to kar a shiga hak'insu
Mgnar. Khadija kuwa ni inaga kunya takeji ace ita bazawara zata Auri saurayi kuma k'aninta dan haka kar a tuntub'eta da zancen
In inna samu zama zama nanda kwana 4 zanje gun Alhj Sani muyi mgnar zanzo mu tafi da kai din
Kuma ko iyayensu mata a bari sai mun gama komai a gaya musu kasan zasu iya yin k'ananan mgn ganu a kai.

A haka suka Ajiye shawara shiko Mahmoud duk abinda ake ciki mlm kan kirashi ya gaya mai.

sannan sunje sun samu Baba Sani
Shi ba Abin da yace sai sanya Alkhairi.

Sannan sun tsaida zance za,a daura Auren randa za,ayi na Amira.

Shi kuwa Mahmoud yana sane da komai Amman baiyi gigin gayawa Khadijan da itako bata san komai ba akan zancen.

Sai dai yana yawan shige mata shak'uwa kuma mai k'arfi ta k'ara shiga tsaka ninsu.


Yau ta kama jumma,a kuma gone asabar ne ta kama Daurin Auren Amira da Amir d'inta sai kuma Mahmoud da Amarya Khadija da bata san da zancen ba.

Ran jumman kuma akayi walima mai k'aya tarwa.

Da daddere bayan sallan insha,a
Khadija ne cikin sauri ta nufi d'akin su Mahmoud d'in cikin d'an had'e fuska ta lek'a parlon hank'oshi tayi yana kwance kan 3 str daga shi sai 3 qtr a jikinshi.
ganin shi hakan sai taji wani irin nauyi ya rufeta da sauri ta juya tana.

Dan Allah ka fito kazo ka kaini
Target zan karbo dinku nanmu gun Yaxid yace yana jirana".

Cikin kasala ya mik'e tare da rataye rigarsa a kafad'a ya fito ya tsaya a gabanta da sauri ta kuma juyawa dan wlh bata son ganin shi hakan
Shi kuwa rigar yasa cikin kasala yace.

"Muje ko".

Ita kam tuni tayi gaba cikin mota ko cikin sanyi ya dan rink'a mata hira har sukaje suka karbo dinkunan suka juyo suna dawowa.
tuk'in yake cikin sanyi da k'orewa tafiya yake a hankali sun mik'e kan titin da zai maidasu cikin Yola a hankali kamar maiyin rad'a cikin kasala da wani yanayi ya juyo yana mata wani irin kallo yace.

Khady gobe fa...



By Garkuwan Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writer's
P.m.l.w

_Dedicated 2 my lovely Namecy Aysha Aliyu tsamiya😍😘😍😘😍_


Juyowa ya kuma yi gareta tare da tsura mata ido,
Itama idon ta zuba mai tare da cewa

"aha inajin ka"

A hankali ya k'ara rege tafiyar tare da maida hankali shi gareta cikin tsareta da ido yace.

"Khadija gobe fa zanyi Aure".

Da sauri ta cilla mai harara tare da tab'e baki ta kuma juyo cikin yanayin kai yaro ne tace.

" Auren ai ba wasan yara bane kuma ba iya zance bane bare kace ka iya kai yanzu ko nauyin kalmar bakaji ba"?.

Tun da ta fara mgn ya tsura mata ido bakinta kawai yake kallo sai da tai shiru sannan yace.

"Na tab'a miki irin zancen nanne"?.

Kai ta girgiza sannan ya k'ara juyowa yana fuskantan ta yace.

" Toh wlh ki yarda gobe zanyi Aure insha Allah tare dana Amira za,a daura".

Itama kara juyowa tayi cikin tab'e fuska tace.

"Ya za,ayi na yarda tunda ban tab'a sanin kana neman Aure ba sannan banji zancen daga bak'in manya ba hakazali ka ai da sauran ka ina kai ina Aure shin kama san mene Auren"?.

Fuska ya had'e nan da can ya kafeta da ido cikin had'e murya yace.
" ki

2 Comments On NAMIJI BAYA KADAN
avatar
yarima-ummi

12 months ago

Reply

Why won't I download it?

avatar
abasu-kala

12 months ago

Reply

Replying to yarima-ummi

You have to subscribe for our package before downloading

Please Login or Register in order to submit comment