Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ran mahaifiyarta. “
'Ta yadda da ingancin aikin bokan nan, tun da har ya san abinda ke zuciyarta, to amman kuma ta ya ya mahaifiyarta za ta rasu bayan ranta ba a hannunsu yake ba?.'
Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.
"Zan tura mata ciwon da zaiyi sanadiyar mutuwarta, daga nan ba ki da sauran Katanga tsakaninki da Shukhura, ke za ta dingaiwa kallon mahaifiyarta, amman kafin nan sai an fara raba tsakaninsu da me gidanku, a kuma rufe bakinsa, babu case ga wannan tsohuwar matar idan har kina sakar mata abin Duniya. Su kuma 'yan uwanta za'a raba soyayyar da ke tsakaninsu, saboda ta na matuk'ar son su fiye da son da takewa kanta.“
Farin ciki ne ya dabaibaye zuciyar Umma, ta dinga sharara masa godiya, suka rabu akan za ta dawo ta kawo masa abinda ya Buk'ata.“
Akwatinan Nimha ta kwashe da wasu kaya daga ciki taje ta sayar ta kai masa kud'in da kajin da ya buk'ata, ya bata wani ku'ullikan magani, d'aya ta zuba a cikin abincin da Mama za ta ci, d'aya ta zuba cikin ruwan turaren da za'aiwa Shukhura kamu da shi, d'aya cikin abincin da Baba zai ci, sai laya da za ta saka a bayan gadon Shukhuran, babu wanda zai lura da layar sai ita da ta saka da kanta, sauran abubuwan kuma shi zai ji da komai.



Shirye²n biki su Mama suke hankali kwance, don yanzu saura sati guda a fara shagul gulan biki, duk da Mama ta fara fuskantar wasu sauye² daga Baba hakan baisa ta tayar da hankalinta ba, da Allah ta dogara shi kuma taci gaba da mik'awa buk'atunta, don a 'yan kwanakin nan wasu mugayen mafarkai take mara dad'in ji ko kad'an, kawai ta na danne damuwarta ne saboda yaranta, don wani abu da Shukhura kuma ta tsira shine, duk dare sai ta sanyata a gaba ta na kuka ta na rok'onta akan a fasa wannan bikin, ta na jin kamar wani babban al'amari zai tunkaro su idan har akayi wannan auran, sai dai ta lallasheta da nasihohi masu ratsa jiki, don babu damar tunkarar Baba da wannan maganar, bare ya dube su, don ita kanta Mama yanzu ba ta buk'atar auran, to Baban gaba d'aya yanzu ya sauya musu da Nusrat kad'ai yake zama ya yi hira, hakan ya kuma tayar da hankalinsu gaba d'aya amman a haka suka daure suka cigaba da shirye shiryen da ba'a rasa ba.
Ranar juma'a akai kamu anan cikin gidan, Iya ce ta kama duka amaren guda biyu, yayin da taiwa Shukhura amfani da turaren Nimha, taiwa Nimha da na Shukhura wannan kuma duk tsarin Umma ne.
Ranar juma'ar da daddare akai Dinner d'in gidan su Mustapha, da Baba yace Shukhura ba za ta ba, da k'yar Nusrat ta lallab'a shi ya barsu suka je, kuma diner d'in ta k'ayatar da dukkan wanda ya halarci gurin.
Washe gari asabar sukayi walima anan cikin gidan don Baba ya hana DJ kuma walimar ta yi gwanin ban sha'awa.
Washe gari lahadi kuma aka d'aura auran.
Safiya Abdullahi Ahmad da angonta
Mustapha Faruoq Fanda
Zainab Abdullahi Ahmad da angon ta.
Saminu Yusha'u Hamza.
Tun da aka d'aura auran Shukhura da Nusrat ke kuka, gaba d'ayansu suna jin wani miki a zuciyarsu ya na musu ciwo amma ba su san dalili ba, Mama ce tai k'ok'arin rarrashinsu duk da itama ba ta jin dad'in jikinta, amman saboda mutanen da ke shigowa ana kallonsu shiyasa ta rarrashesu, su d'aki falle d'aya bare tace su shiga ciki suyi kukan nasu babu wanda ya gansu, ta san dai kukan rabuwa suke, wannan kuka kuwa dole su yishi, sun taso tamkar 'yan biyun da suka zauna a mahaifa d'aya, suna matuk'ar son junansu ko kyauta za'a yi musu sun fi son ayi musu a tare, idan kwa aka bawa d'aya to tare zasui amfani da shi, musamman Shukhura da ki mata kyauta gara kiyiwa Nusrat za ta fi matuk'ar farin ciki, hakan da Mustapha ya gani ne yasa komai zai yiwa Shukhura sai ya yi musu tare da Nusrat , wataran ma Nusrat d'in kad'ai yakewa kyauta don kawai yaga farin cikin sahibarsa.

K'arfe biyar dai² aka kawo motocin d'aukar amarya Shukhura, ita Nimha sai bayan sallar Isha saboda babu nisa, a lokacin kukan Nusrat da Shukhura ya k'ara k'arfi suka rungume juna suna kuka kamar ba sa rabu ba, Iya ce tazo ta janye Shukhura ta na sababi.
"Meye kuma na kuka bayan Allah ya 'yanta ki ya kaiki gidan daula, ki daina biyewa Nusrat bak'in ciki take miki don ita Allah ya yota me nauyin k'afar tsiya har yau ko mashin shini babu. “
Shukhura kukanta kawai take, Iya ta dank'ata hannun Aunty Maryam suka shiga da ita d'akin Baba, yayin da Mama ta rungume Nusrat ta na jin itama kamar ta fashe da kukan, takai dubanta ga Yusra da take ta aikin matse k'walla, da hannu ta yafito ta itama tazo gareta ta rungumesu ta na jin wani iri a zuciyarta.
Nasihu masu ratsa jiki Baba ya yi mata, ban da kuka babu abinda take ta cikin mayafinta daga k'arshe Baba ya sanya mata albarka aka fito da ita, ganin ana k'ok'arin fita da ita yasa ta fisge hannunta ta ruga d'akinsu da gudu, jikin Mama ta fad'a ta ruk'unk'umeta ta na kuka me ban tausayi, ta na jin kamar shi kenan daga yanzu sun rabu rabuwa ta har abada, shafa kanta Mama ta yi, don ta kusa sanyata zub da k'walla kawai ta na jajircewa ne.
"Allah ya yi miki albarka Shukhura, kije kiyi hak'uri ki kuma rik'e gaskiya a duk in da kike. “
"Mama ki yafe mini.“
"Babu abinda kika tab'a yi mini Mamana, ko da kinyi mini nan gaba na yafe miki Shukhura Duniya da lahira, fatana ki rik'e 'yan uwanki da daraja, kada ki bada damar da za'a rusa ginanniyar katangar k'aunar da na gino a tsakaninku tun kuna yara, idan kikai mini haka kin biyani Duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka baki d'ayanku, Amin, muje maza ana jiranki. ”
Ta rik'o hannunta had'e da na Nusrat, don Yusra tun d'azu ta fice k'ilama har ta samu mota, a hannun Aunty Maryam Mama ta kuma dank'a ta had'e da fad'in.
"Allah yasa ki shiga a sa'a, insha Allah mutuwa ce za ta fito dake daga wannan gida cikin salama da aminci, Allah kuma ya baku zaman lafiya na har abada amin, Yayarsu kije ki raka 'yar uwarki d'akinta. “
Daga haka ta saki hannun Nusrat d'in ta shige d'aki, daga jin k'arshen maganarta ka san kuka take.


Sai da aka kai Shukhura gurin Hajiya Suwaiba da gurin Inna kana aka huce da ita sashenta dake gefen gidan.
Sashen Shukhura gaskiya ya had'u iya had'uwa, komai walwali yake da k'yalli, bed room d'inta ma ciki da falo ne, anan aka yi amfani da kayan da Baba ya siya mata, don cewa sukai ba sai an mata komai ba, Baba yace a barshi dai ya siyawa 'yarsa mutumci, ko ba komai itama za tayi alfahari da haka, kamar yadda ko wace amarya ke yi.
Kayan da Baba ya yi musu suma ba laifi sun yi kyau iya kyau.
Kowa ya watse daga Shukhura sai Hidaya da suke jiran angwaye su zo suma su kama gabansu, tara dai² Mustapha ya kira Shukhura yace gasu a k'ofar gida zasu shigo don haka sai suka k'ara d'an kimkimtsawa suka fito da ita babban falo suka zauna, abokan nasa biyune sai shi cikon na uku, addu'oi aka yi akan Allah ya basu zaman lafiya kana abokan sukai musu sallama suka fita yabi bayansu don ya yi musu rakiya, su Nusrat ma suka tashi zasu tafi, rik'o hannunta Shukhura ta yi gam tace.
"Dan Allah Yayarmu kar ki tafi ki barni.“
Ta fad'a jikinta na rawa, hawaye ne ya zirarowa Shukhura haka zalika Nusrat d'inma suka rungume juna suna kuka, karo na farko kenan da zasu nesanta da juna tun tasowarsu, gurin kwanciyarsu d'aya, filon da suke d'ora kai guda d'aya a haka zasui bacci Shukhura ta rungumo Nusrat ta baya, ta gaba kuma Yusra ta rungumeta, gashi yau zasu kwana ba tare da Shukhuran ba, aure kenan me kawoka wata sabuwar bigiren rayuwa.
"Kar ki tafi ki barni, ba na son ki barni, ki zauna tare da ni kinji Yayarmu don Allah.“
"Ai muna tare Shukhura, ba wai mun rabu kenan ba, gobe ma insha Allahu zamu zo, ke dai ki rik'e nasihohin da akai miki, azkhar d'in nan na safe da yamma kada ki sake ki wasa haka zalika nafil fili ma. “
Daga haka ta zare jikinta daga nata ta bi bayan Hidaya saboda tun d'azu Mustapha yace su fito abokansa su sauke su a gida, ledar kaza da youghort Mustapha ya bawa Nusrat ta yi godiya ta shiga motar suka tafi shi kuma ya juya cikin gidan.
Ya sha rikici sosai da lallami ya lallamata har sukai sallah suka mika godiyar su ga Ubangiji, daga bisani suka d'an tab'a kazar amarcin don dukkaninsu basu saki jiki sun ci ba, sun d'an jima a zaune, ta na kwance a jikinsa ya kanainayeta kana sukai shirin bacci suka kwanta, Mustapha ya hankad'o ni daga d'akin yace mini.
"Asuba ta gari kema kije ki huta. “
Don haka na tafi hutawa sai kuma gobe in kun jini......











300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.




Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.




#N.W.A
#Team KTG
#Sonso fisabilillah
[10/8, 3:43 PM] Binta Lawan: *KTG*




Wattpad@Rashuna
https://my.w.tt/Cjpv9nxoJ9?utm_






____________
*ELEVEN*
(ZANEN K'ADDARA)

A wannan dare su Nusrat basui bacci ba, zazzab'i ne me zafin gaske ya rufe Mama da kuma matsanancin ciwon kai, wanda bacci ya k'auracewa idanuwanta, haka zalika ma Nusrat ba ta iya rintsawa ba ko kad'an har garin Allah ya waye.
Fitowa ta yi ta nufi d'akin Baba don ta sanar da shi sai taji muryar Umma tace.
"Nusrat.“
Juyowa ta yi ta na kallonta don ba magana ce ke had'asu ba, face gaisuwa idan Nusrat d'in ta gaisheta.
"Cewa na yi Shukhura kuwa ta kiraku? Kinga ni har ta kirawo ta gaisheni."
"Ai tun da nai sallar asuba mukai waya da ita. “
Nusrat ta ba ta amsa, don yanzu ba lokacin da za ta tsaya yin tunani akan maganar ba ne, d'akin Baba tai shigewarta, ya na kishin gid'e bacci har zai fara fusgarsa ya ji alamun shigowar mutum, a hankula ya sauke idanuwansa akan fuskar Nusrat yace.
" 'Yar baiwa lafiya? “
"Baba, Mama ce ba ta da lafiya tun cikin dare. “
"To sai akai ya ya kuma. “
Tsura masa ido Nusrat tai, kamar ba Baban nan nasu ba, mai k'aunar mahaifiyarsu, ta hango lokacin da tai wata rashin lafiya yadda duk ya firgice ya fita daga hayyacinsa, ya zamo tamkar shine mara lafiyar.
Wani yahu me tauri ta had'iye tace.
"Dama chamise zamu je. “
"To sai kun dawo don ni ficika ba na magani. “
Ba tace komai ba ta juya ta bar d'akin, dama ba kud'insa suke buk'ata ba, kawai dai ta gaya masa ne a matsayinsa na me jagorantarsu gaba d'ayansu.
Umma kuwa bak'in ciki ne yai mugun kama ta da taji wai Shukhura sun yi waya da Nusrat, a yadda bokanta ya sanar mata idan har Shukhura ta kwana a kan gadon nan to sunyi rabuwa ta har abada ita da 'yan uwanta, tsakaninsu kuwa sai dai kallo, ita kuwa Mama na mutuwa, to tabbas ita za ta zamo mahaifiyar Shukhura kuma babu wanda ya isa yai magana akan hakan, dad'inta d'aya ne da ta fuskanci Mama ba ta da lafiya, tsakanin Shukhura da Nusrat kuma za ta zuba ido ta gani.

Sun ci sa'a me chamise d'in ya fito, ya yi mata allurar zazzab'i ya bata kuma magun guna, kud'i ya kama 1500 Nusrat ta bashi 2000 ya basu cangin 500 suka kamo hanya suka taho gida.
To Alhmdlillh sai jikin nata ya d'anyi sauk'i kad'an, har Nusrat ta had'a mata shayi me kauri ta sha, ganin jikin Maman ya yi sauk'i sai a sannan ta yi tunanin Shukhura har yanzu ba ta kirasu ba, amman gashi ta kira Umma sun gaisa, ta na cikin wannan tunanin sai ga Hidaya ta shigo tace mata tafiya zasuyi, amman zasu fara biyawa gidan Nimha da Shukhura in da sak'on da za'a kaiwa Shukhura a bada, kafin Nusrat ta mik'e ta bawa Hidaya sak'on sai wayar Hidayan ta yi k'ara sai Hidayan cewa ta yi.
"Kinga ma Shukhuran na kirana bari muji meye to. “
Ba ta jira me Nusrat d'in za tace ba ta d'aga wayar, ta can b'angaren Shukhura tace.
"Hello Hidaya kice a had'o mini duka akwatinana ku taho mini da shi.“
"To, shi kenan za'a taho da su, ga Nusrat za tai miki magana. “
Hidaya ta fad'a don ganin kallon da Nusrat d'in take mata, alamu ne na ta na son magana da 'yar uwar ta ta, k'ittt kike ji Shukhura ta kashe wayarta mamaki gaba d'aya ya kama su, a haka Nusrat ta shiga had'awa Shukhura duka akwatinanta da abubuwan da ba'a rasa ba, suka samo yara duk suka fita da su aka zuba a mota, kana sukai sallama da su Hidayan Nusrat tace.
"Ku gaishe mini da Shukhuran ku gaya mata Mama ce ba taji dad'i ba."


A tunanin Nusrat idan aka cewa Shukhura Mama ba taji dad'i ba za ta kira waya, in ma fishi take da ita ko tai mata wani laifin da ba ta sani ba ai ta kira layin Maman ta ji, amman har dare Shukhuran ba ta kira ba, ganin yadda duk Nusrat d'in ta bi ta damu yasa Mama tace.
"Bani wayata na kirata. “
Saboda tun d'azu Mama tace ta kirata tak'i, saboda ta na ganin kamar ta na da dalilin da yasa tak'i nemansu gara su d'an d'aga mata k'afa su gani. “

Ringin d'aya Shukhuran ta d'aga da murnarta tace.
"Hello Ma.......“
Cak taji maganarta ta tsaya ta kasa furta Maman da take buk'atar fad'a, Mama ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i a hankula ta furta.
"Innalillahi wainna ilaihir raji'un.“
Kafin taji saukar kukan Shukhura a kunnenta.
"Shukhura lafiyarki kuwa?“
Cikin kuka tace.
"Nima ban san me ke damuna ba, daku na kwanta a raina da ku kuma na tashi, tun da mukai sallar asuba nake son kiran wayarku amman na k'asa, sai na ji ana rad'a mini a kunnena wai ke ba mahaifiyata bace, Umma ce mahaifiyata ko kuma ace su Yayarmu ba 'yan uwana bane Nimha ce kad'ai 'yar uwata, na san Yayarmu ta damu sosai amman wallahi ko muryarta ba na son jin, ina cikin damuwa zuciyata ta na mini zafi, da na san haka auren zai zo mini da babu abinda zai sakani yinshi. “
Ta na kawowa nan ta fashe da wani matsanancin kuka, Mama kuwa Innalillahi kawai take ambata a zuciyarta, yayin da Nusrat duk ta na jin abubuwan da Shukhuran ta fad'a, had'a kanta tai da guiwa ta fashe da kuka me ciwo, 'yar uwarta da take sonta fiye da son da takewa kanta yau itace ta furta ba ta son jin muryarta, me yake shirin tunkaro rayuwarsu ne, waye me buk'atar rusa Katangar farin cikin da suka dad'e da ginata a zuciyoyinsu?
Majina Shukhura ta jaa taci gaba da cewa.
"Mama kicewa Umma me mukai mata take son rusa rayuwarmu gaba d'aya, in wani abu mukai mata sai mu nemi yafiyarta, na san dai itace ta shiga tsakaninmu saboda da sassafe ita na fara kira na gaisar, bayan ko anan cikin gidan ba kullum nake gaisheta ba. “
Numfasawa Mama tayi tace.
"Umma ba ta isa ta miki komai ba Shukhura, ki saka hakan a ranki, babu wani abu wanda yake faruwa a rayuwa face dole sai da wani zare da ya haddasa hakan, kuma bama iya ganin zaren, shi wannan zaren shi ake kira ZANEN K'ADDARA.
Dan haka kada ki kuma danganta abinda ya same ki da wani d'an adam, duk abinda ya sameki to ki tabbata yana cikin k'addararki, ki kuma kai kukanki ga Ubangiji domin shi kad'aine zai baki ikon cinye jarabawar da yai miki har ya yaye miki abinda ke damunki, yanzu kije kiyo auwala ki d'auki qur'ani ki karanta za kiji sanyi a ranki, maza jeki, Allah yayi miki albarka, ki kuma daina wannan kukan.“
Muryarta can k'asa tace.
"Tom“
Mama ta kashe wayar ta lumshe idonta kana ta bud'esu akan Nusrat da ke gurshek'an kuka......


Jiya ba ku jini ba, chargi ne ban samu ba wutarmu ta lalace, gobe da jibi ba lallai ne ku jini ba saboda muna hidimar biki.




300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB GTBANK
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya.






Allah ka k'arawa
mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.



#N.W.A
#Team KTG
#Son so fisabilillah[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna



KATANGA...



...............
12


Cikin dare sosai jikin Mama ya tsananta kwana sukai basui bacci ba washe gari aka nufi asibiti da ita, suna zuwa ruwa aka fara saka mata don ta jigatu sosai, kafin a fara gwaje gwaje da aune aune wanda kuma basu hango komai dake damun Maman ba don haka suka rubuta musu tasa tasai.
Nusrat ce kad'ai ke jigila da Maman dukkan abinda aka buk'ata da kud'in Maman take yi don tun tahowarsu babu wanda ya biyo bayansu. Typod da
Maleria ce ke damunta har ta kusan cin k'arfinta don haka aka shiga mata treatment inta zuwa washe gari jikin nata ya d'an samu ba laifi sai bacci take sha abinta ganin hakane yasa Nusrat ta barwa na kusa da su ajiyarta akan zata je gida ta daho, tana fitowa ta samu d'an sahu har k'ofar gida ya ajiyeta ta bashi kud'insa ta shiga ciki, tana jin Iya na k'wallo mata kira don taga giftawarta amman tai biris kamar ba taji ba, tana shiga gurinsu da Umma ta fara cin karo d'an zaburowa tayi tana kallonta kafin tace.
‘’Ta rasu?‘’
Mamaki ne ya kama Nusrat ‘’To me take nufi‘’ Shine abinda zuciyarta ke tambayarta banza tayi mata ta saka kai za ta shiga d'akinsu taji muryar Baba ya k'wallo mata kira.
‘’Ke 'yar baiwa zo nan‘’
Fasa shiga d'akin ta yi ta juya zuwa d'akinsa, so yake ya tambayeta ya jikin Maman amman bakinsa yayi nauyi.
‘’Kiyi hak'uri kinji, Allah yayi miki albarka.’’
‘’Amin‘’ Tace tana dabarar goge k'wallar dake k'ok'arin zubowa kafin ta kuma cewa.
‘’Jikin nata da sauk'i ma, bacci na barota tana yi.‘’
‘’To masha Allah, Allah k'ara mata lafiya‘’
‘’Amin‘’ Tace kafin ta mik'e ta bar d'akin, Yusra ta tarar tana ta malelekuwa a tsakar d'aki, tana ganinta ta taso da gudu ta rungumeta.
‘’Yayarmu ya jikin Maman?‘’
‘’Da sauk'i,lafiya na ganki haka?‘’
‘’Yunwa ce Yayarmu rabona da abinci tun d'umaman jiya da safe, akwai garin amman ba kud'in cefane Baba bai samo ba ita kuma tak'i girkawa ni kuma na duba babu ko ficika a d'akin nan‘’
200 ta cira ta bata kafin tace.
‘’Ki anso taliya gidan tabawa kizo kici, amman ki sauri don tare zamu koma kya dinga ragen da wani abu kafin a sallamomu.‘’
‘’Tom‘’ Tace tana mik'ewa ta d'au hijabinta ta fice ita kuma ta fara tub'e kayanta da hanzari don duk hankalinta yana kan Mama, bayan fitowarta daga wanka tana ganin Umma da Iya a d'akin Baba tana jin ko tambayarsa jikin Maman suke su dai suka sani ta fad'i hakan a ranta, tana jin Umma na fad'in.
‘’Mutum sai wani fad'in rai yake, sai kace mu muka saka masa nauyin k'afar to sai dai bak'in ciki ya kashe shi aurene dai an riga anyi.‘’
Ko d'aga kai ta kalleta ba tayi ba ta shige d'aki saboda ba maganganunta ne a gabanta ba, a gaggauce ta shirya, ta d'aukarwa Mama kaya da hijabai, sai 'yan abubuwan da ba zaa rasa ba da zasu buk'ata a can, har ta gama had'a komai Yusra ba ta gama cin abinci ba.
‘’Ke matsalata da ke kenan wani yaron ma yafi ki saurin cin abinci .‘’
‘’Na ma k'oshi Yayarmu bari na wanko hannuna.‘’
Muryar Iya taji tana cewa.
‘’ Mik'o min na cinye Yusra.‘’
D'aukar kwanan tayi ta fita, almajiri taji yana bara ta kwa k'wallo masa kira yana zuwa ta juye masa ta wanke hannunta tana jin Iya na ta sababi tqna tsine mata tai banza da ita ta shige d'aki hijabinta ta d'auka had'e da fad'in.
‘’Muje Yayafmu.‘’
Fitowa,sukayi Nusrat ta kulle d'akin, suka lek'a d'akin Baba ta mishi sallama had'e da ajiye masa 500 tana jinsa yana ta sanya mata albarka.....





200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta


#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna



KATANGA...



...............13

Washe gari sai Mama ta tashi jikin nata da d'an dama, har wanka tayi ta sauya kaya suna ta hira da su Nusrat wanda farin ciki duk yabi ya dabaibayesu sunga Maman nasu ta samu sauk'i.
‘’Yayarsu kin gayawa Shukhura kuwa muna asibiti?‘’
Mama ce takewa Nusrat wannan tambayar yayin da Nusrat tace.
‘’Na kirata ba ta d'aga ba ni kuma ban kuma kira ba.‘’
‘’Kar kice zaki fishi da ita, domin kece zaki zame musu mahaifiya yayin da bana duniyar, nidai ina dad'a baki hak'uri, ki zamo mai hak'uri ga k'annenta, kirawo mini ita a wayata ki bani.‘’
Ji tayi ta kasa yiwa maganar Maman fassara taji kalaman wani iri a k'wanyarta, cikin wannan tunanin ta lalubo number Shukhura ta danna mata kira, tana fara shiga ta bawa Mama wayar sai da ta kusa katsewa sannan aka d'aga, cikin sanyin murya ta furta.
‘’Mamanmu‘’
‘’Na'am Mamana, nayi kewarki‘’
cewar Mama, yayin da Shukhuran tace.‘’Nima nayi kewarki, kina nan lafiya Mama, wallahi wani mugayen mafarkai nakeyi.‘’
‘’To dai yanzu Alhmdlillh, amman ina kwance a asibiti, ki rik'e addu'oi insha Allah babu abinda zai faru, so nake na ganki idan zai yuhu ko da daddare ne kisa ya kaho ki.‘’
‘’Tom shikenan insha Allah zamuzo tare, a turon addres in asibiti.‘’
‘’Toh Allah ya kawoku ya yiwa rayuwa albarka.‘’
‘’Amin Mamanmu‘’ta fad'a a sanyaye.

Suna gama maganar da Mama ta lalubi number Mustapha ta kirashi, yana ganin kiran nata ya kashe ya biyo‘’Ba dai jikin bane‘’
Ya jefo mata tambayar da yake ya fita ya barta da zazzab'i a jikinta.
‘’Uhhm uhmm ya ma sauka, Mama aka kwantar a asibiti, shine tace tana son ganina‘’
‘’Toh subhanallah ganinan zuwa‘’
Bai jira cewarta ba ya datse kiran.
Sai da ya fara zuwa sashen H Suwaiba da H Inna ya gaya musu, duk suka ce bara su shirya kafin su fito suma suje su dubata.
Da tagumi hannu bibbiyu ya tarar da Shukhuran da sassarfa ya k'arasa gareta yana cire hannuwan nata had'e da fad'in.
‘’Kin san fa ba'a son yin tagumi.‘’
‘’Bani da wani zab'i da ya wuce na tagumin sam wani iri nake jina duniyar ba ta mun dad'i.‘’
‘’Ki kwantar da hankalinki insha Allah Mama za taji sauki', muje ki sako hijabi mu tafi, Hajiya da Hajiya Inna sunce zasu.

Iya, Umma, Mmn Amima (Matar Baffa Shamsu)suka zo duba

Please Login or Register in order to submit comment