Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jaho Hibba jikinki ki nuna mata soyayya, to tabbas zata sake da ke za kuma tafi girmamaki da nuna miki soyayya."

"Zan gwada"

Ta fad'a a tak'aice had'e da mayar da hankalinta kan wayar don ganin waye ya mata miss call, Ishaq ta gani, tana k'okarin bin kiran ya kuma kira, picking tayi had'e da kwanciya akan gadon tayi rigin gine, yaya sukaje gida shine abinda ya tambayeta ya kuma ce mata kada ta manta ta turo masa Addres in gidan nasu tace masa insha Allah baza ta manta ba, suna gama wayar ta tura masa tana k'udirewa a ranta ko ta yaya ne sai ta cusa Nusrat din cikin rayuwarsa yadda zata bar mata Rj inta ita kad'ai.....


Ina fama da rashin chargi shiyasa zaku dinga jina shiru.
[4/26, 8:43 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG 25


Washe gari da Ishaq yazo masaukin bak'i Hidaya ta sanya aka kai shi, kana ta tura Hanne me aikinsu ta kai mishi juice da ruwa da d'an abin motsa baki daga bisani ta nufi gurin nasa ta bar Nusrat tana kintsawa bayan ta lallab'ata da dad'in baki akan taje ta saurareshi taji da me yazo, in yaso sai ta sanar da shi abinda ke ranta.

Gaisawa sukayi cikin mutumci, kana ta sanar mishi Nusrat in tana shiryawa ne kafin ta zayyana mishi cewa ko da Nusrat in ta sanar masa akwai wanda taiwa kanta alk'awari to ba haka zancen yake ba, kawai dai tana tsoron maza ne saboda wani da ya yaudareta ana gab da bikinsu yace ya fasa, to amman ya bita a hakan, in yaso sai yace yana son su k'ulla abota, duk yadda dai zaiyi yayi ta anshi abotarsa ita kuma za ta dinga taimaka masa a hankula sai dai Nusrar in ta tsinci kanta cikin soyayyarshi, yayi na'am sosai da shawarar da ta bashi ya dinga zuba mata godiya yana k'ara ganin girma da kimarta.

Itace da kanta taje ta taho da Nusrat in, daga bakin k'ofa ta tsaya tayi mata nuni da ta shiga ita kuma ta juya.
Ta d'an jima sosai a bakin k'ofar kamar ta shiga kamar ba ta shiga ba, ta b'angaran Ishaq kuwa yaji tsaiwar mutum a bakin k'ofa da sabon k'amshin turaran da ya ziyarci hancinsa amman shiru yaji ba'a shigo ba, a hankali ya mik'e ya nufi bakin k'ofar, yana d'aga labulen itama ta d'aga kenan za ta shigo idanuwansu ya sark'e guri d'aya, d'an ja baya tayi a ranta tana yaba tsarin kyahunsa duk da bai kai Yaa Rj ba da wannan me kyahun da sukai karo har sau biyu a asibiti ba, mtsss taja tsaki a ranta ko meye na tuno shi kuma?

Ja da baya yayi har lokacin idonsa bai bar kanta ba, yana jin yadda k'auna da soyayyarta ke karya kuzarinsa.

"Bismillah zo ki shige."
Ya fad'a yana me nuna mata hanyar da hannunsa, babu musu ta shige a sanyaye don idanuwansa sun fara kashe k'arfinta da ta fito da shi, bayan sun zauna gaba d'aya k'asa tayi da kanta tana mai gaisheshi cikin muryarta da ta k'ara yin sanyi wacce shi kuma ta k'ara sanyashi mutuwa sosai cikin k'aunarta, bayan sun gaisa babu kwane kwane ya zayyana mata abinda ke tafe da shi wanda itama ba tayi nauyin bakin sanar da shi akwai alkawarin wani a kanta ba inda shi kuma ya nuna mata buk'atarsa ta yin abotaka tunda ba ta amshi soyayyarsa ba, ita kwa tace sam babu abotaka tsakanin mace da namiji baza ta amsa ba, da k'yar dai ya shawo kanta akan in ya kira waya zata amsa ko ba ko yaushe ba, kuma in ya bukaci ganinta za ta amince ko da a wata sau d'aya ne ba ta amince masa ba sai da sukai alk'awarin bazai dinga kashe mata kud'i ba kafin daga bisani sukai sallama ya bata rafar 'yan dubu akan ta baiwa Hidaya, taso k'in amasa ta kuma nuna mishi zai fara karya alkawarinsu tun yanzu yace ai ba ita ya bawa ba Hidaya ya bawa.



A haka rayuwa take juyawa tana tafiya, shekara ta zama tamkar wata, wata tamkar sati, sati tamkar kwana aya, kwana aya, kwana aya tamkar huni, anyi azumin watan ramadana cikin hukuncin Ubangiji, wanda suka dinga iban garar girkuna kala kala gurin Nusrat, don har searching in girkuna ta dunga yowa a wayar Hidaya,don ita kanta girkinma yana sanyata nishad'i kuma tasan kanta take taimaka don ta tabbata duk mijin da ya aureta to tabbas sai yayi alfahari da ita indai a b'angaran girki ne.
Sam ba tayi wasa gurin ibada ba, ta mayar da hankali sosai tana rok'awa iyayanta rahama gurin Ubangiji, su kuma da kyakkyawar rayuwa a garesu tare da miji na gari, da kuma dawo da KATANGAR kaunar dake tsakaninsu da Shukhura.


Har yanzu bata da waya babba, Daddy ne yaso siya mata amman Momy tace masa Nusrat in ba ta da ra'ayin rik'e babar waya gara ya siya mata k'arama, don ta sanshi mak'udan kudi zai saka ya siya mata wayar musamman yadda yake kwasar girkunanta masu dad'i, to shine ya siya mata waya 'yar k'arama me kyau me kuma tsada, dama tana da sim inta a ajiye ta d'auko ta d'orashi akai.
Kud'in kayan sallah ma da ya tashi bayarwa kai d'aya duk ya bayar har Nusrat don sosai yake jinta a ransa kamar 'yar da ya haifa, amman Momy sai da ta zaftare rabi a na Nusrat in, amman duk da haka Nusrat in ba iya kanta tayiwa siyayyar sallar ba har da Yusra, ta kuma siyawa yarinyar da Aunty Hafsa ta haifa me suna Nuru kaya set biyar masu matuk'ar kyau da tsada duk a cikin kud'in nata amman Hidaya ce ta k'ara mata kud'in wanda itama Ishaq ne ya bata yace ta san yadda za tayi ta bawa Nusrat in ba tare da ta san shine ya bata ba.

Uku ga sallah suka d'unguma sukai zariya, farin ciki duk ya cika zuciyar Nusrat burinta kawai ta isa mahaifarta ta ganta gata ga Yusranta, cikin Umma da Iya babu wanda yake ta ita, ko kuma ya nuna murnar canjawarta, don ba k'arya ta goge ta k'ara kyau musamman da take amfani da mayuka da aabulu da shower gel in da Hidaya ta siyo mata, sosai fatarta ta kuma gogewa kyahunta ya kuma baytana a fili, to duk bak'inci suka nuna mata a fili da habaicin da suka saba suna fad'in duk kwad'ayinta dai baza ta samu miji tamkar ya na Shukhura ba, babu wanda ta tankawa kamar ko yaushe ta janye jikinta ta nufi d'akinsu ta bud'e ta shiga da kayanta da na su Yusra da ta siyo musu.

D'akin ta gyara komai yayi nead, kana ta nemi guri ta zauna, tana jin b'acin ran da su Iya suka sanyata yana damunta duk kwa k'ok'arinta na ganin ta kawar da shi ta yakice shi daga ranta, kallon d'akin nasu take sosai tana tuna rayuwarsu a ciki kamar yanzu komai yake faruwa cikin kwanyarta, rayuwa kenan, number Yusra ta lalibo ta danna mata kira saboda in ba haka ba kuka za tayi wanda kuma kukan bazai shafa mata lafiya ba.

Wani wawan ihu Yusra ta saki yayin da Nusrat ta sanar mata tana cikin garin zariya.
"Gani nan gani nan Yayarmu"
Shine abinda take fad'i cikin zallar d'auki da farin ciki, katseta Nusrat in tayi akan ta bari gobe za tazo, k'in yadda tayi da k'yar ta lallasheta kana ta hak'ura, suna gama wayar, wayar Ishaq ta shigo mata don yaji ya suka isa zariyar.

Washe gari tun da safe ta shirya ta yiwa Momy sallama akan ta tafi unguwar fulani, acan Uncle Iliyan yake a zaune, Hidaya taso yi mata rakiya amman ciwon kai take fama da shi don haka kawai tace ta gaishesu, yayin da suka tafi da Hibba da tace zata bita don itama tana son ganin Yusran.

Tunda Nusrat ta sanar da Yusran suna hanya Yusra ta kasa tsaye ta kasa zaune, tana jin sallamarsu da gudu taje ta d'afe Nusrat in suka ruk'un kume juna cikin murna da farin ciki, yayin da Hibba ta tsaya tana ganin ikon Allah tana jin a ranta inama suma irin hakanne ke wakana tsakaninsu da Hidaya, duk laifin Momynsu ne da ta gina musu irin Katangar da Mamansu Yusran ta gina musu da yanzu hakan bazai bata sha'awa ba.

A yau dai farin cikin Yusra da Nusrat bazai rubutu ba masu karatu ku hasasho kawai, musamman da taga irin siyayyar da Yayar tasun ta jibgo mata, duk da yanzu Alhmdlillh duk wani abin buk'ata Auncle Iliya yana iya bakin k'ok'arinsa ba k'aramar murna tayi ba ta dinga jero mata addua tare da iyayansu da suka rasa.
Aunty Hafsa ma tayi murna ga kuma kayan da ta bayar a sakawa Nuru, godiya ta dungai mata, tana k'ara ganin girma da kimar Nusrat in tare da jinjinawa mahaifiyarsu da yi mata adduar dacewa.

Ko da suka tashi tafiya Yusra had'o kayanta tayi akan za ta bisu, in yaso in suka tafi ta dawo, amman Nusrat ta hanata, duk da k'asan ranta tana son kasancewa da k'anwar tata, kuka sosai Yusran ta samu guri tana yi kamar k'aramar yarinya,ganin haka yasa Aunty Hafsa ta d'au waya ta kira Auncle Iliya ta sanar masa abinda ke faruwa kawai yace suje din in sun tafi ta dawo.

Tsalle da murna Yusran ta hau yi yayin da Aunty Hafsan ta gaya musu abinda Auncle Iliyan yace.


Satinsu d'aya da zuwa zariya Shukhura ma suka zo, tazo gidan da sha tara ta arzik'inta wanda Umma ta dinga yadarwa da su Nusrat in magana, Yusra taso tankawa Nusrat in ta hanata, huni ranar Shukhura tayi a gidan amman ba ta neme su ba suma basu nuna sun san da zuwanta ba, Nimha kuwa da tazo har d'akin da suke ta shigo suka gaisa, don haka suma suka saka rana suka je gidanta har da su Hidaya suka huni sur a can, don su Nimha anyi kud'i ana ta fantamawa.


Satinsu biyu cur a zariya suka tarkata nasu ya nasu suka tafi, Yusra da Nusrat suna ta kewar juna, don sati biyunnan da sukayi tare ya tayar musu da tsimin abubuwa masu yawa, har ba taso tafiyarsu ba tayi tunanin wata guda zasui, duk da yanzunma Momy tace Daddy ne yace su dawo saboda Rj jibi zai dawo kar ya dawo gidan ba kowa, duk da tasan Daddynma a matse yake da su dawo don ya gaji da kame kamen abinda yake ci·....


Juma'a asabar lahadi zaku jini shiru·
[4/26, 8:44 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG 26


Ana ya gobe Rj zai dawo Hidaya ta tsame jikinta ta tafi saloon akai mata gyaran jiki da na kai, Nusrat kallonta kawai take yadda take ta rawar kan dawowar Rj in, hatta kayan da zata saka sababbi ne ta siyo su, zuciyarta ta fara zargin anya Hidaya da Rj in ba soyayya suke ba ya ninketa a bai bai yasa ta mishi alk'awari amman ko ma dai meye za ta zuba ido taga dawowarsa da wani taku zaiyi, idan kwa ya tabbata Hidaya son RJ take to tabbas zata haramtawa kanta shi tun kafin a haramta mata zuciyarta ta samu matsala.

Biyar da rabi na yamma Hidaya da Daddy suka tafi filin jirgi taro Rj saboda yace shida dai dai jirginsu zai sauka, shidan kwa a filin jirgin tayi musu hakan yayi dai dai da isowar jirgin nasu, idanuwa waje Hidaya ta zuba tana jiran saukowar annurin zuciyarta.

Murmushi kwance akan kamilalliyar fuskarsa ya fara saukowa daga jirgin yana wurga idanuwansa ra inda zai hango Daddy, idanuwansa akan Hidaya suka sauka wanda itama nata idanuwan akansa suke zuciyarta tana wani irin bugawa had'e da yamutsawa da zallar soyayyar yayan nata, murmushi ya sakar mata wanda ya kuma matar da ita a zallar k'aunarsa kafin ta sakar masa nata murmushin shi kuma a lokacin ya d'auke idonsa daga kanta ya mayar kan Daddy da ke gefenta suka sakarwa juna murmushi kafin ya nufo gurin da suke a tsaye.

Rungume juna suka yi da Daddy, yana jin soyayyar d'an d'an uwan nasa na kuma huda ko wata k'ofa ta zuciyarsa, yana jinsa sosai cikin ransa kamar shine ya haifesa, yayin da shima Rj in soyayyar Daddyn nasa ke kuma ninkaya cikin zuciyarsa, shi maraya ne amman baisan wani abu maraici ba, duk wata k'ofa da zata sakashi tuna shi maraya ne Daddy ya toshe masa ita, Daddyn yakewa kallon mahaifinsa tunda da shi ya tashi ya bud'i ido mahaifinsa ya rasu ba tare da ya mallaki hankalinsa ba sai Allah ya bashi wani mahaifin wanda suka shak'u da juna yake kuma share masa hawayensa a duk sanda sukai kokarin zuba.

Kallonsa Hidaya take kamar ta lashe shi, ya k'ara kyau ya k'ara girma fatarsa ta goge ya zama ingarmar namiji, wani sonsa da k'aunarsa take ji yana kuma shiga ruhi da zuciyarta, ashe hotunan da ya turo mata b'oye wani kaso daga kyahunsa sukayi.

"Hidaya na canja miki ne?"

Rj ya jefo mata wannan tambayar ganin irin kallon da take masa, wata kunya ce ta kamata ta rufe fuskarta da hannuwanta tana dariya kafin tace."Allah Yaa Rj ka canja sosai, kamar ba kai ba."

"Ke ba kiga canjawar da kikayi ba kenan sai tawa?"

Wani dad'i ne ya ziyarci ruhinta cike da jin dad'i tace.
"Dan Allah Yaa Rj na canja?"

"Kin canja mana, tunda ba haka na tafi na barki ba."

"To wata iriyar canjawa nayi."

Tana so taji yace ta k'ara kyau ne, kamar yadda ta gani a tare da shi, muryar Daddy ce ta katsesu da cewa.
"Ku muje gida mana, in munje kwayi hirar."
A ransa yana adduar Allah ya cika masa burinsa ya had'a zuciyoyin Hidaya da Rj in guri guda.


Sai da ya fara shiga suka gaisa da Mommy, Abbas da Hibba sukai masa barka da dawowa kana ya fito ya nufi phart insa da ke gefen gidan zuciyarsa cike da murad'in ganin Nusrat, yana mamakin rashin ganinta da baiyi ba kuma ba ya son tambayar Hidaya don ya fuskanci ba ta so, tunda babu yadda baiyi da ita akan ta had'ashi da Nusrat in a waya tak'i ba, kullum da k'aryar da zata shafto masa, haka da yace ta d'au hotonta ta turo masa ta shiriritar da zancen, ya rasa inda Hidayan ta saka gaba, shi dai a iya saninsa bai taba nuna mata wata alama ta yana sonta ba don shi zuciyarsa Nusrat kawai take so da ita kad'ai yake jin zai iya rayuwa, kwana yake yana mik'awa Allah kukansa akan yabar masa Nusrat insa ba tare da wani ya aureta ba har ya dawo, sai gashi Allah ya amshi adduarsa, Nusrat ta rik'e alkawari da yardar ubangiji.

Wanka yayi da ruwa mai zafi yadda zai huce gajiya, ya d'auro alwala ya fita masallaci bayan ya shirya cikin black in jus da red in t shirt a gaggauce kar ya rasa jam'i, a masallacin ya zauna har sai da yayi sallar isha kana suka shigo cikin gidan tare da Daddy suna tab'a hira a tsakaninsu duk akan aikinsa da cigaban da ya samu, shekararsa biyu da gama karatunsa suka rik'esa a can yayi musu aiki saboda kaifin basira da k'wak'walwar da Allah ya bashi, yanzu ma sun so cigaba da rik'e shin yak'i yarda gaba d'aya hankalinsa yayo gida, shekara uku sukayi da Nusrat sai gashi ya d'ebi shekaru har biyar, inda Allah ya taimakeshi ma ta rik'e masa alk'awarinsa wanda bai tsanmata ba ganin ya sab'a k'aida.


A dining sukayi masauki, Hidayace yau tayi serving in kowa da k'ayataccen girkin da Nusrat in tayi saboda RJ inta.
"Yau ina Nusrat in?"

Daddy ya fad'a yana kallon Hidaya, wanda ya nuna ita yakewa tambayar, d'an sosa kanta tayi kafin tace.
"Cewa tayi kanta na ciwo ba za ta iya fitowa ba."

Mayar da kallonsa yayi kan Hibba kafin yace.
"Maza jeki ki kirahomin ita."

Rj ji yayi kamar Daddy ya tsunduma shi a aljanna da ya tura a kiraho hasken idaniyarsa.



Ina fama da rashin chargi shiyasa kuke jina shiru, ni kaina na k'agu naga munyi nisa cikin labarin amman ko tsakiya ba muzo ba, idan komai ya daidaita zakuna jina sosai da sosai na gode.
[4/26, 8:44 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG27

Waya suka gama da Yusra, sai ta fara yin game a k'aramar wayarta, saboda ji tayi sam ba ta buk'atar fita cin abincin ba ta san ya gamuwarsu da Rj zata kaya ba, jin za'a murd'a handle in k'ofar yasata d'aga kanta don ganin me shigowar, Hibba ce ta shigo da sallama a bakinta, Nusrat ta amsa mata tana mayar da kanta kan wayarta.

"Aunty Hidaya ce tacewa Daddy wai kanki na ciwo, shine yace nazo na kiraki."

Hmmmm Hidaya me take nufi da ni ne, don kawai ba ta son na fita mu had'u da Rj har sai tayi mini k'aryar ciwo?

Shine tambayar da Nusrat kewa kanta, kafin tacewa Hibban.

"Kicewa Daddy na samu bacci kawai."

"Toh" Ta amsa mata da shi ta fita.
"Ta samu bacci."
Shine abinda ta cewa Daddy, kai kawai ya d'aga mata saboda ya fara cin abinci, yayin da Rj bai yadda da zancen Hibban ba, to tunda tak'i fitowa shi zaije har d'akin ya same ta, bayan Daddy ya kammala cin abincin ya kalli Hidaya da ke ta cin abincin cikin yanga saboda do take kowa ya fashe a barta daga ita sai Rj intadon shima ta fuskanci cin yangar yakewa abincin,yace.

"In kin gama ki iba mata abincin, ga awararta nan, ki tabbata kin tasheta taci tasha magani."

Da "Toh" Ta amsawa Daddyn da ya tashi ya bar dining in Mommy ta mara masa baya saboda ta gama itama, Hibba da Abbas suka tashi kowa ya nufi d'akinsa ya zamto sai su biyu kad'ai akan dininin in, a hankali ya mik'e don dama ya k'oshi da abincin jira yake a bashi guri, plate ya d'auka ya zuba abinci d'an dai dai kana ya d'auki awarar da Daddy yace ta Nusrat ce ya haye sama, baki sake Hidaya ta saki tana kallonsa har ya gama haye matattakalar.

Gajiya tayi da game in don haka ta kashe ta gyara kwanciyarta sosai akan gadon ta ja duvet ta rufe rabin jikinta, a hankula ta lumshe idanuwanta ta luntsuma cikin kogin tunanin nemo mafitar zuciyarta akan soyayyar Rj don yadda taga take taken Hidaya yafi kawai ta sanyawa kanta ruwan sanyi ta hak'ura da shi, tun da dama ba wai cewa yayi yana sonta ba itace take haukanta.

knocking yayi murya can k'asa tace.
"Shigo."
Tana tunanin Mommy ce don itace me yi musu knocking kafin ta shigo, a hankula ya turo k'ofar ya shigo idanuwansa gaba d'aya suka sauka cikin nata, a lokaci d'aya bugun zuciyoyinsu suka sauya, kallon cikin idonta yake sosai wanda ta kasa jurewa hakan ta kautar da kanta gefe, wani d'an k'aramin center table ya janyo ya d'ora plate in da ledar awarar, sai da yayi gyaran murya kafin yace.

"Ni gani nazo tunda guduna ake, saboda ni anki saukowa cin abinci to gashinan abincin ya biyo ki sai ki d'auka ki ci."

Bagarar da zancen nashi tayi da cewa.

"Ina wuni, an dawo lafiya.?"

"Tambayeni kiji."

"To ai tambayar taka nayi."

Baice mata komai ba ya hau dube dube d'aga can duba can kallonshi tayi da mamaki had'e da fad'in.

"Wai me kake nema?"

"Murmushinki nake nema, so nake na lalibo shi a duk inda kika b'oyeshi saboda nayi kewarsa mara misali."

Wani bazataccen murmushi ne ya sub'uce mata had'e da wata siririyar dariya, dariyar shima yake ya tsaya yana mata wani narkakken kallo kafin cikin wata murya mai shauk'i ya kira sunanta.
"Nusrat."
A hankali ta d'ago kanta idanuwansu suka gauraya guri guda, wani maganad'iso ne yake janshi daga cikin idanuwanta ji yake idan bai furta abinda ke k'irjinsa shekaru masu yawa ba yana k'ara yin nauyin da ke k'ok'arin yi masa illa gaba d'aya ba kamar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa ne, cikin wata shauk'ak'k'iyar murya tace.

"Ilove you Nusrat, ban san da wani baki zan gode miki ba, kinyi namijin k'ok'arin da ba ko wacce mace ce zata yishi ba, kin toshe kunnuwanki daga jin gori da habaicin rashin aure saboda cika alk'awarin da kika d'aukar mini duk da ni na sab'a k'aidar k'ara shekaru biyu kan ukun da na ibar miki wanda nima ba a son raina hakan ya faru ba, ban tab'a tunanin zan dawo na tarar kina jiranaba sai gashi kin bani mamaki, tabbas na jinjina miki jinjina ta ban girma sarauniyata, ina so a bani damar da zan shayar da ke ruwan soyayyata mai gard'i wacce na dad'e ina tanadinta da b'oyeta duk saboda ke Nusrat."

Zuciyarta wani irin bugawa take da sauri, tana jin yadda take bud'ewa da karb'ar sak'on soyayyar Rj in me girma, ashe da ba jin sonsa take ba,yanzu ne take jin aininhin soyayyarsa cikin zuciyarta wanda ba ta shiryawa hakan ba saboda hango tari matsalar da ke gabansu amman da dukkan alamu zuciyarta ta shiryawa hakan ba tare da tabi shawararta ba, wani irin yanayi take ji a cikinta mara misaltuwa."

"Kinyi shiru Nusrat, kice wani abu mana pls."

Ya fad'a da karyayyar muryarsa yana kallonta.



Momy ce ta sauko daga benen Daddy ta tarar da Hidaya ita kad'ai a zaune akan dininng tayi zurfi cikin tunani, ranta gaba d'aya a dagule, d'an zungurunta Momy tayi had'e da fad'in.

"Ke kuma lafiya kowa ya tashi ya bar ki a zaune, me kike zaman jira ina Rj in?"

D'an sosa kanta tayi tana b'oye yanayin da zuciyarta ke ciki tace.

" Shine yace na jirashi yaje ya dawo."

"Ok"
Mommyn tace tana hayewa samansu, ajiyar zuciya Hidaya ta sauke tana jin yadda zuciyar tata tayi mata nauyi, number Ishaq ta lalibo ta danna masa kira ta sanya ta free kana ta haye saman ta murd'a handle in k'ofar a dai dai sanda Rj in ya kuma fad'in.

"Pls Nusrat, say something mana"

Yakai k'arshen maganar yana dak'una fuska, kafin gaba d'aya su zubawa k'ofar ido don ganin me shigowar, zuciyar Nusrat na bugawa da tsoron ko Momy ce, ganin Hidaya ce yasata sakin b'oyayyar ajiyar zuciya, mik'o mata wayar Hidaya tayi had'e da fad'in.

"Ishaq ke magana."

Don a lokacin muryarsa ta bayyana tarwai yana.
"Hello."

K'irjinta yana wani irin bugawa ta karb'i wayar cikin sanyin muryarta tace.
"Salamu Alaikum"

Jin muryar Nusrat ya sanya Ishaq cikin wani matsanancin dad'i, yau shi Nusrat ta kira akan k'ashin kanta, tabbas dole yau yayiwa Allah godiya da yasa ya fara samun matsayi gurin Nusrat in,muryarsa cike da zallar farin ciki yace.
"Wa'alaiki salamu da My Nuss, da fatan dai kina cikin k'oshin lafiya?"

Wayar ta ciro daga kunnenta ta kalla kafin ta d'aga kai ta kalli Rj da ya mik'e tsaye cikin matsanancin b'acin ran da ya kasa b'oyuwa akan kamilalliyar fuskarsa, zuciyarsa wani irin tuk'uk'i take masa mai zafi ya bud'e k'ofar ya fice, Hidaya ta bi bayansa d'auke da b'oyayyen murmushi....
[4/26, 8:45 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG28

Da sassarfa ta had'a ta taddashi a farfajiyar tsakar gidan yana dosar inda sashensa yake saboda tsabar saurin da yake zubawa.

"Ai Yaa Rj Nusrat da Ishaq suna matuk'ar son junansu, kuma wallahi mutumin kirki ne sosai, yanzu haka ma maganar kawo kud..."

Ba ta k'arasa ba sakamakon wata muguwar tsawa da ya daka mata wacce ita tayi sanadiyar had'iye sauran maganar tata, da hannu ya nuna mata hanya yana jifanta da wani mugun kallo na tambayarki nayi, ko ni sa'anki ne, ina wasa da ke?
Sim sim ta shige idonta yana cikowa da k'walla yayin da shi kuma yaja tsuka yayi gaba zuciyarsa tayi bak'ik'k'irin, rigin gine ya kwanta a kan gado ya zubawa pop ido kamar yana karantar yadda aka zana shi yayi masifar kyau amman ba haka zancen yake ba, tunaninsa gaba d'aya yana kan Nusrat, bai jin zai iya jure rad'ad'in rasata ko kad'an, bai san so ko k'auna ba sai a kanta,a kanta zuciyarsa ta fara bud'ewa kuma yana jin akanta za ta rufe har abada, a komai nasa ita yake gani cikin idanuwansa kamanninta

Please Login or Register in order to submit comment