Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hukunta wanda ya aikata hakan, ina so a isarmin da sak'on camerar nan hannun Ibrahim Gogel ko kuma Aashiq Aliyu Gogel, kaf ahalin GOGEL ESTATE mutum biyunnan na aninta sak'ona ya isa garesu."
Wata jik'ak'k'iyar zufa Abba ya goge, tashin hankali na bayyyana k'arara akan fuskarsa, to shi da baisan fuskokin wa'yannan mutane biyu ba ta ina zai ganesu? Bashi da me bashi wannan amsar, ko da ya kunna camerar kasa cigaba da kallon abinda ke ciki yayi hankalinsa na mugun tashi, a take shima yaji zai iya salwantar da rayuwarsa muddun wannan sak'o zai isa ga wa'yannan mutane biyu, bayansu bai jin zai iya bawa kowa sai dai in su d'auki ransa, d'aga tabarmar dake shimfid'e a tsakar d'akinsa yayi ya hak'a rami ya zira camerar a ciki had'e da takaddar ya rufe ya mayar, a ranar cike da wannan zulumin ya kwana.

Bari yayi sai da aka ibi kusan wata guda da faruwar hakan kana ya nufi GOGEL ESTATE dake GRA, securitin dake bakin gate in a k'alla sun kusan su goma kuma majiya k'arfi, to shin ta ina ma zai tunkari wannan gida yace zai shiga? Ya tabbata sai sun rud'asa da tambayoyin gurin wa yazo, shikwa bai shirya amsoshinsu ba don hakan bai san wata matsala za ta janyo ba, yana gama wannan tunanin kawai ya juya zai bar layin, wata motace tasha gabansa da sauri yayi saurin ja baya yana kiran sunan Allah, kafin wasu mutane su fito daga ciki su dannashi cikin motar suka jata da gudun gaske.



Har bayan sallar isha Baba bai dawo gida ba, Nusrat sam ta kasa samun nutsuwa a zuciyarta, haka kawai take jin k'irjinta na ta mugun bugawa hakan yasa ta d'aukar carbi tana jaa, tun tana jin motsin Umma har taji shiru alamun itama ta kwanta, Yusra kuwa dama ta jima da yin bacci saboda yau tashi tayi ba ta jin dad'i, Nusrat ba tayi aune ba sai gani tayi har d'ayan dare tayi babu Baba babu labarinsa abinda bai tab'a yi ba kenan, fita tayi taje bakin k'ofar d'akin Umma ta k'wank'wasa mata.
Tsaki taji Umman ta jaa had'e da fad'in.
"To nima yau babu abinda na dafa sai kaje gurin shafi da man 'yarka ta baka don itace dolenka, haba da kai zanji ne ko da tshohuwar kwad'ayayyar matar can da komai aka kawo mun idonta yana kai, mtsss."
Wani bak'in ciki Nusrat taji ya kawo mata wuya, yanzu ya dace ta gayawa mijinta haka don kawai Allah ya jarabceshi da babu, ta manta duk irin d'awainiyar da yayi a lokacin da yake da shi, kuma rashin mutumcin bai tsaya kansa har da uwar da ta diroshi duniya, duk lalacewar iyaye ai iyaye ne ba'a isa a canja musu suna ba, juyawa kawai tayi ta nufi gurin Iya, k'wank'wasa mata k'ofar tayi kafin taji muryarta tace.
"Waye nan?"
"Iya nice, cewa nayi kinga Baba shiru har yanzu bai dawo ba."
"Ke kinjimu da fi'ilin yarinya, Baban naki k'aramin yaro da zai b'ata ko kuwa? Kika sani ko wata harkar samun kud'ince tazo masa."
Haushine ya kuma turnik'e Nusrat, wannan son kud'i irin na kakar tasu ba ta san irinsa ba, ita sam babu wani yare da take ganewa sai yaran kud'i masu shi kawai take mutumtawa take darajawa inkwa baka da shi kai da banza duk d'aya hatta a cikin 'ya'yanta ma, Allah ka rabamu da irin wannan zuciyar amin.
Gidan Baffa Shamsu ta nufa tana bubbuga musu gida, inda Allah ya taimaketa basui bacci ba kasancewar Mmn Amima ta fita unguwa ba ta dawo da wuri ba hakanne yasa girki yayi mata dare sai kusan shabiyu ta kammala, to shiyasa bayan sun gama ci suka zauna don abincin ya tsarga musu mai makon sui zaman shiru sai suka kunna tv film in da ake kuma yaja hankalinsu har suke buk'atar ganin k'arshensa to sai kuma suka ji bugu wanda ya tsorata Amima da mmanta, Baffa Shamsu ne kawai bai tsorata ba yazo yana tambayar. "waye?"
"Nusrat ce"
Ta fad'a da muryarta mai son fashewa da kuka, bud'e gidan yayi yana tambayarta.
"Lafiya Nusrat kuwa?"
"Babane har yanzu bai dawo ba." Ta fad'a tana mai fashewa da kuka, don haka kawai take jin kamar da akwai abinda ya faru da Baban.
"Kuma an kira wayarshi?"
"Bani da waya ai."
Ta fad'a da shashshek'ar kuka.
"Kinga kiyi shiru babu abinda ya faru insha Allah sai alkhairi shigo ciki in kira wayarsa muji."
Ya kira yafi sau a k'irga ana sanar masa a kashe take, amman yaki ya gasgata hakan gani yake kamar sharrin network ne, shima kuma sai hankalinsa yayi mugun d'agawa, don haka yacewa Nusrat bari yaje kasuwar tasu ya gano, Nusrat ta mak'ale akan sai ta bishi yace tazo su tafi, yacewa Mmn Amima ta rufe gidan in sun fita....









200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.



#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna


®️NAGARTA WRI.ASOCIATION


KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............17
Ba ko wasu mutanene suka d'auke Baba ba face mutanen da suka biyo wannan mutumin da ya bashi camera, yadda suka ga jinin sosai a bakin shagon Baban hakan yasa suka d'ora masa ayar tambaya, har suka sanarwa da ogansu ma'ana wanda ya sanyasu aikin shi kuma ya basu umarnin bin diddiginsa had'e da d'ora masa ido akan dukkan wani motsi da zaiyi, sun so rabuwa da shi da suka ga an ibi kusan wata baiyi wani motsi ba alamun zatonsu bai tabbata ba, amman sai ogan nasu yace suci gaba da sanya masa ido don akwai mutane masu matuk'ar wayo zai iya yuyuwa don ya b'atar da tunaninsu yayi hakan to sai yau kuma ya kawo kansa don suna ganinsa a bakin estate in suka san me ya kawo shi.

Azaba iri iri suka gana masa bayan sun gama bincikeshi ba su samu abinda suke so ba,kuma shi sam ya nuna musu bai san akan abinda suke magana ba don haka ogansu ya basu umarnin su kashe shi kawai ta yadda zargi bazai biyo kansu ba suje su wullar da shi a bakin shagonsa.
Wuya suka shak'e masa har sai da suka tabbatar ya daina numfashi kana suka sanyashi a mota suka zo suka wullar da shi anan bakin shagonsa, bayan sahun mutane ya auke gaba aya, to ko da Nusrat da Baffa Shamsu suka zo anan bakin shagon suka tarar da shi a yashe, Baffa Shamsu ya d'aukesa suka nufi hospital da shi Nusrat kuwa sai kuka take don sam ta kasa control in hawayen nata.
Kusan asibiti hudu sukaje babu gado sai a Gogel Hospital suka samu aka anshesa nan da nan aka bashi taimakon gaggawa anan suka gano doguwar suma yayi, sai da Nusrat taji wannan bayani na likitoci kana ta samu sanyi a ranta, amman duk da haka k'in bin Baffa Shamsu tayi tace yaje ita za ta k'arasa kwana da Baban, amman don Allah ya lek'a mata Yusra ba dad'i itama take ji ba.
Sai da garin Allah ya waye kana Baba ya farka, ya riga ya fidda tsammanin cigaba da rayuwa cikin duniya, ya saddakar a cikin kabari zai bud'i idanuwansa sai gashi ya bud'esu cikin duniya, sai dai bakinsa yayi mishi nauyi, kamar 'yar baiwa yake gani a kwance a k'asa amman baijin zai iya kiran sunanta, d'ankwalinta ta shimfid'a tayi sallar asuba sai a lokacin gwanin iya sata ya saceta ta takure cikin hijabinta.

Zuwan su Baffa Shamsu ne ya farkar da ita daga baccin da take kuma ta farka da mugun ciwon kai, akan Baba idonta ya fara sauka, duk sun bi sun zagayeshi kowa da tambayar da yake jefo masa bayan sannun da suke masa shi kwa sai binsu da ido kawai yake, murmushi ne ya sauka akan fuskarta sai taji ciwon kan da ta farka da shi yana raguwa a hankula tashi tayi ta k'arasa gaban gadon tana cewa.
"Sannu Baba,bara na kirawo likitan."
Jinjina mata kai yayi wanda babu wanda ya samu hakan daga gareshi sai ita kad'ai.
"To gwanar iya sai ki dinga nuna kamar kinfi kowa damuwa da shi, duk soyayyar da zaki masa baza dai ta huce wacce ni uwar da na kawo shi duniya nake masa ba, don haka kya iya dakatawa don tuni Shamsu ya tafi kirawo likitan tun da muka fuskanci ba ya magana."
Ba ta saurari zancen Iyan ba kawai tayi ficewarta, sauri kawai take zubawa sai ji tayi sunyi karo da mutum zuciyarta ce tayi wani irin harbawa har sai da ta danne k'irjinta tayi baya tana k'ok'arin tsugunawa ta d'aukowa mutumin sandansa da ya fad'i hannunsu ya sauka kai a tare d'agowa tayi tana me kallon fuskarsa yayin da shi kuma ya d'auki sandarsa ba tare da ko d'agowa yayi ya kalleta yayi gaba abinsa, fuskarshi kawai da ta kalla taji gabanta yayi wani mugun fad'uwa, a hankali kuma kyakkyawan murmushi ya bayyana a fuskarta can k'asan zuciyarta kuma taji tana fad'in.
"Kai kyakkyawa da shi, kamar yadda sandansa yake mai kyau."
Ganin tahowar Baffa Shamsu da likitan yasa ta juya ta koma d'akin har lokacin wani annuri ne ke fita akan fuskarta wanda ita kanta ba ta san dalilin zuwansa ba.(Nikwa nace bare kuma ni, ban sani ba ko masu karatu sun sani?)


"Zaiyi magana insha Allahu, yana buk'atar hutu ne sosai, don haka kamata yayi dukkaninku ku koma gida, muna da masu kula da marasa lafiyarmu don haka bama buk'atar d'an jinya ko d'aya, idan da matsala zan kirawo wayarka."
Yakai k'arshen maganar yana sauke idonsa akan Baffa Shamsu ma'ana da shi yake kenan yayin da Baffa Shamsun ya jinjina masa kai had'e da cewa duk su tashi su tafi, yayin da Nusrat tayi rau rau da ido za tayi kuka tacewa Baffa Shamsu.
"Wallahi duk sauran d'akunan naga da masu jiyya, shine zaice mu mu tafi, duk kulawar da za'a bashi ai ba ta kai wacce zamu ba shi ba."
"To ai su ba mu san irin ciwon nasu ba, shi ba kiji yace yana buk'atar hutu ba ?"
"Kai ka tsaya ma kana mata bayani me kafiyar tsiya ba a banza ba kika rasa mashin shini ai, naga in zaman jinyar nema nice zan zauna tun da mijina ne, ko kuma a bakacin uwarki zaki zauna tun da naga kishi kike tayata bayan rai."

"Me ya kawo maganar nan kuma Mamn Nimha, ku shige dan Allah muje."
"Kyaleta Shamsu ta wanke min ita tass, yarinya ta d'auki bak'in hali ta d'orawa ranta, kaga fa yadda ita da Yisra suka d'auki karan tsana suka d'orawa Shukhura don kawai yarinya 'yar albarka tana kula da mu, tafi son ta tare kawai a gindinsu saboda bak'in halin tsiya to ke wa ya hana ki fito da naki mijin."
"Allah dai ya kyauta, Iya don Allah ku muje ance ba ya son hayaniya kuma neman tayar da hayaniyar kuke."
Babu wanda ya kuma cewa komai suka d'unguma suka fita.



"Yayarmu ya jikin Baban, naga kuma dukkaninku kun dawo?"
Yusra ce da ke suyar waina ta jefowa Shukhuran wannan tambayar, tashi tayi jikin nata da d'an dama, to ganin an riga an hada komai na wainar miyarma tun jiya da daddare Yayartasun tq hadata to shine take yinta dalilin da yasa ma ba ta bisu asibitin ba kenan ta bari idan wainar ta k'are ta bi bayansu sai kuma gasu sun dawo.
"Da sauk'i jikin nasa, eh likatanne yace mu taho wai basa buk'atar 'yan jinya."
"To su kuma haka tsarin asibitin nasu yake, ko kwa akanmu suka fara yin hakan?"
"Wa ya san musu to Yusra."
Tana kawowa nan tai shigewarta d 'aki ziciyarta sam babu dad'i, kallo Yusran ta bita da shi tana jin kamar da akwai wani abu dake damin Yayartasun, sai kwa ga Amima tazo siyan waina kafin layi yazo kanta suna dan taba hira da Yusran sai kwa Yusran cewa tayi.
"Nikwa Amima akwai wani abu da ya faru da Yayarmu ne na ganta wani iri?"
Aikwa Amima ta kwashe komai ta gayawa Yusran, bak'in ciki yazowa Yusra wuya ta bud'e murya tace.
"To dai dad'in abin kowa yasan Katanga akai mana tsakaninmu da 'yar uwarmu saboda tsabar son abin duniya, kuma Allah yana nan ba ya,bacci bazai tab'a barin zalincin da akai mana ya tafi a banza ba, uwarmu kuwa da aka ambato tana kwance a kabarinta mun bar mutum da Allah don shi kadai zai mana maganinsa, miji kuwa ba ta isa ta bawa kanta ba sai ranar da Allah ya kawo mata shi, kuma muna nan da rai da lafiya na tabbata wata rana sai kun shiga inuwar Yayarmu, zuciyarta da ban take ba irin tamu bace ni da Shukhura don wallahi na tabbata Shukhura ta dawo hayyacinta ba za ta tab'a yafe muku ba amman Yayarmu kuwa duk abinda kukai mata ba shi zai hana watarana ta tsamo ku daga rana ta sanyaku cikin inuwarta ba."
Daga Iya har Umman duk suna jinta tana ta bambami babu wanda yayi tari alamun yana jinta, don Yura iskokan nata ma sunfi na Shukhura tsaf zuciya za ta jaho ta canja musu kamanni in suka kulata.


Bayan sallar azahar Yusra tacewa Yayarsu ta tashi ta rakata gurin Baba itama ta ganshi in yaso sai su dawo, tashi tayi ta shirya don itama hankalinta gaba d'aya yana kan Baban, nik'af inta ta sanya kana suka fito suka rufe d'akinsu suka tafi, ko da sukaje zasu shiga d'akin da Baban yake sai aka hanasu shiga ganin hakan yasa Nusrat ta nufi office in likitan, ta kai hannu za ta b'urd'a handle in k'ofar taji wata kakkausar murya na fad'in.
"Wannan allurar kawai zakai masa itace za ta k'arasa shi har lahira."
Da sauri ta d'auke hannunta daga kai jikinta yana wani irin rawa, tayi saurin barin gurin a gigice.
Dama haka asibitinnan yake kashe mutane suke yi, ko wa kuma zasu kashe?Shine abinda zuciyarta ke ta tambayarta kuma bata da me bata amsa, gaba d'aya nutsuwa ta bar gangar jikinta, Yusra sai tambayarta take meke faruwa amman ce mata take kawai ki bari bana cikin hayycina Yusra.
"To kenan baza muga Baban ba."
"To dai gashi sun hanamu ganinsa Yusra, ni bansan asibitinn me suke nufi da mu ba wallahi."
Takai k'arshen maganar kamar za ta kece da kuka, Yusra kuwa bayan wata nurse ta bi ta had'ata Allah annabi akan ta taimaketa taga mahaifinta, nurs in ta rasa yadda za tayi da Yusra duk ta inda ta b'ullo mata sai ta goce, k'arshe dai wasu kayan ta bata irin wanda nurs in ke sakawa tace ta saka sai ta shiga babu wanda zai hanata, godiya Yusran tayi mata ta karb'a ta saka, kasancewar tana da tsayi da girman jiki babu wanda zaice shekarunta goma sha uku kacal, har tazo ta shige Nusrat ba ta lura ba saboda gaba d'aya hankalinta yana kan office in likitan so take taga shi da waye zasu fito daga ciki.


Sun samu labarin Baba bai rasu ba don haka suka shiga binciken wani asibiti aka kaishi daga k'arshe suka gano yana nan gogel hospital, shine ogan nasu yayiwa likitan waya akan kar ya bar kowa nasa yaje inda yake, wannan dalilin ne yasa aka koresu zuwa gida yanzu kuma aka hanasu ganinshi, ogan nasu kuma yazo da kansa gurin likitan saboda kasancewar asibitin a k'ark'ashinsu yake kuma likitan ya saba mishi irin wannan aikin idan buk'atar hakan ta taso, shiyasa suka k'ule cikin office insa suna tattaunawa wanda tsautsayi yasa Nusrat ta jiyowa kunnuwanta abinda ya rikirkitata.

Tana nan tsaye suka fito shi da likitan, ta cikin nik'af inta take k'are masa kallo, saurayine kyakkyawa da shi amman yake wannan d'anyen aikin shikwa me yasa, ba dai zai wuce kud'i ba wanda tasan sune zasu saka likitanma ya amshi buk'atarsa, a ranta kawai taji tana adduar Allah yasa kar dai likititan ya amshi buk'atarsa, kai da ma wuya kam don irinsu in baa amshi buk'atarsu ba kashe mutum suke.
Yusra ce itama ta taho bayan ta fito daga d'akin da Baba yake, sakin baki tayi tana kallonta yayin da likitan ya nufota yana kiranta "Murja" Da alama sunan wacce ta bata kayan kenan, yayin da k'irjin Yusra ya fara wani irin bugu ta daskare a gurin a tsaye...



Nayi k'okari ai, dogon typing yana bani wuya, amman zanyi kokari kullum ina post in banyi ba to kumin uzuri ban samu lokaci bane na gode.










200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.



#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna


®️NAGARTA WRI.ASOCIATION


KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............18’
"Likita"
Nusrat ta fad'i haka tana shan gabansa wanda hakan ya bawa Yusra damar bacewa daga gurin kamar walk'iya.
"So muke a sallamemu."
Ta fad'i hakan tana d'age nik'af in fuskarta domin ya shaidata.
"In lokacin sallamar yayi ai zan sallameku ba sai kun bukaci hakan ba."
"To ai asibitin naku ne yayi tsauri da yawa ance babu masu jinya sannan kuma yanzu an hanamu shiga muga mahaifinmu, ai abin baiyi tsari ba sam wallahi."
"Ke yarinya ce baza ki gane abinda muke nufi ba, amman zamuyi magana da d'aya namijin."
Ya fad'i haka yana neman barin gurin yayin da Nusrat tayi saurin shan gabansa.
"Nifa bazan bar asibitin nan ba sai naga mahaifina wallahi."
"K'warai kuwa Yayarmu, mu da mahaifinmu ai mana k'arfa k'arfan hanamu ganinsa, bayan duk ga sauran d'akunan marasa lafiyan ana ta shige da fice sai mu za'a hana shiga."
Cewar Yusra da ta nufo gurin da suke a tsaye.
"Mahaifinku yana buk'atar hutawa sosai, wannan dalilinne yasa muka hana kowa ganinshi, da wani yare kuke so nai muku ku fahimta ne?"
"Toh munji, amman yanzu muje tare muganshi sannan sai mu tafi." Suka fad'i hakan a kusan tare, ganin dai babu yadda zaiyi da su don Yusra har gefen rigarsa ta rik'e yace.
"To sakeni ku muje d'akin"
A ransa yana addu'ar Allah yasa Aasad yayi abinda zaiyi ya fita to sai kuma suna karya kwana suka ci karo da shi, don haka likitan yace su jirashi anan bara yaje ya daho, bai jira me zasu ce ba yabi bayan Aasad in.
Cikin muryar tashin hankali Aasad in yace.
"Likita akwai matsala"
"Bai mutu bane ko wanine ya ganka?"
"To ai in wani ne ma ya ganni da sauki don akwai hanyar da zan bi na aikashi lahira shima, ya gudu, baya cikin d'akin na duba ko ina da ina kaga takardar da ya bari akan gado"
INA NAN DAWOWA
Innalillahi likitan ya hau ambata bayan ya gama karanta takardar.
"Yanzu meye mafita, me zan cewa wa'yannan yaran su fahimta"
Ya zauna dab'as akan kujera yana jujjuya kansa ya rasa mafita guda d'aya gareshi.
"Kai ta abinda zaka cewa iyalinsa kake, ni kuma ta abinda zaije ya daho nake, don haka nayi alkawarin sai na binciko inda ya shiga a duk fad'in garin nan in kwa bai wasa ba sai na kashe dukkanin ahalinsa."
Yana kawowa nan ya fice daga ofis in yana banko k'ofar da k'arfi ta bada k'ara mai sauti, likita dai kulle kansa yayi a ciki don in ya fita baisan me zai gayawa wayancen yaran ba don ya tabbata sai sun tara masa mutane, musamman wacce ta rik'e gefen rigarsa don yaga alamun rigimammiya ce, su kuwa da suka gaji da tsaiwa sai Yusra cewa tayi.
"Yayarmu zo mu tafi ina jin dai likitannan wayo yayi mana ya gudu, tunda dai na samu na shiga na ganshi ai shikenan."
"Wai kayan wa kika saka ne?"
"Wallahi wata nurs ce ta bani, ina zuwa kuwa ba tambayar wani d'aki zan shiga tun da sun ganni da uniform, amman dai har yanzu ba ya magana yasa na mik'o masa biro da takarda da aka ajiye kan drowa yayi rubutu a jiki ya bani na baki."
Takai k'arshen maganar tana mik'o mata takaddar, karb'a tayi tana fad'ii.
"Mu tafi gidan, amman wallahi gobe duk bura'ubar da za'ayi sai dai ayi sai naga Babana."
Jinjina kai Yusra tayi, tunda suke bata tab'a jin Yayarsu tayi zagi ba sai yau, soyayyar Baba da Yayarsu daga Allah ne, sun kwana da sanin yafi k'aunarta a cikinsu kamar yadda Mama tafi k'aunar Shukhura sai dai b'oyewa da suke k'ok'arin yi.

Likita ya shiga mugun cakwakiya ya rasa yadda zaiyi, taya zaai ace paitent a cikin asibitin nan ya gudu?Dole sai 'yan uwansa sun tuhumesu kuma hakan zai tab'a kimar asibitin wanda ya tabbata Aashiq yaji bazai tab'a k'alewa ba kuma tabbas hakan zai iya sawa ya binciko abubuwa masu yawa da suka bunnesu, don haka kawai ya yanke shawarar zuwa mutuware, ya samo gawar da ba'a gane fuskarta kana yaje yayi report wa 'yan sanda bayan suma ya basu cin hanci me tsoka kana washe gari ya kirawo Baffa Shamsu akan yazo asibiti akwai matsala.

Tunda Amima ta shigo ta gaya musu cewar Baffa Shamsu ya tafi asibiti an kitashi akan akwai matsala Nusrat take zabga uwar gudawa mai azaba ta tashin hankali, gaba d'aya gidan kowa ba ya cikin nutsuwarsa,can bayan jimawa da tafiyarsa suka ji hayaniya ar mutane a waje, Nusrat ce ta zabura ta mik'e had'e da fad'in.
"Shi kenan sun kashe shi wallahi."
Dai dai nan Baffa Shamsu ya shigo, fuskarsa kawai ta kalla ta saki murmushin rashin mafita had'e da fad'in.
"Kun gani dama na fad'a wallahi sun kashe mini Babana."
Iya da Umma Baffa Shamsu yaja gefe yana gaya musu abinda ya faru k'asa k'asa.
"A yadda likitan da police sukamin bayani wai fitowa yayi da niyar guduwa daga asibitin shine su kuma suka bi bayansa a k'ok'arinsa na tsallaka titi mota tabi ta kansa,kuma sunce har yau basu gano dalilinsa na yunkurin guduwa ba, ga gawarsa can na shiga da ita can gida zan had'ata."
A tare Iya da Umma suka saki salati da gunjin kuka, hakan yasa Nusrat da ke ta k'ok'arin k'wacewa daga rik'on da Mman Amima tayi mata na sai taje gurin da su Iya suke magana, fasuwar kukansu yasa ta samu amsar da take son zuwa juyowa, a hankali idanuwanta suka k'afe k'af numfashinta ya d'auke gaba d'aya."


A hankali idanuwanta suke washewa yana dad'e tariyo abinda ya sameta, cak idonta ya

Please Login or Register in order to submit comment