Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cewar Hibba da ta d'auke ganinta ga kowa illa Daddy da ta fuskanta, duk da ta tsorata da tsawar da Mommy ta daka mata hade da cewa ta fice ba da ita ake magana ba amman Daddy ya dakatar da ita da fadin yana jinta, tabbas za ta fadi gaskiya ko da kwa Momy za tayi gunduwa da naman jikinta.

"Yayarmu ba ta san maganar Ishaq ba Aunty Hidaya ce ta tsara komai, kuma Momy tayi mata gargadi akan ta amshi maganar auran Ishaq in don Aunty Hidaya ta samu Yaa Rj a hannu."

"Jeki abinki Hibba, Allah ya yi miki albarka."

"Amin Daddy."
Ta tashi ta fita tana kuma tsoron haduwarta da Mommy don sai huci take ta Hidaya kuwa me sauki ce.

"Tabbas Ridwan na so had'a auranka da Hidaya, don duk a tunanina kun jima da hada kanku ashe ba haka abun yake ba, da Hidaya da Nusrat duk daya na daukesu a gurina, idan naki Nusrat tamkar naki Hidaya ne, don haka zanje na nema maka auran Nusrat insha Allah, kuma ba zaa ja lokaci ba kamar yadda kake so."

"Amman banji dadi ba, meyasa Daddy tun tuni ba ka sanar da ni wannan kudirin naka ba?"

"Saboda ba na son ku tirsasa zuciyoyinku yin abinda bashi take so ba, don haka kada kasa komai a ranka, duk sona duk kaunata na ganinku inuwa daya da Hidaya idan Allah bai so ba hakan bazai taba faruwa ba."
Yana kawowa nan ya kalli Hidaya yace .
"Sai ki warware auren da kika so kullawa, don wallahi muddun suka zo gobe to ke zan basu, kuma daga yau kisa a ranki ita soyayya ba'a kwacenta ta dole Allah ne yake dasawa bayinsa ba tare da saninsu ba, da kin mikawa Allah lamuranki kina iya samunsa ta cikin sanyi ba tare da kinsha wahala ba idan har mijinki ne a rubuce bazai taba gogewa ba."

Yana kawowa nan ya tashi zai shige bedroom don wani irin zafin Momy yake ji, saboda irin turbar da ta dora 'yarsa akai, Nusrar da kukanta ya fara yin k'asa ta kirashi.

"Daddy"

Tsayawa yayi yana jiran jin abinda za tace.

"Daddy na hak'ura da Yaa Rj na barwa Hidaya, wallahi ban san da maganar aure tsakaninsu ba, kuma ban san tana sonshi ba duk da ban bude zuciyata gareshi ba, Daddy ni me iya sadaukar da komai ce ga Hidaya muddun hakan zai sama mata kwanciyar hankali."

Gaba daya ya juyo ta zubawa fuskarta idanu, yana kuma jinta cikin ransa, kafin yace.
"Ke da ake so, kinji zaki iya sadaukar mata da shi, amman ita da ita take so ta kasa sadaukar miki sai ma k'okarin cusaki wani guri da take, Hidaya wannan nuni ne gareki, yadda Nusrat ta daukeki ba haka kika dauketa ba, Allah yayi miki albarka Nusrat, tabbas kin samu kyakkyawar tarbiya, amman ina so ki sani aure da ke da Ridwan sai dai in babu shi a rubuce."

Yana kawowa nan yayi shigewarsa d'aki.


。。。。。。

Daddy yaje ya nemawa RJ auran Nusrat gurin Baffa Shamsu, ya kuma bashi babu jaa don duk abin na gida ne, a take ya bada kud'in aure suka tsayar da rana bayan sallah babba.

Rj gaba d'aya ya kasa gane kan Nusrat don duk ta sauya, kullum cikin kunci da damuwa zaka sameta da yayi magana za tace ita wallahi ta hakura ta barwa Hidaya shi, shi kuma ransa yakan baci da jin kalaminta sai yaga kamar dama can ba son nashi take ba, ita kuwa tsoron abinda zai biyo baya take yi, don yanzu Mommy ko gaisuwarta ba ta amsa haka Hidaya ko kallon inda take ba tayi, duk da nasihar da Daddy ya zaunar da ita yayi mata duk a banza, tana tsoron yadda wannan aure zai tafi ya raba zumunci tun kan a daura shi.

Tsakanin Momy da Daddy kuwa babu wani shiri, don tayi mugun shaka da yace Nusrat ta samu tarbiya yana nufin ita ba ta bawa nata yayan tarbiya ba kenan, shiyasa da ya watsar da ita itma ta watsar da shi don tana shirin yadda za ta watsa rayuwar Nusrat ne kawai don diyarta ta samu abinda ta ke so don har ciwo Hidayan ta kwanta bayan ankai kudin Nusrat in.



Hibba ce take b'allo mata magun gunanta na ulcer tana bata ta sha, don kwana biyu ulcer ince ta takura mata sosai, a had'e ta bata su gaba daya ta korasu da ruwa ba tare da ta duba ko guda nawa bane don da ta lura za taga da karin guda daya wanda Hidayace ta jefa mata shi a ciki don ta sha su samu plane insu ya tafi dai dai, sun samu Daddy yayi tafiya, sai da Hibba ta bar d'akin sannan Momy ta shigo.
" Ki had'a komai naki driver yana jiranki zai mayar da ke gida."
Shine abinda tace mata ta juya ta bar d'akin, jiki a sanyaye take had'a dukkan wani abu da ta san nata ne cikin wata k'atuwar akwati da Rj ya bata, tana hadawa kirjinta na dukan tara tara, ko da ta gama had'a kayan nata sai ta nemi wayoyinta babba da karamar ta rasa, har Momy ta dawo tana neman wayar.
"Naga dai ba da ita kika zo cikin gidan nan ba, don haka kizo ki shige driver yana jira."

Ba tace komai ba ta janyo akwatinta ta shige, amman ta so ko da sim inta ne ta cire don shi take yiwa tunda dama da abinta tazo ba anan ta same shi ba.


Idanuwanta ta lumshe bayan dai daituwarta cikin motar driver ya ja suka fara tafiya, kafin wasu zafafan hawaye su biyo kuncinta har lokacin kirjinta yana wani irin bugu don ba ta san me suka shirya mata ba .....


Last free page
09037093702
[4/26, 8:46 PM] Rabi: 31

Sun kusan cin rabin tafiya taji mararta tayi wani irin k'ullewa had'e da murd'a mata, rintse idanuwanta tayi tana jin yadda marar tata ke murd'awa da alamu dai period inta ne ke hanya duk da tayi mamakin zuwansa a wannan lokaci don lokacinta bai k'arasa ba ba tafi sati biyu da gama wancan ba sai dai kawai tayi la'akari da wani zubin yakan canja lokacin zuwansa, fatanta dai har su isa gida bai zo ba gudun kar ta b'aci saboda ba shirin zuwansa tayi ba, sai dai fatanta nata bai ciyu ba suna karya kwanar layinsu taji yayi wani ambaliya ya fito saboda sama da kasa da motar tayi saboda jakin baban gida da suka tsallaka, innalillahi take ambata a cikin ranta tana adduar Allah yasa ba ta bata motar ba don in ta jikinta ne da sauk'i saboda dogon hijabine har k'asa a jikinta kuma copee ne kalar baza ta fito ba sai dai danshi, kuma ba matsala tunda har k'ofar gida za ta sauka.

Ko da yayi parking a k'ofar gidan nasu ji tayi tana jin nauyin mik'ewa don yanzu ta riga ta tabbatar tayi rushing sosai, inda Allah ya taimaketa sai ya fita daga cikin motar don fito mata da akwatinta da ke cikin boot, idonta ne ya sauka akan dostar motar tayi saurin janyota kafin ta zira k'afafuwanta waje a hankula ra fita daga cikin motar kana ta d'an durk'uso tana goge gurin da dostar, kana ta saka ruwa ta kuma gogewa sai ta rik'e dostar a hannunta don ba za ta iya ajiye mishi ita a haka ba kuma ba za ta iya wullar da jininta ba har sai ta wanke.

Daga nan suka yi sallama da driver ya juya saboda babu yunwa a tattare da shi ko kishirwa duk da abinsa ya taho saboda Momy tace yana ajiyeta ya juyo ko gidan ba ta yadda ya shiga ba.
Jan akwatinta tayi ta nufi cikin gidan nasu da duk wani taku da za tayi da bugawar kirjinta yake tafiya wanda ba tasan dalilin hakan ba, da sallama a bakinta ta shiga inda ta tarar da IYa da Baffa Shamsu da Umma a tsaye a babban tsakar gidan sun zubo mata idanuwa wanda hakan yasa zuciyarta wani irin harbawa, kafin sautin maganar Baffa Shamsu ya sauka cikin kwanyarta.

"Me kika zo yi mana? tunda abinda kika zab'awa rayuwarki kenan ai sai kiyi gaba don baza kizo ki bata mana sunan gida ba."
Yayin da Iya tace.
"Banda abinka zuwa tayi ta shafa mana bak'in fentin da ta shafowa kanta, don sunan zuriarmu ya b'aci, inama Malam zai dawo yazo yaga wacce yake kira 'yar baiwa yau ga baiwarnan mun gani a k'asa, baiwar karuwanci ba."

Saurin rintse ido Nusrat tayi tana jin saukar kalmarta ta k'arshe tare da sarawar b'arin kanta, kafin Umma tace.

"To ai dama ai ba abanza taki yin aure ba, dama jira take ta samu guri ta fito da zallar ainihin abinda take aikatawa, gashinan kuwa mun gani anyi walk'iya ta haska mana, ku kalli k'afarta ga jini nan yana d'igowa da alama cikinne ya fara fita."

Wani ululun bakin ciki ne ya kama Baffa Shamsu, yana jin takaici da tsanar abinda Nusrat in ta aikata, banda daga bakin Aunty Maryam yaji to tabbas bazai yarda ba a yadda yasan tsananin tarbiya a gurin Nusrat in da kamun kai, yayin da Iya kuma ke ta rafka salati tana bin jinin da ke diga a kasa da kallo.

"Tun kan hannuna ya sauka a jikinki ki kama hanya ki bar gidan nan, duk randa zuciyarki ta tsarkaka zaki iya dawowa amma da sharadin sai na aurar da yata don bazanyi saken da zata kasa auruwa kamar ki ba, wannan shine hukuncin kawai da zan iya yi miki."
Cewar Baffa Shamsu

Wasu zafafan hawaye ne suka ziraro ta kuncinta tana jin yadda zuciya da ruhinta ke wani irin radadi, radadi mai zafi me huyar fassarawa, karuwanci shine abinda ke yawo cikin kanta kuma ta kasa bashi maauni wanda zai auna ya bata me kalmar ke nufi.

"Nifa ban fahimci me kuke magana akai ba, bansan me na aikata ba kumin bayani don Allah yadda zan fahimta."

"Mu zaki mayar 'yan iska kidahumai, to anki a miki bayanin, ki bace mini da gani na daina ganin bakar fuskar nan taki me kama da ta 'yan ruwa."
Cewar IYa
Ido ta k'urawa Iyan kamar a fuskarta za ta karanci amsoshin da take son ji yayin da Iyan ta fara rarumar wani ice da ke gefenta had'e da cewa.
"Zaki fice daga cikin gidannan ko sai na karya kasusuwanki, don naga alamun don baa taba fatar jikinki ba ne kika tsaya kina mana taurin kai."

"Zan fita, amman don Allah ki barni na fara gyara jikina."

"Alqur'an kinyi kad'an, cikin gidan malaman zan bari a wanke jinin shege, sakamakon da za kiyiwa soyayyar da Mallam da Audu suka nuna miki kenan, to ba da Zainabu ba wallahi."

"Ki barta ta fara gyara jikin nata mana."
Cewar Baffa Shanmsu.

"Alqur'an baza ta wanke mana d'an shege ba a gidan nan, idan ta k'ara can gaba koma dandalin karuwanne ta wanke."

Meye laifinta ne, me ta aikata musu suka tsaneta?Idan dan son da Rj yake mata ne itace tace ya sota, ko kwa ita ta dauki sonta ta d'ora masa, yanzu wannan laifin har ya kai su tsaneta ya kuma kai matakin da zasu yiwa rayuwarta wannan qullin, qullin da Allah ne kad'ai zai iya fidda ita?

Tafiya take tana jan akwatunta zuciyarta bak'ikirin, duk wani bayani tayi musu na cewar ba ta san maganar da suke ba sunk'i fahimta kuma ba ta san da wani yare za tayi musu bayanin da zasu fahimta ba, ba ta da wani zab'i da ya wuce na ficewa daga gidan don Iya ta tsaya kai da fata ko gyara jikin nata ba za ta bari ta shiga tayi ba.

Tafiya take ba ta san inda zata dosa ba, ba ta da kowa su d'innan dai sune nata, kuma ga abinda suka yi mata, duk maraici shine ginshik'in da ya kawo rayuwarta a haka ta tabbata da yanzu tana jikin Mamanta wacce ta katangesu daga dukkanin wasu matsaloli, amman gashi k'addara ta kawota bigiren da gidan mahaifinta ma ya gagare ta zama bayan k'azamar kalmar da suke kiranta da shi.

Idan tace gidan Auncle Iliya za taje, wani nauyin za taje ta kuma d'ora musu, idan kuma tace cikin gidane to tabbas babu wanda zai iya rikonta a ciki sai dai wuk'a da ta d'auko ta kuma dabawa cikinta, don zasu tambayi dalilin korarta idan ya fasu kuwa sunanta ya riga ya gama b'aci wanda babu me wanketa sai Allahn da ya halicceta, don haka kawai ta mik'i titi tana tafiya ba tare da tasan inda take jefa k'afafuwanta ba, da kuma inda ta dosa ba, ina kuma rayuwa za ta d'auketa ta kaita?
[4/26, 8:46 PM] Rabi: 32
A gajiye ya shigo cikin gidan lik'is, tun safe da ya fita sai yanzu da ake magana da sallar isha ya samu kansa sakamakon wani aiki da ya tattare masa guri aya, bashi da wata bukatada ya huce na yin wanka tare da sauke sallar ishar da ta rage masa ya nemi makwanci kuma don wuce gajiyar gaba d'aya, amman kuma sam zuciya da idaniyansa sun kasa hak'uri Nusrat kawai suke da burin fara gani, tun bayan fitarsa da sukayi waya ba su sake yi ba saboda bai samu kansa gaba daya ba a wunin yau din.

Kansa tsaye cikin gidan ya nufa yana fatan ya sameta a falo ko daga nesa ne ya kalleta zuciyarsa ta samu nutsuwa ya juyo ba tare da magana ta shiga tsakaninsu ba, sai dai kuma Hibba kawai ya tadda a falon tana mutumin nata, sannu da zuwa tayi masa da ka ya amsa mata kafin yace tayi masa magana da Nusrat sai cewa tayi.

"Wallahi Yaa tun dawowata daga islamiya nake mata nocking don na kuma duba jikin nata amman shiru ba ta bud'e ba, to nayi tunanin ko bacci take shine na rabu da ita, to yanzu zamana kenan na gama nocking in shiru, naiwa Aunty Hidaya don naji ko lafiya sai tace mini tana toilet Momy kuma da naje sallah take, shine nake jiran idarwarta naji ko lafiya"

"To Allah yasa lafiya, jeki ko ta idar, sai ki taho da safayar makullin dakin a bud'e a gani"
Ya fad'a da gajiya cikin muryarsa da ta had'e da fargaba da tashin hankali, ko da Hibba ta koma dakin sai ta tarar Mommyn ba ta idar ba don haka ta d'ebo safayar mak'ullan gaba aya da ke cikin drower gado don ba ta san wanne ne daga ciki ba, tunda ba fiya amfani akai da dakin ba sai yanzu da Nusrat in ta zauna bayan sun raba daki da Hidaya.

Da Allah ya taimakesu suna gwada maullli na uku sai d'akin ya bud'e, wayam d'akin ba kowa a cikinsa, duk da kirjinsa da ke bugawa amman sai ya bawa kansa k'warin guiwar cewa Hibba.

"Kiyi knocking a toilet ko tana ciki."
Itama dama tunanin da take kenan don haka ta karasa bakin kofar toilet in tana nocking, tayi kusan sau uku amman shiru don haka kawai ta bud'e, nan dinma dai babu kowa a ciki, ban dakin ma a bushe yake da alamu an jima baa shiga cikinsa ba.
"Yaa ba ta ciki." lumshe gajiyayyun idanuwansa kawai yayi, yayin da ita kuma idonta ya sauka kan wata farar takadda da ke kan drower gado da sassarfa ta isa gurin takaddar had'e da wareta gaba aya.

"Yaa RJ
shine a farkon layin rubutun don haka tayi saurin janye idonta hade da mika masa, har lokacin idanuwansa a lumshe suke don haka sai da ta hada da cewar.
"Yaa ga takadda ta bar maka."
"Fad'i meye a ciki"
Ya fada ba tare da ya bude idanuwansa ba.

"Yaa Rj kayi hak'uri bazan iya auranka ba saboda bani da kima da darajar da ko wace mace ke bawa mijinta, Ishaq ne ya cuceni yaci amanata ya b'atan rayuwa, ciwon da na kwanta nace muku ulcer ce to ba ulcer bace laulayin ciki nake, tun da na tabbatar da ciki nake dauke da shi naji bazan iya hada ido da kai ba da Aunty Maryam da Daddy don haka kawai na yanke shawarar barin gidan tun kafin ku gano tab'ar gazar da na aikata, don Allah ku gafarce ni."
NUSRAT


Bazai ce ga yadda akai ya kawo kansa d'aki ba kawai dai ya tsinci kansa ne a ciki, kayan jikinsa kawai ya tub'e ya fada toilet hade da sakarwa kansa ruwan d'umi ya dade ruwan yana sauka a kansa kafin yayi wanka da d'auro alwala, yana gabatar da sallar ya fad'a gado a rigin gine, duk yadda yakai ga buk'atar sanyawa cikinsa wani abu, ji yayi bakinsa bazai iya karb'a ba bare har ya kaiwa cikin a yadda yake jin ransa gaba aya a jagule, zuciya da k'wak'walwarsa gaba aya a cunkushe suke ya rasa wani irin tunani ma zaiyi abu d'aya ne dai kawai ya san Nusrat ba za ta tab'a aikata abinda ta rubuta ba, ko ma dai meye yana son ji daga bakinta don haka tun asuba zai d'auki hanyar zariya yanzunma don dare yayi ne.


Gurin Momy Hibba ta nufa da takaddar a hannunta, takaddar kawai ta bata ba tare da tace komai ba.
Momy na gama karantawa ta hau tafa hannu da sallallami kafin tace.
"Dama sai da jikina ya bani babu yadda baayi da ita ba aje asibiti tak'i yadda ta kafe akan ulcer inta ce ta tashi a siyo mata magani kawai, aini yadda naga tana ta tashin zuciyar nan da amai ta kuma cinye goron d'ari nasan akwai bayani, ashe cutarmu 'yarnan tayi cikin shege ta yo mana a cikin zuriarmu, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun."
Sai ta fashe da kuka yayin da Hidaya ta fito tana tambayar abinda ya faru Mommyn tana gaya mata, Hibba dai zare jikinta tayi ta bar d'akin sam ba ta yadda da wannan zancen ba, ta tabbata ba haka zancen yake ba, ita damuwarta ma ina Nusrat in ta tafi fatanta dai Allah yasa tana zariya sai aji komai daga bakinta."



Daa da yadda zaiyi ya cire son Nusrat daga zuciyarsa da yayi, saboda zargin da yake tayi hakanne kawai don gujewa auransa saboda ya auri Hidaya, idan sonshi ta daina yi ai ba sai ta shafawa kanta bak'in fentin da ba ya kankaruwa a jikin mutum.
Memakon yaji son nata na raguwa sai dai ma dad'uwa da yaji yana yi burin idaniyanshi kawai ya saukesu a kanta.
Yana idar da sallar asuba kamar yadda ya k'udurce a ransa ya d'auki hanyar zariya, sai dai zancen da ya samu daga bakin Baffa Shamsu duk ya gama dagula masa lissafi, har yanzu zuciyarsa ba ta gasgata abinda ake zargin Nusrat in da shi ba, shi babban tashin hankalinsa ma da aka koreta, ina ta nufa ina taje duk bai sani ba kuma bai san wanda zai sanar da shi ba, Yusra ce ta fad'o masa a rai don haka ya lalibo numberta ya danna mata kira.

"Yaa Rj kai nake lalibowa zan kira ka had'ani da Yayarmu tun jiya nake kiranta ban sameta ba."
Maganar Yusra ta sauka cikin kunnuwansa rintse idanuwansa yayi yana jin yadda kansa yayi wani mugun sarawa, ji yayi bazai iya yi mata magana cikin halin da yake ciki ba don haka kawai ya kashe wayar gaba d'aya.




。。。。。。。

Ko ina ta samu jefa k'afafuwanta take saboda yadda k'arfinta gaba d'aya ya k'are gashi dama ba ishashshiyar lafiya gareta ba, ga kuma b'acin rai da cunkushewar zuciya, da kuma tunanin rasa makoma, akwatin nata ji tayi kamar ta wullar saboda yadda yayi mata nauyi ta gaji da jansa, sai dai akwai abubuwanta masu matuk'ar muhinmanci a ciki, tun tana iya taka k'afar tata har ta kai ta kasa d'agata ma, ga hadari da ya had'o yayi murtuk gari yayi bak'ik'k'irin dama magariba ta kawo kai da alamu sallar yake jira ruwa ya sakko gaba aya, gabas yamma kudu arewa duk ta duba ba ta hango wata mafaka da za ta fake ba kafin saukowar ruwan, don haka ba ta da wani zab'i da ya huce zama a gefen titin don k'arfinta ya k'are har ankai matakin da k'afafuwanta ba zasu iya d'aukar gangar jikinta ba.

Ana idar da sallar magariba kuwa ruwa ya kece kamar da bakin k'warya, har sai da Isha ta gabato kana ya fara tsagaitawa, wanda gaba d'ayansa ruwan akan Nusrat ya sauka kuma ruwan har da k'ank'ara, ta fice gaba d'aya daga hayyacinta numfashinta sai sama yake da k'asa daga k'arshe ta tsaya cak da aiki....
[4/26, 8:46 PM] Rabi: 33

Motoci ne farare k'al guda uku a jere sai zabga uban gudu suke akan titi kamar zasu tashi sama, har sun gota gurin da Nusrat ke yashe ba ta da maraba da gawa motar da ke tsakiya tayi ribas ta dawo, a dai dai gurin da Nusrat ke yashe dreban yayi parking, yana fitowa a hanzarce rik'e da lema a hannunsa, sai dai ya tarar har ogan nasu ya fito ya nufi gurin da Nusrat ke yashe ga mamakinsa sai gani yayi yasa hannu ya ciccib'ota sai yayi saurin bud'e masa murfin motar ya sakata a ciki, sai jin saukar dakakkiyar muryarsa yayi cikin kunnuwansa yace.

"Ka saka akwatin cikin boot."
daga haka ya nufi gaban motar ya bude barin da ke zaman banza ya shiga saboda babu space in da zai zauna a bayan duk ta cikeshi.

Asibiti direct suka nufa da ita wanda sina zuwa aka karb'eta aka shiga bata taimakon gaggawa, sai da suka ga komai ya dai daita kana suka baro asibitin.


Tun kafin isowar motocin nasu securityn da ke bakin babban get in sun wangale musu, suna jiran k'arasowarsu, a guje a kuma jere suka shige suka d'auki titi d'od'ar kafin su tsaya a wani plat mension da ya gaji da matuk'ar had'uwa, ko da suka yi parking a harabar ajiye motocin babu wanda yayi yunk'urin fitowa ganin ogan nasu har lokacin bai fito ba, don drivern da ya tuk'oshi yana parking ya zaga side in da yake ya bud'e mishi k'ofa yana jiran fitowar tasa wanda sai da ya gama shan k'amshin shi kana ya fito ganin haka yasa yaransa sukayi saurin fitowa had'e da take mishi baya har zuwa asalin k'ofar da za ta sadashi da asalin cikin gidan kana suka jaa birki har sai da ya danna code jikin k'ofar ta bud'e ya shige kana suka juya kowa ya tafi yin uzurin gabansa.

Falo ne k'ayatacce wanda aka cikashi da dukkannin wani kayan k'awa na duniya, Baba Azumi ce kawai a falon, itama abincinsa ta had'o a babban tray za ta kai masa.
"Sannu da zuwa d'an uwana."
"Yauwa Baba sannu da k'ok'ari, sai dai yau ba na buk'atar abinci tea kawai zaki taimaka mini da shi me yaji."

"An gama d'an uwana."
Ta fad'i hakan tana k'ok'arin juyawa yace.
"Amm Baba Hadiza taje parking space Khalil yana jiranta."

"Insha Allah zan isar da sak'onka."

Kai kawai ya jinjina mata had'e da nufar b'arin dama inda zai sadashi da sashensa, falo ne k'awatacce wanda yafi na farkon k'awa sai dai shi wannan babu hayaniya a cikinsa, akwai dining area da 2 bed rooms a ciki, d'aya daga cikin bedroom in ya nufa wanda da shi kawai yake amfani, komai na ciki jajaye ne saboda kalar da yake auna kenan, kayan jikinsa ya tub'e had'e da shigewa toilet ya had'a ruwan wanka ya shige ciki kafin ya lumshe kyawawan idanuwansa wanda suke d'auke da dogayen eye lashers zara zara.



Tea in da Baba Azumi ta kawo masa yake sha a hankula yana lumshe idanuwansa, wayarsa da ke gefensa ce tayi k'ara a hankali ya sauke idonsa kan wayar, Bro Asghar shine abinda ke yaho akan secring in wayar d'auke idonsa yayi daga kai yaci gaba da sipping tea insa sai da yayi mishi miss call uku a jere ba tare da yayi peking ba, sai kuma wata wayar ta shigo da ban shima sai a miss call na biyu kana idonsa ya sauka yaga ba na

Please Login or Register in order to submit comment