Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa sun dad'e da mannewa cikin idanuwansa, yana mugun sonta, idan yace so yana nufin so na hak'ik'a wanda babu d'igon algus a ciki.
Bazan iya jure rashinki ba NUSRAT ki taimakeni ki gaya mini ba ki bud'ewa kowa zuciyarki ba sai ni don Allah na rok'eki ba don ni ba kar ki karya alk'awarin da nake murnar kin rik 'e mini shi.
Abinda yake sak'awa daga can k'asan zuciyarsa kenan yayin da wani b'ari na zuciyarsa yake jin kamar gaske ne maganar da Hidaya ta gaya mishi, tun da lokacin da yake saurarar jin ta bakinta shiru tayi masa alamu kenan na ta riga ta bud'ewa wani zuciyarta, kai ina ba haka bane tana dai da wani dalili nata.



Bayan fitarsa zubawa wayar ido tayi da Ishaq yake ta faman hello hello da ya gaji ya kashe wayar, rintse idanuwanta tayi tana jin yadda jijiyoyin kanta suke mik'ewa.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda take ambata cikin ranta ko za ta ji zafi da rad'ad'in da zuciyarta take zai ragu, sai yanzu ta fuskanci dalilin da yasa Hidayan ta mik'o mata wayar saboda ta gane itace ta kira Ishaq d'in ba shi ya kirata ba, tayi hakanne don ta b'ata tsakaninta da Rj yayi mata kallon me karya alk'awari tun da ta gaya mata shine wanda ta yiwa alkawari, sam ba ta d'au Ishaq a matsayin saurayi ba sai dai tana bashi girma saboda yadda yake hak'uri da ita da bata kulawa duk da shi yaga zai iya hakan, to hakanne yasata karb'ar wayar tunda ba ta san me zaice mata ba may be kuma ya kira wayarta yaji ta a kashe don da ta gama game in kasheta tayi gaba d'aya, ba tayi tunanin wayar a speaker take ba da kuma Rj in bai san tsakaninta da Ishaq ba, amman za tayi k'ok'arin fahimtar da shi kada yayi mata kallon me karya alk'awari.

Da wannan abin da Hidaya take gara tazo ta tareta suyi me yuyuwa yafi, amman tunda haka ta zab'a to itama za ta zuba mata idanuwa taga inda wasan nata zai tsaya, ita dai baza taki amsar soyayyar Rj ba saboda dama ita take jira don ta tura shirmen mafarkinta gefe, sai dai tana tsoron inda makomarsu za ta tsaya saboda ga Momy ga Hidaya a gefe, don ta tabbata Momy ba za ta bar 'yarta ta zab'eta ba amman ko ma dai meye Allah ba ya bacci, idan har Rj mijinta ne zai kawo musu hanya mafi sauk'i.





Washe gari ko break bai tsaya yayi ba ya d'auki hanyar kaduna dama al raedy Daddy da Mommy sun san da tafiyar tasa, Hajiya, (Haka suke kiran mahaifiyar tasu da k'annensa mata guda biyu da ta haifa a kadunan, suma dukkaninsu sunyi aure ko wacce tana da yara bibbiyu) tayi matuk'ar farin cikin ganin d'an nata, hakama k'annen nasa Safiya da Hafsa ko wacce tazo don ganin d'an uwan nasu don sun san halinsa na son girma da manyance sai yace bazai je musu ba duk da zolayar da suke masa yanzu na sun girmeshi dole ya basu girman saboda sun rigashi dire 'ya'ya.

Bai baro kaduna ba sai cike da tarin k'aunar mahifiyarsa da 'yan uwansa sai dai zuciyarsa cike take da tashin hankalin abinda yaji daga bakin Hajiyarsu wanda ko da wai bai tab'a hasasho hakan ba, ta sanar mishi ne akan maganar Aurensa shi da Hidaya nan da shekara d'aya idan Hidayan ta kammala karatunta, duk da ita Hajiyan ta so yana dawowa yayi aure sai dai sunyi maganar da Daddy inda yake ce mata so yake Hidayan ta kammala karatunta shekara me zuwa ya had'asu aure don yaga alamun ma sun dai daita kansu, farin ciki sosai Hajiyan ta shiga don Daddy mutum ne ba abun yadarwa ba, had'a zuri'a da shi kuwa babban rabo ne, kasa rik'e farin cikin nata tayi shiyasa da Rj in yazo tayi masa zancen, ganin tarin farin cikin da mahaifiyar tasa take ciki ne yaga bazai iya katse mata shi ba kawai yabita akan hakane, amman fa zuciyarsa gaba d'aya a cunkushe take tunaninsa ya katse ya rasa wani irin tunani zaiyi.


Yana doso hancin motarsa harabar gidan idonsa ya sauka akan Nusrat da Ishaq suna tsaye da alamu sallama suke zai tafi don a jikin motarsa suke a tsayen, hankalinsa ne ya kasa kwanciya da yai ta kiran wayar ba'a peking, Hidaya da ta shigo taga tarin miss call insa sai tayi masa tex akan yazo gobe tana son ganinsa a zuwan Nusrat ce ta tura masa shi kuwa Ishaq ganin wannan tex in sai ya kwantar masa da hankali ya kuma tsundumashi cikin farin ciki don ya fara ganin alamun nasara daga Nusrat in, kuma dama yana son zuwa ya ganta don ya kwana biyu bai zo ba gashi zaiyi tafiyar da bai san kwanaki nawa za ta ibeshi ba.
Nusrat kuwa tana tsaka da had'a dinner ya kirata gashi ya k'araso, ta shiga d'inbin mamaki don ba suyi da shi zaizo d'in ba to amman sai taji ba za ta iya wulakanta shi ba tun da har ya riga yazo, Allah ya taimaketa ta kusa gamawa sai ta k'arasa a gaggauce ta bar Hibba da jerawa akan dinning, dama a shiryanta take cikin bak'ar doguwar riga da ta kuma fito da hasken fatarta, turare kawai ta kuma fesawa ta d'auki siririn jan mayafi ta yafa ta fita fuskarta na bada wani annurin kyahu.

Sun d'an tab'a hira ba laifi aka fara kiran sallar magariba ya tashi zai tafi shine ta yo mishi rakiya bakin motarsa.



Wani irin duhu Rj ya fara gani cikin idanuwansa yana jin wata sabuwar damuwar na kuma ninkaya cikin zuciyarsa, ko parking bai dai daita sosai ba ya fito yana rik'e kansa da ke mugun sara masa a hankali yake tafiya ya nufi sashensa, Nusrat kuwa hankalinta gaba d'aya yana kansa har Ishaq ya shiga motarsa ya ja ya tafi da sassarfa tabi bayansa tana kiran sunansa amman ko nuna alamun yaji bai yi ba da gudu ta had'a tasha gabansa tana d'an haki na gudun da tayi, d'ago da rinannun idanuwansa yayi ya aza a kan kyakkyawar fuskarta, kallon cikin ido sukewa juna, a hankula yaji zuciyarsa tana sanyi duk wata damuwa tana kwaranyewa saboda abinda yake karanta cikin idanuwanta, zare idonta tayi daga cikin nasa saboda yadda taji kuzarinta yana karkaryewa had'e da karsashinta, zoben da ya saka mata ta murza ta d'ago da hannun ta nuna masa had'e da fad'in.

"Ka saka nayi maka alk'awari ba tare da ina da tabbacin sona kake ba, haka nayi k'ok'arin cika maka shi tare da jure dukkan wani k'unci, saboda rashin cika alk'awari alamace ta munafiki, amman sai gashi da rashin fahimta za ka saka mini, Ishaq ba saurayina bane, ya dai nuna yana sona ban amince masa ba na gaya mishi da alkawarin wani a kaina, sai ya buk'aci yin abota da ni naso k'in amincewa amman ya kafa mini naci na barshi a zuwan idan ka dawo mayi rabuwar mutumci da shi saboda ba ka san halin mutum ba.
Akan ka zuciyata ta bud'e, kaine ka fara shiga cikinta ka samu babban masauki ina fatan kuma akanka za ta rufe idan ka bata damar hakan."
Tana kawowa nan ta juya za ta tafi.

"Nusrat"

Ya kira sunanta, d'an dakatawa tayi ba tare da ta juyo ba.

"Kiyi hak'uri don Allah."

"Laifi indai naka ne ba ya zama a zuciyar Nusrat, musamman wannan da rashin fahimta ne kawai, har an tayar da sallah bara na k'arasa ciki."
Wani kyakkyawan murmushi ya saki yana bin bayanta da kallo da ta wuce ba ta jirayi me zaice ba, ina sonki Nusrat yaji zuciyarsa ta ambaci hakan kafin ya shafa kansa ya nufi sashensa cike da karsashi da sabon kuzari, don duk sai yaji wata damuwa tasa ta yaye kawai zai tunkari Daddy da maganar yana son Nusrat tun kafin ya tunkareshi da maganar Hidaya don bazai iya kaucewa hakan ba saboda matsayi da kimar Daddyn a gurinsa, ita kuma Hajiya ya san ta yadda zai b'illo mata.....
[4/26, 8:45 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG29

Wata sanyayyar soyayya ce ta fara gudana tsakanin Nusrat da Rj wacce sam Mommy ba ta ankara da ita ba saboda ba kasafai take sakkowa k'asa ba, tana da komai na buk'ata a cikin d'akinta, abinci kuwa Nusrat ce ke kai mata ta kuma sakko da kwanukan, sai yamma take sakkowa ta koma sashen daddy saboda tararsa shine sai a had'u ayi dinner tare, yanzu kuwa da Daddy ba ya nan dinner ma ba ta sakkowa a d'akinta take wuni sir abinta tana karatun novel idan 'yayan suna bukatarta sai suje gareta, duk da babu wata shak'uwa tsakaninsu saboda ba ta ginosu akan haka ba.

Tafiya ce ta kama Daddy dalilin da yasa kenan Rj bai tare shi da maganar soyayyarsa da Nusrat ba ya bari ya dawo tukunna in yaso sai ya sameshi da maganar don ba ya fatan shi ya rigashi yi masa maganar Hidaya don bazai iya kaucewa hakan ba, sannan kuma a yadda yake jin soyayyar Nusrat bazai tab'a iya kwatanta rayuwa babu ita ba yana jin kawai sai dai ya had'asu su biyun ya aura idan hakan ta faru.

Ko da wasa bai tab'a bari Nusrat in tasan da maganar aure tsakaninsa da Hidaya ba don yasan muddun ta san hakan tabbas za ta ja jiki da shi, haka ma Hidayan sam bai nuna mata yasan abinda take nufi da shi ba duk kwa na k'okarinta gurin nuna mishi irin tarin soyayyar da take masa sai ya dinga kakkauce mata yana nuna mata shi sam bai gane me take nufi ba Nusrat itace zab'in zuciyarsa.

Tsakanin Hidaya da Nusrat kuwa babu abinda ya canja, don Hidaya tana k'okari gurin danne zafin Nusrat in da take ji saboda zumunci, amman dai ba ta fasa cusa Ishaq cikin rayuwar Nusrat in ba saboda ta bar mata Rj dinta don a yanzu tayi amannar muddun Nusrat na nan ba ta ishi Rj kallo ba indai a barin soyayya ne, don haka ta d'au alkawarin sai tayi silar da Nusrat za ta auri Ishaq ko da ba ta so ta hakanne itama za ta samu muradinta, shiyasa ta k'agu Daddy ya dawo domin ta fara shirinta.

Nusrat kuwa gaba d'aya ta gama karantar Hidayan tsaf son Rj take, wanda shima Rj in ta lura yasan da hakan kawai yana kakkauce mata ne, Allah ya gani tana son Rj so ba na wasa ba shima kuma yana sonta wannan dalilin ne yasa ta biye mishi suke soyayyarsu amman fa can k'asan ranta tsoro ne fal cikinsa musamman sanda Rj in ya rarraba musu tsaraba ita har da tanfatsetsiyar waya ya bata wacce ya siyo mata ita ta musamman to da taje nunawa Momy sai ce mata tayi.

‘’ Ki dai tsaya matsayinki banda shishshigin shiga hurumin da ba naki ba domin ba dake ya kamata ba, idan kuma kinki ji duk abinda ya biyo baya babu ruwana."

To wannan ne yake sawa wani zubin duk sai ta sare tana hango tafiyarsu da Rj in babu inda zata je wanda hakan itakam bazai shafa mata lafiya ba, duk da Rj in yakan kwantar mata da hankalin Daddy yana dawowa zai sameshi da maganar auransu don ba lokaci yake so a jaa, to idan tayi laakari da sauk'in kan Daddyn wanda tayi amannar bazai hanashi auranta ba sai taji hankalinta yana d'an kwanciya.


Wata d'aya Daddy yayi ya dawo wanda yazo ya tadda familyn nasa cikin murna da d'aukin dawowarsa sai ya alakanta hakan akan bai tab'a yin kwanaki irin haka ba idan tafiya ta sameshi.
A daren da Daddy ya dawo Hidaya ta d'au wayar Nusrat tayiwa Ishaq tex akan ta amince da shi gobe ya turo magabatansa gidansu sak'o inji Daddy, sai da ta tabbatar ya shiga kana ta goge ta saka number tasa a black list kana ta ajiye mata wayar cike da zallar farin ciki tana ganin tarkonta kamar ya gama danuwa.

Ishaq da yaga message in Nusrat ya shiga matuk'ar farin ciki duk da kasan ransa yana mamakin anya kwa Nusrat ce tayi mishi wannan tex in don sun riga sunyi sallama ya daina kiranta ma don ta sanar mishi wanda za ta aura ya dawo kuma ba ya son muamalarsu don haka sai yayi mata fatan alkhairi yazo ya fara jinyar cire soyayyarta a ransa don yanzu yayi amannar ya rasata kenan har abada sai kuma gashi tex inta ya riskeshi a yau don gaka baiyi k'asa a guiwar danna mata kira ba amman sam tak'i shiga don haka sai ya juya akalar kirannasa ga number Hidaya.

Gaisawa sukayi bayan nan ya buk'aci ta had'ashi da Nusrat tace masa tayi bacci da yake kanta na mata ciwo, nuna rashin jin dadin ciwon kan nata yayi kafin ya tambayeta game da tex in da Nusrat in ta turo masa, nan ta k'ara masa k'arfin guiwa had'e da tabbatar masa gaskiya Nusrat in ta fad'a don gobe ma an shirya tarb'arsu.
Cikin zallar farin ciki Ishaq yajishi yana yawo don haka a wannan dare yaje ya samu mahaifinshi ya gaya mishi, sai dai mahaifin nashi yace zasuje amman tambaya kawai zasu yi sai anyi bincike kafin su kai kud'i.


Hidaya suna gama waya da Ishaq tayi tsalle ta dire don ita kad'aice a dakin Nusrat ba ta shigo ba suna can tare da Rj, Hijabi ta saka ta nufi sashen Daddy, shi kadai ta tarar a kishingide yana cin tufa yana kallon tsofaffin fina finan indiya a cumpuiter insa.

"Daddy Nusrat ce ta aiko ni."

"To ina jinki."
Yace mata yana gutsirar tufarsa.

"Dama manema auranta ne suka ce zasu zo gobe, shine tace kunyarka take ji ni nazo na gaya maka."
"Wannan yaron da yake zuwa gurinta?"
"Eh shine Daddy"

"To masha Allah, Allah ya nuna mana goben ya kawosu lafiya, amman me yasa momynku ba ta sameni da maganar ba?

"Amin Daddy, ai itama ba ta sani ba yanzu in na fita daga nan zanje na shaida mata, kunyar Nusrat ce tayi yawa.
"Ni na shaida hakan, Allah yayi muku albarka gaba d'aya, in kinje ki turon Momyn taku da alama yau ta manta da ni."

" Amin, tom zan turota."
Daga haka ta fice daga sashen cike da zallar farin ciki, a kwance ta tarar da Mommyn tasu tana karatun novel, wani littafi take karantawa K'addar rayuwarmu, ya d'auki hankalinta sosai ko d'auke idonta daga kan wayar ba ta son yi shiyasa ba tajewa Daddy ba don ta san bazai barta tab'a wayar ba musamman da yau ya dawo daga tafiya kuma tana son jin k'arshen littafin shiyasa ta bari in ta gama sai ta tafi gaba d'aya.

Idonta akan wayar ta amsa sallamar Hidayan, gefen gadon ta samu ta zauna tana sauke idonta kan mahaifiyar tasu da babu ruwanta da lura da damuwoyinsu myddun in ba sune suka zo suka gaya mata ba.
"Mommy magana nake so muyi."
Ta fad'i hakan da sanyi a muryarta, haka kawai sai taji tana son bawa 'yar tata hankalinta don haka sai ta ajiye wayar tamik'e zaune tana sauke idonta akan Hidayan kafin Hidayan tace.

"Momy kince akwai maganar aure tsakanina da Yaa Rj amman shi Nusrat yake so, yanzu haka ma soyayyarsu suke sha abunsu, ni kuma Mommy ina mugun sonshi soyayyar da tayi mini muguwar illar da ban jin zan iya warkewa don haka naji bazan iya barwa Nusrat Yaa Rj ba don na fita buk'atarshi shiyasa nayi amfani da Ishaq saurayinta don ya aureta na samu ta bar mini muradina don idan soyayyarsu taje kunnen Daddy zai aura mata shine ni kuma sai dai sonshi yayi ajalina."
[4/26, 8:46 PM] Rabi: BEBE'ARTH


KTG30


Shiru Mommy tayi zuciyarta na wani irin tafarfasa, tun da tazo ta nuna mata irin kayan da ya bata ta fara zargin wani abu tsakaninsu duba da shakuwarsu tun kafin tafiyarsa makaranta dalilin da yasa kenan tayi mata gargad'i gargad'in da ba taji ba kenan.

"Me yasa tunda kika fahimci suna soyayyar ba kizo kin gaya mini ba?"

Ta fad'i hakan tana sauke idonta akan Hidayan wacce gaba d'aya ta zama wata iri saboda rashin nutsuwa amman ta kasa ganin hakan wani irin b'acin rai taji yana taso mata zuciyarta tana zafi.

"Ay nayi tunanin kin sani, sai daga baya na lura,ba ma kisan abinda ke faruwa ba ."
Hidaya tace da ita haka.

"Jeki ki kira mini ita."
Ta fad'i hakan had'e da had'iye wani abu me d'aci a zuciyarta.

Kaya take sauyawa zuwa na bacci, tana yi tana sakin murmushin samun kwanciyar hankali, saboda rabuwarsu da Rj kenan yace mata gurin Daddy zaije ya sameshi da maganar auransu.

Murd'a kofar da Hidaya tayi ne yasata juyawa har lokacin da murmushi akan fuskarta.
"Kizo inji Mommy"
Hidaya tace da ita had'e da juyawa ta bar dakin.
Saukar maganar Hidayan tare suka zo mata da fad'uwar gaba, jiki a sanyaye ta d'auki hijabinta har k'asa ta sanya ta fice.

Tun da ta d'ora idonta akan fuskar Momyn taji gabanta ya fara dukan tara tara bama uku ba.
Guri ta samu a kasa ta zauna hade da fadin. "Gani Momy"
"Nusrat"
"Na'am" Ta fada da rawar murya.

"Watakan gargadin da nayi miki bai shiga jikinki ya zauna ba har sai da kika aikata abinda zuciya da ruhinki yake so ko, ban isa nayi miki katanga da shi ba saboda kin rainani kika tsallake kika janyo ra'ayinsa ke ga mara mutummci me kike tak'ama da shi ne?‘’

"Ba ke kika haifeshi ba."
Hidaya ta fad'a tana turo baki gaba, Nusrat kuwa k'asa tayi da kanta ba tare da tace komai ba tana saurarar yadda kirjinta yake bugu har ma da zuciyarta a yanzun.

"D'ago ki kalleni"
Momy tace da ita, a hankali ta cire kanta ta sauke idanuwanta kan Mommy wanda suka d'an sauya kala hade da girkicewa.
"Kina tak'ama don bani na haifi Rj ba shiyasa kika tsallake maganata?"

girgiza kai tayi hade da fadin "Kiyi hakuri."
"Hmmm babu wani hak'uri da zanyi sai dai ki karb'i hukuncinki a yanzu, duk da bani na haifi Rj ba amman na haramta aure tsakaninku, kinga matarshi nan wacce akayi mishi tanadinta jira ake kawai ta gama karatunta amman kikazo kina cusa kanki gareshi har sai da kika sauya mishi tunani gaba daya saboda na dauko rayuwarki daga talauci na tsundumoki cikin daula."

Idanuwanta sun kuma kad'awa sunyi jazur sun tara ruwa ruwan da ta kasa rik'eshi har sai da suka zubo ta gefen idanuwanta cikin murya cike da son yin kuka tace.
"Wallahi Momy ban son da maganar aure tsakanin Hidaya da Rj ba da bazan bashi damar da ya nema a gareni ba, ba nice na cusa kaina gareshi ba shine ya cuso kansa gaba d'aya cikin rayuwata kuma ba tun yau ba tun ban fahimci mece soyayya ba, da na san da maganarsa da Hidaya da bazan bud'e zuciyata gareshi ba, amman yanzu tabbas lokacin rufeta yayi rufewa ta har abada, amman ina buk'atar komawa gida hakan zaifi shafawa rayuwata lafiya ."

"Ni kuma bazai shafa mini lafiya ba, kiyi aure kawai shine kwanciyar hankalina."
Cewar Hidaya yayin da Momy tace.

"K'warai kuwa Nusrat auranki shi zai tabbatar mana da samuwar Rj a hannun Hidaya, don haka ina me sanar da ke gobe manema auranki zasu zo daga gidan su Ishaq samun nutsuwarki ki mik'a wuya zuwa ga wannan aure idan kuwa kika k'i to tabbas zan wulakanta rayuwarki fiye da yadda kike zato don zan iya sauka akan ko wani mataki don ganin yarinyata ta samu farin ciki da nutsuwa."

Wayarta ce tayi k'ara wacce kirane daga Daddy akan suzo ita da Nusrat da Hidaya, gasunan kawai tace tana kashe wayar ta ajiye gami da sauke idonta kan Nusrat wacce kawai ga tanan a zaune ne ta kasa sarrafa k'wak'walwarta hade da zuciyarta.
"Ki musa maganar auranki na tabbatar miki da abinda nake nufi, muje falon Daddy yana son ganinmu."

Tana fadin haka suka mik'e tare da Hidaya suka nufi k'ofa wanda ya bawa Hibba damar dai daita nutsuwarta a bakin k'ofar kamar a lokacin za ta shigo, a tare suka murd'a kofar suna budewa babu wanda yace da ita komai kallo daya suka yiyyi mata suka huce.

A hankali take mik'ewa daga zaunen da take tana jin yadda k'afafuwanta suka yi sanyi, sanyin da ba tayi tunanin zasu dauki nauyin gangar jikinta ba, wani irin kunci da zafi zuciyarta take mata, Tabbas iyaye wata babbar katanga ce ga 'yayansu ta tabbata da ace daya daga cikin mahaifanta na raye da bda irin wannan zancen ake a yanzu ba da babu abinda zai kawota zama cikin gidannan bare har hakan ta faru,da ace tasan irin wannan k'addarar na zaman jiranta to tabbas da ba ta yadda zama ya kawota cikin gidannan ba, sai dai kuma ba ka tara sani ga Ubangiji.
Cikin matukar sanyin jiki ta nufi k'ofa za ta fita daga d'akin Hibba na biye da ita da kallon tausayi har za ta fice Hibban tayi saurin fadin.
"Yayarmu, kada ki aikata abinda zuciya da ruhinki ba zasu taba samun nutsuwa da shi ba, ki cire tsoro a ranki babu wani abu da zai faru da rayuwarki face abinda alkalamin kaddararki ya rubuta, an dauke alkaluma kuma takaddun sun bushe."

Juyowa tayi tana kallon Hibban cike da kwarin guiwar da ta samu, murmushi ta sakar mata hade da fadin.
"Thanks"
Tana jin Hibban cikin tamkar yadda take jin Yusranta, murmushi itama Hibban ta sakar mata tana jinta tamkar ciki daya suka fito don har ga Allah ta fi jin shakuwa da ita fiye da Hidayan da suka fito ciki daya.



RJ ne ya sameshi da maganar yana son Nusrat kuma sunma dai daita junansu, duk da yaji wani iri cikin ransa don har ga Allah yaso hada auransa da Hidaya kuma a yadda yake ganinsu yayi tunanin sun dade da dai daita kansu har yake ta tsimayin Rj in yazo ya sameshi da kanshi, a yanzunma da yazo yayi tunanin akan Hidaya ne ashe akan Nusrat ne sai yanzu yakewa maganarsa ta rannan fashin baki da suna dinner yake cewa tabbas zaiyi kewar girkin Nusrat idan tayi aure, yana jin anya kullum ba gidanta zai dinga zuwa dinner ba, sai Rj in yayi dariya yace watakila ma ta wutashsheka zuwa idan ya kasance a kusa kuke kullum da kai za ta saka sanwa.
To maganarsa tana nufin idan shi ya auri Nusrat in kenan, bazai ce bai ji dadin soyayyar Rj da Nusrat inba don itama yana jinta tamkar Hidaya da ya haifa, kuma ya san sun dace da aamun kamilar surika to sai dai kuma kansa ya daure da maganar da suka gama yi da Hidaya yanzu, ga kuma Rj in yace da sanin Nusrat in yazo gurinsa don yanzun nan ma suka rabu wannan dalilin ne yasa ya kira Mommy yace tazo da su gaba d'aya.

Daga Mommy har Hidaya sun firgita da jin Rj inne ya samu Daddy da maganar auren Nusrat, amman kuma sai Hidayan ta kafe akan Nusrat ince ta aikota gurin Daddy akan maganar Ishaq don ba ta son Rj ya riga zuwa saboda ba shi zuciyarta take ainihin so ba, a tare RJ da Nusrat suka daga kai suna kallonta wanda taki yadda ta kalli daya daga cikinsu.

"Nusrat"
Daddy ya kira sunanta ta amsa cikin rawar murya. "Na am"

"Mene ne ainihin gaskiya."

Kuka kawai ta fashe da shi, wanda yazo mata da karfinsa na gaske kuma ba ya bukatar a tsai da shi a yanzu.

"Ga ainihin gaskiya nan, tunda ba'a karya da maganar aure, shi Rj in tun da ba ta sonshi ba sai ya hakura ba, dama aishi Hidaya ce matarsa banda abinka."

Cewar momy kenan, yayin da zuciyar Rj take ta mugun tafarfasa jijiyoyin kansa sun fito rada rada, Daddy kuwa yayi shiru cikin nazari yayin da Nusrat kukanta yake kara karfi.

"Daddy zan gaya maka ainihin gaskiya"



Please Login or Register in order to submit comment