Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai misalin k'arfe takwas Mama ta dawo, kallon Nusrat da ke kwance ta yi tace.
"Ina Mamana, Yusra taci abinci da kika barta tai bacci?”
"Cikin gida tace mini za ta shiga tun d'azu, Yusra kuma sai da taci abinci tukunna tai bacci. “
"Lafiyanki kuwa naga kina yatsina fuska? “
Ta tambayeta duk da a ranta mamakin wai Shukhura ce tace ta tafi cikin gida, bayan ba k'aunar zuwa gidan take ba, aike ma da dole take shiga.
"To ki tashi ga fura na taho miki da ita kisha sai ki sha magani.“
Da hanzari ta mik'e don dama yunwa take ji kuma har ga Allah ba ta k'aunar cin tuwon donma ta d'an ci d'atan da Baba ya kawo mata duk da wasu sunce shima ya na faifaye ciki, ita kuwa Mama sanin halin d'iyar ta ta yasa ta yo mata guzurin furar.

Sauke idanuwanta ta yi akan kular tuwon da Shukhura ta ajiye, a fili tace.
"Allah ya shirya mini ke mamana. Maza Nusrat ki gama kije ki kira mini ita. “
Ta na rufe bakinta ta jiyo sallamarta suka amsa mata.
"Laa Mamanmu kin dawo ashe? sannunki da dawowa. “
Fuska a had'e tace.
"Yauwa, me kika je yi cikin gida? “
"Nifa ba cikin gida nace mata zanje ba, gidan su Farha nace mata za ni kallo.“
Takai k'arshen maganar ta na kallon fuskar Nusrat.
"Ban hana ki zuwa kallo ba?to da Babanku kawai zan had'aki na huta, Ke kuma ai ga shinan kin rufa mata asiri ta tonawa kanta. “
Takai k'arshen maganar ta na kallon Nusrat, yayin da ita kuma ta saki murmushi.
"Kiyi hak'uri Mamanmu bazan sake ba. “
"Sau nawa kina fad'in haka? “
"Allah da gaske nake Mamanmu daga wannan bazan sake ba. “
"To wancan uban tuwon da kika ajiye da fatan abincinki ne na sati guda ko?“
"Haba² Mama, sai kace wacce uwarta ta tsine mata duniya ta juya mata baya zan jera sati guda ina cin tuwo, tuwonma ba sabo za'a dinga yi mini ba. “
Mama ta so yin dariya amma ta kanne tace.
"Koma me zaki ce kice, amma wancen tuwon sai kinyi sati kina cinsa a gidan nan tun da ke kunnenki na k'ashi ne ba ya jin magana, bacin sau nawa zance ki daina cika mini kula kina kawo mini d'aki? “
Sai da ta fara turo bakin nan gaba kana tace.
"To kina dai kallo duk ran girkinta sai ta cika kula fam ta kai d'aki, bacin daga ita sai 'yarta d'aya kamar rai, mu kuwa ta milliro mana, ta cikawa Baba da sirikarta kwano, nima kuwa yau na rama na millira musu na millirawa Iya ma, Baba kuwa na cika masa kwano har ya na zuba. “
Salati Mama ta yi ta saki baki ta na kallon Shukhura.
"To don ita ta na cika kula ta kai d'aki ita ta shafa, sune mayunwata ba mu ba, ga shinan yanzu kin sakani a bakin duniya, tijarar Iya ma kad'ai ta isheni, don cewa za tai ina sani na baki girkin shiyasa har ga Allah ban son na bar miki girki na fita. “
"A to don wallahi muddun ni nai girki bazan fasa ciko mana kula na kawo d'aki ba, ko ba za muci ba sai dai mui asararsa. “
"Me kika ce?“
Mama ta tambayeta kasancewar k'asa² tai maganar.
"A'a cewa na yi kiyi hak'uri bazan kuma ba. “
"To zo ki fice mini da kular, kije ki k'ara musu tuwon.“
Ta na jin haka ta saki k'ara.
"Waishhhhhh Mama kashi² ina zuwa ta fice da gudu zuwa ban d'aki, murmushi Mama ta yi a ranta ta na nemawa Shukhura shiriya ta d'auki kular tuwon ta fita, murmushi ma Nusrat keyi tun fara dramar Maman da Shukhura, don dama sun riga da sun saba......



300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB
GTBANK
In kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biyama ki turo cikinta.
09037093702.
In katin wayane 400 Za ku biya.


Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.





Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.




#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I. Pls share


*BEBE'ARTH*



Wattpad@Rashuna


*KATANGA*



____________
*THREE*

Ashe ba kallo Shukhura taje ba, can bakin titi taje gurin me saloon ta siyo farata koraye shar da su, ta biya gurin me zob'o ta siyo, ta sayi cewing gum ta jefa a baki sannan ta yo gida, a wani d'an lokon babban tsakar gida ta ajiye faratan da zob'on kana ta shigo.
Sai da ta bari d'aya ta gota ta tabbata a lokacin baccin kowa ya yi nisa ta salallab'a a hankula ta zare sakatar gurinsu ta fice, bayan ta d'auko farar hodarsu, ko tsoron duhun dare ba ta yi, bursuna farar hodar ta yi tun daga fuskarta har wuyanta, ta cire hijabinta sai ta bar wata hula me cibiri cibirin gashi a kanta, rigar jikinta dama ta wani tsohon uniform d'inta na islamiya ne da take bacci da ita.
Cikin dabara ta man manna faratan a yatsunta da chewing gum, ta d'aga jarkar zob'on nan ta shanye ta bar d'an guntu a ciki, nan da nan bakinta ya yi jajir, ta guntsi ragowar a bakinta, turmi ta taka ta zira hannunta ta saman k'ofar d'akin Iya a hankula ta zare sakatar kana ta tura ta shiga ta mayar ta rufe, kallon Iya da ke bacci akan gado ta yi, sakamakon haska 'yar k'aramar cocilan d'in da ke hannunta da ta yi a ranta tace.
'Za ki gane kurenki ne.'
Kan ruwan cikinta ta hau ta zauna, cikin bacci Iya ta ji masifar nauyi ya ziyarceta, a hankula ta bud'e idanuwanta duk a tunaninta madannin dare ne ya danneta, ido biyun da ta yi da Shukhura nan take wani mugun tsoro ya kamata ta bud'e baki za tayi ihu Shukhura ta yi saurin toshe mata baki da wani tsumma da ta yayibo a gefenta, cikin wata iriyar murya me ban tsoro tace.
"Kada ki mana ihu a nan, in ba haka ba zamui daga daga da namanki. “
Nan da nan jikin Iya ya fara rawa kar kar ta fara biya duk wata addu'a da tazo bakinta, son tashi take amma gaba d'aya ta k'asa tashi, hannu Shukhura ta Saka ta karto gefen fuskar Iya had'e da juyar da idanuwanta, rintse ido Iya ta yi kafin ta ji saukar muryar Shukhura a kunnuwanta.
"Al'quran kika kuma tsangwamar Nusrat a cikin gidan nan sai mun cire miki k'afa d'aya da hannu d'aya, mu kuma maidar miki bakinki k'eyarki, sannan mu d'aukeki zuwa cikin ruwa, kima gode Allah kin fara manyanta da wallahi yau sai mun sakaki murmushi da hak'ori d'aya.“
Iya firgita Iya ta firgita, wani mugun tsoro ne ya kuma shiga jikinta ko k'wak'k'waran motsi ta kasa, ta na san magana amman ba dama saboda ta toshe mata baki da t'summa kuma ta rik'e da d'aya hannunta, um umm kawai take ta na girgiza kai hawaye na zuba a idonta, tausayi ta bawa Shukhura don tasan ta sha nauyi, don Iya irin siraran tsofaffin nan ne, ita kuwa Shukhura ta na da jiki, d'agata ta yi ta sauka daga kan gadon ta cire hannunta daga bakinta had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki mana ihu don wallahi zan maidar miki da idonki goshi ki zama mai ido d'aya. “
Ta na maganar ne ta na ja da baya, yayin da Iya tace.
"Allah ya baku hak'uri wallahi na daina takura mata, ba iya ita kad'ai ba ma wallahi dukansu na daina shiga harkarsu.“
Wani ihu Shukhura ta yi ta na zaro harshe ya yin da Iya ta yi wani hantsile ta koma k'arshen gado goshinta ya bugi da bango, duk azabar da ta ratsa ta k'wak'wal warta amma haka ta d'inke bakinta saboda tsoron kar ta yi ihu a maidar mata da idonta goshi, ja da baya Shukhura ta ci gaba da yi had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki juyo sai mun b'acewa ganinki in ba haka ba kuma zamui sama da ke zuwa fadar sarkin aljanu. “
Ta na kawowa nan, ta bud'e k'ofa ta fice, ta taka turmi ta maidar mata da sakatar ta, kana ta d'auke turmin ta mayar da shi mazauninsa, sannan ta d'auki hijabinta ta shige ciki, ta na k'ok'arin mayar da sakata ta ji muryar Baba yace.
"Waye nan?“
K'irjinta ta ji ya yi wani irin bugu nan da nan wani mugun tsoro ya kama ta ta fara rawa da bakinta.
"Um nice, fitsari na fito naga kamar ba'a saka sakata ba, shine na duba. “
Ta na kawowa nan ta yi saurin fad'awa band'aki don gudun kada ma ya fito ya ganta.
Fuskarta ta wanke da sabulu, ta cire faratan ta jefa a shadda, kana ta fito ta koma d'aki, sai bayan da ta kwanta a shimfid'arta wata muguwar dariya tazo mata, fashewa ta yi da dariya sosai ta na hango yadda idanuwan Iya suka firfito gaba d'aya kamar na mayyar da aka kama, wata dariyar ta kuma fashewa da ita, Nusrat da ke gefenta ta farka ta na kallonta a tsorace.
'Anya kuwa babu almutsutsai akan Shukhura kuwa. '
Taji zuciyarta ta jefo mata wannan tambayar kafin ta ji muryar Baba ya na k'walo mata kira.
" 'Yar baiwa“
"Na'am Baba. “
Ta amsa, ta tashi ta fita jiki a sanyaye.
"Lafiya kuwa nake jiyo dariya a d'akin ku?“
"Wallahi Baba Shukhura ce, kuma ban san me takewa dariyar ba, anya Baba ba za'a nema mata magani ba, ni wasu abubuwan in ta na yi gani nake kamar ba ita kad'ai ba. “
Murmushi Baba ya yi yace.
"Shukhura. “
"Na'am.“
Ta amsa cikin muryar shagwab'a ta fito ta na sosa kai.
"Me ya sakaki dariya cikin tsohon daren nan? “
Sai da ta fara turo baki gaba sannan tace.
"Kawai tuno yadda na tumur mushi hadiza d'azu a makarantar allo na yi, tsokanar Yayarmu ta yi ni kuwa na had'a mata jini da majina ta mik'e da k'yar jiki duk yai tsami kamanninta duk sun sauya bakin nan kamar zunb'utun zakara. “
Ta kuma fashewa da wata dariyar.
"To jeki ki kwanta, kinga dare ne kada ki kuma dariyar, kinji Mamanmu. “
D'aga masa kai ta yi, ta koma d'aki, ya bita da idanuwa a zuciyarsa ya na nema mata shiriya, duk da a zuciyarsa shima ya fara tunanin ba ita kad'ai bace, don al'amarin nata akwai ban tsoro, shiyasa ya daina dukanta ko me Iya tace tayi mata, don ya san itama Iyan da laifinta, kuma duk irin dukan da zaiwa Shukhuran ba shi zai hana ta samo ta inda za ta rama akan Iya ba.
Duban Nusrat ya yi yace.
"Je ki kwanta 'Yar baiwa, zamui maganar da Mamanku da safe.“
"Toh“
Tace had'e da juyawa ta koma d'akin, ta na kwanciya Shukhura ta rungumota ta baya ta na sakin dariya.
"Ina sonki Yayarmu, matuk'ar ina numfashi bazan tab'a bari a tab'a mini ke ba na k'yale, da a tab'a ki gara ni a tab'a ni. “
Wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Nusrat wa'yenda ba ta san dalilin zubowarsu ba, hannu ta saka ta baya ta rik'e hannun Shukhura gam had'e da fad'in.
"Nima ina sonki k'anwata, amma don Allah ki daina fad'a kinji k'anwata. “
"Zan daina, idan har aka daina tab'aki, fatana na saka tsoron ki a zuciyar duk me tab'aki, yadda ko ganinki ya yi sai yai shayin yi miki magana."
Ta na kawowa nan ta kuma rungumota a haka bacci ya d'auketa saboda ba ta da wuyar yin bacci, Yusra da ta farka ta jita ba jikin Nusrat ba ta yi juyi ta shige jikinta, hannu Nusrat ta saka ta na shafa kanta, ta na shafo kan Shukhura da d'aya hannun, har lokacin hawaye na zuba a idanuwanta, ta tabbata hawayen k'aunar da 'yan uwanta suke mata ne, kyakkyawar Katanga mahaifiyarsu ta gina musu a zuciyoyinsu na k'aunar junansu, babu ruwansu da k'yashi ko bak'in cikin anyiwa wani abu a cikinsu ba'aiwa d'aya ba, ta na fatan soyayya da k'aunar da sukewa junansu suci gaba da ita har k'arshen numfashinsu, kada Allah ya bawa wani nasarar rusa katangar alak'ar da take ginanna a zuk'atansu.
Dubanta ta kai ga mahaifiyarsu da ke baccinta cikin kwanciyar hankali, duk abubuwan da suka faru ba ta san anyi ba, kasancewarta me nauyin bacci, shiyasa ko wani abun Baba ke buk'ata a gurinsu sai dai ya k'wallowa Nusrat kira.
A b'angaren Iya kuwa k'wak'wame da bango wani wahalallen bacci ya yi gaba da ita, ba tare da ta shirya zuwansa ba.


Washe gari da safe Nimha da taje kaiwa Iya abincin kari, kasancewar girkin Ummanta ne, anan ta samu Iya da kumburarran goshi, gefen fuskarta a karce.
"Ayya Iya sannu me ya same ki?“
"Ke dai bari 'yar nan, duhun dare ne irin na damuna, na tashi fitsari na nemi cocilan d'ita na rasa nai shahada na fito haka shine na sha k'asa.“
"Ayya sannu Allah ya kiyaye, ga karin kumallon ki nan.“
Cewar Nimha, daga haka kuma ta juya ta fita kafin Iya tace.
"Amin. “
Nimha na zuwa ta gayawa Ummanta abinda ya samu Iya, tab'e baki Umman ta yi had'e da fad'in.
"Wa ya sani ma ko karkashin aljanar yarinyar cen ta kuma kad'awa ta zuba mata, ni ban tab'a ganin tak'adiriyar yarinya irin Shukhura ba, Iya na cewa Nusrat 'yar aljanu ai Shukhura ce 'yar aljanu ba Nusrat ba.“
Maganar da Umma ta yi kaf a kunnen Shukhura suka sauka, wani murmushi ta yi a ranta tace.
'Allah ya had'amu za kwa kiyi kallon tak'adiranci.'
Kowa na gidan sai da ya shiga ya duba Iya, Nusrat da Shukhura a tare suka shiga duba ta, abinda ya bawa Nusrat mamaki ganin Iya ta kirata da Nusrat abinda tsawon rayuwarta ba ta tab'a kiranta da shi ba, sai dai ta kirata da Ai, ba ma za tace Ayshan ba, duk don Malam ya ji haushi.
Sannan kuma har suka fito ba ta sanyata aiki ba, kasancewar duk sanda ta shiga gurin ba za ta fito ba sai ta moreta ko ya ya ne, kuma ta na kallon Shukhura ta na ta sunkui da kai ta na matse dariya, shine da suka koma d'aki ta dubi Shukhuran tace.
"Wai dariyar me kike ta matsewa ne a d'akin Iya? “
"Yo ba dole na yi dariya ba, kinga kuwa goshinta kamar mulmuleliyar daddawa sai shek'i yake. “
Ta fashe da dariyar da ke cinta tun d'azu.
"Allah ban yadda da ke ba Shukhura, duk yadda akai ta dalilinki Iya ta ji ciwon nan. “
" To ni me ta mun da zan saka ta ji ciwo? “
Ta fad'a ta na d'an turo baki gaba.
"Kefe kika ce sai kin saka tsorona a zuciyar duk me takura mini, kuma yau kallon da Iya ta yi mini ya bam bamta da wanda ta ke mini a kullum.“
Rik'o hannuwanta Shukhura ta yi had'e da fad'in.
"Tabbas 'Yar baiwa ce ke Yayarmu.“
Kana ta shiga labarta mata yadda sukai da Iya ta na dariya, murmushi Nusrat ta yi tace.
"Tabbas Iya tai namijin k'ok'ari da ba ta sume miki ba, don in nice wallahi sumewa zan yi, a gaskiya kin d'au hak'k'in 'yar tsohuwa, don ta tsorata sosai tun da gashi ko labarin ainihin abinda ya faru ba ta bayar ba.“
"Wallahi ba wani hak'k'in ta da na d'auka, in hakane ita sau nawa ta na d'aukar hak'k'unanmu. “
Girgiza kai Mama ta yi, a kwance take duk a tunaninsu bacci take, duk abinda Shukhuran ta fad'a ta jishi, kuma ta na nemawa 'yar tata shiriya, don Baba yace da kansa zai dingai mata rubutu ta na sha, don abin nata ya fara yawa duk abinda akai mata tace sai ta rama ko ta halin k'ak'a.
"Kya ci gidanku, bari Babanku ya dawo sai na gaya masa, kuma ki tashi kije yau ke za ki mata shara ki wanke mata band'aki. “
Zunb'uro baki gaba tai ta mik'e, don in ba ta ta shi ba ta san Mama na iya jefo mata duk abinda ke kusa da ita, bayan fitarta Mama ta yi tunanin may be taje ta kumai mata wata muguntar don haka ta shiga k'wala mata kira kafin ta tashi ta bi bayanta.......




300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya


Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.



Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.



#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: *BEBE'ARTH*


Wattpad@Rashuna


*KATANGA*



____________
*FOUR*

Washe gari da safe misalin goma da rabi, zaune suke suna cin jolof in taliya a babban tray, kasancewar Baba ba ya nan ba a gida ya kwana ba kuma girkin Umma ne sai tak'i toya k'osai ta dama zallar kunu kad'ai ta bawa Nimha 200 ta siyo musu iya su da Iya kawai, wannan dalilin ne yasa Mama ta yi musu jolof in taliya saboda kunu kad'ai bazai rik'e cikinsu ba kuma Nusrat ba ta shan kunu sai koko.
Muryar Hidaya suka ji ta na k'wallowa Nusrat kira tab'e baki Shukhura ta yi bayan ta zuba taliyar a bakinta tace.
"Ga su shafi da mai nan an faso. “
Wata muguwar harara Mama ta jefeta da shi, kawai sai tai murmushi ta sunkui da kai, daga bakin k'ofa Hidaya ta tsaya, ta tsuguna har k'asa ta gaisar da Mama kana ta dubi Nusrat da ke kallonta ta na murmushi, ta yafitota da hannu had'e da fad'in.
"Kizo Yaa RJ ne ke kiranki, tsam Nusrat ta mik'e dama jikinta da hijabi saboda ba ta rabo da shi a jikinta ta bi bayan Hidaya suka fice Mama ta bita da idanuwa, Shukhura ce tace.
"Nifa Mama sai nake ganin Aunty Maryam kamar ba ta son Yaa RJ ya na kula Yayarmu.“
"Rufe mini baki ko na dakar miki shi da hannuna, na fa gaya miki ba na son irin magan ganun nan ko? Idan ma ba ta son ya kulata naga ta dalilinta duk kuka sanshi.“
"Yi hak'uri Mama, amma kuma in saboda kar wata alak'a ta shiga tsakaninsu ne to ta sha kurumunta in Allah ya yarda mijin Yayarmu ba daga tsatson mijinta zai fito ba ehe. “
Girgiza kai kawai Mama ta yi don zuciya ta kusa ciyota ta k'wala mata mificin da ke kusa da ita, zama Shukhura ta gyara had'e da gyara murya tace.
"Mamarmu nidai na gaji wallahi, ko yaushe sai ki dinga hanamu fad'a ana kuma k'wararmu, nidai wallahi idan Baba ya dawo zan kwashe duk abinda matarsa ke mana a gidan nan in gaya masa, haka kawai yanzu da ba dan muna da wannan taliyar ba sai dai fa mu zauna da yunwa har rana da ranar ma ba wani ishashh......“
Dakatawa ta yi da maganar sakamakon mificin da Mama ta rafka mata don taga hararar da take wurga mata ba za ta saka ta rufe mata baki ba sai ta had'a da duka, mik'ewa Shukhura ta yi ta na zunb'uro baki, ta figi hijabinta da ke kan k'ofa, ta na matsar k'wallar k'arya ta fice ta na.
"Wallahi na kusa yin maganin wata a cikin gidan nan.“
Ta fad'a da k'arfi yadda Umma da ke d'aki za ta jiyo ta.

Aunty Maryam na shiga d'aki ta tarar da Iya da kumburarran goshi.
"A'a Iya me ya sameki haka?“
"Zamewa na yi na fad'i na buge da bango. “
"To wannan karcewar ta gefen fuskarki fa?“
"Ke nifa ba na son tambaya, na gaya miki zamewa na yi na fad'i, me kuma kike son ji, kin wani titsiyeni kamar wata uwata sai kinji abinda ya sameni sai kace wani abu za ki iya a kai, mtssss. “
Taja tsaki taci gaba da sababi yayin da Aunty Maryam tace.
"Allah ya huci zuciyarki.“
Ta fice daga d'akin, in ba haka ba ba za ta daina sababin ba, ta shiga d'akin Umma don su gaisa.


A cikin mota Nusrat ta samu Yaa RJ, tun fitowarta yake sakar mata murmushi ta cikin gilashin motar har ta k'araso gaban motar, a bud'e murfin motar yake don haka ta shiga ciki ta zauna suka had'a ido da Hidaya da ta juya ta koma cikin gidan.
Shiru ne ya biyo baya sai kanta da ta sunkuyar k'asa ta na watsa da yatsan hannunta, yayin da shi kuma ya kafeta da idanuwansa, ya na jin wani sabon yanayi a kanta, ya san Nusrat yarinya ce ta yi k'ank'anta ya furta mata kalmar soyayya, amma ya na jin tsoron ya dawo ya tarar wani ya riga shi nasarar karb'ar soyayyarta, sanyin halinta, yanayin tafiyarta, yanayin maganarta komai ya yi dai-dai da yadda yake son matarsa ta kasance.
"Ina wuni Yaaya?“
Nusrat ta katse shirun da yake tsakaninsu ta kuma katse shi daga tunanin da ya tafi, rintse idanunwansa ya yi ya busar da wata iska mai sanyi saboda yadda muryarta ta shiga jikinsa ta zauna, wani siririn zoben azurfa ya ciro daga d'an k'aramin yatsan hannunsa.
"Muga hannunki. “
Zara zaran yatsunta ta mik'a masa ya zira mata a yatsanta na kusa da babban yatsa.
"Daga nan kaduna zan wuce ta nan jirginmu zai tashi zuwa Uk nan da shekara uku zan kammala karatuna na dawo, ki mini alk'awari ba za ki bawa ko wani saurayi damar k'ulla soyayya da ke ba. “
Ba ta gane inda maganarsa ta dosa ba, don haka ta tsira masa idanuwanta kamar me karantar amsoshin tambayoyin da ke dank'are a zuciyarta, yayin da shi kuma yake jin kallon da take masa har tsakiyar zuciyarsa.
'Meye dalilin da yasa ka bani zobe, me yasa zan maka alk'awarin k'in kula ko wani saurayi bayan ba ni da tabbacin sona kake,
idan ma sona kake anya auranmu zai yuhu kuwa, kana ganin Aunty Maryam za ta bar Katangar alak'ar da take ginanna a tsakaninsu taci gaba da ginuwa?'
Wa'yannan tambayoyin sune cunkushe a ranta amman ta k'asa furta ko da kalma d'aya, ji take bakinta yai mata matuk'ar nauyi.
Hannunta ya matsa had'e da fad'in.
"Pls Nusrat. “
Tsintar kanta kawai ta yi da d'aga masa kanta, ya saki kyakkyawan murmushi, ya d'auko wata leda ya d'ora a kan cinyarta.
"Na gode Nusrat, Allah ya baki ikon cika mini alk'awarina, bari ni zan wuce, ki gaida mini da su Mama. “
"Za su ji insha Allah, Allah ya kaika lafiya, ya kuma baka sa'a akan karatun naka.“
"Aminnnnn“
Yace yana me jin dad'in addu'arta yayin da ita kuma ta fice ba tare da ta d'au ledar da ya ajiye mata ba, murmushi ya yi don ya san za'a rina, a dai-dai lokacin Shukhura ta fito ta na zunb'uro baki, da hannu ya yafitota tazo gareshi, d'an risinawa ta yi ta gaisheshi yace.
"Ga leda nan d'auki ki kaiwa Mama kice ina gaisheta.“
"Tom, an gode. “
Ta d'auki ledar shi kuma ya ja motarsa yai gaba.



_RIDWAN JIBRIL shine cikakken sunansa yayin da ake masa inkiya da RJ, mahaifinsa da Yusuf mijin Aunty Maryam uwarsu d'aya ubansu d'aya, mahaifinsa ya rasu tun ya na yaro a gurin mahaifiyarsa yake da take aure a kaduna, tun bayan auran Yusuf da Aunty Marya ya d'auko RJ ya dawo gurinsa da zama suka rik'eshi tamkar d'ansu na cikinsu, bayan gama karatunsa na_ _secondary ya turasa Uk acan yake had'a karatunsa a fannin jarida._
_Hidaya da Nusrat tasu tazo d'aya sosai, suna k'aunar junansu hakanne yasa Nusrat take yawan zuwa hutu gidansu, yayin da shak'uwa me k'arfi ta shiga tsakaninta da Rj, har ta rikid'e ta koma soyayya a

Please Login or Register in order to submit comment