Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mama a motar Baffa Shamsu, shi ya kawo su ma, sam basui tsamnanin zuwansu ba tun da har yau kwanansu biyu da zuwa, su na shirin tafiya sai ga su Shukhura nan suka koma suka zauna ana ta gaishe gaishe, Iya sai shishshigewa H Inna take, Shukhura kuwa gefen Mama taje ta zauna suna dad'a gaisawa, daga d'aya gefen Maman Nusrat ce ta sunkui da kanta k'asa tana wasa da gefen hijabin Yusra da tayi matashi da cinyarta tana bacci cikin sanyin murya ta ambaci sunanta.
‘’Yayarmu‘’
'Dago kanta tayi wanda suka cika da ruwan hawaye tana kallon Shukhuran, to itama Shukhuran nan da nan nata idon ya kaho ruwa, Baffa Shamsu ne ya lek'o yayiwa su Umma magana akan su yake jira don haka sukayi musu sallama suka fita, Hajiya Suwaiba ma sallamar sukai musu ta ajiyewa Mama dubu ashirin a sayi magani da ita, Mama ta dinga godiya to Mustapha ma dubu hamsin ya bawa Nusrat a hannunta ta rik'e ko wani abu zai taso suka tafi suka bar Shukhuran sai dare zaizo ya d'auketa.

Hira sosai aka sha tsakanin Mama da tagwayen yaran nata wanda yawanci kalaman Maman kamar nasiha take musu akan su rik'i junansu suci gaba da gina katangar da ta gino musu tun a yarinta, ta had'e hannuwansu duka su ukun ta kalli Nusrat tace.
‘’ Yayarsu kece babba kimin alk'awarin kula da rayuwar k'annenki baza ki bari sui kuka ba, zaki zame musu katangar da zasu jingina da ita.‘’
‘’Na miki alkawari Mama, amman me yasa kike irin wa'yannan maganganun?‘’
Me makon ta bata amsa kawai sai tayi murmushi ta kalli su Shukhura.
‘’Ku mini alk'awarin mayar da yayarku tamkar mahaifiyarku, ku gaya mata damuwarku ni na tabbata za ta share muku hawaye don baku da tamkarta.‘’
‘’Mun miki Mama‘’
Suka had'a baki ita da Yusra gurin fad'a
‘’Masha Allah, ku rik'e zumunci, ku rik'e mahaifinku, da 'yar uwarku Nimha, Yayarsu ki had'a kawunanku kuyi zumunci sosai, kar ku rik'e abinda wani yayi muku kuk'i zumunci da shi, kuyi zumunci da shi domin Allah ba don halinshi ba.
‘’Mama kina tayar mana da hankali, kalamanki kamar wasiyya kike yi mana.‘’
‘’In wasiyar ce ma na gode Allah Shukhura da ya bani damar yi muku,ita mutuwa rigace a jikin kowa,dama haka yake ko na rigaku tafiya ko ku rigani, fatana idan ta Allah ta kasance gareni ku rik'e junanku ku kuma rik'e zumunci ku d'auki jimirin yi mini addua to zan kwanta a kabarina cikin salama.‘’

Dukkaninsu shiru sukai ko wanne da abinda yake sak'awa a ransa, amman har lokacin hannunsu a dunk'ule yake har na Maman tana binsu d'aya bayan d'aya da kallo.



Hankalin Umma in yayi dubu ya tashi, ita da boka yace muddun Shukhura ta kwana a gadon nan ta musu Katanga da 'yan uwanta to ya hakan bai faru ba, dole ta koma gurin bokan nan, kuma tana son ma dangin mijin nata ta mallakesu suma su dingai mata kallon babar Shukhuran, yanzu tana ji tana gani ji kud'in da sirikar Shukhuran ta ajiyewa Mama, shima Mustaphan wa yasan adadin nawa ya bawa Nusrat in,don haka ta yanke gobe da sassafe can gurin bokan nata za tayiwa tsinkayi.



~WASHE GARI~
Ta gurfana gaban boka kamar wacce ke shirin yi masa sujjada, bayan ta gama zayyana masa abinda ke tafe da ita.
‘’ Kin fiya gaggawa in baki wasa ba aljani bela zai fatattaki aikinki gaba d'aya daga nan gurin.‘’
Cikin rawar murya Umma tace.
‘’ Allah ya huci zuciyar aljani bela, na tuba kaina bisa wuya, idan aiki ya kammala na maka alk'awarin dubu d'ari biyar.‘’
‘’Aljani Bela yaji dad'in kyautar da kikai masa don haka yace ki koma gida ki kwantar da hankalinki, kina zaune zakiga al'amura suna canzuwa hatta sirikan nata sai sun dawo gurfana miki.‘’
‘’Godiya nake, godiya nake aljani Bela.‘’
Ta fad'i hakan tana barin gurin da baya da baya.....




200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.



#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna



KATANGA...



...............14

Rashin zuwan Baba sosai yake damun Mama amman ba ta fito ta gaya musu ba, amman abin yana mugun bata mamaki ainun,amman duk da hakan ta nayi mishi uzuri may be wani abu ne ya hana shi zuwa, amman yau tabbas za ta saka Nusrat ta kira mata shi, don tana son su gana kafin ta Allah ta kasance a kanta, don wannan ciwon nata ba ta jin na tashi ne, da mugun zazzab'i ta kwana, sai da gari ya d'an sha sannan ya sauka gashi yanzu ma tana jin alamun dawowarsa, kallon Nusrat tayi tace.
‘’ Yayarsu yau in kinje gida kicewa Babanku yazo ina son ganinsa .‘’
‘’Tom insha Allah zan gaya masa, jikinne naji muryarki wani iri?‘’
‘'Zazzab'in ne yake son dawo mini kin sanshi da naci'’
'‘Sannu, insha Allah ma bazai dawo ba, ni wallahi har ina saka ran sallama ma da naga jiya jikin naki yayi kyau'’
‘’Wallahi nima haka Yayarmu, har na fara murna zaman asibitin nan sam ba dad'i‘’Cewar Yusra.
‘’Zaman asibiti ina yaga dad'i ai sai dole sai kuma ta kama ka, bari naje gida yanzu don na dawo da wuri, ki kula da Maman.‘’
‘’Tom shikenan sai kin dawo, ki tahon da wani kayan na sauya wannan.‘’ ‘’Tom‘’
Kafin ta matsa jikin gadon tace.
‘’Mama na tafi‘’
‘’Tohm sai kin dawo, kar ki manta ki kirawo mini Baban naku.‘’
‘’Insha Allah, na san bai fita ba ma tun da yanzu goma tayi.‘’ Tana kawowa nan ta saka kai ta fice.

Ta kwa samu Baban a gida, d'akinsa ta fara shiga suka gaisa kana ya tambayeta jikin Maman tace ‘’Da sauk'i, tace ma in ka samu dama kaje tana son magana da kai.‘’
Shiru yayi kamar bazai ce komai ba daga bisani ta numfasa yace.
‘’Na rasa me yake damuna ne wallahi, sam bana jin dad'in jikina in zauna inyi rubutu ma in sha abin ya gagara amman bara ki gani‘’
daga haka ya nufi ma'ajiyarsa ya lalibo wata takadda, ya d'auko alk'alami da tawada da allo ya mik'o mata.
‘’Ungo maza rubuta mini ita yanzun nan na sha. ‘’
Karb'a tayi had'e da amsa mishi da ‘’To‘’Kafin ta gyara ta fara rubutun, to da yake tana da saurin rubutun sai nan da nan ta gama ta wanke masa, ya karb'a yayi bismilllah ya shanye tas yayi hamdala.
‘’Ki tafi da takaddar ki ajiye a gurinki, in kin samu lokaci ki dinga rubutawa insha Allahu ba dai mutum yayi tasiri a kanki ba.‘’
‘'Tohm na gode '’
Cikin hanzari tayi duk abinda za tayi ta koma asibitin tana zuwa ta tarar da jikin Maman sosai ya rincab'e likitoci ne ma a kanta, Yusra na gefe tana kuka.

Likitan ne ya juyo ya kalli Yusra yace.
‘'Ina me jinyar nata?‘’
Kafin Yusran tace wani abu Nusrat tayi saurin cewa. ‘’Gani nan‘’ had’e da shigowa ciki.
‘’Ana buk'atar jini da hanzari, don zazzab'in ya k'one mata jini.‘’ Cikin tashin hankali Nusrat tace da shi.
‘’To a ina zan samo jinin?‘’

‘’Baza kije ki tambaya ba ko ni kike so na rakaki?‘’
Yace mata a kausashe, girgiza masa kai tayi had'e da ficewa da hanzari k'walla na taruwa a idanuntaa, da tambaya ta samu ta isa d'akin da ake sayar da jinin, tana zuwa suka tambayeta wani gruop za'a bata, sai a sannan ta tuna shaf ta manta jininma kala kala ne baki na rawa tace musu bara ta koma ta tambayo, har da gudu gudu ta had'a tana haki tana tambayar likitan kafin ya gaya mata sai da ya balbaleta da masifa.
‘’Ke wata irin dak'ik'iya ce tun kan ki tafi ya kamata ki tambaya, idan kika jaho ta rasu ai bani nayi asara ba , kice 'O' zasu baki.‘’
‘Ai ba ta bari ya rufe bakinsa ba ta kwasa da gudu ta na ayyanawa a ranta da Shukhura ce sai dai su d'ebi 'yan kallo da likitan nan, don taga alamun tijararre ne tun zuwansu ake fad'arsa har ba'a so dutynsa ya kama itama taso kafin zuwansa an sallamesu don ba ta son hayaniya.

Sai da ta koma ta kuma tuna ba ta tambayeshi guda nawa ba, kawai ta amso leda biyu ta juyo, tana zuwa ya ansa yana b'alla mata harara yaje ya sakawa Maman inda Allah ya taimaketa dama biyun ake buk'ata, guri ta samu tana mayar da numfashi 'yan gefen gurinsu sai sannu suke mata Yusra kuma ta d'auko ruwa ta bata.
‘’Na gode.‘’
Tace da ita tana cisge bakin ledar ta hau sha.
Ana fara sakawa Mama jinin ta samu bacci, sai kuma ga Baba yazo, baiji dad'i ba da ya tarar tana bacci amman sai ya kasa tafiya yaja kujera ya zauna daga gefenta yana jiran ko za ta farka, ganin Baban ya zauna yasa Nusrat da Yusra suka fita harabar asibitin sai gashi sun ci karo da Nimha da mijinta suna ta zagayen neman inda suke, gaisawa sukayi suna tambayarsu me jiki su kuma suna basu amsa kafin suce suzo su shiga ciki su ganta duk da bacci take, suna shiga kuma sai suka tarar ta farka suna magana da Baba, wanda yafiyarsa take nema, tana bashi amanar yaranta, shi kuma sai kwantar mata da hankali yake yana alak'antamagan ganun nata da zafin ciwo ne.
Cike da tausayawa Nimha ta k'arasa gaban gadon tanaiwa Mama sannu, Saminu kuma ya durk'usa gaban Baba suna gaisawa kafin itama ta tsuguna ta gaisheshi, basu wani jima ba sukai musu sallama suka tafi, bayan sun ajiye lemon zak'in da suka kawo ana ta musu godiya, Baba kuwa ranar har dare yakai a asibitin da ya motsa za ta rik'e shi, sai da dabara yake zuwa yayi sallah ya dawo.



Tun daga wannan rana ya zamto kullum sai an k'arawa Mama jini leda uku, saboda zazzafan zazzab'in da take fama da shi, shi yake k'one mata jinin.
Duk kud'in hannun Nusrat sun k'are, duk wani abu da za'a amfana da shi a d'akinsu ta siyar saboda siyan jini, hatta wayarta ma ta siyar ta Mama ce kad'ai a hannunta, gashi har ta kai yau babu kud'in da za'a siyi wani jinin, ga Shukhura tun zuwan da sukayi d'in nan ba ta dawo ba, ta kirata yafi sau a k'irga ita da Mustaphan babu wanda ya d'aga bare ya biyo.
‘’ Yusra ungu d'ari biyun nan, ki hau mota maza kije gidan Shukhura ki gaya mata halin da muke ciki tun kafin azo buk'atar jinin nan.‘’
‘’Tohm‘’ tace tana karb'an kud'in ta tashi ta fita.
‘’Yayarsu.‘’
Taji Mama na kiranta da muryarta da ba ta fita sosai yanzu, matsawa tayi sosai kusa da ita, ta kamo hannunta had'e da fad'in.‘'Sannu Mama’'
‘’Kiyi hak'uri Yayarsu, ki kula da rayuwar Yusra, Allah ya azurtaku da miji na gari yayi muku albarka baki d'ayanku.‘’
‘’Amin, ki daina irin magan ganun nan, insha Allah zaki ji sauk'i mu koma gida ‘’
Murmushi kawai tayi mata, murmushin da ita kad'ai tasan ma'anarsa.

Allah Allah take Yusra ta dawo tun kafin a buk'aci jinin nan, tun da ta riga tayi amannar ko Shukhuran ba ta biyota ba za ta bayar da wani abu a kawo musu, amman ga mamakinta sai taga Yusran zik'au sai magana mara dad'i da tazo mata da ita, cewar Shukhuran tana bud'e k'ofarta taga Yusran ta mayar ta rufe, babu bugun da ba tayi ba tana kuka tana magiyar ta bud'e had'e da gaya mata halin da suke ciki amman tak'i ta bud'e, Innalillahi take ambata a zuciyarta tana jin wani mugun rad'ad'i tun daga can k'asan ruhinta, tashi tayi ta fita daga asibiti ba tare da ta san ina ta nufa ba, kawai dai taga ta tari me napep tayi mishi kwatancen gidan Shukhuran, tana zuwa me gadi yake sanar mata yanzu aka fita da Shukhuran asibiti, sakamakon farfasa kayan gidan da tayi.
Jiri taji yana neman kayar da ita, da sauri ta jingini da bango tana dad'a ambaton innalillahi.
Me yake shirin faruwa da su ne, wata k'addara ce ta kutso cikinsu ba tare da sun shirya mata ba ?Babu babu babu me bata wayannan amsoshin.
Ko ina ta samu jefe k'afafuwanta take ba ta da ko biyar da ta rage mata wacce za ta hau mota ta mayar da ita asibitin, ga wani bak'k'k'irin d'in hadari da ya,had'o ta gabas ana ta iska da walk'iya, iskar sai kokarin cire mata hijabi take, ba ta damu da hakan ba ita dai duk inda ta samu jefa k'afafuwanta take, har ruwa ya saukko taci gaba da tafiyarta cikin ruwan wani me adai daita ne ta bashi tausayi ya tsaya a gabanta yace ta hau, godiya tayi masa ta shiga har lokacin k'irjinta wani irin zafi yake mata da tiriri ga gabanta da,yake ta mugun fad'uwa ko kad'an innalillahi ba ta bar lab'b'anta ba, tana shiga d'akin da suke Yusra ta taho da gudu ta rungumeta tana kuka.
‘’Yayarmu, Mama mama mama ta rasu‘’
Kawai ji tayi tana fad'ar Innalillahi wainna ilaihir raji'un da k'arfi wanda sai da d'akin gaba d'aya ya amsa, kafin ta sauke idonta kan gadon da Maman take an lullub'eta gaba d'aya har fuskarta....










200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.



#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna



KATANGA...



...............15

Wani rugugi da hargagi take ji a cikin kwanyarta kafin ta runtse idanuwanta tana karanto dukkanin addu'ar dake bakinta, a hankali taji 'yar nutsuwa na shigarta ta mik'e daga zaman borin da tayi tana rarrashin Nusrat tayi shiru, kafin ta tashi ta fara cuku cukun karb'ar gawar, bayan ta kira Baba ta sanar masa ga sunan zuwa taje ta taro mai taxi, da mai taxi din da wasu samari ne suka taimaka aka sanya gawar cikin motar.

Mutane dank'am suka tarar a k'ofar gidansu, mutuwar ta riga ta gama fasuwa.
Babane da kansa ya yiwa Mama wanka ya had'ata, ya kirawo su Nusrat suyi mata addu'a, Yusra kuka kawai take yayin da Nusrat ta rintse idanuwanta tana mata addu'a da zazzak'ar muryarta da ta cika gidan gaba d'aya kafin tace da Yusra.
‘’Mama ba ta cancanci zubar hawayenki a yanzu ba, ki rakata da addu'a shi tafi buk'ata.‘’
Share hawayenta tayi ta fara yiwa Mama addu'ar a ranta tana ganin k'arfin halin Yayar tasu ko tace k'arfin imani da tawakkali.

Sai da akayi sallar magariba saboda ta riga ta kawo kai kana a kazo fitar da Mama gidan rud'ewa yayi gaba d'aya ana binta da addu'a masu had'awa da kuka suna yi, Yusra kuwa guri ta samu tana kuka da birgima tana fad'in
‘’Kada ki tafi ki barmu Mama, ki dawo garemu dan Allah.‘’
Sai a wannan lokaci Nusrat taji idonta ya fara ruwa, abinda take buk'ata kenan ko za taji sanyin abinda ya dunk'ule mata a zuciya da tsakiyar kwanyarta, janyo Yusran tayi ta rungume tana bubbuga bayanta.
‘’Yayarmu yanzu Mama ta tafi ta barmu?‘’
‘’To ya zamuyi, dole muyi hak'uri mu karb'i k'addarar da tazo mana a haka, Allahn da yafimu k'aunarta shi ya karb'eta mutuwa tayi mana Katanga da ita, sai dai mu bi bayanta da addu'a shikad'ai ne abinda zamui mata gata da shi, sai dai kuka ya zama dole, dole ne muyi kuka, kukan rashi rashi mafi girma a garemu, amman na kasa ko da d'igar da hawaye, gara na zubar da hawayen Yusra akan azabar da nake sha cikin kwanya da zuciyata.‘’


Har aka share zaman makokin Mama Nusrat na fama da zazzafan zazzab'i da ciwon b'arin kai d'aya, gaba d'aya ta fige ta fita hayyacinta donma Baba yana mata rubutu na kariya da dangana to shine samun d'an lafiyarta, amman da duk ta tayarwa da Yusra hankali don itace me jinyar tata sai Baba idan ya dawo ya lek'osu ko ya kawo mata rubutu ta sha. A hankali suka fara sabo da rashin Mama da rayuwarsu su biyu a cikin d'aki sai Baba idan ya dawo daga kasuwa ya lek'osu, idan ya samu ciniki a kasuwar yakan taho musu da gurasa da nama don idan ba'ai girki a gidan ba wuni suke ba su ci ba babu ruwan wani da su, Nusrat gani tayi rayuwa ba za ta b'ille da su a haka ba in ba so suke su kashe kansu da yunwa ba, don yanzu k'irjinta ciwo yake mata alamun ulcer inta na gab da tashi, gurin Maman Ameema taje ta rok'eta akan tayiwa Baffa Shamsu magana akan ya bata 5000 za ta ja jari (Don yanzu ko Iya ce take da buk'ata sai ta biyo ta hannunta)
To sai Allah ya d'orata a kanta a washe gari tayi kiranta ta bata dubu biyar d'in godiya ta dungai mata har da 'yar k'wallar ta kafin ta nufi kasuwa.
Sana'ar wainar Shinkafa ta fara yi da miyar taushe da nama, da me k'uli-k'uli in mutum na buk'ata, ciniki take yi sosai don cika gidan ake da masu siyan waina, idan ba ranar makaranta ba ce Yusra ce ke tayata idan kwa ranar makaranta ce ita kad'ai take yi, a haka rayuwa taci gaba da gangarawa yau fari gobe tsumma, suna samu su rufawa juna asiri da wannan sana'ar wainar da take yi.



SHUKHURA

Bayan barin Yusra gidan kuka ta dinga yi tana jifa da komai na gidan kamar wacce ta zare ta fita hayyacinta a cikin wannan halin Faruoq ya dawo ya tarar da ita, kamar jira take ya dawo numfashinta ya d'auke gaba d'aya shine ya fita da ita a gigice.
Dogon suma tayi wanda ya ibeta tsawon kwana uku ba tare da ta san inda kanta yake ba kafin ta farka, babu wanda yayi gigin gaya mata mutuwar Mama saboda Baba da kansa yayi musu waya ya gaya musu kuma dukkaninsu sunje gaisuwa, sai da ta kwana biyu ta k'ara wartsakewa sosai sannan Mustapha ya d'aukota ya kawota gida a cewarsa bazai iya gaya mata mutuwar Mama ba domin baza ta tab'a iya goge wannan memoryn ba, Baba ne da kanshi ya gaya mata babu abinda tace sai kuka kawai da ta wuni tana yi a d'akin Umma don ko k'ofar d'akinsu ba ta taka ba, suma babu wanda ya nuna ya san tazo Yusra ma mugun haushinta take ji, tana ganin kamar ita ta janyo sanadiyar da suka rasa Mama.

Umma buri ya cika, kud'i sosai Shukhura ke sakar mata, duk wani abu da ta yayibo ita take kawowa, Mustapha kuwa ya bawa Saminu jari me kauri yanzu su Nimha ma fantamawarsu suke, Nimha taso yin magana ganin yadda Shukhura ta juyawa su Yayarsu baya amman ta kasa saboda itama sai da ta d'aure mata baki, amman duk da haka ita tana taimakonsu a b'oye, sabulun wanka, na wanki omo 'yan kud'i haka tana bawa Yayar tasu, duk da suma yanzu Alhamdlillah suna samu sosai cikin sana'ar wainar da suke yi, suyi girkinsu, su d'inka suturarsu, su biya kud'in makarantar Yusran su kuma kashe gararin gabansu, Yusra ba ta tab'a bari a ci musu mutumci duk wanda ya tab'a Nusrat sai dai idan ba ta gidan, a haka rayuwa ta dunga tafiya tana gangarawa gashi har yanzu shekara guda da k'asa ta rufewa Mama idanu, a wannan shekara babu ranar banza da za tazo ta fad'i ba tare da sun nemawa Mama rahamar Ubangiji ba, tsakaninsu da Shukhura kuwa har yanzu sai kallo, ko jiya da tazo yiwa Umma da Baba sallama zasu koma kano tana ta laulayin ciki ba tace musu ba suma ba suce mata ba.....

200 ne kacal katin waya 300
ga masu buk'ata zasu turo ta wannan accaunt in.
0567838462
FADILA SHU'AIBU NABABA GT BANK

In katin wayane ki turo ta wannan number
09037093702, shaidar ki ta biya ma ki turo cikinta

Duk wacce za ta sayi littafina ta sayeshi da sharad'in in na mutu ban k'arasa ba ta yafe mini da rai da rayuwa duk a hannun Allah suke, bani da tabbacin zan kai lokacin sai dai muna fatan fin hakanma, Allah kasa mu cika da imani amin.



#NWA
#KTG
[4/26, 8:42 PM] Rabi: BEBE'ARTH


Wattpad@Rashuna


®️NAGARTA WRI.ASOCIATION


KATANGA...

In baki siya ba ya kamata ki mallaki naki a hannu kar garab'asar ta wuce ki, in na gama free page zaki siyeshi akan 300 ne,kuma in kin siya yanzu zaki samu damar karanta CIN AMANA kyauta, kada ku bari wannan garabasar ta wuceku, kada ku manta akwai abin amfani a ciki.

Masu tambayata document in na gama, shi kuma zaku sameshi akan 500kacal.

...............16
Babane zaune a shagonsa ya kunna 'yar tsohuwar redionsa yana saurare, yau tun da ya fito ko biyar baiyi ba kamar wanda akaiwa tofin Allah tsine, ko kuma don kayan nasa sunyi k'asa ne Allah ne dai masani.
Wani mutum ne ya taho yana jan k'afa d'aya d'aya k'afar da alamu harbinsa akayi don ga jini nan na d'iga daga saman kafad'arsa ma harbinne, sai da yazo saitin da Baba yake ya ajiye masa wata 'yar k 'aramar camera da 'yar farar takarda, "Ka kula sosai rayuwarka za ta iya shiga had'ari, dukkan bayanan na cikin takaddar, kayi k'ok'ari gurin ganin ka isar mini da sak'ona,don tawa ta k'are bazan tab'a shaa ba, amman zanyi farin ciki muddun a hannu me amana na dank'a sak'ona."
Yana kawowa nan yayi saurin juyawa yabi ta gefen shagon nasa, kafin lokacin Baba yayi saurin d'auke abinda ya ajiye masa ya b'oye a aljihunsa, yaci gaba da saurarar redionsa amman zuciyarsa cike take da taraddadin wannan al'amari.
Wasu mutane ne suka tsaya daga bakin shagon nasa suna nazarin gurin ganin jini ya d'id'd'iga, daga ganin fuskokinsu ba imani zasui ba, zuciyar Baba sai bugawa take cike da tsoro amman ya maze yana saurarar redionsa wanda ba ya ma fuskantar abinda ake fad'i a ciki, kafin su kuma subi hanyar da ya bi saboda d'igar jinin da ya ankarar da su.


Baba cike da tsoro da taraddadi ya huni a wannan rana, gashi bai san ya takaye tsakanin mutumin nan da wayannan mutanen ba, a haka har lokacin tashinsa yayi ya tashi ya nufi gida cike da mugun zulumi.
Sai cikin dare ya warware takaddar da ya bashi ga abinda ta k'unsa;
"Ina fatan sak'ona ya isa hannun me rik'on amana, wanda zai iya siyar da rayuwarsa kamar yadda na siyar da tawa, na san muddun ka kalli abinda ke cikin camerar nan muddun kana da imani za ka so

Please Login or Register in order to submit comment