Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farkon bane wannan Bro Asad ne, dole ya d'aga wayarshi don ya tabbata yau a yadda yake jinsa idan ba da taimakonsa ba bazai iya rintsawa ba, yana peking in wayar bai tsaya saurarar me zaice ba yace.
"Ka shigo." A takaice kana ya ajiye wayar ya mayar da idanuwansa ya rufe.

Wani shegen murmushi Aasad ya saki yana kallon Asghar kafin yace.
"Ko a yanzu ka tabbatar na fika muhimmanci a gurunsa, don haka abinda yafi sauk'i ka ja jiki a gurin da baka da kwarjini, ka kuma daina yunk'urin kub'utar da Damisan da ya dad'e da aminta da zaki, don baza ku tab'a jituwa ba idan har kana kawo sukar zaki a gare shi har abada, idan nace har abada ina nufin har abadan abadina."
Yana kawowa nan yasa kai zai huce yayin da Asghar ya sanya hannu a kafad'arsa had'e da fad'in.
"Magana d'aya zan gaya maka, domin bani da lokacin da zan tsaya ina musayar magana da kai, ina so ka dinga tunawa da kalmar nan ta hausawa da kan cewa, rana dubu ta b'arawo rana aya tak ta me kaya idan ka isa ka hana wannan ranar zuwa."
Yana kawowa nan ya shige cikin motarsa had'e sa yin revers ya fice daga cikin gidan yayin da Aasad yayi wani shu'umin murmushi a ransa yace.
"Idan ma rana ayan za ta zo to na tabbata sai ta tab'a zuciyarka domin za kaga abinda zatonka bai tab'a zata ba."



。。。。。。

Lafiya ta gagari Rj har sai da ta dangana shi da asibiti, kwanansa biyu a asibiti Daddy ya dawo, inda yaji labarin komai daga bakin Momy, shi kanshi abin ya matuk'ar d'aure masa kai sam bai yadda Nusrat za ta aikata haka ba, amman dai yayi musu shiru yaja Hibba ba tare da kowa ya sani ba suka tattauna akan lamarin, inda Hibba sam ta nuna itama ba ta yadda musamman rubutun da Nusrat in ta bari ba nata bane don ta tab'a taya Hibban wani note da ta d'auko ta had'a sam basu zo aya ba.

Ishaq Daddy ya nema, inda ya saka Hibba sato numbersa a wayar Hidaya, da haka ya sameshi har suka tattauna, shima dai ya nuna bai san da wannan zancan ba ko kad'an, shi tun fara alakarsu da Nusrat ko farcanta bai taba k'ok'arin rik'ewa ba inama yaga fuskar yin hakan.

Satin RJ biyu a asibiti aka sallameshi ya d'an fara samun sauk'i, sai dai abinda yake cikin zuciyarsa ne sai Allah kuma, Daddy yana ta tausarsa da kwantar masa da hankali na cewar ya saka a nemo Nusrat in acan garin zariyan, duk da har yau dai babu wani labari nata da aka samu, ya dai d'ora alhakin komai akan Momy, don ya gaya mata duk abinda ya samu Nusrat in hakk'in ya rataya a wuyanta, idanma tayi hakanne don Hidaya ta auri RJ in to ya haramta aure tsakaninsu, ko bayan ransa bai yadda RJ in ya auri Hidaya ba ko da kuwa za ta rasa ranta ne saboda son da take masa zai bar ma wasiyya a rubuce, wannan shine hukuncin da suka sanya zuk'atan marayun Allah a ciki, kafin su karb'i hukuncinsu gurin Ubangiji kuma, duk da rantsuwar da sukai na babu hannunsu cikin lamarin amman sam Daddy bai yadda ba, cikin kwana biyu tak Hidaya ta fara d'and'anar zafin rashin masoyi, zuciyarta ta shiga k'unci da zafi da rad'ad in da ta Rj da Nusrat take ciki, tun da ta riga ta aminta babu aure tsakaninta da RJ in duk yak'in da suka yi ya tashi a banza kenan a take nadama ta fara nuk'urk'usar zuciyarta .

(Hhhh yadai Hidaya nadama da wurwuri haka?)



A b'angaran Yusra kuwa sam ba ta cikin kwanciyar hankali, don da ta kira Hidaya ta zayyana mata abinda ya faru, ba tayi k'asa a guiwar zuwa gidansu ba hankali a tashe, nanma Iya ta zayyana mata komai, tun daga can take kuka tana ita sam ba ta yadda da wannan sharrin da aka k'agawa Yayarsu ba, saboda su marayu ne babu idon iyayansu shiyasa babu bincike babu komai zaa kama a koreta, Allahn da ya halicceta yana gani kuma zai tallafeta idan ma anso ta lalace ne zai kareta daga haka insha Allah.
Kullum cikin kuka take tare da kaiwa Allah kukanta akan ya kare mata yayarta a duk inda take...
[4/26, 8:46 PM] Rabi: 34

A hankali idanuwanta suke bud'uwa har suka bud'e gaba d'aya, akan fankar da ke tsaye cak ba ta aiki, sabili da ruwan saman da aka tafka jiya da daddare shiyasa aka tashi garin yau da sanyi, GOGEL HOSPITAL shine abinda ke jikin fankar, wani sanyin dadi taji a ranta sabili kuwa ta san tabbas yau za ta bak'unci lahira, ita kuwa tafi buk'atar hakan a yanzun sama da komai don tana son ta huta sosai.
"Alhmdlillh, na godewa wanda ya kawoni asibitin k 'arasani, me likitan yake har yanzu bai k'arasar da ni ba ne? Ku kirashi don Allah ya k'arasani."
Takai k'arshen maganar had'e da fashewa da matsanancin kuka, tsorata sosai Baba Hadiza tayi, don a tunaninta ko dai mahaukaciya ce, don haka ta juya kirawo likitan sai ta tadda su shi da likitan sun nufo d'akin don haka tun a hanya take basu labarin abinda ta farka da shi.

Ta tashi daga kwancen da take ta had'a kai da guiwa tana ta gurshek'an kuka, shi kuwa ya tafi tunanin ina yasan wannan sautin kukan, sautin da ya zauna cikin kwanyarshi daram, saukar sautin muryarta ya kuma ji da takewa likitan magana yayin da yake duddubata.
"Dan Allah na rok'eka ka k'arasani, na gaji da duniyarnan ina so na huta."
"Mu ai bama kisa, kuma baza mu fara ta kanki ba, tunda ranku ba'a hannunmu yake ba. "
"Mahaifina fa?"
"Mahaifinki ya,mutu a nan ne?"
Gyad'a mishi kai tayi, yayin da shi kuma yace.
"To kwanansa ne ya k'are."
"Amma ai ana baku kwangilar kashe mutane ko?"
Gabansa ne ya fad'i, a tare tsoro da rud'u ya bayyana akan fuskarsa , yayi saurin kallon gurin da Aashiq yake a tsaye yayi folding hand insa had'e da zubawa fuskarta kyawawan idanuwansa, fuskar da ta zauna cikinsu tun ranar farko da ya fara d'orasu a kanta.
Da sauri likitan ya janye idonsa daga kansa ya mayar kanta, yana me addu'ar Allah yasa bai ji abinda ta fad'a ba.
"Inma ba kwa karb'ar kwangilar to ni yau na baku ku k'arasani na huta don Allah."
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke a b'oye kana yace mata.
"Ke musulma ce?"
Gyad'a mishi kai tayi."
"Idan har ke musulma ce kin kuma yadda da k'addara to don me yasa zaki buk'aci mutuwa, bayan mutuwar ba a hannunmu take ba?"
"Na yadda da k'addara, don da ban yadda da ita ba titi zanje na kwanta mota tabi ta kaina, zafi da rad'ad'i nake ji a k'irjina, ina so na daina jinsa, baza ka gane ka kuma fuskanci yadda nake ji ba, da ace Mama da Baba suna nan sune zasu fi fuskantata."
Sai ta fashe da wani matsanancin kukan, yayin da Aashiq ya kalli Baba Hadiza ba tare da yace uffan ba kuma ta fahimci yaren da yayi mata, kana ya kalli likitan yayi mishi inkiya da suje kawai.

Kuka take sosai, yayin da Baba Hadiza ta shiga bata baki had'e da yi mata wa'azi, a hankula cikin hikima take hilyatarta har sai da ta zayyana mata abinda yake faruwa da rayuwarta
, saboda yadda da taji tayi da matar tun a kallo d'aya da tayi mata, kafin ta tambayeta ya akai aka kawota asibiti, ita kuma ta sanar mata da cewar KATANGARSU ne ya kawota kuma ya umarci idan ta aminta su tafi gida da ita, babu inda zata je ba kuma ta san inda zata nufa ba don haka ba ta da wani zab'i da ya wuce ta bisu kafin taga yadda Ubangiji zaiyi da rayuwarta don ba ta san k'addarar da ke jiranta a gaba ba.



Sallama likitan ya rubuta musu, Khalil ya d'aukesu ya nufi gida da su, tayi mamakin ganin sun nufi GRA sai kuma taga sun shiga gogel estate ta kalli Baba Hadiza tana son jin wani abu daga gareta anman ba tace mata kpmai ba don haka itama ta kama bakinta tayi shiru.
Har zasu shige ciki, bayan sun danna door bell Baba Azumi ta bud'e musu, sai Khalil ya tsayar da su, ya basu akwatin Nusrat in, tayi matuk'ar farin cikin ganin akwatin nata don daa har ta saddak'ar ya salwanta.
Fuska sake Baba Azumi ta tareta yayin da itama ta gaisheta cike da fara'a don ji tayi matar ta burgeta ta kuma shiga ranta sosai da sosai, D'aki Baba Hadiza ta kaita ta nuna mata toilet.
Wanka tayi sosai ta gasa jikinta, tayi mamakin ganin jinin ya d'auke don haka kawai sai tayo wankan tsarki ta fito, sai da ta gama shiryawa kana ta zauna a bakin gado tana sauke idon kan wani hoto da ke manne a bangon d'aki, idan ka cire fuskokin mutum biyunnan da ta gani to babu wanda kuma ta sani, Baba Hadiza ce ta shigo tace ta taso taci abinci sai ta sha magun gunanta.

Baba Hadiza ce da kanta tayi sarving nata ta fara cin abincin a hankula kafin suji k'arar door bell, Baba Hadiza ta nufi babban falon don bud'e k'ofar.
Yara ne su uku, mata biyu namiji d'aya sai kuma budurwa kamar Yusranta suka shigo, Baba Azumi ce ta kalli 'yar budurwar had'e da fad'in.
" Ba dai har an tasheku ba?"
Dak'una fuska tayi kafin tace.
"Kai Baba duk dad'ewar nan da nake ganin munyi."
Takai k'arshen maganar tana sauke idonta kan Nusrat kafin ta kalli Baba Hadiza.
"K'aruwa muka samu."
Baba Hadiza tace mata, murmushi ta saki had'e da k'arasawa gurin Nusrat in tace.
"Sannu Aunty, sunana Fa'iza, nice autar gidannan, wa'yannan yaran da kike gani arosu mukayi nan da anjima zan wulla ko wacce gidansu."
"Aunty nice nan auta sunana Aalisha Baby."
"Wallahi Aunty nice nan Auta sunana Falisha Beauty."
"Ni kuma nine babbansu sunana Yaya Aliyu, Aunty da ni kad'ai zaki dinga zuwa shan ice cream ko duk nafi Aalisha da Faliisha hankali."
Murmushi tayi tana jin wani sanyi a ranta had'e da mamakin Yaa Aliyu da alamu Falisha da Aalisha zasu girmeshi amman sai yaci girman yace shine babba tunda su daga jin Faiza tace itace Auta suka ara suka yafa.
"Ni kuma sunana Nusrat, naji dad'in kasancewata a cikinku."
Takai k'arshen maganar tana sauke idonta kan Faiza.
"Muma munji dad'in zuwanki sosai da sosai, bara mu cire uniform."
"Godiya nake, a fito lafiya."
"Allah yasa Aunty."
Daga haka taja hannun su Falisha zuwa ciki."

"Haka kuke da karamci?"
Ba ta san lokacin da bakinta ya jefowa Baba Hadiza wannan tambayar ba, murmushi Baba Hadiza tayi had'e da fad'in.
A kanshi aka rainemu Nusrat dole ne mu kasance muna yinsa.

_"A hali na hauka na tsinci kaina daga wannan bola zuwa wannan bola nake rayuwa, babu wanda ya tausaya mini ya kalleni a matsayin yar adam sai shi, shi ya d'aukeni ya kaini asibiti akayi mini magani har na samu kaina, ko da na warke Nusrat ban san ni d'in wace ce ba, ban san komai akan kaina ba, haka ya d'auko ni ya kawoni cikin gidan nan ya bani ci ya bani sha had'e da sutura, ya kuma bani farin ciki, wannan farin cikin sune wannan ahalin_"
Takai k'arshen maganar tana ajiye hoto a gabanta window size, kana taci gaba.

_Falisha, Nabila, Ramla, Rabi'ah, Farida, Faiza, Baba Azumi, Baba Hadiza ni kenan, sai kuma k'anwarsa uwa d'aya uba d'aya Aalisha._
_Wa'yannan sune farin cikin da Aashiq ya bamu, domin sun d'aukemu ni da Baba Azumi tamkar mu muka tsuguna muka haifesu, mun sosu sun somu, mun k'aunacesu sun k'aunacemu, rayuwa muke me cike da farin ciki da annushuwa, dukkaninmu marayu ne don bamu da kowa ba mu san kowa namu ba, Aashiq shine KATANGARMU domin yayi mana katanga da k'unci da damuwa, da kuma rayuwar k'ask'anci da wulak'ancin da muka taso a cikinta, da badan shi ba da tuni muna can muna garari a cikin duniya amman sai ya had'emu guri d'aya ya bamu farin ciki wato junanmu muka zamo ahali d'aya, wanda har daga k'arshe rik'on k'anwarsa ya dawo hannunmu._
_Faiza 'yar Baba Azumi ce ta cikinta, Nabila, Ramla,Rabi'ah,Farida duk mun aurar da su, Falisha 'yar wajen Rabi'ah ce, Aalisha kuma ta gurin Nabila, Aliyu shi kuma na Farida ne, Ramlah ce ita kuma sai yanzu Allah ya kawo rabon tana goyan 'yan biyu Safa da Marwa._

"Allah ya,biyashi, ya kyautata rayuwarsa kamar yadda ya kyautata tamu gaba d'aya, amman Falisha da Aalisha fa?"
Cewar Nusrat kenan yayin da Baba Azumi da Baba Hadiza suka hada baki gurin cewa."Amin ya Allah" Kafin tambayarta ta dakesu, dukkaninsu sai da idanuwansu suka kad'a kafin suce.
"Allah yayi musu rasuwa."
"Allah yayi musu rahama, kuyi hak'uri"
Sam ba taji dad'in yanayin da taga sun shiga ba sai taji dama ba ta tambayesu su ba, ta hak'ura da iya abinda suka sanar mata......

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment