Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta biyo bayanta.

Kamar an jefota ta shigo ta na kallon Nusrat da ke zubar da shara.
"Sannu"
Tace mata, kafin ta shige zuwa gurin Iya, iya na ganinta ta d'aure b'arin goron da ta b'antara a gefen zaninta kana tace.
"To rasa kunya b'eran tanka, kinzo kimin rashin kunyar taki ne? “
Kar katar da kai Shukhura ta yi tace.
"Ashe 'Yar aljanu na da rana tun da har an iya sakata aiki, me yasa ba ki kirawo 'yar lelen taki tai miki ba sai ita za ki saka, amma in abu zaki bayar babu wanda ke gabanki sai Nimha, amman in aikine sai wacce kika raina, don kin san Nimha ko tsintsiya ba za ta iya d'aga miki ba.
Bayan kuma kitso zamu je kina gani kuma Mamanmu na zaman jiranmu“

"Tunda dai ba ke na saka ba, ki shige ki bani guri, kiyi can da rashin kunyarki. “
Cewar Iya
"Waa aini kin san abinda bazai tab'a yuyuwa bane, don wallahi bazan bautawa wanda bai san ina yi ba, in cin mutumci ne ya taso azo a tarkace mini, lalalala wallahi, itama ita taga za ta iya.“
"Ni kikewa cin mutumci Safiya, Allah ya dawo da Audu, wallahi za ki gane Ubanki na haifa. “
"Amin, ya dawo d'in ki gaya masa, wallahi duka d'aya yamin kinsan sai na bi ta inda zan rama, Allah ya baki sa'a. “
"Wai da sa'ar ki kikeyi ne Shukhura?“
Cewar Nusrat ta na kallonta, ba ta bata amsa ba ta fice ta na zunb'uro baki, Iya kuwa k'ifi² ta yi da ido tunowa da ta yi sanda ta saka Nusrat a gaba ta na zaginta Shukhura ta amshe ta hayayyak'o kamar za ta daketa har sai da Mama ta fito ta kikkifawa Shukhura mari, shine Baba ya na dawowa Iya ta kwashe ta gaya masa, aikwa ranar Shukhura ta sha duka gurin Baba, ita kuwa ta d'auki aniyar wallahi sai ta rama akan Iya, sai da ta bari duhu ya yi ta kad'a karkashinsu me yauk'i taje ta zuba a band'akin Iya,don ta na da tabbacin yanzu za ta fito ta shiga band'akin ta lab'e a bayan k'ofa, Iya na shiga ta yi sufa ta fad'i Shukhura ta fito ta na ta k'yak'yata mata dariya, tace mata kad'an ta gani muddun ta na sakawa Baba na dukanta, Iya kuwa jiki yai tsami da k'yar ta iya mik'ewa.


"Yanzu Mama kina kallo ga Iya can ta saka Nusrat aiki.“
Shukhura ta fad'a ta na turo baki gaba. “
"To meye, don ta sakata aiki?“
Mama ta fad'a ta na cigaba da tankad'en da take.
"Amma Mama kefa kikace a fara mata kitson saboda za ki bar mata girki.“
"Yanzu kuma na fasa ba, kije ke a fara miki sai ki baro Yusran a can in Yayar taku tazo sa taho tare sai ki karb'i girkin na samu na fita. “
"Amma Mama....“
Dakatar da ita Mama ta yi had'e da fad'in.
"Ban san jin komai ki shige kije kiyi abinda na saki. “
Fita ta yi ta na tutturo baki Mama ta girgiza kai had'e da fad'in.
"Allah ya shirya. “




Sai da Iya ta kinta tanci dawowar Baba ta fito babban tsakar gida ta k'wama kujera ta na jiran dawowarsa, aikwa ta na jin sallamarsa ta saki kuka me k'arfi, a gigice ya nufota ya na tambayarta.
"Lafiya Iya, me ya faru kike kuka haka?"
Face hanci Iya ta yi tace.
"Wai ni yau A'i za ta kalli tsabar idona ta zageni ta uwa ta uba. “
" 'Yar baiwa.“
Baba ya k'wallawa Nusrat kira, Nusrat da ke d'aki tun da ta dawo daga kitso kanta ke ciwo shine ta nemi guri ta kwanta, ta na jiyo abinda Iya ke cewa Baba gabanta ya yanke ya fad'i, da ta ji kwa ya k'wallo mata kira nan da nan idonta ya yi rau-rau zai fidda ruwa, a hankali ta mik'e ta fito ba tare da ta amsa kiran ba, kallonta Shukhura ta yi da ke kwashe tuwo ta cika k'atuwar kula ta kai d'akinsu, tace.
"Kinga dai da abinda ta saka miki ko? kuma wannan ba shi zai hana gobe idan tace yimin kaza kiyi mata ba. “
Ba tace mata komai ba sai juya idonta da tayi da ya fara fitar da ruwa ta nufi tsakar gidan, Shuk'hura kuwa taci gaba da kwashe tuwonta ta na mamakin sanyin hali irin na Nusrat, ta yi k'wafa a hankali, a ranta tace.
'Iya kenan, ai gara ki tab'ani akan ki tab'a Yayarmu wallahi, don ba ki son son da nake mata bane.'

Baba na ganin ta taho a sanyaye ya saki murmushi had'e da fad'in.
"Taho mana 'yar baiwa. “
Ganin murmushi akan fuskar Baban nata yasa ta samu k'arfin guiwar k'arasawa gareshi, bak'ar ledar hannunsa ya mik'a mata, me d'auke da d'ata manya-manya kasancewar yasan ta na matuk'ar son d'ata, kana yace.
"Ga masoyin naki.“
Murmushi me sauti ta saki tace.
"Na gode Babana. “
Baki galala Iya ta saki ta na kallonsu daga bisani ta tafa hannuwa tace.
"Yau naga lalacewa ni Asabe, yanzu ina gaya maka abinda yarinyar nan ta yi mini amma kai d'ata ka d'auka ka bata, gani ni wacce na yi silar zuwanka duniya ka san da cewa ina mutuwar son ka'za amma baka tab'a siyowa ka bani ni kad'ai a gidan nan ba, sai dai ka siyo gaba d'aya aci, amman ita da yake shafi da mai ce ka ware ta cikin 'yan uwanta uku, ture biyunma tunda su cikinsu d'aya ai ko Nimha ka siyowa don gudun fitina.“

"D'atan da na siyo mata na tabbata ba za ta cishi ita kad'ai ba, rabawa zasui gaba d'aya da ita da 'yan uwanta, zancen kuma Nusrat ta zage ki wallahi Iya ko jikina duk kunne ne bazan tab'a yadda za ta iya zaginki ba, ko da kuwa dukan mutuwa kikai mata a cikin gidan nan, bare kuma na san halinta ba sawa ba fitarwa, da dai Shukhura kika ce to tabbas wannan zan yadda amma 'yar baiwa lalala, sai dai kice Shukhura ce ta zageki kikace 'yar baiwa ce saboda.... ”Da sauri Iya ta dakatar da shi da fad'in.
'Ni wallahi bance maka Safiya ba, ko sunanta ban ambata a gurin nan ba in ba yanzu ba, jama'a ko kunji na ambaci Safiya? “
Ta fad'a da k'arfi yadda 'yan ciki zasu jiyo ta, murmushi Baba kawai ya yi ya ja hannun Nusrat sukai ciki.
"Kedai Mero kin haifi jarabar aljanu a gidan nan, yarinya ta bi ta zamar muku masifa duk kunfi k'aunarta cikin 'yan uwanta, su kuma hakan ko kad'an hakan ba ya damunsu, wannan wata iriyar musifa ce?
Kai kuwa Audu k'atuwar asara ce ta hau kanka don zan iya dafa qur'ani kafi son wannan 'yar aljanun ko nace 'yar ruwa akan ni da na diroka duniya, bacin haka har maganata za ka k'aryata ka zab'i d'iyarka, babu komai ai gobe Shamsu zai zo garin, Allah sarki d'an albarka na san gobe miyarmu da ka'ji zan cisu har na ture, don ni ina jin idan yazo ma tattara kayana zan na bisa, don wallahi na gaji da cin shinkafa 'yar hausa da tuwon garin masara kullum suna cushe maka a ciki, don na ji ana rad'e rad'en tuwon masara gini yake a cikin mutum, haka kawai na zauna naje na kashe kaina tun wa'adina bai cika ba. “


Sai misalin k'arfe takwas Mama ta dawo, kallon Nusrat da ke kwance ta yi tace.
"Ina Mamana, Yusra taci abinci da kika barta tai bacci?”
"Cikin gida tace mini za ta shiga tun d'azu, Yusra kuma sai da taci abinci tukunna tai bacci. “
"Lafiyanki kuwa naga kina yatsina fuska? “
Ta tambayeta duk da a ranta mamakin wai Shukhura ce tace ta tafi cikin gida, bayan ba k'aunar zuwa gidan take ba, aike ma da dole take shiga.
"To ki tashi ga fura na taho miki da ita kisha sai ki sha magani.“
Da hanzari ta mik'e don dama yunwa take ji kuma har ga Allah ba ta k'aunar cin tuwon donma ta d'an ci d'atan da Baba ya kawo mata duk da wasu sunce shima ya na faifaye ciki, ita kuwa Mama sanin halin d'iyar ta ta yasa ta yo mata guzurin furar.

Sauke idanuwanta ta yi akan kular tuwon da Shukhura ta ajiye, a fili tace.
"Allah ya shirya mini ke mamana. Maza Nusrat ki gama kije ki kira mini ita. “
Ta na rufe bakinta ta jiyo sallamarta suka amsa mata.
"Laa Mamanmu kin dawo ashe? sannunki da dawowa. “
Fuska a had'e tace.
"Yauwa, me kika je yi cikin gida? “
"Nifa ba cikin gida nace mata zanje ba, gidan su Farha nace mata za ni kallo.“
Takai k'arshen maganar ta na kallon fuskar Nusrat.
"Ban hana ki zuwa kallo ba?to da Babanku kawai zan had'aki na huta, Ke kuma ai ga shinan kin rufa mata asiri ta tonawa kanta. “
Takai k'arshen maganar ta na kallon Nusrat, yayin da ita kuma ta saki murmushi.
"Kiyi hak'uri Mamanmu bazan sake ba. “
"Sau nawa kina fad'in haka? “
"Allah da gaske nake Mamanmu daga wannan bazan sake ba. “
"To wancan uban tuwon da kika ajiye da fatan abincinki ne na sati guda ko?“
"Haba² Mama, sai kace wacce uwarta ta tsine mata duniya ta juya mata baya zan jera sati guda ina cin tuwo, tuwonma ba sabo za'a dinga yi mini ba. “
Mama ta so yin dariya amma ta kanne tace.
"Koma me zaki ce kice, amma wancen tuwon sai kinyi sati kina cinsa a gidan nan tun da ke kunnenki na k'ashi ne ba ya jin magana, bacin sau nawa zance ki daina cika mini kula kina kawo mini d'aki? “
Sai da ta fara turo bakin nan gaba kana tace.
"To kina dai kallo duk ran girkinta sai ta cika kula fam ta kai d'aki, bacin daga ita sai 'yarta d'aya kamar rai, mu kuwa ta milliro mana, ta cikawa Baba da sirikarta kwano, nima kuwa yau na rama na millira musu na millirawa Iya ma, Baba kuwa na cika masa kwano har ya na zuba. “
Salati Mama ta yi ta saki baki ta na kallon Shukhura.
"To don ita ta na cika kula ta kai d'aki ita ta shafa, sune mayunwata ba mu ba, ga shinan yanzu kin sakani a bakin duniya, tijarar Iya ma kad'ai ta isheni, don cewa za tai ina sani na baki girkin shiyasa har ga Allah ban son na bar miki girki na fita. “
"A to don wallahi muddun ni nai girki bazan fasa ciko mana kula na kawo d'aki ba, ko ba za muci ba sai dai mui asararsa. “
"Me kika ce?“
Mama ta tambayeta kasancewar k'asa² tai maganar.
"A'a cewa na yi kiyi hak'uri bazan kuma ba. “
"To zo ki fice mini da kular, kije ki k'ara musu tuwon.“
Ta na jin haka ta saki k'ara.
"Waishhhhhh Mama kashi² ina zuwa ta fice da gudu zuwa ban d'aki, murmushi Mama ta yi a ranta ta na nemawa Shukhura shiriya ta d'auki kular tuwon ta fita, murmushi ma Nusrat keyi tun fara dramar Maman da Shukhura, don dama sun riga da sun saba......



300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
NABABA FADILA SHU'AIB
GTBANK
In kuma katin waya ne ki turo ta wannan layin, shaidarki ta biyama ki turo cikinta.
09037093702.
In katin wayane 400 Za ku biya.


Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki dinga turawa gruop ba, in hakan za kiyi ki sameni a layina muyi magana.





Allah ka k'arawa mahaifanmu lafiya da nisan kwana, Amin.




#Team KTG
#N.W.A
[10/8, 3:42 PM] Binta Lawan: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I. Pls share


*BEBE'ARTH*



Wattpad@Rashuna


*KATANGA*



____________
*THREE*

Ashe ba kallo Shukhura taje ba, can bakin titi taje gurin me saloon ta siyo farata koraye shar da su, ta biya gurin me zob'o ta siyo, ta sayi cewing gum ta jefa a baki sannan ta yo gida, a wani d'an lokon babban tsakar gida ta ajiye faratan da zob'on kana ta shigo.
Sai da ta bari d'aya ta gota ta tabbata a lokacin baccin kowa ya yi nisa ta salallab'a a hankula ta zare sakatar gurinsu ta fice, bayan ta d'auko farar hodarsu, ko tsoron duhun dare ba ta yi, bursuna farar hodar ta yi tun daga fuskarta har wuyanta, ta cire hijabinta sai ta bar wata hula me cibiri cibirin gashi a kanta, rigar jikinta dama ta wani tsohon uniform d'inta na islamiya ne da take bacci da ita.
Cikin dabara ta man manna faratan a yatsunta da chewing gum, ta d'aga jarkar zob'on nan ta shanye ta bar d'an guntu a ciki, nan da nan bakinta ya yi jajir, ta guntsi ragowar a bakinta, turmi ta taka ta zira hannunta ta saman k'ofar d'akin Iya a hankula ta zare sakatar kana ta tura ta shiga ta mayar ta rufe, kallon Iya da ke bacci akan gado ta yi, sakamakon haska 'yar k'aramar cocilan d'in da ke hannunta da ta yi a ranta tace.
'Za ki gane kurenki ne.'
Kan ruwan cikinta ta hau ta zauna, cikin bacci Iya ta ji masifar nauyi ya ziyarceta, a hankula ta bud'e idanuwanta duk a tunaninta madannin dare ne ya danneta, ido biyun da ta yi da Shukhura nan take wani mugun tsoro ya kamata ta bud'e baki za tayi ihu Shukhura ta yi saurin toshe mata baki da wani tsumma da ta yayibo a gefenta, cikin wata iriyar murya me ban tsoro tace.
"Kada ki mana ihu a nan, in ba haka ba zamui daga daga da namanki. “
Nan da nan jikin Iya ya fara rawa kar kar ta fara biya duk wata addu'a da tazo bakinta, son tashi take amma gaba d'aya ta k'asa tashi, hannu Shukhura ta Saka ta karto gefen fuskar Iya had'e da juyar da idanuwanta, rintse ido Iya ta yi kafin ta ji saukar muryar Shukhura a kunnuwanta.
"Al'quran kika kuma tsangwamar Nusrat a cikin gidan nan sai mun cire miki k'afa d'aya da hannu d'aya, mu kuma maidar miki bakinki k'eyarki, sannan mu d'aukeki zuwa cikin ruwa, kima gode Allah kin fara manyanta da wallahi yau sai mun sakaki murmushi da hak'ori d'aya.“
Iya firgita Iya ta firgita, wani mugun tsoro ne ya kuma shiga jikinta ko k'wak'k'waran motsi ta kasa, ta na san magana amman ba dama saboda ta toshe mata baki da t'summa kuma ta rik'e da d'aya hannunta, um umm kawai take ta na girgiza kai hawaye na zuba a idonta, tausayi ta bawa Shukhura don tasan ta sha nauyi, don Iya irin siraran tsofaffin nan ne, ita kuwa Shukhura ta na da jiki, d'agata ta yi ta sauka daga kan gadon ta cire hannunta daga bakinta had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki mana ihu don wallahi zan maidar miki da idonki goshi ki zama mai ido d'aya. “
Ta na maganar ne ta na ja da baya, yayin da Iya tace.
"Allah ya baku hak'uri wallahi na daina takura mata, ba iya ita kad'ai ba ma wallahi dukansu na daina shiga harkarsu.“
Wani ihu Shukhura ta yi ta na zaro harshe ya yin da Iya ta yi wani hantsile ta koma k'arshen gado goshinta ya bugi da bango, duk azabar da ta ratsa ta k'wak'wal warta amma haka ta d'inke bakinta saboda tsoron kar ta yi ihu a maidar mata da idonta goshi, ja da baya Shukhura ta ci gaba da yi had'e da fad'in.
"Kada kuma ki sake ki juyo sai mun b'acewa ganinki in ba haka ba kuma zamui sama da ke zuwa fadar sarkin aljanu. “
Ta na kawowa nan, ta bud'e k'ofa ta fice, ta taka turmi ta maidar mata da sakatar ta, kana ta d'auke turmin ta mayar da shi mazauninsa, sannan ta d'auki hijabinta ta shige ciki, ta na k'ok'arin mayar da sakata ta ji muryar Baba yace.
"Waye nan?“
K'irjinta ta ji ya yi wani irin bugu nan da nan wani mugun tsoro ya kama ta ta fara rawa da bakinta.
"Um nice, fitsari na fito naga kamar ba'a saka sakata ba, shine na duba. “
Ta na kawowa nan ta yi saurin fad'awa band'aki don gudun kada ma ya fito ya ganta.
Fuskarta ta wanke da sabulu, ta cire faratan ta jefa a shadda, kana ta fito ta koma d'aki, sai bayan da ta kwanta a shimfid'arta wata muguwar dariya tazo mata, fashewa ta yi da dariya sosai ta na hango yadda idanuwan Iya suka firfito gaba d'aya kamar na mayyar da aka kama, wata dariyar ta kuma fashewa da ita, Nusrat da ke gefenta ta farka ta na kallonta a tsorace.
'Anya kuwa babu almutsutsai akan Shukhura kuwa. '
Taji zuciyarta ta jefo mata wannan tambayar kafin ta ji muryar Baba ya na k'walo mata kira.
" 'Yar baiwa“
"Na'am Baba. “
Ta amsa, ta tashi ta fita jiki a sanyaye.
"Lafiya kuwa nake jiyo dariya a d'akin ku?“
"Wallahi Baba Shukhura ce, kuma ban san me takewa dariyar ba, anya Baba ba za'a nema mata magani ba, ni wasu abubuwan in ta na yi gani nake kamar ba ita kad'ai ba. “
Murmushi Baba ya yi yace.
"Shukhura. “
"Na'am.“
Ta amsa cikin muryar shagwab'a ta fito ta na sosa kai.
"Me ya sakaki dariya cikin tsohon daren nan? “
Sai da ta fara turo baki gaba sannan tace.
"Kawai tuno yadda na tumur mushi hadiza d'azu a makarantar allo na yi, tsokanar Yayarmu ta yi ni kuwa na had'a mata jini da majina ta mik'e da k'yar jiki duk yai tsami kamanninta duk sun sauya bakin nan kamar zunb'utun zakara. “
Ta kuma fashewa da wata dariyar.
"To jeki ki kwanta, kinga dare ne kada ki kuma dariyar, kinji Mamanmu. “
D'aga masa kai ta yi, ta koma d'aki, ya bita da idanuwa a zuciyarsa ya na nema mata shiriya, duk da a zuciyarsa shima ya fara tunanin ba ita kad'ai bace, don al'amarin nata akwai ban tsoro, shiyasa ya daina dukanta ko me Iya tace tayi mata, don ya san itama Iyan da laifinta, kuma duk irin dukan da zaiwa Shukhuran ba shi zai hana ta samo ta inda za ta rama akan Iya ba.
Duban Nusrat ya yi yace.
"Je ki kwanta 'Yar baiwa, zamui maganar da Mamanku da safe.“
"Toh“
Tace had'e da juyawa ta koma d'akin, ta na kwanciya Shukhura ta rungumota ta baya ta na sakin dariya.
"Ina sonki Yayarmu, matuk'ar ina numfashi bazan tab'a bari a tab'a mini ke ba na k'yale, da a tab'a ki gara ni a tab'a ni. “
Wasu hawaye ne suka zubo a fuskar Nusrat wa'yenda ba ta san dalilin zubowarsu ba, hannu ta saka ta baya ta rik'e hannun Shukhura gam had'e da fad'in.
"Nima ina sonki k'anwata, amma don Allah ki daina fad'a kinji k'anwata. “
"Zan daina, idan har aka daina tab'aki, fatana na saka tsoron ki a zuciyar duk me tab'aki, yadda ko ganinki ya yi sai yai shayin yi miki magana."
Ta na kawowa nan ta kuma rungumota a haka bacci ya d'auketa saboda ba ta da wuyar yin bacci, Yusra da ta farka ta jita ba jikin Nusrat ba ta yi juyi ta shige jikinta, hannu Nusrat ta saka ta na shafa kanta, ta na shafo kan Shukhura da d'aya hannun, har lokacin hawaye na zuba a idanuwanta, ta tabbata hawayen k'aunar da 'yan uwanta suke mata ne, kyakkyawar Katanga mahaifiyarsu ta gina musu a zuciyoyinsu na k'aunar junansu, babu ruwansu da k'yashi ko bak'in cikin anyiwa wani abu a cikinsu ba'aiwa d'aya ba, ta na fatan soyayya da k'aunar da sukewa junansu suci gaba da ita har k'arshen numfashinsu, kada Allah ya bawa wani nasarar rusa katangar alak'ar da take ginanna a zuk'atansu.
Dubanta ta kai ga mahaifiyarsu da ke baccinta cikin kwanciyar hankali, duk abubuwan da suka faru ba ta san anyi ba, kasancewarta me nauyin bacci, shiyasa ko wani abun Baba ke buk'ata a gurinsu sai dai ya k'wallowa Nusrat kira.
A b'angaren Iya kuwa k'wak'wame da bango wani wahalallen bacci ya yi gaba da ita, ba tare da ta shirya zuwansa ba.


Washe gari da safe Nimha da taje kaiwa Iya abincin kari, kasancewar girkin Ummanta ne, anan ta samu Iya da kumburarran goshi, gefen fuskarta a karce.
"Ayya Iya sannu me ya same ki?“
"Ke dai bari 'yar nan, duhun dare ne irin na damuna, na tashi fitsari na nemi cocilan d'ita na rasa nai shahada na fito haka shine na sha k'asa.“
"Ayya sannu Allah ya kiyaye, ga karin kumallon ki nan.“
Cewar Nimha, daga haka kuma ta juya ta fita kafin Iya tace.
"Amin. “
Nimha na zuwa ta gayawa Ummanta abinda ya samu Iya, tab'e baki Umman ta yi had'e da fad'in.
"Wa ya sani ma ko karkashin aljanar yarinyar cen ta kuma kad'awa ta zuba mata, ni ban tab'a ganin tak'adiriyar yarinya irin Shukhura ba, Iya na cewa Nusrat 'yar aljanu ai Shukhura ce 'yar aljanu ba Nusrat ba.“
Maganar da Umma ta yi kaf a kunnen Shukhura suka sauka, wani murmushi ta yi a ranta tace.
'Allah ya had'amu za kwa kiyi kallon tak'adiranci.'
Kowa na gidan sai da ya shiga ya duba Iya, Nusrat da Shukhura a tare suka shiga duba ta, abinda ya bawa Nusrat mamaki ganin Iya ta kirata da Nusrat abinda tsawon rayuwarta ba ta tab'a kiranta da shi ba, sai dai ta kirata da Ai, ba ma za tace Ayshan ba, duk don Malam ya ji haushi.
Sannan kuma har suka fito ba ta sanyata aiki ba, kasancewar duk sanda ta shiga gurin ba za ta fito ba sai ta moreta ko ya ya ne, kuma ta na kallon Shukhura ta na ta sunkui da kai ta na matse dariya, shine da suka koma d'aki ta dubi Shukhuran tace.
"Wai dariyar me kike ta matsewa ne a d'akin Iya? “
"Yo ba dole na yi dariya ba, kinga kuwa goshinta kamar mulmuleliyar daddawa sai shek'i yake. “
Ta fashe da dariyar da ke cinta tun d'azu.
"Allah ban yadda da ke ba Shukhura, duk yadda akai ta dalilinki Iya ta ji ciwon nan. “
" To ni me ta mun da zan saka ta ji ciwo? “
Ta fad'a ta na d'an turo baki gaba.
"Kefe kika ce sai kin saka tsorona a zuciyar duk me takura mini, kuma yau kallon da Iya ta yi mini ya bam bamta da wanda ta ke mini a kullum.“
Rik'o hannuwanta Shukhura ta yi had'e da fad'in.
"Tabbas 'Yar baiwa ce ke Yayarmu.“
Kana ta shiga labarta mata yadda sukai da Iya ta na dariya, murmushi Nusrat ta yi tace.
"Tabbas Iya tai namijin k'ok'ari da ba ta sume miki ba, don in nice wallahi sumewa zan yi, a gaskiya kin d'au hak'k'in 'yar tsohuwa, don ta tsorata sosai tun da gashi ko labarin ainihin abinda ya faru ba ta bayar ba.“
"Wallahi ba wani hak'k'in ta da na d'auka, in hakane ita sau nawa ta na d'aukar hak'k'unanmu. “
Girgiza kai Mama ta yi, a kwance take duk a tunaninsu bacci take, duk abinda Shukhuran ta fad'a ta jishi, kuma ta na nemawa 'yar tata shiriya, don Baba yace da kansa zai dingai mata rubutu ta na sha, don abin nata ya fara yawa duk abinda akai mata tace sai ta rama ko ta halin k'ak'a.
"Kya ci gidanku, bari Babanku ya dawo sai na gaya masa, kuma ki tashi kije yau ke za ki mata shara ki wanke mata band'aki. “
Zunb'uro baki gaba tai ta mik'e, don in ba ta ta shi ba ta san Mama na iya jefo mata duk abinda ke kusa da ita, bayan fitarta Mama ta yi tunanin may be taje ta kumai mata wata muguntar don haka ta shiga k'wala mata kira kafin ta tashi ta bi bayanta.......




300 za ku biya domin samunsa cikin sauk'i.
0567838462
In kuma katin wayane ku turo ta wannan layin, shaidarki ta biya ma ki turo cikinta.
09037093702
In katin wayane 400 zaku biya


Garab'asa gareku masoyana duk wacce ta sayi wannan littafin za ta sami wanda zan rubuta gaba kyauta, ban yadda ki sayi littafina ki

Please Login or Register in order to submit comment