Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma kunya ce take lullubeta domin har lokacin da yake kissing dinta duk ya dauka,

"Lahhh kaga namanta bari inje infadawa Maman amir tafadawa baban amir kadawo.."

"To amma karki dade"

Hijabi ta dauka tafita bata jima ba sai gata tadawo,

Kayan wankin data hada ta nufa zata diba,

"Zo nanah.."

"Yaya yusleem ni kabarni inyi wankin nan"

"Ehh zan barki kiyi, zo kigani"

Fasa diban kayan tayi takoma wurinshi nan suka shashance awurin suna kallon hutananshi wanda ya dauka lokacin yanada arziki kuma yana tsaka da cin daula domin mafi yawansu akasashen turai ne idan yaje sai wadanda yadauka anan gida nigeria tareda mutanenshi ada wadanda suke harka tare wanda mafi yawansu manyan mutane ne kalilanne yara irinshi, haka suka lalace wurin kallon hotunan daga karshema kashe laptop din yayi ya kwantar da ita ajikinshi babu bata lokaci bacci ya kwasheta, ahankali ya zare jikinshi yatashi bayan ya kwantar da ita, kayan yadiba yadauki sabulun wanki ya shiga bathroom, bucket guda biyu ya dauka yafita rijiya ya debo ruwa yadawo yashiga bathroom din ya fara wanke kayan, shi kansa yasan bazai iya tuna ranar da yayi wanki da hannunshi ba sai dai da washing machine,

Kafin Hafsat tatashi har ya gama wankin domin dama bamasu yawa bane, yana cikin yin dauraya sai gata tashigo,

"Yaya yusleem me kakeyi?"

"Daga tashinki?"

Bokitin ta kalla wanda yake dauraye kayan aciki nan idonta yasauka akan kayan baccinta wadanda tasaka shekaran jiya sukayi staining, sannan ga bra guda biyu,Kunyace ta lullubeta ta mika hannu ta janye bokitin,

"Menene haka?" Ya tambayeta yana kallonta,

"Kabarshi inkarasa"

"To ai nagama"

"Ehh katafi dai zan karasa"

Fita yayi yabarta acikin bathroom din takarasa dauraye kayan ta kinkima zuwa tsakar gida wurin igiyar shanya, shanya kayan tayi takoma daki,

"Yaya yusleem wallahi koko da kosai nake sha'awa, zaka sha?"

"Zansha mana"

"A'a idan baka so dan Allah kafada min"

"Wallahi ina so"

Daukar flask tayi da kudi,

"Bari to inkaiwa amir yasiyo mana"

Kai yagyada mata yabita da kallo har ta fice, shi kansa bazai iya fassara yanayin da zuciyarshi ke cikiba gameda ita.

Idanuwanshi ya lumshe nan yaji hannuwanta akan kasumbarshi tana shafawa, bude idonshi yayi ya kalleta,

"Baban amir ne yake magana dakai yana waje.."

"Toh bari inje"

Tashi yayi yafita, yana fita ta dan gyara dakin ta dora ruwan wanka,

Tana fitowa daga wankan yusleem nashigowa cikin dakin rikeda koko da kosan da ta aiki amir ya siyo,

Fita yasake yi domin yabata damar shiryawa saboda yasan indai yana cikin dakin takura zatayi,

Saida ya daidaici cewar tagama shiryawa sannan yakoma, tana zaune tana shafa mai akafarta bayan ta saka kayanta atamfa pink colour riga da zani,

Akusa da ita yazauna, "nima bari inyi wankan ko?"

"To ga ruwan zafin can"

Girgiza mata kai yayi,

"Nida ruwan sanyi zanyi"

"Kai yaya yusleem"

"To aini babu abinda zaiyi min, kece dai zaiyi miki illa idan kika fiya amfani dashi especially ma yanzu da kike period, ku mata idan kuna period anfiso ku yawaita amfani da ruwan zafi sannan ku yawaita shan shi.."

"To ai yanzun ma da ruwan zafin nayi wankan" tace dashi kanta akasa,

"To ki diba kisha idan kin gama"

"Toh.."

Bai sake magana ba ya tashi ya shiga bathroom, maganar Maman amir tajiyo awaje dan haka ta tashi ta fita domin da ita kadai suke yin shiri amma duk sauran matan gidan gaisuwa ce kadai ke hadasu.

Lokacin data koma cikin dakin yusleem yana saka kaya, juyawa tayi zata koma ya dakatar da ita,

"Ina zakije?"

"Waje zanje"

"Me akeyi?"

"Babu komai"

"To dawo ki zauna"

Komawa tayi ta zauna batare da ta kalli wurin da yakeba, har saida ya kammala yazo kusa da ita ya zauna suka fara karyawa,

Abaki yasa mata kosan yana kallonta kawar da kanta gefe tayi tana murmushi,

"Au bazaki ci ba? To ni bani inaso"

Kasa bashin tayi dan haka lokacin data dauko takai bakinta yayi gaggawar rike hannun nata yakai bakinshi maimakon bakinta,

"Nanah wai wannan kunyar duk ta menene uhm...?"

Hannunta nahagu tasa ta kare fuskarta,

"To indai baki saki jikinki kin daina jin kunyata ba zamu bata dake"

Murmushi tayi batace komai ba, da haka suka gama cin abincin duk tana takure,

"Yaushe zamuje kayi askin?"

"Sai dai idan zakiyi min"

Waro ido tayi ta kalleshi,

"Dame?"

"Shaving stick"

Kanta ta cusa cikin pillow tana dariya, binta yayi ya dora kanshi akan bayanta.

Kan keken sakarta tahau tana yin sakar hula shikuma yana kan katifa yana gyara farcenshi da nail cutter,

"Yaya yusleem albishirinka"

"Goro"

"Hula nake saka maka da sunanka ajiki.."


Ajiye nail cutter din yayi yanufi inda take, abayanta ya tsaya yasaka hannuwanshi ya dafe jikin keken sakar bayan ya dan rankwafa yayi mata runfa,

"Shine baki kirani na tayaki ba?"

"To ai baka iyaba"

"Basai ki koya min ba"

Murmushi tayi taci gaba da sakarta yana tsaye yana kallo da haka har ta kammala hada mishi hular wanda ajiki ta rubuta sunanshi,

Karba yayi yasa ya kalleta,

"Dame zan biya?"

"Ni kyauta nayi maka"

"To zo ki kwanta ki huta"

"A'a ba yanzuba saboda maman amir tace inyiwa amir kayan sanyi zata siya mishi"

"To ki dan huta sai kiyi"

Hakura tayi takoma kusa dashi ta kwanta nan kuma yasoma cakulinta, daga ita har shi dariya suke wanda bata taba ganin yayiba sai yau,

Sai yanzu ta tabbatar da rayuwa cikin rufin asiri shi yafi komai dadi fiyeda azauna cikin daula amma babu farin ciki.

Daren ranar ta matsa mishi suje tarakashi aski amma yaki yace itace zatayi masa dole babu yadda zatayi haka ta yadda sukaje shago suka siyo shaving stick suka dawo, candle ta kunna suka shiga bathroom, sabulu ya mika mata bayan ya lumshe idonshi yana jiran yaji tafara......




*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_





*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_



_GAISUWA MAI DUNBIN YAWA GA MASOYAN HAFSAT DA YUSLEEM, FANS NAGODE DA SOYAYYARKU GA ALWASHI....!_



*34*




***Saida ta rintse idanuwanta sannan ta goga mishi sabulun ajikin kasunbar tashi bayan ta shafa ruwa,

Ahankali tasa shaving stick din tafara shaving kasumbar tashi wacce take bala'in burgeta domin itace takara kawata fuskar tashi,

"Nanah tunanin me kikeyi ne kike nema ki hada da fatata..."

Taji muryarshi bayan yarike hannunta, sai lokacin tadawo daga duniyar tunanin data tafi, dan murmushi tayi,

"Babu komai..."

"Ban yarda ba"

"Saboda me?"

"Saboda nasan ba gaskiya kika fada ba"

Cigaba da yimasa shaving din tayi tana murmushi,

"Ohh yaya yusleem.."

"Ohh nanah..."

Dariya tayi, "angama"

"Inji wa?" Ya tambayeta yana shafa habarshi,

"Allah angama ko sai nakawo maka mirror kagani?"

"A'a tunda kince angama shikenan"

Candle din tabar mishi tafita, tana zuwa tsakiyar dakin taga ankawo wuta, ita sai yanzu ma ta tuna da wata wutar nepa domin tunda suka dawo wannan gidan ba ataba kawowa ba sai yau,

Wurin da zasu kwanta ta gyara musu ta shirya ta kwanta,

Maganar yusleem ce tasata dan juyawa ta kalleshi,

"Nanah shine baki fada min ankawo wuta ba?"

"Au dama baka saniba? Ai nazaci kwan ban dakin akunne yake.."

"Inajin dai wutar cikin ban dakin batayi gaskiya.."

Kaya yasaka ya dauki laptop dinshi yajona charge, da Hafsat har ta kwanta amma ganin wuta yasata tashi taje zata dan rage sakar dake gabanta,

"Wai ke bakya gajiya da sakar nanne?"

"Ina gajiya mana, amma yanzun dai ban gajiba..."

"To asauko lafiya.."

"Amin yaya yusleem.."

Kunna laptop dinshi yayi yafara game ita kuma tana kan keke tana sakarta amma dan jefi jefi suna yar hira,

Wata wak'a taji ya kunna yanabi ahankali,

_"Ehh shin yanzu idan kika barni ina zan kwana....,so naki yake tab'a raina, nagane da cewa yanzun so ne asalina,ki aminta dani alkawari mu rikewa juna,inhar nabarki inane zansa kaina,kimin uzuri kome nai sone sanadina,duk mai kaunarki sahibine ni awurina...."_


Shiru tayi tana sauraren yanda yake bin wakar yanayi ahankali cikin muryarsa mai sanyi, da zarar wakar takare sai taji yasake dawo da ita farko yanabi kamar mai yin hadda, murmushi tayi,

"Yaya yusleem dama ka iya waka?"

Rage volume din wakar yayi,

"Ban iyaba amma nakoya saboda wata yarinya guda daya..."

"Lallai...."

"Ina son wakar nan Allah nanah, duk lokacin da nake jinta jinake kamar danni mawakin yayita..."

Murmushi Hafsat tayi,

"To akunna min nima inji mana"

"Gata kiji, na sadaukar miki da ita"

Volume din wakar yakara yanda zata jiyo sosai nan yaci gaba da bin baitikan wakar har takare yasake kunnawa,

Har Hafsat tagama hada rigar da take yiwa amir tataso bai daina jin wakar ba yana kwance laptop din nakusa dashi,

"Yaya yusleem akashe wakar nan haka zanyi bacci.."

"Inkunna mana american film dai mu kalla.."

"To shikenan kunna kafin bacci yayi gaba dani.."

Kwanciya tayi ata bayanshi tadora kanta akan pillow tana kallonshi yana kokarin lalubo film din da zai kunna musu,sai taga yakara kyau saboda gyaran fuskar da tayi mishi, fuskarshi tafito fes sai kyalli take,

Black men shine film din da yasaka musu, juyawa yayi ya kelleta,

"Wannan ai nakare miki bakya gani.."

Janta jikinshi yayi yadauki kanta yadora akirjinshi suka cigaba da kallon wanda yakaisu har karfe 1 nadare sai lokacin bacci yasace Hafsat baima san tayi baccin ba saida yayi magana yaji shiru,

Kashe kallon yayi ya kashe laptop din yasake gyara mata kwanciyarta ajikinshi.


Rayuwarsu haka ta kasance, Hafsat ta hanashi yafita ya nemi aiki idan yayi magana sai tace to me suka rasa ai basu rasa komai ba, shi kansa yasan babu abinda suka rasa din amma wani lokacin yakan zauna yayi tunani tunda bazasu dawwama ahaka ba gashi lokuta da dama kewar maminshi data yan uwanshi tana damunshi domin yana mutukar sonsu sannan ya shaku dasu sosai,

Hafsat koda yaushe cikin kwantar mishi da hankali take tana nuna masa cewar wannan halin da suke ciki shine kadai marufar asirinsu da zarar sun koma wurinsu Mami to asirinsu zai tonu asan abinda yafaru, hakura yayi ya zauna bai fita ya nemi aiki ba koda yaushe suna daki shida ita tana aikin sakarta shikuma yayi musu girki ya kunna wakar da yazamar da jinta kamar ibada , yana bi yana abinda yake yi, hatta sauran matan dake haya agidan sun saka musu ido koda yaushe suka zauna gulmarsu sukeyi wai su jarababbu ne kullum suna daki basa rabuwa kuma baya barin Hafsat tana fitowa,

Da dan kudaden sakar da Hafsat takeyi suke samun na cefane kuma duk da haka suna zaune cikin rufin asiri basu da wata damuwa saita rashin danginsu atare dasu.

Yau tunda safe yusleem da rashin lafiya yatashi domin yajima baije yaga likitansa ba kuma akwai magungunan da yakesha wanda yajima baisha ba shiyasa lalurar ta tashi mishi tun daren jiya amma yayi kokarin boyewa kada Hafsat tagane, haka ya lallaba suke Yar hira sama sama har abin yafara fin karfinsa domin wani zazzafan zazzabine ke yimasa sallama....



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writer_



*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_



_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



_ANTY JIDDA MUSA ahar kullum kedin tadabance agareni,saboda haka ga kyautar page 35 na mallaka miki dan jin dadinki..._




*35*





***Daurewa yusleem yaci gaba dayi bai bari ta fahimci komai ba har tagama shiryawa ta fita kitso wurin maman amir,

Kafin tadawo tuni har zazzabin ya rufeshi, akwance tadawo ta tarar dashi yayi ruf da ciki,

"Yaya yusleem kayi salla kuwa...?"

Shiru taji nan tayi tunanin kodai barci yake yi dan haka ta nufeshi da niyyar tashinshi,

Agaban katifar ta zuba gwiwowinta ta dan kai hannu da niyyar taba jikinshi amma sai tajishi zafi zau,

Cikin rawar jiki ta daddafa shi,

"Yaya yusleem menene? Baka da lafiya? Meya sameka?"

Juyo da kanshi yayi ya bude idanuwanshi wadanda sukayi jajur ya kalleta,

"Nanah cikina ke ciwo gashi zazzabi ya kamani.."

Zama tayi agefenshi fuskarta kamar zata fashe da kuka,

"Sannu yaya yusleem, to yanzu wanne magani zan samo maka? Ko paracetamol zaka sha?"

"Uhmm Kawo min insha to"

Har tatashi sai tadawo ta zauna,

"To ai bakaci abinci ba"

Girgiza mata kai yayi,

"Bazan iyaci ba bana sha'awar kowanne irin abinci, zan dai sha ruwan zafi"

"Yaya yusleem amma da ka daure kaci abincin komai kankantarshi..."

Daga mata kai yayi alamun to saboda ganin yanda tadamu ta daga hankalinta lokaci daya,

Shinkafa da wake da mai da yaji ta zubo mishi dama ita ta dafa tunda safe,

Zaune ya tashi ta gauraya masa shinkafar tasoma bashi, cokali uku kacal yayi ya mike yashiga toilet da sauri nan yafara kwara amai baji bare gani, da sauri tabishi cikin toilet din inda yake aman ta rikeshi, bayan yagama amayar da abincin da yaci dinma bai daina aman ba,

Ruwa ta zuba masa ya wanke bakinshi bayan ya gama, rikoshi tayi suka koma cikin daki hawaye suna zuba daga cikin idanuwanta,

Kwanciya yayi yadan bude idonshi ya kalleta ganin tana hawaye yasashi rikota zuwa jikinsa ya kwantar da ita tareda dora kanta bisa kirjinshi,

"Menene na kuka?"

Shiru tayi bata amsa ba, amma kuma hawayen basu bar fita daga idanuwanta ba,

Kokarin kwantar mata da hankali yayi ta hanyar zame dan kwalin dake kanta,

"Baki nuna min kitson da akayi miki ba..."

Goge hawayen fuskarta tayi tana jinshi yana kirga adadin yawan kitson duk da cewar acikin karfin hali yake yi amma ita tadan ji sauki acikin zuciyarta saboda ganin ya dan ware,

"Kayi salla ne?"

"Banyi ba, dafa min ruwan zafi insha sai nayi alwala saboda naji ruwan kamar da sanyi"

Tashi tayi ta dafa masa ruwan zafin ta zubo masa a cup tasa Lipton da sugar tabashi yasha sannan takai masa wani ban daki ta rakashi yaje yayi alwala yafito,

Kwanciya yayi ruf da ciki bayan ya idar da sallar yaja bargo ya lulluba, tagumi Hafsat tayi tana kallonsa idonta fal fal da hawaye,

Haka suka wuni acikin wannan hali har dare yayi tunda dare yayi kuma bacci yagagari idonsu domin wani irin shassheka yusleem yakeyi kamar wanda yayi gamo, kuka Hafsat tasashi agaba tanayi ga kakarin amai da yaketa yi amma kuma yakasa banda zazzafan zazzabin da yake jikinsa gashi dama throughout yau baici komai ba cokali ukun da yayi ma a shinkafa da waken data dafa saida ya amayar da ita tass ruwan zafi kadai ya iya sha,

Rirrikeshi hafsat tayi tana kuka domin ita bata ma san yanda zatayi ba ganin dare yayi sosai bare tace su tafi asibiti,

Addu'a take ta tofa mishi afuskarshi zuwa can bacci ya daukeshi, lullubarshi tayi tazuba masa ido tana kallonsa, har asubah tayi bata runtsa ba,

Tashi tayi tai salla zuwa can taji kakarin amai alamun yatashi, tashi tayi da sauri taje ta rikeshi,

"Sannu yaya yusleem, sannu..."

Kai yake daga mata har yasamu yadaina kakarin aman,

Ruwan zafin data dora mishi ta je ta sauke ta zuba mishi yayi alwala yayi salla tabashi tea yasha, kwanciya yayi yadora kanshi akan cinyarta jikinsa zau dan zafi,

Bacci taji yasake komawa nan ta zame tatashi taje ta harhado kaf kan kudadenta dake cikin dakin wanda ta lissafasu Dubu goma sha daya ne da dari biyar,

Tagama yanke hukuncin zasuje asibiti idan gari ya waye saboda wannan rashin lafiyar ta yaya yusleem da karfinta tazo idan ba atareta da wuriba gaba sai azo asha wuya,wurinshi takoma ta zauna ta taba jikinshi har lokacin akwai zafi da alama zazzabin bai sauka ba.

K'arfe 9 suka gama shiryawa domin tafiya asibitin,

"Wanne asibitin zamuje?" Yusleem ya tambayeta,

"Private mana yaya yusleem"

"Private akwai tsada nana, muje general"

Girgiza masa kai tayi,

"Yaya yusleem general hospital babu confidential saboda asibiti ne na kowa da kowa yanzu idan mukaje can wallahi sai kowa yasan abinda ake ciki nikuma bana son sirrinmu ya fita amma kaga idan private ne babu ruwan kowa da mu balle har musa ran wani zaiji maganar"

"Shikenan tunda kince haka"

Tashi tayi ta rikeshi yatashi yasa takalmi suka fita, maman amir ta biyosu tana yimusu Allah ya kiyaye hanya,

Sai da sukaje bakin titi sannan suka samu keke napep nan ta tare musu suka shiga suka nufi wani private hospital,

A reception yusleem ya zauna taje ta bude mishi polder dubu biyu sannan za abiya kudin ganin Dr dubu biyar,sannan sai anfara yimishi general test na komai da komai domin ayi saurin fahimtar matsalarshi daga nan sai aturashi wurin likitan da yadace yaganshi dan haka sai ta biya kudin test dubu biyu, duk haka ta biya takoma wurinshi suka nufi laboratory,

Babu bata lokaci akayi masa duk gwaje gwajen da za ayi aka basu result sannan aka nuna musu wurinda zasuje suga likita,

Zama sukayi suna jiran na ciki yafito bayan yafito ta rikeshi suka shiga cikin office din wanda ajiki anrubuta sunan likitan wato Dr Sufyan,

Dan siriri ne likitan baki kyakkyawa yana sanye da bakaken suit da farin glass a idonshi,

Bude sakamakon da suka Kawo masa yayi yaduba kafin yadago yana kallonsu bayan ya cire farin glass din dake idonshi,

"What..." Yafada ahankali yana kallon paper din,

Maida kallonshi garesu yayi, yajanyo wani dan karamin card yafara rubutu,

"Me yasameshi? Tun yaushe ne bashida lafiya? Yana iya cin abinci?,ya kakejin ciwon cikin? Menene yafi yimaka ciwo ajikinka?"

Duk wadannan tambayoyin yusleem ne ya amsasu da kanshi, card din Dr yamika musu bayan yagama rubutun da zaiyi,

"Ok ga wannan kuje pharmacy Ku siyi magani, zai rinka shan guda daya kwal akullum.."

Karba sukayi suka fita, a reception tabar yusleem tatafi pharmacy domin siyo maganin, takardar ta mika domin abata maganin,

"Hajiya kwali daya ko biyu?"

"Abani kwali biyu"

"Ok kudinki yakama dubu dari da sittin"

Idanuwa Hafsat tazaro,

"Dubu dari da sittin?"

"Ehh ai duk guda daya dubu tamanin ne"

"Ok tom ina zuwa bani takardar"

Karbar takardar tayi tafita tanufi office din Dr sufyan, knocking tayi sannan tashiga,

"Madam ya akayi?"

"Dr maganin naje zan siya naji ance wai dubu tamanin ne guda daya"

Gyara farin glass dinshi yayi yanuna mata kujera ta zauna,

"Kin san mijinki gay ne?"

"Ehh nasani likita.."

"To wannan maganin shine kadai maganin da zai rinka sha domin samun lafiyarshi saboda idan bakuyi kokari yasamu maganin nan yana sha ba komai zai iya faruwa dashi,dan haka am advising you kiyi kokari ku mallaki wannan maganin duk tsadarshi.."

"To shikenan likita za asiya insha Allah"

"Ok Allah yabashi lafiya"

"Amin, nagode"

Tashi tayi tafita tanufi wurin yusleem zuciyarta cikeda tunanin inda zataje ta samo kudin domin ita yanzu dubu biyu ne da dari biyu da hamsin kacal awurinta.....



_Fatan alkhairi ga dunbin masoyan ummi shatu wadanda yawansu bazai bari sunansu ya bayyana ba, ahar kullum kuna cikin raina..._






*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



_Kuna ina? Group members na Duniyar makaranta group 1&2 wannan shafin mallakinku ne domin jin dadinku...!_


*36*




***Kafin ta k'arasa wurin yusleem tayi karfin halin tsaida hawayen dake yi mata ambaliya akan kuncinta,

Murmushin karfin hali ta kakaro tayi lokacin da ta isa wurin yusleem,

"Yaya yusleem tashi muje..., anjima zan dawo na sai maka maganin saboda yanzu kudin hannuna bai kai ba"

Kallonta yayi yana jingine ajikin kujerar dake jere acikin reception din,

"Nawa ne?"

"Ka tashi muje kawai yaya yusleem..."

Bai sake yin magana ba yatashi, hannunshi ta rike suka fita, suna fita suka samu keke napep suka shiga,

Lokacin da suka koma gida ruwan zafi kadai ta dafa mishi domin baya iya cin abinci komai yaci sai yayi amansa, tana kokarin fita maman amir ta aiko mata da dan wake,

Kasa zaunawa taci tayi saboda idan har ba kudin nan taje ta nemo ta siyowa yusleem magani ba hankalinta bazai taba kwanciya ba,

Wurin kafintocin da suka siyi kujerunta takoma tasake kai musu tallar dayan kujerun nata na babban falo babu bata lokaci suka tafi gidan taje ta bude musu,

Duk haduwar kujerun nan da kyawunsu amma sai kafintocin sukayi mata tayin wulakanci wai dubu 60 zasu siya, kin siyarwa tayi nan suka kara dubu goma yazama dubu saba'in,ganin kudin basu cikaba yasata fito musu da wani show glass dinta wanda aka zuba mata humra da turaren wuta aciki, dubu goma sha biyar suka siya,

Saida suka fitar da kayan sannan ta rufe gidan tatafi, kai tsaye asibitin da sukaje da yusleem ta koma taje pharmacy ta siyo mishi maganin sachet daya,

Lokacin data koma gidan samunshi tayi yana bacci dan haka ta ajiye mishi maganin ta shiga wanka tafito, harta shirya bai tashi ba sai da ta idar da salla sannan taji motsinshi, juyawa tayi ta kalleshi,

"Sannu yaya yusleem"

"Yawwa, kin dawo?"

"Nadawo lokacin kana bacci.."

Mikewa tayi taje kusa dashi ta zauna,

"Yaya yusleem ga maganin nasiyo maka"

Kallonta yayi bayan ya gyara zamansa,

"A ina kika samo kudin da kika siyo?"

"Yaya yusleem kujerun nan naje nasiyar, lafiyarka yanzu ni tafi min komai.."

Hannunshi ya dora akan nata,

"Amma meyasa kika zabi sayar da kayanki? Ba ga nawa kayan ba wayoyina da laptop dina"

Girgiza masa kai tayi,

"Nawa kayanma naka ne, sannan nasan yanzu aduniya baka mallaki komai ba sai wayarka da laptop wannan dalilinne yasa bazan bada goyon bayan mu siyar dasu ba.."

"Nanah agaskiya ban san da wanne baki zan yimiki.."

Saurin rufe masa baki tayi bata barshi yakarasa ba,

"Inbaka maganin kasha yanzu ko zaka dan ci abincin da Maman amir ta Kawo min?"

"Bazan ci komai ba, bani maganin kawai nasha"

Tashi tayi ta dauko mishi ta hado da ruwa, abin mamaki kwata kwata kwayoyin maganin kwallo 6 ne aciki bamasu wani yawa bane sai dan karen tsada abinda yayi mutukar tayar da hankalin Hafsat,

Saida taga yasha maganin sannan ta dauko dan waken da maman amir takawo mata taci,

Hannu ya mika mata bayan tagama cin abincin ya kwantar da ita akusa dashi, kasa kasa yake yi mata magana suna yin yar hira.

Tunda Hafsat taga yakusa shanye maganin hankalinta yatashi nan tasake komawa wurin kafintoci ta sayar musu da gadajenta gaba daya taje ta siyo mishi magunguna saboda sam bata son ta doshi umminta ko abbanta da lalurar yusleem domin tasan asirinsu yana iya fallasa,

Haka taci gaba da daga kayanta tana sayarwa tana siya masa magani wanda yanzu haka bata da komai domin hatta su fridge dinta da sauran kayan kallonta duk ta siyar ta hada kan kudin ta ajiye wani kuma ta saiwa yusleem magani, yanzu abu dayane ke damunta shine kullum yusleem yana shan magani amma sauki baya samuwa kuma har yanzu baya iya cin abinci sai ruwan zafi gashi kusan 3weeks da zuwansu asibitin,

Sake shiryawa sukayi suka koma asibiti ganin dr sufyan, bayan yagama dudduba yusleem sun kama hanyar fita har sun kai kusa da gate Hafsat ta dakatar da yusleem,

"Yaya yusleem tsaya zo mukoma wurin dr akwai abinda nake son fada mishi"

"To Nana shiga kifito mana, bari injiraki anan"

Komawa office din dr sufyan Hafsat tayi, zaune tasameshi yana rikeda cup yana kurbar tea,

"Madam ya akayi?"

"A'a babu komai likita dama cewa nayi ko zaka sauya mana wani maganin saboda wannan din yayi tsada da yawa kuma har yanzu bai warkeba gashi baya iya cin abinci..."

Tunda tafara jawabi ya kura mata ido baya ko kiftawa har saida ta gama, ajiye cup din dake hannunshi yayi ya dora hannuwanshi akan table,

"Wato madam abinda zaki fahimta shine mijinki dan homo sexual ne wanda kusan lalurar ma taci karfinsa so dole sai magani mai karfi zai rinka sha, wannan maganin ba ako ina ake samunsa ba saboda tsadarshi dan inajin ma gaba daya garin nan baifi chemists guda uku zaki samu ba wadanda suke kawoshi, amma ni zan taimaka miki zan rinka baki maganin free mutukar zaki amince da abinda zan fada miki.."

"Likita ni sassauci nake son kayi mana ka sauya mana wani maganin wanda bai kai wannan tsada ba.."

"To ai madam condition din da mijinki yake ciki yanzu dole irin wannan maganin zai rinka sha,amma ni zan taimaka miki.."

"To nagode dr, nagode madalla.."

"A'a ai ba wani abu bane, zan baki card wanda yake dauke da address din gidana dake cikin G. R. A. Governor road.." Yakarashe maganar yana lasar lips dinshi,

Sai lokacin Hafsat ta fahimci inda maganar tashi ta nufa,

"Dr aini ba yar iska bace sannan banyi kamada matan banza ba wadanda zasu iya cin amanar mazajensu ba..."

Hannu ya daga mata,

"Amma shi mijin naki meyasa yaci taki amanar yaje maza suka bata masa rayuwa? Shifa da maza yan uwanshi ma yarinka alaka,Bari infada miki gaskiya kidaina wahalar da kanki akan mijunki domin situation din da yake ciki yanzu bazai taba kallonki a matsayin mace ba bare har ya iya kusantarki saboda lalurar dake tare dashi, gaba daya bayanshi yakusa lalacewa domin sperm din dake shiga ciki babu

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment