Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar aiki waye yakarba?"

"Malam ilu ne yakarba"

"Yanzu yana ina?"

"To inajin dai acan kauyen madaci yake domin shima yanzu yabar yimusu aiki"

"To baba nagode, idan nasamu lokaci zan dawo, nagode madalla"

"Ah babu komai yarinya, sai kin dawo"

Sallama tayi musu tafita, tana fita matar Malam audu ta dubeshi,

"Malam wannan yarinya da tambaya take? Aba kamar na'urar nasara?" Dariya dukkaninsu sukayi shida ita,

Da fitarta motarta tabude tashiga bata zame ko inaba sai kauyen madaci domin ayau dinnan take son ganin Malam ilu.

Tasha mutukar wahala Kafin tasamu gidan malam ilu, lokacin da tasamu gidan tashiga baya nan yatafi kasuwa sai matanshi da yaranshi, kasuwar tabishi wurin da yake sayar da kayan masarufi,

Acikin rumfarsa ta zauna ta fara gabatar masa da kanta, dukkan tambayoyin da tayiwa Malam audu shi tayi masa yana bata amsa har akazo wurinda take son ji domin tanan ne kadai zata samu saukin binciken da take yi,

"Malam ilu tun lokacin da kake zaune agidansu yusleem baka taba ganinshi da wani hali ko dabi'a wadda take bata gariba?"

"Ehh hajiya gaskiya nidai ban sanshi da wani hali marar kyau ba amma dai wata rana ina cikin falon mahaifiyarsa domin karbar albashi na naji ya bugo mata waya amma banji abinda yaceba nadai ji ita tanata fada tana cewa baya son zama da mata domin wannan itace mace ta goma da ya aura yasaki acikin kasa da shekera biyu... To wannan dai itace matsalarshi ina jin amma bayaga wannan agaskiya ban sanshi da wani mummunan haliba..."

"Nagode baba ilu sai nasake dawowa akaro nabiyu domin da yuyuwar zan kara dawowa"

"Shikenan yarinya Allah yadawo dake"

Sallama sukayi tashiga motarta tafita lokacin misalin karfe 1:30 narana, inbanda yunwa babu abinda takeji saboda ko breakfast batayi ba tafito da sassafe,

Kai tsaye gida tawuce tana zuwa tashiga kitchen tazubo abinci, tana zama hajiya mahaifiyarta nashigowa,

"Hafsat ina kikaje ne yau tun safe?"

Murmushi tayi takalli hajiyarta,

"Hajiya ina wani bincike ne akan wani case da zanyi..."

"To ai ku dama lauyoyi kullum aikinku kenan investigation, bakuda wani batu sai wannan, Allah yabada sa'a amma ina fata case din ba akan kisan kai bane ko maita dan bana sonki da karbar irin wadannan case din domin hatsarinsu yawa gareshi..."

"Bashi bane hajiya amma zanyi miki tambaya, hajiya mutumne yakeda matarsa sai tafara ciwon hauka kuma ance asirine to da yataba auren wasu matan kafin ita, dan Allah waya kamata azarga?"

Shiru hajiya tayi zuwa can tace,

"To zato dai zunubi ne amma babu tabbas ko acikin kishiyoyinne wata tayi mata asirin.."

"Hakane hajiya nima abinda nake tunani kenan amma dai bari zan bincika"

Abincin da take ci ta ajiye tawuce bedroom dinta, wanka tayi tai salla tazura wata bakar doguwar riga tayi rolling fuskarta babu makeup tafito, motar hajiya ta dauka tafita da ita, can tsohon gidansu yusleem tawuce kai tsaye B/Q din gidan tashiga inda malam hassan driver da matarsa Hadiza ke zaune,

Malam hassan baya nan domin har yanzu yana aiki dasu Mami sai matarsa ta samu nan tazauna suka gaisa ta gabatar mata da kanta,

"Malama Hadiza a iya tsawonki da Mami da yusleem mata nawa kikasan ya aura?"

"Gaskiya ban san adadinsu ba amma sunfi goma"

"Kuma duk shi yagansu yana so har ya auresu?" Hafsat ta jefa mata wata tambayar,

"A'a gaskiya duk mahaifiyarsa ce ke wahalar nemo masa"

"To meyasa yake sakinsu?"

"Saboda yace baya sonsu,ita kuma mamin bata hakura har sai ta sake yimasa wani auren"

"Wacece matarsa tafarko?"

"Wallahi namanta amma dai anan garin take"

"Daga cikin matan da ya aura waccece kike ganin kamar tafi sonshi?"

"Gaskiya duk suna sonshi shine dai baya sonsu"

"Zaki iya fada min guda uku daga cikin matan da ya aura?"

"Ehhh zan iya"

"Yawwa nagode"

Tsawon wani lokaci suka dauka suna tattaunawa sannan tayiwa Hadiza sallama tatafi, tana driving tana share zufar datake keto mata duk da cewar ta kunna air condition acikin motar,bata taba yin case mai kalubale irin wannan ba duk da cewar tajima tana yin cases daban daban to amma wannan yazo mata da wani salo daban,

Yanzu tunaninta shine inda zata samu matan da yusleem ya aura abaya domin amsa mata wasu tambayoyi, gida takoma domin magrib tayi, koda taje gidanma bata hutaba kwakwalwarta sai kaiwa da komowa takeyi domin gano ta inda yakamata tafara.

Washe gari gidansu kamal tayiwa tsinke wanda shine kukun da yake dafawa mami abinci, yana daf da zai fita taje,

Bayan tagabatar mata da kanta ne tasoma yimasa tambayoyi,

"Ranki yadade ni babu abinda nasani dangane dasu yusleem domin aikina shine kawai dafa abinci"

Murmushi Hafsat mori tayi,

"To amma kasan matarsa bata da lafiya ko?"

"Kamar yadda nafada miki nifa ban san komai ba"

"To shikenan nagode"

Sallama sukayi tafita tanufi motarta, chamber din Barrister Aminu ta tafi amma koda taje akofar office dinshi tasameshi yana kokarin fita alamun cikin sauri yake,

"Barrister da zuwa nayi kamin wani taimako"

"Gashi kuma barrister kin sameni akan hanya domin wata tafiya zanyi yanzu zanje bayelsa state domin yin wani case kuma gaskiya zanfi 1 month acan, amma abinda za ayi zan hadaki da barrister aiman insha Allah zai baki duk wani taimako kamar yanda zan baki"

Godiya tayi masa takarbi number din barrister aiman din tatafi amma duk jikinta yayi sanyi.

Tsawon 3 weeks ta dauka tana bincike amma har yau bata samu wata matsaya guda daya ba ganin lokaci yana kurewa yasata neman barrister aiman nan ta gayyatoshi gidansu domin bata sanshiba kuma bata taba ganinsa ba,

"Barrister narasa ta yanda zan bullowa case dinnan, wacce shawara zaka bani?"

"Barrister gaskiya case dinki yana bukatar dogon bincike, amma ke wakike suspecting?"

"To ai yanzu barrister kowa ma abin zargine harda ni kaina, yanzu bincike sai yabi takan kowa ciki harda ni, sannan ya auri mata da yawa abaya narasa tayanda zan samosu balle har inyi musu tambayoyi"

Murmushi barrister aiman yayi wanda kyawunsa ya bayyana domin kyakkyawan matashine wanda shekarunsa 32 kacal aduniya,

"Karki damu insha Allah zan taimaka miki, just give me 3 days i will find out duk wani information da muke bukata"

"Nagode barrister"

Hira suka dan taba daga nan yatafi, duk da barrister aiman yayi mata alkawari bata saki jikiba, itama cigaba yin nata binciken tayi cikin sa'a tasamu damar gano mata uku daga cikin matan da yusleem ya aura,

Lokacin da barrister aiman yadawo yazo mata da information masu yawa nan itada shi suka fara bibiyar tushen faruwar rashin lafiyar Hafsat amma sun kasa ganowa har bincikensu yaje karshe yanzu yarage iya gidansu yusleem kadai,sai ko kadan daga cikin matan da ya aura wadanda basu ganosu ba,

Samun barrister aiman tayi cikin sanyin jiki tace,

"Barrister nagama karaya, ina tunanin duk yanda akayi wanda yayi wannan abun nagida ne domin kaga yanzu duk mun gama bincikar kowa amma babu alamun laifi atattare dasu, yanzu kawai gidansu yusleem zanje inji yaushe abun yafaru,suwaye suke gidan alokacin,kai har ma wanda yashiga gidan aranar sai na bincikeshi koda kuwa dabbace.."

Dariya barrister yayi yace,

"Idan kikaje dakanki kuma ai magana ta lalace kibarni nine kawai zanje so sai muyi amfani da hidden camera kirinka ganin duk abubuwan da zamu tattauna dasu"

"Shikenan barrister amma fa ka binciki kukun nan dakyau domin ban yarda dashiba last time ma ni kin amsa min tambayoyi yayi"


Sallama sukayi tatafi, aranar da daddare tana tsaka da shiryawa barrister aiman tambayoyin da zaiwa su mami gobe taji wayarta na kara nan tadauka saboda ganin shine,

"Ansake samun wani information, akwai wata mata da ya aura guda daya bari zan turo miki massage ta whatsapp yanzu"

Katse wayar tayi tajira sakonshi, sunan da matar ke amfani dashi shine Big girl, nan tayi searching dinta a Facebook tayi adding dinta domin da pic da komai nata barrister aiman yaturo kawai matsalar sun rasa sunanta nagaskiya, creating din sabon account na facebook Hafsat tayi acikin wannan daren,

Friend request Hafsat tatura mata nan tayi accepting suka fara gaisawa, kamar yadda suka shirya da barrister aiman haka tayi tanuna mata cewar ita kawarta ce wadda suka dade basu haduba da ta tambayi Hafsat sunanta sai tace sunanta na'ima Abbas ashe kuwa big girl din nada kawa mai wannan suna nan tayita sakin baki suna hira har taturowa Hafsat sabuwar number dinta ta whatsapp,

Tsawon 3 days suna chaten nan Hafsat tafara tambayarta wurin wanne boka take zuwa yanzu, kamar wacce ke jira tafara fada mata cewar a Niger yake amma tabari sai zataje sai su tafi tare kuma abin haushi tun daga wannan rana bata kara ganin big girl ba ko a online gashi wayarta bata shiga,

Barrister aiman tasamu tafadawa yace sujira har big girl din tadawo online nan Hafsat ta girgiza kai tace,

"No barrister gaskiya bazamu jiraba, ni aganina muje office din masu sim din datake amfani dashi tana chat gaba daya atattaro mana chat dinta wanda tayi da kowa da kowa"

"Kuma fa kin Kawo idea barrister, tashi muje"

Office din masu layin da big girl ke amfani dashi sukaje nan aka tattara musu komai aka basu domin tunda sukayi bayanin kansu ma'aikatan suka karbesu hannu bibbiyu amma kuma wani abun mamaki hatta register sim din da take amfani dashi namijne yayi shiyasa babu damar ganin information dinta,

Gida Hafsat takoma tashiga daki tarufe ta nutsu tafara bincikar chaten din big girl daya bayan daya har tazo nakan wani malam Dahiru Niger, nan taga chaten dinsu, daukar number dinshi tayi dasafe takirashi tace kawarta ce ta turota wurinshi yayi mata kwatance zai musu wani aikine, nan yafayyace mata yanda zata ganshi idan tazo Niger, sallama sukayi barrister aiman nazaune yana jinsu daga nan suka fara tsara yanda zata shirya tafiyarta zuwa Niger.

Ajirgi tatafi aranar da taje bata samu ganin Malam Dahiru ba domin yana can maradi, saida ta kwana sannan washe gari tashiga mota tatafi maradi,
Bayan sun gaisa tayi masa bayanin cewar kawarta ce taturo ta akan asirin nan da tasashi yayi yakarya shi nan yarike kai yace,

"Ai nafadawa big girl din shifa wannan asirin bazai karyeba har sai mijin shida kansa shine yakona"

"Ehh tasani shiyasa ma tace kabayar atafi dashi akarya acan"

Tashi yayi suka tafi makabarta domin acan ya binne asirin, acan aka tono asirin yabata,duk abinda ke faruwa akan idon barrister aiman ne wanda ke zaune yana gani ajikin laptop dinshi domin hafsat tana makale da wata yar karamar hidden camera ajikinta,

Tana komawa hotel din data sauka ta tattara kayanta domin dawowa Nigeria saboda jikinta yabata cewar akwai abinda zai biyo baya......



_Gaisuwa da fatan alkhairi ga makiyan Hafsat mori domin nasan bata da fans ni kadai ke yinta..... Lol!_






*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:21AM, 4/16/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*




*ALWASHI....!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_




*64*



***Kamar yadda Hafsat ta zarga hakance kuwa tafaru domin bayan tahowarta daga wurin malam D'ahiru sai ga wayar big girl takirashi da wani sabon layi saboda akwai wani sabon aiki datake son yayi mata cikin kankanin lokaci nan yake sanar mata da cewar kawarta wacce taturo yabata wannan sakon yabata har tatafi nan big girl tayi zumbur tana tambayarsa wanne sako domin ita dai a iya saninta bata turo kowaba, ai kuwa hankalinta ba karamin tashi yayiba lokacin dataji abinda yafada wai asirin da akayiwa matar yusleem tuni takashe wayar tasoma neman mafita, wayar na'ima kawarta takira domin taji ko itace amma koda na'iman ta dauka sai tama nuna ita sam bata san da wannan zancenba, hatta chaten dinsu da maganganun da sukayi a facebook duk na'iman ta nuna bata san anyiba,hankalin big girl kara tashi yayi nan jikinta yabata cewar koma wacece wannan dabara tayi mata ta shammaceta domin tacika nata burin,idan kuwa hakane yazama dole tadauki fansa akan koma wacece tayi mata wannan shisshigin akan yusleem.


Kasancewar Hafsat agarin dake makotaka da jaharsu tasauka daga nan mota tahau zuwa garinsu, ba karamar tafiya suka shaba domin har misalin karfe 10 nadare suna kan hanya, daf da zasu shiga garin yan fashi sukayi niyyar taresu nan drivern yaki tsayawa garin guduwa yan fashin suka harbi tayar motar guda daya nan motar ta nufi cikin jeje taje tarinka bugar bishiyoyi da duwatsu tana dungurawa, sai da mutanen cikin motar suka jigata sannan motar takife, bayan kamar rabin awa da faruwar abun sai ga jami'an tsaro, sune suka dauki su Hafsat zuwa asibiti wanda saida tashafe tsawon kwanaki biyar acan, daga asibitin ta tafi gidansu yusleem amma koda taje sai mai gadi yace basa nan nan ta matsa masa da tambaya har saida ya sanar mata inda suka tafi shine tabiyosu,

Shiru kowa yayi acikin falon bayan Hafsat ta kammala basu wannan labarin,

Cikin sanyin jiki tareda nadamar irin cin mutuncin da suka yiwa Hafsat din dafarko Ummi tace,

"Lallai kin cika yar halak sannan kin cancanci kowacce irin jinjina, amma ni abinda nake fatan sani kuma na matsu da insani shine wacece big girl?"

Ajiyar zuciya Hafsat mori tasauke tana wani tunani acikin ranta, kukan amal ne yacika cikin falon wanda yabawa kowa mamaki banda Khadija dake faman fitar da kwalla tana kuka marar sauti,

"Bayan wannan accident din da nayi, big girl tanata kokarin ganoni domin tadauki fansar abinda nayi mata amma cikin ikon Allah barrister aiman yana bibiyarta shima sannan yana sane da duk wani yunkurinta, har asibitin da nake taje bayan taganoni wanda barrister aiman ne yashirya mata kofar rago har tazo hannu yanzu haka tana can ahannun hukuma domin kotu zamu shigar da ita..."

"Bata fada miki sunanta ba? Ko kuma wacece itaba?" Alh sa'eed yabukata,

"A'a ai ban samu zarafin ganinta ba ma bare har nayi mata interview, munyi magana da barrister dai yace min har yau taki amsa masa ko ita wacece..."

"To yanzu tashi zakuyi muje muganta domin musan ko wacece" inji Mami,

Amal kowa keta kallo wacce tadage sai kuka take, rungumeta Hafsat tayi tana hawayen itama,

"Kiyi hakuri amal ai gashi nasamu lafiya"

"Sister abubuwa da yawa nake yiwa kuka ciki kuwa harda yunkurin rabaki da masoyinki na hakika dasu Ummi sukayi niyyar yi tahanyar aura masa ni, nakanyi kuka mai yawa aduk lokacin da naga irin kulawar da yake baki da irin kaunar da yake yimiki, yau ina cike da farin ciki marar misaltuwa, wannan kukan da kikaga inayi wallahi nafarin cikin kin samu lafiyane zaki koma ga mijinki kuma masoyinki"

"Babu komai amal haka Allah yashirya, ni nasan su Ummi bazasu taba yin abinda zai raba kawunanmu ba ko ya cutar damu ba..." Takarasa maganar tana share hawayen dake kwaranya a idonta,

"Ku hanzarta kutashi mutafi" inji alh sa'eed,

Mikewa sukayi dukkaninsu suka dunguma har hafsat mori, kai tsaye police station suka wuce lokacin da sukaje aka fito musu da big girl, dukkaninsu basu santaba illa Mami da yusleem ne kadai suka santa,

"Rahina....." Yusleem yakira sunanta cike da al'ajabi,

"Yusleem..." Big girl ta amsa tana mai daure fuska,

"Dama kasanta ne?" Hafsat mori ta bukata,

"Ehhh itace matata tafarko da nafara aura wacce aka yimana auren zumunci da ita, cousin dinace"

"Amma Rahina kin bata wayonki, meya kaiki cutar da yarinyar mutane?" Mami tafada idanuwanta fal kwalla,

Ita dai Rahina shiru tayi tana kallon kowa daya bayan daya, Hafsat itama kallonta take saboda ko kadan bata taba ganinta ba,

"Bari naje asibiti" Hafsat mori tafada domin kanta wani irin ciwo yake mata,

"To bari muje mu kaiki" Hafsat ta amsa mata tana kallon yusleem,

Tare suka fita domin mayar da Hafsat mori asibiti, sit din baya tashiga yayinda Hafsat tashiga gaba yusleem yaja motar suka tafi, babu wanda ke magana acikin motar sai da sukayi nisa sannan yusleem ya tambayeta wanne asibiti zasuje nan tafada masa,

Har Room din da aka kwantarta suka rakata daga nan suka fito suka tafi,

Kallon Hafsat yusleem yayi cikeda so,

"Muje gida basai mun koma gidansu ummi ba ko?"

"A'a mu koma kaga munbar su Mami acan"

Murmushi yayi yashafi sajenshi,

"Babu damuwa muje ai yau ango nake"

Murmushin itama tayi batace komai ba har suka koma gida, dukkansu suna cikin falo azaune kamar da farko,

Zama Hafsat da yusleem sukayi domin sun iske su ummi sunata jajanta abinda Rahina tayi wadda shi yusleem dinma yajima da mantawa da ita,

Gyaran murya alh sa'eed yayi yafara jawabi,

"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah, hakika Allah shine abin godiya domin yabawa yarmu lafiya a lokacin da bamu tsanmata ba, agaskiya yusleem kayi namijin kokari sosai wurin jajurcewa har matarka ta samu lafiya, sannan abaya da muka umarceka daka auri yar uwarta bamuyi haka dan fifita wata akan wata ba domin dukkaninsu yayanmu ne, lokacin da tana wannan rashin lafiyar likitoci sun bincika jininta da komai nata ansamu sakamako cewar jininmu ce kamar yadda muka tsanmata domin dama tun asali mahaifiyarsu yan biyu ta haifa amma sai akace daya namijin Allah yayi masa rasuwa aka bamu gawar jariri ashe ba haka bane dayake Allah shine gwanin iya tsara rayuwa sai gashi ya hadamu da yarmu jininmu agidan marayu wanda bamu san waye yakaita canba, koma dai wanene mu yanzu muna cike da farin ciki domin yarmu tadawo garemu kuma tasamu lafiya, Allah yasake hada kanku yabaku zaman lafiya, ke kuma Hafsat kamar yadda kika daukemu a matsayin iyayenki to hakanne mune iyayenki na ainihi...."

Shiru kowa yayi inbanda Hafsat dake hawayen farin ciki,

"Abu yayi kyau Allah yakara tsaremu,Allah yakiyaye gaba, yanzu sai kutashi mutafi" Mami tafada tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,

"Mami kuje kawai ni zamu taho da Hafsat" inji yusleem,

"Haba yusleem kabarta mana zuwa gobe sai arakota"

"Mami gara dai kawai mutafi da ita din"

"Tunda yafiso kutafi taren babu komai ai sai tatashi tashirya kutafi" Alh sa'eed yafada yana murmushi,

Tashi Hafsat tayi tashiga daki amal tabi bayanta tana cemata,

"Sister mijin nan naki yanaji dake, yadamu dake wallahi kirikeshi dakyau karki yi wasa..."

Murmushi Hafsat tayi,

"Amal kenan, insha Allah zanyi yanda kikace"

Yan kayayyakinta tadebo tafita amal na biye da ita, sai lokacin tafahimce cewar Khadija bata nan tun lokacin da sukaje police station kila tatafi gida,shidai yusleem duk sai binta da kallo yake yana jin tausayinta yana shigarsa saboda jin wai agidan marayu ta taso,

Sallama sukayiwa su Ummi suka dunguma zuwa gidan Mami, suna shiga part din Mami sukaga ankawatashi da decoration mai kyau banda kayan cima da kayan sha wadanda aka tanada musamman saboda murnar dawowar Hafsat, kowa baki yasaki yana kallo saboda mamaki sam basu san lokacin da yusleem yasa ayi hakanba,

"Yaya kabamu surprise fa..." Khalifa yafada yana daukar wani biscuit zai ci,

Sury dake rungume da Hafsat cikin murmushi tace,

"Nidai yau nafi kowa murna, yar kwanana tadawo..."

Harara yusleem ya wurga mata, aranshi yace "zakiga yar kwana" afili kuwa sai yace,

"Mami walima nashirya mana ta farin cikin dawowar Hafsat"

Cikin fara'a da so mami takarasa tazauna bayan tadauki cake guda daya,

"Allah yasa albarka, gashi muma zamu ci musha ai..."

Nan walima tafara gudana su Abdul aka kunna music suka fara cashewa tun yusleem yana musu fada yana cewa shifa ba party yashirya ba walima yashirya har yagaji yahakura daga karshe shima yashiga ya dan taka, Hafsat sai dariya take yimasa,

Dakin sury tashiga tayi wanka bayan surayya tawanke mata gashinta domin tasan yusleem ba barinta taje saloon zaiyi ba,

Tana tsaka da shiryawa Sury nayi mata kwalliya yashigo cikin dakin lokacin karfe 5 saura na yammaci,

"Me kukeyi ne haka? Hafsat fito mutafi"

"Ina?" Ta bukata,

"Part dinmu mana"

Hada ido sukayi itada surayya tacikin mirror sukayi dariya,

"Haba ya yusleem, mubari sai zuwa dare mana"

Murmushi yayi yajuya yafita saboda surayya nawurin,

Kasa suka sauko bayan surayya tagama tsarawa Hafsat kwalliya, yusleem sai binta yake da ido kamar yaune yafara ganinta, wata sabuwar walimar ce tasake tashi domin order din kalolin abinci yasake yi daga wani hotel,

Har dare suna shagali sai wurin karfe 9 saura sannan suka fito domin shiga part dinsu, sury ce tabiyosu,

"Yaya inzo intayata kwana?"

Banza yayi da ita yakama hannun Hafsat tareda karata agefen jikinshi suka nufi part dinsu cikin rada rada yace mata,

"Yarinyar nan sury taraina ni saboda taga yanda na matsu inkebe dake shine wai harda tsokanata"

Murmushi Hafsat tayi tare da sake lafewa ajikinsa.....






*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[7:05AM, 4/18/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*


_DEDICATED TO MISS XOXO_



*65*




***Tana rungume agefen jikinshi har suka karasa part dinsu, budewa yayi suka shiga cikin falon wanda yake ta faman tashin kamshi na turaren wuta da sanyayyan air freshener,lumshe idanuwa kawai Hafsat tayi saboda kamshin yayi masifar ratsata ga wani irin sanyi na musamman da ya gauraye falon, idanuwanta alumshe kafin ta farga sai ji kawai tayi yusleem ya ciccibeta, ahankali yarinka hawa steps din har yasamu ya isa falonsu da ke sama, kai tsaye bedroom dinshi yawuce dasu,

Agefen gadonshi ya ajiyeta ya durkusa agabanta yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi wanda idan fassarashi za ayi yanada ma'anoni masu yawan gaske,

Tausassan hannunshi yakai bisa kan nata ya dafe,

"Baby Nanah..."

Kasa amsawa tayi saboda yanda yakira sunan nata yau dabanne da sauran lokutan da yakirata abaya,

"Nanah kinga kaddarar da Allah ya jarrabcemu da ita ko? Amma nasan insha Allah alkhairai ne masu tarin yawa zasu biyo baya ciki harda rayuwa dake da zanyi har abada da kuma yara masu yawa da zaki haifa min..."

Jin abinda yace yasata juyawa dasauri tabashi baya cikeda kunyarshi, tashi yayi yarabu da jikinta ya kwanta abayanta bayan yariko hannayenta,

"Nanah tun dazu tausayinki da tausayin irin rayuwar da kikayi abaya nake tayi, kibani labarin rayuwarki agidan marayu..."

Sai lokacin ta iya yin magana bayan tayi nasarar mayarda kwallar data cika idonta,

"Ya yusleem hakika kaima ka cika dan halas domin amal tabani labarin duk dawainiyar da kasha dakuma ALWASHIN da kadauka nazama dani aduk yanayin da nake ciki, insha Allah nima nadaukar maka ALWASHIN cigaba da rayuwa dakai duk rintsi..."

Katseta yayi ta hanyar mirgino da ita jikinshi, akan ruwan cikinshi ya kwantar da ita yana shafa bayanta,

"Zan iya yin komai saboda ke baby, Allah kadai yasan adadin irin son da nake yimiki acikin zuciyata, i love you..."

Tsabar farin cikin jin abinda yace Hafsat hawayene suka fara zarya akan kumatunta, tashi yayi yana rike da ita yarada mata akunnenta,

"Zo muje muyi wanka muzo muyi shirin bacci ko?"

Kai tadaga masa hakan yabashi damar kokarin fara tubeta, rikeshi tayi,

"Ya yusleem towel dinfa?"

Hannu yamika ya dauko yana murmushi,

Kinkimarta yayi zuwa cikin bathroom din ya kunna ruwa, wanka sukayi da sabulai masu mutukar dadi da kamshi kun san mutumin naku akwai son kamshi shiyasa tuni ya rikice mata,

Sun dauki lokaci mai tsawo acikin bathroom din sannan suka fito yana goye da ita, abakin gado yadireta yajuya ya dauko mata wasu zafafan turare guda hudu sannan yakoma ya dauko mata sleeping gown light purple mai kamada abin tace koko domin bata kauri sam,

"Ya yusleem wannan rigar..."

Zaman da yayi akusa da itane ya hanata karasawa,

"Ai salla zamuyi mu mika godiyarmu ga Allah da baki lafiya da yayi, amma da bacci zamuyi ma basai kin saka ba"

Murmushi tayi takarba cikeda kunya tasaka, shi dinma farar jallabiya yasa bayan yasaka boxer, wurinda yakebe musamman domin yin ibada yajata bayan tasaka katon hijabi nan suka fara sallolin nafila har dare yaraba,

Agogo ya kalla yaga karfe 3 nadare, kallonta yayi ya kama yan yatsun kafarta,

"Nanah tashi muje muyi wata ibadar, wannan ta isa haka.."

Hararar wasa tamishi ta dauke kanta,

"Nifa bacci nakeji kuma nagaji"

"To ai dama gajiyar zan rage miki"

Shiru tayi masa bata kara maganaba nan ya mike tsaye yana rike da ita, kiciniyar cire babban hijabin dake jikinta yashiga yi daga bisani kuma yadireta akan gado,

"Yaya yusleem Allah bacci nakeji"

"Nima haka" yace da ita yana mai lalubar dukkan sassan jikinta, ayanda taga take takenshi yau kam bai hakura har sai ya amsa sunansa na cikakken ango,

Duk da irin lallabatan da yayi da kuma tausayinta da yakeji hakan bai hanata shiga mawuyacin hali ba, zufa ce tarinka karyo mata duk da sanyin air condition din dake ratsa dakin,

Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar asubah lokacin hankalin yusleem yadawo jikinsa, wata runguma mai tsauri yayi mata yana share kwallar dake fita daga idanuwansa wanda shi kansa bai san ko ta menene ba, ita kam Hafsat tuni bacci yayi gaba da ita saboda tarin gajiyar dake tattare da ita.

Tunda tafara bacci bata ko motsa ba sai da karfe 7 tayi, tana kokarin tashi daga kan gadon yusleem yashigo cikin dakin, wani kyau na musamman taga yayi domin ya gyara fuskarshi sosai sannan wani sheki fuskar tashi keyi, yana sanye

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment