Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi suka tasamma kofar fita, shirun itama tayi aranta tana jin wani irin babban lamari agame dashi, jin har suka fita baiyi magana yasata fahimtar yan miskilanci nashi sun motsa,

Har saida sukaje cikin part din mami sannan yayi magana,

"Zo inji cikinki kinci abinci kuwa?"

Zame hannunta tayi tagudu tarigashi shiga cikin falon,

Mami nazaune tana cin tuwon shinkafa miyar lalo,

"Yau hira tayi muku dadi keda khadija, sai yanzu tatafi?" Mami tace tana murmushi,

"Ehh mami.."

"Mami karya take tun dazu khadija tatafi" yusleem yafada lokacin da yake shigowa,harararshi hafsat tayi ita kuma mami tace,

"Kajishi ko taya yasani shida baya nan"

Murmushi hafsa tayi gamida yimasa gwalo,

Tuwon hafsa tazuba yazo yazauna akusa da ita yasa hannu aciki, duk da tasan sun saba cin abinci tare amma saida taji kunyar mami sai dai ita mamin babu ruwanta bata ma san sunayi ba domin ta maida hankakinta akan labaran da take kallo atashar NTA hausa.

Hafsat tariga kowa tashi daga falon saboda ciwon da taji cikinta yanayi, kwanciya taje tayi acikin bedroom,

Daga mami har yusleem babu wanda yakawo wani abu dan haka suka cigaba da hirarsu har wani lokaci, sai wurin 10 sannan mami tashiga dakinta, saida yusleem yabari bayan shigar mami kamar da mintuna 15 sannan shima yatashi yanufi wurin hafsa,

Akwance ya sameta dafe da cikinta zuwa mararta,

"Lafiya?"

Girgiza masa kanta tayi, "cikina ne ke ciwo"

"Da kuma mararki ko?"

Daga mishi kai tayi bayan tarufe idonta, zama yayi yadauketa yadorata ajikinshi yasoma shasshafa mata cikin nata har zuwa mararta ahaka suka raba dare har saida bacci yadauketa sannan ya kwantar da ita shima ya kwanta.

Washe gari tariga shi tashi har ta shirya bai tashiba,

Tana tsaka da fesa turare ya bude idonshi ya kalleta,

"Har kin tashi? Marar taki tadaina ciwo?"

Kai ta daga mishi, "tadaina, naji sauki"

"Har yazo kenan"

Shiru tayi masa,

"Zo inji kamshin wannan turaren saboda wallahi kamshinne yatada ni..."

Ajiye turaren tayi takarasa kusa dashi, cusa fuskarshi yayi ajikinta har na tsawon wani lokaci, dakyar yabarta yatashi yafita,shiryawa yaje yayi yafito yazo tabashi breakfast yaci wanda kusan ma tare suka ci, zama yayi suka fara yin game din temple run awayarshi, saida yajira mami tafito suka gaisa sannan tarakashi zai tafi,motar yabude yashiga bayan yaja hancinta, ramawa itama tayi ta hanyar jan nashi, zama yayi acikin motar yasauke glass yana kallonta, leka cikin motar tayi nan tahango takalmin mata mai tsini ajiye akan kujerar gaba,

Dauke kanta tayi ta daga mishi hannu yaja motar yafice, tunda taga wannan takalmin sai kuma taji hankalinta yakasa kwanciya, wani irin zafi takeji acikin zuciyarta, da wannan takalmin tawuni aranta.

Yusleem kuwa lokacin da yaje gidan alh musa mori samu yayi har angyara mishi tayoyin motarsa an wanke motar tas sai wani sheki takeyi, packing yayi yafito yana kokarin rufe motar yasoma jiyo takun tahowar hafsat domin dama tana tsaye tana sauraren zuwanshi, juyawa yayi,tana sanye da bakar doguwar riga da dan mayafi kamar kullum wannan fitinannen kamshin nata yana yawo acikin iska,

"Barka da zuwa ya yusleem"

Dan murmushin yak'e yayi, "yawwa, ga motar nagode fa,thank you"

Karbar key din tayi ta dan shagwabe fuska,

"Ni ya yusleem kadaina yimin godiya dan Allah, saikace wanda nayi maka wani babban abu?"

Murmushi yayi yajuya yafara tafiya,

"Duk da haka nagode"

Tsayawa tayi tana kallon yanda yake tafiya yasa hannunshi guda daya cikin aljihun wandonshi, akan idonta yashige cikin sashen Alh musa mori....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:10AM, 2/27/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฉ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


_DEDICATED TO MISS XOXO_



*53*




***Tsaye tayi tana kallonsa da murmushi akan fuskarta,har ya bacewa ganinta bata iya yin kwakkwaran motsiba,

Tana nan atsaye har yafito daga sashen mahaifin nata sai lokacin ta dauke idonta daga kallon kofa tamayar kan kyakkyawar silbebiyar wayar dake rike a hannunta,

Har ya nufi motarshi sai yafasa yanufi wurinta,

"Sai yanzu nakula ashe ma angyara min tayoyin..."

Batare da ta dago ta kalleshi ba tayi magana cikin aji da yauki,

"Uhm karka damu.."

"To nagode, bari naje"

"Am bakaji ba, phone number dinka nake so saboda wata rana"

Murmushi yayi, "babu damuwa"

Wayarta ta mika masa ya amsa ya rubuta mata sannan ya wuce, motarshi ya dauka wacce keta faman tashin daddadan abin kamshin da aka saka aciki,

Kansa tsaye banki yawuce wanda kusan acanma yau yabata lokaci domin sai bayan sallar azahar sannan yagama dasu, duk wasu kudadensa wadanda ke hannun alh musa ayau yaturo masa kayanshi sannan zai mallaka masa takardun gonakinsu da na filaye,

K'arfe uku da yan mintuna ya koma gida, iya mami kadai ya tarar afalo tana kishingide tana hutawa, samun wuri yayi yazauna cikeda alamun gajiya atare dashi,

"Ya akayi naganka duk kayi la'asar?" Inji mami,

"Mami wallahi nidinne agajiye nake, yanzu haka daga banki nake"

"Sannu, bari akawo maka abinci"

"To mami, ina yar taki tayi naji banji motsinta ba?"

Dan murmushi mami tayi bayan ta tashi domin Kawo masa abinci,

"Tana ciki inajin bacci ma take yi"

"Lallai tana hutawa"

Murmushi mami tayi bata sake magana ba tawuce dining area ta zubo masa abinci ta Kawo masa, fried rice with chicken salad sai coconut juice mai dan banzan sanyi,

Diban abincin yayi acikin filet ya nufi cikin bedroom din hafsa, tana kwance akan gado tana bacci, agefenta ya zauna yaja babban yasanta na kafa,

Har yagama cin abincin bata motsa ba, yana shirin ja mata hanci yaga tana kokarin yin juyi, riketa yayi nan ta bude idonta ta ganshi,

"A'a yaushe ka dawo?"

"Tunda jimawa, nazo kinata bacci"

Murmushi tayi ta mika masa hannunta yarike ta tashi zaune,

"Yau kadawo da wuri"

"To ai yawon yau bai kai najiya ba"

Murmushi tayi tai shiru saboda tarasa ta inda zata fara,

Ji tayi ya matsa gareta sosai,

"Sai naga kamar akwai abinda kike son fada,hakane?"

Murmushi tayi,

"Hakane amma bana son fada yanzu"

"Saboda me?"

"Saboda kar ka ga kamar banda juriya"

Murmushi yayi yasa hannuwanshi duka ya tallafo kumatunta,

"Bazan yi wannan tunaninba dan haka karki ji tsoron komai fada min"

Shiru tayi tasaki fuskarta ta kawatata da murmushi,

"Dama cewa zanyi har ka mayar mata da motar tata?"

Dan dam yayi jin abinda tace, cikeda mamaki ya kalleta,

"Wacece?"

"Ita wadda ta baka aron motar mana"

Murmushi yayi yasake matsarta,

"Kece kika santa amma nidai ban san wata mai bada aron motaba"

"Ohh dama nima hasashe nayi saboda naga takalminta aciki shiyasa nazaci ko..."

"Ko me? Ni ban san motar ko ta macene ko ta namiji ba saboda nidai kawai bani aro akayi"

Murmushi tayi ta kalleshi,

"To shikenan magana tawuce,kuma har hankalina ya kwanta"

Murmushin shima yayi ya kalleta yana nazarin maganganunta duk da bata fito fili ta fada ma amma yafahimci kishi ne fal zuciyarta saboda takalmin hafsat dataga acikin motar,

"Yanaji kayi shiru?"

"A'a babu komai, kawai dai tunanin fara fita aiki inbarki ke daya nake"

Murmushi tayi, "to basai muna tafiya tare ba"

"Hakama za ayi"

"Ko?" Tace tana murmushi,

"Ehh mana"

Zamewa tayi zata kwanta ya riketa ya langabe Kai, babu yanda ta iya dole sai tare suka kwanta.

Acikin yan kwanakin ya dauketa suka fita ta zazzabo masa kayan sawa nafita office tun daga kan kananan kaya, suit, shaddodi,yadika da takalma, banda turaruka da sauran kayan bukata,

Cikin lokaci kankani yusleem yadawo yusleem dinshi na ainihi dan gaye mai ji da kwalisa,

Wata Lafiyayyiyar mota sabuwa mai tsada yasa aka Kawo masa yasiya saboda zuwa office,

Ranar Monday yafara fita bayan mami da hafsa sunyi masa addu'o'i masu tarin yawa, ciki suka koma bayan sunga tafiyarshi, laptop dinshi hafsat tadauka wacce yabar mata aro tayi game domin debe kewa kafin yadawo,

Tana cikin bedroom azaune tana yin game din wizo taji sallamar khadija,da murna tatareta domin yanzu khadija yar gidace ba bakuwa ba nan suka bude babin hira har hafsat ke sanar da khadija yusleem yafita office,

K'arfe 3 hafsa tashiga kitchen da kanta ta hadawa yusleem abinci, shinkafa da salad da miyar dafaffen kwai,

Shirya masa abincin tayi akan table taje tayi wanka tafito tashirya bayan ta hade jikinta da turaruka masu kamshi,doguwar riga ta atamfa tasa wacce ta tsuke daga kirji sannan ta baje daga kasa,

Yusleem bai samu dawowa gidanba sai karfe 5:30,tana tsaye cikin falo taji kamshin turarensa, cikin nutsuwa da jan hankali tajuya ta kalleshi tana yimasa murmushi, shi dinma murmushin ya aika mata dashi,dauke kanta tayi taci gaba da abinda takeyi har ya karaso kusa da ita, kafadarshi yasa ya bugi tata,

"Babu sannu da zuwa baby nanah..?"

Murmushi tayi ta dubeshi,

"Da akwai mana, sannu da zuwa..."

Hular kanshi yacire yana shafa sumarshi,

"Mami fa?"

"Yanzu tafita, baku haduba?"

"A'a bamu haduba, kuma naji dadin jin hakan domin ko babu komai zan dan sake da ke before tadawo, kima fara shiri mun kusa barin gidan nan.."

"Ko zamu bari amma ai kabari kaje Cairo kadawo tukunna ko?"

Murmushi yayi ya lakuce mata hanci,

"Kafin sannan dinma inada bukatar kasancewar mu mubiyu.."

Kawar da zancen tayi ta hanyar fadin,

"To zo muje kayi wanka sai kazo kaci abinci..."

Bai musa mataba yabi bayanta suka nufi part din da yake, itace ta taimaka masa yayi wanka yashirya cikin kananan kaya bakar t shirt round neck da bakin boxer,part din mami suka koma tazuba mishi abinci tasoma bashi abaki, hannunta yarike cikin nashi yana yin wasa dashi domin har acikin ranshi yana yaba irin kulawar da take bashi batare da nuna gajiyawa ba,

"Baka bani labarin office ba"

Hadiye abincin dake bakinshi yayi,

"Zan baki amma ba yanzu ba sai dare yayi idan munzo yin bacci"

"Kai wai ya yusleem baka da magana sai ta dare"

"To ai lokacin ne nafi samun nutsuwa"

Kawar da kanta tayi ta ci gaba da bashi abincin har ya koshi nan kuma ya kinkimeta ya dorata bisa cinyarshi suka fara buga game,

"Meyasa aka yimiki wannan zip din tabaya? Arinka yimiki tagaba.."

Hannunshi tarike cikeda kunya,

"Ta gaba kuma sai kace wata mai shayarwa..."

Dariya yadanyi ya hade hannuwanshi da nata,

Ahaka mami ta dawo ta iskesu, bayan sallar magrib yakirata wai ta rakashi unguwa, a motarshi suka fita domin zaga gari kawai, basu suka koma gidaba sai 9, kullum haka ce take faruwa kamar doka sai sun fita yawon zaga gari da daddare,

Tuni cikin kankanin lokaci harkokinshi suka soma mikawa suna hababbaka, alh musa kuwa ya maidashi tamkar mahaifinshi domin har mami yadauka taje ta gaidashi, kusan kullum sai yaje gidan saboda yazama tamkar dan gida, hafsa kuwa akullum da tunaninsa take wuni take kwana saboda zuciyarta da ruhinta sun yaba dashi kuma sun aminta da nagartarsa,

Yau kam kasa daurewa tayi dan haka ta kuduri aniyar sanar dashi sirrin dake cikin zuciyarta wanda ya jima yana azabtar da ita,

Waya tayi mishi tace abbanta na son ganinshi domin yau throughout baizo gidan ba, cemata yayi gashi nan zuwa nanda 20 minutes, cikin sauri tafada bedroom dinta tasoma shirin tarbarshi.....




_Fatan alkhairi ga Zarah B~B & Ummu Bashir, yau shafin nakune ku kadai batare da kowa ba...._




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:31AM, 3/2/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*





*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_




*54*



***Sauke manyan idanuwanshi yayi masu mutukar haske akan fuskar hafsa wacce ke zaune tana hada masa green tea,

"Yaya yusleem ina zakaje?" Ta tambayeshi tana juya tea din da spoon,

Kafarshi ya dora akan hannunta dake ajiye yadan taka ahankali,

Yar kara tasaki ta runtse idonta,

"Ahh sorry, zo mugani" yace da ita yana murmushi kasa kasa,

"Ya yusleem Allah da saninka ka takani.."

"Bada sanina bane baby nanah, zo ingani"

Tashi tayi tana yarfe hannun taje wurinshi inda yake zaune agefen gado, riko hannunta yayi ya zaunar da ita bisa cinyarshi yakama hannun yana hurawa,

"Yi hakuri bazan sake ba"

Daga masa kai tayi,

"Ina zakaje? Naji kamar kana yin waya kana zaka fita"

"Ehh ba jimawa zanyiba, gidan alh musa zanje, yau banje na gaidashi ba shine yake nemana"

"Zan bika..."

Murmushi yayi yasoma shafa bayanta,

"Ai nima ba jimawa zanyiba, yanzun nan zaki ganni nadawo"

Makale kafada tayi,

"Nidai ban yarda ba zan bika"

"Kai nanah irin wannan rigima haka, ashe kema rigimammiya ce"

"To kace zakaje dani"

"Bazaki bani tea din bane insha sai yahuce?"

"Lahh mantawa nayi..." Zumbur tayi taje ta dauko masa tea din takawo tazauna a inda tatashi, abaki tarinka bashi yana sha har ya shanye,

Wata mika yayi sannan yasauke idanuwanshi akanta,

"Ga lafiya iya lafiya ga karfi amma sai dai inyita kallonki..."

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi,

"Bawani kallona da kakeyi bayan akwai abunda kake y..."

"Wannan ma ai sake takurani yake idan baki saniba... Danke fa nakeyi, tsaya ma yanzu..."

Yunkurin tashi tagudu tayi yayi saurin riketa yana dariya,

"Daga magana sai gudu?" Yayi maganar yana shafa cikinta daga nan yafara yimata cakulkuli babu shiri tafara dariya tana kokarin kwacewa,

Tashi yayi da ita ajikinsa ya isa gaban drewar, ajiyeta yayi,

"Canja min kaya saboda wannan sunyi kananu da yawa bazan iya zuwa dasu ba"

Wata ash colour din shadda sabuwa fil ta ciro masa, tayashi sakawa tayi taciro masa hula tasa masa, gaban mirror sukaje ta dauki turare ta fesa masa,

"Irin wannan kwalliya haka baby nanah kamar mai shirin zuwa zance?" Yafada yana rungume da ita agefen jikinshi bayan ya kalli mudubi,

"Ina sone duk inda mijina yaje arinka jin yana kamshi kuma aganshi fes fes, nafi son kafi kowanne namiji kyau da kwalliya.."

Murmushi yayi ya manna mata kiss a goshinta,

"Allah yayi miki albarka, Allah yasaka miki da gidan aljanna"

"Amin,muje katafi karka yi dare, dan Allah karka juma"

Sake rungumeta yayi suka fita, har gaban motarshi ta rakashi, saida taga fitarshi sannan ta juya takoma cikin gida.

Yana driving ahankali yana wani tunani acikin zuciyarsa,


Kome yatuna oho sai kawai yadan saki murmushi, yau jinsa yake acikin farin ciki banda nishadin da yake ciki,

Kamar koda yaushe yauma kansa tsaye yatura hancin motarsa cikin gidan yanufi parking space, saida yadan jima acikin motar sannan yabude kofa yafito yana fitowa yashaki daddadan kamshinta wanda ya yakawowa harabar wurin sumame babu bata lokaci ko ina yadauka,

Ahankali take takowa Kwas kwas cikin takunta na hamshakan mata masu ji da aji,

"Barka da zuwa jarumin maza..." Tafada daidai lokacin data karaso gab dashi,

Dan bude lumsassun idanuwanshi yayi ya kalleta, yau wani kyakkyawan leshi purple colour tasa dinkin riga da skirt ta yafa purple din mayafi marar nauyi atakaice dai irin shigarsu tayi ta yaran masu kudi,

"Waye yace miki ni jarumi ne?..." Yace da ita yana kokarin rufe motarshi,

"Ai basai anfada minba domin zan iya tabbatar da hakan batare da wani yafada ba..."

Murmushi yayi yajingina ajikin motar ya zuba hannuwanshi cikin aljihun rigarshi,

"To yau dai na fuskanci tsokana kikeso.."

"Ko daya bahaka bane, gaskiyata dai nafada maka.."

Dan murmushi yayi,

"To yagida lafiya?"

"Lafiya lau, ya aiki?"

"Aiki babu dadi hafsat"

"To ko zaka kawo intayaka?"

Murmushi yasakeyi ya kalleta,

"Me zai hana idan har zaki iya"

"Zan iya mana, ka kawo kagani"

"To shikenan, yanzu dai bari inshiga wurin abba saboda naga idan nabiyeki anan zan bata lokaci"

"To ai abban baya nan, yau baima wuni agari ba..." Tafada tana danyi masa dariya,

"Amma da ai kece kika fada min yana nan"

"To ai son ganinka nake yi kuma nasan idan ba hakan nayiba yau bazan samu ganinka ba bayan kuma ni zuciyata bazata iya jurewa ba"

Idanuwa yazuba mata yana kallonta tsawon mintuna biyu yayinda ita kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da zobunan gold din dake sanye cikin yan yatsunta.

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi magana,

"Sai dai kuma hafsa ban gane abinda kike nufiba.."

Kunyace ta dan kamata har tasa mayafinta ta rufe gefen fuskarta,

"Wallahi har cikin zuciyata naji kana burgeni tun farkon ganin da nayi maka wannan dalilinne ma yasa na kuduri niyyar baka amanar zuciyata.."

Bugun da zuciyarsa keyi yaji ya tsananta batare da yasan dalili ba,

Kafin yayi mata magana wayarshi dake cikin aljihunsa tafara kara, zarota yayi nan yaga hafsat ce,

Cikin sanyin murya ya daga,

"Hello baby ya akayi?"

"Ya yusleem kaje lafiya?" Hafsat tafada daga can bangaren,

"Lafiya lau, yagidan"

"Lafiya, dama mami ce tace ka taho mata da maganin tari idan zaka dawo, nima kuma ina son ka taho min da maganin ciwon mara"

"Toh, dama har yanzu baki warware ba amma kika ki fada min?"

"Saura kadan amma naji sauki, sai kadawo dai"

"Korata kike yi hafsat?"

Jin yakira hafsat yasa hafsat din dake tsaye kusa dashi tayi saurin dagowa ta kalleshi,

"A'a ba korarka nakeyi ba, sai kadawo dai"

"Toh sai nadawo"

Katse wayar yayi ya maida cikin aljihu yayinda hafsat tunani fal yacika zuciyarta banda tarin tambayoyin dake ta faman kai kawo acikin kwakwalwarta,

"Wannan hafsat din da yusleem yakira wacece ita? Meye alakarshi da ita? Wanne matsayine da ita awurinsa? Sonta yake? ...." Wadannan tambayoyin su taketa jerowa acikin ranta har maganar yusleem takatse mata tunani,

"Hafsat am..., bawai fahimtarki ne banyiba, na fahimci abinda kike nufi sannan kuma babu wani namijin da zai ki karbarki a matsayin matarsa, sai dai kuma ni ahalin yanzu inada mata..."

Dagowa tayi da sauri ta kalleshi idanuwanta jajur,

Girgiza mata kai yayi alamun sake jaddada mata abinda yafada,

"Inada mata hafsat, sunanta hafsat"

"To ni yanzu menene makomata da matsayina agareka? Baka sona? Baka kaunata? Bazaka aureni ba?..."

Batare da tajira amsar tambayoyin da tayi masa ba takwasa gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin gida, tana jinshi yana kiranta amma bata tsaya ba,

Yajima tsaye awurin kafin yashiga motarsa jikinsa asanyaye yafita daga gidan, tukin ma kawai yana yinsa ne cikin wani irin yanayi wanda shi kansa bai san abinda ke damunsa ba, a wani chemist ya tsaya yasaiwa su mami magungunan da suka bashi sako sannan yawuce gida,

Kasancewar mami bata jin dadi mura tasakota agaba shiyasa lokacin da yakoma gida bai sameta afalo ba iya hafsat kadai yatarar tana zaune tana kallon wani Indian film kites,

Jiki asabule yazauna akusa da ita ya mika mata maganin ta karba tana kallonsa bayan tahada ledar maganin da hannunsa ta ruke,

Jingina da jikinta yayi ya ajiye kansa bisa kafadarta......



_Gaisuwa mai tarin yawa ga besty na Phertymarh Xarah._




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[4:47AM, 3/3/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฉ *HASKE WRITERS ASSO.*




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*




_DEDICATED TO MISS XOXO_




*55*



***Hular kanshi ta cire tasoma shafa sumarshi ahankali, dan lumlumshe ido yafara yana sake nanuka jikinta domin wani kamshine yake fusgarsa,

"Yaya yusleem lafiya kuwa?" Tace dashi tana rike hannunshi,

"Lafiya lau baby, kamshinki ne yake neman tada min da hankali..."

Saurin juyowa tayi ta kalleshi,

"Meyayi? Ko kamshinsa ne baiyi maka ba?"

Murmushi yayi yadafa kafadarta,

"Easy, ba abinda nake nufi kenanba, tsananin dadin kamshinshi ne ke neman juyar min da kwakwalwa..."

Murmushi tayi ta tureshi ta tashi tanufi dakin mami domin kai mata maganin da yasiyo mata,

Mintuna kadan tafito ta dauki ruwa roba daya tasake komawa, wannan karon ta dan jima sannan tafito, amike taganshi kwance kan doguwar kujera,

Durkusawa tayi akasa ta dora hannuwanta ajikin kujerar,

"Ba yanzu zaka shiga ka kwanta ba?"

Hannuwanta duka ya riko yajata kan ruwan cikinshi,

"Gani nayi kinje wurin mami kinyi zamanki shiyasa na kwanta anan..."

"To ba gashi nafito ba"

Yana kokarin kai hannunta guda daya bakinshi mami tafito,

Tashi hafsat tayi gaba daya kunya tagama lullubeta domin tasan mami tagansu, sum sum tawuce cikin bedroom batare da tayi magana ba,

Zaune yatashi yana kallon mami wacce tawuce dining area batare da ta kalli wurin da yakeba,

Handset dinta yaga ta dauko wanda da alama mantata tayi awurin,

"Sannu mami, yajikin naki"

"Yawwa sannu, dasauki"

Mami tace dashi tareda wucewa bedroom dinta, yajima zaune awurin kafin ya mike ya nufi bedroom wurin hafsat, tana gaban mirror daure da zani tana shafa wasu dadadan turaruka, khalta maryam,da musk altahara,

Ajiye mata ledar maganinta yayi yatsaya kawai yana kallonta,

Juyawa tayi ta kalleshi itama,

"Ya yusleem ya akayi?"

Hannunta yariko cikin nashi yazauna agefen gado ya zaunar da ita ajikinshi,

"Yau basai kinsa sleeping dress ba" yarada mata acikin kunnenta, kunyace ta rufeta, dan dukan kirjinshi tayi ahankali, ta cusa kanta agefen wuyanshi,

"Kaga dazu ma haka kasani naji kunya"

"Da nayi me?"

"Da ka sa mami tazo taganmu mana"

Mikewa yayi ya kwanta ya kwantar da ita ajikinshi yana murmushi,

"Ai ba laifina bane"

"Laifin waye?"

"Laifinki mana"

"Laifina fa kace"

Lumshe idanuwanshi yayi yana sake matseta ajikinshi,

Sun jima ahaka zuwa can bata san meya faruba sai ji tayi ya sassauta rungumar dayayi mata yafada kogin tunani,

Kin bari yayi ta fuskanci cewar akwai abinda yake damunsa nan ya lallabata bacci ya dauketa, kwantar da ita yayi yatashi zaune yayi shiru yana nazari,

Jin zaman ya gundureshi yasashi tashi tsaye yafara kai kawo acikin dakin, sam yau bayajin bacci sannan yarasa dalilinsa na damuwa da lamarin hafsat yar gidan alh musa, haka kuma yana jin wani irin abu mai kamada tausayi tausayi yana yimasa yawo akirjinsa gameda ita,

Kukan da yaga tatafi tanayi shine yafi komai tsaya masa arai,kusanma shine makasudin rashin baccinsa, yarasa ta inda zaibi ya bullowa wannan al'amari domin shi dai ara'ayinsa baida niyyar kara aure, yafi son ya zauna da Hafsat ita kadai ya nuna mata soyayyar da sauran mata basu samuba to amma kuma ita rayuwa kana nakane Allah yana nashi kuma komai mukaddarine daga gareshi,

Bude idanuwanta tayi nan taganshi tsaye yayi shiru abisa dukkan alamu baiyi bacci ba,

Sauka tayi ahankali daga kan gadon tanufi wurinshi, dafa kafadarshi tayi nan yayi saurin juyowa yana kallonta,

"Ya yusleem...., meke damunka? Menene ya hanaka bacci? Tunanin mekakeyi?"

Kago murmushin dole yayi yasa tausasan yan yatsunshi ya kamo nata,

"Babu abinda nake tunani baby nah, baccin ne naji yaki daukata shine kawai nataho nan nake dan zagayawa"

Murmushi tayi ta dan sake yin kasa da muryarta,

"Kafada min gaskiya dai, kodai?"

Murmushin shima yayi mata ya dauketa cak yanufi makwancinsu da ita,

"Kema kindai san idan nace miki bata damuna karya nake yimiki...."

Mayar da fuskarta gefe daya tayi tana murmushi aranta tana tunanin abinda zaije yazo duk ranar da aka tabbatar masa da yagama samun lafiya domin shima taga kamar fitinanne ne,

"Yanaji kinyi shiru?"

"Ehh bacci nake son komawa"

Mirginata yayi takoma kasa yayi pillow da kirjinta, tun tana dan shafa sumarshi har yaji shiru alamun tayi bacci, shikam dakyar yasamu ya iya bacci cikin wannan dare.

Tunda wannan maganar ta shiga tsakaninsu da Hafsat shikenan bai sake ganinta ba koda yaje gidan sai dai kusan kullum yana ganin massage dinta taturo mishi,

Bayan kamar sati biyu da faruwar al'amarin da wani yammaci yaje gidan bayan sun gaisa da alh musa yafito ya hangeta tsaye jikin motarshi tana wasa da key din motarta wanda da alama dawowarta kenan taga motarshi,

Dan hade rai yayi yanufi wurin,

Ganinshi haka yasata yin dan murmushi,

"Ya yusleem menene abin bata ran? Dama kawai tsayawa nayi mugaisa sannan in tambayi lafiyar takwarata da na yaranta"

Batare da yasaki fuskarshi ba yace,

"Tana lafiya"

Bashi wuri tayi ta tsaya tana kallonshi bata kara maganaba yashiga motarsa yafita daga gidan, yana cikin driving yaji karar shigowar text massage,

_Ya yusleem insha Allah sai na aureka kuma zakace nafada maka..._

Cilla wayar kan kujera yayi yaci gaba da driving dinshi bayan yagama karanta sakon.

Akasalance ya karasa gida,babu kowa afalon mami dan haka kai tsaye yawuce cikin bedroom dinta nan dinma bata nan sai lokacin yatuna da cewar baiga motarta ba lokacin da yashigo, dakin hafsat yawuce ita dinma bata ciki, fitowa yayi yana tunanin to kodai tareda mamin suka fita da wannan tunanin yakarasa cikin bedroom,

Zaune yaganta tana goge mishi kananan kayanshi data wanke ta kunna laptop dinshi tana sauraren wakar dayake muradin so wadda kusan koda yaushe sai yajita,

Tsaye yayi yana kallonta yana dan murmushi domin yasan bata san yashigo ba,

Ahankali ya sadada yarufe mata ido da hannuwanshi ai kuwa ta kurma wani uban ihu tana salati,

Dariya ce taci karfinshi ya fada jikinta yanayi bayan ya bude mata idanuwan,

Kashe iron din tayi tahau dukanshi, hada hannayenta duka guda biyun yayi ya rike yana yimata dariya,

"Allah ya yusleem sai nafawa mami abinda kayi..."

"Yi hakuri hafsat, ke dince kika bani dariya sosai"

"To bakaine ka tsorata ni ba"

"To kiyi hakuri, kinga anjima dama ina son ki rakani anguwa"

Fadada murmushinta tayi,

"Tom shikenan, yanzu bari inhada maka ruwan wanka idan ka shirya sai muje kaci abinci"

"To tashi ki hada min"

Tashi tayi tashiga bathroom kafin tafito yayi sauri ya cire kayan jikinshi yabita ciki dole sai tare sukayi suka fito tanata kumbura fuska,

"Shikenan bazan karaba tunda bakya son ladan, kiyi hakuri"

Kin kallonshi tayi yayinda shikuma ya kafeta da nashi manyan idanuwan, bai san daliliba bakar fatarta tana yimasa kyau,

"Gaskiya koda ace mata hudu zanyi to duk bakake zan aura"

Dan harararshi tayi taci gaba da shafa masa mai,

"Kullum kuma sai kaita ganin kala daya babu canji?"

"Ehh mana ai tafi kyau"

Shiru tayi masa takarasa shiryashi takoma shirya kanta, kananan kaya yasa dark blue din

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment