Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


_Dedicated to MISS XOXO_




*5*

aishaummi.blogspot.com




***Ahankali yake ratsawa har zuwa cikin falon mami inda suke zaune itada surayya,

Tunda yaga fuskarta yasan tana cikeda bacin rai,

Zama yayi acikin daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake girke acikin falon,

Tamkar basarake haka yajingina da jikin kujerar ya kishingide,

"Yusleem kana son inyi maka mugun baki..?"

Mami tafada ahasale cikin fada, shiru yayi bai amsa ba hakan yasake tunzurata, cikin tsawa tasake yin magana,

"Ba dakai nake yin magana ba?"

Dan kallonta yayi,

"Mami laifin me kuma nasake yi?"

"Ban saniba, ohhh watonma tambayata kake me kayi? Harma ka manta abinda kayi kenan..?"

Jijjiga kai mami tashiga yi ta maida dubanta ga surayya wacce ke zaune tana jinsu,

"Lallai surayya gaskiyarki ne dole sai an binciki kwakwalwarsa, kinji yanzu wai tambayata yake me yayi, watonma shi har ya manta, dole ka manta mana tunda ka cimin mutunci a idon duniya, sannan ka nunawa duniya ban isa dakaiba, ka cuci yar mutane ka mayar da ita bazawara.."

Nunashi da yatsa tayi,

"To wallahi kaji tsoron Allah yusleem, ina fada maka kaji tsoron Allah domin wallahi bazai barka ba indai kaci gaba da wannan mummunar dabi'ar taka ta auri saki"

"Mami yanzu shikenan anty khadijan tatafi bazata dawoba?" Surayya tayi tambayar tana kallon mami,

"Surayya ai babu macen da za ayiwa irin wannan wulakancin ta yarda tasake dawowa, yayanku bashida hali mai kyau mugun mutum ne.."

Da sauri ya kalli mami, sai lokacin yayi magana,

"Mami muguntar me nayi? Ita khadijan ce tace miki ni mugune?"

Kallonsa mami tayi cikeda masifa,

"Ai basai ta fada minba, kai yanzu acikin halayenka har sai wata tafada min? Acikin halayenka wanne ne bansani ba?

Kai cikakken mugune, miskili, mai shegen tinkahon tsiya da girman kai,

To bari kaji infada maka, komai tinkahon mutum da girman kansa idan yashiga wurin matarsa kaskantar da kansa yake komai sarautarsa da kudinsa, amma kai hatta matarka wannan shegen kasaitar taka da girman kai kake nuna mata.."

Shiru yayi bai sake maganaba, yayinda mami taci gaba da zuba masa fada har saida tayi mai isarta sannan ta sassauta,

"Yusleem nakasa gane damuwarka, tun kana karami kai mutumne mai zurfin ciki, amma ai bakada wanda zaka iya fadawa damuwarka sama dani da na haifeka, idan wani abune yake damunka kasanar dani.."

"Nifa lafiya lau nake mami, babu abinda yake damuna" yabata amsa,

"Karya kake, tayaya zan yarda dakai bayan kana yin abu irin na marassa lafiya, tunda bazaka fada minba to ya zama wajibi agareni inkaika adubaka, yanzu maganar zuwa chairo da nayi maka dazu to harda kai zamuje, zan kaika kaima su bincika min kwakwalwarka agani domin inajin kasamu tabin kwakwalwa a wannan accident din da kukayi da mahaifinku.."

Murmushi yadanyi saboda maganar ta mami dariya taso bashi,

"Mami tabin hankali kuma? Nidin?"

"Kai kuwa, ai ni har yanzu ban tabbatar da cewa kanada cikakken hankali ba har sai kikitoci sun tabbatar da hakan.."

Mikewa yayi domin yunwa yakeji, dining ya nufa nan mami tabishi abaya,

"Kullum kai kenan azuwa cin abinci gidan nan, yanzu da kanada matarka kuma ka riketa da daraja da ba kana can ta hada maka dinner mai ban sha'awa ba"

Baiyi magana ba yaja kujera ya zauna yafara bude flask din dake jere agabanshi,

Surayya ce ta kwaso da gudu,

"Yaya Karka taba wannan nawane.."

Daure fuska yayi yabude flask din, farfesun dankali ne da hanta da kwai da alayyahu yasha curry sai kamshi yake,

Kamar bazaiyi magana ba,daga ido yayi ya kalli surayya sannan ya mayar da dubanshi ga mami,

"Mami zan fasa bakin yarinyar nan.."

"Akan me? Abincinta fa ka taba, da kayi zuciya ka rike aure ka rike matarka hannu bibbiyu ai da duk ba akai ga hakaba" mami tace dashi tana kokarin zuba tuwon accah miyar egusi,

Bai tanka ba ya debi farfesun dankalin acikin flate ya fara tsakura yana ci,

Cigaba da yi masa gugar zana mami tayi shi dai bai kulaba, wannan yana daya daga cikin abinda yasa mami take ganin ba kowacce macece zata iya zama dashi ba domin ko zaka shekara kana yi masa magana sai ya gadama zai amsa idan bai gadama ba har kayi ka gama bazai amsa maka ba, yusleem miskili ne nagaske,ahaka ya karaci cakule cakulen abincin yagama yatashi ya nufi gidanshi wanda ke can wata unguwa daban bata su mami ba.



***

Daga can baya su Hafsat suka tsaya itada amina suna hangen bakin dake fitowa daga cikin motocin da suka zo yanzu,

Wata bakar jeep mai dauke da glasses masu duhu aka bude nan wani matashin saurayi ya fito, yana sanye da suit blue colour da bakin face idanuwanshi sakaye aciki wanda ya karawa fuskarshi haiba,ashekaru bazai wuce shekaru 30 ba zuwa 31,

Dan yatsina fuska yake kamar wani mace ko kuma kamar wanda yaga kashi,

Kallon hafsa amina tayi,

"Hafsat kalli wancan mutumin, yanzu dama aduniya akwai irinshi?"

"Uhm amina kenan, mu ai kinsan muna nan akumshe dan haka baza mu san me duniya take cikiba"

Jin anfara bayani akan bakin nasu da suka Kawo musu ziyara yasasu maida hankulansu can.

Bayani akayi sosai tareda gabatar musu da mutumin da ya jajurce wurin basu gudun mawa akoda yaushe, har akayi aka gama baice ko uffan ba, shugaban gidan marayun ne yayi jawabin godiya a madadin marayun tareda mika wasu tarin bukatunsu wadanda suke son gwamnati tayi musu ko kuma masu hannu da shuni,

Take awurin matashin saurayin Wanda suka sanya masa suna da baya goya marayu yabada gudun mawar naira biliyan goma, yana gama saka hannu ajikin cheque din da yabada yabude motarshi yashiga batare da yatsaya yaji karshen jawabin godiyar da jama'ar wurin keyi masa ba,

Shiru Hafsat da amina sukayi acikin zuciyoyinsu suna tambayar kansu to shi wannan wanne irin mutum ne mai alheri wanda baya bukatar godiya?.





*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI....!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_



*6*




***Suna tsaye suna kallonshi motar tashi ta lula tabar wurin yayinda yan rakiyarsa suka yi hanzarin shiga nasu motocin suka mara masa baya,

"Mutumin nan Allah yasaka masa da alkhairi, dan haduwa ya hadu amma kuma nidai banji dadin yanda ya karbemu ba lokacin da ana gabatar masa damu.." Amina tace da Hafsat tana girgiza kanta,

"To in banda abinki amina mudai ina ruwanmu da yanda ya karbemu,mudai dama taimakonmu kawai muke so yayi kuma yana yi iya daidai gwargwadonsa sannan dama kin san masu kudi ance wulakanci garesu"

"Hakane Hafsat amma kuma ai daraja mutum ma wani abune mai muhimmanci.."

"Kedai amina korafinki kullum baya karewa, dadina dake kenan"

"To shikenan Hafsat nayi shiru.."

Amina tafada tana kokarin jan hannunta.



***

Tunda yashiga cikin lafiyayyen gidan nasa yaja burki acikin kasaitaccen falonsa na alfarma wanda za a iya kira da aljannar duniya,

Kasa zama yayi dan haka ya mike yafara yin sintiri yana kaiwa da kawowa acikin falon nasa,

Yau kwata kwata baya jin barci sannan yasan barcin ma dama bazai zo gareshi ba saboda halin da yake ciki,

Maganar mami ce ta fado masa nacewa zata kaishi domin a binciki kwakwalwarshi,

Shi dai a iya saninsa yasan lafiyarshi kalau bashida wata lalura wacce keda alaka da tabin hankali,

Haka yaci gaba da ire iren wadannan tunane tunanen har dare ya raba, saida yayi sallar asubah sannan yasamu bacci yayi awon gaba dashi,

Misalin karfe 10 daidai nasafe yatashi, wanka yayi ya shirya yafito cikin bakaken suit wadanda sukayi mutukar karbarshi domin rigar da yasaka aciki ja ce shikuma red colour tana mutukar amsarshi,

Fita yayi zuwa wurinda aka tanada musamman domin adana motoci, motocine gasu nan ajere kala daban daban tamkar wurin saida motoci,

Wata dark blue ya bude yashiga yayi mata key yafita daga gidan, kamar ya biya ta gidan mami yayi breakfast sai kawai yawuce batare da yabiya ba domin yasan idan yaje ma fadan dai da take ta yi zata dora daga inda ta tsaya,

Kamfaninshi na sarrafa takalma da jaka ya nufa domin yana da meeting da ma'aikatan company din nan yabata lokaci mai tsawo bashi ya tashi ba sai 5 na yamma dan haka agajiye ya tasamma gidan mami,

Yana tafe yana kokarin cire necktie din dake wuyanshi daf da zai shiga falo su surayya suka fito itada kawarta wacce ta Kawo mata ziyara,

"Barka da zuwa yaya.." Surayya tace dashi lokacin da saka zo daf dashi, ko kallonta baiyi ba bare ya amsa mata sannun da take yimasa,

Dayake tasan halinshi sai ko damuwa batayi ba maimakon hakama sai murmushi da tadanyi ta waiwaya lokacin har yashige cikin babban falon,

"Sury wannan kuma waye?"

Kawar tata ta tambayeta tana dafa kafadarta,

"Wallahi billy brother nane.."

"Au wai dama kinada wani brother din bayan Abdul da khalifa?"

Murmushi surayya tayi,

"Wannan shine first born namu ai sunanshi yusleem"

Kada kai billy tayi tana dan murmusawa,

"Masha Allah, amma duk yafiku kyau, inama ace zaki bani shi.."

"A'a billy bazanyi Fatan ki auri yaya yusleem ba domin daga karshe kawancenmu dake sunanshi kararre"

"Meyasa kikace haka?" Billy ta tambayeta,

"Kedai kawai mubar maganar, idan mun koma school zamu karasa, nidai bazan samu komawa next week ba sai dai upper week"

"To shikenan Allah yakaimu"

Sallama sukayi billy tatafi ita kuma surayya tashiga cikin gida, akan dining ta iske yusleem yana cin abinci,

"Yaya wallahi kayi kasuwa.."

Banza yayi mata yaci gaba da cin abincinsa, bedroom din Mami ta shiga ta fara tsegunta mata maganar kawarta billy, ahaka yusleem yasamesu,

Agefen gadon mami yazauna yadan kishingida,

"Mami maganar visa dinnan inaga kawai kufara shiri domin nanda kwana 4 zata iya zama ready.."

"Allah yakaimu, Allah yayi maka albarka yusleem.."

"Amin mami".


Cikin kwanaki hudu visa tafito suka shirya suka tafi kasar chairo, bincike sosai mami tasa ayi mata a kwakwalwar yusleem dan agano mata abinda ke damunsa, cikin kwanaki 2 likitocin suka kammala sakamako yafito...




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_




*7*

aishaummi.blogspot.com

***Mamaki ne ya kama mami saboda ganin sakamakon dake jikin takardar, wurin surayya taje ta mika mata bayan ta zauna agefenta,

Itama surayyan mamaki ne ya bayyana akan fuskarta ganin wai yusleem lafiyarsa kalau bashida matsalar komai,

"To yanzu mami menene mafita kuma?"

Surayya tayi tambayar tana kallon mamin,

"Surayya mujira tukunna mu koma gida sai asamo mafita"

"To Allah ya kaimu".

Satinsu biyu suka koma gida nigeria, bayan sun hutane mami tasake sakashi agaba ta koro masa jawabi kamar haka,

"Tunda munje asibiti sun tabbatar mana da cewar kwakwalwarka lafiya lau take tofa akwai sauran bincike domin yanzu kuma malamin rukiyya zan samo yazo yayi maka rukiyya ya rabaka da wannan aljanar data aureka.."

Ware ido yayi ya kalli mami,

"Rukiyya kuma mami? Ni me ya hadani da rukiyya kuma?"

"Kai kuwa keda hadi da rukiyya yusleem domin dukkan alamu sun nuna cewar kana tareda aljana..."

"Wallahi mami ni banida wata aljana, lafiyata lau.."

"Ai bazan yarda dakai ba har sai masu bincike sun bincika sun tabbatar"

Mikewa yayi yafita, tun daga nan bai sake komawa gidan ba sai ranar da surayya zata koma makaranta,

Acikin kitchen ya iske mami itada kukunta suna soya dambun kifi da nama wanda surayya zata tafi dashi makaranta,

"Mami barka da aiki.."

Kallonsa mami tayi ta dauke idonta taci gaba da aikinta,

"Sai yau zaka zo gidan? Akan ina nemamaka lafiya shine kuma zaka daina zuwa gidan nan? Yayi kyau"

Shiru yayi baice komai ba dama kuma tasan ba komai din zaice ba,

Wucewa yayi zuwa cikin falo inda surayya take zaune tanata harhada kayanta wadanda zata wuce school dasu,

"Yawwa yaya dama kai nake jira, pls ka bani kudi zan sai phone wallahi kaga wannan din ta fashe jiya ina..."

Bai bari ta karasa ba yayi saurin katseta,

"Nawa kikeso?"

"Yaya duk abinda nasamu"

"Kijira zan turo miki anjima harda kudin karatunki, inyaso idan kikaje can sai kisiya"

"Nagode yaya, Allah yabaka mata tagari"

Wata uwar tsawa ya daka mata,

"Ke....."

Saurin rufe bakinta tayi tai shiru, mami ce ta shigo tana rikeda dambun nama akan flate, yusleem ta ajiyewa agabanshi ta samu wuri ta zauna tana kallonshi,

"Gobe idan Allah yakaimu malamin da zai yimaka rukiyya zaizo zaku fara"

Baiyi maganaba illa idanuwansa da ya tsayar akan tv din dake kafe abangon falon tana aiki,

"Ko bakaji ne? Ina yimaka magana"

"Inaji.."

"Yawwa dan haka gobe da safe inganka agidan nan"

Dambun naman yaja yafara tsakura yana ci har surayya ta kammala shiryawa nan ya daukesu a motarshi itada mami ya kaisu airport, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka dawo gida, bai shiga gidan ba ya juya ya nufi gidansa.

Washe gari kamar yadda mami tace haka ya nufi gidan, lokacin har mai yin rukiyyar yazo, tun aranar aka fara amma shiru babu alamun aljanu atare dashi,

Tsawon kwana 7 aka dauka ana gudanar da rukiyyar amma babu abinda ya canja dan haka malamin yacewa mami daga ranar angama kuma lafiyar yusleem kalau,amma bai saniba ko aljanar kin bayyana tayi,

Shiru mami tayi tai tagumi tarasa abin fada amma har lokacin zuciyarta bata amince mata da cewar yusleem baya tareda aljana ba.

Sallamar malamin mami tayi ta zubawa yusleem ido,

"Yusleem ka fada min abinda ke damunka saboda ni har yanzu jikina yana bani da akwai wani abu"

"Mami babu abinda yake damuna"

"Da akwai yusleem, akwai abinda yake damunka, kafada min gaskiya idan baka da lafiya a matsayinka na d'a namiji?"

Dan sunkuyar da kai yayi yasoma shafa sumar kanshi saboda nauyin da maganar ta mami tayi mishi,

"Mami nifa banida kowacce irin matsala wallahi lafiyata lau"

"To shikenan tunda kafadi haka amma ina son daga yau dinnan kafara duba matar aure domin agaskiya bazan juri ganinka ahaka babu mata ba"

Kallonta yayi amma sai yayi shiru baiyi magana ba domin shi ba kasafai ya fiya son yayita magana ba, nasiha mami tashiga yimasa sai da tayi tagama sannan yatashi ya fita,

Tun daga ranar mami tashiga nemar masa matar aure domin acewarta bata son ganinshi haka babu aure,shikuma tasan ba samowa zaiyi dakanshi ba ko tabashi dama tunda abaya tasha gwada irin hakan amma abun ya faskara.

Cikin sa'a aka samo mata wata yarinya mai hankali Nusaiba yarinyar bazata wuce shekaru 20 ba domin ko jami'a bata shiga ba, duk da iyayenta sunji labarin irin auri sakin da yusleem yakeyi hakan bai sasu yunkurin hanashi aurenta ba domin suna ganin kamar wannan wata damace da suka samu wadda zasu dandani zakin arziki.





*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



*8*



aishaummi.blogspot.com


***Tamkar zaiyi kuka yasa mami agaba yana rokonta akan ta janye maganar auren nan domin bashida burin sake yin aure nan kusa,

"Mami tunda dai sakin nan da nakeyi bakya so, shi yafi komai daga miki hankali to kiyi hakuri kibar maganar auren nan domin bana bukatarsa.."

"Kai ka isama? Ai ko bakaso sai nayi maka wannan auren domin cikar kimarka shine aganka da iyali, haba yusleem wacce irin rayuwa kake son yi ne? Haka kake so inzuba maka ido ka zauna babu mata atare dakai? Ina abinda bazai yuyu ba kenan.."

Bai sake cewa komai ba yaciro wayarshi dake cikin aljihun wandonshi yafara latsawa,

"Aikinka kenan latse latsen waya, babu dama ayi magana ta minti 5 dakai, ai dole ka rasa macen da zata zauna dakai..."

Nan dinma dai shirun yayi baice komai ba, nan mami taci gaba da mita tana tayi shidai yayi shiru har tayi tagama ta tashi takoma bedroom dinta bai sake cewa koda uffan ba,

Yadade zaune acikin falon kafin ya mike ya fita, washe garin ranar yan uwan tsohuwar matarshi khadija suka zo suka kwashe kayanta kaf basu bar koda cokali ba,

Ita kuwa mami shirye shirye nema masa aure taci gaba dayi, tuni har tabada sautin ahado masa lefe tun daga kasar dubai, amma har yau yusleem bai san koda kalar yarinyar da Mami keson aura mishi ba,

Neman auren saida yayi karfi sosai sannan Mami tace ya shirya yaje yaga yarinyar,

Baiyi musu ba yace to zaije amma kuma baije dinba, shiru shiru baije gidansu nusaiban ba har aka wuce sati biyu, kiranshi Mami tayi tace yazo ya sameta,

Lokacin da yatashi daga office yawuce kiran da mamin keyi masa, a falo ya sameta itada sa'ade mai yimata kitso da kunshi domin Mami irin matan nanne yan gayu shiyasa koda wasa bazaka taba cewa itace ta haifi yusleem dinba domin jikinta bai nunaba gayunta ya boye tsufan,

Zama yayi acikin daya daga kujerun falon yazaro wayarshi yasoma latsawa,

Gaidashi sa'ade mai kitso tayi ya amsa dakyar, saida mami ta sallami sa'aden tatafi sannan ta juya ta fuskanceshi.

"Yusleem meya hanaka zuwa wurin matar da zan aura maka? Tunfa rannan nace maka kaje ku gaisa amma shine bakaje ba?

To lallai lallai kaje yau"


"Mami yarinyar shekararta nawane? Tayi 22?"

Girgiza kai mami tayi, "banajin zatafi 20 gaskiya"

"To agaskiya Mami ni tayi min kankanta da yawa, ina laifin ma yar 23 zuwa 25,amma kawai ni akawo min wata karamar yarinya tazo tana yimin yarinta.."

"Kajishi sai kace wani abun arziki yake yiwa matan idan ankai mishi, ina ruwanka da kankantarta? Kaida duk aure auren nan da kayi bana jin akwai mace kwaya daya da zakace kunyi rayuwar aure da ita, duk fa sakinsu kake yi kafin wani abu yashiga tsakaninku..."

Kawar da kanshi yayi bai kalli bangaren da mamin takeba,

"Koba haka bane..?"


"Mami wai sune suka fada miki hakan?" Yafada yana kallon wani wuri,

"Kai kasani dai,nidai kaji abinda nafada maka yau dinnan kaje wurinta ku gaisa"

Bai amsa ba yatsiri danne dannen waya,

"Wai idan ana yimika magana sai ka hau danne dannen waya, kaji abinda nafada?"

"Naji mami..."

"Ba maganar kaji bane, dama ai nasan kaji, so nake ka aikata abinda nasaka, sannan idan kasan kanada matsala ka fada min tunda wuri sai in nemo maka magani..."

Sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi, shi baya son yaji mami tana irin wannan maganar,

"Kaji abinda nace?"

"Naji, mami dan Allah kibar maganar nan nifa lafiyata kalau"

"Yusleem ai dole inyi wannan maganar domin tazama dole, idan ba marar lafiya ba wanne namiji ne za arinka aura masa kyawawan yanmata yazauna yana kallonsu sai ankwana biyu ka sakesu? Nidai har yau ina nan akan bakana nacewar kana tareda aljana dan haka ya zama wajibi inci gaba da nemar maka mafita"

Sajensa yafara shafawa kansa asunkuye idanuwansa akasa,

"Yanzu katashi kaje kaci abinci inyaso sai ka karasa gida ka shirya kaje can gidansu nusaiban"

Tashi yayi yaje yahau kan dining ya dan fara dudduba abubuwan da aka dafa, tuwon shinkafa da miyar ganye ya saka yadan ci ya mike, har lokacin mami na zaune acikin falo, lekata yayi yai mata sallama yafita,

Shi dai adole zaije wurin yarinyar nan, yasan tunda mami takafe akan sai anyi auren nan to ko me zaiyi bazata fasaba ba, da wannan tunanin yashiga cikin gidansa yaje yayi wanka ya shirya,

Kananan kaya yasaka dark blue din t shirt mai gajeren hannu da bakin jeans, fuskar nan ahade babu alamun fara'a,kamshin turaren albahrainil madina ne ke ta faman tashi daga jikinsa,

Saida yayi sallar magrib a masallacin dake kofar gidanshi sannan ya dauki mota yafita lokacin gari yasoma dan yin duhu,

"Mtswwww.." Yaja dogon tsaki, tsakin yayi tayi yana bin kwatancen da mami tayi masa har yasamu ya gano gidansu nusaiba,

Yana hakimce acikin motarshi ya tura yaro ya kirata, gidan yaketa bi da kallo yana daga cikin motar, gidan ba wani babba bane sai dai rufin asiri,

Yana daga ciki azaune ya hango ta tana fitowa daga ciki, kawar da kanshi yayi daga kallonta sannan kuma bai fito daga cikin motar ba har ta karaso,

Glass din motar ya zuge yayi kasa dashi yana kallonta fuska ahade....



*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



*9*



aishaummi.blogspot.com



***Fuska adaure yusleem ke karewa nusaiba kallo aranshi yana mamakin wai shine zai auri wannan yar karamar yarinyar domin shi aduk matan da mami ke aura masa ma babu wacce take kasa da shekaru 23,

Muryar nusaiba ce ta katse masa tunaninsa,

"Ina wuni..?"

Sai da yayi kamar bazai amsa ba sannan ya amsa gaisuwar tata da kyar,

Daga nan yayi shiru itama shiru din tayi domin bata da abin cewa, kallonshi nusaiba keyi yana cikin mota a zaune ita kuma ya barta awaje atsaye saboda tsabar mulki,

Wayarshi ya dauka yafara latsawa zuwa can ya dan kalleta kamar wanda akayiwa dole,

"Sai anjima..."

Glass din motar yayi sama dashi nan ta matsa tabashi wuri yaja motarshi yayi gaba, bin motar da kallo nusaiba tayi acikin ranta tana yaba kyawun siffarshi amma kuma akwai iya tsare gida da dan karen wulakanci nan da nan taji auren nashi ya fice mata arai,

Shikam yusleem tun lokacin da yabar gidansu nusaiba yayi watsi da maganar aurenta domin gaba dayanta bata yimasa ba,

Bai samu zarafin zuwa gidan mami ba sai washe gari da yamma,

Acikin bedroom dinta ya sameta tana yin waya da su khalifa,

Wuri yasamu yazauna akan stoll din mudubinta yana kallonta,

Sallama tayi dasu khalifa ta juya tana fuskantarshi,

"Barka da hutawa mami.."

"Yawwa sarkin taurin kai.., yanzu kai haka dama ake yin zance? Kaje ka tisa yarinya agaba da harara, fuskarka adaure kamar mala'ikan mutuwa.."

Zamanshi ya gyara,

"Mami shiyasa nace maganar auren nan kibarshi kawai, yanzu ahakura da maganar auren wannan yarinyar, ki bani lokaci zanyi miki magana da kaina kuma da kaina zan gabatar miki da yarinyar da zan aura.."

Shiru mami tayi tana dan nazari,

"To yanzu baka jin idan nace afasa iyayenta zasu yimana kallon kananan mutane? Kuma ma duk ba wannan ba, kai dinnan ba tabbas garekaba, nasan ko na baka shekara azuwan ka fito da matar aure ba lallai ne ka iya yin hakan ba"

"Mami kidai bani damar ki gani nidai burina yanzu ki hakura da maganar auren nan wallahi yarinyar nan tayi min karama kofa surayya batayi ba ashekaru.."

"Ehhh to, bari dai sai nayi shawara"

"To shikenan mami Allah yasa ki amince da bukatata.."

"Ai bukatar taka ne bata alkhairi bace amma tunda ka dage zan duba nagani.."

"To mami.."

Mikewa yayi yafita Mami ta rakashi da ido ita yanzu tausayi ma yake bata saboda takamaimai ba asan abinda ke damunsa ba,

Aminiyarta hajiya fa'iza ta Kira wato mahaifiyar khadija matar yusleem tada wacce yasaka,

Shawararta mami ta nema dangane da auren da take nemarwa yusleem, ajiyar zuciya hajiya fa'iza ta ajiye sannan cikin sanyin murya tafara magana,

"Hajiya siyama nidai aganina ki rabuda yaron nan karki sake yimasa wani auren har nan da wani lokaci,

Abinda yasa kikaji nace haka shine, kinga dai nafarko sakin auren da yusleem yakeyi yayi yawa kuma hakan yana haifar da bacin sunansa acikin al'umma sannan kuma suma yaran da yake sakin kinga yana rage musu wata kima da daraja a matsayinsu na yanmata domin koda babu abinda yataba shiga tsakaninsu tofa da zarar ya sakesu sunansu zawarawa sannan iyayensu kamar fa anshiga hakkinsu shiyasa ni nake ganin ahakura da batun auren nan inyaso sai kici gaba da lallabashi har yasamu ya sanar dake matsalarshi..."


Itama mami ajiyar zuciyar ta sauke,

"Hakane hajiya fa'iza, hakika gaskiya kika fadi shikenan insha Allah zanyi yanda kikace"

"Babu komai siyama,Allah dai yabamu mafita"

"Amin ya Allah"

Sallama sukayi mami ta katse wayar, tabbas tasan abinda hajiya fa'iza tafadi gaskiya ne shiyasa ma ta kuduri niyyar zuwa gidansu nusaiba da kanta domin tayiwa iyayenta bayani,


Aranar da yamma taje gidan, lokacin da ta shiga dama ta iske Baban nusaiban da mahaifiyarta sun sakata agaba sai fada suke ta inda suke shiga bata nan suke fitaba saboda tace bazata auri yusleem ba ita tsoranshi takeji,

"Ko zaki mutu kuwa dolenki sai kin aureshi.." Inji mahaifin nusaiba, ganin mami yasa suka dakata daga fadan da suke yiwa nusaiba, nan mami ta sanar dasu anjanye maganar aure amma dukiyar aure wacce aka kai anbar musu,

Bacin rai da tashin hankalin da iyayen nusaiba suka shiga ba kadan bane itada dai mami nan tayi musu sallama tatafi tabarsu da mita.


***

"Hajiya kubra dan Allah ki hakura kidaina kukan nan haka, haba kamar wadda aka yiwa mutuwa? Karfa ki manta tafiya ba mutuwa bace"

Dago da jajayen idanuwanta

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

1 year ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment