Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kujerun tamayar gidan ta rufe ta nufi kasuwa da kudin, komai da tasan zasu bukata na kayan abinci saida ta siya musu, data gama siyayyar kuwa adaidaita sahu ta nema ta zuba kayan yakaita har kofar gida.

Yusleem na kwance agefen katifa bayan ya kammala dafa musu ruwan zafi wanda zasu sha tea sai gata tashigo niki niki da kaya, manyan idanuwanshi yazuba mata,

"Daga ina haka?"

"Ina zuwa yaya yusleem ai zan fada maka"

Tashi yayi ya taimaka mata suka karasa shigo da kayayyakin,

Kudin hannunta ta ajiye ta zare hijabin jikinta ta zauna,

"Yaya yusleem nagaji sosai gashi ina jin yunwa"

"Bari inhada miki tea.."

Kafada ta makale,

"Gaskiya ni bazan sha tea da wannan uban zafinba, tunda ga kayan abinci sai ka dafa min abinci inci"

"To ai baki fada min a inda kika samo wadannan kayan abincin ba.."

"Zan fada maka kafara bani abinci inci tukunna mana"

"Nifa ban iya girki ba sai dai kiyi guiding dina"

"To fara kunna risho din ka mayar da ruwan zafin can ka dora.."

Kamar yadda tace haka yayi, yanayi tana kwatanta mishi har yadafa musu farar taliya yasoya mai,

Acikin filet ya zuba musu yakai gabanta inda take kwance, hannunshi ya mika mata amma sai tayi kamar bata ganiba ta tashi zaune cikeda kunya,

Saida suka gama cin abincin sannan ta fada mishi duk yanda akayi,

"Yanzu ga 10 thousands din wannan alhajin cikon kudin hayarshi idan yazo sai abashi, wannan kuma 9 thousands din sai mu ajiye.."

Rasa abinda zaice yayi yatsaya kawai yana kallonta saboda yasan acikin mata dari dakyar za asamu irinta guda goma, Hafsat tayi masa halacci acikin rayuwarsa, ta rufa masa asiri, tayi sanadiyyar fitarshi daga cikin halaka, gashi tana zaune dashi a lokacin da bashida madafa har tana salwantar da abubuwan data mallaka saboda shi,

"Nanah banida bakin da zan gode miki illah..."

Tashi tayi tabar dakin ta wuce toilet saboda bata son yayi mata godiyar abinda tayi,

Cikin dare ta tasheshi tana makale da cikinta saboda wani irin ciwo mararta keyi mata, riketa yayi acikin duhun da suke yana tambayarta menene,

"Yaya yusleem cikina ne yake ciwo"

"Ciki kuma? Sannu to yi hakuri"

"Bani ruwa insha.."

Ruwa ya Kawo mata takarba tasha takwanta, candle ya kunna yajata jikinshi yadora kanta akirjinshi ya rungumeta yasoma rarrashinta hannunshi yakai kan cikin nata nan tayi saurin ture hannun,

Kwanciya luff tayi ajikinshi sakamakon duk gabobinta ciwo suke yimata, tambayar duniya yayi mata akan tafada mishi abinda yasa mata ciwon cikin amma tayi shiru saboda kunya takeji tace mishi period pain ne,

Ajikinshi ta kwana har asuba tayi sai lokacin tasamu saukin ciwon da marar tata keyi bacci yadan dauketa kwantar da ita yayi ya nufi toilet,

Sai wurin karfe 6 sannan tatashi daga baccin nan tarasa yadda zatayi tana son tafada mishi kuma tana kunya, komawa tayi ta kwanta ta kalleshi,

"Yaya yusleem kira min amir dan gidan maman amir.."

"Meya faru?"

"Aikenshi zanyi.."

"Toh bari naje"

Tashi yayi yafita ita kuma ta rakashi da ido...



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



*31*




****Bai wani jima da fitaba sai gashi yadawo, kusa da ita yakarasa ya tsugunna agabanta,

"Su maman amir din basu bude kofar su ba inaji basu tashiba.."

Gyada mishi kai tayi taja bargo zata lulluba, rike bargon yayi,

"Kitashi kiyi salla mana kafin kisake kwanciya"

Shiru tayi masa tasake yunkurin lulluba, kara maimaita maganarshi tafarko yayi,

"Ba yanzu ba.."

Ganin ta dage taki tashi yasashi rabuwa da ita tasake lulluba takoma barci, gefenta yaje ya kwanta,

K'arfe 8 tafarka ta kalli yusleem wanda ke gefenta akwance,
"Yaya yusleem dubo min ko su Maman amir din sun tashi.."

Tashi yayi yafita jim kadan sai gasu sun dawo tareda amir din,

"Yaya akwai biro awurinka?"

"A'a babu"

"Amir jeka wurin ummanka kace tabani aron biro da yar paper kaji"

Tafada tana ciccije lebenta, fitar amir tasa yusleem komawa wurinta,

"Har yanzu ciwon ne?"

Daga mishi kai tayi,

"To ko asibiti zamuje?"

"A'a"

Shigowar amir yasa sukayi shiru dukkaninsu, karbar takarda da biron tayi tana daga kwance ta rubuta mishi abinda zai siyo mata ta kalli yusleem,

"Yaya yusleem bashi dari biyu acikin kudin nan"

Tashi yusleem yayi yadauko kudin yabashi, sake gyara kwanciyarta tayi ta tukunkuna har amir yadawo kasancewar yusleem yana tsaye bakin kofa yasa amir bashi ledar pad din,karba yusleem yayi ya leka cikin ledar, sai yanzu ya fahimci abinda yake damunta,

Tana kokarin tashi domin yin wanka ya dakatar da ita,

"Tsaya indafa miki ruwan zafi sai kiyi wankan dashi zaki fi jin dadin jikinki"

Komawa tayi tasake kwantawa shikuma ya dora mata ruwan zafin bayan ya kunna risho,

Bathroom yashiga ya dauko bucket yazo ya juye mata ruwan aciki yakai mata cikin toilet tareda sirka mata shi,

"Ga ruwan wankan can nakai miki, tashi kije kiyi"

Dakyar ta tashi tajuya ta dan kalleshi ganin ba ita yake kalloba hankalinsa yana kan ruwan da zai sake maidawa ya tafasa yasata saurin tashi bayan taja zanin wankanta tashige cikin bathroom.


Bata dade sosai ba tafito lokacin har yusleem ya kammala hada musu abinda zasu karya dashi, kallonshi take kasa kasa saboda duk yau atakure take,shi kansa ya fahimci haka shiyasa ma yajuya mata baya bayan ya kwanta bisa katifa,

Ganin baya kallonta yasata dan sakewa tashirya tasaka wata blue din atamfa dinkin riga da skirt wanda dayane daga cikin irin dunkunan da mami tayiyyi mata,

Zama tayi abakin katifa wanda yayi sanadiyyar juyowar yusleem,

"Kin gama?"

"Uhm" tabashi amsa,

Tashi yayi ya debo mata tafasasshen ruwan zafi acikin cup,

"Kisha wannan ruwan zafin zai dan rage miki radadin ciwon da marar taki keyi"

"Ni ba ciwon Mara nakeba ciwon cikine"

Murmushi yayi ya mika mata cup din,

"Ashe dai ke dinma kin iya karya ban saniba, meye hadin period da ciwon ciki? Ai nazaci mahaifa a mara take ba acikin cikiba ko ke taki acikin ciki take?"

Karbar cup din tayi tasoma kurbar ruwan zafin batare da tayi magana ba har saida ta shanye,

"To ga abinci kuma taliya"

Girgiza masa kai tayi ta kwanta babu jimawa sai bacci, rasa abinda zaiyi yayi saboda dama idan tana ido biyu ne suke yin yar hira, shi dinma kwanciyar yayi tun yana yan tunane tunane har bacci ya daukeshi,

Hafsat ce tafara farkawa yanzu taji dadin jikin nata sannan kuma ciwon ma yaragu sosai sai kadan kadan, ganin yusleem din bacci yake yasata zuba abincin ita kadai ta danci tana gamawa yatashi, fita tayi tace mishi zataje wurin maman amir,

Dayake mata babu wuyar sabo tunda taje suke hira da maman amir din kasancewar itama mijinta baya nan dama kuma police ne,

Yau duk taki sakewa ta zauna wuri daya da yusleem saboda kawai yagane abinda ke damunta, da tashiga dakin zata fice takoma wurin maman amir shi kanshi yusleem din ya lura da ita,

Tun azahar da tashiga wurin maman amir sai yamma lis tadawo wannan dinma dan wanka zatayi ne, yana kwance ta shigo taki kallon inda yake tadauki abinda zata dauka tashiga wanka bakar ledar da tasaka pad din data cire da rana taga ya dauke yadora akan window din bathroom din, acikin toilet din tashirya dan haka koda tafito iya kaya kawai tasa tashafa dan mai tagama tafita.

Wasa wasa har karfe 8 nadare tana dakin maman amir saboda ita so take sai yusleem yayi bacci sannan zata koma dakin, shi kuma yau duk kadaici yakeji saboda bata cikin dakin ganin har 8 ta dan gota yasashi fita yanufi dakin maman amir daidai lokacin da aka dan fara yayyafi yif yif alamun ruwa yana daf da tsinkewa,

Abakin kofar dakin yatsaya,ahankali yayi magana,

"Nanah..!"

"Na'am"

Hafsat ta amsa tareda tashi, kallonta maman amir tayi,

"A'a keda wa? Banji magana ba sai ji nayi kawai kin amsa"

"Yaya yusleem ne yake kirana"

"Anya kuwa? Kodai kunnenki ne"

"Wallahi shine, bari inje"

Duk da haka maman amir bata yarda ba saida ta leka nan taga ashe shidinne kuwa yana tsaye akofar dakin,

"Lahh ashe dagaske shine, kinga kuwa ni banji maganarshi ba, mijin naki ne ma ni sai inga kamar baya magana"

"Dama ai nafada miki shine, bari inje, saida safe"

Fita tayi lokacin har ruwan yadan soma karfi, wucewa yayi tabishi abaya, suna shiga daki yajuya ya kalleta,

"Da ban kiraki ba sai yaushe zaki dawo?"

"Sai anjima"

"To ke haka akeyi mata da mijinta kije ki zauna musu adaki tun rana"

"Mijin nata fa baya nan"

"To amma ai ke naki mijin yana nan ko? Shine zaki kama hanya kitafi kibarshi"

Shiru tayi bata amsaba, maimakon ma tazauna sai kawai ta dauki kayan baccinta tanufi toilet, shi yau yarasa wacce irin kunya takeji sam taki sakewa dashi shikuma yafi son tasaki jiki dashi sosai tadaina jin kunyarshi,

Yana nan zaune tafito sanye da rigar bacci wacce tadora zani da hijab akai,

"Ga abinci nan ko zaki ci"

Girgiza masa kai tayi, "Allah nakoshi tun abincin da naci da rana"

Maimakon tazo ta kwanta sai yaga tadauki candle ta tafi kan keken sakarta, nan ta farayi babu ji bare gani, yana kwance yana kallonta har 11 nadare kuma har lokacin ba adauke ruwan da ake tsugawa ba,

Lumshe idanuwanshi yayi yabudesu akanta take zuciyarshi tafara kissima mishi siffarta, baka ce yar doguwa sannan ita ba ramammiya bace kuma bata da kiba can, tanada round face mai dauke da madaidaitan idanuwa sai dan dogon hanci wanda yake daf da dan karamin bakinta, tanada gashin gira sosai da gashin ido haka kuma gashin kanta ma yanada dan yalwa,

Ido ya tsura mata domin ta dade da cire hijabin dake jikinta dan haka daga ita sai wata rigar bacci cotton mai hannun shimi milk colour mai digon fari da ja da baki da pink da blue duk dai kaloli ne aka diddiga ajiki, sai hula mai santsi kalar ruwan siminta dake kanta saboda duk tunaninta yusleem yayi bacci, sakarta takeyi bil hakki da gaskiya tana son ta kammala rigar da tafara kafin ta kwanta bacci gashi har candle din data kunna yakusa cinyewa shiyasa taketa sauri takarasa kafin ya mutu,

Tashi yusleem yayi sadaf sadaf ya nufi wurinta baki yasa ya hure candle din take ya mutu ita kuma ya daukota cak daga inda take zaune, tsorone ya ziyarceta hankalinta yatashi domin bata taba zaton yusleem bane kokarin kurma masa ihu take yayi saurin rufe mata bakinta da hannunshi ahaka suka karasa kan katifa ya kwantar da ita, laluben hannunshi tafara domin tananne kadai zata gane idan shine cikin sa'a ta lalubo zobenshi na azurfa wanda ke sanye cikin babban dan yatsanshi na tsakiya,

Duk da tagane shine gabanta bai daina faduwa ba sannan kuma jikinta bai daina rawaba domin tayi mutukar tsorata,

Pillow yaja yadora kanta akai,cikin maganarshi mai sanyi ahankali yace,

"Ke yau bazaki yi bacci bane?"

Dan matsar da jikinta take kokarin yi amma ya hanata saboda irin yanda ya manne gefen jikinshi da nata domin hatta kanshi yau akan pillown ta yake,

"Yaya yusleem wata riga naso da inkarasa kafin inyi baccin.."

"To kiyi hakuri kibari sai gobe.." Yayi maganar asaitin kunnenta ahankali,

"Amma wallahi kabani tsoro, kaji yanda na tsorata kuwa?"

"Kin zaci wanine yazo saceki?"

"A'a nazaci ko aljanine saboda fa lokaci daya naga candle din ya mutu sannan anyi sama dani.."

Murmushi yayi yaja bargo ya lullubesu,

"Sanyi akeyi ne kuma wallahi inajinsa sosai kekuma kin tafi da dumin kin barni shiyasa na dauko ki"

Shiru tayi saboda kunya bata amsa ba, sarai yagane kunyace ta hanata magana,

Jikinta taji ya shige sosai yadora kanshi atsakiyar kirjinta,

"Yaya yusleem...." Takira sunanshi,

"Na'am nanah.."

"Gaskiya to banda juye juye ka ajiye kanka wuri daya dan wallahi kirjina ciwo yake" tayi maganar cikeda shagwaba kamar zatayi kuka,

Murmushi yayi saboda yagane abinda take nufi,

"Nasani ai, bazan fama ki ba, kiyi barcinki"

Shiru tayi takasa magana,shi dinma shirun yayi amma dai aranshi yana jin cewar kullum haka zai rinka yi mata har tasamu tasake dashi yadda ya kamata,

Saida yaji tayi bacci sannan shima yasamu zarafin yi. Dayake kusan kwana akayi ana ruwa sai karfe 6 harda wani abu ya iya tashi,

Yana zaune bayan ya idar da salla Hafsat tatashi, brush tashiga bathroom tayi tafito ta kunna risho ta dora ruwan wanka,

Sam takasa kallon koda gefen da yake zaune,

"Masak'iya babu magana? Ya saka?"

Murmushine ya subuce mata saboda jin abinda yace sai yanzu tagane ashe shidinma ya iya tsokana,


"Ai wallahi jiya ka tsoratani"

Murmushi yayi yakoma ya kwanta,

"Ke dince ai gani nayi kinfi bawa sakarki muhimmanci fiyeda barcinki.."

Ruwan wankanta ta juye ta dora wani tashiga wanka.

Duk da dai yanata janta da magana amma bata sake dashi ba sosai saboda yanzu har ma tafi jin kunyarshi fiyeda jiya, tashi tayi da niyyar fita zuwa dakin maman amir,

"Ina zakije?" Taji ya tambayeta,

"Dakin maman amir zanje"

"Shikenan to nima bari intashi inleka kofar gida inzauna tunda kema fita zakiyi"

Murmushi tayi tafita, tashi shidinma yayi yasa takalminsa yafita kofar gida wanda bama wai taba fitowa yayiba tun zuwansu unguwar sai yau,

Kan wani dan dutse yasamu yazauna, yana zama ko minti 5 baiyi ba wasu mutane sukazo a mota kimanin su biyar suka kamashi suka saka a mota suka tafi dashi......



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to MISS XOXO_



*32*




**Hafsat tana dakin maman amir bata san abinda ke faruwa ba domin duk tunaninta yusleem yana daki baima fita ko ina ba,

Tajima adakin maman amir kafin ta mike ta nufi dakinsu,lokacin data shiga taga baya nan duk tunaninta ko yana cikin bathroom amma kuma koda ta dan jira yafito sai taji shiru hakan yasata zuwa ta duba nan taga wayam,

"Hmm lallai yaya yusleem kenan wajen yafita da danshin nan baya tsoron sanyi ko..?" Tayi maganar afili tana kokarin gyara bedsheet din dake shimfide akan katifarsu,

Dakin tagyara ta hau keken sakarta tasoma kokarin karasa sakar da tafara yi adaren jiya tanayi tana rera yar wakarta,

"Tunda nai nisa ankirani baza najiba, naki inkosa hidimarka bazan gajiba, bani inlasa Zuma ta sonka bazana ki ba, yau nake taku wata rana baza nayiba...."

Har ta kammala hada sakar nan yusleem bai shigoba, kan katifa tahau ta kwanta domin ta dan huta, tana nan kwance har rana tayi bata farga ba sai jin kiran sallar azahar tayi nanne kuma taji hankalinta ya koma ga yusleem dan haka tatashi ta dauki hijab dinta tafita amma abin mamaki baya nan, bata koma cikin gidan ba ta mike tabi hanyar da zata sadata da bakin titi,har bakin titin taje amma bata ga koda alamarshi ba nan hankalinta yatashi mutuka,

Duk wanda tagani sai ta tsayar dashi ta tambayeshi ko yaga yusleem amma duk wanda ta kwatantawa kamanninsa sai yace bai ganshi ba, kasa komawa gida tayi taci gaba da tafiya tana nemanshi amma har yamma tayi bata ganshi ba,

Gidan tasake komawa wai ko bayan fitarta yadawo amma yanda tatafi tabar dakin haka tadawo ta iskeshi, hankalinta atashe tana kokarin sake fitowa daga cikin dakin sai ga maman amir tashigo rikeda wani kwano wanda takawo mata alalan gwangwanin data dafa,

"A'a ko fita zakiyi..?"

"Maman amir yaya yusleem ne ban ganiba tun safe lokacin da nabaro dakinki baya nan.." Tayi maganar hawaye na gangarowa akan kumatunta,

"Kodai wani wurin yatafi?"

"Da wani wurin zaije ai da zai fada min, wallahi ina jin saceshi akayi saboda tun safe nake nemansa ban ganshi ba"

"Sacewa kuma? Sai kace wani karamin yaro"

"Wallahi kila saceshi akayi saboda dama yanada wadanda ke nemanshi, gashi kuma sun samu dama sun daukeshi watikil ma su kasheshi..."

Jin abinda Hafsa tace yasa maman amir zaro ido, ajiye kwanon hannunta tayi ta kalli Hafsa,

"Kinga to zo muje ga Baban amir can yadawo yarakaki division dinsu kikai report.."

Bin bayanta Hafsat tayi tana aikin sharar kwalla, maman amir ce ta yiwa mijin nata bayani daga nan yadauki Hafsat din abayan babur dinsa suka tafi office dinsu,

Dukkan wani bayani da ake bukata kuma ya kamata aji Hafsat tafada nan yan sandan sukace tayi hakuri takoma gida zasu yi iya kokarinsu insha Allah,

Tun a police station din take kuka har suka koma gida, gaba daya dakin yayi mata kunci, maman amir ce ke tare da ita take bata baki,

Tunani Hafsat tayi kodai taje tafadawa Mami abinda ke faruwa saboda kar nan gaba mamin ta rinka ganin kamar itace tayi sanadiyyar salwantar yaronta,

Wani sabon kuka tasake fashewa dashi jin har mangariba tayi amma yusleem bai dawoba, yanda tatashi tun safe bata sakawa cikinta komai ba har yanzu takasa shan koda ruwa babu abinda yake cikinta sai iya ruwan zafin da tasha da safe, idanuwanta kamar jan gauta saboda uban kukan data sha,ita addu'ar da take Allah yasa kar su kasheshi.

Tana zaune ita kadai acikin duhu bayan maman amir tatafi misalin karfe 10:30, taji motsin mutum, zaune tatashi cikin dasasshiyar muryarta tayi magana,

"Waye...?"

Kamar acikin mafarki taji muryar yusleem,

"Nanah..."

Zabura tayi ta nufeshi acikin duhun,

"Yaya yusleem"

"Na'am.."

Rungumeshi tayi ta kankameshi, shi dinma rungumetan yayi,

"Yaya yusleem ina katafi tun safe? Kasa duk hankalina yatashi.."

Daukarta yayi zuwa bakin kafita ya zauna yadorata ajikinshi gaba daya ma ita ta manta da cewar akwai wata aba wai ita kunya sai shisshigewa jikinshi take,

"Yi hakuri kinji, kuka kikayi ne naji muryarki ta dishe?"


Kwantar da kanta tayi bisa kirjinshi,

"Haba yaya yusleem ba dole inyi kukaba, tun safefa nake nemanka har yamma ban ganka ba..."

Kanshi ya dora akan nata ya zagayeta da hannuwanshi,

"Wallahi Hafsat ba laifina bane, dama nafada miki mutanen nan bazasu barni ba..."

"Yaya yusleem me suka yimaka? Sunyi maka wani abu?" Tafada tana lallaluba jikinshi,

"Babu abinda suka yimin amma sunce mutukar na tona musu asiri zasu kasheni..."

"Nida cewa nayi ko infadawa abbanmu gaskiyar abinda yake faruwa? Saboda ayi muku tsakani dasu yaya yusleem inma wurin yan sanda zakuje ayi muku tsakani sai kuje tunda har gunsu dazu naje nakai report.."

Murmushi yusleem yayi yashiga shafa gadon bayanta alamun rarrashi,

"Nanah mutanen nan fa sunada gatan da bakowa keda shi ba, sunada fada fiyeda yadda kike tsammani, koda kayi kararsu to daga karshe kaine zaka kwana aciki shiyasa ni bazance zanyi kararsu ba, tunda dai bukatarsu kar intona sirrinsu to shikenan bazan taba tonawa ba tunda Allah yana kallonsu shi yasan yanda zaiyi dasu"

"Hakane, shikenan Allah yakara kareka daga sharrinsu.."

"Amin nanah.."

Hannunshi yasa ya shafo cikinta,

"Kinci abinci kuwa?"

Girgiza masa kai tayi,

"Meyasa?" Ya tambayeta har lokacin hannunshi yana kan cikinta,

"Taya zan iya cin abinci alhali ban ganka ba? Ni ko girki ma banyi ba, maman amir ma takawo min alala amma ko budashi banyi ba"

"Wallahi nima banci komai ba kuma sun Kawo min abincin amma naki ci.."

"Allah ya shiryar dasu, kasan duk inda ka kai da son wani ya shiryu bazaka iyaba mutukar Allah bai nufeshi da shiriyar ba domin shiryarwa awurinshi take.."

"Amin Hafsa, Allah yaganar dasu suma, ya ciwon marar taki?"

Sake lafewa tayi ajikinshi,

"Da sauki,dayake ina cikin damuwa ma ni harna manta da wai banda lafiya"

"Allah sarki nanah, sannu kinji, bari in dafa miki ruwan zafi kisha sai kici abinci"

Kwantar da ita yayi yakunna candle sannan yakunna risho ya dora ruwan zafi, taliyar da yadafa musu da safe tana nan ayanda take batayi komai ba dayake sanyi ne dan haka ya dumama musu ita,

Acikin cup yazuba mata ruwan zafin yasa sugar dan kadan yajefa Lipton,

"Tashi kisha ruwan zafin sai muci abinci ko?"

Tashi tayi ta amshi tea din ta kurba,

"Ya haka dalam babu sugar?"

Murmushi yayi,

"To keda bakida lafiya inake ina shan zaki? Ko kina son kiyita bleeding ne?"

Shiru tayi taci gaba da kurbar tea din har ta shanye,

Taliya yazuba musu suka ci, bayan sun gama ta shiga toilet ta dan gyara jikinta ta fito sanye da kayan bacci riga da wando, kwance ta sameshi ya dan jingina da jikin bango yana wasa da candle din dake hannunshi yana d'isa ruwan candle din a hannunshi,

Kusa dashi takarasa ta kwanta jikinta ajikin nashi,

"11 fa tawuce bazaka kwanta ba?"

Hannunta yakamo ya disa mata ruwan candle din, zabura tayi ta tashi zaune tana yarfe hannun, diff taga yabushe candle din,

"Yaya yusleem da zafifa, wallahi ka kona ni"

Kamota taji yayi zuwa jikinshi, bargo yaja ya rufesu ya kamo hannunta wanda ya disa mata ruwan candle din,

"Sannu, kawo mugani..., nimafa kinji inda ya diddisa a hannuna taba kiji"

Kanta ta kwantar agefen wuyanshi numfashinta yana sauka akan wuyanshi.....



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO*




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_



_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_




_Dedicated to MISS XOXO_



*33*



***Lumshe idanuwanta tayi tana jin yanda yake hura mata iskar bakinshi awurin da ya diga mata ruwan candle,

"Wai dagaske kin kone ne..?"

"Ehh.."

"Kai nanah banda karya dai, naji anacewa bakar fata tafi fara kwari to ya akayi ni ban koneba sai ke?"

"To ai kai namiji ne"

Murmushi yayi yaci gaba da busa mata wurin,

"Da ban dawo ba shikenan sai dai ki kwana ke kadai ko?"

Dayan hannunta takai ta dora akan bakinshi,

"Yaya yusleem dan Allah kadaina fadin haka, bana burin wani dare yazo wanda zan kasance ni daya ba tare da kai ba..."

Murmushi yayi yajuya ya rungumeta tsam tsam,

"Gobe akwai maganar da nake son muyi tare dake amma yanzu kiyi bacci ki huta.."

Makale kafada tayi kamar yana ganinta,

"Uhm, uhm muyi yanzu mana.."

"Meyasa bazaki bari sai goben ba?"

"Ni bana jin bacci yanzu"

"Nikuma kinga bacci nakeji sosai dan har idanuwana rurrufewa suke saboda tsananin bacci..."

Hannu takai tafara laluben fuskarshi har ta tabo idanuwanshi wadanda ke rufe,gangarowa tayi har zuwa kasumbarshi wadda ta dan fara taruwa,

"Yaya yusleem gaskiya gobe ya kamata inkaika kayi aski, jifa yanda kafara zama wani tsoho.."

Murmushi yayi yadora hannunshi akan nata wanda ke bisa kasumbar tashi,

"Nine nafara zama tsohon? Har yanzu fa ni saurayine nanah..."

Jin abinda yace yasata boye fuskarta cikin kirjinshi,ahankali yasake magana,

"Askin ma sai kin kaini...?"

"Ehh mana.."

"Kina tsoro kar su oga dalma su kara kamani ko?"

"Insha Allah ai bazasu ma sake ganinka ba bare su daukeka,yanzu dai muyi maganar da kace zamuyi"

"Ai nace miki sai gobe saboda yanzu bacci nakeji"

"Tom shikenan tunda dai bazaka fada min yanzu ba..."

Zamewa tayi daga jikinsa ta juya daya bangaren, matsawa yayi ya rungumeta ta baya mintuna kadan taji yayi bacci,

Ita kam kasa yin baccin tayi sai tunane tunane barkatai da kwakwalwarta ke yi daga karshe itama bata san lokacin da baccin ya dauketa ba.


K'arfe 6:30 ta bude idanuwanta, yusleem tagani zaune akasa ya bude laptop dinshi yana latse latsen da bata san ko na menene ba,

Bathroom ta shiga tayi brush tafito ta karasa wurin kayan sakawarsu, kayan da yasaka da wanda tasaka taware zata wanke,

Har ta dibi kayan ya daga kai ya ganta,

"Ina zakije kuma daga tashinki?"

"Wanki zanyi wai kafin rana tafito"

"To ai nace miki zamuyi magana ko kin manta?"

"Gani nayi ai kaima akwai abinda kakeyi shine zan yi kafin kagama"

"A'a zo mu gama maganar tukunna.."

Ajiye kayan tayi takarasa inda yake, daukar laptop din yayi suka koma saman katifa,

"To ina jinka.."

"Sana'ar yi nake son ki zaba min sai infara.."

"Yaya yusleem Sana'a kuma?"

"To nanah zanyi ta zama hakane? Ai yakamata insamu abinyi komai kankantarsa"

"To shikenan amma dai banda aikin karfi da sauran ayyukan wahala"

"Meyasa? Bakya son karfina yakare ne?"

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta cike da kunya, janta jikinshi yayi ya dora hannunshi akan kafadarta kyass taji karar camera, dago da idonta da sauri tayi nan taga ya kuma daukar wani ajikin laptop din,

Kallonshi tayi, "yaya yusleem wannan wanne irin hoto ne da kayan bacci?"

Sake dauka yayi yana murmushi,

"Kinyi kyau ne shiyasa, kuma kinga kayan baccin ma sunyi miki kyau.."

Kokarin tashi tayi yahanata ta hanyar matseta ajikinshi,

"Ki tsaya mugama mana, so nake muyi hotuna kamar guda 50 ayanzu.."

"Sai har charge yakare kenan.."

"Waya fada miki zai kare?" Yakarasa maganar yana cusa fuskarshi tsakiyar kirjinta,

Tureshi tayi tana murmushi,

"Kai yaya yusleem,dan Allah kabari.."

"Au bakya son hoton?"

Kallar screen din laptop din tayi nan taga har lokacin da yasaka fuskarshi a kirjinta saida ya dauka,

"Dan Allah ko goge wannan.. Idan wani yagani fa"

"Sai infada mishi nida matata ne"

Ta bude baki da niyyar sake yin magana taji lebenshi kan nata dolenta tayi shiru, kan kumatunta yakoma daga nan yakoma goshinta, habarta, wuyanta,

Zamewa tayi, "nidai gaskiya hoton nan ya isa haka"

"To shikenan, zo ki gansu"

Matsawa kusa dashi tayi tasoma kallon hotunan tun daga kan nafarko, wani idan tagani

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment