Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali tana cewa babu komai,

Saida lokacin salla yayi sannan Hafsat ta dauki kayanta ta nufi bedroom din surayya, akwance ta samu yusleem amma ba bacci yakeyi ba,

"Yaya yusleem tashi kayi salla..."

Tashi yayi yana kallonta,

"Hafsat meyasa baki fadawa mami gaskiyar abinda yafaru ba? Saboda ko dan nan gaba ya kamata ace tasani"

Zama tayi kusa dashi,

"A'a yaya yusleem fadar bata da alfanu hakan dai da akayi shine daidai"

"Shikenan.." Abinda yace kenan yatashi zai fita, bin bayanshi tayi zuwa falo ta dauki trolley din kayanshi tabishi, part dinsu Abdul ya bude yashiga, bedrooms biyu ne aciki sai falo domin suma samarin kowa da dakinshi, dakin khalifa yashiga tana biye dashi, juyawa yayi ya kalleta,

"Wai kina nufin ke adakin surayya zaki zauna?"

"Ehh mana"

Murmushi yayi ya karbi trolley din hannunta,

"Ashe dama karya kike da kikace bazaki iya kwana babu niba.."

Murmushi ne ya kwace mata tajuya zata fice yayi hanzarin rikota,

"Debo kayanki kidawo nan"

"Tohm" ta amsa amma bawai aikatawar zatayi ba domin tana jin nauyin mami ba kadanba,

Sakinta yayi tafita shikuma ya nufi cikin toilet.

Koda takoma part din mami salla tayi tafito falo nan ta hango kuku yana shirya lunch akan table, fitowar mami ne ya katse mata tunaninta,

Kan table suka hau, fried spaghetti da salad kukun yadafa sai kunun shinkafa, suna ci suna hira har suka gama, kunun Hafsat ta dauka tatafi kaiwa yusleem ko zai iya sha,

Akan carpet din salla ta sameshi yana tura sako ta email dinshi ackin laptop,

"Yaya yusleem ga kunu.."

Dagowa yayi ya karba ya dan kurba, zama tayi agefen gado, babu laifi yadan sha kunun ganin haka yasa taji dadi sosai, maganinshi ta dauko mishi ya karba ya hadiya daga nan tatashi tafita.

Wayarta ta Kunna bayan ta koma, ko minti biyu ba ayiba Ummi takirata, cikeda zumudi ta dauka suka gaisa nan take fadawa ummin cewar yau suka dawo amma suna gidan mami,

Suna gama waya da ummin kiran Amina yashigo, ita dinma korafin bata samunta awaya tayita yimata gashi ta jima da haihuwa mijinta yanata zuwa gidan domin yafada mata amma baya samunsu, Allah yaraya Hafsat tayi mata tace sunyi tafiya ne amma tunda sun dawo tana nan zuwa,

Komawa wurin mami tayi bayan sunyi sallama da Amina, nan take fadawa mami yusleem yadan sha kunun da takai masa tunda hakane zata rinka dama masa kullum.

Misalin karfe 8:30 nadare suna zaune afalo suna kallon tashar zee world itada mami sai gashi yashigo da cup din kunun data kaimasa, zama yayi yasoma kurbar kunun, Hafsat da mamine ke dan yin hira lokaci zuwa lokaci yana zaune yana jinsu,

Yana kallo hafsat ta shige daki bayan tayi musu saida safe, itama mami ba ajima ba tashiga nata dakin suka barshi afalo shi kadai, sai wurin 11 yakashe tv da sauran kayan wutar dake cikin falon, dakin surayya wadda Hafsat ke ciki ya shiga ya maida kofa ya rufe, gani yayi harta jima da yin bacci, bargon yabude yashiga yayi kwanciyarshi tareda mannuwa ajikinta.

Said a asubah sannan Hafsat tasan yana cikin dakin, tashi tayi tashiga bathroom tayi alwala tafito, ahankali tafara tashinsa saboda bata son mami ta jiyo,

Tashi yayi yana lullumshe ido alamun baccin bai isheshi ba,

"Yaya yusleem katafi saida safe..."

Hammar da yafara ya karasa sannan ya kalleta,

"Ina zan tafi?"

"Masaukinka..."

Baice komai ba yasauka daga kan gadon yanufi toilet, lokacin da yafito har ta idar da raka'atanul fijr tana kokarin tada ikamar sallar asubah,

Tashi yayi yakoma kan gadon ya kwanta bayan ya idar da sallar, yana kokarin lulluba da bargo Hafsat ta bazamo tazo tana masa magana kasa kasa,

"Dan Allah yaya yusleem katafi.."

"Ina?"

"Dakinka mana, bana son mami tazo taganka"

Kafin yabata amsa suka fara jiyo knocking abakin kofa da sauri Hafsat ta diro, maganar mami tajiyo tana cewa,

"Hafsat, Hafsat kitashi asubah tayi.."

"Na'am mami"

"Au ko kin tashi ma?"

"Ehh mami"

"To shikenan.."

Daga nan tajiyo alamun tafiyar mami,hannu ya mika mata yana daga kwance,kafada ta makale ta kwabe fuska, shi dinma hakan yayi kamar yadda tayi,

"Zo dan Allah"

Kan gadon ta hau ta mika masa nata hannun, kama hannun nata yayi yajata ya kwantar da ita yaja musu bargo.



_Fatan alkhairi ga Hajjaju, Chuchu, Maman sultan, pheey, Maman humy, Anty sis, Dshanty, Reane_Gh,meela adeel,meernah parrot,khadija sadeeq,Billy s fari, Billy s jega, ummu abrar, anty Baraka, Maman mujahid da duk wadanda ban ambata ba, wannan shafin nakune kyauta domin jin dadinku._


*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[11:40AM, 2/4/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*




*ALWASHI....!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*



_DEDICATED TO MISS XOXO_



*Yau shafin nakune kawayena, Lubabatu mai tafsir, fiddausi sodangi,phertymah xarah Maman khadija, cwt Kausar Luv, Teemah Cool,Khaleesat Haidar, Hafsat bunza, Zee Rumah,Maman Shakur Benaxir oamar,Billy Galadanchi, ina yimuku fatan alkhairi aduk inda kuke...*



*41*


_Ina cikiyar RIRI TURAKI marubuciyar halal dina, idan sakona ya riskeki ni Ummi Shatu ina nemanki urgently._



***Misalin karfe 9 Hafsat tafarka daga bacci, juyawa tayi ta kalli yusleem wanda ke rike da hannunta yana kanannade da ita, dakyar ta iya tureshi daga jikinta ta tashi,

Wanka tashiga tayi tafito ta shirya agurguje, falo ta leka tagani ko mami tafito domin sam bata so mamin ta fahimci cewar yusleem awurinta ya kwana, ganin mami bata fito ba sai masu aiki dake faman mopping din falon yasata sakin ajiyar zuciya,

Juyawa tayi tasake komawa cikin dakin, tashinsa tasoma yi tana dan bubbuga gefen pillow din da kanshi ke kai,

"Yaya yusleem...,yaya yusleem katashi"

Ido guda daya ya bude ya kalleta,

"Me zan yi miki?"

"Safiya fa tajima dayi dan Allah katashi"

Mayar da idonshi yayi ya rufe yajuya mata baya yasake jan bargo ya lulluba, tashi tayi tafita, kuku ta hango yana jera musu breakfast akan dining,

Zama tayi acikin falon tama rasa me zatayi, ajiyar zuciya tayi aranta tana fadin dama matsalar gidan masu kudi kenan ko katashi da wuri karasa abinda zakayi,

Tana nan zaune tana kallon shirin gari yawaye a tashar arewa 24 har mami tafito, kamar kullum mamin tasha kwalliya kamar me shirin zuwa gidan biki,

Sauka kasa tayi tagaida mami, cikin fara'a da sakin fuska mami ta amsa domin tana jin son Hafsat tamkar na yar da ta haifa,

Kan dining suka dunguma suka fara karyawa,suna daf da gamawa mami ta kalleta tace,

"Shi wannan sarkin baccin bai tashi bane? Ai da yatashi saboda maganar zuwa asibitin ko"

"Ehh gaskiya kam, bari nagama sai inje in tasoshi.."

Kafin Hafsat ta rufe baki sai gashi ya bude kofa yafito yana yamutsa fuska, sunkuyar da kai Hafsat tayi kamar ruwa ya cinyeta, mami kuwa dubanshi tayi ta kawar da kai,

"Ka manta da maganar zuwa asibitinne kaki tashi da wuri?"

"Wallahi ina sane mami, ban manta ba" yakarasa maganar yana kallon Hafsat ta gefen ido wadda yasan ba haka tasoba,

"To ai sai kaje kashirya.."

Wucewa yayi yafita zuwa part din su khalifa, wanka yayi yafito ya zauna domin shafa mai, yana zama Hafsat tashigo hannunta rikeda jug dan madaidaici,

"Ga kunun..."

"Babu gaisuwa?"

Yafada lokacin da yake shafa man a hannayenshi,

"Ina kwana?"

"Ni bazan amsa ba, zo nan.."

Dan sake matsawa tayi tana kallonsa,

"Gani.."

"Kinsa Mamie tana yimin fada ko, bayan kuma kece kikayi sanadiyyar makarata saboda dumin jikinki da naji"

Juyawa tayi zata fita daga dakin fuskarta dauke da murmushi,

"Zo nan, Allah karki fita"

Dawowa tayi ta tsaya, tana nan tsaye har yagama shiryawa ya dauki kayanshi yasa,

Kunun da ta Kawo mishi yasha sannan suka fita domin Tafiya asibiti,

Afalo suka iske mami cikin shiri nan suka dunguma domin tafiya amma kuma suna fitowa compound din gidan sai ga motar khadija ta kunno kai kuma tareda mahaifiyarta suke wannan dalilinne yasa mami fasa zuwa asibitin tace da yusleem da Hafsat kawai suje driver yakaisu ita kuma takoma ciki itada hajiya fa'iza da khadija,

Ganin irin gaisuwar da yusleem sukayi shida khadija yasa Hafsat yimasa magana domin daurewa khadija fuska taga yakeyi bayan kuma ita bataga laifinta ba, ganin baya son maganar yasata yin shiru ta kyaleshi.

Lokacin da sukaje asibitin Hafsat kin shiga office din dr sufyan tayi tai zamanta awaje sai yusleem ne yashiga shi kadai, ya dan jima aciki kafin yafito,

"Yaya yusleem ya kukayi?"

"Yace nanda 4 days nakara dawowa lokacin result din taste din da yayi min yafito.."

"To Allah dai ya jiyar damu alkhairi"

"Amin, muje mu tafi gida tunda babu abinda yayi saura, Dr din yana tambayarki wai yau banzo da matata ba nace tare ai muke kina waje wai ai dama yasan bazaki barni nazo ni daya ba..."

Dan murmushin yake tayi batace komai ba amma acikin ranta fadi take "Dan iskan Dr",

Lokacin da suka koma gida sai mami ita kadai domin su khadija sun tafi, ganin sun dawo da wuri mami tace Hafsat ta shirya taje driver yakaita gidansu tagaisa da iyayenta,

Garin dakakkiyar busasshiyar kubewa da kuka da daddawa wanda Maman khadija ta Kawo wa mami su mamin tabawa Hafsat tace takaiwa umminta tsaraba,

Yusleem yana kwance akan kujera mami na kujerar kusa dashi Hafsat din tafito zata tafi,

"Mami idan nadawo zan biya ta gidan amina kawata, haihuwa tayi shine zanje inga babyn.."

"To sai kin dawo, Allah ya raya.. Ki gaida hajiya kubran"

"To mami zataji"

Fita tayi nan yusleem yatashi yabita, tana daf da fita daga cikin kitchen yayi saurin rikota,

"Mami zaki tambaya unguwa saboda itace take aurenki ko? To gidanku kadai na amince kije daga nan karkije ko ina"

Juyawa yayi zai koma falo tayi saurin rikoshi,

"Dan Allah kayi hakuri yaya yusleem.. Kaji"

Shiru yayi mata ita kuma taci gaba da yimasa magiya, dakyar ya amince yace taje.

Acikin kitchen ta iske Ummi lokacin dataje gidan, ba karamin dadin ganinta hajiya kubra tajiba nan suka baje suka fara hira irinta uwa da 'ya da haka har Alhaji sa'id yazo ya samesu yadawo daga buga bugarsa domin shima ya haduda jarrabawa irinta rayuwa sai dai ita Hafsat bata saniba har saida ummi tayi mata bayanin abubuwan da suka faru na iftila'in da ya afkawa alhaji sa'id din bayan ya sayar da kadarorinsa ya tura asiyo masa kayayyaki amma har yau kayan basu fitoba gashi saboda rashin kudi kwangilar ma ba samuwa takeyi ba dan dai kawai yanada amini ne mai fada aji,

Kuka Hafsat tayi ba kadanba dalilin jin wannan labarin da hajiya kubra ta bata amma kuma tasan jarrabawa ce daga Allah shiyasa ma bata daga hankalinta ba,

Dayake sun dade basu hadu da umminba yasa Hafsat takasa tafiya da wuri har saida aka kira sallar magrib, bayan tayi sallane tatafi lokacin driver yazo daukarta, ko gidan aminan ma bataje ba gida ta wuce direct,

Mami kadai ta tarar afalo tana waya da surayya nan ta zauna har mami ta kammala wayar itama tabata suka gaisa domin rabonsu da juna tun lokacin da surayyan takoma school,

"Hafsa kin dawo? Ya kika baro mutanen gidan?" Mami ta tambaya tana kokarin ajiye wayarta,

"Lafiya lau mami, suna nan lafiya, Ummi tana gaidaki tace ayi miki godiya..."

"Babu komai wallahi, kayan ma nawa suke.."

Zama sukayi dan shiru suna kallon tv zuwa can Hafsat ta mike ta nufi bedroom, tana shiga ta iske yusleem akwance,

"Lafiya kuwa yaya yusleem?" Ta tambaya,

"Wallahi zazzabi ke damuna hafsa"

Ahanzarce takarasa kusa dashi jin jikinsa zafi zauuu tayi gashi yana dafe da cikinsa wanda ke ta faman murda masa,sannu ta shiga yimasa yana amsawa dakyar, zuwa can taji ya kamo hannunta ya dora akan cikin nasa,

Jikinta rawa yafara saboda ganin yanda yusleem yake yin murkususu gashi bata son taje tafadawa mami hankalinta yatashi,

Ruwan sanyi ta dauko tasoma shafa masa acikin nashi nan yaji ciwon yafara lafa masa ahaka har bacci ya daukeshi, ganin yasamu bacci yasa ta fita wurin mami wadda take zaune akan abin salla ta idar da sallar isha tana jan carbi,

"Hafsa ga tuwo can, wallahi yau shi naji ina sha'awa shine nace kuku yayi.."

Murmushin yake Hafsat tayi ta girgiza kai,

"Kafin nataho ma agidan Ummi saida naci abinci,wallahi na koshi.."

Wuri tasamu ta zauna amma lokaci zuwa lokaci tana dan shiga bedroom din taduba yusleem sai dai har 10 tayi bai tashiba, har sukayi sallama da mami tashiga dakinta itama ta shiga daki yusleem bacci yake,

Akusa dashi ta kwanta tana kallonshi yana rike da cikinshi, sai wurin 11 sannan yatashi yayi sallar magrib da isha wadanda ke kanshi domin bai samu damar yiba,

Kalau yayi sallar ya idar tana zaune tana kallonshi yana idarwa kuma yace sai ta dama masa kunu yasha yunwa yakeji, tare suka fita zuwa kitchen din ta tafasa ruwa ta dama masa kunun suka koma daki, saida yagama sha sannan suka kwanta, tana ji yafara tsokanarta kamar bashi bane dazu yake murkususu kamar zai mutuba,

Bata San lokacin da yagama tsokanar tataba domin bacci tayi tabarshi, can tsakiyar dare kuma kamar acikin mafarki take jin kakarin amai nan tatashi taganshi kwance yana juyi yana rikeda cikinsa, ruwan sanyi ta debo tafara shafa masa amma yanzu ji yake kamar ruwan zafi tafasasshe take Shafa masa, kunun da yasha kuwa saida yayi amansa gaba daya,rikeshi tayi nan ya kuwa kankameta kamar zai koma cikin cikinta daga shi har ita babu wanda yasake runtsawa har asuba tayi ita dai agaba tasashi tana hawaye,

Ganin abin yayi yawa gashi yana yin wani irin amai kore kore yellow yellow yasa hafsa zuwa ta sanarwa da mami lokacin karfe 5:30,

Driver mami tayiwa waya kasancewar a B/Q yake zaune, nan da nan yafito suka kama yusleem suka nufi asibitin Dr sufyan dashi,

Kallo daya zaka yiwa mami da Hafsat kagane acikin tashin hankali suke domin kowannensu fuskarshi kunshe take da tashin hankalin,

Emergency aka kai yusleem bayan kamar mintuna 30 Dr mufid yafito dauke da file din yusleem domin lokacin Dr sufyan bai fitoba,binsa mami da Hafsat sukayi abaya domin jin abinda zaice,

"Hajiya in my opinion ni ina ganin cewar is better for u idan kuka fitar da patient dinku kasar Cairo ko kuma India saboda sincerely speaking yana cikin bad condition domin cutar dake tattare dashi itace take cousing din wannan ciwon cikin da yake fama dashi, and kuma akwai wani aiki da zasuyi masa wanda mu bazamu iyaba, so idan zai yuyu in the next 3 days ku samar masa visa sai ku fita dashi domin magana tagaskiya bama karbar patients wadanda lalurarsu tazama chronic kuma worst saboda kinga nan is private hospital dole sai mun zama muna him takatsantsan..."

Yana ida wannan bayanin yagyara farin glass dinshi yayi gaba, sororo mami da Hafsat sukayi kowannensu yana tunanin hanyar da za abi har akai ga fitar da yusleem kasar waje....




*_Ummi Shatu_*
[3:05PM, 2/8/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI...*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_


_Fatan alkhairi ga yan kungiyar haske writers association, shafin yau nakune ku kadai domin jin dadinku..._



*42*



***Daga mami har Hafsat ji sukayi kamar ruwa ya cinyesu dalilin jin bayanin da dr yayi musu nan hankalin kowanne acikinsu yakai kololuwar tashi,

Mami ce tafara magana fuskarta cikeda murmushin yake,

"Hafsat babu komai kinji, karki daga hankalinki insha Allah zamu samu yanda zamuyi..."

Wasu hawaye ne suka zubowa Hafsat tasa gefen hijabinta ta share batare da tayi magana ba,

Kama hannunta taji mami tayi suka bar wurin suka koma reception,

"Yanzu Hafsat ina zuwa bari naje gida nadawo kinji..."

"To mami sai kin dawo, Allah kiyaye hanya.."

Tashi mami tayi tafita, yayinda ita kuma Hafsat taci gaba da zama awurin zuciyarta kunshe fal da tarin tunani.

Tana nan zaune tarasa abinda yake mata dadi tahango dr sufyan yana kokarin shigowa cikin reception din hannunsa dauke da wata yar madaidaiciyar bag, ko kallonsa batayi ba ta dauke kanta takaishi can gefe, shikuwa kura mata ido yayi har ya bace ya nufi office dinshi,

Kimanin mintuna 30 da tafiyar mami sai gata ta dawo, tun kallon farko da Hafsat tayi mata ta fahimci cewar akwai damuwa a tattare da ita amma dai sai batayi magana ba domin daga ita har mami din kowa ba son yin maganar yake ba,

Emergency suka shiga wurin da yusleem ke kwance yana bacci, gaban gadon sukaje suna kallonsa,

"Ni wannan abu ya daure min kai, wai menene takamaimai abinda yake damunsa ne? Ni duk ban fahimci bayanin da Dr yayiba hafsat..." Mami tayi maganar idanuwanta na kan yusleem wanda yake kwance yana fitar da numfashi,

"To nima dai mami maganar dr ta daure min kai amma a iya sanina dai wannan ciwon cikin shine ke damun yaya yusleem"

"To ko komawa zanyi wurin Dr din insake tuntubarsa inji?"

"A'a mami da dai mun hakura kawai munyi yanda yace din.."

"To yanzu hafsat ina zamu samu kudaden da zamuyi hakan? Hafsat yanzu ba babu abinda muka mallaka inbanda wannan motar kwaya daya da nake hawa sai ko gidan da muke ciki..."

"Babu komai mami ki kwantar da hankalinki insha Allah komai zai zama daidai saboda Allah baya taba dorawa bawansa abinda bazai iyaba"

Ajiyar zuciya mami ta yi suka fita daga cikin emergency room din suka koma waje suka zauna,

Wuni guda cur yusleem yana bacci sai yamma yafarka, hafsat ce ta karasa wurinsa domin ita mami tatafi gida ta dawo wanda tafiyar tata bazata rasa nasaba ba dayin wanka sannan da shiryo abinci,

"Sannu yaya yusleem.."

Kai ya daga mata ya lumshe idanuwansa,

"Yaya yusleem zaka sha kunun?"

Girgiza mata kai yayi bayan ya bude idonsa, kicin kicin yaga tayi tabata fuska kamar zata saka kuka, ganin haka yasashi daga mata kai alamun zaisha,ita kanta tana lura dashi sam yanzu baya son yaga bacin ranta,

Dan murmushi tayi ta tsiyayo masa kunun acikin cup ta zauna agefen gadon, yunkurawa yayi yafara kokarin tashi ta taimaka masa, duk da cewar dakin basu kadai bane akwai mutane da yawa aciki amma haka ta rinka bashi abaki yana kurba idan kuma ya disa sai ta lashe, kallonta kawai yake yi da idanuwanshi wadanda suka dan firfito har tagama bashi duk da dai bai shanyeba amma yadan sha dayawa,

Taimaka masa tayi ya kwanta ta gyara masa kwanciyar, ta zauna tana kallonshi, hannunta taji ya riko acikin nashi tareda lumshe idanuwanshi ahaka har wani baccin ya sake daukarshi.

Zuba mishi ido tayi takai hannunta bisa kuncinshi tasoma shafawa ahankali tana jin wani irin tunani yana ratsa zuciyarta, ahaka Mami ta dawo ta isketa jikinta sukuku wanda daga gani ranta abace yake gaba daya,

Jugum sukayi babu wanda yake yin magana acikinsu har tsawon wani lokaci domin kowa shi yasan tunanin da yakeyi,sai can Mami tayi karfin halin yiwa hafsat magana,

"Hafsa kitafi gida kije kiyi wanka sai kidawo.."

Duk da bata son tafiyar amma bata musawa Mami ba haka tayi mata sallama tatafi bayan ta leka yusleem ta window nan taganshi har lokacin bacci yakeyi ga drip nan ahannunshi wanda ba ajima da daura masa ba domin duk jikinshi yayi yaushi,

Mami saida ta tabbatar da cewa hafsat tatafi sannan tatashi ta nufi office din Dr sufyan,

Kimanin mintuna samada arba'in mamin ta shafe acikin office din na dr sufyan sannan daga bisani tafito, tana zama hafsat nadawowa,

Zama suka cigaba dayi har zuwa dare, lokacin ne aka fito da yusleem daga emergency aka kaishi wani daki wanda gado ne guda daya aciki irin na marassa lafiya sai fridge dan karami sannan ga yar karamar tv nan daure ajikin bango sai dan madaidaicin bathroom aciki,

"Hajiya wannan dakin kwana uku kadai zamu bashi muna treating dinshi domin dama narigada nafada miki cewar fitar dashi outside shine kadai solution agareku, therefore nan da 3 days zamu baku sallama so sai kuje gida kuci gaba da kula dashi idan kuma before time din kun sami kudin fitar dashi outside sai ku fitar dashi.." Dr mufid yafada yana sunkuye yana rubutu ajikin file din yusleem,

Kallonshi Mami da hafsat sukayi har ya kammala jawabin sannan yafita,

"Hafsat wuce kije kitafi gida ki kwanta inyaso idan Allah ya nuna mana gobe sai musan abinyi.."

Girgiza kai hafsat tayi ta kalli mami,

"A'a Mami kibarni anan din ke kitafi gida, ni zan kwana tare dashi.."

"Hafsat kije ki huta kinji, babu komai"

"Dan Allah mami kibarni kitafi, wallahi ko naje gidan ba iya barci zanyi ba"

"To shikenan tunda kinki, bari ni naje natafi, Allah yabashi lafiya"

"Amin mami"

Saida mamin tasake duba yusleem din sannan tayiwa hafsa sallama tatafi,tana fita harabar asibitin tahango dr sufyan tsaye ajikin motarshi kirar Benz new series 2017 yana sanye cikin kananan kaya, wurinshi mami takarasa dama abisa dukkan alamu ita yake zaman jira, bude mata kofar motar yayi tashiga tazauna sannan yazagaya side dinshi bayan yarufe yaja motar suka bar harabar asibitin.

Cikin dakin hafsat tashiga ta zauna akan wata kujera tana kallon yusleem wanda keta faman barci, lokaci daya ta tashi zunbur ta isa gefen gadon ta zauna, bude idonshi taga yayi,

"Sannu yaya yusleem"

Kai ya daga mata sannan yadanyi murmushi,

"Yaya yusleem ko kana bukatar wani abu ne..?"

Kanshi ya girgiza har lokacin fuskarshi tana dauke da murmushi, shiru tayi ta dan jingina da jikin bango, gyangyadi ta dan soma yi amma da zarar baccin yafara daukarta zatayi firgigit ta bude idonta,

Matsawa yusleem ya danyi yakamo hannunta, idonta Wanda yake cike da barci ya bude domin daren jiya bata samu tayi ba,

"Kizo ki kwanta..."

"Bari inshinfida hijabina akasa kawai sai in kwanta saboda kar intakura maka"

"Gashi na matsa miki"

Girgiza kai tayi zata sauka daga kan gadon, tashi shima yayi da niyyar sauka tayi saurin rikeshi,

"Haba yaya yusleem kaida bakada lafiya,dan Allah kakoma ka kwanta"

Dakyar ya kwanta din hannunshi rikeda ita dole ta hakura ta kwanta akusa dashi,

Sassafe saiga mami tazo, office din dr sufyan tafara zuwa amma lokacin bai fitoba, wurinsu hafsa taje, hafsat din tana zaune akan kujera shikuma yusleem yana kan gado akwance,

Tare da mamin suka cigaba da zama har karfe 9 tayi lokacinne driver yakawo musu abinci amma ita mami bata samu damar cin abincin ba domin hankalinta yana can office din Dr sufyan, hajiya kubra da alhaji sa'id ne suka zo duba yusleem din bayan an dan gaggaisa mami ta zare jikinta ta fita, office din Dr sufyan tashiga wanda yake abude alamun yana ciki,

Lokacin da hafsat tafito domin raka su hajiya kubra sukayi kicibus da mami, godiya mami tayiwa su hajiya kubra sukayi sallama suka wuce ita kuma tanufi dakin da yusleem yake,

Hafsat kam saida ta rakasu har wurinda motarsu take sannan tajuya ta takoma, tana shiga cikin dakin ta iske mami tana shirya kudi rafa rafa sabbi kal yan dubu dubu acikin jakarta wadanda zasu doshi samada naira dubu dari tara, cikeda mamaki hafsat ta karasa gaban mami wacce ke zaune akan kujera.....




_Fans kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu, kun san jiki da jini amma alhamdulillah naji sauki sosai, hakika bani da bakin da zan gode muku,duk wadanda suka kirani suka gaisheni da wadanda suka min text nagode Allah yabar zumunci._



*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[10:11PM, 2/9/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_



*43*




***Gaban Mami hafsat takarasa ta tsugunna fuskarta cikeda mamaki,

"Mami wannan kudin fa?"

Fadada murmushi mami tayi batare da ta dago ta kalli hafsat ba domin hankalinta yanaga kan kudin da take lissafawa,

"Hafsat wani al'amari ne ya gudana wanda yayi sanadiyyar samuwar wannan kudin, kinga dr kwana uku kacal yabamu yace daga nan sallamace zata biyo baya to shiyasa naga gara fa intashi atsaye innemo kudi duk inda yake domin mu fitar da yusleem kasar Cairo.."

"Hakane mami, amma yanzu kin san kudi yana wuyar samuwa shiyasa nace garin yaya aka samo wadannan kudaden masu yawa.."

Rufe handbag din mami tayi ta maida hankalinta gurin hafsat da niyyar yimata bayani amma kafin takai ga farawa sukaji anturo kofar dakin da suke ciki anshigo, dukkaninsu maida idanuwansu wurin sukayi domin ganin wanda zai shigo,

Khadija ce ta shigo hannunta rikeda basket din abinci, tana sanye cikin bakar doguwar riga ta yane kanta da mayafin rigar inbanda kamshi babu abinda take zubawa,

"A'a khadija ce? Sannu da zuwa" mami tayi maganar tana fadada fara'arta,

"Yawwa sannu mami" khadija tafada tareda ajiye basket din hannunta ta durkusa kasa tagaida mami,

"Mami ina kwana? Ya mai jikin? Allah yabashi lafiya"

Cikin raha mami ta amsa gaisuwar, kallon khadija hafsat tayi tayi mata sannu da zuwa sannan suka gaisa,

Gaban gadon

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment