Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurinda zai fice shine sai yarinka taruwa yana taruwa har idan yakai wani stage sai wurin ya lalace har tsutsotsi su rinka fita ta wurin dan haka kidaina wahalar da kanki abanza, ni zan rinka bashi magani kyauta duk da tsadarshi mutukar kin amince da bukatata domin nan asibiti nane wadannan magungunan kuma tun daga India nake iyo ordersu ake kawo min.....!"

Sassauta muryarshi yayi cikeda yaudara da son janyo hankalinta,

"Kinga maimakon ki zauna kina yimasa wahala bayan bazai iya amfana miki komai ba gara kisamu wanda zai rinka debe miki kewa duk lokacin da kika so...!.







*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI...*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_




*Assalamu alaikum warahmatullah yan uwana masu karatu, hakika duk korafinku yasame ni gameda irin rayuwar wahala da talauci wanda Hafsat da yusleem suka samu kansu aciki ahalin yanzu, to abind nake son inja hankalinmu shine nafarko dai mun san acikin rayuwa kowa da irin jarrabawar da Allah yake yi masa sannan arayuwa ta zahiri akwai wadanda sukafi Hafsat da yusleem shiga kuncin rayuwa kuma suna nan acikinta,wasu kuma sunada arziki amma daga baya sai Allah ya jarrabesu ta hanyar karbe dukiyar sannan akwai wadanda sukafi su shiga talauci da hali na rashi sai dai duk abinda ya kamata mu fahimta shine annabi yafada mana mutum baya dawwama acikin yanayi guda daya domin farin ciki yana tare da bakin ciki, fari yana tare da baki, nasara tana tareda hakuri haka kuma tsanani yana tare da sauki, dan haka kada mu zamanto masu gajen hakuri da saurin yanke hukunci, muyi hakuri muci gaba da bibiyar labarin har mu samu nasarar fahimtar sakonnin da yake dauke dasu domin ayanayin da muke ciki yanzu ba kowacce macece zata iya yin abinda hafsat tayiba ace ki samu mijinki da babban laifi kiyi masa nasiha ki rufa masa asiri sannan kishiga kunci da talauci duk ata dalilinshi, gaskiya ni ina ganin kadanne acikinmu wadanda zasu iya yin hakan, to koma dai menene masoya na sadaukar da wannan shafin agareku baki daya...!*



*37*



***Cikeda tsana da takaici hadeda bacin rai wanda ya bayyana fushi mai tsanani akan fuskarta Hafsat take kallon Dr sufyan wanda yake zaune bisa kujerarshi yana dan juyawa ahankali abisa dukkan alamu ko auren farima dakyar idan yayi duba da yanayinsa haka kuma ahaife yusleem bazai girme mishiba,

"Madam bakice komai ba, abinda nake son ki fahimta shine wallahi idan kika cigaba da zama da wannan mijin naki dan homosexual to zaki nak'asa rayuwarki ne domin babu abinda zai amfana miki saboda yanzu shi yamafi bukatar dan uwanshi namiji sama dake domin masu aikata irin wannan mummunar dabi'ar akwai wani stage wanda idan har suka kai wannan level din to wallahi zai zamana bama sa kaunar mace kwata kwata bare har suyi sha'awarta, mijinki ayanzu dai haka presently bazanyi saurin yanke hukunci ba but yana daf da karasawa wannan stage din muddin baku dage da bashi wadannan magungunan yana sha ba.."

"Likita ni dama sassauci nazo nema wurinka bawai maganar banza ce takawo ni ba kuma har tunda sassaucin bazai samuba to babu matsala amma kaji tsoron Allah..."

Takarasa maganar cikeda fushi ta mike saurin dakatar da ita dr sufyan yayi,

"Haba yar kyakkyawa kyakkyawa, wallahi kinada kyau dan Allah..."

"Allah ya shiryeka tunda bakada aiki sai fasikanci da matar aure..."

Bata sake jiran abinda zai fada ba tafice daga cikin office din gabanta yana tsananta faduwa domin babu Wanda yataba tunkurarta da maganar banza irin wannan sai Dr sufyan, ko yusleem da yake mijinta bai taba yimata magana makamanciyar wannan ba,

Jan kafarta tayi zuciyarta tana yimata wani irin kunci da radadi, kamar amafarki ta jiyo muryar dr sufyan abayanta yana yimata magana da alama sake biyota yayi bai hakura ba da mugun nufinshi,

"Hajiya tsaya kiji, dan Allah kibani 5 minutes kacal infada miki wata magana.."

Afusace tajuya ta kalleshi,

"Dr nahadaka da girman Allah karabu dani, kadaina bina, yanzu idan mijina yaga kana bina me zai yi zargi?"

Jin yanda ta bude murya tana neman tara masa mutane yasashi tsayawa, ahankali yafurta,

"Zan barki amma bawai dan nahakura ba.."

Juyawa yayi yakoma ita kuma tabishi da kallon mamaki zuciyarta tana harbawa da karfi,

Wurin yusleem ta tasamma komawa kwakwalwarta abirkice saboda abinda taji dr sufyan yafada gashi kuma nanda 2 weeks dole su sake dawowa asibitin domin za asake checking din yusleem agani,

Awurinda tatafi tabarshi anan tasake samunshi yana tsaye ya dafa gate din asibitin yana jiranta,

Hannunshi takama tarike acikin nata,

"Yaya yusleem mutafi ko.."

Kallonta yayi yana dan murmushi,

"Au kin dawo?"

"Nadawo muje gida kawai abinda naje nema bai samuba dama nufina wai asauya maka maganin nan zuwa wani tunda naga har yanzu babu wani improvement.."

"To me likitan yace miki?"

Cewa yayi wai wannan din dai shine zaka cigaba dasha.."

Shiru yusleem yayi har suka samu adaidaita sahu suka shiga baice komai ba, daidai lokacin da zasu tare keke napep din khadija tsohuwar matar yusleem wacce yasaka last kafin ya auri Hafsat tana cikin motarta tadawo daga makaranta tacikin glass ta hangi wani kamar yusleem parking tayi da niyyar komawa wurinsu amma kafin ta juyo har sun shige keke napep din sun tafi,

Bata hakura ba tabi bayansu acikin motarta, ahankali take binsu ta yanda babu wanda zai gane cewar su takebi har suka shiga layin unguwar da suke,

Tsananin mamaki ne yakama khadija domin har wata zuciyar tana cemata wannan ba yusleem bane yayinda wata zuciyar kuma take gasgatata cewar shine,

Adaidai kofar gidan da suke suka sauka bayan hafsat tabaiwa mai keke napep din kudinshi, hannunshi rikeda na Hafsat suka fito zasu shiga ciki, saurin fitowa daga cikin motarta khadija tayi tabisu da sauri,

Dakin da suka shiga ta tasamma shiga domin yau ta rantse kuma ta dauri aniyar sai taga kwakwaf,

Suna shiga cikin dakin akan katifa suka yada zango, tunani Hafsat takeyi shin tafadawa yusleem yanda sukayi da dr sufyan ko tayi shiru saboda bata san abinda zaije yazo ba sannan bata son kuma tayi shiru wani abun yasake bullowa tarasa mafita,

Kanta taji yusleem yana shafawa ahankali yana yimata magana,

"Wai meke damunki ne?"

Kakaro murmushin dole tayi ta kalleshi,

"Babu komai yaya yusleem kawai dai nagaji ne"

Kafin wani acikinsu yakara magana tuni muryar khadija ta karade cikin kunnuwansu wacce ke tsaye akofar dakin tana doka musu sallama, Hafsat ce ta amsa sallamar sannan tatashi daga jikin yusleem inda take kwance ta tafi duba ko wacece ke sallamar domin ita duk atunaninta ma daya daga cikin yan hayar gidanne ke sallamar......




*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*

*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_

*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_

_Dedicated to MISS XOXO_

*38*

***Kallon mamaki Hafsat ke yiwa khadija lokacin da ta fita kofar dakin domin ganin ko wacece ke sallama ganin khadijan yasata shiga cikin mamaki domin bata taba ganinta ba,

Dan gyara tsayuwarta kadan khadija tayi bayan ta zubawa Hafsat idanuwanta tana yimata kallon kurulla domin tun daga kafarta tafara kallonta har zuwa samanta,

"Baiwar Allah wakike nema?" Hafsat ta katse shirun nasu ta hanyar tambayar khadija,

"Ammm yusleem nagani shine nabiyoshi saboda ina son yin magana dashi.."

Shiru Hafsat tayi kafin tasake yin magana,

"Ok to amma daga ina kike kuma wa zance mishi?"

"Anan garin nake, kice mishi khadija mu'az ce.."

"To ina zuwa.." Hafsat tace tareda juyawa takoma cikin dakin,

Bin dukkan lungu da sako na gidan khadija keyi da kallo tana mamakin yanda akayi har yusleem yake iya yin rayuwa acikin wannan gidan na haya wanda babu komai na alatun more rayuwa aciki,

Acan cikin daki kuwa koda Hafsat takoma wurin yusleem zama tayi agefenshi gabanta yana faduwa,

"Yaya yusleem watace tazo nemanka wai sunanta khadija.."

Dan damm taga yayi kafin ya yunkura yatashi zaune,

"Yanaji kayi shiru ko akwai matsala ne? Ni tsoro nakeji kar asirinmu ya tonu,kar taje tafadawa mami.."

"Babu abinda zai faru insha Allah, ki shigo da ita"

Tashi Hafsat tayi ta sake lekawa inda khadija ke tsaye tana faman touching din phone dinta,

"Yawwa bismillah shigo.."

Tare suka shiga cikin dakin, ganin yanda dakin yake awani takure yasa khadija sake shiga cikin tsananin mamaki,

"Yusleem... Dagaske kaine anan? Me yafaru? Lafiya kuwa? Me yakawoka rayuwa a irin wannan gidan?"

Duk wadannan tambayoyin khadija ta jero sune cikeda mamaki lokacin da take yunkurin zama akasan carpet din dake dan shimfide agaban katifarsu,

"Yusleem wai dagaske kai dinne kodai idanuwana ne kemin gizo.."

"Khadija nine nan.." Yusleem yabata amsa yana kallonta,

Jijjiga kai tayi tagyara zamanta,

"To meya faru dakai har kazo nan? Saboda ni ban san wani abu yafaru dakaiba domin ko jiya agida da yamma muna tareda mami agidanmu.."

"Khadija wata matsala aka samu babba wadda ta tilasta min dawowa nan.."

"Amma dai mami bata saniba ko?"

"Ehh to gaskiya ban bari tasani ba har yanzun nan danake yimiki bayani saboda wani dalili.."

"To amma yusleem meyasa zakazo nan wurin kazauna? Irin wannan rayuwar sam bata dace dakai ba, dubi yanda duk kabi kasauya ka dawo wani kala..."

Murmushi yusleem yayi,

"Khadija kenan kin san dai ai komai yana faruwa ne da dalili, kawai dai ki kalli wannan a matsayin wata kaddara wacce take tawa kuma dole saita sameni.."

Jijjiga kai tayi,

"Hakane, to Allah ya rufa asiri.. Sannan insha Allah nayi alkawari zan baka gudun mawa dari bisa dari acikin rayuwarka.."

"Nagode khadija amma ni babu wata gudun mawa da nake nema daga gareki.."

Jin abinda yace yasa Hafsat saurin kallonshi, tashi khadija tayi tai musu sallama tafita, har kofar daki hafsat ta rakata bayan taga fitarta ne takoma wurin yusleem,

"Yaya yusleem gaskiya banji dadin abinda kafada ba, ai ni sai nake ganin ko babu komai wanda ya nuna yanayi dakai yafi..."

Bai barta takarasa ba yajata jikinshi ya rufe mata baki da hannunshi yana kallonta,

"Nanah akwai dalilin dayasa kikaji nafadi haka, wallahi ba dan Allah khadija zata taimaka mana ba, akwai wata manufa atare da ita.."

"Taya kasani?"

"Saboda khadija matatace ada, saida muka rabuda ita sannan na aureki.."

"To ai ba lallai bane abinda kake zargi yazama gaskiya ba, nidai dan Allah idan tasake dawowa next time karka yi mata irin wannan.."

Kura mata ido yayi saboda jin abinda tafada, lallabashi takoma yi har ya amince,

Washe gari da safe misalin karfe 11 saiga khadija tasake dawowa gidan lokacin hafsat na gyarawa yusleem farcenshi, da fara'a Hafsat ta karbeta suka gaisa, fuskar yusleem kuwa babu yabo babu fallasa,

Cigaba da yimishi gyaran farcen Hafsat tayi yayinda ita kuma khadija ta zauna tana kallonsu aranta tana tunanin yanda akayi har Hafsat tasamu irin wannan damar awurin yusleem domin abisa dukkan alamu tasamu fada mai girman gaske awurinshi sabanin su da ko kallo basu isheshi ba lokacin da yana tareda su,

Ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta kalli yusleem wanda idonshi ke kan hannayensu shida Hafsat wanda ta rike nashi cikin nata acikin zuciyar shi kuwa dan murmushi yakeyi saboda ganin yanda kalolin fatarsu guda biyu ta hadu tashi fari tata kuma bak'a,

"Uhmm yusleem dama cewa nayi bari nabiyo na dubaku saboda naga kamar baka da lafiya ko? Domin duk ka sauya"

Kafin yayi magana Hafsat ta amsa,

"Ehh wallahi zazzabi yake fama dashi amma hakanma da dan sauki.."

"Ayya Allah yakara bashi lafiya.."

"Amin.."

Kallo na tsanaki khadija ta rinka bin dakin dashi aranta tana mamakin tayadda akayi wai yusleem yadawo haka duk da cewar jiya yayi mata bayani amma gaskiya har yanzu bata gamsu da bayanin dayayi mata ba duba da irin tarin dukiyarshi da matsayinshi ada,

Mikewa tayi tsaye tana murmushi,

"Yawwa bari naje na tafi sai wani lokacin idan nadawo.."

Cikeda fara'a Hafsat ta kalleta,

"Zaki tafi? To mun gode madalla Allah yasaka da alkhairi.."

"Nagode khadija, sai anjima" yusleem ya fada yana damke hannun hafsat acikin nashi, fita khadija tayi tana fita yusleem yaja hafsat jikinshi yana murmushi, lakuce mata hanci yayi,

"Yau fa banga kinci abinci ba?"

"Kaima ai bakaci ba, gara ma ni amma kai yaushe rabonka da abinci"

Murmushi yayi ya matse kanta akan kirjinshi tayanda har tana iya jiyo bugun zuciyarshi,

"Hafsat wani tunani nafara gameda ke da rayuwarki..., ni ina ganin kodai in sawwake miki ne kitafi gidanku kije kici gaba da rayuwarki cikin kwanciyar hankali saboda nasan na takura rayuwarki da yawa ba kadanba..."

Jin abinda yafada yasa gabanta mummunan faduwa bayan zuciyarta ta harba da karfi, dagowa tayi ta kalleshi idanuwanshi sun danyi ja kadan, ganin ta kura mishi ido abinda bata taba yiba yasashi sake mayar da kanta ya kwantar bisa kirjinshi,

Daga shi har ita shiru sukayi babu wanda ya iya cewa uffan domin kowa da abinda yake sakawa acikin ransa.

Abangaren khadija kuwa bayan tafita daga wurinsu yusleem tafi minti goma sha biyar tana tsaye ajikin motarta takasa shiga, tunani take anya kuwa yadace tabar yusleem acikin wannan halin?

Girgiza kai tayi,

"Am sorry yusleem dan gaskiya yazama dole nasan abinyi..."

Shiga motarta tayi tai mata key tafita daga unguwar, fitarta keda wuya bata zame ako inaba sai gidan mami mahaifiyar yusleem, cikin sa'a kuma mamin na gida bata fita ko inaba,

Lokacin da khadija ta shiga kawataccen falon na mami mamin na cikin bedroom dinta tana shiryawa kamar me shirin zuwa unguwa, jin sallamar khadija yasata fitowa falo,

Kallo khadija ta dan bita dashi, tana sanye cikin wani swiss les dan gaske golden colour sannan tasaka sarka da earrings da warwaro duk golden gashi tasha jan lalle kai idan kaganta bazaka taba cewa ta ajiye samarin yara ba,zama mamin tayi tana murmushi saboda ganin khadija......

_Fans kuyi hakuri da wannan please,ina cikin hidima ne..._

*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_



_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_


_DEDICATED TO MISS XOXO_


*Sakon fatan alkhairi gareku members na haske writers asso fans, this page is for u...*




*39*



***Gaisar da mami khadija tayi bayan sun gaisa ne khadijan tafara tunanin ta inda ya kamata ta bullowa da mami maganar yusleem, zuwa can dai ta dan nisa tace,

"Mami nikuwa yusleem yana kasar nan..?"

Murmushi mami tayi,

"Yusleem baya nan khadija, nikaina rabon da inyi magana dashi kota wayane anjima, daga yin tafiya shikenan shine har yau..."

Jijjiga kai khadija tayi,

"Ai kuwa Mami naga yusleem, yana nan agarin nan babu inda yaje domin naganshi da idona kuma har magana munyi dashi jiya da yau, yanzu ma daga wurinshi nataho nan.."

Mamakine ya bayyana akan fuskar mami,

"A ina kika ganshi khadija? Yaushe yadawo..?"

"Ai dama mami babu inda yusleem yaje yana cikin garin nan kawai dai wurin zama ya sauya, agaskiya mami na tausayawa halin da naga yusleem aciki.."

"Meya sameshi khadija? Dan Allah fada min idan wani abune ya sameshi" mami tayi maganar cikin rudewa,

"Ba wani abun tada hankali bane mami, kawai dai muje inkaiki gidan da yake ki ganshi da idonki.."

Da hanzari mami ta tashi tashiga bedroom dinta ta dauko mayafi ta fito jikinta har wani yar tsuma yake saboda taraddadin halin da zataje taga yusleem aciki,

Acikin motar khadija suka fita, ganin irin yanayin unguwar da khadija ke kokarin shigar dasu yasanya mami fara kokwanton anya kuwa khadija yusleem dinta tagani kuwa? Kasa hakuri mamin tayi har saida tayi magana,

"Khadija anya kuwa idanuwanki sun gane miki gaskiya?, me yusleem zaizo yayi anan? Sannan tayaya za ace waima yadawo kasar nan amma ni a matsayina ta mahaifiyarshi inkasa sani..."

"Mami ai magana kam takare tunda gamu munzo kofar gidan da yusleem ke ciki, zaki ganewa idonki komai"

Shiru kawai mami tayi amma bawai dan ta yarda da khadija bane a'a sai dan dai kawai ba abokiyar yin mahawararta bace shiyasa bazata yita jayayya da itaba,

Bude kofa kowaccensu tayi ta fito daga cikin motar, nan suka tasamma cikin gidan gadan gadan bayan khadija tarufe motarta,

Wani mamakin ne yasake lullube mami lokacin da suka shiga cikin gidan saboda yanda taga tsarin gidan yake dakuna ratata banda kaca kacan da gidan yayi sannan ga mata nan atsakar gidan kowacce tana harkar gabanta, watama ko riga babu saiko daurin kirji,

Kofar dakin da su yusleem suke khadija ta karasa dasu suka tsaya khadija tafara doka sallama,

Cikin barcin da ya daukesu sama sama kunnuwansu suka fara amsar sallamar da khadija keyi,

Hafsat ce ta dan bude idonta gamida sake kankame yusleem wanda take kwance ajikinshi,

Jin ansake kwada sallamar da karfi yasanyata tashi tana jan dan karamin tsaki, shi kanshi yusleem din shima baiji dadin wannan katse mishi baccin da akayi ba, juyi yayi yasake gyara kwanciyarshi ita kuma Hafsat ta dauki dan kwalinta tafita,

Tana yaye labulen tayi arba da mami da khadija wadanda ke tsaye akofar dakin, tamkar acikin mafarki haka Hafsat tagani, take kuma gabanta yashiga faduwa,

Tunda mami taga Hafsat tasan abinda khadija tabata labari gaskiyane dan haka yanzu bata da sauran kokwanto kuma,

Cikin rawar baki Hafsat tace,

"Mami..."

"Na'am Hafsat, ashe dagaske kuna nan kuna rayuwa batare da sanina ba..?" Mami tayi maganar cikin sanyin jiki,

"Mami shigo daga ciki"

Shiga cikin dakin mami tayi bayan tacire takalminta, cikeda mamaki take bin kowacce kusurwa ta cikin dakin da kallo wanda take ganinshi kamar dakin girki irin na kauye,

Har lokacin da suka shigo yusleem baisan cewar mami bace domin baccinshi yakeyi hankali kwance amma jin maganarta yasashi juyowa da sauri bayan yatashi,kallon mamin yakeyi fuskarsa dauke da mamaki gamida al'ajabi,

"Mamie..." Yakira sunanta yana mutsutstsuke ido,

"Yusleem wacce zuciyarce tabaka wannan mummunar shawarar har kazo nan kake rayuwa batare da sanina ba? Meyasa zakayi min karya?"

Wadannan sune tambayoyin da mami ta jefo masa batare da ta amsa kiran da yayi mata ba, fuskarta kunshe da fushi da bacin rai take kallonshi.......




*_Ummi Shatu_*πŸ‘ŒπŸ»
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twinsπŸ’žπŸ˜πŸŒΉ: Β© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_





*ALWASHI...!*πŸ’
_(Labarin Hafsat)_




_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_



_DEDICATED TO MISS XOXO_




*40*




***Rasa abinda zaice yusleem yayi illa kallon mamin da yakeyi wadda itama shi take kallo kafin daga bisani ta mayar da kallonta kan Hafsat wacce ta sunkuyar da kanta kasa,

Dakin nasu mami takoma tafara kallo kusurwa bayan kusurwa,

"Mami dan Allah kiyi hakuri wallahi akwai kwakkwaran dalilin da yasa kikaga hakan tafaru, zamuyi miki bayanin komai...." Hafsat tayi karfin halin yin magana,

Mami bata bawa Hafsat amsar maganarta ba illa sake balbale yusleem da fada da tayi,

"Ka dauko yarinyar mutane kazo ka ajiyeta anan kana wahalar da ita, dubi yanda takoma, kalli kaima yanda ka zama duk kabi ka rame kayi baki daga gani kana cikin mawuyacin hali, to da ace khadija bata ganku taje ta fada minba da sai yaushe zaku nemeni? Da sai ka kashe musu 'ya sannan zakaje min da mummunan labari? Yayi kyau"

Mikewa mami tayi ta kalli khadija wacce ke zaune ta sunkuyar da kai tana sauraren duk abubuwan dake faruwa,

"Tashi mu tafi khadija"

Kallon yusleem mami tayi,

"Kai kuma na baka nanda mintuna 20 ku tattaro duk kayanku kuzo gida ku sameni, idan kuka wuce haka to ina mai tabbatar maka ranka sai ya baci.."

Fita mami tayi daga cikin dakin khadija ta rufa mata baya,

Kallon yusleem Hafsat tayi bayan mami tafita,

"Yaya yusleem katashi mu bita, idan munje gidan sai muyi mata bayani atsanake kaga kamar fa tayi fushi..."

Dafe kanshi yayi wanda ke yimasa wani irin ciwo,

"Kibari kawai muci gaba da zama anan idan ta huce sai muje mu bata hakuri"

Girgiza kai tayi bayan ta rike hannunshi cikin nata,

"A'a yaya yusleem, mubi umarninta mu tattara kayanmu muje, bai kamata muyi watsi da maganarta ba.."

Tashi tayi batare da tajira abinda zaiceba ta shiga tattara kaya dama kuma kayan ba wadansu masu yawa bane, cikin toilet ta shiga ta kwaso inner wears dinsu dake shanye tazo ta zuba acikin trolley, har lokacin yusleem na zaune baiko motsa ba,

Kayan da tasan bazai yiyu su tafi dasu yanzuba ta tattara wuri daya ta adana sannan tafita daga dakin taje dakin maman amir tayi mata sallama, kasancewar sunyi sabo maman amir harda kuka, ita kanta Hafsat din da hawaye tadawo cikin dakin,

Tashi yayi ya rungumota jikinshi yana murmushi,

"Menene na kukan kamar ance bazaku sake haduwa ba..., sorry.."

Har lokacin hawayen basu bar zuba a idonta ba,

"Ya isa haka, kiyi shiru dan Allah"

Dakyar ta iya tsayar da hawayen yusleem ya dauki trolley dinsu suka fita acikin ranshi yana mamakin mata su babu wuya yanzun nan zasuyi maka kuka,

Har waje mutanen gidan suka rakasu duk da ba wai wani zumunci mai zurfi sukeyi ba,

Adaidaita sahu suka shiga yakaisu har gidan mami,

Gidan yana nan kamar da babu abinda ya sauya sannan ga ma'aikata nan kowa yana aikinsa kamar yanda suka saba, ganin su yusleem yasa masu gadin gidan saurin amsar kayan dake hannunsu suka shigar musu dashi ciki,kowa sai sannu da zuwa yake yiwa yusleem domin duk atunaninsu daga doguwar tafiya yadawo,

Acikin falo suka iske mami tana zaune tana shan ruwan lipton sannan ga soyayyen chips with kidney sos tana dan tsakura kadan kadan tana ci da dukkan alamu sai yanzu take yin breakfast,

Jin sallamarsu yasanyata dagowa ta kallesu bayan ta amsa, akasa Hafsat ta zauna yayinda yusleem yazauna akujerar dake kusa da ta mami,

"Hafsa ga abinci can maza tashi kije kici kinji..."

"Wallahi mami munci abinci sai dai idan anjima.."

Shiru mamin tayi batace komai ba taci gaba da kurbar ruwan tea dinta, suna nan zaune shiru babu wanda yasake magana har mami ta kammala cin abincin,

Sunkuyar da kai Hafsat tayi tasoma bawa mami hakuri,

"Mami dan Allah kiyi hakuri da abinda yafaru, wallahi ba laifinsa bane laifina ne domin nice nabashi wannan shawarar kuma nima nayi hakanne dan gudun kada mu tayar miki da hankali, amma dan Allah kiyi hakuri.."

Ajiyar zuciya mami tayi ta kalli yusleem sannan ta kalli Hafsat,

"To shikenan Hafsat nahakura, amma meyake faruwa? Nasan dai duk yanda akayi akwai abinda ke faruwa daku"

"Ehh mami da akwai, bashin banki yaya yusleem yaci sukuma kin san dokarsu idan baka biyasu ba sai sun sayar da komai naka, to shima yaya yusleem din hakance tafaru kuma lokacin nasan idan kikaji hankalinki tashi zaiyi shiyasa nace mubari tukunna sai zuwa wani lokaci sai mu fada miki..."

Tafa hannuwa mami tashiga yi tana salati,

"To garin yaya?"

Kallon yusleem tayi,

"Kai agarin yaya kaciyo bashin banki batare da sanina ba?"

"Mami tsautsayi da kaddara, saboda dama tun asali da wannan bashin nasu nayi arziki, komai da kika sani nasune, nikuma nayi hakanne dan incika burinki inzama mai wadata kamar yadda kike muradi..."

Katse shi mami tayi cikin fada tace,

"Ungo nan.." Dakuwa tayi masa sannan ta dora da cewa,

"Shikenan kuma dan ina son kayi arziki sai kaje ka aikata ba daidai ba? Ai ni bance kayi kudi kota halin kaka ba, haba yusleem meyasa zakabi shawarar zuciya? Ko dan gaba karka sake aikata makamancin wannan, yanzu da ace sun kamaka sunje sun daureka me gari yawaya?"

Dan zamewa yayi ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya lumshe idanuwansa,

Kallon Hafsat mami tayi,

"Bashida lafiya ko?"

"Ehh mami amma da sauki, matsalar dai baya iya cin abinci"

Shiru mami tayi ta danyi tagumi,

"Hakika wannan wata jarrabawa ce daga Allah, domin ni dinma duk kudaden dake cikin account dina na turawa yan makaranta domin sun kusa dawowa, gashi na sissiyo kayan abinci wadanda zasuyi mana 1 month,ma'aikatan gidan nan ma wallahi wannan watan ko albashi ban biyasu ba nace suyi hakuri sai yusleem yadawo.."

"To ai babu komai mami duk wannan ba wani abu bane Allah zai bamu mafita" inji Hafsat,

"To hafsa rashin lafiyar tashifa? Ni duk ita tafi daga min hankali"

"Mami babu komai insha Allah zai samu lafiya, gobe zamu sake komawa asibitin ma ayi masa test..."

"To wai menene ke damunsa?" Mamin ta tambaya cikin damuwa,

"Mami harda ulcer dai saboda baya cin abinci wallahi"

"To Allah yabashi lafiya, goben sai muje asibitin mugani"

Shi dai yusleem yana jinsu baiyi magana ba da zaman kujerar ya isheshi ma dakin surayya yashiga wanda yake makotaka da na mami yaje ya kwanta akan gadonta,

Ita kuma mami afalo duk tabi ta damu sai jajanta rashin lafiyar yusleem takeyi, Hafsat dince ma mai karfin halin kwantarwa da mamin

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment