Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana kallon mai gidan nata wanda ke zaune kusa da ita,

"Haba Alhaji, dole nayi kuka ai, yanzu bazan sake ganin amal ba sai nanda shekara daya.."

"Haba hajiya kubra sai kace yarinya, ya kike abu irin na yara ne, ai naga ga waya nan akoda yaushe zaku rinka gaisawa.."

Cigaba da kukanta tayi bata amsa ba, yana shirin sake yi mata magana wayarshi dake aljihunsa tafara ringing nan yacirota yaduba, ganin Wanda ke kiran nashi yasashi saurin mikewa yana kallonta"

"Hajiya kubra ina zuwa, Alhaji Abubakar ne yazo,dama munyi dashi zaizo yanzu, ina zuwa"

Bai jira amsarta ba yayi azamar ficewa daga cikin bedroom din nata yafita zuwa part dinshi...



*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to MISS XOXO_




*10*


aishaummi.blogspot.com



***Amininshi Alhaji Abubakar ya hango tareda tawagarsa masu rufa masa baya domin ayanzu haka aminin nashi shine ke rike da mukamin mataimakin gwamna na wannan jiha,

Hannu Alhaji Sa'id yabawa Alhaji Abubakar tareda janshi zuwa cikin falonshi,

"Ya banga uwar gidan ba, ko taje unguwa ne?" Alhaji Abubakar ya tambaya cikin raha,

"Ai hajiya kubra yau zuciyar tata babu sauki ranka ya dade domin kuwa tunda amal tabar gidan nan ta tafi kasar India karatu jiya shikenan hajiya ta rasa sukuni acikin ranta.."

"Allah sarki, kasan ai rabuwa da d'a sai dole balle ma ita da bata da wasu yayan sai iya amal.."

"To amma ranka yadade ba hakuri akeyi ba? Dukkan al'amarin duniya ai hakuri akeyi,idan ma amal bata tafi wata kasar karatu ba to nan gaba wani garin zata tafi aure, kaga kuwa ai babu amfanin sakawa zuciya damuwa tunda ita mace ansan cewar komin daren dadewa zata bar gida..."

"Hakane Alhaji sa'id, abin dai sai hakuri kasan lamarin mata, yawwa kafin in manta, dama abinda yasa kaga nazo yanzu shine so nake kayi min rakiya zuwa wani wuri, amma ba jimawa zamuyi ba, yanzun nan zamu dawo.."

"Atoh indai hakane ina zuwa, bari inje in sanar da kubra cewar nafita, ina zuwa"

"Amika min gaisuwa dan Allah" inji Alhaji Abubakar,

Fita Alhaji sa'id yayi zuwa part din matar tashi wato hajiya kubra, tana zaune kamar yadda yatafi yabarta tana sharar hawaye,

Hakuri yasake bata sannan yayi mata sallama yafita,

Acikin mota akan hanyarsu Alhaji Abubakar ya dubi aminin nashi yace,

"Ni da sai nake ganin kamar inhada kayan inkaiwa wasu mutane daban magidanta wadanda ke fama da talauci"

"A'a ranka yadade, gidan marayun dai ya kamata mukai domin suna bukatar taimako mutuka, sannan kaga ni ina ganin gidan yari ma (jail, prison) suma suna bukatar taimakon ku domin suma suna cikin wani hali, ya kamata arinka taimaka musu da barguna da kayan sanyi idan lokacin sanyi ne, idan kuma da zafi ne shima arinka duba abinda yafi cancanta da ataimaka musu dashi.."

Murmushi Alhaji Abubakar yayi,

"Hakane Alhaji sa'id, agaskiya ka Kawo shawara mai kyau kuma mai amfani shiyasa akoda yaushe nake farin cikin kasancewata dakai domin baka bani gurguwar shawara, yanzu abinda za ayi to bari mufara kaiwa gidan yarin ziyara inyaso idan mun fito sai mu karasa sauran wuraren.."

Karya kan motar driver yayi yadauki hanyar gidan yari nan sauran motocin suka rufa musu baya,

Ba karamin kaya aka saukewa gidan yarin ba domin abun tausayi ne idan kagansu gashi suna fama da babu, bayan sun kammala da nan dinne suka kama hanyar zuwa gidan marayu domin suma abasu nasu tallafin,


Su Hafsat suna ta kiciniyar yin sak'a kamar yadda suka saba aka sanar dasu zuwan bakinsu,dukkan yaran dake cikin gidan aka tattara aka kai wurin da mai girma mataimakin gwamna yake,

Bayan ansauke kayayyakin da aka kai musu ne aka jerasu alayi mataimakin gwamna yafara basu sadakar kudi sabbi fifil fifil,

Amina da Hafsat sune akusan karshe domin dama yanmatan ba yawa garesu ba basufi su shida ba,

Dai dai lokacin da Hafsat takarasa dan karbar kudin idon Alhaji sa'id yasauka akanta jin gabansa yayi yafadi nan take zuciyarsa tashiga harbawa da karfi,

Binta yayita yi da kallo har ta karba ta matsa Amina ta maye wurin,

Da hannu ya yafito shugaban ma'aikatan gidan,yana zuwa ya nuna masa Hafsat yace abashi ita zai tafi da ita zuwa gidanshi ma'ana zai cigaba da riketa,

Saida Alhaji Abubakar ya kammala rabawa marayun kudin sannan Alhaji sa'id ya sanar dashi cewar yaga wata yarinya budurwa ya nemi izinin abashi ita zai tafi da ita gidanshi,

Ba ayi wani dogon cike cike ba shugaban gidan marayun yace anbawa Alhaji sa'id hafsat yatafi da ita duba da wanda suka zo tare dashi,

Hafsat da Amina sun dauki hanya kenan zasu nufi wurin da makwancinsu yake taji ana kwala mata kira,

Komawa tayi tabi ma'aikacin gidan wanda aka turo kiranta, suna zuwa shugaban gidan ya kalleta,

"Yawwa Hafsat ke yau Allah yakawo karshen zamanki agidan nan, gashi kin samu wanda zai cigaba da kula dake.."

Kafin tayi yunkurin magana tuni har anbude mata kofar mota saboda har su Alhaji sa'id sun shiga cikin mota, ita kawai ake jira,

Sakin baki tayi nan shugaban gidan ya daka mata tsawa babu shiri tafada cikin motar wacce mutum biyune kacal aciki daga driver sai wani sss guda daya agaban motar,

Babu bata lokaci motocin suka nufi hanyar fita, Amina kuwa kawar hafsa sai shugaban gidan ne yayi mata bayani cewar antafi da Hafsat, kuka Amina tasa domin sunyi mutukar shakuwa komai tare suke yi tun tasowarsu acikin gidan domin kamar kusan lokaci daya ma aka kaisu gidan.


***


Koda Mami takoma gida bata nunawa yusleem cewar anfasa bikin ba shikuma sai faman bata rai yake yana shan kamshi,

Yau ma rai abace yashiga cikin gidan domin yau su khalifa da Abdul zasu dawo daga Malaysia,

Lokacin da yashiga gidan har sun dawo suna falon mami sunyi kaca kaca da kayayyakin tsarabar da suka zo da ita,

"Yaya yanzu muke cewa ko sai munje bikonka ne.." Abdul yafada yana dariya,

Wuri yasamu ya zauna yana kallonsu daya bayan daya, dukkaninsu samarine masu kamarshi sai ko dan banbancin da baza arasaba,

"Yaya lafiya kuwa?" Khalifa yace,

"Kuma dai kun san halin yayanku idan aljanunshi na rashin son magana suka motsa" Mami tafada tana bude dan karamin akwatin dake kan cinyarta wanda su abdul suka taho dashi,

"Yaya gafa babbar tsaraba mun Kawo maka, domin Mami tafada mana ka kusa yin aure.." Inji abdul,

Harara ya aika musu da ita,

"Yaran nan kun rainani ko? Wai ni sa'anku ne?"

"Haba yaya kagafa kayan da muka siyo mukace sai ka kara akan lefen da zaka hada" Khalifa yace yana gumtse dariyarshi,

Baice dasu komai ba ya gimtse fuska ganin haka yasasu fara gaidashi nan ya amsa yana ciccin magani,

Tabe baki Mami tayi,

"Ai sai ka saki fuskarka idan maganar aurece to anfasa.."


D'aga ido yayi ya kalli Mami batare da yayi magana ba....





*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_




*11*


aishaummi.blogspot.com



***Gidan Alhaji sa'id tawagar mai girma mataimakin gwamna suka wuce direct, hafsat tana zaune abayan mota sai zazzare ido take yi domin bata ma san inda suka nufa ba kasancewar ba fitowa sukeyi ba,


Wani kayataccen gida taga sun shiga wanda ya tsaru mutuka fadin girman gidan kuwa bata baki ne,

Bude mata kofar motar akayi tafito tana bin gidan da kallo,

Wurinta alhaji sa'id ya karasa bayan sunyi sallama da aminin nashi wanda tuni har tawagar tashi tafara fita daga cikin gidan,

Atsorace hafsa take binsa da kallo saboda rashin sabo gashi kuma uwa uba bata taba ganinshi ba,

"Zo mu karasa ciki.." Yace da ita lokacin da yakarasa kusa da ita,

Kamar kurma haka tayi domin bata iya amsawa ba illah bin bayanshi da tayi tana mai cigaba da karewa gidan kallo,

Tana biye dashi abaya har zuwa cikin wani hamshakin falo wanda ya kayatu mutuka da kayan alatun more rayuwa,

Tunda suka shiga cikin falon alhaji sa'id yake kwallawa matarshi kira,

"Hajiya kubra.... Hajiya kubra...,hajiya kubra ko bakya kusa ne?"

Amsawar da yaji hajiya kubran tayine ya dakatar dashi daga kwalla kiran da yake yi mata, falon tafito tana magana muryarta adashe saboda kukan da ta dade tanayi,

"Alhaji gani, har kun dawo?"

"Mun dawo kuma munyi farar tafiya tunda harda tsaraba nakawo miki.."

Hafsat ya nuna mata da yatsanshi, ido ta zaro ta bude baki cikeda mamaki domin da lokacin da ta fito sam bata lura da Hafsat dinba sai yanzu da ya nuna mata ita,

"Alhaji a ina kasamo amal? Dawo da ita kasa akayi?"

Dan murmushi alhaji sa'id yayi, "kidai kalleta dakyau kigani.."

"Alhaji ai naganta, amal ce, ai bai kamata kace adawo da itaba tunda karatunta karuwarmu ce gaba daya.., amal meyasa kika dawo?"

"Hajiya kubra wannan fa ba amal bace mai kamada amal ce, ganin kin tada hankalinki kina neman tayar da nawa hankalin shiyasa na Kawo miki ita.."

Sai a lokacin hajiya kubra tafara bin Hafsat da kallo tun daga kafarta zuwa kayan dake sanye ajikinta, ko shakka babu wannan ba amal bace amma kuma bata da banbanci da amal din sai ko gayu da wayewa wadda amal din zata fita dashi amma hatta kalar fatarsu da komai iri dayane kawai hutu da jin dadi fatar amal zata nunawa ta Hafsat,

"Ikon Allah baya karewa,tabbas wannan babu abinda zai hanani karbarta a matsayin amal domin kamar tasu ta isa.." Hajiya kubra tafada tana takawa har izuwa wurinda Hafsat ke tsaye nan tashiga kare mata kallo,

"Yawwa tunda bukatata tabiya shikenan dama burina ki cire damuwar dake ranki akan amal ki karbi wannan amadadinta"

"Alhaji ina kasamo min ita? Wallahi yarinyar nan batada maraba da'yata.."

"Hajiya kubra zanyi miki bayani daga baya saboda kinga yanzu lokacin sallar magrib yakawo kai, amma abinda nake so dake shine wannan yarinyar nakawo miki ita amana duk da cewar nasan zaki kula da ita tamkar yar da kika haifa saboda tayi kama da jininki amal, yanzu kije kibata duk abinda ya kamata.."

Narai narai da ido hajiya kubra tayi ta kalleshi,

"Amma dai alhaji ba aro aka bani itaba ko? Saboda bana son itama kwana biyu azo ace za arabani da ita"

"Kisha kuruminki hajjaju wannan yarinyar babu abinda zai rabaki da ita domin tazama'yarki halak malak.."

Farin cikine ya bayyana akan fuskar hajiya kubra wanda har saida takasa boye hakan,

"To alhaji, amma naji dadin wannan maganar,nayi mutukar farin ciki.."

Juyawa yayi yanufi kofar fita, cikin farin ciki hajiya kubra ta kama hannun Hafsat tana kallonta,

Tana rikeda hannunta har suka fice daga cikin falon suka shiga wani tafkeken dakin bacci wanda ke dauke da Italian bed pink colour,haka komai na cikin dakin kalarshi pink domin hatta bed sheet din dake shimfide akan gadon pink colour ne,

"Ya sunanki?" Hajiya kubra ta tambayi Hafsat har lokacin tana rikeda hannunta,

Sai a lokacin Hafsat tayi magana tun shigowarta gidan,

"Sunana Hafsat.." Tabata amsa,

"Hafsat, kamarku daya da tilon 'yata kwaya daya amal shiyasa lokacin da naganki naji ina sonki har cikin zuciya..., nan dakinta ne ina so ki daukeshi a matsayin naki, kiyi amfani da duk wani abu wanda kika ganshi acikin dakin nan ko kuma cikin gidan nan.."

Sakin hannunta hajiya kubra tayi tajuya tafita, kan Hafsat adaure tafara bin dakin da kallo tana yaba irin haduwar da yayi domin kamar akasar turai, kan gadon ta kalla nan taga wasu jibga jibgan teddies guda biyu a jingine, kan mirror din dake cikin dakin kuwa kayan make up ne jere tamkar wani dan karamin shago,

Kananan frames ta hango guda hudu ajiye akan bedside drewar nan ta nufi wurin domin tahango kamar akwai hoton wata budurwa ajiki, nan ta nufi wurin da Sauri......




_*Ummi Shatu*_๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_



*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_




*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_



*12*


aishaummi.blogspot.com



***Gaban frames din hafsat ta karasa da sauri ta mika hannu ta dauki guda daya ta kura masa idanuwa tafara kallo,

Gabanta ne yafara faduwa zuciyarta tana bugawa da karfi da karfi Wanda har saida ta kaita da zama asaman gadon dake gefenta,

Ko shakka babu badan rayuwarta agidan marayu tayita ba to da zata iya yarda da cewar wannan ta jikin hoton itace, sake kallon hoton tayi akaro na biyu wanda yarinyar jiki ke sanye da english wears pink din riga da farin wando, kanta sanye da hula pink colour,

"Ikon Allah..." Tafada ahankali tana mai sake dauko wani hoton tafara kallo, nan ta lalace wurin kallon hoton batare data kosa ba.


Kasa koda zama hajiya kubra tayi illah kaiwa da kawowa da take ta faman yi dan tsananin farin ciki, tabbas wannan wani al'amari ne daga Allah Wanda shi kadai yabarwa kansa sani,

Ganin zama yagagara yasata fita ta nufi part din alhaji, shima shigowarsa kenan daga masallacin dake kofar gidansa,

Zama tayi akan kujerar dake makotaka da tashi,

"Alhaji nidai kaganni tsabar farin ciki nakasa zaune nakasa tsaye.."

Murmushi alhaji sa'id yayi,

"To in banda abinki hajiya menene abin kasa tsaye da kasa zaune? Yanzu ina ita yarinyar take?"

"Alhaji dole inkasa zaune in kasa tsaye mana,ai farin cikin da nake ciki bazai barni inyi hakaba, tace min sunanta hafsat, tana can dakin amal nakaita tayi wanka ta shirya sai tafito muyi dinner.."

"Hakan yayi daidai hajiya kubra,nidai abinda nakeso dake shine dan Allah ki rike yarinyar nan bisa amana duk danasan zaiyi wuya ki gallaza mata tunda bata da maraba da amal to amma wani lokacin ku mata ana ganin kamar kunfi kowa tausayi da rauni sai dai akan gallazawa yaran da ba nakuba kunfi kowa nuna rashin tausayi da rashin rauni, dan Allah ki riketa amana tunda kinga daga gidan marayu na daukota wannan yana nuna cewar ita maraya ce..."

"Haba alhaji ai basai kayi min wannan nasihar ba domin ko wanine yakawo min wannan yarinyar wanda bakai ba wallahi zan kula da ita..."

"Nasani hajiya kubra, Allah yayi miki albarka, yanzu ina tunanin ai tagama ko?"

"Ehh to bari indubo ingani"

Tashi tayi tafita takoma part dinta, dakin amal ta tura tashiga nan ta iske hafsat zaune ta kurawa hotunan amal ido ko kifawa bata yi,

"Hafsat..." Ta kira sunanta bayan takarasa kusa da ita, dagowa hafsat tayi ta kalleta,

"Na'am"

"Ya bakiyi wanka kin canja kayan jikinki ba? Tashi ki shiga bathroom kiyi wanka indan kin fito ga drewar din kayan amal nan ki duba duk wanda yayi miki kisaka.." Ta karasa zancen tana nuna mata drewar din da dan yatsanta,

"To" hafsat ta amsa har lokacin tana cike da mamaki domin ganin abubuwan dake faruwa take yi tamkar acikin mafarki,

Fita hajiya kubra ta sake yi ganin haka yasa hafsat tashi ta shiga cikin bathroom din, komai wanda ake bukata akwaishi acikin bathroom din babu bata lokaci tayi wanka ta fito, man da zata dan shafawa fatarta ta shiga nema domin duk wadanda ke kan dressing mirror din lotion ne dan haka dakyar tasamu wani me dan kama da Vaseline tashafa,

Gaban drewar taje ta bude nanfa mamaki yacikata domin kayane iya ganinta shake acikin drewar din,

Wata doguwar riga kalar ruwan hanta ta zaro da dan kwalinta tasaka ta dauki hijabinta tayi salla,tana saman abin sallar azaune a inda aka kebe musamman domin yin salla hajiya kubra tasake shigowa fuskarta dauke da murmushi,

"Hafsa kin idar ne?" Tajiyo muryar hajiya kubra na tambayarta,

"Ehh na idar.." Tabata amsa tana kokarin mikewa,

"Yawwa to taso kizo muje wurin alhaji"

Bin bayanta tayi suka fita, tiryan tiryan tana biyeda ita har suka shiga falon alhaji sa'id Wanda ke zaune yana kallon labarai a tauraron dan adam,

Ganinsu yasashi rage volume din tv din ya fadada murmushinsa yana kallonsu domin sai yake ganin kamar hajiya kubra ce da amal suke dososhi kamar yadda suka saba akowanne dare domin yin hira,

"Alhaji...,labarai kake kallo?"

"Wallahi kuwa hajiya, keda 'yar takine?"

"Ehh amma har yanzu dai banga alamar zata sake ta saki jiki damu ba saboda ganinmu take baki agareta" hajiya kubra tafada fuskarta da yar damuwa,

"To wannan kuma dama ai sai ahankali,kin san ai yau tafara ganinmu,sai asannu ko Hafsat?" Yakarasa zancen cikin barkwanci,

Hafsat kam shiru tayi takasa koda kallonsu, sai dai wani lokacin ta dan saci kallonsu ahaka har lokacin sallar isha yayi nan alhaji sa'id yafita masallaci yabarsu a cikin falon nashi,

Anan Hafsat da hajiya kubra sukayi sallarsu,suna nan zaune har alhaji sa'id yadawo dan haka hajiya kubra ta mike domin gabatar musu da abincin dare,

"Hafsat zo muje kitchen.."

Mikewa Hafsat tayi suka fita zuwa cikin kitchen wanda kallo kawai Hafsat ta bude ido tanayi saboda ita ba taba ganin irin shi tayiba,

Akan babban faranti hajiya kubra ta jera flasks din abincin nan Hafsat din ta karba ita kuma hajiya kubra ta debi filet da sauran abubuwan da suka kamata,

Zama Hafsat tayi bayan ta ajiye farantin, acikin dan madaidaicin filet hajiya kubra ta zuba musu abincin, tuwon semo miyar danyar kubewa,

"Hafsat zo muci abincin.."

Matsawa hafsa tayi tasa hannu ita a zatonta iya ita da hajiya kubran ne kadai zasuci amma sai taga sabanin haka domin shima alhajin saka hannu yayi saboda al'adarsu tare suke cin abincin tare dashi da hajiya da amal, Hafsat ji tayi kaunarsu ta fara darsuwa acikin zuciyarta, duk da cewar taki dan sakin jiki dasu amma hajiya kubra sai sakota take acikin hirar tasu dahaka suka kammala cin abincin.

Suna falon alhaji sa'id azaune har misalin karfe 9 nadare lokacinne hajiya kubra ta mike ta kalli Hafsat,

"Hafsa taso muje ki kwanta naga kamar bacci kikeji ko?"

Dan murmushin yake Hafsat tayi ta tashi ta kalli alhaji sa'id,

Dan rissinawa tayi, "Alhaji saida safe"

Cikeda fara'a ya amsa tabi bayan hajiya kubra suka fita,

"Abba zaki rinka cewa alhaji kinji, nikuma ummi saboda haka amal ke kiranmu, kinga tunda yanzu kema mune iyayenki.."

Hajiya kubra tace da ita akan hanyarsu ta zuwa part dinta,

"Tohh Ummi.."

Dadi hajiya kubra taji jin Hafsat ta kirata da Ummi,

Sai da safe Hafsat tayiwa hajiya kubra tashiga daki,zama tayi akan gado tana mai bin dakin da kallo.....




*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



_*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to MISS XOXO_



*13*



aishaummi.blogspot.com



***Kasa bacci Hafsat tayi illa tunanin rayuwarta da take ta faman yi,

Ji tayi kamar ta fashe da kuka a sakamakon fadowa ranta da kawarta Amina tayi,

Duk da tasan abin atayata farin cikine saboda canjin rayuwar data samu amma duk da haka tana jin radadi acikin zuciyarta na rabuwa da gidan marayu da tayi domin tariga da ta saba da mutanen ciki,

Wadannan tunane tunanen da tarinka yi sune suka hana idonta bacci har aka fara kiran assalatu, a kunnenta aka shiga sallar asubah nan ta tashi tashiga bathroom ta dauro alwala tafito, salla tayi tareda addu'o'i masu yawan gaske, anan inda tayi sallar anan bacci ya kwasheta.

Misalin karfe shida da rabi na safe hajiya kubra ta shiga cikin dakin ganinta kwance tana bacci yasata juyawa tafita batare data tasheta ba domin ta fahimci cewar tayi sallar asubah,

Hafsat dai bata samu damar tashi daga wannan baccin ba mai cikeda mafarkai iri iri wadanda takasa tuno koda guda daya daga ciki lokacin data farka, ba ita tatashi ba sai misalin karfe 10 zuwa da rabi, hajiya kubra kuwa ta leka dakin yafi sau akirga,

Zama tayi tana bin dakin da kallo kamar yanzu ne tashigo ciki, daga bisani ta sauke idonta kasa ta mike, fita tayi acikin falo ta hango hajiya kubra tasha kwalliya cikin wata shadda kamfala tana faman jejjera abin Karin kumallo akan dining table,


Sam hajiya kubra bataji fitowarta ba har saida tayi magana,

"Ummi ina kwana.."

Cikeda farin ciki hajiya kubra ta juyo ganin Hafsat atsugunne yasata kamo kafadunta ta tada ita tsaye tana murmushi,

"Lafiya lau Hafsat, sai yanzu aka tashi? Ai na shisshiga dakin kinata bacci"

Murmushin yake Hafsat tayi,

"Ummi akwai abinda za ayi ne?"

"Kamar mefa Hafsa na?"

"Na aikin gida.."

"A'a Hafsa babu abinda za ayi, har ankammala gyara gidan ai, inada ma'aikata na masu yimin komai da kika sani, girki ne kadai nake yin abuna dakaina, yanzu kije kiyi wanka ki shirya ki fito mu karya lokacin abbanku shima ya fito"

"Toh" ta amsa tareda juyawa takoma cikin daki, wanka tayi ta shirya ta fito zuciyarta cikeda mamaki na irin tarba da soyayyar da hajiya kubra ke nuna mata wadda abisa dukkan alamu zata riketa amana kamar itace ta haifeta,

Atamfa ta saka dinkin riga da zanine pieces kalar atamfar kalar ruwan hoda, hijabinta da tazo dashi tasa ta fita,

Lokacin data fita tuni har su hajiya kubra sun hau kan table suna jiranta, durkuwa tayi tagaida Alhaji sa'id,

Fuska asake ya amsa gaisuwarta yakare maganar da fadin,

"Tashi, tashi, zo ga kujera ki zauna"

Mikewa tayi taje ta zauna akusa da hajiya kubra wacce tafara kokarin hadawa Alhaji tea,

"Hafsa babu wasu hijaban ne akayan amal naga kinata saka wannan?"

"A'a ban duba ba"

"To ai kuwa inajin tabar hijabai dan bata tafi da komai nataba duk agida tabarsu..."

"Ashe yar uwarta tabarwa bata saniba" Alhaji sa'id ya karbe zancen,

Dariya hajiya kubra tayi,

"Ai so nake idan ta sai sim ta kira inyi mata albishir"

"To ai kuwa da dai nine naso inyi albishir dinnan amma naga kina nema ki rigani.."

Dariya sukayi dukkaninsu inbanda Hafsat wacce dan murmushi kawai tayi,

Abinsu gwanin sha'awa suna karyawa suna hirarsu har suka kammala nan Alhaji sa'id ya mike yana gyara babbar rigar dake jikinsa domin wurin aiki zai fita,

"Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" Hafsat tace dashi tana rakube ajikin kujera,

"Amin Hafsat, nidai abinda nakeso dake shine ki saki jikinki ki dauka cewar nan gidanku ne sannan kuma mu iyayenki ne, kinji? Allah yayi miki albarka"

"Amin, amin..." Hajiya kubra ta amsa tana murmushi,

Juyawa yayi yafita hajiya kubra tana biye dashi ganin haka yasa hafsat tattare kayan da sukayi amfani dasu wurin karyawa ta nufi kitchen, tana tsaka da daurayesu hajiya kubra ta dawo daga rakiyar da ta yiwa alhaji,

"Ahh hafsat ai ban sakiba, waye yace ki wankesu? Nafada miki akwai masu aiki zasu yi har wanke wanken"


"Babu komai Ummi nima gani nayi babu abinda zanyi shiyasa nace bari in wanke.."

"To shikenan ai kin kyauta, ke baki da son jiki ba irin amal ba, amal bata son motsi nan da can koda yaushe tana nade akan gado kamar wata mage.."

'Yar dariya Hafsat tayi taci gaba da wanke wanken yayinda ita kuma hajiya kubra taci gaba da bata labari akan amal wannan yasa Hafsat sake fahimtar cewar ba karamin so hajiya kubra ke yiwa yar tata ba domin magana daya biyu sai ta sako zancen amal,

Tsaf Hafsat ta gyare kitchen din bayan ta kammala wanke wanken, falo suka koma suka zauna suka fara kallo atashar tauraron dan adam,

Wannan zaman da suka yi shine yabawa Hafsat damar sakin jiki sosai da hajiya kubra domin ta dan warware suna yin hira har tana bata labarin irin yanda rayuwarta ta gudana agidan marayu.....



_Fatan alkhairi ga masoya masu bibiyar labarin..!._


*_Ummi Shatu_*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป
[6:37PM, 2/1/2018] ~Maman_twins๐Ÿ’ž๐Ÿ˜๐ŸŒน: ยฎ *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_




*ALWASHI...!*๐Ÿ’
_(Labarin Hafsat)_



*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to MISS XOXO_



*14*


aishaummi.blogspot.com




***Sosai hafsat ta sake da hajiya kubra domin hatta girkin rana tare suka yi suka shiryashi akan table saboda alhaji sa'id yana dawowa cin abinci daga office,

Har dare suna tare suna hira afalon alhaji sa'id wanda kusan rabin hirar ta amal ce, yauma kamar jiya atare suka fita ita da hajiya kubra suka yiwa alhaji sai da safe,

Yauma saida tayi karfin hali sannan tasamu bacci ya dauketa domin har lokacin tana kewar gidan marayu da kuma kewar kawarta amina,

Washe gari da safe suna kan table suna karyawa amal ta kira mahaifinta,nan hajiya kubra ta shiga murna domin bakinta yaki rufuwa,

Mikawa hajiya kubra wayar Alhaji sa'id yayi bayan sun kammala gaisawa shida amal din, cikin farin ciki hajiya kubra ta fara yiwa amal albishir na zuwan Hafsat gidan, Hafsat tana zaune tanaji bata dai jiyo abinda amal din taceba kawai dai taga hajiya kubra ta mika mata wayar

2 Comments On ALWASHI
avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

avatar
aliyu-1-5-2

12 months ago

Reply

I appreciate it

Please Login or Register in order to submit comment