Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gudu Salem ma ya taho, mami tsaya kallon ikon Allah tayi, yanmatan gidan har dasu tima da deeja suna tsaye tsakar gidan suna kallon su, don dazu da suka wuce sun gansu, kuma yanzu sun san sir Salem ne, tima so tayi tashiga part din mami amma sauran yan Matan Suka hanata.

Tawa shiga cikin palace tayi, tundaga bakin palace din tayi kneeling tafara rarrafawa har gaban oba, su Abba da OBJ kallon ikon Allah kawaisuke, Salem na tafe bayan ta, tafiya yake ahankali yana kallon yanda take kuka tana crawling kasa, cikin shessheka tafara cewa
"Grandpa.. Nasan shi....I know him...and... I love him... Am...sorry..." Yanda take maganan kaman ranta zai fita yasa oba daga mata hannu, amma batayi shuru ba ta cigaba dacewa
"Grandpa... I love.. Him..." Kai oba ya gyada mata alaman I understand, mami na tsaye bakin fada tana jin abinda tawa take cewa, duk mutanen wurin jikin su yayi sanyi Abba kam kaman zaiyi kuka yakeji, OBJ kam baki ya saki don tunda yake bai taba ganin event din da ya bashi tausayi irin wannan ba, Salem har lokacin bai bar hawaye ba ahankali shima yayi kneeling bayan ta, saida ya goge hawaye shi ya daidai ta murya sannan yafara cewa
"I promise... To take care of her...i will make sure she's happy.... She will be the only gueen of my heart... I will do everything.... For her...." Mami duk tana jin abinda yake cewa oba daga kai yayi ya kalleta
"History is repeating itself..." Oba ya fada cikin ranshi, kallon tawa da Salem yayi
"Ni ba dangin uban Tawakaltu bane...am amatsayin na na sarkin gari da kuma grandpa dinta...na baka Tawakaltu..." Da sauri OBJ da sauran mutane suka kwanta kasa suna godiya, shima Salem kwantawa yayi, duk yanmatan gidan suna tsaye bakin window suna kallon kuma suna jin abinda ake cewa, dukkan su ihu suka fara suna tsalle, tima hannu tasa bayan kunnenta kaman tana sauraron wani few seconds later tace
"I can hear a wedding bell ringing.." Dukkan su ihu suka karayi, jikin mami ba kwari ta bar bakin palace ta koma part dinta, dukkan mutanen komawa sukayi suka zauna, ahankali Salem ya mike yakara kneeling, har lokacin tawa bata tashi ba, ahankali ta juya zamanta ta fuskanci Salem, cikin rawan murya tace
"Am sorry..." Girgiza mata kai yi
"No...am sorry for hitting you..." Yafada cikin whisper yana kallon yanda ya bar hannun shi kan fuskanta. Ahankali ta mike shima ya mike, tafiya ta farayi amma kaman iska na kadata, da kyar ta kai baki palace, Salem na bin bayanta don inda babu Abba awajen da daukan ta zaiyiko gaban uban waye, tana fita yanmatan suka rungume ta ta fada jikin su tana kuka, dukkan su tsaya kallon sir Salem in flesh and blood sukayi, Dan murmushi yayi sannan yace
"Excuse me ladies..." Dukkan su daria sukayi suka sakar mashi tawa. Hannunta ya rike suka kama hanyan part din mami, har sun kai bakin kofan tawa tadan tirje tana girgiza mashi kai, shima girgiza mata kai yayi sannan bude kofa, mami ce zaune sai hawaye take, babu abinda take tunawa sai irin tsangwaman datasha wurin family mijinta, gani suke ita tasa ya juya masu baya wai don tana princess. Ahankali Salem ya saki hannu tawa ya zauna gaban mami, ahankali yafara cewa
"Mami... Nasan bani ke bakiso ba...halin mutanen mu da kika zauna dasu ke bakiso...Ni ina daukan maki alkawarin zan kula da yarki kaman yanda zan kula da kaina..." Mami goge hawayenta tayi sannan tace
"Allah ya ba ikon kula da yata... Dan Allah duk laifin dazatayi maka..please kar ka saketa...ka hukuntata...please" dan murmushi yayi
"Sakin mata baya cikin dictionary dina...insha Allah I will show you that we are not all the same..." Kai kawai ta gyada mashi
"Kam irin wannan wahalan Dana sha kanta zan saketa?... Ai intayimin laifi ubanta zanci mu shirya.." Yafada cikin ranshi. Mikewa yayi ya bar dakin, tawa kam rakubewa tayi jikin bango don gani take mami zata cimata for going against her order. Mami mikewa tayi ta koma bedroom dinta, da sauri tawa tashiga nata bedroom din ta kwanta tana jin dadi.
Salem na fita ya hangi yanmatan zaune cikin balcony suna ganin shi suka fara kus2 kuma maganan shi suke, kallon white leg dinshi mara takalmi sukayi, har ya Dan wucesu ya dawo wurin su,
"In-laws.. Can I know the names of these beautiful ladies?..." Ya tambayesu sounding so naughty, da sauri suka fara introducing Kansu dan murmushi yayi yana godewa Allah da bada Khalid yazo ba don yasan babu abinda zai hanashi flirting dasu in yana nan, bayan sun gama
"Lovely names.." Yafada yana saka hannu cikin aljihunshi, ATM ya fiddo sannan ya fara cewa
"Ga ATM ...Ku shiga cikin gari Ku nemawa princess dina the most expensive phone... Sannan each and every one of you should spend 200k..." Ihu suka farayi suna Neman tada palace din,
"For us?.." Suka fada gabaki dayansu, murmushi yayi yana daga gira daya
"Yes..babies...you know money is not the problem..."
"We know handsome!" Suka fada in chorus, wacce tafisu shekaru mai suna mufida ta amshi ATM din sannan ta kalli sauran
"Sis Ku kirani nan in dauko car keys.."
"OK" kawai suka amsa mata, Salem wani murmushi yayi ya kama hanyan cikin palace.

Su Salem na barin palace OBJ ya kalli oba sannan yace,
"Tunda an gama wannan sai Ku bamu list da kuma ranar introduction.." Oba dariya yayi
"So soon haka?" Abba dadi yaji yanda OBJ yasan abinda ke cikin ranshi
"Meye na wasting time kuma?... Kawai mu gama mu dauki yarmu.." Dukkan su dariya sukayi sannan oba yace
"To yanzu zan aikawa iyayen yarinyan maza...zuwa next two weeks kuzo sai Ku amshi list..." Kai OBJ ya Dan girgiza
"Ranka shi dade two weeks yayi mana yawa...ka Dan rage mana..."
"OK...bakomai... Ku dawo zuwa next week..."
"Godiya muke.. So ranar zaayi fixing din ranar introduction ko?.." wani uncle Salem ya tambayi oba
"Insha Allah..."

Salem na shigowa ya zauna kanshi kasa, acikin zuciyanshi kam dadi yakeji Mara misaltuwa.
Yanmatan sa suka tafi shopping kam basu dawoba sai 5:30pm lokacin su Salem sun dawo daga masjid suna zaune palace, hira kawai su Abba da oba suke, shikam so yake ya kara komawa wajen tawa su danyi hiran wedding preparations, hakuri yayi tunda ba yau zasu koma ba, da sun koma government [truncated by WhatsApp]
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ9โƒฃ


Tawa najin anbude kofan dakinta tayi saurin mikewa zaune, mami tagani tashigo jikinta duk babu kwari, gaban tawa ne yafara disco cos gani take mami dukanta zatayi, mami batace komai ba ta zauna gefen gadon, tawa rakubewa tayi jikin bango, mami tafi minti biyar zaune batace kala ba, sai daga baya tayi ajiyan zuciya sannan tafara cewa
"Yanzu tawa duk maganan danayi maki saida kika nuna kin sanshi?.. " tafada cikin sanyin murya, tawa bata ce komai ba tafara sabon kuka, hannu mami ta daga mata alaman tayi shuru, nan take ta hadiye kukanta
"Yanzu tawa har kinyi girma da bazaki bi umarni na ba?... Ko kina ganin farincikin ki ke banaso" shuru tayi for a moment sannan tacigaba dacewa
"Sam ba haka bane...kawai banason abinda zsai tabamin ke..kuma banason ki sha wahalan Dana sha...yana making promise wai zai yi this and that... Its all lie.. There is something he sees in you..the moment ya dauki wannan abun zai ajiyeki gefe ba fata nake maki..." Tawa ji tayi gaban ta na faduwa don gani take maganan mami gaskiya ce ba kaman in ta tuna yanda yake maganan sex cikin waya, taji mami nacewa
"Kuma tunda ummanshi bata sonki koshi baiyi aureba dole zata aura mashi mata yarensu lokacin zaki koma..." Shuru tayi dataga tawa ta fara kuka sosai, mami tsaya kallon ta tayi
"Ki bar
wannan kukan cos there is no going back..." Cikin kuka tawa tace
"Mami..yace Umma ta yarda.." Baki mami ta tabe sannan tace
"Allah yasa..nidai kullum inayi maki aduan kar Allah yasa kisha wahalan Dana sha a baya..and I will continue praying for you..." Tawa batace komai ba ta cigaba da kuka, ahankali mami ta jawota jikin ta.

Bayan su Abba da Salem suka dawo daga sallan magrub sukayi dinner, har lokacin oba ya hanasu tafiya, saida sukayi sallan ishai sannan sukayi masu bankwana suka fita Salem kam tunani yake ai babu inda zashi har sai ya gan tawarshi, suna zuwa wajen motocinsu ya kalli Abba
"Abba da akwai wani friend dina nan garin...yace zaizo ya kaini gidanshi.. So kilan in kwana chan..." OBJ dariya yayi yana yi mashi naughty look, Abba dai baice komaiba ya shige mota, cikin ranshi yana cewa
"Yayan zamani..Allah dai yasa ba zani kuke ba.." Suka tada mota suka bar Salem tsaye wurin, suna tafiya ya fara waige2, daya daga cikin yanmatan yagani tana kallon shi daga kan bene, hannu yayi mata alaman tazo, da sauri ta sauko daga kan benen, gaidashi tayi ya amsa mata
"Please sis I want to see my princess.. Is it allowed if I go there now..." Da sauri ta daga mashi kai
"Yes sir...I can escort you if you want me to..."
"OK..help please" yafada yana dariya, gaba tashiga ya bi bayanta, daidai falon mami tayi sallama baa amsa ba alaman babu kowa wurin
"Sit sir.." Ta fada mashi sannan ta shiga bedroom din tawa, lokacin tana zaune tayi tagumi tana kallon kwallin wayan dake gaban ta, ta sanya kayan bacci tana tunanin hiran dazasuyi da Salem yau, ga kuma maganan da mami ta fada mata yana yi mata yawo a kunne. Tana gani idayat ta dawo hankalinta, sauka tayi daga kan gado
"Sis how far..." Ta tambayeta cikin sanyin murya
"Cool.." Ta amsa mata tana kallon sexy nighty dake jikinta, idayat shuumin murmushi tayi sannan tace
"Kizo..." Ta fada tana nufan kofa,
"Inji wa?..." Ta tambayeta surprisingly cos mami bata dade da barin dakin ba,
"Inji mami.." Tafada tana fita daga cikin dakin, tana zuwa falo tayiwa Salem OK sign da hannun ta sannan ta fita daga falon, tawa batayi wasting time ba ta fito a haka, kuma abun takaice bata ga Salem ba da wuri, shikam tana fitowa ya kura lustrous skin dinta ido, tana waigawa sukayi ido hudu, da sauri tasa hannu ta kare kirjinta, Salem murmushi yayi tare da kauda kanshi gefe,, da sauri ta koma ciki, dafe kirjinta tayi tana nishi sama2, da sauri ta dora zani kan kayan bacci sannan ta saka hijjab datayi sallan sannan ta sake fitowa, Salem murmushi yayi da ganta, kanta kasa ta durkusa ta gaisheshi, amsawa yayi, zama tayi kasa gabanshi amma har lokacin bata daga kai ta kalleshi ba,
"Hmmm...habibty yau baki kallo na?.." Ya tambayeta yana kallon yanda take wasa da Dan yasanta,
"Habibty kin rame da yawa...what happened to you?.." Dan baki ta turo sannan tace
"You.."
"Seriously?..." Hararan shi tayi
"You always make me cry..."
"Ohhh...sorry... You caused it...you landed me on the hospital bed..."
"Is that why you said you are getting married?..." Daria yayi
"But that was you..." Shuru tayi, hannun ta ya kama yana kallon yatsunta,
"I think this lovely finger need a diamond ring.." Yafada yana rike da yatsanta na tsakiya, wayanshi ya fiddo, wata number yayi dailing, few seconds akayi picking bayan sun gaisa Salem yafara cewa
"I need a very big diamond ring..."
"Na Umma?.." Aka tambayeshi daga chan bangaren
"No..for my princess.." Ihu mutumin yafarayi daga chan bangaren, har saida Salem ya cire wayan daga kunnenshi don kar ya kashe mashi kunne
"Sir finally... Who is this lucky girl?...". Salem kurawa tawa ido yayi
" she's not the lucky girl.. Am the lucky guy..so kuna da big gem diamond ring?... ".
" yes..yes...da akwai... What size.. " Salem dan murzan yatsanta yayi ahankali
"Kawai zansa pilot dina ya zo Lagos first thing tomorrow morning ya amso different size,..in na zaba jibi Sai a maido maka.."
"OK..sir..my regards to your princess.." Salem bai kara cewa komai ba ya kashe wayan. Gucci's online shopping site ya shiga sannan ya dan duka ya nuna mata pictures na expensive dresses
"Habibty duk Wanda yayi maki ki nuna...we have to start shopping.." Tawa dagawa tayi ta kalleshi ya daga mata gira sannan ta maida idonta kan wayan, gani tayi dukkan kayan kan page din babu na kirki, kara kallonshi tayi ya kashe mata ido
"Gaskiya I can't pick any cloth from here .."
"Why..."
"There don't have decent clothing.." Salem Dan daria yayi
"Ai habibty those clothes are for home... Kuma bana nan Nigeria bane..kawai just select.. Zan tura aje wajensu a dauko ayi filling closet dinki na instabul..." Tawa Dan baki ta turo
"Gaskiya I can't wear any of those clothes..."
"Hmmm...we shall see..." Yafada sannan ya fara selecting sexy wears, bikinis, bunny slippers etc, yana gama wannan yabude Adrienne Vittadini shopping website, saukin wurin duk Arabian dresses ne, suma kaya yayi selecting da yawa sannan ya koma Chanel nan takalma da bags kawai yayi selecting, tawa kam Sai kallon ikon Allah take don dukkan kaya dayake selecting da dollar price ne ajikin su kuma babu Wanda is less than 1000$
"Wai is this necessary yanzu?" Ta tambayeshi ahankali
"Yes..princess.. Time is not on our side.. Kinsan insha Allah in the next one month we will be couple..." Ido tawa ta zaro,
"One month kaman an gaji dani?...gaskiya Aa.." Daria Salem yayi
"Ai am eager...you know why?..." Ya tambayeta, tasan halinshi, kin amsa mashi tayi
"Na ga phone.. Nagode.." Banza yayi daita yacigaba da murza yasanta yana cewa
"Kinsan yanda kika wahalal dani saina rama..."
"Kodai ka wahalal daniba..."
"No..ke.kika wahalal dani...kin gudu kin barni.. Yau kuma kin kusa aikani lahira..you will plead for that..."
"Am sort.."
"Ba yanzu ba.. Nan gaba kadan..." Ita kawai shuru tayi tana tunanin maganan mami sannan tana mamakin yanda yake magana...hira suka danyi sannan ya mike
"Habibty zan tafi...please kina iya bani kwatancen wani hotel nan kusa?... Cos I can't go to the government house now..."
"Nidai ban san koina nan ba...amma muje in raka bakin gate ka tambayi guards"
"OK then..." Yafada tare da mikewa, itama mikewa tayi, ya rike hannun ta suka fita waje, katon compound din babu kowa, ga haske kaman rana, hannun shi cikin nata har sukazo wurin masu guiding gate, nan suka tsada mashi taxi ya hau..kaman kar ya bar ta yakeji, hannu suka dinga dagawa juna har ya bar wajen.

Wacegari gidansu tawa yayi breakfast, a lokacin oba baisan yana palace ba, mami a bedroom dinta taci abinci shikam da tawa kan dinning. Around 9am pilot dinshi ya kawo sako daga lasgidi, diamond ring ne kala2, hannun ta ya rike ya dinga gwada rings din har aka samu size dinta, bayan ya sallami pilot din da sauran diamonds din. Cewa yayi zai tafi.
Sallama yayi dasu mami ya fito waje, suna fita balcony ya amshi zoben daya bata.
Daga saman bene su idayat da sauran su suka sauko Sai zolayan tawa suke, Salem sai murmushi yake, saida suka kai bakin gate da dukkan yanmatan, yace su rakashi har bakin titi, haka suka bishi riiii. Har da tawa, saida suka kai bakin titi cikin mutane sosai, ya juya yana kallon tawa, dukansu basu ankaraba Ahankali yayi kneeling gaba tawa, dukkan mutane tsayawa sukayi suna kallon su, sisters din tawa baki suka rike, nan take mutane suka zagaye suna ana cewa wannan kaman that billionaire... Tawa kokarin rike shi take yatashi amma yaki, saida yaga mutane dayawa sun taru kuma lokacin ansan Salem ne, wasu unknown yanmata Sai hawaye suke, mutane Sai dauka suke cikin waya, ahankali Salem ya kalli tawa eye ball to eye ball sannan ya fara cewa
"Tawakaltu.. Abinda akayi jiya a palace ba kowa ya saniba...thats why inason in tambayeki gaban wayan nan dumbin jamaa..." Yafada yana nuna mutanen dake tsaye suna kallon su sannan ya maida kanshi wurin tawa, a lokacin banda hawaye babu abinda tawa keyi,
"Tawakaltu.. Will you dome the honour of making me the happiest man on earth... Will you marry me?..." Tawa cikin kuka ta gyada mashi kai, dukkan mutanen tafi suka farayi, wasu Sai kuka suke mussanman yanmatan dake tunanin how they wish they are tawa, hannun ta ya kama ya sa mata zoben, mikewa yayi, da sauri idayat ta kama hannun tawa tana nuna masu zoben tana cewa
"It's a diamond.." Tawa kam rufe fuskanta tayi tana kuka har suka koma gida, Salem kam taxi ya hau har government house sannan suka kama hanyan yola.

Ko hour dayan baa kaiba latest news ya koma
THE NIGERIA MULTI BILLIONAIRE PROPOSED HIS YORUBA GIRLFRIEND IN PUBLIC
Nan take aka fara nunawa Cikin news channel na gida Dana waje, don har lokacin dayake kneeling agaban ta aka dinga nunawa, cikin wayanda suka gani kama har da family da kawayen ameera.

๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’šโค


Upp..upp..uppa..kanamstar..." Ameera ke ta maimaitawa tana rawa a tsakar gidan, dukan yayan hinde Sai clapping suke yimata, tana rike da wayanta da tawaka itakuma Sai bi take da baki tana girgiza jiki, hinde na zaune tana figan kasa Sai cewa
"Wannan yarinyan baidai rawaba" diyan hinde dake ta wanke cefene ta mike tazo wuce ameera ta riketa
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’šโค
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’šโค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)


5โƒฃ0โƒฃ

"Zo muyi rawa$" ta fada mata, daria diyar hinde wacce take kira da zombie tayi
"Ai anty ban iyaba" ameera dake ta shaking kaman her life depends on it ta riketa
"Come on...kawai girgiza jiki.. It's good for your health.." Rike mata two hands tayi cikin nata suka cigaba da rawa, wai dole Sai ta koyi rawa wakan karewa tayi ta saka watch me
"Watch me..ohhh.watch me Nene..watch me..watch me...ohhh" ta farayi, cikin jindadi kawai take kona meye oho, sauran yaran hinde Sai kallon ta suke cikin jindadi cos dukkan su yanzu gidan suke, dukkan uban abincin da aka ajiye sun kusa karewa, kullum cikin dafa abinci suke yanzu Sam ameera bata zaginsu, dukkan su cikin katon faranti suke zuba abinci su ci tare, kuma ba karamin kayan dadi sukeci ba, yanzu ameera ta gane kudi bai kan darajan mutane bha, yanzu ta maido jikin ta feye da kwanakin baya, saidai har yanzu bata maida haskenta ba cos babu spa. Har cikin ranta babu wani zancen Salem, kawai jira take ya sallameta ta tafi, kullum suna cikin waya da family and friends, mom tana jin hayaniyan su hinde amma data tambayeta saitace new friends dinta, mom kam ta dau aniyan kiran Salem tayi mashi godiya kan chanjin takeji cikin muryan ameera, Sam kaman ba yarta ba.
Ameera dai tasan ta chanza, yanzu ta rage kyamatan mutane amma fa ba dukaba cos ance mai hali baya fasawa.
$"anry kibani kudin markadan" karamar diyar hinde ta fada mata, ajiye wayan yayi ta shiga ciki ta bude gefen Ghana ta dauko Dari biyar, kallon sauran kudin tayi tace
"Allah yasa sauran kudin nan su ishemu kafin ya sallameni" tafada tana ajiye sauran kudin da bazai wuce 70k ba,
"Gashi "tacewa yarinyan, tana daukan waya don cigaba da rawan ta wayan ya fara ringing, tana dubawa taga zeenat, da sauri tayi picking
" kawas..." Tafada kaman mara problem, zeenat kallon wayan tayi don Sam ba yanda taso jin muryan ameera bane especially with the news going on
"Friend ya kike?" Ta tambayi ameera
"Lau wallahi.. Meke tsalle banda frog?" Tafada cikin zolaya
"Hmmm..friend you tell me... Ashe mijinki zaiyi aure baki fadamin ba...?" Da sauri ameera taji kafafunta sunyi mata sanyi don sam she wasn't expecting this, dan baya2 tayi ta zauna bakin kofa, zeenat tacigaba dacewa
"Is all over the news... Har kneeling yayi gabanta.. Kuma Yoruba..." Ameera kasa cewa komai tayi, cikin zuciyanta tana jin wani irin zafi,
"Best baki ce komai ba.." Ahankali ameera ta fara cewa.
"Hmmm..what can I say....komai lokaci ne..."
"Lallai ma..duka yaushe kukayi aure?...kuma kema kin san with the kind of your attitudes baki da chance against Yoruba.." Itadai ameera batace komai ba
"Nidai wallahi ina tausaya maki..." Cikin sanyin murya ameera tace
"Kar ki tausaya min...Everything will be alright..."
"Babu alaman damuwa tattare dake,"
"Me kikeson inyi?...ki barni da abinda ya dameni..." Ta fada sannan ta katse wayan ta, tana katsewa wayan yafara ringing, gani tayi wata kawarta ce, kin dagawa tayi, kai ta hada da gwaiwa tana tunani
"Yanzu da gaske auren zaiyi...why is this man wicked?.. Meyasa baya yafiya?... I know abinda nayi is bad amma two months is enough...I want to stay with you..." Tafada tana hawaye, hinde juyawa tayi taganta zaune tana hawaye, da sauri ta saki yankan kazan taje wajenta
"Lafiya kike kuka?" Ta tambayeta tana dafa kafadanta, kallon hinde tayi da wet face dinta
"Mutumin daya ajiye nan zaiyi aure kwanan nan..." Tafada tana kirkiro murmushi karfin hali,
"Insha Allah.. Na kusa barin wurin nan..." Tafada tana Dan jinginawa da hinde dake tsaye kusa daita, hankalin hinde tashi yayi don ita gani take ita da yaranta zasu koma gidan jiya na wahala, wayan ta yafara ringing, tana dubawa ta ga mom da sauri ta dauka tana fashewa da kuka
"Habibty meye haka nakeji..." Ameera batace komai ba tacigaba da kuka
"Ke zaa yiwa kishiya?... You that is so reckless..."
"Mommy.. Don't worry about me..."
"Haba yazakice I should not worry.. Ke baki tashi kika ganni da kishiya ba..how will you cope...kuma the most annoying part shine da gani yafison wannan yarinyan kanki...habibty am worried about your happiness.." Cikin kuka ameera tace
"Mom karki damu..I will soon be home...."
"What do you mean?.." Mom ta tambayeta cikin sauri, shuru tayi tana tunanin ta fadawa mom, kuma tasan sauran don kilan tana karawa kanta more time nan don yanzu ta yarda Salem ba karamin mutum bane, at the same time he's a man of his word
"Habibty please tell me...am worried..." Ahankali tace
"Mom..zan ziyarce Ku..this days insha Allah..."
"No habibty... That's not what you intended saying.. Please tell me the truth are you facing any marital problems?..." Cikin sanyin murya tace
"No...mom...am..OK..."
"Then kar kizo kar ya zama kaman don zaa yimiki kishiya mukeson kwulla wani abu... Anty Sadiya zatazo da sisters dina one of this days..." Da sauri ameera ta girgiza kanta tare dacewa
"No mom...karsu zo...ni zanzo.."
"Habibty meyasa duk lokacin da nace mutane zasuzo Sai ki hana...something is wrong I know..."
"Ba komai.. Kawai banason yayi tunanin don kudin shi ake binshi..." daga chan bangaren mom lumshe idanuwa tayi tana jindadi da hankalin da ameera tayi
"Amma habibty ya kamata ace family sun San mazauninki..."
"Hmmm...mom no problem.. Am OK...amma dagaske ne Yoruba zai aura?"
"Bai fada maki bane?"
"Ya fadamin.. Amma bai fadamin yarentaba..."
"Ance jikan sarkin kwara state ce...shiyasa hankalina ya tashi"
"Relax mom...everything will be OK" tafada tana goge hawayenta, hira suka kara for few more minutes sannan sukayi ban kwana ta kashe wayan ta gaba daya ta kalli hinde dake tsaye kusa daita har lokacin sannan tace
"Zan kwanta..in abincin ya dahu kuci kar Ku tadani" tafada tana mikewa, ahankali ta shiga dakin ta kwanta, duniyan tunani ta shiga, ada tana tunanin kawai Salem yayi ya aure ya sallameta amma yanzu she's feeling so sad
"Oh Allah what's happening to me?...am I falling for the lover of another woman?...ya rabbi kar ka barni inyi son mason wani don babu komai cikinta Sai wahala.." Ta fadawa kanta.


๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค


Tun a hanya aketa kiran family din Salem anayi masu congrats, shi kanshi Salem har ya gaji da amsa waya cos calling dinshi ake kaman hauka cikin su kam har da turawa da larabarawa da suka sanshi, governors da ministers Sai kiranshi suke, Khalid kam cewa yayi
"Guy I will take care of the wedding planners...zan biya komai..." Salem dariya yayi
"Ai wedding planners din yawa zasuyi tunda da akwai na kwara sannan na yola and friends party na abuja kuma yanzu bill gate ya fadamin zaayi organising small get together a Washington DC..."
"Zan kula da dukan party na Nigeria..." Cikin jin dadi Salem yace
"Don't worry.. Ka ajiye wannan kudin...kawai remind me of promises din dana dauka kan in na auri tawa...cos nasan ina Iya mancewa
saboda commitment.."
"OK.." Dan hira sukayi sannan ya kashe wayan shi. Suna isa yola yan jeridu da yawa kofan gidansu, Allah ya taimakeshi cikin jet suke da basu samun hanyan shigowa, suna sauka Umma ta rungume shi tana nuna jin dadinta, sisters dinshi suka fito daga part din Umma, dagudu suka fada jikinshi, mamakin ganisu yayi
"Ya akayi hubbies dinku suka bar Ku kukazo?..." Babban ilham Dan hararan shi tayi
"Yanzu yaya ace zakayi aure saidai mu gan kayi kneeling bamu taba samun labarin ba.." Dariya Salem yayi
"Nasan ko bazaki yardaba..." Ido ilham ta gwalo
"Ni?... Ai wallahi kowa kake so am 200% behind you.." Dariya Salem yayi, itakam autansu wacce baa Dade da aurenta ba mai suna salma amma ana kiranta da shuwa, don ita da Salem kaman an tsaga kara
"Yaya am so

Please Login or Register in order to submit comment