Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maida kofanta ta rufe.

Affan sauka kasan yayi tare da zuwa wajen mommy
"Mom kin ga wani ya aikeni kiran anty ameera Amman tace inje in gayamashi bata zuwa ko?" Matan ajiye remote control dake hannuta tayi kafin ta mike, direct dakin ameera ta tafi don Matan bata da matsalan ko kuma ince gurin daya wuce ameera tayi aure ba Dan komaiba illah don ganin hakan yana Iya kawo chanji a rayuwan ameera, tana bude kofan ameera dake zaune sanye Da bump short tare da half vest tayi saurin mikewa ,
"Wai bake ake dema ba?" Tafada fuskanta daure, da Sauri ameera tace
"Nice"
"Then why are you not dressed.." Bata gamaba ameera ta yi saurin bude wardrobe tare da dauko wasu pink gown da dan karamin Vail blue, Matan tafita tanacewa
"Kiyi sauri ki fito kar ranki yayi mugun baci" .
Da sauri ameera ta saka kayanta don bata tsoron mutuwa yanda take tsoron mommy ba kaman in dad dinta bayanan.

Tana zuwa kasa ta kalli affan tace
"Go and tell him tana zuwa" da sauri affan ya fita waje yana tsale2, Salem na ganin shi yayi tunanin same old story ne Amman sai yaji yaron yace
"Sir gata nan zuwa"
"Thanks" Salem yace mashi, yaron yacigaba dacewa
"Da tace you should fuck off....sai na gayawa mom" daria Salem yayi
"Stop using that f**k word..babu kyau ga yara "
"OK sir" yaron yace sannan ya juya da niyyan tafiya amman sai yakara juyowa sannan yace
"Sir kana dan kama da wani dake cikin photo din dad dina dake office dinshi" Salem dan shuru yayi sannan ya girgiza mashi kai
"Gaskiya bani bane... Shiyasa kake kirana sir?"
"No sir...wata antymu mai suna Mrs adeoye tace indai mutum ya girmemu mu dinga kiran su da sir ko mam"
"Good boy..keep it up"
"Yes sir" yafada kafin yabar wurin da gudu ya koma kan field.

Ameera kam da sauri tafito kaman wata mutuniyar kirki, har zata wuce mom takira
"Haka zaki tafi hannu rabbana?..dalla wuce kitchen ki dauki drink ki kaiwa bakonki, ameera kaman ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki gashi babu daman gardama mom ta suburbudeta,
Kitchen ta shiga ta dauki juice da ruwa tare da cup ta ajiye kan tray, har ta fito sai wani mugun tunani ya fado mata cikin rai ta kara komawa cikin kitchen ta dauki cup din ta zuba barkono sannan ta zuba juice saman shi tare da rufewa da saucer ta fito.

Salem da har lokacin yake jingine jikin motanta ya hangota ta taho, haka nan sai ya tsinci kanshi da faduwan gaba, kura mata ido yayi yana tunanin Allah yasa ba wannan yarinyan ke muguwarba
" Allah yasa su biyu ne..." Yafada Cikin zuciyanshi, kara daga kai yayi ya kalli yanda take tafiya kaman tana runway show, tamkar tana modeling cos duk step dinta is marvelous, fuskanta ya kalla yaga tamkar anyi mata albishir da mutuwan Wanda tafiso aduniya, tafiya da takeyi a ahankali ya bashi daman kallon kafanta don gown dake jikinta bai kai kasaba, wasu silver ankle lace ya gani kafanta sannan da ganin fingers dinta fixing tayi, bai ankaraba yaji kaman daga sama ance
"Malan wane bashi naci wurin ka ban biyaba?" Sai lokacin Salem ya dawo hayyacinsa, kallonta ya sake yi
"Kiyi...." Bai karasaba tace
"Kaman kaine taxi driver din da ya daukomu last week ko.." Ahankali Salem yace
"Nine...." Still bai karasaba ta kara katseshi da wani irin daria rainin hankali tana cewa
"Halan aiki kake nema...don gaskiya gidan nan babu vacancy" Dan murmushi karfin halin Salem yayi before saying
"Ba aiki nake nema ba...wajen ki nazo" kallonshi tayi from head to toe sannan ta kalli kanta sannan tace
"Ina jinka...low classer" still murmushi Salem ya sake yi
"Na ganki kuma kinyi..."
"Wow..what a courage.. Dan Allah Malam ka kalleni...ko ban shafawata kana Iya saye?.." Salem zaiyi maganan tadaga mashi hannu tare dacewa
"Shut your pit toilet am not don talking.." Gira daya Salem ya daga don tunda yake bai tabajin zagin daya tsotsa mashi rai kaman wannan ba
"For your information.. I don't mingle with low life pest..bana harka da non entity.. Bana magana da mutane that a from gutta... Bana harka da mutane da basu da hope don da ganinka you look hopeless...and ina warning dinka ...."
"Hey!!!" ya daka mata wani razannen tsawa
"What do you think you are... Kina ganin kinada chance awurin high class babes?..well for your information Iyakanki nan kano..shiyasa you are so arrogant..." Clapping ameera tafarayi
"Ashe matsiyacin ya Iya speaking..kace who am I ..any way ni ba kowa bace amman nafin uwarka da ubanka.." Nan take idon Salem ya koma ja don tunda aka haifeshi babu Wanda ya tana kaishi makura kaman wannan yarinyan
"Sam ban gan laifinkiba....ammn you are not worth my precious time.. Sannan bani da lokaci...da time gareni danayi maganinki koda na dan lokacine"
"Look at this bastard..uban WAYE kai!!?" Ran Salem Kara baci yayi
"Baki chanchanci kisan KONI WAYE ba.." Yana kaiwa nan ya juya ya fara tafiya, ameera daukan juice mai yajin tayi
"Jimana" tace mashi Amman yayi banza ya shigaba da tafiyanshi, kawai baiankaraba yaji saukan ruwa bayanshi, allah ya taimakeshi bai shiga idonshiba, tsayawa yayi kaman dutse don tunda yake baitaba zama so humiliated kaman yauba , kasa juyawa yayi ita kuma ameera tacigaba dacewa
"Wash up you son of a bitch" at that moment Salem jiyake yana iya shake ta ,dukkan masu gadinsu da driver da mai wankin motansu Salem suke kallo suna magana ahankali
"What can you do?" Ta sake cewa adaidai lokacin da akayi horn a bakin gate , da gudu mai gadi ya bude gate wata babban jeep ya shiga gidan ,affan dake kwallo ya taho da gudu ,sai lokacin ya lura da abinda ya faru maimakon yaje wurin dad dinshi dake fitowa daga cikin mota sai yayi cikin falonsu da gudu yana kiran mommy, daddy ameera na fitowa ya kurawa Salem ido yana tunanin wannan kaman sir Salem amman yasan wannan bashi bane don salem din dayasani is filthy billonare , shima Salem yana daga kan shi ya ga mutumin ya ganeshi sai dai baisan sunanshiba amman yasan suna haduwa a board meeting
"Waye wannan?" Dad ameera ya tambaya cikin shagwaba ameera ta fara cewa
"Dad Wai wannan low class bastard din ne yace yana sona" dad ameera dirty look ya watsawa Salem sannan yace
"Haba dan nan ina kai ina ameeran daddy..." shi kam Salem baice komaiba yafara tafiya, ita kuma ameera da dad dinta suka shiga falo, bai kai bakin gate ba yafara Jin ihun ameera, Salem tafiya yake kaman kazan da ruwan sama ya doka. Saida Yazo bakin gate ya tsinci muryan mai gadi nacewa
"Dan nan kayi hakuri..daman naso in fada maka amman nace kar inyi shishigi...Sam yarinyan bata ganin kowa gashin arziki... Hajiya da affan kawai ke da mutunci amman alhaj da yarinyan nan halin su iri daya ..." Salem ba idajin abinda tsohon ke cewa ba ya fita yana rawan sanyi ga bayanshi yana yi mashi zafi saboda barkono cikin lemon. Yana tafiya yana cewa
"ZAKISAN KONI WAYE
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ2โƒฃ

Mom ameera dukanta take kaman an aikota, duk yanda dad ke son kwatan ameera kasawa yayi don tunda yake bai taba ganin bacin ran matanshi kaman yau ba, don kaman bai mitanen boye ta koma, tana dukan ameera tana cewa.
"Me nayi maki kikeson sa jinina ya hau,..me nayi maki kikeson jamin zagi da shaidan banza wurin jamaa...irin tarbiyan danayi maki kenan?..yau mai amsanki hannuna sai Allah" haka ta shigaba da dukanta har Allah yabawa dad saa ya amsheta daga hannun mommy.

Salem kam yana fita yana rawan sanyi don sam bai wanka da ruwan sanyi balle abinda ameera ta zuba mashi direct daga cikin fridge yake, bayan shi wani irin zafi yake yimashi kaman ansa mashi garwashin wuta, Salem yana tafiya yana tunanin abinda yafaru, yau dashi talakkane da ya hadiyi zuciya ya mutu don bakin ciki, yana zuwa inda ya ajiye motanshi yabude ya shiga, zama yayi yana tunanin abinda zaiyiwa ameera da zai huce don alokacin gani yake koda zaa yankata gabanshi bazai tausaya mataba
"She called me a bastard...non entity... Ta zagi uwata..oh gossh..me zan wa family dinki?...wane irin fansa zan dauka kanki?...I will deal with you and am going to enjoy every bit of it...you and your hopeless father are going to eat your vomit..you will beg for mercy.." Maganan tsohon ya dawo mashi
"Karshen rashi kunyaki da rashin tarbiyanki yazo...filthy bitch" Haka shi kada ya dinga surutu, yafi hour daya zaune wurin yana tunanin, ringing wayanshi ya farayi ya dauko wata costurmise phone Wanda baifi guda goma a duniyab ya amsa wayan, daga chan bangaren Abdul yace
"Sir are you alright? "
"Yes..just ka nemo min the best doctor kafin in dawo gidan..." Cikin tension Abdul yace
"Sir are alright?... What's wrong with you sir?" Ahankali Salem yace
"Am ok...just get me a doctor" Abdul zai sake magana ya katse wayan.

Still Salem zaune yayi wurin yana tunani, don har lokacin bai san abinyiba amman yasan ko me zaiyi ba abu bane mai kyau.
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" ya dinga maimaitawa don ji yake kaman zuciyanshi zai bude kirjinshi abinka da mai zuciya.

Sai bayan sallan magrub ya koma gidan yana tuki yana tunani, yana zuwa gida ya tadda Abdul zaune da wani mutum a falo, Abdul na ganin shi yayi saurin mikewa yana cewa
"Sir me ya sameka?"
"Nothing" ya amsa masa atakaice, Abdul kallon yanda fararen idanuwanshi suka koma ja yayi sannan yace
"Sir something is wrong..."
"I said am fine!!!!" Ya daka mashi tsawa sannan ya kwantar da murya yace
"Where is the Doctor?"
"Gashi nan" ya nuna mashi wanda ke zaune,
"Follow me" ya umarshi doctor, yayi hanyar bedroom dinshi, yana juyawa Abdul yaga bayan riganshi da jirwaye,Abdul yasan wani abune ya sameshi Amman baisan meye ba kuma yasan duk abinda ya sameshi shine sanadi don shine ya bashi shawaran suyi abinda yakeyi. Duk sai yaji ya tsani kanshi, yasan in har wani abu ya sami Salem shi zaayi holding responsible, ahankali yace
"Sir am sorry.." Juyawa Salem yayi ya kalleshi
"For what?" Shuru yayi baisan abinda zai ce ba.
Suna zuwa bedroom dinshi yacire rikanshi ya kwanta kan gado tare dayin rub da ciki sannan yace
"Doc dubamin bayana da akwai wani ciwone?" Dukawa doc yayi tafara observing bayan shi
"Sir da akwai abinda ya sami bayan ka ne?" Ya tambayi Salem, kai Salem ya daga mashi sannan yace
"Eh...dazu nazo wucewa mistakingly wani ya zubamin juice ajiki...kuma naji wurin yana yimin zafi" kara kallon wurin doc yayi sannan yace
"Sir bayan ka ba ciwo...Amman inajin juice din da aka zuba maka yana da wani Abu ciki shiyasa kake jin zafi ...zan rubuta maka magani yanzu" kai kawai Salem ya daga mashi, cikin ranshi yana cewa
"Har wani abu lta zuba ciki don ta illatani...daga cewa ina sonta" yana cikin tunani wayanshi ya fara ringing, yana dubawa yaga Khalid ne, saida yace.
"The person I need.." Sannan yayi picking, daga dayan bangaren Khalid yace
"Driver what's up..." Salem shuru yayi baice mashi komai ba, Khalid yacigaba dacewa
"Na yanka mana ticket din zuwa kallon kwallon man united...ko taxi driving bazai barka kajeba.." Salem dan murmushi karfin hali yayi sannan yace
"Bazanje...." Bai karasaba Khalid ya katseshi dacewa
"Kan uban nan...dan taxi driving sai ka ruguza mana aladanmu da muka saba..." Ahankali Salem yace
"Ba laifinka bane..." Khalid kara katseshi yayi
"Guy ya akayi naji muryan ka kasa...kodai yan matan Kano sun cima uwane?"
"Ba kadanba" Salem ya amsa mashi, wani irin daria rainin hankali Khalid yafara yi yana cewa
"Me sukayi maka" yafada har lokacin bai bar daria ba, ahankali Salem yafada mashi abinda yafaru, shima Khalid ranshi yayi mugun bashi, Salem yacigaba dacewa
"Kuma abin haushi shine har yanzu bansan abinda zanyiwa yarinyan nan in huceba...don nayi tunani har nagaji.." Shuru Khalid yayi na dan lokaci sannan yace
"Guy ko insa ayi kidnapping dinta muci mata uwa..." Kai Salem ya girgiza kafin yace
"Mom da brother dinta are nice.. Kawai inason abinda zanyi in bata mata da dad dinta..." Shuru suka sakeyi kafin Khalid yace
"Kaima matsala gareka...yanzu wake ta wani true love.. Kawai kasamu mace mai kyau ciki da waje ka aura, ka biya mata bukatunta da rana itakuma ta biya maka bukatanka da dare..that's life now... Amman true love no longer exists,..." Bai gamaba Salem yace
"Best kasan I want a woman that can sacrifice her self for me.. Nasan there is a woman out there for me..."
"Kana nufin bazaka yi giving up ba kenan... Ko sai ansumu yarinyan da ta watsa maka acid a handsome face dinka zaka hakura....." Tsoki Salem yaja kafin yace
"Dalla yimin shuru...kawai ka gayamin abinda zai yiwa yarinyan nan I huce"
"Nace muyi kidnapping dinta kaki...to bari inda a dauko maka ita kayi raping..." Wani dogon tsoki yayi sannan yace
"Amman bestie baka da hankali..ai ko ina mazinaci bazan kusanci wannan yarinyan ba balle kasan ba halinabane..kawai inason in gan yarinyan nan under my control... I want her to beg for my mercy... Wallahi guy yarinyan sam batayiba....killan shiyasa Allah ya turani gidan don in koya mata hankali" shuru suka danyi sannan Khalid yace
"Yanzu meye abinyi?"
"I don't know.."
"To marry her...tunda kanason ta zauna karkashinka...sai kayi yanda ka gandama daita.." Salem bai karasa jin abinda Khalid zaice ba ya kashe wayanshi.

Bayan hour daya Abdul ya kawo mashi magaggunan da akayi mashi prescribing, still Abdul tambayan shi yayi abinda yafaru Amman still Salem ce mashi yayi bakomai.

Tundaga wannan ranan Salem ya rufe fita, daga bedroom sai masjid, kullum cikin tunanin abinda zaiyiwa ameera yake Amman still bai samu solution ba daga baya ya bawa kanshi hakurin ya kyaleta Allah ya hadata da daidai daita tunda shi ba abinda yazoyi ba kenan.

Bayan sati daya da faruwan abun Wanda yayi daidai da satinsu uku a garin Kano, Salem yasa Abdul ya kira mashi makeup artist ya gyara mashi fuska.

Gidan Salem a zoo road yake , kuma duk Wanda yasan zoo road yasan hanyarta busy road ne, saboda da akwai masu business kala2 a wurin , bayan sun fito, basu dade da barin gidaba wani dan almajiri yazo tsallake titi garin Salem ya kaushe mashi mistakenly ya Dan gogi wata murano, da sauri yayi parking don bawa mai motan hakuri shima mai motan parking tayi tafito, Salem da Abdul na fitowa, Salem ya gane Ashe mai motan ameera ce, da sauri ameera ta dubi motan bayan motanta da Salem ya goga, wani irin ashar ta saki sannan ta daga kai ta kalli Wanda ya goge motanta, tana ganin Salem ne tanufeshi gadan2, tana zuwa gabanshi ta sharara mashi wani wawan mari, nan take ya dafa cheeks dinshi, cikin zafin nama Abdul yazo wucewa da sauri Salem ya rikeshi da hannu daya still hannunshi daya rike da cheeks dinshi,
Ameera kallon Abdul tayi sannan tace
"Oh kana son tabani?..please bring it on...da saina koya maka hankali..." Sannan ta juya wurin Salem da har lokacin bai saki kuncinshiba tace
"Kai kuma ka bar bina kuma motata da kayi scratching saiya sayi uwarka da ubanka" Salem tsayawa yayi kaman bara lakka, muryan wata yarinyan ya tsinta tanacewa
"Ke Allah ya wadar halinki..." Bata idaba ameera tace
"Daga ke harshi kunci uban da ya haifeku banzaye matsiyata..." Yarinyan ta sake cewa
"Kece matsiyaciya tunda har zaki iya daga hannu ki mari Wanda ya girmeki saboda wannan motan..." Salem ji yayi wata tace
"Tawa..amebo watin concern you"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›
ZAKISAN KONI WAYE
โค๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’š
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ3โƒฃ

Yarinyan da aka kira da Tawa ta kalli Salem taga kaman da jini hancinshi, bata ce komai ba ta nufi wani chemist dake kusa da wurin, Salem na kallonta ta cire kudi cikin apron din dake jikin ta don da alaman abinci suke saidawa awajen, ba da dadewaba ta dawo rike da cotton wool, tana zuwa ta mikewa Abdul, ahankali Abdul yace
"Me zanyi dashi?" Yarinyan nuna Salem tayi da yatsa kafin tace
"Habo yake.." Sai lokacin Abdul ya lura da jinin dake hancin Salem, da sauri Abdul ya amshi cotton wool din yafara goge mashi hanci, har lokacin Salem bai dawo daidai ba, don tunda uwar da ta haifeshi baa taba taba mashi lafiyan jikiba, sannan daga nursery school zuwa secondary school Turkish international school yayi kuma ko kadan baa dukan yara, amman shine yau Mace ta mareshi yau, duk da yasan yana da saukin zuciya yasan he can't let this go.
Itakam ameera tana ganin yafara habo ta dauki motanta ta bar wurin Amman fa har lokacin bata bar zaginshi ba.

Abdul yafara Goge mashi hanci, shima sai lokacin Salem yasan yana nasal bleeding, cikin ran Abdul kam ji yake in shi aka mara zai fi mashi sauki sau dubu, don zuciyanshi tafasa yake kuma abinda yafi bashi haushi shine yanda Salem ya hanashi ya Koya mata hankali, Salem ya ji wata babban mace nacewa
"Tawa..na my money you use buy cotton wool?" Ahankali tajuya wurin matan sannan tace
"Zan biya ki cikin kudin da zaki bani anjuma " Mata da ganintaba mutunci kuma da alama ita Tawa takewa aiki
"Ai dole ki biyani..makulmaciya...ko wa ya kiraki oho..oya wuce ki bawa mutane abinci" nafa wayanda suke aiki tare suka fara yi mata dariya, itakam juyawa tayi wurin Salem sannan tace
"Oga sorry..Allah zai sak maka...kuma insha Allah kaima watarana Allah zai baka motan daya fi nata..." Salem tsaya kallonta yayi sannan yace
"Thank you"
"Bakomai..." Ta juya ta tafi tana cewa
"Daman masu kudi basu ganin talaka as anything... Allah zai saka mana".

Salem kallon Abdul dake ta goge mashi hanci yayi yace
" take me to the hospital " kai kawai ya daga mashi don kunyan hada ido da Salem yake,
Cikin mota suka koma Abdul yafara tuki shi kuma Salem har lokacin hannunshi rike da cotton wool a hancinshi cos jinin ba bar zuba ba, Abdul dan kallonshi yayi
"Sir ka kwantar da kanka baya kadan" babu musu ya kwantar da kanshi baya.

Free hand dinshi yasaka cikin aljihunshi ya dauko wayanshi, wata number da aka rubuta Nigeria head of NGO yayi dialling, cikin kankanin lokaci akayi picking tare dacewa
"Sir..good afternoon.. How is your holidays"
"Fine" kawai Salem ya amsa atakaice sannan yacigaba dacewa
"Ka turo min Pictures da details na yan northern NGO"
"Sir yaushe kake bukatanshi?"
"Right now" yana kaiwa nan ya katse wayan shi, tare da lumshe idanuwanshi,
"Allah nasan kanason in koyawa yarinyan nan hankali... Don nasan haduwata da ita ba coincidence bane destiny ne" yafada cikin ranshi.

Suna zuwa hospital aka nubashi doc yace abinda ya sameshi ya zo mashi unexpected ne shiyasa yake bleeding, ice block aka sa agaban goshinshi for a moment jinin ya tsaya sannan suka bashi magunguna.

Suna kan hanyan dawowa emails suka shigo mashi, bai budeba har suka isa gida. Suna zuwa gida ya dauki makeup remover ya goge fuskanshi nan ya kara ganin hannun ameera kwance kan fuskanshi, wayan shi ya dauka ya dauki photon fuskanshi ya turawa Khalid nan take Khalid ya kirashi
"Guy meye wannan?"
"Same yarinyan nan ta mareni..."
"What... Karshen mari kenan... She really have to be taught an unforgettable lessons.. If you are not doing anything kawai ka barni in sa aiyi maganinta.." Ahankali Salem yace
"I have a plan... Zanbi shawaran ka..." Nan ya kwace abinda yayi niyyan yi ya gayawa Khalid, shewa kawai Khalid yayi yana cewa
"Best ko shaidan zai jinjina maka.."
"Ai friend nasan ba haka nan Allah yake ta hada ni daita ba...yanason in koyamata rayuwa..and am not let him down.." Cikin daria Khalid yace
"Yanzu zaka hakura da taxi driving ko?" Shuru Salem yayi for a moment kafin yace
"No.." Cikin zolaya Khalid ya kara cewa
"Haba ango gashi zakayi aure?" Salem katse wayan shi yayi ya dauki iPad dinshi ya ya bude emails dinshi.

Nan ya ga emails da shugaban NGO na Nigeria ya tura mashi,hotuna ya fara kallon don tantance dad ameera, yana cikin dubawa yaga alh umar Adam gezawa
"Yes wannan shine Wanda na ganin gidan su wannan shaidaniyan yarinyan" yafada wa kanshi, budewa yayi yafara karanta details dinshi, Ashe shine head na Kano zone,
" mere state head shine yarka take yanda ta gandama kaman yar Aliko dangote..let's see what happens... " wayanshi ya dauka ya kara kiran head na Nigeria, mutumin na picking yace mashi
"Terminate umar Adam gezawa's appointment... In yayi complain ka bashi details din da zansa secretary dina ta turo maka...ka gaya mashi ina Kano Kuma gidana nada GPS so yayi searching location dina..am sure motnashi yana da navigation"
"Yes sir " kawai mutum ya fada sannan Salem yayi hanging off.
Mikewa yayi yana cewa
"Am going to enjoy this" bathroom yashiga ya dauro alwallah sannan ya fito falo, yana shiga Abdul dake zaune yasha jinin jikinshi , ahankali Abdul ya daga kai ya kalli fuskan Salem, yaga gefen fuskanshi jajur kauda kanshi yayi, kallon shi Salem yayi
"Alh Abdul let's go to masjid" yayi maganan kaman babu abinda ke damunshi, Kallonshi Abdul yayi
"Sir am very sorry.. Ni na kawo silly idea dake jamaka wulakanci...dan Allah in ranka bazai baciba mu bar wannan hunting..." Karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Tausayamin kake?..to for your information banason self pity sannan bani bane abin tausayi..wannan shegiyar yarinyan ce abin tausayi...kuma kaga wannan quest din yanzu muka farata don ya koyamin abubuwa da dama and most especially ya koyamin ba duk abu mai kyalli keda kyauba wato not all that glitter is gold..ka ga tafiya ta masjid" ya fita ya bar Abdul nan zaune, yana fita Abdul yabi bayan shi da sauri.


๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค๐Ÿ’œโค๐Ÿ’›

"Mami kin san abinda ya faru wajen aikina yau?" Tawa ta tambayi mamanta, Matan girgiza kanta tayi sannan tace
"Ya zaayi in sani tunda ba wurin aikimki nakeba" Matan ta amsa mata da yarensu itakuma tawa tana magana da hausa kasancewan tanajin yarensu Amman bata Iya yinshi itakuma Maman bata Iya hausaba sosai, tawa ta cigaba dacewa
"Mami wata yarinyce ta mari wani babban mutum a gaban restaurant dinmu..wai dan ya dan gogi motanta da taxi dinshi... Wallahi mami mutum saida jini ya fita a hancinshi... Ni kuma nayita zagin yarinyan...." Da sauri mami ta katseta dacewa
"Kini...meye ruwan ki ?..kinason ki ja manako?" Dan turo baki tayi
"Mami mutum zai girme brother tajudeen fa..."
"Ina ruwanki koya girmi babanki...please karki jamana matsala... Kinga ta abinci muke ..." Ahankali tawa tace
"Yes mami.. Gobe zan saya maki inhaler ki don madam ta cire daribiyu cikin kudin aikina don na sayawa mitumin da aka Mara cotton wool... Kuma mami cotton wool din ashirin na tsaya Amman Dan zalunci ta cire min Dari biyu" ahankali Matan tace
"Naji Allah ya saka maki..Amman karki kara shiga abinda ba ruwanki"
"Yes mami" tafada sannan ta mike ta sauke abinci dake kan stove cikin Dan karamin tukunya ta zubawa mami sannan ta dauki mafici tana hurawa mami suna labari kaman yanda suka saba.


๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค

Aranar da ameera ta mari Salem taje office din babanta take bashi labarin abinda yafaru da kuma yanda ta maka mashi mari, dad dinta jinjina mata yayi yana cewa
"That's daddy's angel" wuri ta samu ta zauna acikin daya daga cikin wasu relaxing sofa dake office din dad, sannan ta kurawa photo Salem da dad dinta dake manne jikin bango. Da alaman Salem baisan ana daukanshi photon ba Amman still he's looking breathtaking. Kurawa photo ido tayi tana tunanin
"Wannan mijin mai rabone" tafada tana lumshe idanuwanta
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’šโค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’™๐Ÿ’šโค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ4โƒฃ

Sai tunani take tana cewa
"Duk wacce Allah ya zaba amatsayin matan wannan bawan Allah ta huta...imagine being married to the most handsome and the richest guy in africa...kam kome kakeso a hannunka..ka hau the latest car...ka saka the latest version of clothes and kaci abinci daga the best cook in Nigeria sannan ka zauna in the best house Kuma ka maida kasashen waje kaman zuwa toilet..." Tana cikin tunanin wata zuciya tace mata
"Ameera ki farka daga mafarkin da kike...don sam baki da chance... Kilan bazaki taba ganin shi ba har ki mutu" bakinta ta tabe tare da gyara kwaciyanta, sai dab da magrub suka koma gida, motan dad dinta gaba nata bayan nashi.

Bayan sun gama dinner wayan dad yayi ringing, yana ganin mai kira ya gwalo idanuwanshi tare dacewa
"Allah ya sa lafia.." Yafada yana picking wayanshi
"Hello sir..good evening.." Shuru dad yayi yana sauraron abinda oganshi yake cewawa sannan yace
"Sir ban bude emails dinava " mutum magana yayi kafin dad

Please Login or Register in order to submit comment