Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yafada in a funny way
"Nidai kar kasha...we will look for another way...."
"Princess babu other way..."
"Da akwai mana..." Tafada tana daga mashi gira... " murmushi yayi,
"Tell me.." Ya fada mata, kiranshi tayi da dan yatsa daya, lumshe idanuwa yayi ya matsa daf daita,
"Bring your ear..." Ta fada mashi, ba gardama ya kai kunnenshi saitin bakinta, magana ta fara gaya mashi ahankali, gani nayi Salem na murmushi , daga kanshi yayi ya kalleta taka daga mashi gira
"Are sure you will be doing that?..." Murmushi itama tayi
"Yes...I have done it before.. Haven't I?..."
"Yes you have..." Yafada yana shawota jikinshi,
"And I will buy you a house in lekki and Dubai..." Dariya tayi
"There is no need for that..."
"Nidai Sai na saya maki...." Yafada yana kissing dinta.


Wacegari around 10 Khalid yazo yiwa ameera ban kwana, yanda yake magana gwanin ban tausayi,
"Baby don Allah don't choose somebody else... Wallahi I need you in my life ...nasan sanadin ki rayuwa ta zata chanza..." Ameera dake sanye da fitted gown na super red da red Vail, batace komai ba don kanta kasa, bata gane abinda yake nufi da ta sanadin ta zai chanza ba and she don't want to know, all she knows is that she has fall in love with him,
" zan tafi ...Sai next week..."
"Ok...Allah yatsare...." Tafada ahankali
"Zanyi missing dinki..."
"Me too..."
"Pls escort me..." Yafada, bata kara cewa komai ba ta bi bayanshi har wajen motan shi, yana shiga ya mikawa mata wani white Leda mai kyauri bai da girma, kaman ba zata amsa ba ta sa hannu ta amsa tayi godiya, tana bude Dan ledan ta ga kudi bandir din 1k guda uku,ido ta bude zatayi magana ya ja motannshi yana waving dinta ya bar wajen, ameera dana sanin amsan kudin tayi don sam bata San kudi bane.
Cikin falo ta koma ta bawa mom kudin
"Ki bar amsan kudin shi tunda baki da tabbas zaki aureshi..." Mom ta fada mata tana amsan kudin daga hannun ta, wrapping kudin tayi da ledan ta ajiye cikin drawer. Jiki ba kwari ta mike ta koma dakinta ta kwanta.

Tana bacci wajen karfe twelve tanaji ana taba kafanta, tana bude ido ta ga zeenat tsaye, mikewa tayi zaune tana murmushi
"Yaushe kikazo?.."
"Yanzu nan..." Zeenat ta amsa mata tana zama bakin gadon,
"Babe ki shirya muje shopping..." Ahankali ta girgiza mata kai alaman aa, idanuwa zeenat ta kwalo
"Kam...lallai kin chanza ke da baki gajiya da shopping?..."
"Kayan ne sunyi min yawa kuma baka Iya saka biyu lokaci daya...."
"Nasani amma yaya sultan ne yace zaikaimu shopping.." Tanajin yaya sultan Sai ta tuna da abubuwan daya fada mata jiya.
"Sis I think my yaya is in love with you..." Zeenat ta fada mata, ameera shuru tayi tana kallon zeenat, Ahankali ta fada mata duk abubuwan da Sultan ya fada mata don babu secret tsakanin su, ta kara dacewa
"Kuma Khalid ya rigashi..." Tsaki zeenat taja
"Uban waye Khalid..
." harara ameera ta balla mata
"Ban saniba..." Ta amsa mata cikin tsiwa, Dariya zeenat tayi
"Ai wallahi dole ki zabi yaya...remember am talking about sultan... The real Madrid football player..."
"Babe stop.... Gaskiya inason Khalid... Kuma har ga Allah sultan is my first crush...nidai am confuse..." Zeenat shuru tayi tana kallon kawarta, zatafi kowa murnan auren sultan da ameera,
"Allah yasa yayana zaki zaba donkunfi dacewa...amma Allah ya zaba maki Wanda yafi alkhairi..."
"Ameen"
"Yanzu tashi ki shirya mu tafi shopping kar yaya yayi tunanin kina disgashi..."
"To amma pls pretend...karki nuna mashi na fada maki komai.."
"No...problem" zeenat ta amsa mata, ahankali ameera ta mike ta shiga wanka.
Bayan ta fito ta shirya cikin Arabian gown, gyara gashin kanta tayi sai, zeenat na zaune Sai kallon ta take tana aduan Allah yasa sultan zata zaba. Zeenat Sai binta take da ido
"Babe wannan kallon fa?..." Ta tambayeta tana shafa wet lip gloss
"Ba komai.." Tafada cikin nutsuwa, har lokacin bata bar kallon ta ba, perfumes ta fesa jikinta Sannan tace
" muje wajen mom in fada mata zan fita..."
"Ok.." Zeenat ta fada tana bin bayanta. Wurin mom sukaje ta bata izini Sannan suka sauka downstairs, sultan ne zaune da drink gabanshi yana ganin ameera ya kura mata ido ko blinking baiyi, gaidashi tayi ya amsa cikin cool voice Sannan suka tafi, ajikin motan shi yayi saurin kaiwa tare da bude kofan gaba, yanmatan tsayawa sukayi suna kallon junansu, da gangan zeenat tayi kokarin shiga sultan ya tureta yana cewa
"Dalla matsa... Ko saurayinki yayi kadan in bude mashi kofa balleke..." Zeenat Dariya tayi, ya kalli ameera
"Angel pls enter..." Cikin nutsuwa ta shiga. Suka bar wajen.
Wani katafaren super market suka shiga, sultan Sai daukan ta pics yake batare data saniba, ameera bata dauki komaiba, duk abinda zeenat ta dauka Sai sultan yace tayi doubling dinshi, daga nan suka shiga cikin gari zuwa wani Indian restaurant, nan sukayi lunch, sultan Sai kallon ameera yake, ameera kam banda tunanin Khalid babu abinda takeyi, Allah Allah take su koma gidandon ta kirashi, kawai Sai wayanta ya fara ringing, sam ta mance gabansu sultan take, tana picking Sai tace
"Babyna I miss you..." Maganan ne ya makale mata abaki ganin yanda sultan ya bata rai cikin few seconds,


_Jamaa kuyi hakuri zakujini shuru gobe saboda zanje wedding, insha Allah Sai ranar lahadi, in muna da rai. Once again thanks for your love and affections_๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’šโค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ


ยฎzuwairat(ummu Maryam)


7โƒฃ6โƒฃ




Fuskan shi kaman bai taba Dariya ba, ahankali ameera ta mike daga kan kujeran ta, ta kalli zeenat
"Babe bari in dawo.." Zeenat balla mata harara tayi ta dauke kanta, sultan kam ajiye spoon din hannun shi yayi don Sai yaji abinci ta fita ranshi, yasan he just came into the game, amma bashi da aduan data wace Allah yasa ameera ta amince dashi don gani yake in ya rasa ta yana iya rasa ranshi.
Gefe daya ta tsaya ta sha hiranta da Khalid don har mancewa take dasu wurin, sultan kam ya shika yayi fam, duk yanda yake kokarin sakin fuska ya kasa daman gashi bai saba da sakin fuskan ba, Sai bayan minti talatin ta dawo ta zauna kaman Mara gaskiya, kallon ta yayi ya sakar mata Murmushin karfin hali, kincin sauran abinci tayi
"Finish your meal..." Sultan ya fada mata yana kokarin daidaita muryanshi,
"AI yayi sanyi...ta bar abinci ta tafi gulma..." Inji zeenat dake taya yayanta kishi, ameera daga kai tayi ta harareta. Mikewa sukayi suka koma gida babu mai cewa komai, bayan yayi parking mai gadi ya bawa kayan ameera ya kaimata cikin gidan. Wurin ta yazo Sannan yace
"Can I come tonight?..." Ya tambayeta cikin nutsuwa,
"Yes.." Ta amsa mashi ciki sanyin murya don gani take bata kyauta mashi ba data amsa waya gabanshi.

_One month later_

Yanzu Tawakaltu ta maida jikinta, Sai yanzu tafara jin dadi honeymoon, no more stress daga Salem, yanzu tafara amfani da abubuwan da Haj kudirat ta koya mata, kulawa ta mussanman Salem yake bata, har yanzu basu bar Hawaii ba, duk abinda Tawakaltu kesonyi Sai ya hanata yana cewa bi ahankali karkiyi dismounting Dana ko diyata, kullum Abdul na bashi labarin soyayyarshi da ameera Sai ya tsinci kanshi da jin haushi, shi kanshi yana mamakin yanda yake ji duk sanda Khalid ya fada mashi maganan ameera,, yana kwance kasan carpet daure da towel, Tawakaltu na zaune bayan shi da alaman massage takeyi mashi, wayanshi ya fara ringing, saida tawa ta bugi keyanshi Sannan ya dauki wayan yana cewa
"Wai waye..." Yana ganin Khalid ne yaja tsaki Sannan yayi picking, as usual labarin ameera ya fara bashi,
"Dan Allah in baka da abinda zaka fadamin Sai maganan ameera then you should stop calling me..." Yafada afusace tare da kashe wayan, tawa sauraron yanda yake magana tayi
"Sugar..." Ta kirashi tana shafa shoulder dinshi,
"Yes my princess..." Ya amsa mata
"Kasan me?..." Ta tambayeshi, kai kawai ya girgiza mata, Sannan ta cigaba dacewa
"I know you love ameera..." Hannun yasa ya fallawa naked laps dinta duka har saida ta saki kara
"What did you do that for?..."
"For saying am in love with ameera..."
"AI banyi karyaba...I can hear jealousy in your voice..." Dariya yayi
"How can I love Aisha when I have a full package with me...kawai kiranshi yana damunane...yanzu gashi ya katse min jindadi...."
"Kadai fadi gaskiya shaidanyaji kunya...." Tana shafa waist dinshi da aloe vera moisturizing cream tace
"Naga yanda friendship dinka da Khalid zai kasance bayan ya auri sis ameera..." Kaman an fixgi magana daga bakinshi yace.
"Basai ya aureta ba..." Sai kuma ya kama bakinshi, Dariya tawa tayi tana cewa
"Nidai am not jealous cos nasan I have a special place in your heart.. So kowama is welcome...." Tafada tana maida hannun ta chest dinshi, ya saki kara....
Yana cewa
"Yanda kike rikitani ai all the heart is yours...you are killing me with your love... Ban ganin kowa saike..." Yafada yana nishi saboda yanda take massaging bare chest dinshi,
"Kuma wallahi kome kike so is yours..." Yafada kaman zaiyi kuka, Dariya tayi,
"Hmmm ai baka yimin kukan dadinba..." Tafada tana kara chanza salon massage din da take yi mashi, kaman zaiyi kuka da gaske yace
"Zan...zanyi..."
"Ai banjiba ko?.." Tafada cikin shagwaba, ihu ya fara ahankali kaman zaiyi kuka
"Please.. Wallahi zanyi ma'am...." Dariyan keta tayi, ta sakeshi ta mike,
"Princess don't leave me now..." Yafada yana Dan juyowa Dan kallon ta,
"Sugar relax.. Wani abu zan dauko cikin fridge..."
"Let me carry you..." Yafada yana kokarin mikewa, juyowa tayi
"Don't move an inch..." Tafada mashi in a commanding manner
"Yes ma'am..." Yafada yana maida kanshi kan pillow, fridge ta bude ta dauko bowl din ripe strawberries, ta dawo, ajiye bowl din tayi ta dauki daya ta sa ciki bakinta Sannan ta dauko dayan
"Open up..." Ta umarce shi, ba musu ya bude mata bakinshi ta sakala mashi strawberry daya Sannan tace
"Hold on to it...karkayi biting.." Murmushi yayi baice komai ba cos babu bakin magana, wasa tacigaba dayi mashi, baisan lokacin da yayi chewing strawberry dinba, da sauri ya juya yana cewa
"Pls princess go to the main part..."



Alhamdulillah yanzu an fara hidimomin bikin zeenat, komai da ameera akeyi, abinda yake bawa ameera mamaki yanzu shine yanda bata iya zaba tsakanin sultan da Khalid, da tana ganin tafison Khalid amma she was wrong, don yanzu tsohon son yarinta data yiwa sultan yafara lighting up, don tana jinshi har cikin jininta, yanzu in zaa tsareta da wuka ta zabe daya daga cikin su saidai a kashe ta cos bazata San Wanda zata zaba ba, bata taba tunanin zuciya daya na Iya kamuwa da son mutane biyu ba don har browsing tayi taga result din inda ake cewa is not possible wai dole Sai daya ya fi daya, itadai she loves them both, kuma tana shin saa basu kara tadda junansu ba, duk week end Khalid ke shigowa, Sai tayiwa sultan dubara kan zata gezawa cos kusan kullum yake zuwa gidansu, affan kam yana son sultan sosai don kullum inyazo Sai sunyi training, dama gashi da on football kuma ga international football har gida, abinda ke bawa ameera haushi shine wai har affan baison zuwan Khalid wai shima yana taya sultan kishi, last week da Khalid yazo ta fada mashi suna da biki kar yazo wannan week end don suna bikin zeenat, da kyar ta shawo kanshi don cewa yayi zaiyi attending, ranar kunshi, yan matan sunfi su talatin zaune, dukkan su sunsa ankon riga da skirt, black skirt da red top Sai Vail, yawancin yan Matan ameera ta taba wulakantawa mussanman lokacin aurenta da Salem,
"Ayiiiirrrrr...." Wata tayi guda Sannan tafara cewa
"Yanzu muka san ana biki...komai is well organized...." Kusan su biyar suka bushe da Dariya Sannan wata tace
"Hmmm wasu Sai wulakanci amma duk wulakancinsu saida bayerabiya ta koresu daga gidan miji..." Bata idaba ba wata ta katseta dacewa
"Gidan miji?.... Kin manta mutumin in questions cewa yayi bai taba aureba Sai lokacin auren shi da wannan bayerabiyar...." Ameera dake zaune kusa da zeenat ta mike, da sauri zeenat ta rike mata hannu ta maidata zaune Sannan ta kalli yanmatan tafara cewa
"Dan Allah banason haka...duk wacce tasan ba dan kunshi ta zoba kawai ta tafi...after all ko wacce nada matsalan ta amma Sai Ku ajiye gefe Ku hau na mutum...pls let's take care of our problem first before looking at others people's lives..." Zeenat ta fada hannun ta rike da hannun ameera da take kokarin kwacewa don barin wurin,
"Anya wannan itace wancan?...cos wancan is rude and arrogant...." Inji wata, ameera kallon zeenat tayi da idanuwanta da suka chanza kala
"Babe ki sakar min hannu in koma gida..." Tafada cikin whisper kaman zatayi kuka, itama cikin whisper zeenat tace
"Haba babe...saboda those nonentities zaki tafi?..."
"I need to go home now...I can't stay... Pls kiyi hakuri.."_tafada hawaye na faruwa idonta,
" OK...bari in kira yaya ya maidaki gida..." Zeenat ta fada tana dauko wayanta, text ta rubutawa sultan kaman haka
" _Yaya pls ka zo ka dauki ameera ga friends suna ta zolayanta kan abinda ya faru tsakanin ta da sir Salem"_ ta tura mashi, bayan kaman minti talatin sultan yazo cikin ranshi yana aduan Allah ya hada shi da Salem
"He will pay for making my ameera a laughing stock..," yafada yana shiga inda yanmatan suke, suna ganin shi ko wacce ta bude baki kaman sakara don dukda yana baki babu abinda farin mutum zai nuna bashi, fuskan
Babu faraa Ya nufosu, wasu da basu sanshi ba sai cewa suke
"Wannan kaman popular Dan kwalo sultan..."
"Eh mana....bakusan yayan zeenat bane shi?..$ wata ta amsa masu duk suna magana cikin whisper, zeenat na ganin shi ta Dan taba ameera data sadda kai kasa hawaye na zuba amma babu Wanda yasan kuka takeyi
" babe ga yaya...." Zeenat ta fada mata, da sauri ta goge hawayenta tare da mikewa, Vail dinta Sannan ta dauki bag dinta ta nufo sultan batare data daga kantaba cos batason ya gane tana kuka, shikuma yana ganinta ya San kuka take, ta taho shima ya taho Sannan ya fara cewa
"My jewel waya taba min ke!.." Yafada yanda duk wacceke wurin zaiji abinda yake cewa, yacigaba dacewa
"Sai ki zubda hawayenki saboda wata idiot..." Dukkan su kallon shi sukayi yafara nuna su da yatsa yana cewa
"Wallahi duk wacce ta kara sanadin hawayen my jewel Sai nayi maganinta... Ko yar wacece...." Yana kaiwa nan yakama hannun ameera data cigaba da hawaye suka bar wajen.
Suna fita waje ya bude mata kofan motan ta shiga, zagayowa yayi ya shiga, tsayawa yayi yana kallon ta, har lokacin hawayenta bai tsaya ba, daga kanta tayi ta kalleshi,
"Da baka fada masu komai ba..." Tafada cikin natsuwa, hannun shi yasa ya goge mata hawaye Sannan yace
" I have to warn them,..and shi kuma Salem I will deal with him..zan nuna mashi gaba da gabanta... Am just waiting for the right time... " kai ameera ta girgiza mashi
"No... Salem help my life... He changed me...taimaka min yayi..."
"I don't bloody care...what he did was barbaric...he have to learn his lessons...kawai just wait and see..." Kuka ta farayi tana cewa
"Wallahi babu ruwanka da sir Salem... He..." Katseta yayi dacewa
"Do you love him?... Why are you covering for him... Duk Wanda zaiji abinda yayi maki knows it is wrong..." Kuka ta farayi sosai tana cewa
"Bance ina sonshi na...kawai don't go near sir Salem or this relationship is over..." Tafada tana kokarin fita daga cikin motan, da sauri ya rike mata hannu
"Sorry for the accusations... Da nayi niyyan yi mashi rashin mutunci.. Amma na bari...since it is what you want..." Yafada cikin natsuwa, har lokacin yana rike da hannun ta, komawa tayi tare dayin relax tana goge hawayenta.


Daga wannan ranar duk yanmatan basu kara gigin yi mata habaiciba, duk events da ita akeyi amma ba daita ake tashi ba don sultan daukan ta yakeyi su yita yawo cikin gari kafin ya maidata gida.

Yau akayi walima gidan amarya, ameera tayi mamakin gidan don sultan bai barta kai amarya ba, Mahmoud din data raina ashe shima yana da hali daidai kwarkwado don gidan ba karamin tsaruwa yayi ba, cikin bedroom ameera ta shiga lokacin tana shirin komawa gida kallon zeenat datayi tsuru2 tayi ta fashe da Dariya,
"Amarya ni zan tafi...yaya sultan yana jirana waje...." Ameera tafada mata, rike hannun ta zeenat tayi tana cewa
"Yanzu babe bakisan yanda first night yakeba?..." Ameera shuru tayi tana kallon zeenat, Sai Tawakaltu ta fado mata a rai,
"Hmmm...sis ya zaayi in Sani tunda ban taba ba...kawai get ready for the worst..." Idanuwa zeenat ta kwalo
"The worst fa kika ce..."
"Eh mana...baki ganin yanda Mahmud yake zumudi?..." Tafada tana dariya,
"Bakomai ai... Nasan duk wahala zuwa gobe nawuce wurin... Amma ke keda sauran wahala... Remember my bros is an athlete...." Baki Ameera ta tabe
"Ba Sai na zabeshiba..." Harara zeenat ta galla mata tana cewa
"Naga ta yanda zaki CI amanan yayana..." Ameera kwace hannun ta tayi tana cewa
"Babe Sai munyi waya..I will call you first thing in the morning..." Tafada tana fita daga dakin.


After three day which is Friday Ameera tana kwance tana tunanin zuwan Khalid gobe don basu dade da wayaba, juya kwanciyan ta tayi tare da kara daukan wayanta, YouTube ta shiga tana duba, latest wedding ta fara dubawa Sai taga the wedding of the year nasu Salem da tawa, murmushi tayi ta bude tana cewa
"Let me see your handsome face...." Relaxing tayi ta fara kallo, few minutes later taga kaman Khalid tsaye yana bada jawabi, da sauri ta maidashi baya tana cewa
"It can't be..." Kara kallo tayi taga confirm shine, ido ta kwalo
"Oh my Allah!....." Tafada tana mikewa da sauri.
Tun kafin ta shiga dakin mom ta fara kuka tana kwalawa mommy kira
"Mommy!...mommy!..." Ta dinga kwalawa mom kira,da sauri mom ta fito ta tare ta, fadawa tayi jikin mom
"Meye!.." Mom ta tambayeta cikin tension, Ameera bata samu bakin cewa komai ba sai kuka take, girgizata mom tayi da karfi
"Wai meye Dan ubanki kike neman tadamin hankali?.." Mom ta sake tambayeta, tana kuka ta mikawa mom wayan
"Mom ki kalla ki gani...Khalid friend din sir Salem ne..." Tafada cikin kuka, kin amsan wayan mom tayi
"Saboda wannan kike neman sa hawan jinina ya tashi?... AI shikenan ba sai kin aureshiba don bazaayi sakin wawa dakeba...." Ameera shuru tayi bata ce komai ba sai kuka
"Shima munafiki ne...AI Sai ya fada maki gaskiya amma ya boye maki..da niyyan shi sai kunyi aure ki gane gaskiya ko?... To alhamdulillah Sai ki godewa Allah da bai bar hakan ya faruba..." Ameera kuka ta cigaba dayi
"Dalla rufemin baki..." Da sauri taja bakinta ta tsuke
"Yanzu mom me zan fada mashi?... Inason..." Buge mata baki mom tayi
"Na anyi magana Sai kice kinason sonshi...Khalid... Kinason shi....sultan kinason... Bari ubanki ya dawo..." Tafada tana komawa dakinta, Ameera zama tayi nan kasan tiles tacigaba da kuka
"Ashe daman Salem yasan Khalid?..."
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’›โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™
ZAKISAN KONI WAYE
โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu Maryam)



7โƒฃ7โƒฃ



Tafada tana kuka,
"God have mercy on me..." Mikewa tayi ta koma dakinta ta cigaba da kuka atakaice aranan bata yi baccin kirki ba da tunanin yanda gobe zata kasance ta kwana don tasa ya zama dole ta rabu da Khalid, bazata iya auren best friend din Salem ba, she wants Salem ta be her past and not the best friend of her hubby, kashe wayan ta tayi gaba daya don batajin zata iya magana da mutum daya cikin su.

The next day as usual tayi preparing tarban Khalid kama kullum, wanka tayi ta saka kaya masu kyau amma ko kadan babu kwalliya a fuskan ta, asalima idanuwanta sun kumbura ko kallon ta mom batayiba. Da kam baice kala ba don mom tayi briefing dinshi kan abinda ke faruwa kuma ya fada mata don Khalid na abokin Salem ba zai hana aure atsakanin shi da Ameera ba saidai in Ameera batason auren shi. Amma mom ta jaddada mashi kan ya fadawa Ameera ta fidda mijin aure. Haka akayi don bayan sun gama lunch alokacin an jera abinci dakin saukan baki dad ya kira Ameera ta sameshi dakinshi, tana zuwa ya fada mata ta fidda mijin aure shuru tayi bata ce komai ba. Dad sallaman ta yayi tana komawa daki Khalid ya kirata ya shaida mata ya iso, jiki ba kwari ta yafa Vail dinta taje wurin shi yana tsaye jikin motan shi looking more handsome than ever, murmushi karfin hali ta sakar mashi Sannan ta kaishi sakin saukar baki yaci abinci kaman babu abinda ke faruwa don sam bata nuna mashiba, saida ya gama ya kalleta ta yana murmushi
"Baby kaman idanuwanki sun kumbura..." Itama murmushi tayi
Sannan tace
"Dan Allah inason ka fadamin alakar dake tsakanika da sir Salem..." Kaman an sokawa Khalid arrow yaji don he never see that coming, da sauri ya kalleta
"Angel what are you talking about?..." Ya tambayeta muryan shi na rawa kaman mara gaskiya, Sai lokacin ameera ta daure fuska, yanayin ta ya bawa Khalid tsoro don baisan such beautiful face yana Iya turning pale haka ba. Mikewa tayi cikin nutsuwa
"To shikenan... I thought you are truthful but am wrong..." Dasauri Khalid ya rike mata hannu
"Baby am so sorry..." Bai idaba ta kwace hannun ta, cikin tashi hankali ya fara cewa
"Baby am sorry for keeping it from you... Salem has been my closest and childhood friend..." Kai Ameera ta gyada mashi ahankali,
"Very good... So nasan kasan abinda ya faru tsakanina da Salem..." Khalid dake sweating ya gyada mata kai
"I know everything... Baby am sorry for all that.. I should have told you the truth..." Murmushin karfin hali Ameera tayi
"Wallahi ba komai..." Khalid kallon ta yayi don tabbatar da ba komai amma he knows something is wrong, Ameera dake tsaye har lokacin tace
"Nidai yanzu hakuri nakeson baka..." Da sauri Khalid ya fara cewa
"No!... No....pls don't do this to me...wallahi tunda Salem ya bani labarin ki na fara sonki...son da nakeyi maki yasa nayi forcing dinshi ya bani takardan ki bayan ya shaida min bashi da raayin zama da mata biyu...pls ki yafemin kar ki barni...pls..." Ya karashe maganan kaman zaiyi kuka
Murmushin takaici Ameera tayi wato itace topic of discussion dinsu, ita Ameera suka maida abin chanji, wato shi Salem baya sonta Sai ya barwa abokinshi dayake sun dauketa mara galihu
"Dan Allah kar ki rabu dani saboda Salem...." Taji Khalid nacewa, murmushi ta karayi daka ganta Sai ka rantse abun bai dametaba
"Nagode da sonka agareni...amma it can't..." Da sauri Khalid ya sa hannun shi kan bakinta
"Pls don't say it... Pls I beg you..." Ahankali ta cire hannun shi daga bakinta sannan tacigaba dacewa
"Kayi hakuri.. Allah zai baka wacce ta fini..." Kai ya fara girgiza mata
"Dan Allah karki bari laifin Salem ya shafeni..."
"Nidai kayi hakuri kawai,.,,..I can't marry my ex's best friend..."
"In kinason in rabu da Salem I can forget about him amma kar kiyi min haka...you are the best woman for me...nasan son da nakeyi maki zai chanza min yanayin rayuwa...."
"Kawai kayi hakuri... Yau zan fadawa sultan ya aiko iyayenshi..." Tafada tana kokarin fita, da sauri ya tari gabanta yayi kneeling,
"Baby look at me..." Ya umarceta cikin sanyin murya, ba musu ta kalleshi, ahankali yafara cewa
"Zan fada maki dirty secret dina Wanda ko gidanmu babu Wanda yasan ina da wannan hali..." Shuru yayi ya hadiyi wani Abu Sannan ya cigaba dacewa
"Ni mazinaci ne!...I have slept with numerous women...." Gaban Ameera ya fara dukan uku2 tana kallon how innocent his face looks,
"Amma tunda na ganki na fara nadaman halina...tunda na ganki na daina ganin ko wacce mace da kyau ko wani abu... Your love alone change me..in kin zama matata it will change me for ever..zaki samu ladan haka...please don't leave me..." Ameera shuru tayi tana neman hanyan bi, gani take yana iya raping dinta, acikin zuciyanta tana tausayin shi in har abinda ya fada mata gaskiya ne amma har ga Allah bazata iya zama Matan aminin Salem ba, da kyar ta samu courage ta fara cewa
"I know there is another woman out there for you... Pls am sorry..." Wiwi Khalid ya fara kuka kaman yaro yana cewa
"I can't love any other person.. Ke nakeso...if I loose you I loose my life... Dan darajan manzon tsira ki rufamin asiri.. Pls don't dump me ..." Ameera bata taba ganin saurayi yayi kneeling gaba mace yana kuka ba sai a film. Amma gashi yau a very handsome and flamboyant guy is kneeling before her not only begging for her love but crying for it, kura mashi ido tayi tana tunanin irin kalan zuciyanta, tanason Khalid likewise

Please Login or Register in order to submit comment