Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

what's your reason for calling"
"Daman ummace ta aikeni zoo road shine nace inzo ki rakani?" Ameera kaman jira take
"Yes kizo daman nagaji da gidan nan kuma mom ta hanani fita"
"OK..gani nan zuwa Amman please ki shirya don nasan halinki"
"Don't worry yanzu nan zan shirya" suka katse wayan. Da sauri ameera tabude katon wardrobe dinta Wanda ke shake da kayan sawanta,wash purple Arabian gown ta fiddo tare da Dan figigin Vail din kayan.
Dagudu tashiga bathroom ta watsa ruwa sannan tafito, cikin sauri ta shirya cikin kayan sannan ta dauko makeup kit dinta ta zauna gaban mirronta ta tsara kwalliyanta looking so breathtaking, sannan ta fesa turuka masu kamshin gaske. Wurin shoe rank dinta ta nufa ta dauki wasu light purple high heels sannan ta zauna bakin gadonta tana jiran zuwan kawarta mai suna zeenat.

Batafi minti 20 dazamaba zeenat tazo, taganinta ta window taga batazo da motaba
"Kambu ..badai da motata take son mujeba..." Bata karasaba zeenat tashigo
"Babe ina motanki.." Ameera ta tambayeta
"Tana wurin gyara wallahi...muje da naki..." Da sauri ameera ta girgiza kanta sannan tace
"Babu fuel kinsan daddy yana abuja kuma kona gayawa mom bazata bani ba..so yanzu meye abunyi?"
"To zai mu hau taxi..." Dan table baki ameera tayi sannan tace
"Amman fa kinsan banson hawan public car...mutum na iya kamuwa da wani communicable disease.. Balle bakasan ubanwa da uwarwa suka taba hawaba...." Tunda tafara maganan zeenat ke kallon ta, saida ta gama sannan tace
"Ke dai kullum halinki bai chanzawa...kawai daga hawan taxi sai my kamu da disease?... Dalla taso mu tafi time is not on our side" tafada tana fita daga dakin.
Zeenat kyakyawace Amman ko kadan bata kama kafan ameera ba...Amman when it come to character she's an angel.

Itama ameera fita tayi tabi bayanta Amman saida ta dauki dettol disinfectant spray tasaka cikin handbag dinta.

Dakin mom dinta suka tafi tana ganin ameera ta hada giran kasan dana sama, zeenat na shiga dakin ta saki fuskanta, bayan sun gama gaisawa ameera tace
"Mom zan raka Zainab zoo road" Matan shuru tayi kaman bataso sannan ta daga kai ta kalli agogn dake jikin bangon dakinta
"Kunga this is after 4, Ku tabbatar kun dawo kafin 7" da sauri suka amsa
"da yes mommy" sannan suka fita
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œโ™ฅ๐Ÿ’›
ZAKISAN KONI WAYE
โ™ฅ๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค๐Ÿ’›
ยฎzuwairat(ummu maryam)

8โƒฃ

Suna fita suka tsaida taxi amman mutum in na tsayawa ameera ta kalleshi sannan tace
"Malam ka wuce" mutum kallon ta yayi
"Malama ai bake kika tsaidaniba " mutum ya amsa mata, ameera tabe baki tayi sannan tace
"Kayita tsayuwa nan" ta gayamashi a tsiwace, itakam zeenat ta saba da halin ameera, mutum ya watsa mata mugun kallo sannan yace
"Shegiya mai kama da aljannu" itama ta kalli mutum Wanda akalla ya girmi ubanta tace
"Shege mai kama da shaidanu" mutum fixgan motan yayi yabar wurin yana cewa
"Banza mara tarbiya" dukda mutumin ya tafi bai hana ameera cewan
"Uwar data haifekace mara tarbiya" kallonta zeenat tayi tare dacewa
"Haba shekira ai wannan mutumin ya girmi daddy fa?.." Harara ta ballawa zeenat sannan tace
"Daddy ki ya girma..don ni kam bai kai ubanaba balle ya girmeshi" Dan tsoki zeenat taja kafin tace
"Wata rana sai kin ja ruwan dafa kanki wallahi...nonsense kawai" itama ameera tsaki taja sannan tace
"Kema kinsan baa haifi mutum ba wallahi..kuma kika kara cemin nonsense sai injuya gidan ubana ai ba dole bane in rakaki" haka suka dan taba chan2 baki kaman yanda suka saba kafin kowa tayi shuru.

Sunfi minti ashirin tsaye, duk dan taxi din da suka tsaida sai ameera ta kare mashi kallon sannan tace ya wuce,saida suka tsaida taxi yafi biyar, suna tsaida na shiddan zeenat tayi sauri ta shige.

Itakam ameera saida ta fesa dettol disinfectant spray a inda zata zauna, mai motan juyawa yayi ya kalleta, itama ta kalleshi tare dacewa
"Non entity". Ko kallon zeenat batayiba har suka isa zoo road.

Karfe shida da rabi suka fita daga gidan yayan zeenat, dan takawa sukayi kafin su karasa bakin titi, kaman dazunma duk mai taxi din da suka tsaida sai tace suna kama da kazamai ko kuma tace sun cika muni

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’™๐Ÿ’™

Salem kam har ya mikawa Abdul car ya daga kai sai ya hangi wasu yanmata su biyu tsaye, maida key din yayi Wanda hakan yasa Abdul cewa
" sir ya akayi kuma" ya tambayi Salem, dan murmushi yayi sannan yace
"Kalli wasu babe chan.bari muje don wancan mai purple gown din tayimin.." Dan daria Abdul yayi sannan yace
" sir ai magrub ya gabato..." Salem ya katseshi da cewa
"Don't worry...in har suka tsadamu to zamu san gidansu, gobe sai muje"
Rage gudun motanshi yayi lokacin daya kusa zuwa inda suke tsaye, aikam zeenat na ganin taxi sai ta tsaidashi, dadi Salem yaji cikinranshi don ya gagara yaji muryan budurwan dake sanye da purple gown. Yana tsayawa ameera ta zubawa Salem ido, shima zuba mata ido yayi yana kallon ta bako kiftawa, bai ankaraba yaji dayan budurwan tayi saurin bude motan tashiga, itakam saida taga gama kallon Salem sannan ta ja wani irin dogon tsoki tare da kauda kanta gefe
"Please babe ki shigo mu tafi kinga magrub ta gabato" yaji budurwan da tashiga motanshi tace, itakam ameera tafi minti biyar sannan ta bude handbag dinta ta dauko dettol disinfectant spray ta fesa inda zata zauna, Abdul da Salem juyawa sukayi suna kallonta, itama kallonsu tayi da sexy eyes dinta kafin tace
"Malan wannan kallonfa..ko Baku taba ganin disinfectant bane?" Tafada tana gyara zamanta, Salem kam beautiful mouth dinta ya kurawa ido yana imagining yanda zasuyi tasting. Juyawa yayi ya tada motan lokacin da zeenat tace
"Malan GRA zaka kaimu" .
Yana tafiya yana kallon ameera ta mirror, Abdul nuna mashi hanya yake amman dukan hankalinshi ya tafi ga ameera data fiddo iPhone 7 tana danne2, kaman ance ta daga kai, sukayi 4 eyes, wata irin mugun harara ta balla mashi tare dacewa
"Malam ijn idonka yayi maka ya ka ciro mu raba ...village monger" Salem sauke idonshi yayi tare da yin murmushi, cikin ranshi yana cewa
" wai ne take cewa bakauye alhalin nasan inda naje aduniya da kyar taje kafin ta mutu"

Zeenat matsawa tayi kusa da ameera sannan cikin rada tace
" babe kalli hannun wannan mutumin tare da agogon hannunshi" baki ameera ta tabe sannan tace
"For what?" Salem yaji suna magana ahankali yadan saci kallonsu ta mirror, yaga zeenat nayiwa ameera rada, Amman bayajin abinda suke cewa
"Babe please ki kalla mama"zeenat ta sake cewa ameera, sai lokacin ameera ta daga kanta ta kalli hannunshi.

Gani tayi hannunshi farin kal sannan ga Rolex kwance kan fatan hannunshi, baki ta tabe kafin tace
" kilan barawo ne...INA taxi driver INA Rolex watch " Salem da Abdul Dan kallon juna sukayi dan sunji abinda tace cos baa ahankali tayi maganan ba. Abdul kam murmushi yayi cos yasan they don't know who they are dealing with.

Cikin minti 50 suka isa gra, a wani katafaren gida suka tsaya
"Babe ki shiga gida kawai su wuce dani" zeenat tafadawa ameera,
"Sai munyi waya" ameera ta amsa mata kafin tafita, Salem bayanta yabi da kallo
"Angel" ya furta ahankali
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โ™ฅ๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’šโ™ฅ
ยฎzuwairat(ummu maryam)

9โƒฃ

Bayan su ajiye zeenat, suka samu wani masjid sukayi sallan magrub sannan suka koma gida.
Suna isa aspirin yafara sha kafin akawo mashi abinci, abin mamaki sai ya tsinci kanshi da tunani yarinyan daya sauke, daya kai loman abinci sai yayi murmushi, Abdul kallonshi yayi
"Sir meke saka daria?" Ya tambayeshi cikin girmamawa
"Wallahi yarinyan dazun ce...halinta ya bani mamaki.." Ya gayawa Abdul, shima Abdul daria yayi
"Ai sir yarinyan ta iya ban daria, ga tsiwa" Salem ajiye spoon din hannunshi yayi yana daria
"Wai baku taba ganin dettol disinfectant spray bane?" Salem ya fada cikin irin muryan ameera, daria suka sake yi,
"Wai village monger" Abdul ya fada, Salem kam daria har da rike ciki,.

Wace gari Salem har Allah2 yake mai makeup dinshi yazo yayi mashi don kwana yayi tunanin yarinyan, musamman yanda take tafiya sannan har lokacin bai bar jin kamshi turarenta ba. Har karfe biyu artist din bai zoba, yana kwance kan wani lafiyayyen gado ya dauki wayanshi ya kira Abdul, bayan ringing biyu Yadaga yana cewa
"Sir me kake bukata?"
"Alh ka kira artist din nan yazo mana" dam murmushi Abdul yayi kafin yace
"Sir yau da wuri zamu fitane?"
"Eh" kawai ya fada a takaice

Wajen karfe uku yazo yayi mashi chanjin kala sannan ya fiddo kayan sawa jeans da riga polo, baa taba sa kayanba Amman sun Dan koke saboda wankin da Abdul yayi masu, dagasu yayi yaga sunyi over squeezing, daukosu yayi yaje wajen Abdul
"Alh ka gogemin wannan kayan" ya fadawa Abdul
"Sir...talaka Nada lokacin guga?" Dan daria Salem yayi sannan yace
"Ai ba talakan bane, kuma gaskiya bazan iya tsayawa gaban wannan yarinyan babu gugaba "
"But..." Abdul tafara cewa bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"No but...am commanding you as your boss" da sauri Abdul ya amshi kayan ya gogesu.

Bayan sallan asar suka tafi pizza hut suka danyi eating sannan suka kama hanya gidansu ameera dake sultan road,
Around 5 suka isa gidan, haka nan Salem ya tsinci kanshi da fadiwan gaba ko dan bai taba zuwa gidan budurwa zance bane oho. Wani wuri Abdul yayi parking kasancewan shike tuki, bayan yayi parking Salem yafito, ya nufi bakin gate din gidansu, yafi minti biyar tsaye kafin ya daga gorgeous hannunshi yayi knocking a katon gate din gidan.
Wani mutum ya bude da alaman shine mai gadin gidan ne,
"Lafia?" Yaji mutumin ya watsa mashi tambaya, ahankali Salem yace
"Ina wuni" ya gaida mutumin, saiya ga yanayin mutumin ya sauya zuwa na murmushi
"Lafia lau dan nan..wa kake nema?"
"Budurwan gidan nan nake nema" Salem ya amsa mashi kuma saida yagama furta maganan yaji ba haka ya kamata yace ba.
"Ya sunanta" mutumin ya tambayeshi, dan shafa silken hair dinshi yayi
"Hmmmm...ban san sunantaba...jiya ta manta wani abu cikin taxi na shine nakeson bata" yafada kaman Mara gaskiya, mutumin kura mashi ido yayi for a while kafin yabude mashi kofan
"Shigo" yace mashi, Dan juyawa yayi ya kalli Abdul tare da kanne mashi ido daya shikuma kuma Abdul ya daga mashi hannu alaman good luck, yana shiga ya daga kai ya kalli katon gidan mai shegen kyau amman is not compared to gida daya cikin slim estate, wasu kujeru ya gani gefen parking lot din gidan.

Kan daya daga cikin kujeran ya zauna yayi balancing kaman gidanshi while mai gadin ya shiga cikin don kiran ameera.

Afalo ya tadda ameera da affan zaune suna kallon geet, sallama yayi yashiga gabanshi na disco saboda sanin halin ameera, bata daga kai ta kalleshiba tace
"Ya akayi?" Ahankali yace
"hajiya...wani mutumne yake nemanki.."
"Go and tell him to call me" don kaidanta kenan, duk Wanda zaizo wurin ta sai tabashi appointments, mai gadin baijin turanci, jikinshi na rawa yace
"Hajiya...banji..."
"Kai illiterate.. Cewa nayi kace mashi ya kirani...misfit kawai" ta fada tana wulla mashi irritating look, dan kara runtsunawa yayi kafin yace
"Hajiya cewa yayi wani abu kika mance cikin taxi dinshi.." Bai karasaba ta katseshi dacewa
"Je ka gaya mashi na bar mashi ko menene" mai gadin yafito da sauri don yanda ameera take mulkasu ko mom albarka, direct inda Salem ke zaune ya nufa, Salem upright ya zauna yana jiran abinda mutumin zaice.

"Malam tace tabar maka" Salem kurawa tsohon ido yayi for a moment kafin yace
"Kace mata its important..tazo bazan bata mata lokaciba" mutumin kaman bazai jeba, Amman sai yajuya.

Sallam yakariyi yashiga falon, afusace tace
"Wai ya akayine?" Dan runtsunawa ya karayi sannan yace
"Hajiya yace bazai bata maki lokaciba .."
"Wai baka da common sense ne...cewa nayi kace mashi nabar mashi" jikin na rawa ya fita, Salem kallon yanda mutumin ke tafiya jikinshi da bari yayi,
"Malam dan Allah kayi hakuri kar kajamin..tace tabar maka" ahankali Salem yafara cewa
"Kayi hakuri dan Allah..ba wani abu ta manta ba...kawai inason ganintane...please kaje ka gaya mata...nayi maka alkawarin bazan kara aikenkaba..." Jim mutumin yayi sannan yayi shahada ya koma.

Sallama yayi yashiga
"Hajiya..." bai karasaba ameera tacire room slippers din dake kafanta ta jefeshi.

Salem dake zaune ya hangi tsohon ya fito da gudu yana shafa keyanshi
"Dan girman Allah ka tafi" yafadawa Salem sannan ya juya ya koma bakin gate har lokacin bai bar shafa inda ameera ta jefeshiba.

Salem kam mamaki yake, Amman baisan abinda ya sami tsohon ba Amman tunani yake killan hajiyan gidance ta yimashi wani abu sam baiyi tunanin ameera ba.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’šโ™ฅ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โ™ฅ
ยฎzuwairat(ummu maryam)

๐Ÿ”Ÿ

"Dan Allah Malam kayi hakuri" yagayawa maigadin lokacin daya karasa bakin gate ,
"Bakomai" ya amsa mashi.
Salem fita yayi jiki ba kwari amman bai fidda niyyanshi na san ganintaba,
"I will not give up" ya fadawa kansa, yana fita ya hangi Abdul tsaye jikin motan, yana ganin Salem yagane basu daidaitaba, takawa Abdul yayi ya karasa wurin Salem dake tafiya kaman Wanda kwai ya fashewa aciki.
"Sir how far" Abdul ya tambayeshi, ahankali Salem yace
"Ban gantaba"
"No yawa...zamu dawo gobe" ya cewa Salem, daga mashi kai Salem yayi, Abdul yayi mamaki chanjin yanayin Salem cos tunda suka baro abuja sukazo Kano baitaba bin yarinya gidansu ba ,kawai daya sauke yarinya zai nuna yanasonta amman dasun disgashi bai kara takansu amman wannan karin gashi yazo gidan yarinya kuma bai samu ganintaba Amman ya yarda su dawo.

Bakin mota suka isa Abdul yayi saurin bude mashi baya ya zauna,sannan shi yazoma ya zauna driver seat suka bar wajen.

Har suka bar wajen bai bar tunanin abinda yafaruba, kuma shi bai tabajin yanason ganin mace sau biyu kaman yanda yakeson ganintaba
"Ohhh..I don't even know her name" yadawa kanshi ahankali,
"Sir kayimin magana ne?" Abdul yajuyo tare da tambayanshi, kai kawai Salem ya girgiza mashi.

Ahaka suka isah gida babu mai cewa komai. look
Wacegari tunda wuri akayi mashi chanjin fuskata sannan aka kawo masu lunch daga cilantro Indian restaurant. Suna gamawa suka kama hanya gidansu ameera, still yau ma Abdul ne ke tukin motan, suna zuwa yayi parking inda yayi jiya Salem ya fito yana aduan Allah yasa ya samu ganinta.

Bakin gate yaje yayi knocking, still tsohon jiya ya bude mashi, yana ganin Salem yanayin fuskanshi ya sauya
"Malam kai kuma..."
"Ina wuni" Salem ya gaiceshi, mitumin irin mutanen nan ne masu son yara masu girmama manyansu, ahankali yace
"Lafiya lau..." Kafin ya kara magana Salem yayi saurin cewa
"Baba dan Allah kayi hakuri ka kiramin yarinya nan.." Mutumin shuru yayi yana tunanin wai meyasa wannan dan arzikin yake zuwa Neman wannan shaidaniyan yarinyan, kaman yacewa Salem ka bar yarinyan nan bata da halin kirki Amman sai yayi shuru don ba abinda aka kawoshi yi bane
"Malam so kake in rasa hanyar bawa yarana abinci?" Girgiza mashi kai Salem yayi
"To indai bakason in rasa aikina kar kara aikena kiran yarinyan nan" Dan jinginawa Salem yayi da gate din sannan yace
"Baba...nawa ne albashinka?" Kallonshi mutumin ya danyi sannan yace
"Dubu hamsin" Dan murmushi Salem yayi kafin yace
"To in na biyaka albashinka na wata hudu zaka ..." Bai karasaba mutumin ya zaro ido tare dacewa
"Ban ganeba " yafada yana kallon Salem
"Ina na baka 200k zaka kiramin ita?" Washe hakori mitumin yayi
"Ai sai in kawo maka kanta ma" dariya Salem yayi don furucinshi,Salem komawa yayi wurin Abdul yaamshi wrapper na dubu2 guda biyu, kallonshi Abdul yayi
"Sir in kabashi wannan kudin baka ganin zaka nuna identify dinka?"
"Ai nasan bazai gaya masuba"
"Are you sure?... Don banason a gane ka"
"Don't worry..I will make sure of that" ya juya yakoma wurin mutumin,
Mika mashi kudin yayi kafin yace
"Amman yazama sirri tsakanin mu" washe hokara mutumin yayi
"Nikam wa zan gayawa ... Da ganin ka asan mai naira ne kai dan ko kadan kirarka bata kama dana talaka" shikam Salem banda daria babu abinda yake yi, bude mashi gate din yayi
"Shigo" ya fadawa Salem, yana daria yashiga ya zauna inda ya zauna jiya, sauri ya maida gate din sannan yayi hanyan falo dagudu.

Abinka da Wanda ya saba da hutu yayi relaxing kaman gidanshi yake zaune.

Shika mutumin yana shigan falo ya hangi ameera zaune kan dinning ita kadai,daga ita sai bump short sai shimi Mara kauri, sallama yayi Amman ameera bata daga kaiba balle ta kalleshi ko kuma ta amsa mashi sallaman, ahankali ya kara matsawa kusa daita tare da karfin gwaiwan 200k dake aljihunshi, sallam yakara yi sai lokacin ameera ta daga kanta fuskanta kaman wacce akayi wa albishir da jahannama
"Ya akayi you disgusting creature.." Ahankali yace
"Hajiya wani ne yace in kira..." Wani irin dirty look ta yi mashi kafin tace
" koma waye ya kirani..in kuma bashi da number ta yasan inda dare yayi mashi" tafada tare da maida hankalinta kan abinda take ci, juyawa yayi ya fita.
Salem da yayi balancing kan kujera yana lumshe lulu eyes dinshi ya mike zaune yana jiran yaji abinda tsohon zai ce.
"Alh yace ka kirata...$" tsohon ya fadawa Salem,
"Baba ka bani number ta mana " ido tsohon ya zaro kafin yace
"Alh INA zan samu number ta...gaskiya babu mai number ta cikin maaikatan gidan nan" shuru Salem yayi yana tunanin me zaiyi don gani yake in bai sata a ido ba bacci zai gagareshi
"Baba dan Allah kace mata tabaka number ta" dan murmushi tsohon yayi yana tunanin wannan bawan Allah bai san wancan yar iskan yarinyan ba, don yasan ko duniya zasu taru a kanta bazata bashi number ba Amman bayan son yi mashi gardama
"To " kawai ya amsa wa Salem sannan ya koma.

Ya shiga falo da sallam, ran ameera in yayi dubu to duka sun baci, bata daga kaiba Amman tana tunanin abinda zata yimashi yaji dadi
"Hajiya yace ki bashi numberki" yafada babu tsoro a muryanshi don gani yake tunda yana da 200k cash daidai yake da uban kowa, ameera daga kanta tayi kafin tace
"You creepy being me nayi maka...jiya ka hanani kallon program dina yau kuma ka hanani Cin abincina...any way number yace ka amsar mashi ko?"
" eh " ya amsa mata, mikewa tayi daga kan dinning sannan tace
"Ka jirani" tafada mashi kaman wani abun kirki, saman bene ta hau, direct dakinta ta shiga ta dauko pepper spray wato turare mai yaji ta zauko, hannunta daya rike da turaren dayan kuma rike da takarda, tana zuwa tayi kaman zata bashi takardan, yana miko mata hannun ta fesa mashi turaren direct cikin idonshi, da gudu yafara tsale2 yana ihu
"Wayyo idona!!..idona! ..idona...na shiga uku na lalace...ta kashemin ido...wayyo..idona" ihu kawai yake, ameera kallon hanyan stairs tayi don kar mom ta ji muryan shi taci uwarta , shikam mai gadin ya rasa hanyar fita don idonshi basu buduwa, da sauri ameera ta fara Ingizashi har suka fita waje.

Salem dake zaune ya hangeta daga nesa ta wani turo tsohon waje kuma kaman walkiya takoma ciki tare da rufe kofan falon. Har lokacin tsohon baibar ihunba
"Shikenan idona basu gani..." Da sauri Salem ya taso yazo wurin tsohon, shikam tsohon kokarin bude idonshi yake amman daya bude sai ya kara fashewa da ihu, cikin hanzari Salem ya karasa wurin tsohon
"Baba lafia... Me yasameka..." Cikin kuka tsohon yace
"Alh ka tafi...." Salem rikeshi yayi
"Kayi hakuri...laifina ne... Bari intafi da kai hospital.." Tsohon da har lokacin bai bar kukaba saboda azaban da yakeji cikin idonshi yace
"Ba laifinka bane dana..kwadayina yajamin...kawai ka tafi..." Hankalin Salem yayi mugun tashi cos tunda aka haifeshi bai taba ganin babban mutum yana zubda hawaye hakaba.
"Ko kadan baka da laifi baba..." Bai karasaba tsohon yace
"kai kawai ka tafi ...inkuma kudin ka kake so sai in baka..."
"Aa kar kabani Amman dan Allah ka amsamin tambayata...waya zuba maka wani abu cikin ido?" Tsohon yadan yi kokarin bude idonshi, duk da azaban dayake ji yayi halin maza ya barsu bude
"Subhanallahi... Please baba ka bari in kaika hospital kar idonka ya sami matsala" yafada lokacin da yaga yanda idon tsohon suka koma ja sosai, kai tsohon ya girgiza mashi tare dacewa
"Ka tafi dan son annabi" Salem bai kara cewa komaiba ya tafi.


Mommy su ameera kam bata San abinda ke faruwaba cos tana dakinta tana bacci shikuma sarkin rahoto affan yana dakinshi yana video game.

Salem na fita Abdul ya bude mashi kofan mota, yanayin shi ya nuna babu nasara
"Sir halan yauma baka samu ganintaba"Abdul ya tambayeshi, shuru Salem yayi for a moment kafin yace
" eh bangantaba..Amman am not coming back... Ina tunanin da akwai abinda ke faruwa cikin gidan da bai kamataba ...they is something weird about the family "
"OK sir" Kawai ya amsa mashi don bayason yiwa oganshi shishigi.

Salem kam tunanin tsohon yake, don gani yake kaman da kar idon tsohon su dawo daidai, aranan bai samu sukunin kirkiba don daya tuna yanda idon tsohon yakoma sai tsigan jikinshi ya tashi.
Around 9pm yakira Khalid yabashi labarin abinda yafaru, Khalid cewa yayi
"Slim kana tunanin yarinyan ce ta zuba mashi wani abu a ido?" Salem dake kwance daure da towel yace
"That's what am thinking don na tabbatar ita ce ta ingizo tsohon" dariya Khalid yayi kafin yace
"Taxi driver kodai inzo Kano ka kaini gidansu yarinya mu dan koyawa dukkan gidansu respect?" Salem tsoki yayi tare da katse wayanshi
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’›โ™ฅ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ1โƒฃ

Aranan Salem baiyi dinner ba don tunani kawai yake, amman abinda ya bashi mamaki shine yanda zuciyanshi bai daina son zuwa gidanba,
"Ya Allah... Why is my heart forcing me to a bad place?" Ya tambayi kanshi, Haka ya kwana da tunani iri2 cikin zuciyanshi.

Wacegari bai fitaba, Abdul ya tambayeshi ko lafia bazasu fitaba? Amman ko juyawa baiyiba balle ya bashi amsa.

Atakaice saida sukayi kwana uku basu fitaba, abin takaici Shine acikin kwana ukun zuciyan Salem bai daina shaawan komawa gidanba, yayi2 amman ina ya kasan don anashi tunanin ko baije dan yarinyan ba ya kamata ya koma saboda tsohon da ya jawa wulakanci.
Bayan an chanja mashi fuskah ya fita, shiryawa Abdul yayi Amman sai Salem yace mashi ya zauna gida tunda ba nesa zashiba, Abdul baisoba tunda yasan Salem bai gane gari da zai fita shi kadaiba amman ko kadan bayason yiwa Salem gardama, yana fita direct gidansu ameera ya nufa. Karfe hudu da rabi yaisa gidan, parking yayi sannan ya fito.

Knocking yayi kaman yanda ya saba,tsohon ya dan bude kofa ta yanda zai ga mai knocking
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" Salem ya fada lokacin dayaga yanda idon tsohon ya kara ja yana ruwa kaman zai tsiyaye,
"Baba am so sorry... " tsohon Wanda run randa ameera ta fesa mashi pepper spray ya bar gani sosai Amman yanajin muryan Salem ya gane shine
"Haba dan nan..." Salem ya katseshi dacewa
"Bari zan kaika hospital yanzu nan.." Tsohon ya katseshi dacewa
"Aa...kar ka kara sakani cikin matsala... Wlh Hajiya karama tace zata hallakani in har ka kara zuwa bada appointment ba" shuru Salem yayi kaman mai tunani sannan yace
"To Amman ka budemin in shiga, bazan saka ka kirataba , zan shiga da kaina..kuma nayi maka alkawarin in na fito zamu tafi tare kuma zan baka kudin da zaka iya fara Sana'a". Shuru tsohon ya bude kofan, Salem nashiga ya hangi wani cute handsome boy yana kwallo kan dan field din dake gidan, yaron yana ganin Salem ya tsaya yana kallonshi, ajiye ball dinshi yayi ya ya nufo Salem, yana zuwa gurin Salem yace.
" good evening " murmushi Salem yayi don yaron ya burgeshi
"Evening.. How are you"
"Am fine thank you sir..who are you looking for.. Don in daddy ne yana abuja amma anjuma zai dawo cos yana hanya...and in mom kake nema tana falo inkuma anty kake nema tana dakinta tana rawa" dariya ne ya kufcewa Salem sannan yace
"Anty nake nema.."
"OK...bari in kirata" yafada sannan ya kama hanyan falonsu, yana shiga falo ya hangi mom Amman baice mata komaiba yanufi upstairs, bakin kofan dakin ameera da wakan beautiful liars na Beyonce ke tashi ya tsaya tare dayin knocking
"Come in" ta fada, affan shiga dakin yayi
"Anty wani na nemanki" ya fada mata, hada giran sama Dana kasan tayi
"Waye?" Ta tambayeshi
"Nima ban sanshiba" dan matsawa tayi bakin window ta cos ana ganin komai na compound din, wani ta gani tsaye jikin motanta, juyawa tayi ta kalli affan kafin tace
"Go and tell him to fuck off.." Affan bata fuska yayi
"Anty ba mommy tace ki bar Koran..." Bai karasaba ta turashi waje tana cewa
"Je ka gayamashi ban zuwa" tana kaiwa nan ta

Please Login or Register in order to submit comment