Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

pant da bra uku,
"Gyale fa" ta tambayeshi, Dan girgiza kai Salem yayi
"Ai cikin gida take babu inda zata"
"Ok..zaka saya da shadda da lace ko materials?"
"Gaskiya bani da kudin.."
"Turare fa?" Tasake tambayanshi
"Matan kauye basu shafa turare sai Ku Matan birni" yafada
"Matan birnin ma sai masu halin" tawa tafada cikin ranta
"Kayan kwalliya fa?"
"Bandasu"
"Amman at least ka sayamata man shafawa ko?"
"To rubuta mata Wanda kike shafawa indai bashi da tsada"
"Cocobutter ne kuma karamin 600"
"Rubuta mata babban" ta rubuta
"Yan kunnefa?" Ta sake tambayanshi
"Nawa kudin na kunnenki?" Ya tambayeta yana nuna bariman dake kunnenta
"250"
"Babu Wanda kudin ta bai kai hakaba?"
"Da akwai mana..har na 70 naira da akwai"
"Kirubuuta na 70 guda biyu" ta rubuta.
"Mun gama da kayan sawa now kayan aikin gida..set din tukunya zamu rubuta?" Ido Salem ya zaro
"Me zatayi da set..kawai rubuta kwano, cup , spoon, pot, knife,.. Hmmm saime kuma..rubuta bibbiyu " duka tawa ta rubuta su
"Yarda broom da dustbin ko?"
"Eh yauwa na mance su..".
Haka tawa ta dinga lissafa mashi kayan aikin gida suna rubutawa,
"Sai su gado da kayan daki" inji tawa
"Wane irin gado..kawai rubuta student foam sai ledan daki sai curtains masu sauki don ba kudin gareniba" ta rubutasu
"Sai abinci" tawa ta fada mashi
"The fun part" ya fada cikin ranshi, kallon ta yayi sannan yace
"Kaman ke kina iya cinye buhun shinkafa cikin wata hudu?" Ya tambayeta, ido ta zaro
"Kam ina hauka?..gaskiya bazan iyaba...why do you ask?" Dan jinginawa yayi sannan yace
"Ai don insan irin yawan rice din da zan saya mata,..lissafamin kayan abinci in gani..ki dinga rubuta su"
"OK" ta amsa mashi sannan ta fara rubutawa tana cewa
"Rice, macaroni, spaghetti, indomie.." Da sauri Salem ya katseta dacewa "banda indomie...ni ban ciba balle in sayawa wani...cigaba" Dan murmushi tawa tayi sannan tacigaba
"Garin tuwo, kuskus,.." Salem ya kara katseta
"Nifa ba kayan birni nace ki rubuta ba..kawai rubuta irin garin danwake, alkubus.." Kayan gargajiya Salem ya dinga lissafawa kaman yana cinsu itakuma sai rubutawa take.
"Sai kayan miya..." Ta fada mashi bayan ta kammala rubuta kayan abinci
"To ki fadesu inji" Salem ya amsa mata yana kallon bayan wuyanta da ya dana bayyana, wasu kananun gashi yagani kwance har bisa gadon bayan ta, sai yaji tana cewa
"Kuka, egusi..tasshi, maggi, gishiri,albasa..." Suma haka ta rubuta su, data rubuta mai tsada Salem yace ta gogeshi don bashi da kudin siyansu.
"Mun gama..." Ta fada mashi,
"Kawo su in gani" ya fada mata yana lumshe sexy eyes dinshi kaman mai jin bacci, mika mashi tayi, amsa yayi ya kara hadawa da hannunta, wannan karinma janyewa tayi da sauri, saiyaga ta hada giran sama sana kasa
"Sorry..mistake nayi" yace mata, batace komaiba, kallon list din yayi
"Wow..kina da fine handwriting..ki gama uni ne..?" Kallon shi tayi for few seconds sannan ta sada kanta kasa
"Ka taba gani degree holder yana saida abinci a restaurant?" Shuru yayi bai bata amsa ba tacigaba dacewa
"Ka taba ganin talaka yayi degree?" Salem saiyaji jikinshi a mutu
"Nayi maki alkawarin zaki gaji da karatu" ya fada cikin ranshi sannan yace.
"Ai with Allah komai ma is possible" yafada ahankali
"Hakane" ta amsa mashi sannan ta kara cewa
"Amman kai kayi karatu sosai" dan murmushi yayi sannan yace
"Kin taba ganin degree holder yana tukin taxi?" Tawa dan daria tayi
"Ai Nigeria kenan everything is possible..Amman seriously kayi karatu"
"Meyasa kike ganin kaman nayi karatu?" Ya tambayeta
"Ai naga turancin ka mai dadi" nikam nace dan baki ganshi a office ba.
"Ai yau da gobe..yanzu lissafamin kudin kayan nan da wayanki" yafada mata don abar maganan cos shi mutum ne Mara son karya kuma in ya fada mata baiyi karatuba karyan kara yawa zaiyi tunda doctorate gareshi.

Kara amsa tayi tafara calculating da wayanta don dukkan kayan ta rubuta harda kudin su, bayan kaman minti goma ta daga ta gan yanda ya kurawa bayan wuyanta ido, ahankali ta maida gyalenta daya fadi daga kanta sannan tace
"Gaskiya kudin dayawa" ahankali Salem yace
"Nawa" yafada kaman mai rada
"72k" wara idanuwa Salem yayi kaman Wanda bai taba ganin irin wayannan kudin ba
"Gaskiya oremi.. Duka kudina 70k..suma na kusa shekara ina tarasu" ahankali tawa tace
"Yanzu me zamuyi?" Ta tambayeshi kaman its her problem
"Mu rage wasu kayan.." Dan daria tayi
"Ai dukkan kayan are important.. Wane kake ganin zamu rage" kallon ta yayi eyeball to eyeball sannan yace.
"Underwears" da sauri tawa ta kauda kanta
"anya wannan mutumin ba dan iskabane?..."
"I heard you" ya fada mata ido tawa ta zaro don atunaninta maganan zuci tayi,
"Kasan basai mun rage komaiba..ina da kudin da nake tarawa saboda kudin hayanmu...zan baka 2k sai ka kara.." Mamaki ne kwance kan fuska Salem don kasa boyewa yayi
"In lokacin biyan kudin yayi kuma ban baki bafa?" Ya tambayeta yana karajin sonta cikin ranshi
"Ai insha Allah zan samu wasu kafin time din..." Shuru yayi yana tunani kala2 cikin zuciyanshi
"OK" yace mata.

Fita tayi daga cikin motan ta shiga gida, bayan kaman minti biyar ta fito da kudin, saida ta shiga motan sannan ta mika mashi, amsan kudin yayi yaga yan Dari bibbiyu ne guda goma
"Thanks... Zan biyaki..I promise"
"Ba sai ka biyaniba...so yanzu zamu tafi kasuwane ko yaya?" Shuru yayi ya kalli waje yaga yanda rana ke shining yasan ko kashe shi zaayi bazai Iya shiga rana ba
"Kawai ki barshi da yamma zan shiga kasuwa tunda yanzu zuhr ya kusa"
"Amman cemin kayi bakasan kasuwa ba" kara shafa kanshi yayi
"This gal is smart" yafada cikin ranshi
"Ai wannan abokin nawa zansa ya rakani"
"To shikenan" ta fada feeling disappointed don har lokacin bata gaji da ganinshi ba.
"Rubuta min number ki bayan takardan" yafada mata don yasan da zaran ya fidda wayanshi asirinshi zai tonu. Ba masu ta rubuta mashi kasan list din sannan sukayi sallama, ko wannensu da tunanin dayake.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค
Ranar da Salem yabar gidansu ameera dad ya maidata gidan kanwanahi dake sharada, duk yanda mom tayi yabar ameera gidan ki yayi
"Bari in kai yata inda zaa bata kulawan da amare ke bukata" yafadawa mom. Suna isa gidan dad ya ajiye ameera ya koma, kanwa dad irin wayyanyun Matan nan ne, don tun ranar tafara durawa ameera kayan mata masu kyau da tsada sabanin wayanda tasha abaya,
"Yarinya kisha kiyi tatul don daya dandanaki bazai kara shaawan wata ya mace" inji anty Sadiya kanwar dadi.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค
Salem dawowa daga gidansu tawa, Abdul ya kira ya mikawa list din tare da cewa
"Alh inaso kayi typing din wannan ka turawa agent dina...ka gaya mashi ya sayi dukan kayanan ya ajiyesu cikin wannan gida...and tell him ban yarda akara ko arage wani abu ba"
"Yes sir" abdul ya amsa mashi. masjid ya wuce, yana dawowa yashiga shiga bedroom dinshi wayanshi yafara ringing, murmushi yayi don yasan ummanshi ce
Yana picking yaji tana cewa
"Son what's happening??" Ahankali yace.
"First love ban ganeba..meya faru?" Cikin fada Umma tace
"So you are asking me ko?" Ahankali yakara cewa
"Umma bansan abinda nayiba ko" yafada cikin shagwaba,
"Mutane nata kirana da abbanka sunayi mana congrats wai zaayi aurenka this coming Saturday!?" Salem baki ya rike sannan yafara kalle2 cikin dakin kaman mara gaskiya.



_Nagode kwarai da irin kulawanku, Allah yasaka maku da alkhairi_
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค
ZAKISAN KONI WAYE
โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’š
ยฎzuwairat(ummu Maryam)

2โƒฃ0โƒฃ

Dan daria karfin hali yayi
"Umma aurena kuma?..."
"Kai wallahi kasa na sauka garin Kano yau ranka sai yafi nakowa baci...wato maganan daria na fada maka..." Tafada cikin fada, daka ji muryan ta kasan ciki tension take kuma dajin muryan ta kasan Matan nan ne masu tsiwa, ahankali Salem yace
"am sorry first love.. Amman in zanyi aure baku zakuyimin aureba?...ta yaya zanyi aure bada saninkuba?..please Umma ina kika samu wannan labarin?" Ya fada yana kwalo idanuwa, daka ganshi kasan ko kadan bashi da gaskiya, Umma Dan ajiyan zuciya tayi sannan tace
"Habibi nasan its impossible,..tunda safe mutanen Kano ke ta kiranmu sukayi mana murna ...cewa suke anata sanarwan auren Salem Yusuf sulaiman..."
"Amman Umma mutane da gulma suke...ni kadai ne Salem Yusuf sulaiman? Ai Umma da akwai masu irin sunana da yawa..so just relax" yafada yasauraron abinda ummanshi zata ce next
"I know don abbanku ma baudamu ba..Amman son kazo yola wannan week end" shuru yayi yana tunanin tawa don yanzu ya dauki aniyan zuwa wurin ta kullum har sai ya gama gwadata
"Kaji habibi..I want you in yola Friday night" yaji muryan ummanshi nacewa
"Amman first love ina da aiki dayawa fa.."
"I said I want you here Friday night... You can go back to your duties by Monday?" Ta daka mashi tsawa
"Yes Umma" yafada, Amman da jin muryan shi kasan bayaso. Katse wayanshi yayi , yana kumbure2 kaman agaban ummanshi yake, yana ajiye wayan yafara wani ringing, dauka yayi yaji ana cewa
"Congratulations sir...." Bai ce komai ba ya katse wayanshi, bai gama katsewaba dayan wayan yafara ringing, dubawa yayi yaga Khalid
"Guy how far" yafada bayan yayi picking
"Ango.. Ango..zancen aurenka ya bade Nigeria harda ketare..."
"Wai wake yadawa?" Salem ya tambayi Khalid
"Wai a gidan radio...wasu course mate dinmu suka kirani suna son jin party da zamuyi..." Dariya Salem yayi
"Ashe party.." Shima Khalid dariya yayi
"Eh mana..at least kabamu dama mu girgiza waist da yanmatan mu..."
"Wallahi ka sake kayi organising wani party to karshen friendship dinmu..." Wani darian rainin hankali Khalid ya karayi
"Dalla haka kake magana kaman bazaka yi sex da yarinyan ba..." Murmushi Salem yayi tare da cije lebenshi na kasa
"Ai gara dakace sex don kasan da akwai banbamci tsakanin sex da love making.. Kuma ina tabbatar maka.. Ko itace karshen mata..."
"Haba kana fadi ne kawai...yanda kake fama da shan magunguna sai kasamu mace kaki biyan bukatanka?" Salem banza yayi dashi Khalid yacigaba dacewa
"Wallahi guy ai babu abinda zakayi mata ta dinga kuka sai sex every now and then.."
"Dalla in baka da abun cewa get off my phone... Yarinya data kirani son of a bitch zan taba...yarinyan datacemim motanta zai sayi uwata da ubana zan taba..Ni kasan ba Mara zuciya bane...wallahi ban da niyyan auren ta kawai narasa hanyan mallakanta ne..." Shuru Khalid yayi sannan yace
"Ai yarinyan nan bakai kadai ta taba ba..Ni ma haushinta nakeji...let's forget about her and say something important... Ya yar Yoruba" dariya Salem yayi sosai don wani sanyi yaji cikin ranshi
"Yanzu na baro gidansu..munyi list din abubuwan da wannan shaidaniyan yarinyan zata bukata...kasan guy in bansami Tawakaltu ba sai rijiya.." Cikin daria Salem yace
"Really in love ko?" Salem kwantawa yayi tare da lumshe idanuwa, yafara bawa Khalid labarin yanda tawa ta bashi 2k, daria kawai Khalid yake Salem yacigaba dacewa
"guy inason biyan yarinyan nan in cash and in kind...guy oremi is so beautiful... Bansan da akwai beauty cikin bakaken mataba sai yanzu.." Shuru yayi Khalid yace.
"Yace daman black beauty special suke..." Salem ya kara cewa
"Best duka jikin ta da akwai wasu gashi kwantattu..." Daria Khalid yayi da karfi
"Guy ya akayi ka gan gashin jikin ta.. Kodai kana shan minti.."/
" kai Aa Amman gaskiya yarinyan tana tadani dayawa..ban tabaji ina bukatan aureba sosai sai yanzu.. " ahankali Khalid yace
"Allah yasa su Umma su yarda"
"Hmmm in basu yardaba ai sai dai su dauki gawata...she's the best part of me"
"Nidai mu bawa malamai kudi sufara yimana aduan amincewan Umma don kasan yanda Umma take.." Salem shuru yayi da dan lokaci sannan yayi ajiyan zuciya
"Nima itakadai nake tsoro... Nasan Abba bashi da case...Amman zanji yola this weekend.. Zanyi mata maganan inji abinda zatace.."
"Am wishing you best of luck" ahankali Salem yace
"I will need it" katse wayanshi yayi sannan ya saka hannu cikin aljihunshi ya fiddo kudin da tawa tabashi ya bude wani briefcase mai dauke da mint na 1k da dollars ya saka kudin daga gefen jakkan.
Fita yayi daga dakin ya koma waje ya samu Abdul yana typing din list din daya bashi, amsan list din yayi ya rubuta number tawa cikin wayanshi sannan yace
"Alh. Kar ka rubuta atampopin..anjuma zan baka 12k ka shiga kasuwa ka sayomin yan 2k kusa 6"
"OK sir " Abdul yace mashi sannan ya koma ciki.

Kwantawa yayi tare dayin rub daciki sannan yafara dailing number tawa.

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™

Ameera ce zaune cikin wasu kawayenta da suka ziyarce ta gidan anty Sadiya, shewa kawai suke
"Amman ameera na tausayawa Salem yanda baki da mutuncin..." Zeenat bata gamaba ameera ta tari numfashinta
"Ke banson kutumar burouba...ubanme nayi na rashi mutunci...wallahi..." Bata idaba anty Sadiya ta kawo mata wani magani cikin cup, amsa tayi ta shanye, dariya kawayenta sukayi wata tace
"Shegiya ameera sai zukan magani kike ko tsoron abinda zai biyo baya bakiyi" baki ameera ta tabe
"Me zai biyo baya...banda first
night" daria zeenat tayi
"Ke irin tsoron da amare keyi sam bakiyi...kuma ance first night wahala akesha" dan lumshe idanuwa ameera tayi tana imagining yanda ranan zai kasance cos kaman ta jawo ranar take ji, don tunjiya da antyn ta tafara bata wasu special magani takejin kaman wani abu na yawo cikin wandon ta, ahankali tace
"Karku damu angona will be romantic.."
"Yanzu ya zancen karatunki?" Daya daga cikin kawayanta ta tambayeta,
"Wane karatu zanyi bayan ga already made guy...daman dan kudi ake karatu nikuma yanzu am the wife of the richest man in Africa...so to hell with school" wata cikin kawayenta dan hararanta tayi, irin kawayen nan masu bakin ciki da karuwan dan uwansu. Saida ta gama wulla mata dirty look sannan tace
"aini abinda ke bani haushi wajen wannan auren shine babu wani party ko shagalin da zaayi..." Wani irin disgusting look ameera ta watsa mata
"Meye najin haushi kaman auren uwarki zaayi..."
"Ke ballagaza karki zageni dan nazo wurin ki.."
"Naje na zageki kuma wallahi kiyi min maganan banza in kulleki da uwarki da ubanki don ba ameera da kika Sani bace...an for information events dinmu a Spain zaa yishi duk shegiyan dake da kudin jirgi ta biyo mu" dukansu shuru sukayi sai budurwan data zaga ta mike tare da daukan handbag dinta sannan tace
"Duk wulakancin da kika gandama kiyi min tunda ni nazo wurin ki.. Kunga tafiyata ...Allah yabada zaman lafiya.." Wani irin tsoki ameera taja sannan tace
"Ko baki ce ba"

๐Ÿ’™โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’š

"Oremi am missing you already" yafada lokacin da tawa tayi picking wayanta, dan kashe muryan tayi
"Allah?" Dan daria yayi
"Ni kike kashewa murya?..so kike ki tamin..." Abinka da wacce ba bahausaba sai tace
"In tada maka me?" Salem daria yayi ahankali Kaman maijin bacci yace
"Ni muryan ki is driving me insane...please ki daga muryan ki ko zan barjin yanda nakeji.." Dan daria tayi
"Ni ba kashe maka murya nakeba...ina magana ne ahankali don kada in tada mami dake ciester"
"kinsan komai nake yana driving dina to insanity ..tawa wallahi I think am falling for you..kuma gashi Ni talaka ne..yan Matan yanzu basu son talaka" Dan murmushi tayi tare da lumshe idanuwa
"Ai money is not everything... Happiness, kwanciyan hankali, respect... Matters" Salem kwantar da kanshi yayi kan wani cotton wool pillow mai taushin gaske sannan yace
"Yanzu dukda ina talaka in nace ki aureni zaki amince ?" Tawa shuru tayi sannan tafara cewa
"Ni ban auren bahaushe..." Daria Salem yayi
"Saboda me?" Ahankali tafara cewa
"Bahaushe saurin saki mata, bahaushe saurin Karin aure..gaskiya na kwammace in auri yarenmu.."
"Kawai kice bazaki aureniba saboda banda kudi...Amman ai ba duka aka taru aka zama dayaba..."
"Hmmm...Ni dai banson inzama bazawara" dariya Salem yayi
"Kinsan kamanki bazata zama bazawaraba cos you are ravishing...kin same in kika aureni dagani sai ke"
"Alkawarin karya...nidai ka gayamin abinda yasa ka kirani." Salem dan cije lebe yayi
"Don in tambayeki gashin dake bayan wuyanki haka yake a dukan jikinki?..."
"In kana yimin irin wannan maganan zan bar daukan wayanka..."
"Sorry.. Daman inason tambayan ki inda kike kai dinkinki da tsada?"
"Anayimin na 700 sai kuma na 1k"
"OK please in nakawo dinki kanwata zata yimin kafin ranar Thursday?"
"Gaskiya ban saniba Amman tunda cikin gida take kuma ba customer garetaba dayawa kilan ka samu...ya zaayi agane size dinta" Dan daria yayi
$"sai a auna dake...saidai kinfita hips da boobs don kanwata kaman an mike akuya tsaye take.." Dariya tawa tafara yi sannan tace
"Kafara ko?" Shima dariya yayi
"Sorry.. So please inzo anjuma bayan sallan ishai zaki rakani gurin?"
"Allah yasa mami ta yarda..?"
"Ameen... Wait baki tambayeni abinda nakeso ki ajiye min ba?" Ahankali tace
"Me zan ajiye maka?" Dariya rainin hankali yayi
"Kanki.." Bai karasaba ta katse wayan ta.
Ajiye wayan yayi gefe daya ya rungume pillow yana daria
"Ai sai na kwada ki don nasan yanmatan yare virgins dinsu ba yawa"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š
ZAKISAN KONI WAYE
๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š๐Ÿ’›
ยฎzuwairat(Ummu Maryam)

2โƒฃ1โƒฃ

Bayan sallan ishai ya kama hanyan gidansu tawa da atampopin da Abdul ya sayo daga kasuwa, yana tuki yana daria in yaga atampan, don kaman atampan yan kauye suke. Duk cikin motan sai kamshin turare shi yake.

Wurin dayayi parking da rana ya kara tsayawa, saidai wurin yayi duhu sosai don babu wutan NEPA da sauri ya ja glass din motan shi saboda sauro. Waya ya dauka ya bugamata ya sanar daita isowanshi.

Da kyar tawa tashawo kan mami ta barta ta fita, kuma cewa tayi kar ta dade, powder banquet ta shafa fuskanta tare da wet lips, fuskanta yayi kyau sosai abinka da baka ta shafa farar powder
"Kwalliya me kike?" Mami ta tambayeta, da sauri ta dan goge fuskanta sama2
"Mami ba kwalliya nakeba" ta amsa mata
"Mami na tafi"
"To". Fita tayi ta hangi motan cikin duhu. Tana zuwa wurin motan ta dan kwankwasa glass din motan, dan bude motan yayi
" oremi come in " yafa yana kallon ta, makale kafada tayi don har cikin ranta tsoron shi take don yanda yake magana yasa take tunanin shi rikkeken dan iskane
"Ka fito waje" tafada mashi, dan murmushi yayi
"Kiyi hakuri ki shigo mu fara kai dinkin sai mudawo mu tsaya cikin sauron" Tawa tsaya tayi kaman mai tunani sannan ta ida budewa ta shiga, dan runtsunawa tayi sannan tace
"Good evening" kallon ta ya tsaya yi na dan lokaci sannan yace
"Evening.. Kiyi hakuri inata damunki.."
"Bakomai"
"Shall we?" Ya tambayeta
"Eh..dan mikewa zakayi kadan gidan babu nisa" tafada batare da ta kalleshiba, wani irin kwarjini yakeyi mata,
"To..nagode oremi" tada motan yayi ya bi inda tace.

Haka ya dinga bin hanyan data nuna mashi har suka isa kofan gidan mai dinki,
"Ya isa" tace mashi ahankali, Dan wuri ya samu yayi parking sannan yafito itama ta fito, bayan motan ya bude ya dauko atampopin cikin wata babban Leda ya mika mata tare dacewa
"Gasu" amsa tayi ya kara hadawa da hannunta,
"Ka fara kuma ko?" Tafada tana dan hararanshi," murmushi kawai yayi, ta kara cewa
"Bari inshiga inji yanda zaayi"
"OK love" tawa batace komaiba ta shiga gidan tare da sallama.

Bayan kaman minti sha biyar ta fito tayi mashi sallama ya amsa sannan tace
"Tace duka riga da skirts ko da zani?" Dukda cikin duhu suke bai hanashi kurawa lips dinta idoba, imagining bakinta cikin nashi kawai yake
"Wane iri kike so ayi mata?" Ya tambayeta
"Duk Wanda kakeso, saidai riga da skirt yafi riga da zani tsada.."
"To kawai ayimata riga da zani" naga ameera tana daure zani. Batace komaiba ta koma cikin gidan, few minutes later ta fito
"Tace each zaayi 500 Amman tunda na sauri ne 600 zaka bada.."
"Haba daga yau zuwa alhamis dinne emergency?.. Gaskiya ki gayamata tadan rangwanta.."
"Ai da 700 tace da kyar ta yarda ta rage naira Dari".
" to naji nawa dukan kudin? "
"3600" hannu yasa cikin aljihunshi kaman zai fiddo kudi dukda shi kanshi yasan baya ajiye kudi cikin aljihu
"Babu kudin.. Bari in shiga induba cikin motan in gani" yafada yana shiga motan ,wani wuri yabude ya dauki rap din 1k ya zari guda biyu yanayi yana kallon ko ta ganshi. Fitowa yayi ya mika mata kudin
"Ga abinda ke gareni ranar Thursday zan kawo saura sai mu amshi dinkin" tawa tsawa tayi tana kallon kudin
"Daganin kudin nan suna da yawa inda kafiddo su..kawai ka bada sauran ka huta "Dan daria yayi
" agurin Wanda ya bani kudin ba ?Amman Ni dukan su kenan"
"To shikenan" tafada tare da komawa cikin gidan.

Tana fitowa Suka fara dawowa, kin gudu yayi don mai tafiyan kafa yafi motan shi gudu, kallon ta yayi sannan ya kalli hannuwanta daka kan cinyanta, ahankali ya kai hannunshi daya ya kama mata hannu, daga kai tayi ta kalleshi shima ya kalle ta tare da daga mata gira daya, ahankali ta zare hannunta daga nashi, mai makon ya dauke hannunshi sai ya dora matashi kan cinyanta suma tureshi tayi,
"Haba tawa..meyasa kike yimin haka... Kawai dan na dan tabaki kike turemin hannu?... Kodai baki sona yanda nake sonki..." Tawa galla mashi harara tayi,
"In ina sonka sai ka dinga taba?...haka ya kamata kenan?.." Dan murmushi yayi
"Please ki dan kara harara ta..don idanuwanki is making me horny." Tawa kara tamke idanuwa tayi, yacigaba dacewa
"Nidai kawai baki sona...don nasan yanzu masoya har romancing juna sukeyi...hakan zan kara dankon soyayyansu.." Tawa kauda kanta tayi tare da dan tabe bakinta
"Duk halin maza daya...dukan su kokarin su su shiga cikin pant dinmu mussanman mu da ba yarensu ba" tafada cikin ranta.
"Ai yau sai naga halinki" shima ya fada cikin ranshi. Kallon ta yakari ya dan shafa hannunshi bayan wuyanta, da sauri ta dauke mashi hannun
"Please banson irin wannan wasan kabari"
"Haba kiyi hakuri, sonki kesani hakan..please feel my heart beat" yafada yana kama hannunta, kan kirjinshi ya dora hannunta
"Kinji yanda heart dina yake gudu saboda ke?" Tawa kokarin cire hannunta tayi Amman ya riketa gam.. Sai taji da gaske zuciya shi harbi yake da sauri, Amman tantirin maimakon yabar hannunta kan kirjinshi sai yafara gangarawa da hannunta kan cikin shi, tawa tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, shima kallon ta yake yama mance tuki yake, yaga tsoro kwance kan fuskanta Amman bai bar kasa da hannunta ba, yana zuwa wurin belt dinshi Tawa tayi saurin fixge hannunta
"Ka tsayar da Mota" tafada da sauri kaman mara hankali,
"Why?" Ya tambayeta yanayi mata lustful look, shi da niyyan wasa yake mata Amman har ga Allah jikinshi na amsawa
"I said stop the car!" Ta kara fada cikin tsawa, Salem Dan murmushi yayi batare daya tsayar da motanba yace
"Haba oremi... Sai kace wata yar kauyen?..don kin dan tabani wani abune?..yanmata har sucking sukeyiwa samarinsu..its nothing..common sweetheart we are in the 21 century.." Tawa bata saurareshiba
"Nidai nace ka tsaida motan.." Dan wurin da babu kowa yayi parking Amman sai ya kulle kofan. Tawa naganin yayi parking tayi kokarin fita Amman kofan kulle, kalle2 tafayi taga wurin babu kowa
"Me haka please" tafada kaman zatayi kuka. Salem kara kashe murya yayi
"Minti zamu sha" yafada tare da kwantar da seat din kujeranta, Ido tawa ta zaro
"Please kayi hakuri.." Bata gamaba taji Hannunshi kan boobs dinta sannan fuskanshi daidai nata, zata bude baki tayi Magana ya hade bakin su waje daya, shure 2 tafarayi, Salem kam dake cewa gwadata zaiyi sai yafara fita hiyyacinshi, nan take yaji kaman ya cire kayan jikin ta yayi abinda bai taba yiba, don tunda yake bai taba jin ya fita hayyacin shi kaman yauba. Tureshi kawa tawa take, Amman banda kara romancing dinta babu abinda yake, kuka tawa tafarayi don gani take yariga ya gama daita, hannu yafara turawa cikin pant dinta, kaman zaki ta tureshi ya koma baya, kallon idanuwanta dake subda hawaye yayi, har lokacin bai bar kantaba Amman yacire hannunshi daga jikinta, sai nishi yake ahankali yana kallon tawa dake kuka kaman ranta zai fita,
"Am sorry... Ba halina bane..please forgive me" yafada kaman baison magana, tawa bata saurareshiba ta cigaba da kuka, ahankali Salem ya koma kan seat dinshi, tawa gyara skirt dinta tayi tacigaba da kuka, Salem haushin kanshi yafara ji don sai ya tsinci zuciyanshi yana yi mashi zafi
"Please stop crying.. Am sorry" yakara fada sannan ya tada motan, bai tsaya koina ba sai kofan gidansu. Yanayin parking ya fito ya bude mata murfin din mota, har lokacin tawa bata bar kuka ba kuma idanuanta rufe gam, tanajin ya bude kofa tayi saurin fitowa, saida taga tafito sannan ta Dan goge hawayenta tafara cewa
"Allah yaisa tsakani na da kai..sannan Allah yaisa tsakanina da zuciya ta data kamu da sonka sannan ta yarda dakai...abinda ka yimin bazan taba yafe makaba...kumani ba irin ka bace kaje chan ka nemi irin ka..daga yau kar kakara zuwa gidanmu and don't call me again" tafada cikin kuka sannan ta kama hanyan shiga cikin gida
"Please am sorry.. I don't mean anything I did .." Tawa bata saurareshiba ta shige abinta, ahankali Salem yakoma cikin motan shi, magagganun tawa sai dawo mashi suke, yasan tunda yake bai taba yunkurin tabawa yarinya pant ba, yasan kullum yana da control kan irin wannan case din don sau dayawa shike takawa yanmata birki in yaga suna wuce gona da irin
"Amman nice yau nake niyyan saka hannu cikin pant din yar mutane... Tawa kina da control over me...ban taba jin

Please Login or Register in order to submit comment