Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe mu fara yiwa baby shopping...."
"Sai mu tafi jibi ko?.." Girgiza mata kai yayi
"Sai coming weekend..." Marairace fuska tayi
"No pls... Mu tafi jibi..." Dariya Salem ya karayi yana wulla mata foam din perfume stop dake cikin bathtub,
"Ai ko Mun koma Nigeria ba Kwara zakiba...Sai bayan kin haihu..." Idanuwa ta zaro
"Kam...amma you are joking ko?...".
" no...am serious...you ain't going anywhere with my baby..." Tsaya kallon shi tayi don ta ga if he's joking or not amma Sai ta ga babu wasa fuskan shi,
"Pls baby tell me you are joking..."
"No am not... Ai the next few months is like..." Bai idaba ta mike daga cikin bathtub ta fito ta dauki towel ta daura Salem kallon ta yayi
"Princess don't leave only me in the bathtub..." Ko kallon shi batayiba ta koma falo, da sauri shima ya fito ko towel ba dauka ba ya biyo bayanta, zama tayi ya zauna gefen ta
"What did I say wrong?...." Ya fada kaman baisan abinda ya fada ba, kallon shi tayi ta galla mashi harara, Dariya yayi,
"Haba princess the doc said you should not stress out...kuma shine kikeson zuwa Kwara kiyita zurga2 ki zubda min ciki?.." Hararanshi ta karayi
"Doc yace I should not stress out amma have we stop what he said we should stop?... No..amma shine zaka hanani zuwa ganin mami...." Ta karasa maganan tana kokarin kuka, da sauri ya tallabo fuskan ta
"Shhhhh... Don't cry is not good for you... Zakije amma zamu tafi tare mu dawo tare..." Da sauri tayi hugging dinshi, zare towel dinta yayi yana cewa
"Muje mu cigaba da wanka...." Yafada yana daukanta.

Suna idar da sallah Khalid ya kara feeding dinta da wani abinci da aka kawo daga government house Sannan suka cigaba da hira suna shirya yanda rayuwansu zai kasance, abinda yake bawa Ameera mamaki shine yanda baiyi gigin ko zumudin taba ta ba, around 11 ya dauke ta ya kaita wani bedroom, wani gado ne mai canopy kaman Wanda take gani a Indian film, ajiyeta yayi
"Angel wait for me..." Ya fada yana mikewa, fita yayi daga dakin Ameera ta zauna tana karewa dakin kallo, bai dadeba yadawo da wata kwali hannun shi, bude kwalin yayi ya fiddo wasu elegant sleeping dress Sannan ya karaso wajenta, ya mikar daita tsaye ba musu ta tsaya, zip din riganta ya cire ya zame gown din daga jikinta ya rage daga ita Sai pant and bra,, tsaya kallon ta yayi kallon ta yayi, itakam Ameera sunkuyar da kanta tayi kasa duk kunya ya ishe ta, ahankali ya dauki kayan baccin ya sa mata zaunar daita kan gado Sannan ya kara fiddo wasu kayan daga cikin kwalin, nashi kayan ya cire ya saka kayan baccin ya kwantar da Ameera ya kwanta gefen ta tare da yi mata kiss ya jawota jikinshi
"Good night..." Yayi mata whisper cikin kunnenta, Ameera lafewa tayi jikin shi.

The following day aka kawo abinci da jet daga government house, Khalid serving Ameera yayi ya fara feeding dinta, wayanta dake gefe ya fara ringing, Khalid ne ya dauki wayan don mika mata Sai yaga yaya sultan, tsaya kallon wayan yayi Ahankali ya mikawa Ameera, Ameera kallon screen din wayan tayi ta kalli Khalid
"Pick..." Ya fada mata cikin sanyin murya, ahankali ta sa hannu tayi picking tare da sawa hands free, gaisawa sukayi da sultan Sannan yace
"Ya mijinki?..."
"He's fine..." Ta amsa mashi cikin sanyin murya,
"Daman I want to ask you are question...." Ya fada mata, Ameera kallon Khalid dake sauraron su tayi Sannan tace
"Ok..." Da sauri sultan yace
"Pls wacece wacce suke rawa da mijinki wurin reception?..." Dan ajiyan zuciya Ameera ta saki Sannan tace
"Yaya bakazo ba ya akayi kasan wata tayi rawa da mijina..." Dariya Sultan yayi
"Sorry about that.. Pls tell me wacece?..."
"Kanwar mijina ce...sunanta *habeeba* amma ana kiranta da *queen*...."
"Wowww...sunan yayi daidai daita...pls ki taimaka min da digit dinta..." Ameera kara kallon Khalid tayi tana murmushi, fuskan ta ya shafa
"Ok...bari in yi maka sending..." Tafada Sannan ta katse wayan, Khalid daukan wayanta yayi ya saka number queen ya turawa sultan Sannan suka cigaba da cin abinci..

Around ten na safe suka hau jet zuwa Florida USA.

🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Imagine Zainabu and superstar real Madrid football player, match made in hell....my sweet *anty sis* 💃💃💃💃💃
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: 💚💛💜💙❤
ZAKISAN KONI WAYE
💙💚💜💛❤

®zuwairat(ummu Maryam)


8⃣1⃣


*Ina masoyana this page is your, twist, bind, jam it...do what ever you want with it cos nakune Ku kadai...you guys are taking me to dream land...I love you die, kina ina salma saidu sulaiman... Ummu Maryam loves every moment with you* 💋💋💋💋



A Florida Orlando aka sauke su, Disney resort sukaje, daman wurin ana saya irin time share, daman already Khalid ya saya for two months, fadin girman wurin is a waste of time don gari guda ne, Ameera kallo ta dingayi kaman sakara, murmushi Khalid yayi ya rike waist dinta suka hau lifter zuwa part din daya saya, suna shiga Ameera ta bude baki don katon wuri ne ga katafaren swimming pool, rungume ta yayi suna shakan kamshin turaren junansu.romancing dinta ya farayi yaga kaman tana jin tsoro, murmushi yayi ya kyaleta, baa Dade ba aka kawo jerin abinci kala2 Ameera kam bata ciba sosai don bata saba da irin wannan abinci ba, wani abun ma bata taba ganin shi ba. Wanka yayi ya fito daure da towel, Ameera sunkuyar da kanta tayiya karaso wajen
"Baby...kije kinyi wanka..." Ya umarceta, ahankali ta mike ta bi hanyan daya ba, kallo bathroom ta tsaya yi tana mamakin irin jindadin turawa, Sam basu yarda dasu wahala ba. Naurori kala2, wanka tayi ta daure towel ta kasa fitowa, Khalid bude bag dinta yayi ya dauko mini skirt da top yaje bakin bathroom din ya tsaya, jin shuru for a long time yasa shi cewa
"Baby baki gama ba?..." Shuru tayi bata amsa ba cos tana tsaye bakin kofan daga cikin,
"Baby...am coming in...." Bai idaba ta yi saurin bude kofan ta fito kanta kasa, towel din bai da girma don bai isa rufe laps dinta ba, ajiye kayan kasa yayi ya dauketa Ameera tayi saurin rike towel din cos babu komai ajikin ta, hadeta yayi da bango ya fara romancing dinta.

After twenty minutes bai bar kissing dinta ba don har numfashi ta nema ta rasa bata San lokacin da ta saki towel dinba, wide chest dinshi ya rufe chest dinta dashi, daukan ta yayi ya kaita kan gado, ido ta zaro tana cewa
"Ka bari...pls" Khalid Dan dakatawa yayi ya tsaya yana kallon beautiful body dinta, bai kara tabata ba ya koma gefe, da dasauri ta rufe kanta da duvet cover dake kan gadon, shima Khalid shiga yayi ya jawota jikinshi baccin yayi gaba dasu.

The following day ya fara tour daita, da farko Disney market sukaje, babu abinda ba a saidawa. Sannan Sai parks, Sai dare suka dawo suna dawowa yayi attempting dinta ta rokeshi daya bari kuma baice kala ba ta bari.


Epcot ya kaita daga nan Sai animal kingdom, magic kingdom, SeaWorld, atakaice within a week ya kaita wurare da dama amma dasun dawo yayi kokarin amsan hakkinshi Sai ta fara kuma tana bashi hakuri Sai ya hakura duka ba karamin kokari yake ba amma yayi wa kanshi alkawarin he will not do anything that will hurt her.

Yau Kandy space center sukaje wato NASA a Titus ville. Nan kuma zaiga yanda rocket yake da yadda science yake Sannan kashiga ayi maku yadda ake tafiyan space amma na karya saidai kaman gaske don har space din karya sukayi da inda ba gravity da dai sauran abubuwan space harda kayan space suka saka suka sha selfi kaman kullum.
Yanda Khalid yake mata yasa cikin kankanin lokaci ta manta da wani Salem da sultan, yana nuna mata nobody matters in the world Sai ita

Har cikin ranta take cewa yana da kyau in mutum zaiyi abu ya nemi zabin Allah don gani take babu kaman shi, har ga Allah tanason bashi hakkinshi don har cikin ranta take jin hannun shi duk sanda ya taba ta amma tsoro take ji ba kaman in ta tuna kuka Tawakaltu kuma zeenat na ta fada mata duk kukanta bai hana Mahmud komai ba, amma gashi yau kwanansu tara tare su kwana rungume dajuna amma bai taba forcing dinta, adua kawai take Allah ya cire mata wannan tsoron don ko dazun da sukayi waya da anty Sadiya Saida tayi mata warning kan shiga hakkinshi.

Tana kwance kan wani hadadden sofa kanta kan cinyar Khalid Sai wasa yake da yatsunta, wakan if na davido ke tashi cikin wayanshi,
"Baby let's dance..." Ya ce mata yana kallon yanda take rawada kafafunta ahankali, murmushi tayi
"Nidai ban iyaba...." Ta amsa mashi ahankali,
"Kin Iya mana...zakiyi depriving dina rawanki ma?..." Ahankali ta girgiza mashi kai
"Then let's dance..." Yafada yana mikewa tare da mikar daita tsaye, rungume ta yayi ya fara rawa daita, ahankali ya kai bakinshi saitin kunnenta Sannan yace
"Angel... Yaushe zaki bani hakkina?.." Ya tambayeta cikin whisper, Ameera shuru tayi batace kala ba
"Pls..." Ya kara cewa, ahankali ta daga kanta dake kan kirjinshi ta kalleshi Sannan tace
"Duk sanda kake so..." Tafada muryan ta na rawa, duk idanuwanta sun chanza kala, murmushi Khalid yayi
"Anya you mean what you said?..." Ahankali ta daga mashi kai,
"Ok...we shall see..." Yafada yana dariya, wakan psquare ne ya shika mai suna away, ya fara cewa
"If I tell you say I love you... Omo I love you... See all of them dema want you... But I need you..." Sakinta yayi ya koma tsakiya falon ya maida wayanshi bakin kaman microphone yana wakan yana nuna Ameera at the same time yana rawa, Ameera Dariya tafarayi don Allah kadai yasan irin jindadin da take ciki, da tana tunanin babu Wanda zai kai Salem amma she was wrong cos Khalid ya ninka Salem a wajenta, yanzu bata gani kowa Sai shi, itama wakan tafarayi tana rawa kadan, Khalid daina wakan yayi ya bude hannuwanshi, tana rawa ta fada jikinshi,
"Baby I love you...you are the most wonderful thing that has happened to me..." Yafada yana kallon ta,
"I love you too..." Ta amsa mashi itama tana kallon shi, kallon juna suka cigaba dayi kaman yanda man da geet ke kallon junansu, ahankali yace
"Am happy... I want to be like this for ever..."
"Am very happy too..." Ta amsa mashi,
"I never thought I will be more happier... Ban taba tunanin zan kara samun irin wannan farincikin ba...I thought tunda ina da good job... Ina governor son...am happy... Amma ba haka bane....been together with you makes me happy the most..." Yafada yana shafa fuskan ta,
"Am lucky... I don't know Allah zai hada da mutum irin ka bayan wulakanci Dana yiwa maneman aurena... Amma Allah always gives us a second Chance.. Am happy it's you..." Tafada Ahankali, murmushi yayi Sannan ya tallabo fuskanta,
"When Salem first told me about you... I told him to deal with you... Danayiwa kaina asara...dats why ana cewa in zaka gina ramin mugunta ta ginashi kadan don bakasan Wanda zai fada ba....." Murmushi tayi
"Har dakai aka bada shawaran akaini wannan wurin kenan?.." Tafada tana dariya,shima Dariya yayi
"Aa...ba ruwa na....wannan was his own idea..." Ya fada mata.

Wakoki suka dinga chanzawa suna hira har lokacin sallan ishai, sallah sukayi Khalid ya bukaci da suka kara raka biyu na nafilla, ba musu ta bishi, suna idarwa ya juya yana kallon ta, kanta kasa Sai wasa take da yatsunta,
"Hmmm zan cire wannan kunyan,..." Ya fada yana mikewa, jallabiyan dake jikinshi ya cire ya mikar daita ya cire hijjab dake jikinta,
"Baby let take our bath..." Yafada yana kallon reaction dinta,
"Tare zamuyi?..." Ta tambayeshi
"Yes..." Yafada yana daukanta, wuntsul2 tafarayi da kafanta, yaki ajiyeta sai cikin bathroom direct to bathtub dake cike da foamed water, nan take kayan jikinta suka jike, shima shiga yayi bayan ya cire nashi kayan, Ameera rufe fuskan ta tayi don bata taba ganin nakedness dinshi ba, kayan jikin ta ya cire da kyar don sai cewa take
"Ka bari zanyi wanka ni kadai..." Cike da kunya sukayi wanka ya dauko kaman jaririya. Yana kawota kan bed wasanshi ya chanza dana kullum, dakewa Ameera tayi don tayi wa kanta alkawarin amincewa dashi.
Saida yaje za main part ta fara kuka, lallashin ta ya dingayi amma bai daina abinda ya faraba, Khalid Sai adua yake ta kwararo mata don tunda yake bai taba jin abinda yaji wurin Ameera ba har cikin ranshi yana cewa Salem yayi asara,

Ameera ido ya raina fata dukda Khalid was gentle don Sam bayason kukanta amma saida ta koka sosai, da sauri ya mike bayan ya samu nutsuwa yayi kneeling ya kama hannun ta yana yimata adua har lokacin bata bar kuka ba, rarrashin ta ya dingayi har saida tayi shuru ya shiga bathroom ya hada mata ruwan dumi ya dawo ya dauketa.

Bayan ta gama wanka ta fito tana tafiya ahankali amma tafiyan ta bai bace ba sosai nace ba kama Tawakaltu da aka yiwa dalla dalla ba 😂😂😂. Shima Khalid wanka yayi ya fito yayi kneeling gaban gadon hannun shi rike da nata ya cigaba dayi mata adua, har dasu thanks, Ameera kwance idanuwanta lumshe tana sauraron abinda Khalid ke cewa ranta fal da murnan ta kawo budurcinta gidan mijin ta, aduan Khalid yaki karewa, bude idanuwanta tayi ta galla mashi harara tana cewa
"Ya isa haka nan mana..." Dariya ne ya kufcewa Khalid don kaman ba ita tayi maganan ba, kin tashi yayi ya cigaba da yi mata aduan,, Sai turo baki take tana magana Ahankali batare da Khalid yaji abinda take cewa ba.



Bayan sati daya da wedding din Khalid su Salem suka dawo Nigeria, a lokacin cikin Tawakaltu wata 4 da two weeks, abuja suka sauka duk guys dinshi cewa suke
"Sir daga yanzu ka tashi daga slim... Don kayi fat..." Dariya yayi tana cewa
"Thanks to my princess..." Ya amsa masu
wacegari suka je yola, Abba ma saida yace Salem yayi kiba har yana zargin haka nan yaki zuwa bikin Khalid don babu alaman ciwo ajikin shi.
Bangaren Umma sukaje, Umma na ganin su ta mike da sauri, da sauri itama Tawakaltu tayi kneeling kaman yanda ta saba, fada Umma ta farayi tana cewa
"Kar ki kara wannan kneeling din...baki ganin conditions dinki?...please kar ki kara..." Ta fada tana mikar daita tsaye, cikin girmamawa ta gaida ta itama cikin jindadi ta amsa tana nuna murna ta a fili, tsaraba yan aiki suka shigo dashi ciki,Umma kallon Salem dake ta fama murmushi tayi ta saki murmushi tana tunanin Ashe danta zaiyi kiba haka?
"Amma son lafiyarka lau kaki zuwa wedding din amininka ko?.." Umma ta tambayeshi, murmushi yayi
"Aa...Umma bani da lafiya..." Bai idaba Umma ta katseshi dacewa
"Karya kake...baka kama da Mara lafiya..." Kallon Tawakaltu yayi
"Princess ba bani ba lafiya ba?..." Ya tambayeta yana kanne mata ido daya, Umma dake kallon abinda yake ta dauki pillow ta wurga mashi tana cewa
"Indai lafiyan ka lau kaki zuwa wedding din Khalid baka kyauta ba..."
"Umma da gaske bani da lafiya...ai kinsan haka nan bazanki zuwa auren Khalid ba..."
"Kai dai ka Sani..." Ta fada tana kama hannun Tawakaltu dake zaune kusa daita. Dakinta suka shiga shikuma ya haye dinning yafara cin abinci.
A dakin Umma aka kawowa Tawakaltu abinci Umma ta amsa ta fara feeding dinta kaman yanda ta saba feeding Salem, da farko kunya tafaraji amma daga baya sakin jikinta tayi taci ta koshi,
"Da fatan Salem yana kula dake yanda ya kamata?..."
Umma ta tambayi Tawakaltu, Ahankali ta daga mata kai alaman eh,
"Kar ki boyemin komai.. Ki dauke ni amatsayin maminki...remember amananki akabani...ance in dauke ki kamar su shuwa kuma na dauka...so kar kiji kunyar fadamin abubuwan sda Salem ke yi maki Wanda baki so...." Tawakaltu dadi takeji har cikin ranta
"First love babu abinda yake yimin...." Ta amsa mata kanta kasa
"Bakisan yanda danki yaci min uwa ba kafin in fara sabawa..." Tafada cikin ranta.
"Da akwai inda yake maki ciwo yanzu?.." Umma ta sake tambayan ta,
"Aa...kasala ce kawai Sai dacin baki..." Ta amsa mata cikin natsuwa
"Wannan is normal... Ko zaki zauna nan in kula dake har ki haihu?..." Da sauri ta dagawa Umma kai alaman eh Sai dariyan keta take cikin ranta don tasan Salem zaici kaniyanta
"Amma inason zuwa wurin su mami..." Tafada ciki sanyin murya
"Ai wannan ba matsala bane...Sai akaiki a maidoki..." Umma tayi assuring dinta,
"Kwanta ki huta..." Inji Umma, ahankali tayi kokarin mikewa Umma ta umarceta da ta kwanta kan gadonta. Kwantawa tayi itakuma Umma takoma falo har lokacin Salem na zaune kan dinning, zama Umma tayi opposite to him ta shaida mashi hukuncin data yanke,
"Kambu...Matan nan zata kulla min tsiya..." Ya fada cikin ranshi, azahiri kam saida ya kusa kwarewa da ruwan dayake sha, da sauri ya ajiye cup din yana cewa
"Umma wa zan dinga dafamin abinci..." Yafada sounding out of words, harara Umma ta balla mashi
"Da wake dafa maka?..."
"Ai Umma... Wai itatace zata zauna?..."
"No...ni
Nace ta zauna..." Zaro ido yayi don yasan halin ummanshi
"Kuma ta amince?..."
"Kai bansan iskanci..." Tafada tana mikewa, shima mikewa yayi ya shiga dakinta itakuma ta zauna falo tana kallon dadin kowa atashar arewa 24.
Yana shiga ya hangi Tawakaltu ta bage kan gado, karasawa yayi wajenta ta bude ido
"Princess ya akayi kika amincewa Umma zaki zauna nan bayan kinsan larurata?..." Marairace fuska tayi tana cewa
"Sugar ya zanyi...I can't say no..."
"Yo can't say no?... AI Wallahi yanda kika amince haka zaki koma kice mata zakibi...in ba hakaba duk weekend zan zo nan kuma kinfin sanin sauran...." Dariya tayi cikin kasaita tana cewa
"Ni gaskiya bazan Iya fada mata haka ba..." Mikewa tayi ta matsa kusa dashi har suna shakan numfashin juna Sannan tace
"Amma kai ka fada mata..." Tafada tana lashe bakinshi,
"Daman da gangan kika amince zaki zauna nan...karki damu...nasan Maganin ki..." Yafada yana kaman bakinta, kiss yayi mata, zare bakinta tayi tana cewa
"Meye magani na?../"
"Bazan kaiki Kwara ba..." Yafada yana kara kai bakinta saitin nata kaman bai taba kissing dinta, Dariya tayi mashi tana cewa
"Umma tace zatasa akaini a maidoni..." Takashe maganan tana yi mashi gwalo, Dariya yayi
"To anjuma zansaki kuka yanda zata jiki ta koremu ...." Kwantawa tayi tare da juya baya tana cewa
"Ba Sai ka ganniba?..." Mikewa yayi ya karayi mata kiss Sannan ya fita tare da bugun bumbum dinta da karfi.



*Da fatan ansha ruwa lafiya... Allah ya bada lada ya biya bukatun mu na alkhairi* 🙏👏🤝👏
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: 💚💙💜❤💛
ZAKISAN KONI WAYE
💜❤💛💙💚


®zuwairat(ummu Maryam)



8⃣2⃣



Masoyan zakisan koni waye ina mika godiya ta gareku, thanks for your support


Ban manta dakeba the birthday gal, Sarah am wishing you a fruitful and prosperous years ahead, happy birthday🎂🎂🎂 hope you find all you desire in life.


Yan ummu Maryam page I love you all💋💋

ZAKISAN KONI WAYE fan 1 to 8 duka ina kaunarku.

Yan Zuwairat novel 1 and two I love you die, Allah ya bar zumunci har dake khulud sarauniyar surutu.


Yan khaleesat hydar novel I heart all of you, comments dinku na Sani nishadi.

💛💚💙💜❤

Da yamma Salem ya zo komawa abuja kiri2 Tawakaltu ta ki binshi don har gabanshi umma tace
"Ki bishi in kin yi niyya..." Ta makale kafada tana cewa
"Zan zauna dake..." Salem kam kaman ya hadiye zuciya ya mutu, har bakin jet ta raka shi, ko kallon ta baiyi ba ya shige, hannu yayi mata alaman ta zo, ahankali ta taka ta shiga ya rike ta yana cewa
"Yanzu princess ni zaki yiwa haka?..." Marairace fuska tayi tana cewa
"Ni kunya nakeji ban iya abinka..." Hararanta yayi yana cewa
"Don't worry... In ma guduwa kikeson yi daga gareni ba komai bane cos zan dinga zuwa nan kullum ki bani hakkina..." Dariya tayi batace kala ba, kissing dinshi tayi kokarin yi ya kauda kanshi gefe. Sauka tayi akayi sama dashi.


The following day Umma ta bukaci yasa akawo jet don zaa kai Tawakaltu Kwara.

Ranar da taje kam mami kasa bacci tayi don murna, kowa Sai cewa yake Salem ya Iya kiwo don ba karamin chanza musu tayiba.

Kwana ta biyu hau jet don komawa yola Ashe Salem ya fadawa pilot ya kawota abuja, aikam gidanshi aka kaita, yana jin karan jet ya fito sanye da three quarters da polo, kallon ta yayi yana cewa
"Allah ya kawo min kaza gasassa daga sama.." yafada yana dariya, marairace fuska tayi tana cewa
"Sugar nice kaza?..."
"Ni badake nakeba..." Yafada yana daukanta gaban su majed yayi mansion dinshi daita.

_Two months later_

Su Ameera ansha amarci kaman hauka don har ta saba da rayuwar aure, ba karamin kulawa Khalid yake yi mata ba, kusan komai shi keyi mata har da wanke undies kullum cikin fada mata how much he loves her yake, Ameera har gajiya take da jin I love you.

Yau suka dawo Nigeria kuma da fever ta dawo don tana kwance jikin Khalid Sai rawan sanyi take,bayan kaman hour daya wani abokin Khalid yazo da kayan aiki,

Kasancewan doc ne, tambayoyi ya fara yimata, tana bashi amsa,
"Yaushe kika ga period dinki last..." Doc ya tambayeta, kallon Khalid tayi Sannan tace
" na mance
.." Tafada bakinta na rawa, murmushi yayi yana cewa
"Kuna honeymoon kin mance ko?..." Ya fada yana kallon Khalid, hararanshi Khalid yayi yana murmushi,
"Well from all indications your wife is pregnant... Dukda banyi test ba amma symptoms ne na pregnancy.. Sai ka kawota hospital mu duba lafiyanta..." Tunda yace pregnant Khalid ya wace baki don murna, itakanta Ameera saida ta sake murmushi, kanta kar kirjinshi. Bayan doc ya tafi Khalid ya dauketa ya rungume yana yimata godiya kaman ita ta halicci cikin.

Sanar da iyayenshi yayi suma sunyi murna sosai. Suna kwance bayan sun dawo daga hospital Sai tunanin Salem yake, bai mantaba sanda Tawakaltu ta samu ciki saida Salem ya sanar dashi
"Angel ina tunanin Salem..."
"Pls Ku shirya..." Ta fada cikin sanyin murya,
"Baby baya picking calls dina....har yanzu fushi yake dani...wallahi it is disturbing me..." Kara rungume shi tayi tana cewa
"Kaje wurin shi mana...ka bashi hakuri cos kai ka bata mashi rai..." Inji Ameera dake Kara kankame mijin ta kaman Zaa kwace matashi.
"Sai kinji sauki...I can't leave you now... " yafada yana shafa cikinta.

Abangaren su Salem kam har yanzu Tawakaltu na wurin Umma amma babu abinda hakan ke hana Salem don duk kwana biyu yake zuwa yola, Umma Sai mamakin shi take don da Sai yayi wata baizo gida ba amma yanzu every two days Sai yazo.
Yanzu cikinta ya kai wata shida going to seven duk fuskan ta ya chanza ka pimples, duk sanda Salem yazo yaje inda take Sai ya durkusa kasa yace
"Hajiya inawuni?..." Hakan yana bawa tawa haushi sosai, at times Sai ya kura mata ido ya tuntsure da Dariya, ta shika tayi fam ga takuran ciki ga na Salem.
Suna zaune kan dinning table dukkan su har Abba suna cin lunch, Salem ya daga kai ya kalli tawa ya tuntsure da Dariya, kallon shi tayi ta galla mashi harara ya daga mata gira,
"Zakuje gidan abokinka ko?..." Inji umma, Da sauri Salem ya kalleta,
"Umma wane abokina?..." Ya tambayeta don sam ya manta da su Khalid, hararanshi tayi
"Kana nufin bakasan Khalid ya dawoba?..." Da sauri ya saki murmushi
"Oho...nasani mana...bansan shi kike magana ba..."
"Aboki nawa gareka?..."
"Shi kadai...." Inji Salem, Abba kam baice kala ba cos shi yana daga cikin policy nashi baya magana while eating.

Bayan sun gama lunch ya tafi part dinshi yayi kwanciyan shi, har 4:30 bai nuna alaman zaije wurin Khalid ba donshi har yau bai bar jin zafin abinda Khalid yayi mashi ba, Umma ce ta shigo part dinshi, zama tayi shima ya mike zaune
"Habibi ka fada min gaskiyan abinda ke faruwa tsakanin ka da Khalid..." Da sauri ya saki murmushi
"Babu komai.."
"Da komai mana...Khalid da ya tsaya ya taya ka komai lokacin bikinka bakazo nashina dukda nasan haka nan kaki zu...Sannan yanzu na fada maka ka kai matarka amma nuna alaman kana son zuwa ba...son what is happening..."
"Umma ba komai.... Daman cewa nayi bari rana ta sauka Sai muje tunda na kirashi ya fada min inda gidan yake..."
"To kuyi sauri kuje... Baason mai ciki kan titi da magrub..." Tafada tana barin dakin.

Tawakaltu ya kira ya fada mata ta shirya zasu fita

Bata yi wasting time ba tayi wanka ta aka jallabiya ko kwalliya batayiba don ta kanta take, shima Salem wanka yayi ya shirya tare da sukaje dakin Umma sukayi mata sallama Umma tace
"Ku gaida su..."

Cikin mota suka shiga driver ya jasu sukafita,
"Ka kaini gidana..." Salem ya umarceshi, Tawakaltu kallon shi tayi

Please Login or Register in order to submit comment