Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fada jikin mom ta rungume ta
"Habibty ya hanya?".
" alhamdulillah... "
"Ya su hinde?..".
" suna lafiya.. Sunce in gaisheki..." Tafada sounding very excited
"Habibty.. Why do you seem happy... Ko da akwai abinda kikeson fadamin..." Tafada tana kallon how light up fuskan Ameera yake,
"Mommy.. I have choosen Khalid... Shi zan aura..." Tafada kanta kasa, tsaya kallon ta tayi
Mom dago fuskan ta tayi tari rike cikin palm din ta Sannan tace
"Yanzu habibty kinfi son Khalid kan sultan?..." Ahankali ta dagawa mom kai
"To Allah yasa haka shi yafi alkhairi..." Dasauri tace
"Ameen.." Kwantawa tayi kan gadon mom har dad ya dawo, wajen shi taje ta fada mashi abinda ta fadawa mom,
"Waye babanshi?.." Dad ya tambayi Ameera,
"Governor na Adamawa..." Ta amsa mashi, dadi dad yaji cikin ranshi,
"Zan zama in-law na governor..." Ya fada cikin ranshi, kunsan mai hali baya barin halinshi especially in ya zame maka jiki,
"Ki fada mashi ya turo..." Inji dad, da sauri mom ta kalleshi
"Ai ya kamata ayi bincike ko?.." Gaban Ameera faduwa yayi tana tsoron kar a binciko Khalid
"Wane irin bincike kuma?...waye baisan governor na Adamawa da mutunci da sanin ya kamata ba?..."
"AI bashi zata auraba danshi zata aura...."
"AI ba sai..." Dad bai idaba mom ta katseshi dacewa
"Zaka farako?...haka kayi lokacin aurenta da Salem... Kuma..." Da sauri dad ya daga hannun shi
"Shikenan... Ayi binciken....karki jamin sharri..." Itadai Ameera zama tayi tana sauraron su
"Tashi kije kici abinci..." Mom ta fada mata, mikewa tayi ta koma dakinta, kayan cikinta ta cire ta kwanta Sannan tayi dailing number sultan, nan ta fada mashi she have something to tell him.

Bayan sallan magrub yazo, hakuri ta fara bashi
"Pls can you hit the nail at the head?.." Ya fada mata dukda ya gane abinda ke faruwa, nan ta fada mashi ta fidda miji, murmushin karfin hali yayi Sannan yace
"Haba jewel...saboda wannan kiketa kame2 kaman kinyi abun kunya?... In baki mantaba I told you duk yanda Allah yayi daidai ne....so na dauki kaddara...." Yafada cikin sanyin murya, she never expect to hear that from him,
"Thanks for your understanding..." Tafada ahankali, baice kala ba ya mike
Ya fuskance ta, yana kallon beautiful and innocent face dinta, ahankali ya jawota jikinshi ya rungume ta, da sauri ta zame tana waige2 don ta tabbatar babu Wanda ya ganta, murmushi kawai yayi Sannan ya shiga motanshi ya tafi. Ameera komawa ciki tayi tana shakan free air don ji take kaman ta sauke mountains daga kanta.


Khalid kam yana tuki yana waya da Salem, nan ya shaida mashi Ameera ta amince zata aureshi.

Yana isa gidan su ya shaidawa first lady ya samu Matan aure, murna wurin ta baa magana Cos babu abinda take so kaman first son dinta yayi aure
Tunda Salem yayi aure take aduan Allah yasa shima yayi cos there are bird of the same feathers so there flug together. Dad dinshi ya fadawa shima wise man din cewa yayi
"Sao yanzu ka gandama kenan..." Khalid Dariya kawai yayi,
"Sai ayi bincike kan family dinsu kafin muje ayi maganan aure..." Inji his excellency,


_One week later_

Duk binciken daya kamata su dad sunyi kuma babu Wanda bai shaidan halin Khalid ba, asalima cewa akayi yafi sauran brothers dinshi mutunci, ( hmmm daman bincike baisa agane dukkan halin mutum.. Sai ka zauna dashi)

Abangaren Khalid kam suma anyi bincike amma sun gano yarinyan ta taba aure,
"Yanzu son yarinyan data taba aure zaka aura as a first wife?.." Shine tambayan da mom dinshi tayi mashi, ahankali Khalid yace
"Mom..ita nakeso....kuma duk karyan mutane ne...bata taba aureba...."
"AI ba hanaka zanyi ba tunda ba haramun bane...am happy zakayi aure" Tafada cikin jin dadi.

Bayan sati daya uncles din Khalid da wasu manyan mutane sukaje gidan su Ameera Neman aurenta, kuma da kayan saka rana sukazo, Dad dadi sosai yaji don yasan yanzu yarshi zatayi aure, anci ansha Sannan aka sa sati 8 that's two months.

Tunda daga ranan aka dauko mai koyawa Ameera abinci da sauran aikace2 gida. Ana sauran 7 weeks Khalid ya shigo Kano, ba karamin kyau yayiba, itama tayi kyau sosai saboda gyaran jikin da anty Sadiya ta fara yi mata, kasa daina kallon ta yayi, kanta kasa Sai wasa take da fingers,
"Babyna haduwanki bai faduwa..." Yafada yana murmushi, itama murmushi tayi,
"Do you have any special events in mind?.." Ya tambayeta, ahankali ta girgiza mashi kai
"So ki yarda in sa ashirya all the events?.." Ya sake tambayan ta, ahankali ta daga mashi kai, kallon ta yayi
"Baby wannan kunyan fah?...tunda nazo baki daga kai kika kalleni ba...what have I done wrong.." Ya tambayeta kaman zaiyi kuka
"Nothing..."
"Then pls look at me..." Yafada cikin whisper, daga kanta tayi suka hada ido, ido daya ya kashe mata, tayi murmushi tare da dauke kanta,
"Angel INA kikeso mu zauna?... I have two duplexes in abuja....two in yola Sai one a banana island lagos..." Ameera shuru tayi bata ce komai ba don babu abinda take tunawa kaman ya kusa ganin nakedness dinta,
"Angel say something.."
"Duk inda kakeso..." Ta fada mashi
"Ko in sayi gida nan Kano?..." Kallon tayi ta saki murmushi, Dariya yayi
"Baki idaba yarinya... You want to be close to mommy..." Ya fada yana dariya, Itama Dariya tayi don ya gano ta,
"Ai bance mu zauna nan bako..." Ta fada cikin shagwaba, Dariya ya karayi yana cewa
"sayi gida nan mu dinga sauka in Mun zo Kano..." Daga kai tayi ta harareshi
"Ga gidanmu?..." Baice komai ba ya sa hannu cikin aljihunshi ya dauko wani small jewelry box, ya bude, wani white ring ne mai dauke da diamond stone samanshi, hannun ta ya kama ya sa mata Sannan ya Kara dauko wani envelope ya saka cikin palm dinta, kallon zoben tayi ta saki murmushi cos ba karamin kyau yayi wa hannun ta ba. Sun dade suna hira batare data bude envelope dinba, sallama yayi mata ya kuma shaida mata yanzu saidai su dinga waya cos he will be very busy saboda wedding arrangements.

Tana komawa sama taga credit card ne da pin number kiranshi tayi ta tambayeshi ATM din na meye ya shaida mata ta zari any amount da take bukata for her friends anko.

Duk yanmatan dake yiwa Ameera habaici saida suka dawo suka bata hakuri don ta dama dasu, batayi masu wulakanci ba aka shiga harkoki dasu, zeenat kam bataji dadi abinda Ameera tayiwa sultan ba amma she takes everything in good faith.

Ba karamin gyara Ameera take shaba don abubuwan is to much, jikin ta ya kara kyau fiye da yanda kuke tunani, kullum cikin waya suke da Khalid.

Ana sauran sati four biki aka kawo lefenta, fadin kyau da yawan kayan is a waste of time and strength just imagine lefen yayan governor, kuma civilised one don mom din Khalid wise woman ce ta gidan karshe, akwati 18 aka kawo 12 lv sai 6 gucci traveling bag da mota daya sai kujeran makka 3, mom kam abun tsoro ya bata dad baki har kunne saboda jin dadi, duk Wanda ya zo ganin lefen Sai ya koma da baki bude, aranan Ameera da Khalid suna waya take shaida mashi kayan sunyi yawa, cewa yayi bai ma gansuba Kuma ta dauka duk yawan kayan can never be compired to her beauty.

Abangaren Salem kam duk ya damu ba don komai ba sai yanda Khalid yaki amsan komai daga hannun shi, duk abinda ya bashi Sai ya ki amsa yana cewa bayason rai Ameera ya baci, ko yanzu suna zaune da tawa tawa suna kallo shi kuma yana waya da Khalid,
"Guy gaskiya abubuwan da kakeyi is touching me... Ya zakayi min haka...we grow up together... Amma zakayi aure ka ki amince wa da komai daga gareni..." Inji Salem daga chan bangaren Khalid yace
"Just understand....banason abinda zaisa Ameera bacin rai...remember she almost dump me because of you..." Gyara zama Salem yayi Sannan yace
"Yanzu guy mace zata rabamu da kai kenan?..."
"Haba wake maganan rabuwa...it's just for the main time..." Inji Khalid,
"Ba komai...we will be coming back next week..." Inji Salem yana rike hannun tawa, da sauri Khalid yace
"I beg you in the precious names of Allah... Don't come back now... Wait until five weeks for now..." Ido Salem ya zaro
"Hope this is not what am thinking?..."
"Yes it is... In ka dawo su first lady da first love zasuyi mamakin rashin ganin ka a wedding dina...so pls just wait till after my wedding..."
"Yanzu Khalid are you saying I should not be present at your wedding?.." Ya tambayeshi afusace, ahankali Khalid yace
"am sorry but yes...." Salem bai Kara cewa komai na ya katse wayanshi tare da mikewa daga inda yake zaune kusa da Tawakaltu, da sauri ta bi bayan shi,
"What's wrong?..." Ta tambayeshi,
"Nothing..." Ya fada mata atakaice, rike mashi hannun tayi ya fixge
"I said nothing!...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta ja baya, tana kallon shi, gaba yayi tabi bayan shi Ahankali, afusace ya juyo ya kalleta fuskan shi Sam babu walwala
"See just go back...right now am upset and I don't want to be disturbed..." Kuka tafarayi tana cewa
"So am disturbing you?...to shikenan... Let me keep my distance..." Tafada tana juyawa Ahankali tare da dafa maranta, Salem tsaya kallon ta yayi har ta zaunasai yaji bai kyauta ba cos ba ita tayi mashi laifi ba amma he's taking it on her, komawa yayi wajenta,
"Princess am sorry... Kawai rainane a bace...kiyi hakuri kinji?"... Kai ta daga mashi, hannu yasa ya goge mata hawayenta tare da jawota jikinshi.

Ahankali lokacin ke tafiya inda Khalid ya kawowa Ameera list na events da zasuyi for a whole week, kuma ko wanne rana nada dress code, ana sauran two weeks Ameera ta rabawa friends dinta iv. Yanmatan kam shirye suke don sunji abun nayine.
Gyaran da anty Sadiya takewa Ameera yafi na wancan lokacin cos ta samu enough time and money, Sannan lefen da aka kawo ya Kara nunawa cewa ba anyhow mutum zata aura ba haka yasa kullum da abinda take bata, Sannan yanzu ba laifi Ameera ta iya at least not less than 15 variety of food
Duk Wanda yaga pre wedding pics dinsu Sai yace Ameera da Khalid sis and bro ne saboda yanayin hasken su da pointed noise,guys Sai zolayan Khalid suke suna cewa ya fi abokinshi iya zabe, cikin ranshi kam saidai yace bakusan shi ya fara aurenta ba.

Yau sauran ten days saurin aure, da yamma around 5pm wani moving van ya shigo gidan, mom fitowa tayi tana kallon katon van din Sai mamaki van din take don sai gobe kayan Ameera suke isowa, driver ya fito daga cikin van tare da yaranshi, kallon mom dake ta mamaki yayi Sannan yace
"Sakone daga sultan..." Baki mom ta bude da aka fara sauke kayan, complete set ne na kujera da da gado, exactly irin na zeenat, mom komawa ciki tayi ta fadawa Ameera abinda dake faruwa, kiran sultan tayi amma baiyi picking ba..

Ana sauran nine days daurin aure governor na Kano ya amshe dukkan hotel da quest house saboda baki kuma baban Khalid babban abokinshi ne.
Tun sauran 8 days gayu suka shika garin kano, duk inda kika ratsa handsome guys kake gani daman Khalid yafi Salem hulda da guys kuma yafi shi shiga social life.

Umman da abban Salem Sai kiranshi suke suna why bai dawo ba har zaayi bikin amininshi, karya kawai yayi masu kan he's seriously sick, ammi kam cewa take
"Kuyi adua ya gane hanyar gidansu tunda ya auro mayu...kilan tana chan tana zukeshi...."


Yau aka fara events, inda kunshi aka fara dashi, cikin katon hall dukkan yanmata ne kawai Sai tsantsara masu hyena decor ake. Ga kidi yana tashi.

The following day akayi kauyawa party a gezawa gidan granny din Ameera, shigan original yan kauye akayi, Khalid kam kasa daina kallon Ameera she was looking extra stunning.
Sai Fulani night inda ango da amarya tare da friends sukayi shigan Fulani, followed by Arabian nights Sai mothers night, yawancin Matan governor sun hallaci wannan taron.
Sai picnics,

Atakaice ranar Friday akayi daurin auren Ameera da Khalid kan sadakin dubu Dari, daurin auren ya samu manyan mutanen kasa, abinka da dan governor, Khalid kam bakinshi bai rufuwa saboda
Farin ciki, bayan daurin aure aka wuce reception inda amarya ta sha silver flowy gown daga companin varsace. Khalid ma ya sanyan suit silver mai dan sheki kaman an zuba mashi ruwa.


๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ surprised?....don't be...am full of surprises๐Ÿ’ƒ๐Ÿคฃ
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค
ZAKISAN KONI WAYE.
โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu Maryam)

8โƒฃ0โƒฃ

*My Habeeba I don't know how to show my appreciation... But I want you to know I love you, Allah ya bar kauna...* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹

Ba karamin party akayi wurin reception, dama ga Ameera sarauniyar rawa kuma Khalid sarkin rawa, rawa sukasha har na tashin hankali, Khalid komawa gefe yayi yana kallon yanda matarshi take dansewa, daga baya iyaye tafiya sukayi suka bar yanmata da samari suka shiga da party, wani crazy beat aka saka mai instrumental, fili yan mata suka bawa samari suka shiga da rawa kaman hauka har da kwantawa kasa don dadin dancing, suna cikin haka wata siririyar budurwa ta shigo mai shegen kyau kamar ita tayi kanta, da ka ganta ka ga Khalid saidai ita tafishi kyau kasancewan ta mace, ga hujen hanci rawa ta farayi ta nufo inda Khalid ke tsaye suna rawa, juyowa Khalid yayi ya wangalo idanuwa tare da rungume yarinyan
"Baby ya akayi kika dawo?...bana fada maki kar kizoba?..." Ya tambayeta, marairace fuska tayi tana cewa
"Kun hanani zuwa na yaya Salem Sannan kuma ashe kar inzo naka?...AI bani kadai ke karatu abroad ba..." Khalid girgiza kai kawai yayi ya kama hannun ta yayi introducing Ameera as his wife, yarinyan kissing Ameera tayi a cheeks dinta tana cewa
"Yaya dole ka mutu kanta... Wannan kyau haka?..." Ameera da Khalid Dariya suka, yarinyan wurin mc taje ta fada mashi ya fadawa mutane duka su zauna zata danse da yayan ta, aikam kowa komawa yayi ya zauna ya rage daga yarinyan Sai Khalid cikin katon filin, nan akasaka masu wani sabon waka suka fara rawa kaman mahaukata, banda Dariya babu abinda Ameera da sauran mutane suke, Ameera har da rike ciki saboda Dariya. Atakaice Sai twelve na dare aka tashi aka maida ameera gidansu cos the following day zaa kaita yola, adaren mom ta zaunar daita tayi mata nasiha ba kadan ba, har kuka Ameera ta farayi saboda yanda mom take magana. Sai wajen 3am ta kwanta, wacegari da wuri mom ta tadata tayi sallan Sannan takara yimata nasiha kan zamantakewa Daga nan ta koma dakinta Zainabu ta hada mata ruwan wanka mai dauke da turare, tayi wanka ta fito ta tadda anty Sadiya ta fiddo mata wasu blue lace masu shegen kyau da tsada, dinkin skirt da riga, skirt din har Jan kasa yake, ba karamin kyau tayiba, kwalliya wance aka biya donyi mata kwalliya tayi kyau sosai, mom ta kawo mata tea my kauri da kwai amma ta girgiza mata kai, zare mata ido mom tayi
"Mom na koshi..." Ta fada kaman zatayi kuka,
"Ubanme kike CI da safen nan zakice kin koshi?...come on amsa..." Ta daka mata tsawa, kuka ta farayi, anty Sadiya ta amshi tea din ta fara rarrashin ta tana bata da kanta tana sha har tasha rabi, lifaya aka sa mata mai shegen kyau aka rufe mata kai da hulan, wurin su dad aka kaita sukayi mata nasiha aka kaita wurin mom ta karayimata, kuka ta farayi sosai, hahhh su Ameera anyi hankali, ita kanta tasan Sai yanzu tayi aure. Motocin daukan amarya ne suka fara shigowa gidan, nan su anty Sadiya sukazo daukanta, kiri2 Ameera tace bata zuwa tana kuka kaman ba itace suke dirty dance da Khalid ba jiya. Da kyar aka banbareta daga jikin mom aka kaita kasa Sai ihu take kaman wacce zaa kai lahira, wayanta dake hannun Zainabu Sai ringing take, amma kuka ya hanata amsan wayan, har aka kaita bakin wani white range Rover bata bar kuka ba. Affan na gefen ta yana kuka shima kaman ranshi zai fita, anty Sadiya koreshi tayi yace shima zashi raka anty, dole anty Sadiya ta amince suka shiga cikin mota tare. Motoci 20 aka kawo daukan amarya, kowacce mota mutum biyu baya Sai daya gaba. A haka yanmatan suka shige motocin akayi hanyan Adamawa.

Har suka isa Ameera bata daina kukaba, affan Sai rarrashin ta yake kaman wani babba, wani kasaitaccen unguwa suka shiga, duk unguwan babu mutane Sai manyan gidaje, bakin wani katon gate sukayi horn mai gadi ya wangale gate aka fara shiga da cars, dukkan motocin shiga sukayi kuma da akwai extra space da zaa Iya ajiye wasu motoci da suka fi yawan wayan nan, fadi haduwan gidan is a waste of time don gidan ya hadu Sannan tsarin zamani. Anty Sadiya fitowa tayi ta kama Ameera dake kuka har lokacin suka shiga cikin wani makeken falo. Nan yanmatan da manyan suka fara guda don wurin ba karamin haduwa yayi ba, daya daga cikin bedroom aka kai Ameera basu dade da zuwa ba aka fara shigowa da manyan kula na abinci kala2_ atakaice Sai wacegari akayi walima Sannan aka maida su anty Sadiya da sauran mutane Kano, Ameera kam idanuwanta basu buduwa saboda
Kukan data sha sam bata wannan zumudin da ta dingayi lokacin aurenta da Salem, har cikin ranta take tsoron abinda zai biyo baya, Jitayi kaman ana motsi inda take da sauri ta kame waje daya don girma gidan tsoroyake bata, around 5pm Khalid ya shigo da Sallama amsawa tayi amma bakajinta saboda yanda muryanta ya dashe, Ahankali Khalid ya ya karasa wurin ta ya zauna kasa yana kallon swollen face dinta, shuru yayi ya cigaba da kallon ta for a while Sannan yace
"Baby ji yanda idanuwanki suka kumbura saboda kuka...please stop it already..." Yafada yana goge mata hawayenta, murmushin karfin hali tayi shima ya saki murmushi yana kama hannun ta, "muje kici abinci,.." Ya fada mata, ahankali ta Girgiza mashi kai, marairace fuska yayi
"Please... " yafada yana mikar daita tsaye, bata kara cewa komai ba ta bishi zuwa wani kasaitaccen dinning table na mutum biyu kadai, Ameera Sai shessheka take, kallon ta yayi
"Tell me what you want and i will do it for you..." Ya fada cikin natsuwa,
"Nothing.. Am just missing home.." Tafada Ahankali, murmushi yayi
"Tun yanzu?... Anyway don't worry.. Ko gobe kikeson zuwa gida ina iya kaiki in maidoki...am not among those that makes their wives stay away from their families... Am a civilise man...you will know me better..." Shuru tayi tana sauraron shi yacigaba dacewa
"And if you are scared because of first night don't be...I won't do anything you don't like..." Yafada yana serving dinta, feeding dinta yayi amma ba sosai taci abinci ba, mikar daita yayi
"Angel muje in nuna maki gidanmu kafin magrub ta gabato, ba musu ta mike ya kama hannun ta suka shiga zagaya gidan ita kanta can't believe itace matan gidan cos it is far beyond her expectations, har gym ke da akwai Sannan da kawai underground kuma acikin underground da akwai swimming pool inda zakayi swimming batare da kaji tsoron wani zai ganka ba, suna tsaye jiki pool din hannun ta cikin nashi ya juyar daita tare da rike shoulder dinta ahankali Sannan yace
" nan zamu dinga pool parties dinmu ni dake tunda naga you are a good dancer..." Kauda kanta tayi tana murmushi,
"Muje muyi sallah kafin muyi parking..." Da sauri ta kalleshi
"Ina zamu?..."
"Florida..." Mamaki ne kwance kan fuskan ta, murmushi yayi yana cewa
"Am not that poor you know..." Yafada yana daukanta in a bridal style.
Sallah sukayi Sannan suka zauna hira kaman ba amarya da ango ba, yanda Khalid keyi yasa Ameera sakin ranta don he's very much free.
Yana Dariya yace
"You can ask me anything... I promise to be frank..." Daga kai tayi ta kalleshi directly Sannan tace
"Why sir Salem baizo wedding dinmu ba?..." Murmushi Khalid yayi yafada mata gaskiya bai boye mata komai ba, ahankali tace
"Gaskiya baka kyauta ba....kar yayi tunanin ni nasaka kyin hakan...kasan komai nada sanadi kuma sir Salem shine sanadin haduwata da kai...."
"But you were really angry when you find out the truthful about us...."
"Ni ba friendship dinku ya bani haushi ba...kawai boyemin da kayi ne ya bata min rai"
Khalid kallon ta yayi yana mamakin ashe irin su na samun mata irin Ameera?,
"Ai yanzu fushi yake dani don ko na kirashi bai dauka...." Inji Khalid
"Konice fushi zanyi..." Inji Ameera, Khalid kurawa lips dinta ido yayi Sannan yace
"You beautiful lips... Can't still believe they are mine..." Yafada sounding naughty, murmushi kawai tayi tana kallon bakinshi, tunawa tayi wasu matan sun gama kissing wannan red lips din,
"In kara tambayan ka wani abun?..." Ta tambayeshi ahankali, kaman hannun ta yayi tare dayiwa hannun ta kiss,
"Anything..." Kallon shi tayi Sannan tace
"Ka taba kawo mata nan gidan?..." Ajiyan zuciya ya saki tare sa girgiza mata kai yana massaging yatsunta,
"Ina kake kaisu?...." Ta kara tambayanshi, ahankali yace
"Ban guest House na abuja...." Murmushin karfin hali tayi
"Gidan su kake zuwa daukan su kafin ka kaisu guest house ka lalata su?..." Da sauri ya matsa kusa daita sosai ya tallabo fuskan ta don yaji yanda maganan ke fita daga bakinta da bitterness,
"Angel... Ban taba zuwa daukan mace ba...mostly yan Matan ke kawo Kansu....zasu sameka office dressed almost naked...watama zatazo office dinka da after dress amma data cire zaki ganta daga ita Sai bikini pant wata kuma rough dress... Baby am not an angel...wasu lokutan ina resist dinsu wasu time kuma I can't... Wallahi ban taba tsayar da yarinya nace tazo muyi zinaba...kawai the ladies are looking for connection and we are willing to oblige...." Ameera shuru kawai tayi tana kallon yanda yake moving bakinshi kaman tafiyan tsutsa.
"Hmmm...yanzu ni tsoro nake ji kar kayi resuming office wata ta kawo kanta..." Rungume ta yayi
"Wallahi nayi maki alkawarin no woman except you..."
"Kasan lokacin da akace zaayi bincike kanka I was afraid kar a gano gaskiya game da halin ka amma surprisingly Sai akace you are a nice man..." Dariya Khalid yayi
"Ai is only small boys that play games in their towns... If a girl is interested in me then follow me to abuja...." Itadai Ameera sauraron ikon Allah kawai take don gani take he's not telling the truth...ya zaayi mace ta mikawa namijin da ba halal dinta ba kanta
"Yanzu baka tsoron wata cuta?..." Ameera ta tambayeshi, murmushi yayi yana cewa
"Am no fool...I don't goto woman unprotected...", Ameera shuru tayi ya jawota jikinshi
" baby I will never cheat on you... " yafada yana reassuring dinta, Ahankali tace
"What if you cheat on me?... Ance duk Wanda ya saba da abu baya iya barin shi lokaci guda...am scared?." Tafada kaman zatayi kuka, bakinshi ya kai saitin nata
"If I ever cheat on you...I should wallo in pain and penury... Allah should not forgive me all my sins...baby I can't cheat on you because you gave me a second Chance... Ba kowacce mace zata iya bani second Chance kaman yanda kika bani ba...a matsayina na mijinki ina yimaki fatan samun duk abinda kikeso duniya da lahira...."
"Ameen.." Ameera ta amsa mashi daidai lokacin da ya hada bakin su waje daya, nan ya fara kashewa Ameera jiki da yanayin wasanshi, daukanta yayi yana cewa
"is time for ishai prayer."

Ruwan wanka ya hada mata ta shiga shikuma ya shiga cikin wani dakin yayi nashi wankan ya fito da jallabiya

Salem kam tunda Khalid ya shaida mashi bayason at his wedding ya tattara daga shi har Ameera ya ajiye gefe daya yacigaba da honeymoon dinshi, lokacin resuming aikinshi yayi amma he's the boss so no case, Tawakaltu kam kullum cewa take su koma gida cis tana missing mami da yawa, ciki kam rainonshi suke kaman baa taba haihuwa a duniya ba sai a Kansu, tawa ta fara sabawa da jaraban Salem don har cewa take babu wani matsalan drug daya sha kilan haka nature dinshi yake, kuma bai lalata cikin ba, yau aka daura auren Khalid da Ameera don haka ya fadawa Tawakaltu su fara shopping zuwa gida murna wurin ta baa magana cos she's tired of abroad gida kawai.
Kallon shi tayi
"Sugar zaa gane ina da ciki?..." Ta tambayeshi tana kallon kanta, Dariya Salem yayi yana biting lips dinshi,
"Babu mai ganewa Sai Mara ido..." Hararanshi tayi
"Ai cikin bai fitoba..." "Ko bai fitoba baki ganin yanda boobs dinki suke?... Ai kuma ansan we are matured enough..." Yafada mata,
"Ba dadi duk ansan abinda mu keyi..."
"You are funny... Yanzu

Please Login or Register in order to submit comment