Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan yarinyar kaman buhu gwara rashin aurenta, wanan shirmen za’a bama Ya Imran a matsayin mata ai wlh ancuceshi haba mana” Zainab tace “mugun an cuceshi ma bakiga ko kallo bata isheshi ba, yarinya banda haske babu abinda ya ceceta sai shegen kiba, taga shayi jikinta har rawa yake sabida son abinci” Matar Ibro ne dake wajen tace “wlh irin kibar yarintan nan ne, nima akwai kanwata Ummie haka tun tana karama takeda irin wannan kiban kaman ana hurata tashi daya kuma ta zazzage kiban tass kaman ba itaba itama zata rame ne, kwanan nan ma tunda duk damuwa yamata yawa” cikeda kulewa Sajida tace “ba wannan ake magana ba kekuma Matar Ibro mu bama sonta amatsayin Matar Ya Imran ne, mezaiyi da yarinyar da Kausar ta girma wannan ba cuta bane” daidai nan Kausar tasauko tace “ni wlh na tsaneta Allah ya kyauta Abee dina yay rayuwa da wacce na girma amatsayin mat…..” wani mugun kallo da Hajiya tama Kausar yasa takarasa maganan tace ”zoki saka Hijabinki kibar gidan nan kitafi makaranta nasan Hamza na mota yana jiranki” ba musu ta taho hijabi ta dauka da jakanta tafice Hajiya takalli su Sajida tace “kuzo kubarmini gida babu ruwanku da yarinyar nan, babu abinda ya shafeku da ita dan haka ku kiyayeta, bansonjin wani yakara maganan ta agidan nan, ban yarda kuci zalinta ko zarafinta ba, babu ruwanku tsakaninta da mijinta Imrana shine mai ita shine mai iko da ita, koni ba zamana takeba zaman mijinta take agidan nan, koba komi I expect dukanku ku girmamata amatsayinta na Matar yayanku dan haka ku kiyaye” duk shiru sukayi Hajiya tamike tawuce dakintaEPISODE 2️⃣1️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Abee na zaune a office nashi wuraren 2:30 aka tura kofan office dinshi batare da anyi knocking ba aka shigo dago kanshi yayi kallo daya yama Musty dake sanye da manyan kaya yana kalllonshi yana wani makirin murmushi yadauke kai yacigaba da abinda yakeyi, maida kofan Musty yayi yarufe yakaraso gaban table yace “Ango Ango kai kaga wani glowing dakakeyi ne irin na amarcin nan” dan dariya yayi ganin ko kallonshi Abee baiyiba Musty yace “no bama wannan ba tell me everything about the first night” wani mugun kallo da Abee yamai yasa yawani kalan kyalkyace da dariya yace “inda kallo na kisa da yanzu idanunka sun kasheni yafi sau dari” dauke kanshi Abee yayi yacigaba da duba papers din dake hannunshi yace “idan abinda yakawoka wajena kayi kenan kabarmin office please” hadiye dariyan Musty yayi yakalli Abee yace “to ka ijiye takardun ka kallen mana muyi magana” dan ijiyan zuciya Abee ya sauke ya ijiye takardun ahankali yakalleshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda tsokana Musty yace “yaushe zaka komarda Amarya gidanka? Kasan gidan Hajiya bazai barka kai amarci da kyau bako”? Akufule Abee yatashi pappers din yashiga tattarewa yabar wajen yakoma kan lumtsetsen couch na office din yazauna ahankali yacigaba da abinda yakeyi anatse shikuma Musty yana zaune inda yake yana kallonshi yakai kusan 10min sannan yatashi shima yazo yazauna kusadashi batare da Abee yakalleshi ba yace “zan barmaka office din gabaki daya fa Mustafa” murmushi Abee yayi yace “nasan zaka iya, all jokes apart magana nazo muyi Imran look at me” yanda yay sounding serious yasa Abee yadago idanuwanshi ahankali yakalleshi alamun ina jinka. Ahankali Musty yace “Nasanka to be someone da kana taimako kana tsayama wayanda bama kasansu ba kabi musu hakkinsu ka kwace yancinsu, yaran dakai sponsoring education nasu bansan iya adadinsu ba saisa yauma is still on that matter nakeso nida kai muyi maganan fahimta best friend” shiru Abee yayi still yana kallonshi anatse Musty yace “I know bakason auren nan and you don’t consider this girl your wife” daukekai Abee yayi hakan yasa dasauri Musty yace “hear me out mana Imran bawai inaso nace you should consider her matarka bane wlh ko daya I accept that take as long as u want kafin kai accepting nata kokarkayi accepting nata ni duk dayane awurina but as your friend reminder na musulunci nazo namaka” shiru Musty yakarayi sannan yakalli Abee yace “I know you better than anyone nasan yanda kake idan bakason abu yanda kake wulakanta abin, banso kama dat small innocent girl that kind of treatment Imran, bance kai accepting nataba as your wife but inaso ya zamto ka kiyaye hakkokinta na musulunci, lafiya, ci, sha, sutura and respect, duk kabata kaga idan ka wulakanta yarinyar nan and neglect her mutanen gidanku kap haka zasu mata suma, remember bata tareda dan uwanta ko daya, remember kaman yanda su Kausar basuda mama itama batadashi su Kausar sunma fita gata in the sense sunsan mahaifiyarsu banda haka kaga ga all your sisters and family sun taso cikinsu itako has only her grandma! Just grandma, inaso kajata ajiki be nice to her please Imran, saikuma second abu dazan fadamaka is school idan all this issue yakara sanyi saika nemi wani good school kasata since school datake sun koreta saita fara wani sabo mai kyau kaji Imran that’s the only abu da dama zan maka magana akai kaji”? Dan dauke kai Abee yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma chan yace “naji” murmushi Musty yayi yace “to hurry ka karasa abin nan gashichan ana kiran salla muje muyi saimu wuce gida”.
**


Koda takoma daki kayan tacire tashiga bayi tana wanke kafanta wajen dan ja yayi dan bawani konewan kirki bane towel ta daura tafito tana kallon kulan abinci da tray shayi dataga an kawo mata dabatasan waya kawoba, zama tayi tahada shayin dakanta ta shanye tass sanan tacinye duka chips da egg dake kulan ta shanye farfesun shima tass rabonta da abinci tun jiya hawa gado tayi ahankali sai bacci koda Anty Binta tashigo ganinta kwance kan gado da towel yasa ta murmushi ta kwashe kayan abincin tafita, wajajen azahar ta tashi tashiga bayi da ruwan sanyin still takara wanka tafito tana atishawa hijabi tasa tai salla sannan tazauna kawai tai shiruu tana kallon dakin, duniyan kawai yamata ba dadi, komi ya tsayamata chak, gidan yamata wani kala kawai sai hawaye sosai tayi kuka jin ana taba kofanta ana magana yasa tashare hawayenta da gudu, Anty Binta ne tashigo tareda wata mata kallo daya Anty Binta tamata tagane tai kuka amman tai kaman bata saniba tace “anzo aunaki tashi to” tashi tayi ba musu matan ta aunata tsaf sannan suka fice itada Anty Binta chan saiga abinci wata Yar aiki takawo mata dauke kai tayi wasu hawayen sun sake zubomata that means bara’akaita gidansu ba kenan, tsanan abincin taji tayi jin ana kiran la’asar yasa tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla, jin dakin yamata wani kala sotake tama danga hasken rana babu yasa ahankali ta tashi tai wajen window ta yaye labulen tareda bude window wani kalan iska ne yabuge fuskanta ahankali tasauke ijiyan zuciya tadade tsaye wajen sannan tajuyo akwatin da aka kawo mata tai wajensu tabude duka, robobin daddakkun magungunan ne daban daban da sauri ta maida tarufe dan barata shaba magungunan nan da badadi dayan tabude ganin su chocholate minti biscuits da yogurt daya cika akwatin yasa batasan lokacin datai murmushi ba tawani fashe da kukaba takifa kanta kan kafa ahankali tace “Gwagooooooo” sosai take kuka da sunan Gwaggo, chocholate guda uku ta dauka sannan tarufe akwatin tasaka wani white slippers pink dake dakin masu kyau daidai kafanta tabude kofa ahankali tafito tana mamaki dataji gidan tsit babu ko muryan yara bin ko’ina take da kallo hartakai stairs tafara sauka tana bude chocholate dinta wata Yar mata tagani afalo tana shara matan jin tafiya yasa tadago kanta dan murmushi tayi ganin Lujain tace “ina yini amarya”? Dan turobaki Lujain tayi jin ankirata da amarya takarasa saukowa ahankali tace “ina masu gidan”? Murmushi matan tayi tace “duk sun fice nan makota yau ana sunan matan Kamal” shiru Lujain tayi sokawai take tafita waje juyawa tayi tafara tafiya zuwa kofa itadai Yar aikin tacigaba da sharanta tana mamaki ina Amaryan gidan nan zata daga ita sai towel akirji babu ko hula, bude kofa ahankali Lujain tayi tana kallon babban tsakar gidansu dayaji flowers ahankali tashiga sauka dagakan dakalin tana kallon gate dababu kowa awajen wani zuciyan nacemata tawuce tabude tafice abinda ta tafi gida wani zuciyan kuma nacemata karta fita kotaje gida daga Gwaggo har Baba zasu kara dawo da itane, tafita ma mutane su ganta ayita kallonta ana kiranta Yar iska tunda yanzu duniya gabaki daya sun santa, hawaye taji sunzo mata tunawa datayi abinda yasa tamazo gidan nan in first place, karasawa tayi wani wani plastic chair dake wajen flowers na compound din ta zauna takai chocholate nata baki ta balla tana taunawa still tana kallon gate din, kaganta kaman wata aljana fatarta fari kal kaman jini zai fito idan katabata ga pink towel da slippers ajikinta she looks so adorable and very cute.



Tana nan tanacin chocholate din tana kallon gate aka bude karamin gate dasauri aka shigo mai gadi ne baima lurada itaba key gate yacire da saurinshi sannan yashiga bude gate din sai zare idanu take innocently tana kallo tanakai chocholate bakinta tana balla.
Ana bude gate din daga Abee har Musty dukansu hangota sukayi zaune kan plastic chair daga ita sai towel babu dan kwali akanta hannunta rike da 3 different chocolate data bare tana ballansu all at the same time, da sauri Musty yadauke kanshi yaciro wayanshi yana dannawa kaman baiga komiba shikuma Abee kuri yayi yana kallonta yanda tadage tana kallon wajen gate din har mikarda wuya take kaman wata jimina tanacin chocolate kaman akwai abinda ta ijiye waje, jan motan yayi ciki tabi motan da kallo batare data gane waye aciki ba dan bata iya gani mai gadi yashiga kulle gate din.
Ta glass Abee ke kallonta batare daya fito ba kozata tashi tashige ciki amman ko gezau sai kallon gate din dama tacigaba da yi tanacin chocholate dinta, dan kallo Musty yayi ganin yana danna wayanshi yasa batare daya kashe motanba yace “I need to get something for Hajiya bari na karbo prescription din mutafi” “okay” Musty ya amsashi atakaice hakan yasa Abee yabude kofa yafito tanacikin kallon gate taji karan bude kofan mota hakan yasa takalli wajen da sauri hada idanu sukayi itada Abee dake mata wani kalan kallo wani kalan faduwa gabanta yayi takasa cigaba da tauna chocholate din datakeyi takasa tashi takasa zaune takasa komi, sai kirjinta dake bugawa dum! Dum! Dum! Daidai Abee yakai gabanta batare daya kalleta ba babu alamun wasa a voice nashi yace “follow me” yay gaba tashi tayi hakanan kawai taji jikinta yafara rawa falon itama tashiga amman taga haryay stairs hakan yasa tabishi abaya agaban dakinta taga ya tsaya yay folding hannunshi akirji yajuyo yana kallonta, jitayi legs nata are shaking amman haka tadaure kanta akasa takaraso ahankali gaban dakin ta tsaya tana watsa da yatsunta cikin sanyin murya da yet zaka jishi a zafafe yace “bakida kayan sawa ne”? Girgizamai kai tayi batare data dago kanta sama ta kalleshi ba, cikeda dan zafi Abee yace “then why are you sitting outside da towel”? Dan tabe baki tayi irin na masu shirin yin kuka jin yanda yake mata magana kaman zai daketa ahankali tace “ai kaya tsungulina sukeyi, haka nake zama awajen Gwaggo naa” wani mugun kallo yamata yace “look up” ahankali gabanta na racing tadago idanunta dahar sun cika da kwalla sosai takallai, babu wasa kan kwayar idanunshi yace “this house yamiki kama da gidanku?” Girgixamai kai tayi daidai hawayen na zubowa sharrr yace “then this should be the last time dazaki daura this thing kifito waje understood”? Gyadamai kai tayi ahankali saikuma tajuya da sauri tabude kofan dakinta tashige tareda fashewa da kuka sosai tafada kan gado, yakai kusan 1min tsaye wajen yanajin karan kukanta yadanja tsaki yawuce dakinshi yarasa mesa yakemata magana with anger he’s so pissed of ne wlh.
Wanka yayi ya shirya tsaf cikin jeans da Riga yadauki wasu jersey yahada awani karamin workout bag dan yanaso yabuga kwallo bayan magrib yafito batare daya kalli kofan ba yawuce yasauka kasa..EPISODE 2️⃣2️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Wajen motanshi yayi yabude yashiga ciki yana jefa jakan daya dauko baya yatada motan Musty na kallonshi baicemai komiba saidan murmushi dayayi tareda gyara zamanshi, ganin ba hanyar pharmacy sukayi ba sai barrack dasukayi zuwa filin kwallo yasa Musty kawai murmushi yace “maganin Hajiya fa” changing room Abee yawuce batare daya amsashiba Musty yabishi abaya suka shiga shidayake Musty nada kayan chanzawa a locker shi na changing room shiryawa sukayi suka fito suka shiga field sosai suke buga kwallo team na Abee daban nasu Musty daban Abee saicin kwallon yake kana gani kasan ya iya kwallo sosai ya kware, saida aka fara kiran sallan magrib sannan suka tashi wanka sukayi suka maida kayansu sannan suka wuce mosque.



Saida akayi isha’i sannan yadawo gidan kashe mota yayi yafito yana magana da waya akan kunnenshi, yashiga falo anan ma yake gani suma basu dade da shigowa ba, samin waje yayi yazauna yakarashe wayan dayakeyi sannan ya amsa gaisuwan kannenshi daidai nan Hajiya tafito daga dakinta da charbi a hannunta tace “waini tunda nashigo banga Lujain ba, ke Kausar tashi kije ki kiramini ita nasata a idanu” tashi Kausar tayi ahankali tawuce sama, Hajiya takalli Abee tace “dazu fa kaman nace itama ta shirya tabimu sunan saikuma dai na bari dan bangaya maka ba” shiru Abee yayi baice komiba dan baimaso anamai magananta daidai nan Kausar na saukowa tace “tana wanka Hajiya” amman nafada mata daidainan Anty Binta takawoma Abee shayi zubamai tayi a mug tabashi karba yayi ahankali tace “Yaya nakawo maka dinner”? Girgixa mata kai yayi yace “no” saida ya shanye shayin tass sannan yatashi yace “Hajiya bari naje daki” “to Imrana Allah bamu alkhairi” wucewa yayi yahau stairs yayi sama yana gab da karasawa gaban dakin Lujain Lujain tabude kofan tadakinta tafito tana sanye dawani doguwan riga black tana rawa rawan sanyi dan bala’in sanyi takeji gashin kanta ya dan hargitse ga lema leman ruwa tagaban gashin, juyowa tayi bayan ta maida kofan tarufe karaf suka hada idanu da Abee dake tahowa yana tafiya one one kaman wani sarkin kasa, wani kalan mugun faduwa gabanta yayi dawani kalan sauri har hannunta na rawa tabude kofan dakin takoma cikin dakin dasauri tareda maida kofan tarufe daidai wani atishawa na zuwan mata tayishi, bin kofar dakin nata Abee yayi da kallo yawuce yashiga corridor yabude dakinshi yashiga.


Ahankali tazauna kan gado tai shiru tadade zaune ahaka saikuma ta tashi tacire rigan tadauko towel tadaura tasake dawowa ta zauna bakin gado tasakeyin shiru tanajin wani kalan yunwa, wani kalan kwanciya tayi kaman marainiya tana kallon kofa bude kofan nata akayi aka shigo saida tadan firgita ganin Anty Binta ne yasa dasauri ta tashi Anty Binta tace “kince ma Baba baki kara zama da towel amman kinata zaman ko” sauke kanta tayi ahankali kasa tana wasa da yatsanta batare datace komi ba, Anty Binta takaraso gaban gadon tace “Hajiya na kiranki mesa bakizo”? Dago kanta tayi ahankali takalli Anty Binta saikuma takalli kofan dakin takasa cewa komi, kallon kofan Anty Binta tayi itama ganin kofan take kallo saikuma ta kalleta tace “Ya Imran yahanaki fitowa”? Gyadamata kai tayi ahankali hawaye na gangarowa daga idanunta wani kalan mugun tausayi Anty Binta taji tabata hakan yasa gently tazauna bakin gadon bama tasan mezata ce ba tace “ki yakuri kinji Lujain” kaman jira Lujain take fadawa jikin Anty Binta tayi ta kankameta sai kuka, dan lunshe idanu Anty Binta tayi tabudesu zatama Hajiya magana tagayama Ya Imran yanemi makaranta yasata tun wuri kan wani abu yasami yarinyar mutane gashi babu mai kulata daga ita sai Hajiya ke kulata yanzu idan ta tafi next week yazatayi, tadade tana kuka sannan Anty Binta tace “Ya isa to” Anty Binta takai hannunta kan fuskanta tana sharemata hawayen tana mamakin taushin fuskanta da kumatunta kaman fuskan Yar jaririya, ahankali Anty Binta tace “kinajin yunwa ko”? Gyadamata kai tayi cikin kuka, murmushi Anty Binta tayi tace “to bari naje nakawo miki abinci da shayi, stop crying now konai fushi” hadiye kukan tayi tana kallon Anty Binta, murmushi Anty Binta tayi tajuya tafita daga dakin bata wani jimawa suka dawo itada Kausar daketa kumbure kumbure tadauki tray na kayan shayi itakuma Anty Binta tadauki flask guda biyu Kausar na ijiyewa ko kallonta batayiba tajuya tafita itakuma Anty Binta ta ijiye tace “to sauko kici” ahankali tasauko tana dake goge hawaye.



Zaune yake gaban desktop nashi yana wani aiki dagashi sai singlet dawani dan gajeren wando wayanshi ne yay kara hakan yasa yadauka ganin Hajiya ne yasa yakai wayan kunnenshi yana mamakin meyafaru take kiranshi.
“Ka sameni adakina Imrana” ta katse wayan, ijiye wayan yayi yatashi tareda daukan jallabiya yasaka sannan yasa slippers yafito batare daya kalli kofan dakin Lujain dayake iyajin maganan Anty Binta aciki ba tana mata fira wucewa yayi yasauka kasa Hamza da Abdallah yagani a falo suna buga video game suna ganinshi duk suka natsu dakin Hajiya yawuce da sallama yabude kofan yashiga Hajiya na zaune bakin gadonta tana kallonshi hakan yasa yakarasa ciki yazauna kan lallausan carpet na tsakar dakin ahankali yace “gani Hajiya” karasa jan charbi datakeyi tayi ta ijiye sannan takalleshi tace “Imrana” dan dago kanshi yayi yakalleta yace “na’am Hajiya” ahankali tace “I promise not to meddle with affairs naka dana matarka but I think akwai somethings that I can overlook a matsayina na babba” Hajiya tadanyi shiru saikuma tace “banson damuwa yama Yar karaman yarinyar nan yawa Imran, kaiba kulata kake ba kannenka ma haka, Binta ne kawai ke kula da yarinyan nan agidan nan nikuma baran iyaba dan kafafuna ba barina zasuyi ina hawa saman nan ina saukowa kullum ba” Hajiya takarayin shiru sannan tace “inaso gobe kafin katafi aiki ka dauki yarinyar nan ka kaita makaranta mai kyau kasata, islamiyya kuma zaka sata wanda su Kausar ke zuwa asabar da lahadi, amman dai gobe yarinyar nan tafara makaranta kaga karatu nata wuce ta, tunda bawai wani abu take agidan ba banda zaman kadaici da kuka dan haka ka kaita kasata a makaranta mai kyau kaji ko Imrana” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” Hajiya tabishi da kallo tace “tashi katafi to Allah bamu alkhairi” ahankali yace “Ameen” yatashi yafita daga dakin tareda maida mata da kofan yarufe, sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”? Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….” wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.EPISODE 2️⃣3️⃣



Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado, drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta, kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume tsamtsam.


Karfe uku daidai kaman wata mayya tabude idanunta sabida azababben yunwan datakeji kaman wacce ta kwanta bataci abinci ba tsabagen yanda tasaba cin abinci tsakar dare, ga kanta dake wani kalan sarawa hancinta taji yatoshe da majina hakan yasa dabaki take numfashi ma, ahankali tabi dakin da kallo dan wutan dakin a kunne yake, saukowa tayi daga gadon dasauri zuwa wajen kulolin dake dakin tashiga budewa amman babu komi cikinsu dan tas tacinye komi jiya da daddare, mikewa tayi tsaye tana kallon kofan dakin gabanta na faduwa saikuma ahankali tai wajen kofan gabanta nawani kalan mugun faduwa bude kofan dakin tayi kadan ta leka wutan corridor a kunne hakan yasa tafito da sauri tana gyara daurin towel din kirjinta kanta ba dan kwali, waigawa tayi takalli falon saman gabaki daya babu kowa ko’ina tsit, tafiya tafara ahankali tana taba cikinta da har wani ciwo ciwo yake mata yanadan kugi sabida yunwa stairs tayi tafara sauka tana kallon falon da wutanshi akashe yake gabanta nawani kalan fadi har hadiye yawu take tana sauke ijiyan zuciya takarasa sauka tana tafiya sadaf sadaf kaman wacce zatai sata tayi dining area dayake akwai dan haske dake haskowa daga wutan falon sama, ahankali kaman mai sata tashiga bubbude warmers na abinci dake kan dinning table din tana dubawa ganin akwai naman kaza soyayye dayawa dakuma rice a warmers din yasa tajuyo ahankali zata dauki plate daka cikin dankin wankakkun plate din dake kan dinning table din, mutum tagani tsaye abayanta yay folding hannunshi akirji kaman gunki, wani kalan zaro idanu tayi tawani kalan bude baki zata kwala ihu danta bala’in tsorata cikin zafin nama Abee yawani kalan fizgota tawani fado jikinshi taredakai hannunshi kan bakinta yarufe gam dan yasan tana ihu Hajiya zata farka dan batada nauyin bacci ko kadan tafito tagansu anan and that’s the last thing he needs now, cikin wani kalan low voice kaman mai whispering yace “don’t you dare scream” wani kalan zaro manyan cat eyes dinta take tana kallon fuskanshi dadan haske kadan din dake wajen wanda yazo daga falon sama jikinta ko’ina rawa yake jin gabaki dayan jikinta na manne danashi banda fuskanta dake facing nashi takasa kwace kanta gashi yataushe mata baki kamshin dayake narawa ni ratsa mata hanci, wani kalan kallon kwayan idanunta data zaro yake dudda the place is dark amman harwani kyalli suke, yanda yake kallonta batare daya zare hannunshi daga bakinta ba yasa taji wani kalan natsuwa nashiganta ahankali jikinta yadaina rawa hakan yasa tasaukar da idanunta kasa ahankali danta kasa jure idanunshi akanta, kaman wanda yatuna wani abu zare hannunshi yayi dagakan bakinta dasauri tareda tureta daga jikinshi tangal tangal tayi zata fadi tabuge da table kaman wacce batada stamina dasauri yakama hannunta yarike hakan yasa bata bugeba adan kufule yace “what are you doing here”? Dan kallonshi tayi adan tsorace akuma hankali cikeda sigan shagwaba tace “I am hungryyyy” tai maganan tana kokarin kwace hannunta daya kama dayasa taji hannun yamata wani iri, sakin hannun yayi shima dasauri strictly yace “go back to ur room” kwabe kwabe tayi da fuska kaman zatai kuka saikuma tawuce dasauri batare datace komiba takoma sama kanta na bugawa sosai, shiga dakin tayi batare data kulle kofanba dan tsoro takeji takoma gado tazauna tana dafe kanta dakemata ciwo

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment