Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dadi sukedashi ba, wani black flat takalmi ta zura kafafunta aciki dan yatsun kafanta sukai wani kalan kyau aciki sosai sannan tadauki jakan tafito tana kallon dakin dabata gyaraba dudda bawani datti sauka tayi kasa Hajiya ne kawai a falo sai Kausar dasu Aneesarh da yaran Ibro da Baban su yakawosu yanzun nan yafice, ganin Lujain yasa Hajiya tace “zonan Lujain karna karajin kince barakici abincin agidan nan ba kina jina, ke bakisan kiba rahama bace jibeki kaman asace agudu kina nema ki lalata kanki dawani rama, Allah shiya hallito sirara shikuma ya hallito masu kiba to akanme kikeso kice ke ga wanda kikeso? Kada nakarajin kinyi irin abinda kikayi jiya kinji” gyadama Hajiya kai tayi ahankali kanta akasa tace “baran karaba Hajiya kiyakuri” wani kalan murmushi Hajiya tayi tace “nayi yanzu jeki debo abincin ki kizo nan kici Hamza zai kaiku hadda mijin naki yafita ni banmasan inda yaje yau asabar da sassafen nan ba Imran dabai cika fita weekends ana kiranshi awaya yafice, tafi hado breakfast naki kizo” tashi tayi ahankali tawuce kitchen babu kowa a kitchen din, blending fruits tayi kaman jiya ta shanye a kitchen din tana bata fuska sannan tahada tea batasa madara ba ta debi kwai tafito kin zuwa falon tayi tazauna a dinning ta cinye tass sannan ta tashi takai komi kitchen saida ta wanke sannan tafito Hajiya tace “tashi Kausar kutafi Hamza na tsakar gida” tashi Kausar da itama ke sanye da hijabi tayi tadauki jakanta tai gaba Lujain tabita abaya tace “muntafi Hajiya” murmushi Hajiya tayi tace “adawo lpy” bude kofan tayi ahankali tafita daidai lokacin wani jeep na benz na shigowa cikin gidan motan tabi da kallo daga ita har Kausar suna sauka daga dakali, parking motan yayi bude gaba akayi aka fito Abee ne yana sanye da jean da wani t-shirt fari mai v neck daya kamashi sosai chest dinshi yafito broadly, kafanshi sanye da crocs black, kofan baya yabude ahankali Gwaggo tasauko daga motan tana wani kalan washe baki tana gyara dankwalin kanta dake neman zamiyewa hannunta rike dawata Yar purse da akayita da yadin atampan jikinta takalli Lujain dake kallonta saikuma ta taba Abee tace “jibin mini sha sha shan yarinyar chan taganni kuma ta tsaya sangangan kaman gunki tana kallona uwa bata sanni ba” wani kalan murmushi Lujain tayi jin muryan Gwaggo batasan lokacin data wani kalan kwasa da gudu ba tana zuwa wajen wani kalan mugun tsalle tayi ta rungume Gwaggo tana wani kalan dariya da bala’in murna. “Oyoyoooo Gwaggooo na”.EPISODE 3️⃣5️⃣


Exquisite world collections

Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa ko ina kike ni kuma Ina Abuja.

Wannan shine instagram handle dina.

I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73

wa.me/+2348108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.

Ciro wata Yar katuwan jakan Gwaggo Abee yayi daga motan tareda maida kofan yarufe yadan saci kallon fuskan Lujain, today is the first time daya fara ganin all set na cute white short teeth nata duka sabida how happy she is ga dimples dinta dake wani kalan lotsawa kaman ana operating nasu da remote, ta kankame Gwaggo gamgam tareda lumshe idanu kaman wani zai kwace mata ita, dan dauke kai yayi tareda gyaran murya hakan yasa Gwaggo dake murna sosai ta tureta tace “cikani Lulu mun tarema mijinki hanya” sakinta tayi ahankali tana komawa gefenta batare data kalli Abee ba daidai lokacin Hamza da Kausar sun karaso wajen cikeda girmamawa Hamza yace “ina kwana Gwaggo” washe baki Gwaggo tayi tace “kaga yaro mai tarbiya ba irin nawa jikokin ba basu rusunawa idan zasu gaidani” ahankali itama Kausar tadan rusuna tace “ina kwana Gwaggo” wani kalan washe baki Gwaggo tayi tace “ana ganin kwayar idanunki anga na Babanki yaya sunanki yammata” ahankali Kausar tace “Kausar sunana” Gwaggo tace “Masha Allah Kausar ina zaku haka keda Lulu kukaci hijabia kaman matan limamai” murmushi tadanyi ganin Gwaggo is so lively tace “Hadda zamu” dasauri Lujain amugun shagwabe tana kara kama hannun Gwaggo tace “Gwaggo ni barani ba” ba Hamza da Kausar kadai ba har Abee saida yadan kalleta jin yanda tai magana yadauke kai dasauri, irin Gwaggonta tazo din nan mai taremata, itama Kausar dasauri tadan kalli Abee dasauri taje wajenshi hannunshi takama kaman zatai kuka tace “Abee dan Allah muhuta gobe saimuje eh Abee tunda Gwaggo tazo” dasauri Gwaggo tace “da sunana zakuyi amfani kuyi sabon Allah badaniba” saikuma tadan kalli Abee tace “adan barsu suhuta yau ko Imrana” adan kunyace yace “to Gwaggo” yana maganan yawuce rikeda jakan Gwaggo a hannunshi Kausar da Lujain sukahau tsallen dadi Hamza yace “Allah shiryeku” Gwaggo ta tabe baki tace “tayani fadi dan nan yara kiri kiri suki karatu wanda yafi na yahudun dasuke zuwa amfani, nidai ku kaini cikin gida” tai maganan tana mikama Kausar Yar purse dinta tace “rikamin naira dubu uku da dari biyu da hamsin ne aciki dake na yarda nasan baraki cimin ba amman kinga wannan” tanuna Lujain tace “kuran kudi ce” dariya daga Hamza har Kausar sukayi Lujain ta daure fuska sukai cikin gida, daga Kausar har Hamza wani kalan dadin ganin Gwaggo sukaji, wani kalan uban sallama Gwaggo ta rangada afalo Hajiya dake zaune tareda Abee ta amsa tana murmushi tace “barka da zuwa Gwaggo” cikeda farinciki Gwaggo tace “nasameku lafiya ya Lula incedai bata tadaku da yunwan dare” wani kalan daure fuska Lujain tayi tasaki Gwaggo tawuce tasami waje akasa tazauna Gwahho ta kalleta tareda tabe baki tace “too danna fadi gaskiya shine zakiyi fushi dani aisai kiyi tayi” Gwaggo tai maganan tana zama akan 3 sitter daga Kausar da Hamza suka zazzauna kusada ita suna kallonta kaman sunga tV, Gwaggo tace “Hajiya kinga wannan jikan tawa fitinanniyan yarinya ce ga taurin kai da kafiya ina chan gidan dana amman ina tunanin halin dazata sakamini ku ciki” dan murmushi Hajiya tayi takalli Lujain dake kumbure kumbure tace “Lujain batada matsala bata taba daminmu ba gaskiya” dan dariya Gwaggo tayi tace “ai shine nan, bani jakata kagani Hamza” tashi yayi yadauko jakan yakawo gaban Gwaggo sauka tayi kasan carpet tashiga bude jakan dasauri Lujain dake fushi tazo wajen tace “mekika kawomini Gwaggo”? Hararanta Gwaggo tayi tace “yanzu kinga daman kulani” Gwaggo tai maganan tana ciro wani katon kwano data daka lafiyayyen yaji da bushashen nama da kayan kamshi tace “Hajiya ga yaji dakaina na dakashi kinga wayan nan gantalallun yara su Samira dazaran sunga zan fara aiki guduwa suke su labe hope ke baki kiwuya” tai maganan tana kallon Kausar dake kallonta dasauri Kausar ta girgiza mata kai tace “a’a banda kiwuya” baki Hajiya takama tace “Kausarrrr sannu da aiki” kwashewa da dariya Hamza yayi da Lujain harda kyalkyacewa Abee yadan saci kallonta yanda take kallon Kausar tana dariyan kasan tsokana ce, dan girgizakai kawai yayi yakai coffee shi baki yay sipping, Gwaggo cikeda lallashi tace “karki biyemusu ni ina ganinki nasan baki da kiwuya kin iya shan aduwa da goruba da magarya”? Dasauri Kausar ta gyada mata kai tace “eh” fito da ledojinsu Gwaggo tayi ga goruban duk an kankare jiki sunyi kyau tace “zoki debi naki kafin su wayan nan dake miki dariya” kaman Lujain zatai kuka tace “Gwaggo nifa” daga Abee har Hajiya dawowa yan kallo sukayi Gwaggo entertaining nasu kawai take agidan ana haka saiga Musty da Harun da Ibro da Anty Binta sun kawoma Lujain atampopinta da aka gama dinkawa haba dakin kachamewa yayi wawan goruba ake Musty da Harun harda Yar rige rigen dauka, sosai Musty ke lura da Abee yanda any magana da Lujain zatayi saiya kalleta kodan sabida bata taba magana da dariya irin na wanda takeyi yau ba ganin Gwaggo ta oho shi kanshi Musty kallonta kawai yake she’s so adorable and a very sweet and beautiful girl, he just wish abokinshi zaizo yarinyar nan and open up his heart da yanzun ne xaisan soyayya.


Dan yatsine fuskanta tayi jin maranta ya murda, tashi tayi ahankali Ibro yace “ina zaki ana hira mai dadi dake babu wanda yataba jin muryanki agidan nan haka” Musty yace “sai yau da Gwaggon ta kenan ba” Anty Binta tace “to kishi kuke yarinya da Gwaggonta” Gwaggo tace “ai tunda aka kawota nan gidan ku nahuta jibi yanda tai haske takara kyau ashe haka kikayi sa’an zuri’a dan Allah jibi yanda kansu yake ahade kowa nada kirki, babu yanda banyi da ubanta yakawoni nan nadubata ba yaki kunsan idan yafita sallan asuba baya kara dawowa sainai bacci sabida karnace yakaini, shinefa na kira Hadi dole nasashi yasaka mini number Imrana awaya ta nakira Samira tamini saving nasa kiramini shi, kira daya nama dan albarkan nan jiya da daddaren nan yace shikenan zaizo da safen nan ya daukoni, saiko gashi yazo aike Lulu kinyi miji” wani kalan kunya taji juyawa tayi tawuce stairs abinta tana tafiya ahankali Gwaggo kuma takara gyara zama tabude sabon chapter babu wanda baya dariya adakin nan sai Abee da kawai jinsu yake babu Uhm babu um um, Gwaggo sai zuba take ana dariya a falon harda hawaye.



Tashi ahankali Abee yayi Gwaggo tace “ina zaka Imrana” anatse yace “abu zan dauko a sama” dasauri tace “ayyooo tafi to abinka” stairs yayi Gwaggo tabishi da kallo saikuma takalli su Musty tareda rige murya kaman wacce zatai gulma tace “surukin nawa baida hayaniya kaman ku” haba mezasuyi banda dariya shi kanshi Abee dake stairs yana jinsu dan murmushi yayi yawuce abinshi Musty yace “ai Imrana Gwaggo tun muna yara haka yakeda miskilanci akwai shariya da rashin son magana” Gwaggo dake kallonsu tace “uhmmmm ba shakka” yanda tai maganan yasa suka kara kwashewa da dariya.



Karasawa sama yayi yana tafiya ahankali harya wuce kofan dakin Lujain saikuma yadawo baya ahankali ya tsaya chak gaban kofan yana sauraron sautin kukanta dayaji yakai kusan 1min tsaye awajen saikuma yasaka hannunshi ahankali yatura kofan batare daya shiga cikin dakin ba, tana tsugunne agaban bathroom na dakin da ledan pad da Kausar tabata a hannunta, dan dago kanta tayi tadan kalleshi shigowa cikin dakin yayi yana tafiya one one yakarasa inda take a tsaya akanta ahankali yace “what’s wrong with you”? Gently ta janye hannunta taboye pad din hannunta abayanta sannan takife kanta akan kafafunta murya chan kasa tace “cikina ke ciwo sosai” yana kallonta ahankali yace “stand up” girgixamai kai tayi batare data dago kanta ba, kana ganin yanda take kasan cikin bakaramin ciwo yake mata ba, juyawa yayi yafita daga dakin yanajin yanda kukanta ke karuwa yafito da wayanshi Anty Binta na zaune a falo suna dariyan Gwaggo wayanta yashiga ruri ganin Ya Imran ke kiranta yasa dasauri ta mike tsaye tareda daga wayan takai kunnen tace “Hello Yaya” anatse yace “go and check on that girl” yana maganan yana katse wayan, dasauri Anty Binta takarasa sama dakin Lujain tawuce datagani abude ganinta a tsugunne har yanzu takasa tashi tana kuka sosai yasa tai wajenta dasauri tace “Lujain menene what’s wrong” ganin pad a hannunta yasa tace “Subhanallahi maranki ciwo yakene”? Gyadamata kai tayi Anty Binta tace “tashi to ki kwanta kafin asayo miki magani” cikin wani kalan murya tace “kafana yarike ki kiramini Gwaggo na” dasauri Anty Binta tace “haka kafanki ke rikewa” Gyadamata kai tayi tana kuka, tashi Anty Binta tayi tafita dakin Abee tayi tai knocking tareda sallama, daga taciki yace “shigo” bude kofan tayi tashiga ahankali yana zaune gaban desktop dinshi, kusadashi tayi tace “Yaya she’s having MP cramps ne sosai yana rike mata kafa Ya Imran zaka kaita asibiti ne ko zaka kira Dr yamata prescribing magani asayo?” Batare daya kalleta ba yace “you can go” juyawa tayi tafita daga dakin batare data kara cewa komiba.EPISODE 3️⃣6️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Fita tayi daidai Gwaggo da Kausar data rike mata hannu na hayowa sama Gwaggo na salati tana sallallami tace “bani zaku maida kuturwa agidan nan ba, wannan bene haka haba” karasawa dakin Lujain din tayi atare dukansu ukun suka shiga dakin Gwaggo na ganin Lujain duke tace “ke kinfara ciwon cikin ne ohhh ni wannan ciwon ciki yaushe zaibar Yar nan, ina kukasa akwatinan nan nasaka miki maganin aciki, Binta da Kausar kutayani dagota ahankali kafanta yarike” da Anty Binta da Kausar ne suka dagota da kyar kwantar da ita sukai akan gado sannan Anty Binta takawo mata akwatinan Lujain din Gwaggo ta aika Kausar takawo ruwa, nan da nan Gwaggo tajika mata wasu magunguna saida sukai da gaske sannan tasha kadan Gwaggo tace “kunganta nan banga wanda yakaita laulayin ciwoba tun tana yar yarinyan ta amman tafi kowa tsanan magani” bacci ne ya kwasheta Gwaggo tamike takalli Kausar dake kallonta tace “zomuje ki kaini bayi” daga Kausar har Anty Binta dariya sukayi Kausar tanuna mata kofan bayi tace “ga bayi nan” ahankali Gwaggo takarasa tabude bayin tana kallon komi naciki saikuma tajuyo takalli Kausar tace “yoo ta ina na iya amfani da kalan wanga bayi kaman a film” kaman abinda Kausar da Anty Binta ke jira kenan dariya sukayi Kausar tashiga bayi ta gwadama Gwaggo komi sannan tafito suna duk suka fice yin salla.


Bayan anyi azahar Abee yashigo gidan sama yayi daidai Anty Binta nafitowa daga dakin Lujain dake bacci kaima Gwaggo abinci ledan magunguna yabata dasauri takarba taredayin murmushi tace “thank you Ya Imran” wucewa yayi abinshi itakuma tajuya takoma dakin Gwaggo tabama ledan tace “gashi Gwaggo mijinta yasayo mata magani” wani kalan murmushi Gwaggo tayi tasa hannu takarba tace “yayanku na kulan mini da jika da kyau Allah dai ya sakamai da alheri, idan ta tashi dakaina zan kiraki kizo kibata danni ba gane rubutun maganin asibiti nikeba” murmushi Anty Binta tayi tace “to shikenan” wucewa Anty Binta tayi tafita itakuma Gwaggo tabude kuka ta debi shinkafa da stew da soyayyun kaji dayawa tana murmushi tace “abinda ba’aci agidan ubanki kenan sai salla salla inbadai nina soyamiki” sosai taci tai kat tasha ruwa da lemu anan kasa bacci yay awon gaba da ita.


Vibration yatadata a bacci datakeji kaman a kunnenta bude idanunta tayi ahankali tana dube dube saikuma chan ta hango waya akarkashin gado nakawo haske yana vibration hannu Gwaggo tasa tace “waya manta da wayanshi adakin nan gashi sai kira ake” tashi tayi tafice rikeda wayan dake vibrating bude kofa tayi daidai Abee da dawowanshi kenan daga sallan la’asar a masallaci yahayo saman ganin Gwaggo yasa ya sunnar da kai kasa ahankali yace “ina yini Gwaggo” murmushi Gwaggo tamai itadai bakaramin kima da mutuncin shi take ganiba tace “kaga Imrana bansan ko Binta ko Kausar bane sukabar wayansu ba bacci fa nake naji giririrriii natashi shine naga waya akarkashin gado anata kira itakuma tana bacci balle nabata takawo musu gashi katayani basu bari naje nai salla tunda wayan yatadani” ahankali Abee yakarbi wayan daidai number da akai saving da Mandawari na kira Gwaggo kuma tajuya takoma daki tareda maida kofa tarufe Abee yadade yana kallon wayan harta katse daidai nan kuma yaga hoton Mandawari ajikin screensaver, yakai kusan 2min yana tsaye awajen kallon wayan yake yaji zuciyanshi nawani kalan tafarfasa dayarasa dalilli kafin ahankali yafara tafiya yawuce dakinshi, Binta IPhone 14 take amfani dashi, kannenshi da yaranahi dukan su 13 pro max garesu har Kausar Wanan ne kawai 12 agidan nan, yana shiga dakinshi ijiye wayan yayi kan desk yawuce yafada bayi.



Wuraren 5 tafarka ita kadaine adakin amman tana iyajin muryan Gwaggo anan falon sama tana zuba sai waka takema jikokin gidan su Aneesarh, gently ta tashi zaune tanajin ciwon cikin nadawo mata sabo fresh, sauka tayi dagakan gadon ahankali tawuce bayi wanka tayi da ruwa mai zafi sosai tafito daure da towel shiryawa tayi tsaf tadauki wani simple gown mai spaghetti hand anytime take period she don’t use to feel comfortable at all takurama rayuwanta yake ba kadan ba dan batason saka pant naturally, kuma batason zama da kaya, feffesa turaruka tayi tana kallon kulolin abincin dake dakin amman bakinta baya mata dadi daga kanta tayi tabi dakin da kallo idanunta ne suka sauka kan agogo 15min after 5, wani kalan zaro idanu tayi tamike tsaye dasauri tai wajen gado taleka zata ciro wayan da dazu tacire daga jaka ta tura karkashin gado amman bata gani ba, tashi tayi dasauri taje ta dayan side din gadon tana leka karkashin gadon amman bata ganiba jin anbudo kofa yasa dasauri ta dago Gwaggo ne, zaro idanu Gwaggo tayi tace “ke ciwon cikin keneman sakaki shigewa karkashin gado, zokisha magani mijinki yasayo miki kici abinci” shigowa Anty Binta tayi tace “sannu Lujain kinji Zokisha magani” girgixakai Lujain tayi tafashe da kuka tace “ni naji sauki basainasha magani ba” Gwaggo tace “hakafa take sainai da gaske yarinyar nan keshan magani, ballo maganin kigani Binta” ballo magungunan Anty Binta tayi guda hudu ne tana gani Lujain tawani kalan fashewa da kuka mikewa tsaye tayi dawani kalan gudu tabude kofan tafita daidai Abee dake waya yazo zai wuce wani kalan fadawa jikinshi tayi one two three Abee yay tangal tangal, baya Abee yayi kaman zai fadi saikuma yay sauri yay standing on his feet waya na kunnenshi still yabita da kallo yanda ta rirrikeshi ta kulle idanunta gam danta dauka fadi zatayi ana hello hello awayan da Abee yake yakasa cewa komi hakan yasa gently tadago kanta jin hello da akeyi hada idanu sukai da Abee dake mata wani mugun kallo dawani kalan sauri tafita daga jikinshi takoma baya, Anty Binta da Gwaggo dasuka fito dasauri Gwaggo tace “yauwa Imrana kaga magani take guduwan mawa haka hartanacin karo dakai gashi mugun ciwon ciki take” kallon Anty Binta dake rikeda maganin da ruwa a hannunta yayi babu alamun wasa a muryanshi yace “bata tasha” mikamata Anty Binta tayi tace “gashi” karba tayi ahankali tana wani kalan shagwababben kuka daga Abee har Gwaggo da Anty Binta kallonta suke, Anty Binta sai murmushi take dan gown din datasaka yamata wani kalan kyau shape nata yafito sosai, ruwa tasaka abaki sanan tadau daya zata saka Abee yace “drink all” gyadamai kai tayi ahankali takara sautin kukan datake Gwagho tace “aisai kiyi nagode ma Allah da yanzu inada maganin ki” watsa maganin tayi abakinta tana yunkurin amai Abee yace “don’t you dare” hadiyewa tayi tana batarai tawuce tashige dakin dasauri Abee yawuce yasauka kasa abinshi, abinci taci badawani yawaba dan bakinta badadi gabanta sai faduwa yake tarasa ta yanda zata tambayi Gwaggo wayan haka taja bakinta tayi shiru tun cikin namata ciwo harya daina.Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 3️⃣7️⃣




Bayan salla isha’i ta tashi daga kan gado tanajin dariyan Gwaggo dan turobaki tayi tarasa ganekan wajenta Gwaggo tazo ko wajen yan gidan nan tana gama bata tea yanzun nan takara fita, wanka tawuce tashiga tadade abayin tafito shiryawa tayi tsaf bayan ta shafa mai ta feffesa body spray tasaka wani rigan bacci orange yana nan kaman t-shirt a iya knees dinta kanta babu dankwali saitayi kaman wata Cinderella, sake tsugunnawa tayi taleka karkashin gadon tana kara duba wayan Mandawari but still bata ganiba, wuraren 10:30 Gwaggo tabude kofa tashigo dakin ganin yanda Lujain take daddaga filoli da bargo tana neme neme yasa Gwaggo tace “nashige su mehaka kika juyamin daki wai mekike nema haka kinbar mijinki shi kadai adakinshi ke kina nan tun dazu yatafi ya kwanta” turo baki tayi tazauna ganin bakin gadon tai tagumi ganin bataga wayan ba, karasowa dasauri Gwaggo tayi gabanta takama hannunta tareda mikarda ita tsaye tace “yo wai ke wace kalan yarinya ne Lulu iyye? Oya wuce kitafi dakin mijinki” turobaki tayi tace “ni anan nake kwana” baki Gwaggo tasaki saikuma tamata dakuwa kaman zata tsokale mata idanu da sauri ta kulle idanunta Gwaggo tace “aida kin barshi bude kiga yanda zan tsiyaye miki wayan nan idanuwan magen naki tunda bakida hankali, wuce kitafi dakin mijinki” akufule Lujain tace “ni bansan dakinshi ba Gwaggo kumani ki kyaleni” hararanta Gwaggo tayi kawai ta finciki hannunta tayi waje da ita tana masifa tace “da girmana billahillazi barakisa nayi abun kunya ba nazo gidanku inaji ina gani kizonan ki kwana dani barakije ki kwana da mijinki ba” duk yanda Lujain ke turjewa kin sakinta Gwaggo tayi har gaban dakin Abee kai tsaye Gwaggo tabude dakin tareda wurgata ciki itama tana shigowa Abee dake zaune gaban study yadago kanshi yakallesu yanda Lujain ke makema Gwaggo kafada alamun barata zauna anan ba Gwaggo ta washe baki tana kallon Abee tace “Imrana zan lallasa matar nan naka akanme sabida taganni barata kwana dakin mijinta ba sai wajena, kibiyoni kiga abinda zan miki” Gwaggo tawuce tafita tareda rufomusu kofan tsayawa wajen tayi chak kanta akasa hawaye ya gangaro daga idanunta takai hannayenta tanajan riganta kasa she’s so uncomfortable, Abee cigaba da abinda yakeyi yayi batare daya kara bata second look ba, gajiya tayi da tsayuwa ganin kafafunta na neman rikewa ta tsugunna ahankali akasa saikuma tazauna awajen kaman marainiya tarasa abinda kemata dadi, wuraren 11 tafara gyangyadi awajen.


12 daidai Abee yagama aikin dayakeyi tass yakashe computer sannan yajuyo ahankali yadaura idanunshi akanta gabaki daya atakure take tana gyangyadi kanta na lilo awahale. “Kee!” Wani kalan mugun firgita tayi tabude idanunta dasauri tareda mikewa tsaye tana kallon Abee awani kalan tsorace, mikewa tsaye yayi ahankali tareda zuba hannayenshi acikin aljihun wandon dake jikinshi yafara tafiya yana tahowa inda take, batasan mesaba wani kalan faduwa gabanta yashigayi yawani kalan cika mata idanu yamata mugun kwarjini kasa jure kallon dayake mata tayi dawani kalan sauri tasauke kanta kasa, karasowa yayi gabanta ya tsaya chak hannunshi zube a aljihu yana wani kalan kallonta, tunda take bata tabaganin mutumin dayamata rumfa kaman yanda Abee yamata ba ganin yanda ya tsaya daf da ita ko Baba baya mata rumfa haka, hakanan jikawai tayi kafafunta sun kasa daukanta, dukewa tayi awajen dasauri tana wasa da yatsunta, kallonta yayi cikin kakkausar murya yace “stand up!” Babu musu ta mike tsaye kirjinta nawani kalan bugawa babu kakkautawa bata tabajin kalan faduwan gaba datakeji ayanzu ba wani kalan zati da kwarjini Abee yakedashi da ita kanta bazata iya bayani ba, ganin yanda takasa dago idanunta takalleshi yasa strictly yace “look into my eyes!” Dago idanunta tayi tadaura akan nashi kasa cikakkun 3secs tayi ganin kalan kallon dayake mata zata sauke idanubta kasa azafafe yace “don’t you dare!” kafeta yayi da idanu yana tura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan Mandawari tareda nunamata wani kalan ijiyan zuciya tasauke saida yaji saukan numfashin akan fuskanshi gashi ya tsareta da idanu bayako kyaftawa daburcewa tayi daburcewan dabata tabayiba tunda tazo duniya kawai fashewa tayi da kuka, yatsanshi yakai kan lips nashi hakan yasa tawani kalan hadiye kukan tass, anatse yace “kuka nace kimini”? Girgixamai kai tayi tanawani kalan sauke ijiyan zuciya gwanin ban tausayi, ganin yanda take numfashi kaman zata shide yasa ya sassauta murya ahankali Yace “what did I say?” Adaburce tace “kace wayan waye wannan?” Tsareta da idanu yayi alamun yana jiran amsa, lips dinta har rawa suke kaman an jonamata electric shock tace “Maa…….Man…….d…..wari yab……b……bani” tafada dukta burkice, wani irin kallo dayamata yasa taji cikinta ya murda batasan lokacin datace “a school din nan yakawomini” wani irin kallo Abee yamata yace “ina jinki” kuka ne a muryanta sosai amman yahanata yi in that crying tone tace “ina aji security guy yazo yace Yayana nakirana I thought kaine naje naga shine, he asked me yanda akai auren mu, saiya bani wayan yace zai kirani and he’s inviting me to his welcoming party, da……daz….zu ma yaaaaa…..kir……rani” Abee jiyayi kaman ta watsamai garwashin wuta azuciyanshi, nunata yayi da yatsa yace “listen here girl babu

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment