Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali, bakaramin kyau yayi ba saida kana kallon kwayar idanunshi zakaga yadan fada sosai yarame, direct dakin Hamza yashiga bubbuga bakin gadonshi yayi Hamza yabude idanu ahankali ganin Ya Imran har sake goge idanu yayi zaiyi ihu yatuna maganan Dr, “bazaka tashi bane” Abee yay maganan ahankali murmushi yayi ranshi fess yatashi da sauri yace “natashi Yaya Imran” ficewa Abee yayi daga dakin yashiga dakin Abdallah dake bacci Abdallah daya bude ido yaga mahaifinshi saura kadan yafada jikinshi yadaure baiyiba yatashi yawuce bayi yana murmushi kaman anmai kyautan dream car nashi c300, dakin Kausar yawuce ya kunna wuta yana kallon yanda ta kudundune abargo dakinta kaman fridge AC yafara kashewa sannan yabubbuga gadon yana karbe bargon hakan yasa tabude idanunta ganin Abee dawani kalan sauri ta mike tsaye daga gadon kawai tafada jikinshi dan lumshe ido Abee yayi yabubbuga bayanta, sakinshi tayi tana murmushi tace “Abee sorry na rungumeka banyi wanka ba mafarki nayi na rungumeka saisa ina ganinka nayi” hancinta yaja yace “talkative” washe mai baki tayi yajuya yafice daga dakin kap yatada sister nashi duk wanda yaganshi saikaga smile of happiness akanshi sauka kasa yayi zuwa dakin Hajiya dayaga wutan a kunne ganinshi batasan lokacin data shafe addu’an datake ba tace “zaku wuce masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “incedai wannan mayen baccin Hamza yatashi” dan murmushi yayi yace “yatashi” daidai nan daga waje Hanza yace “to natashi Hajiya kuma naji abinda kikace” murmushi yayi yafito daga dakin Hajiyan suka fice Hajiya tadaga hannu tareda godema Allah daya fito yau dakanshi.


Hi GGM, did you know just because you act different baya nufin kai mahaukaci ne, sometimes is just PTSD! Now check on your family members and share ❤️EPISODE 1️⃣6️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Wuraren 8 yashigo gidan na safe sabida yanda Baba Liman ya tsaidashi sunyi maganganu masu tsawo, da sallama yabude kofan falo yashigo ganin Musty, Harun da Abdul police a tsakar falon kan lallausan carpet suna breakfast da waina yaji man shanu da farfesu, ganinshi yasa da hannu Musty yace “zo wlh saura kadan su Abdul su cinye maka wainar ka” dan murmushi yayi ga mamakinsu tahowa yayi yazauna kusada Musty cikinsu yadauki spoon yafaracin wainar dasu babu wanda hakan baimai dadi ba, sosai yaci abincin kodan baici abinci yau kwana nawa bane oho saida yaji yakoshi sannan yatashi daga wajen dauke da mug na coffee Hajiya sai farinciki take sabida yanda taga yaci sosai, laptop Abdul yaciro daga jaka yakunna yaduba wani abu saikuma yarufe yatashi zuwa gaban TV yace “BBC sun fara sanarwan kuyi shiru muji” BBC suna sanarwa cewa wani ma’aikaccen company shi yahadamai wannan shairin sabida bai bashi miliyan dari ba dakuma takardun company tareda saka hotonshi a tashin kan cewa duk wanda yaganshi hukuma na neman yaron, saikuma nabiyu Alhaji Imran mijin yarinya da ake cewa yay fasikanci da itane ga shaidanan daga iyayensu nan aka fara nuno su Baba dasu Hajiya suna cewa ma’aurata ne, sannan video edit ne su kansu tashar BBC sun tabbatar da hakan sabida ma’aikatansu dasuka tabbatar dahakan, saikuma na karshe suna kirada Al unmma sudaina yada karya idan kunne yaji gangan jiki ya tsira shikuma wannan gayen duk inda yashiga hukuma zasu bishi har wajen akamoshi” adaidai nan news din yakare, yan dakin kowa yashiga cewa Alhamdulillah Alhamdulillah, kurban shayin Abee yayi ahankali su Musty suka shiga janshi da hira sai wajajen 11 yatashi dan yaje ya kwanta, sama yawuce ganin Anty Binta nafitowa daga wani dakin da dagashi sai corridor shiga dakinshi rikeda kaskon turaren wuta bamata lurada shi ba saida tajuyo ganinshi yasa tace “Yaya ina kwana” Gyadamata kai yayi batare daya amsa ba hakan yasa tawuce ahankali yakarasa gaban dakin harzai wuce saikuma yadawo kaman baiso yamika hannunshi yabude kofar dakin, gidansu nada bala’in kyau bana wasaba but dudda haka dakin nan standout agidan gabaki daya yakai kusan 2min tsaye gaban dakin yana kallon cikin dakin batare daya shiga ciki ba saikuma yajawo kofan yamaida yarufe yawuce dakinshi.
*****

Yanda Lujain kejin jikinta ita kanta har mamaki take maganin shawaran kesata jin haka, gashi Gwaggo kullum saita mata dilka ta gurgurza mata jiki hakan yasa fatarta yawani kalan kara kyau dudda tanada fata mai kyau, jikinta yakara wani kalan lumu lumu dawani extra taushi daman yawanci masu kiba nada taushin fata barin ita da fatarta is ultra soft yanzu saiyazama wani extremely soft.
Yauma kaman kullum daga ita sai wani pink towel data daura akirji an tsife nata kalaban dake kanta da alamu ma an wanke gashin sabida yanda bakin keta uban shinning gashinta is so silky and coily ga tsayi an mata parking nashi dawani blue ribbon mai kyau anyi donut da bakin gadhin, tana zaune a tsakar gida kan tabarma kusada Gwaggo dake tankade wani gari hannunta manya manyan chocholate ne guda biyu tanaci tana kallon yanda Gwaggo ke tankaden, dan juyowa Gwaggo tayi takalleta tace “mekike kallona nan nan dazan fita babu yanda banyi dakeba muje tare kinki fita akanme zaki dinga tsoron fita, rabon dakimaje jikin gate kibude ki leka waje harna manta, nace babu abinda mutane zasu miki dazun baki tashiba BBC sun saka sanarwan an wanke ku tass to mezai faru, koma ba’a wanke kiba akwai wanda ya isa yamiki kallon banza ne ina taredake eh”? Dan turobaki tayi tace “Ya Samira fa tanunamini Gwaggo wlh muryana ne sarai ni bansan ya akayi yay tsawon nan ba” hawaye ne yacika idanunta, murya chan kasa tace “kowa yanzu har yan islamiyyan mu kallon Yar iska sukemini koni banmantaba tayaya wayanda suka kalla zasu manta wlh kaman in mut…..” buge mata baki Gwaggo tayi tace “wlh kika karasa fadin kalman nan saina dokeki wawiyar yarinya kawai asalin yan iskan duniya masu fasikancin na rayuwansu suke abinsu ba saike dabaki komiba duk kinbi kin dami kanki duk jibi yanda kika fada kalli wuyanki har yau idanunki basu koma daidai ba sabida kuka” tashi dagakan tabarman Lujain tayi da gudu tashige dakinsu tana kuka Gwaggo tabita da harara tace “aisaiki tayi bakida damuwa ne yarinya tunda inasa kudina ina sayamiki kayan kwalama ubanki nasaya miki ne” Gwaggo tai tsaki tacigaba da tankaden datakeyi Gwaggo tacigaba da masifa tace “yarinya sabida ita yau kwana nawa kenan ban samu nahuta ba amman ta isheni Alhamdulillah yau zanyi bacci nai munshari wahalar ki kuma saidai takoma kan mijinki Imrana nahuta” Gwaggo takarashe maganan ahankali sabida tunda ta tasa rigiman batason auren Gwaggo ta zuzxuba mata karya bata sake mata maganan ba ko anjima akazo kaita da ubanta zata barta ai bata isa tama Babanta wannan haukan da shirmen ba tuni zai karairayata yabama karnuka kashin itane dai data raina takema yan abubuwa, jin kukan yay yawa yasa Gwaggo takasa daurewa dan jin kukan Lujain take har cikin jinin zuciyarta kakkabe hannunta tayi tawuce dakin.


Anayin mangariba Gwaggo takirawo su Samira dukansu kuskus sukayi nadan tsawon lokaci kafin su shiga falon Gwaggon inda Lujain take a zaune tana shan tea, ganin Samira rikeda dawani babban jaka yasa Lujain ta tashi da sauri tace “Ya Samira baby yakawo miki wani abu ne”? Daure fuska Samira tayi tace “banace kidaina kiramin saurayi da sunan danake kiranki ba” dan murmushi tayi mai bala’in kyau tace “to yakuri menene amman ajakan” jakan tabata tace “Baba yace mukawo miki ki shirya bayan isha’i yana nemanki” zaro idanu tayi takalli towel din jikinta tace “Kodai yaganni da towel ne saida ya aikomin da kaya na shiga uku” tai maganan tana fizge jakan dasauri tai uwardaka zata fara farke ledan Samira tashigo tace “Malama jeki wanka” daga falo Gwaggo tai ihu tace “da ruwan maganin nan zaki wanka” wucewa bayi tayi itakuma Samira ta zauna abakin gado tana bude jakan wani simple lafaya lace ne mai kyau red and gold, sai Yar cikinta, sai set na dankunne da sarka na zirconia mai kyau shima sai flat shoe na Zara kayan dai gabaki daya akalla Baba yakashe 35k fitowa tayi tana zaro idanu tana kallon kayan tace “laaaa harda sarka da takalmi anya ni Baba yace akawo mawa kuwa saikace zanje biki” tabe baki Samira tayi tace “idan kinje ki tambayeshi nidai Malama kidauko pant da bra kisaka kizo kisa kayan” tsayawa tayi jimm kaman mai tunani Samira tace “kuma kima kanki fada kidaina daura towel akirji kina zama koda yaushe nonon ki duk zasu zube ne” dan yatsine fuska Lujain tayi tace “Ya Samira ni damuna suke wlh na tsani saka bra da pant, pant na cimini cinya” tsakani ga Allah tai maganan, Ya Samira tace “kiba yasa suke cimiki jiki, ciye ciye yamiki yawa babu namijin dazai soki idan kina haka cus yawan kiba is disgusting” tsayawa tayi tana kallon Ya Samira saikuma tajuya mata baya tasauke towel din ta daura a waist zata fara saka bra, saida tasaka bra din tajuyo tace “saisa su Ya Abida basa sona sabida inada kiba I am disgusting” tsayawa kallonta Ya Samira tayi this is the first time take ganin jikin Lujain haka dudda she’s putting on bra tanada very nice fat boobs gasu a tsaye, inda ace batada kiban nan bakaraman Cinderella za’ayi ba anan gwarama da aka mata Auren nan dan nan gaba kar samarinsu suzo suna ganinta sudinga cewa Lujain takeso, ganin yanda Ya Samira ke kallonta yasa dawani kalan sauri takai hannunta takare kirjinta tace “mehaka Ya Samira”? Tsaki Samira taja tace “Malama kizo kisa kayan nan angayamiki ke nake kallo ni I am lost in my thought ne mezan gani anan da banda shi” karasa saka pant Lujain tayi tazo Ya Samira tashiga shiryata bata mata kwalliya ko dayaba kawai lafayan tasaka da dankunne da sarkan ta tayafamata lafayan akai sai Lujain tayi kaman ba itaba ita kanta Samira saida tace “dayake duk wanda yasanki da towel yasanki inbadai kayan makaranta kika saka ba yau sai kikayi kaman ba kanwata Lujain ba, bakiyi kaman Lulu Gwaggo ba daikika fito tsaf Lujainnnn, kidinga saka kaya kinga yanda kikai kyau ne” kallon kanta Lujain tayi amadubi wani kalan murmushi tayi tace “wlh nai kyau amman kinga harsun soma damuna kayan kaman na kwabe su cizona suke” Ya Samira tace “ki kwabesu Baba ya kwabe ki” kyalkyacewa da dariya Lujain tayi sosai hakan yasa Gwaggo ta daga labulen uwar dakan taleko tace “chakulkuli kike mata ne datake dariya hak……” kasa karasa maganan Gwaggo tayi ganin yanda Lujain tayi kyau, Gwaggo batasan lokacin data yafito su Abida ba tace “kuzo kuga kanwarku” dasauri suma duk sukazo kallonta suka shigayi Lujain sai dariya take tace “nai kyau ko Gwaggo na”? Washe baki Gwaggo tayi tace “kaman hurun ini Lulu ta” tabe baki Abida tayi takoma tazauna Habiba tace “kidinga sa kaya haka jibeki saikika fito kaman mai hankali” hararanta Lujain tayi zatai magana Gwaggo tace “barta da halinta yi maza kiyi isha’i gashichan an sallame a masallaci yanzun nan Babanki zai kiraki” gyadama Gwaggo kai tayi tahau kan dadduma Gwaggo tasaki labulen taja su Abida kitchen tabasu manya manyan jakunkunan da Allah kadai yasan meta hadama Lujain aciki tace “su wuce sukai motan Baba” kaiwa sukayi suka dawo Abida tace “Baba yace kije waje” gyadamusu kai Lujain data tashi daga kan dadduma tayi zata saka slippers Gwaggo tace “saka takalmin da Baban naki Ya Aiko miki mana” sakawa tayi dan kuttubin kafanta yay kyau tayi da cute white feet nata da long long nails dinnan kaman kasa abakinka kaitasha, tana murmushi tawuce tafita lullubin lafayan na zamewa baya kyakkywan gashinta Ya bayyana gate tabude tafita, Baba tagani da Baffan ta guda biyu awajen tsaye jikin mota dukansu tsayawa kallonta sukayi ahankali tace “ina yininku” amsa mata sukayi Baba yazo gabanta ahankali yadaga hannunshi yajawo Dan kwalin lafayanta gaba sannan yakama hannunta zuwa bayan motan yasata aciki Baffa Abdullhadi yashiga maxaunin direba yusuf Ya zauna agaba Baba Ya zauna abaya kusada ita sannan aka tada motar.


Murmushi tayi takalli hanya tace “Baba ina zamu”? Anatse Baba yace “gidan mijinki zamu kaiki!”.EPISODE 1️⃣7️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Don’t miss this book for anything dan yanzu aka fara💃💃



Wani kalan faduwa da gabanta yayi saida taji kanta yasara dum, hannunta Baba yakama yace “namiki laifi da dama Lujain tun kina Yar kankanuwan ki, lokacin banda courage na kallonki ne sabida banda abinda zan kuladake, wannan auren ma bawai dan Gwaggo tadage akai yasa na yarda ba is because that’s the only right thing I can do for u, dakina karama I couldn’t do anything but yanzu I can do anything to protect you, your image, I can do anything dan inga society ya girmamaki, yakuma darajaki, nasan bakisan mutumin nan ba shima baisanki ba but abu daya dana sani shine bazai cutarmini dake ba dan shima yanada kamarki kokuma nace wacce tafiki agida, he’s a father so he can handle you, munyi bincike akanshi shaida daya bamu samu akanshi na cewa mutumin banza bane dan haka inaso ki zama mai tsoron Allah ki manta da komi kicigaba da rayuwanki amatsayin matarshi kinji” wani kalan kukane taji yana tasomata amman kotari takasa tana tsoron Baba dako gardama batayi agabanshi Baba nada dukan yara yasha dukanta dasu Samira ita kuma babu abinda take tsoro kaman duka yanzu wayau Gwaggo dama tamata dasu Ya Samira, sai alokacin hawaye yazubo mata dasauri takai hannunta ta share, amman ina bini bini saisu zubo ta share sunyi tafiya mai nisa sosan gaske sannan sukakai wani mahaukacin estate dinsu bude musu gate akayi dan ansan da zuwansu har gidansu Abee gateman yabude musu gate suka shiga yamaida gate yarufe yatafi ciki da gudu duk suna zaune cikin motan Musty yafito shida Harun duk suna sanye da manyan kaya sai Anty Binta da Matar Harun mai suna Amina sunci atampopi masu kyau sunsha aiki kana ganinsu kama hadaddun mata masu kudi, bude mota su Baba sukayi sannan Baba yasa hannu yafito da Lujain daga cikin mota, gently tasauke kafarta akan interlock na compund din wani kalan sanyi taji yashigeta kaman zata sandare dan har hanjinta taji sanyin, ahankali Baba yaja hannunta tsayawa tayi kikam dayasa Baba yajuyo yakalleta wani kalan fashewa tayi da kuka tana girgizama Baba kai dan sai yanzu ta yarda wani wuri fa yakawota tace “dan Allah Baba karka kaini wlh bansan su ba, Baba baran kara rashinji ba, ban kara zama ba dan kwali, ban kara zama da towel, ban kara aran wayan Ya Samira wlh Baba zanmabar wajen Gwaggo nadawo kwana adaki dasu Ya Samira amman dan Allah kada ka kaini ko’ina mukoma gidanmu” Shi kanshi Baba sanyi jikinshi yayi baitaba kawowa cewa Lujain ce zata fara aure acikin duka yaranshi ba, amman yadaure yay ta maza wani mugun kallo yamata yace “let’s go my friend banson shirme” kafafuwanta har girgidi suke kaman maijin fitsari tabishi kanta akasa tana kuka sosai duksu Anty Binta dasuke dan nesa dasu na kallonsu afuskansu kadai zaka gane suma jikinsu yay sanyi jin maganganun Lujain, karasawa gabansu su Baba sukayi da fara’a aka gaisa sannan sukace bismillan ku, Baba na rikeda ita suka shiga falon sake tirjewa tayi ajikin kofa ganin mutane afalon cike kowa kuma su ake kallo, Hajiya da duka yaranta, sai Abdallah Kausar da matan Ibro sai Abee dake zaune kan 3 sitter da Hajiya ke zaune kai dan anan ta umurce shi da zama yana sanye da shadda anmai dinkin jumper da hula akanshi yay wani kalan kyau kaman kasace shi kanshi na kasa dan shi kadaine adakin wanda ba kofan yake kallo ba, ganin mutane na kallonsu gashi ta turjemai yasa Baba yajata da karfi but karfin dat is not obvious shigowa Anty Binta da Amina sukayi suna ayiriririiiii kujerun dakenan empty su Baba suka zauna da Lujain na kusadashi kanta akasa tana kuka sosai, cikeda dattaku Hajiya tai murmushi tace “barkan ku da zuwa ah’ah amaryan tamu mai kuka ce kodai Alhaji kun tsunguleta a hanyan zuwa ne” dan murmushi Baba yayi yace “munsameku lafiya Hajiya” murmushi tayi tace “lafiya lau” cikeda dabara ta taba kafan Abee hakan yasa anatse yadago kanshi yakalli Baba ahankali yace “ina yini” murmushi Baba yayi shima yace “Alhamdulillah Imrana” kayan ciye ciye aka shiga cika gabansu dashi murmushi Baba yayi yace “Alhamdulillah sassannunku da aiki an gode Allah amfana” mikewa tsaye yayi ahankali sannan yakama hannun Lujain da kanta ke kasa tana kuka har lokacin yadagata yaja hannunta tana biyeda shi Dan murmushi Hajiya tayi tamike tsaye ahankali tareda komawa gefe, gently Baba yazaunar da Lujain kusada Abee kuka take ita bama gani takeba balle tasan meke faruwa hannunta da Baba kerike dashi yadauka yakama na Abee da kanshi ke kasa yasa aciki dudda kukan da Lujain take but she was able to understand hannunta baya cikin na Baba kuma, wani kalan warm serene cold taji akan hannun Abee dake shiga cikin fatar hannunta, matse hannun Abee Baba yayi kan nata hakan yasa Abee yarike hannunta gam addu’a Baba yatofa a hannayen nasu biyu da duka Ya rirrike yahada sannan yakalli fuskan Imran dake kasa ahankali yace “Imrana” gently Abee yadago idanunshi yadaura akan na Baba, ajiyan zuciya Baba yasauke dan Abee nada wani kalan kwarjini da charisma da idan yakalleka dole kagani yace “ga diyata nan Lujain nabaka ita amana, bansanka ba amman na yarda dakai zuciyata ta aminta dakai sama da yanda kake tunani, karikemini ita amana daga yanzu rayuwanta komi nata na hannunta ne banda iko akanta saikai karike amana kaji Imran” Abee jiyayi kanshi yamai nauyi ganin yanda Abee ke kallonshi amsa yake jira yasa ya gyadamai kai batare dayay magana ba dan baijin zai iya magana ba, sakesu Baba yayi yatashi yajuya yakalli Hajiya hannunshi yahade yace “Hajiya ke mahaifiyar muce nan gabaki daya ga diyata nan nakawo muku marainiya ce tun kafin a haifeta mahaifiyarta tarasu, a hannun mahaifiyata ta girma takuma tashi, Lujain goyon kakace, nasan zakuga abubuwa da dama na shirme da rashin wayau dakuma rawan kai ina rokonki da idan batai daidai ba ki tsawata mata dan kin isa ne, sannan ku dorata akan hanya mai kyau, Alhamdulillah nazo na ganku duka naji dadi hankalina ya kwanta dan Lujain tabar family tane tazo tasami even a bigger family dan haka kurikemini amana nan ta, tunda take aduniya yaune rana na farko da barata kwana tareda kakarta ba kokuma agidansu ba ko tafiya bata tabayiba, dan Allah kuyi hakuri da ita sannan ku dorata kan hanya madaidaiciya” wani kalan kuka Lujain take tafara kokarin cire hannunta daga nacikin Abee kallon hannun nata dake cikin nashi Abee yayi saikuma yadauke kai batare daya saketa ba dayaji takeson yayiba, ahankali Hajiya tace “na dauki amana in sha Allah bazamu cutar da Lujain ba namaka wannan alkawarin” murmushi Baba yayi yace “to mungode mungode bari mukoma gida saida safen ku” cikeda girmamawa Hajiya tace “Muma mungode saida safe agaida kowa da kowa” tashi su Baffa sukayi Baba yajuya shima zai tafi jin da gaske Baba tafiya zaiyi yabarta agidan nan wani kalan fizge hannunta Lujain tayi daga cikin na Abee ta tashi da gudu ta kankame Baba tabaya tana kuka sosai har gyalenta na zamewa kasa lafiyayen gashinta da aka kama da ribbon mai kyau ya bayyana cikin kuka sosai tace “Baba dan Allah dan Allah kada katafi ka barni wlh ban sansu ba, wlh kuwa” bata damu da da karfi take maganan ba tarike Baba gam cikin kuka tace “Baba wlh baran kara maka barna ba, Baba nace baran kara aran wayan Ya Samira ba saika siyamini tawa Baba dan Allah kada kabarni anan” tahowa su Baffa sukayi ganin yanda ta rirrike Baba tabaya yakasa motsi kaman zata karyashi Baffa Hadi yace “ke cikashi” cikin kuka ta makemai kafada tace “dani zaku tafi Baffa” Musty daduk suke kallon drama yay murmushi yakalli Anty Binta da Amina hakan yasa suka taho wajen Anty Amina tace “yakuri Lujain ki barsu sutafi” wani kalan ihu tabuga da saida yasa for the first time Abee yadago kanshi yadaura akanta, dudda he’s not seeing her face directly but yaga yanda goshinta har zufa yake ketowa kuka harda majina ga gashinta da aka gyara tsabagen yanda take jujjuyar da fuska abayan Baba harya hargitse babu lallashin duniya da Anty Binta da Amina basuyiba har Hajiya tasa baki ina taki sakin Baba da Baba ta kular dashi wani kalan tsawa yadaka mata Lujain! Yanda taji saukan tsawan saida ta sakeshi tai tangal tangal tama fadi akasan tiles na wajen jikinta narawa sosai tana girgizama Baba kai, kowa na falon su yake kallo jin yanda Baba yadaka mata tsawa, kaman Baba zai daketa yace “stand up go back to your sit ki zauna” juyawa tayi da sauri tana rarrafe ta tashi yanda ta tashi takoma tazauna zaka dauka mala’ikan mutuwa tagani, tahowa Baba yayi azuciye batasan lokacin datai pulling hannun Abee ta kama hannun Abee gamgam ba ta boye fuskanta akafadanshi kaman zata shide tace “Baba dan Allah kayakuri karka dokeni” yanda jikinta ke bari da yanda take numfashi kaman zata shide Abee could hear it, yanda tarike hannun Abee gam tana boye fuskanta abayanshi Musty yakalla daidai itama Anty Binta takalleshi kashe mata idanu yayi tayi murmushi Baba zaiyi magana Hajiya tace “aaaa ina ake haka Alhaji? Har gidana zakazo ka firgitamin diya sabida tayi kuka kan katafi da ita bata sanmu ba yo ai batai karyaba babu wanda tasani anan, kataba ganin inda aka rabu da amarya lafiya dama ai sai sunyi yan koke koken nan, karma kafadi abinda kakeson fadi dan nasan fada zaka mata” dan murmushi Baba yayi akunyace yace “shikenan to Hajiya saida safen ku” anatse kowa yace “Allah bamu alkhairi” fita sukayi hakan yasa ahankali tasaki hannun Abee sannan takoma gefe takifa kanta akafa tana kuka sosai tashi Abee yayi yawuce sama Hajiya tabishi da kallo tashi Kausar itama tayi tawuce fuuuu sama ahankali Hajiya tazauna kan kujeran daidai nan mai gadi yashigo dawasu jakunkuna manya guda biyu yace “Hajiya ina za’a saka wayan nan” Hamza ta kalla tace “jeka kaimata dakinta” gyadama Mamanshi kai kawai yayi yawuce sama ahankali Hajiya takai hannunta tadaura saman bayan Lujain cikeda lallashi yace “kiyakuri kowace mace saitaji irin abin nan dakikeji idan aka kawota gidan mijinta, amman zakigani nan da sati kin warware kin daina tunanin gida ko” ta tambayi su Anty Binta dake tsaye akansu sukace “hakane” murmushi Hajiya tayi tace “ku kaita dakinta Binta” Gyadamata kai Binta tayi dagata itada Amina sukayi suka wuce da ita sama Mama takalli su Sajida da Zainab tace “ku kai abinci dakinta dan ba lallai taci abinci ba” dan tabe baki sukayi saikuma suka tashi itadai Maman Aneesa na zaune tana magana da yaran tace “Aneesarh takarasa maganin ta” gyadama Hajiya kai tayi takalli Abdallah dayay shiru tace “kaikuma fa dakai shiru haka”? Dan murmushi yayi yace “bakomi ni zuwa zanyi ma na kwanta inada lectures gobe” Maman Aneesarh tace “dole abama Abdallah award din shine mai fara zuwa ya kwanta agidan nan kafin kowa” murmushi yayi yawuce abinshi.EPISODE 1️⃣8️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Zaunarda ita Anty Binta tayi akan gado itada Amina sosai take kuka tana kwabe baki kaman yanda yara ke kuka Anty Binta dake kallonta da yanda takeyi kawai fadomata maganan mijinta yadingayi a zuciya she looks so cute, cute sosai yanda takeyi gashi yanda takeda kiba da yaran kumatunta keyi yayi soo adorable kaman kasaceta kagudu she looks

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment