Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya mata yasa tadan lumshe idanu tabude tace “I mean Lujain tun safe bataci abincin kirki ba, smoothie tayi na celery wai na weight loss, yanzu ma takicin abincin da aka kaimata sai kuka take, Ya Imran kamata magana please” wani kalan kallo yamata Hajiya tace “Imrana jeka mata magana haka yara yanzu suke su kawai su gansu sun dawo kaman tsinke Allah day ya kyauta jeka mata magana” wayanshi yaciro batare daya dagokanshi ba yace “kubarta taji yunwa zataci abinci da kanta” baki Hajiya tabude zatai magana yamike tsaye yace “I have to go Hajiya”.EPISODE 3️⃣2️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Fita yayi daga dakin yawuce gym dinshi dake compound din dayake all kayanshi na workout na wajen saisa baimaje sama dan chanza suit na jikinshi ba.


Kallon Binta datai zamanta anan kusada Hajiya tayi tace “tashi kije ki kiramini yarinyar nan munaji muna gani barinta zamuyi ta kashe kanta” tashi Anty Binta tayi ahankali tawuce sama tun kafin takai wajen dakinta taga kulan abincin agaban kofanta tsugunnawa Anty Binta tayi tabude kulan ganin kotaba abincin batayi ba yasa ta murza kofan zata bude taji kofan arufe ita abinma dariya yabata tace “ohhh sabida kada asakici abinci shine kika rufe kofan ko, to Hajiya na kiranki” tashi Lujain tayi ahankali tana rike cikinta tawuce bayi dan batamaso tanajin maganan Anty Binta, maida kofan bayin tayi tarufe ta tsugunna awajen ita kanta mamaki take mahaukacin yunwa takeji bana wasaba tunda uwarta ta haifeta bata tabajin yunwa irin wanda takeji yau din nan ba, amman ita wlh saita daina cin abinci sabida ta rame Mandawari yakara sonta sosai.


Anty tadade tsaye awajen ganin taki bude kofan yasa tajuya takoma kasa Hajiya tace “ina take”? Ganin yanda Hajiya ta damu yasa tace “Hajiya karki damu zataci abincin yanzun nan” cikeda damuwa Hajiya tace “dan Allah Binta koma wajenta ki tabbata taci, hankalina bazai taba kwanciya ba ace yarinya na wajena takicin abinci awani dalili ita ba azumi ba sai bama kai yunwa, yooo ita kibar har guda nawa ke gareta bandama shirme irin na yarintar Lujain, kiba kyau ne azamanin mu idan kinada kiba ba kowani kalan mutun nema zaizo neman aurenki ba sai masu kudi sabida ansan Kinacin abinci mai kyau gidanku babu yunwa ke Yar gata ce, azamaninmu da zaran an ganki mara kiba ramammiya cewa ake gidanku da yunwa baku samun abinci kuci, ni wannan zamanin nema naga gayu ake da siranta kiga yarinya kaman zaka hure da iskan bakinka tafadi wai shine gayu, to wlh bada niba, ni baran miki karyaba Binta ranan da mahaifin Lujain yakawota nan gidan da daddare dana fara daura idanuna akanta abinda nafara cewa shine Masha Allahu yarinya bulbul da ita son kowa kin wanda yarasa akan mene takeson bata kanta, ita batasan rama bazai mata kyau ba, sotake iyayenta suganta ace bamu bata abinci yarsu dukta tsotse jesama idan bataci abinci ba kizo kifadamin dan saina saba mata daga ita har Imran da akacemai taki cin abinci yakama hanya yay gaba abinshi” ganin yanda Hajiya tabata rai yasa Anty Binta tace “a’a Hajiya ai baimakai hakaba zataci ma bari naje” Hajiya tace “kada mata shayi ki tafin mata dashi” kitchen Anty Binta tawuce tahada mata tea a babban flask tadauko a tray da cup tawuce sama gaban dakinta taje ajiye tray tayi akasa tai knocking tareda murza kofan amman har lokacin a kulle at this point Anty Binta jitayi itama ta damu sosai, bubbuga kofan tayi hakan yasa Maman Aneesarh dake daki tafito tace “Ya Binta lafiya” dan murmushi Anty Binta tayi da idanu tamata alamu data koma daki kar Hajiya taji hakan yasa takoma daki itakuma Anty Binta tawuce dakinta dan dauko waya dauka tayi tafito Hajiya dake kasa tace “taci kuwa”? Dasauri tace “eh Hajiya taci” gaban dakin Lujain taje takira number Ya Imran dan shine spare keys ke hannunshi amman har wayan ya katse bai daga ba kusan 3 miss calls tamai bai dagaba sake fitowa Maman Aneesarh tayi jin yanda Anty Binta ke knocking kofarta tazo har wajen tace “Anty Binta wai menene”? Abincin dake gaban dakin tanuna mata tace “Lujain refuse to eat she wants to loose weight kuma yunwa takeji kaman ba gobe” kallon abincin Maman Aneesarh tayi tace “harwani kiban dazata rage takedashi tanadai so tama kanta wani illan kin fadama Ya Imran” cikeda damuwa Anty Binta tace “kema kin sanshi ko kulamu baiyiba danake gayamusu” Kausar da tun dazu tadawo daga school tana bacci bude kofa tayi tafito daga bakin kofa ta tsaya tace “ni wlh dukkan hanani bacci, ku barta mana Anty Binta maybe cikin nan nata yakoma flat kaman nawa” tai maganan tana dariya dakuwa daga Anty Binta har Maman Aneesarh suka mata daidainan Abee yashigo saman kallo yabisu dashi daki Kausar tawuce dasauri Dan babu hula akanta tace “welcome Abee” wani kallo yama Maman Aneesarh da Anty Binta strictly yace “I don’t wanna see any one of you anan” sadaf sadaf kowa yawuce Abee yace “it’s time for magrib” duk dakunan su suka shiga, yace “Fateema” dasauri Anty Binta tafito tadawo har gabanshi anatse tace “na’am Yaya” strictly yace “call your husband kiwuce kitafi gidanki” dan murmushi tayi tace “to Ya Imran” wucewa yayi yashige dakinshi batare daya kalli kofar dakin Lujain ba, wanka yayi yafito ya shirya cikin wasu fararen shadda riga da wando dayawani kalan haskashi yasaka, Wandon as usual iya idon sahu rigan kuma jumper babu aiki ajiki hannun rigan yakamashi hakan yanuna murdaden hannunshi irin full nan dinnan turare ya feffesa jin an tada salla yasa yasaka slippers yafito dasauri yasauka kasa a compound yaga Hamza da Abdallah na alwala shigowansu kenan wucesu yayi yawuce yafita suma suka biyoshi abaya, sai bayan isha’i yafito daga masallacin yana tafiya ahankali Mandawari dake tsaye gaban gidanshi tunda Abee yafito daga masallaci yake kallonshi tunda yake in his life baitaba ganin mutumin da he feels so insecure about ba kaman Abee, tundaga kai har kafa yake binshi da kallo yakasa ganin makusa, gashin kanshi dana gemunshi baki sidik shida yake yaro shine ma yakeda yan furfura akai, tundaga nan kofar gidanshi yana iyajin hadadden kamshin da Abee keyi, hada idanu sukai da Abee daya kalleshi sau daya ya daukekai dasauri shima yadauke kai yana tsaki yace zaiga kaman na damu dashine, kaman daga sama yaji muryan Olusay yace “are you scared kar babe dinka tafara son mijinta danni wlh mutumin nan yafi mini kai kyau sau dubu, just look at a matured classic cool guy dan Allah ga naira, kai kaga shaddan jikinshi kakosan shaddan Oman ne wannan special edition din nan just guda 10 ne aduniya gabaki daya nidakai ba munje siya ba but bamu samuba thats what he is wearing, Mandawari a word of advice this guy no even send you so back off” dawani kalan sauri Mandawari yajuyo azuciye chakumeshi yayi hakan yasa Olusay yadaga hannuwanshi sama alamun yay surrender sannan yamai alamu da idanu kan ana kallonsu masu fitowa daga mosque sakinshi yayi yawuce cikin gidanshi yashige fuuuuu.EPISODE 3️⃣3️⃣




Afalo yasami Musty yana zaune kusada Hajiya rikeda radio nata da screw yana gyara wata Yar waya data katse ciki, dago kanshi yayi jin kamshi dakuma sallaman Abee yace “shine zaka koramin mata to ai gani nan nazo daukanta ko angaya maka nima so nake tana zama agidan dakake zaune bayan kowa yasan you are bad energy” wani kalan mugun kallo Abee yamai batare dayace komi ba, Musty yace “Hajiya kinga irin kallon dayakemini kuwa kimai magana” juyowa Hajiya tayi takalli Abee hakan yasa ya gyara fuskanshi da sauri tareda dan sosa kai yayi yasami waje ya zauna Musty yagama gyara radio tareda kunnawa radio yafara magana yace “gashi Hajiya angama” cikeda jin dadi Hajiya tace “nagode Mustafa Allah ya shimaka albarka” dariya yayi yatashi bayin falo yashiga tareda wanko hannunshi yafito kusada Abee yazauna yana kallon fuskanshi yace “how far”? Kallonshi Abee yayi shima yace “what”? Dan kallon Hajiya yayi ganin hankalinta nakan radio ta yace “about that small boy”? Dan yatsine fuska Abee yayi yace “ohh I can’t even recall his name” dan murmushi Musty yayi yafi kowa sanin halin Imran aduniyan nan this answer kadai na nufin baikarabi takan yaron ba yaron kuma bai karamai magana ba, abinci Kausar takawo musu bayan ta gaida Second Dad dan haka suke kiran Musty tawuce sama.

Wuraren 11 shida Anty Binta sukabar gidan Hajiya tuni ta shige dakinta, tashi Abee yayi yarufe kofa tareda kashe wutan falon yawuce sama abincin dake gaban dakin Lujain yabida kallo dahar lokacin ba’a tababa yawuce dakinshi wanka yasakeyi ya chanza kayanshi zuwa pajamas dark blue, coffee da aka ijiyemai adaki yabude flask din yazuba a mug yadauka ya jingina da gado tareda kaiwa baki yay sipping, drawer shi yabude yaciro novel din dayake karantawa yacigaba da karantawa yanashan coffee.


Wuraren 1 tabude idanunta daga wahalallen baccin datayi dudda wutan dakin a kunne amma wani kalan jiri jiri take gani cikinta namata wani kalan ciwo dabazata iya misiltawa ba sabida yunwa, rabonta da abinci tun chips da Anty Binta tasa taci dan kadan dasafen nan sai ruwa kawai data dingasha, kokarin tashi tayi zaune amman jitayi takasa cikinta yamata kaman gyambo takasa mikewa wani kalan fashewa tayi da kuka ahaka, kofan dakin take kallo da idanunta da key kofan data ijiye gaban madubi tana tunani yanda zata tashi taje tadauki key tabude kofa tadauko abincin bakin kofan taci, da duka dan energy daya rage mata tayi yunkurin tashi wani kalan ciwo da cikinta yamata batasan lokacin data saki wani karaba tafado kasa akife tafashe da kuka sosai…..


Gently Abee yamaida novel din hannun nashi yarufe yay dan jim yana sauraron yanda take kuka wanda kaman akunnenshi takeyi, ijiye novel din yayi akan side drawer ahankali ya yaye bargon daya rufe kafanshi dashi yasauko da kafafun kasa yasaka bedroom slippers sannan yamike tsaye yana kulle boturan gaban riganshi da kyau ahankali yayi wajen kofa, bude kofanshi yayi yafita yana tafiya a natse yafito daga corridor ya tsaya gaban dakinta taredakai hannunshi ya murza handle na kofan jin har lokacin a kulle yasa yay dan jim saikuma yajuya yakoma dakinshi wani drawer yaja da keys daban daban keciki yadauki wani key yatashi yafito gaban dakin yazo yasaka key aciki ya murza sannan yabude kofan ya tsaya chak inda yake batare daya shiga cikin dakin ba, daga ita sai wani dan pink towel data daura kanta babu dan kwali tana kwance akasa ta kife cikinta da hannunta kekai tana kuka sosai dabaima fita da kyau tsabagen yanda ta galabaita idanunta akulle, sai hawayen dake fitowa daga cikinsu kana ganinta kaga wanda yunwa ya mugun galabaitar, juyawa yayi yakoma dakinshi karamin fridge dake cikin dakinshi yabude wani goran almond milk yadauko yamaida fridge din yarufe yafito dan tsayawa yayi agaban dakinta kaman wanda ke tunanin shiga ciki saikuma yashiga ciki ahankali tareda maida kofan dakin yarufe yakarasa zuwa gabanta, gently ya tsugunna tareda ijiye goran Almond milk din agefe, hannunshi yakai ahankali zai daura akan shoulder dinta saikuma ya tsaya tareda maida hannunshi yarufe ahankali yana kallon fuskanta yace “Ke” ahankali take bude idanunta kafin tagama budesu tass tadaurasu kan Abee, jiri take gani sosai amman dudda haka tagane fuskanshi, kwayan idanunta kadai yakalla da yanda sukeyi yagane jiri take gani, with a very calm and light tone yace “sit up” girgizama mai kai tayi dawani kalan sigan shagwaba tana turo pink lips nata, cikin wata kalan murya yar karama tace “carry me” dan kallonta Abee yayi dasauri kaman wanda baisan abinda taceba, ahankali take kuka tana kara kama cikinta dake yakushinta sosai tana kallonshi da idanunta dasuka kankance sosai suke juyawa, gently yazaro hannunshi yamika mata hannun guda daya batare daya tabata ba alamun tarikeshi ta tashi zaune, hannunshi takalla that is so clean ahankali kaman wata yar karaman yarinya tadaga dayan free hannunta dabata kama cikinta dashi ba, gently takai hannun saitin hannunshi dayake bata idanunta na ganin jiri takai hannun awani kalan hankali tasaka hannunta cikin hannunshi hakan yasa soft tafin hannunta yasauka akan tafin hannunshi har cikin brain dinshi Abee yaji wani iri hakan yasa ya lumshe idanunshi kafin yabudesu ahankali yadaura kan cute chubby hand nata dake cikin nashi farcenta farare fat dogaye kaman tana wankesu da farin fenti, ahankali yadan kama hannun da kyau sannan yajawota tashi zaune tayi tawani kalan fashe da matsanancin kuka tayi tace “wayyoo cikina ciwo, Uncle zan mutu” wani kalan mugun kallo yamata baice komiba hannunshi dayan that’s free yamika yabude goran almond milk din sannan yadauka yajuyo tareda mikamata yace “karba kis……” wani kalan kawo fuskanta tayi da sauri takama hannunshi hade da goran takai bakinta tanasha dawani kalan sauri kaman irin yaran dasuka dade basuci abinci ba sunajin extreme yunwa, ahankali yabi hannunshi data rike gam da kallo tanashan milk din zuwa fuskanta gently yadaura idanunshi kan goshinta da gashin kanta suka kwanta lub lub wasu kuma sunyi coiling ga kitson da akamata kanana dasukai bala’in kyau bakin jelan gashin sun soma warwarewa da kansu sosai sabida santsi, idanunta duka biyun a lumshe sai dogayen gashin idanunta dasuka jike sharkar da ruwan hawaye, dauke idanunshi yayi daga kallonta saida ta shanye milk din tass sannan ahankali tasaki hannunshi tana komawa baya ta jinginar da bayanta da gado tana kama cikinta dataji yawani kalan daure mata fiyedana da tana lashe lips dinta dan almond milk din yamata dadi bata tabashan irin madaran ba, hannunshi Abee yakalla sannan ya ijiye goran akasa yakalleta kana ganin yanda take kasan ciwon yakaru ne yace “gobe ma you should starve yourself” hannayenta duka biyun takai kan fuskanta tafashe da kuka sosai dayasa Abee kawai ya tsaya yana kallonta yarinyar nan badai shagwaban banza ba, yunkurawa yayi zai mike tsaye dawani kalan sauri tazo gabanshi kaman zata shige cikin jikinshi dan komawa baya yayi dasauri kaman wani matsoraci yace “Ke what”? Cikin wani kalan kuka tone tace “har yanzu yunwaaaaa” dan hararanta yayi yatashi yajuya yafita daga dakin yamaida kofa yarufe tsugunnawa yayi abakin kofan ya kwashe kulan abincin da flask yawuce yasauka kasa yana tafiya ahankali, bude kulolin dinning yayi babu wani abinci daya rage hakan yasa gently yajuya yakalli kofan kitchen dinsu ahankali yabude kitchen din, rabon daya shiga kitchen dinan harya manta ko ranan a microwave na dinning yadumama abincin yakai mata, dan tsaki kadan yayi yashiga kitchen din ruwa yasa a kettle sannan yay shiru yana tunanin meya iya dafawa mezai kaimata? Idanunshi ne suka sauka akan egg, guda two yadauka yafasa saikuma kaman wanda yay tunanin wani abu yakara two again yafasa yasa pan a wuta da oil juye kwan yayi dayadan soyu yajuya sannan yakwashe a plate yakashe gas din yataho yahada mata tea mai kauri yasa a tray yadau bread yafito yawuce sama yana tafiya ahankali, bude kofan dakinta yayi ahankali tana kwance inda yabarta ganin yashigo da tray da sauri tamike tana zaro idanunta dasuka kankance tana kallon tray daya shigo dashi, karasowa gabanta yayi ya ijiye tray akasa dawani kalan sauri tadauki tea zatakai baki dasauri yace “Ke is hot” fashewa tayi da kuka sosai da abin yaso yama bashi dariya dan girgizakai kawai yayi danbaimasan mezaice ba yace “give it to me” karban mug din yayi yajuya tea tareda daukan bottle water mai sanyi dayasa akan tray yakara ruwa kadan aciki sanan yasake juyawa yadauka yabata dasauri takarba takai bakinta tafarasha, bread yabude yaciro one slice yabata sauke tea tayi daga bakinta da sauri ta ijiye akasa takarbi bread din, da spoon yadebo fried egg din yadaura mata akan bread din dasauri tai folding nasu takai bakinta ta gutsura gadai kwan da zafi amman ko gishiri babu a kwan bare Maggi, dan dago idanunta ahankali tayi takalleshi hada idanu sukayi dasauri ta maida kanta kasa tacigaba dacin bread din da kwan ahaka sannan tadau tea tasha, bread yakara daukowa yabata zai samata kwan ta girgixamai kai alamun a’a bari yayi ta karbi bread din taci, kusan 9 slice of bread ta cin ta shanye tea tass sai alokacin taji ciwon cikin yadaina sosai, half fried egg dake plate din takalla saikuma tadan kalleshi hada idanu sukayi karaf kai tsaye yace “what” dan zaro idanu tayi tareda dan turo baki kadan kaman mai tsoron fadin abinda zata fadi murya chan kasan makoshi tace “you can’t…..cook Uncle” takarashe maganan wani short smile na kubuce mata abaki dayasa dimples dinta suka wani kalan lotsa duka biyun dawani kalan sauri Abee yadauke kanshi yashiga hade komi a tray sanan yamike tsaye batare daya kalleta ba yace “is that your thank you”? Wani kalan sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “thank you” dan dago kanta tayi jin bataji any motsi ba hada ido sukayi wani mugun kallo yamata dayasa ta sauke kanta kasa dasauri yajuya yafice daga dakin, sauka yayi yana maimaita abinda tacemai wai you can’t cook uncle, children of now adays ba basu da at all, kitchen yashiga ya ijiye tray din harya juya saikuma yajuyo hannunshi yakai ahankali ya gutsuri fried egg din kadan yakai bakinshi dawani kalan sauri ya tofar sai yanzu yatuna baisa komi a kwanba kawai ya fasa ne ya soya, wani kalan kunya yaji girgiza kai kawai yayi yawuce yafita daga kitchen din yahayo sama kallon kofar dakin nata yayi yawuce yashiga dakinshi bayi yashiga dan dauro alwala dan yanzu lokacin sallan daren shine.


https://chat.whatsapp.com/DinmgBAo43r4mDZSIUvrBbExquisite world collections

Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa ko ina kike ni kuma Ina Abuja.

Wannan shine instagram handle dina.

I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73

08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.


EPISODE 3️⃣4️⃣




Wuraren 6 tabude idanunta ahankali sosai tayi mamakin yanda babu wanda yatasheta yau tashi zaune tayi ahankali tana taba cikinta dataji baya mata ciwo kuma tamike tsaye ahankali tawuce bathroom dan dauro alwala ganin small blood yasa tai brush tareda wanka tafito daure dawani towel daban zama tayi abakin gado tai shiru tana tunani tunawa datayi da wayan Mandawari yasa tasauka kasa dagudu tana leka karkashin gadon jawo wayan tayi tana dannawa ganin 6 miss calls dinshi dakuma 2 messages from him dasauri tabude messages din.


“Ke kinsan waye ni? Dan kinma samu ina kiranki shine baraki dagamin wayaba dan kina tareda wannan Baban mijin naki don’t ever call me again”
Wani kalan faduwa gabanta yayi gently tashiga second messege din.

“Wlh idan kika bari yamiki wani abu kokuma kika yaudareni Lujain saina wulakanta miki rayuwa! You belong to me Muhammad me only!”
Wani kalan faduwa gabanta yayi duk zuciyanta yamata badadi dialing number shi tashigayi daidai lokacin taji ana shirin bude kofanta dawani kalan sauri ta tura wayan karkashin cinyanta ta gyara zama tana kallon kofan daidai lokacin Kausar tashigo takalleta tace “Hajiya tace ki sauko muyi breakfast ki shirya daganan zamuje hadda” juyawa Kausar tayi zata fice dasauri Lujain tace “Kausar” juyowa Kausar tayi takalleta batare datace komiba, ahankali Lujain tace “please kibani pad bandashi da maganin ciwon ciki anjima kadan cikina zai fara ciwo” dan hararanta Kausar tayi saikuma tace “ni banda maganin ciwon ciki dan banayi” tana maganan tawuce tafita bata wani jimaba tadawo dakin dauke da pad guda biyu masu kyau dan ita kanta Lujain bata taba ganin irinsu ba bata tayi hannu tasa takarba tana murmushi tace “thank you” juyawa Kausar tayi zata fice tace “kuma kiyi sauri” tana fita tamike tsaye tareda daukan wayan taduba gani tayi yama dauki call din but ya katse sake kiranshi tayi tawuce tana shiga bayi tareda maida kofan tarufe, saida wayan yayi kaman zai katse yadauka kafin tamace wani abu yace “who do you think you are Lujain sabida kin samu mutum kaman ni na kulaki bakisan I am doing you a favor bane? Tell me what is good about you? Kene yarinya a sex tape that went viral online, kene gaki nan kaman zaki fashe, yarinya babu shape babu kyau, anhadaki da tsoho yanzu still na tsaya akanki nace zan aureki amman harkin kai matsayin ni Mandawari the biggest footballer in Nigeria na kiranki baki dagamini ba, where were you danake kiranki”? Wasu kalan hawaye ne sukazo mata sabida yanda yake mata ihu yana masifa sosai kaman zai daketa daga wayan, jin yanda tai shiru yasa abin yakara tunzurashi yace “Lujain nike miki magana ni Mandawari kikama shiru kika share? Fine dagayau bani bak……” cikin wani kalan sauri bakinta har rawa yake tace “da……..dan Allah kayakuri” wani kalan lumshe idanu yayi yanajin yanda harshenta ke rawa alamun kuka take yarasa what’s so special about this local girl da Allah yajarabeshi da sonta, idan yatuna yakirata last night bata daukaba saiyaji wani mugun kishi ya turnikeshi, dan calming muryanshi yayi kadan dan baiso yamata ihu jin tana kuka yace “kina ina jiya da daddare bayan nagayamiki zan kiraki wajen mijinki kikaje? Meya miki did he hold your hand? Touch you did he kiss you koko yanzu finally kunyi sex din da akayi accusing naku dashi ne” dasauri tashiga girgizamai kai kaman yana gabanta tace “a’a” cikin ihu k aman yasamu yarshi yace “to me yamiki! Tell me” Yanda ya daka mata tsawa saida ta janye wayan daga kunnenta dan kaman zai fasa mata kunne, maida wayan kunnenta tayi ahankali tace “wlh babu abinda yamini jiya banida lafiya ne” ahankali yace “are you sure”? Gyadamai kai tayi tace “eh” dan sassauta muryanshi yayi yace “meya sami baby na what’s wrong with you”? Dan murmushi tayi jin yanda yakirata da baby ahankali tace “cikina ke ciwo I was so hungry” dan shiru yayi saikuma chan yace “waike akwai abinda kika sani sama da abinci kuwa aduniyan nan? Sabida nahana ki kada kici abinci shine zaki bingile da ciwon ciki, hope bakici abincin ba haka kika kwana”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” dan murmushi yayi yace “good baby, that’s why I love you” wani kalan murmushi tayi mai dan sauti yace “tom yanzu kije ki nika fruits kisha idan akwai salad zaki iya ci, daga yanzu salad su yayan ganye da yayan bishiya ne abincin ki kinji” gyadamai kai tayi tace “tom” ahankali yace “I want to see you today, 4 ne za’a fara event dina a city conference center zan turamiki address din, makesure you look peng okay” gyadamai kai tayi saikuma kaman mai tsoron magana tace “mutane zasu ganni suganene nice ta video” murmushi yamata yace “babu wanda zai ganki you are coming to see me akwai wanda zaizo yadaukeki yakawoki har private room danake ciki okay” gyadamai kai tayi tace “to” murmushi yayi yace “now go and have breakfast Mandawari’s baby, I love you Lujain” wani kalan sanyi taji azuciyanta tadade tana mafarkin rannan da Mandawari zaice mata he loves jitayi kaman zata zauce, wani kalan murmushi tayi zatai magana taji ya katse wayan fitowa tayi daga bayin tawuce tadauki wani handbag cikin wayanda Anty Binta tasaya mata tasa wayan aciki sannan ta shirya tsaf cikin wani Riga da skirt na kanti milk skirt din yawani kalan fito da katon hips nata, inba kasan Lujain ba kaganta zaka dauka all this yaran nan dasuka kai 24/25 ne sabida yanda takeda girman jiki da gabobi saidai idan tayi magana kokuma ka kalli kwayan idanunta dan akwaita da zakin murya ga muryan Yar siriruwa, wani milk hijab sabo fil dake wardobe din tadauko tasaka takoma gaban madubi tana kallon fuskanta wayan hijabin yadan mata yawa kadan hakan yasa yadan zame baya kana ganin gaban gishinta da farko farkon kitsonta da hakan yasa tai bala’in kyau, babu abinda tashafa a fuskanta amman tai wani kalan kyau tai haske sai naman idanunta dasuka danyi ja sabida kukan datayi jiya da daddare dakuma yanzun nan, turarukanta ta dauka ta feffesa tana murmushi bakaramin

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment