Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaman Yar baby Yar yarinya hakanan kawai taji Allah yasanya mata son yarinyar azuciya and idan Abee zaizo yasota she will be so soo happy wlh, zama Anty Binta tayi kusada ita tace “dan Allah ya isa hakanan Lujain kiyakuri” makema Anty Binta kafada tayi tana tabe baki cikin kuka tace “ni gidanmu zani wajen Gwaggo na” murmushi dukansu biyun sukayi Amina tace “to yanzu kidaina kuka kinga tunda babanki yayi fushi yanzu baraki iya komawa ba kibari gobe saimu maidaki gida” rage kukan tasomayi tana kallon Amina dake magana ahankali tace “da gaske zaku kaini wajen Gwaggo na gobe”? Gyadamata kai daga Amina har Anty Binta sukayi atare daidai su Sajida da Zainab na shigowa da kulolin abinci da tray na drinks suka bita da kallo kaman yanda itama ke kallonsu still hawaye nafita daga idanunta amman ba kuka takeba gashin idanunta sun jike sharkab, suna ijiyewa suka fita Anty Binta tace “zakici abinci? Ga abincin ki nan ankawo miki” murya chan kasa tanabin abincin da kallo tace “tea zansha da bread” tashi Anty Binta tayi tace “bari naje nakawo miki” daidai lokacin Sajida tashigo da flask da gwangwanin madara da Milo da chokali da karamin mug da bread Anty Binta tace “yauwa ga kayan tea nan bari nahada miki” karba tayi Sajida tawuce tafita Anty Binta nan da nan tahada mata tea akaramin cup tadaura akaramin tray takawo mata saman gado tabata karba tayi ahankali tana kallon fuskan Anty Binta saikuma takalli tea yanda yake tururi Anty Binta tace “oohh zafi bakishan tea tafashashe haka”? Gyadamata kai tayi ahankali hakan yasa Anty Binta tashiga juya tea ahankali take sauke ijiyan zuciyan kuka saida Anty Binta ta dandana tea jin zata iyasha yasa tamika mata karba tayi takai bakinta ta dandana jitayi yafi na Gwaggo dadi kaman bada milon da aka sabayi aka mata anan ba bread din Anty Binta ta dauka tana kokarin budewa taciro mata slice Lujain tamika mata cup din ahankali tace “Anty akaramin” daga Anty Binta har Amina kallonta sukayi ayanda kadai yarinyar take orobo Masha Allah sunsan bakaramin abinci takeci ba da murmushi Anty Binta tamata shima tasha tareda bread cup uku tasha na tea sannan tace takoshi yunkurin sauka tafara daga kan gadon har lokacin bata daina ijiyan zuciya na kuka ba Anty Binta tace “ina zaki”? Kaman zatai kuka tace “wanka zanyi kayan nan na cizona” wanan karan Amina saida dariya ya kufce mata Anty Binta kuma ta murmusa tace “to ga bathroom naki nan kije kiyi” gyadamusu kai tayi tawuce ciki duk suka bita da kallo suna kallon uban tulin gashinta kodan family su basuda gashine oho jitayi kaman ta deba ta sammata, tashi sukayi Amina ta tayata daukan flask din itakuma Anty Binta tadau cup da tray suka fitada shi suka rufo mata kofa, kowa har yashige dakinshi though bawai anyi bacci bane but babu wanda ke falo ijiye komi sukai a kitchen suka fito Hajiya suka gani tsaye gaban dakinta dake nan kasa tace “taci abincin kuwa”? Anty Binta tace “shayi kawai tasha Hajiya” kallon Amina Hajiya tayi tace “ke ina mijin naki” dariya tayi tace “wlh Hajiya ni baraki kadani natafi yauba kwana zanyi sai gobe zan koma” hararanta Hajiya tayi tace “ai shikenan, saida safenku” “saida safe Hajiya” har Hajiya tashiga daki saikuma tajuyo daidai sun zauna a falo zasu kunna kallo Hajiya tace “Binta” dasauri Binta tadaga kanta tace “naam Hajiya” cikeda damuwa tace “dan Allah kiduba mini Yar mutane kafin ku kwanta dan nasan Imrana ba dubata zaiyi ba” murmushi Anty Binta tayi tace “tom yanzu ma wanka tashiga Hajiya saisa muka dan zauna anan mubata wuri” gyadamusu kai tayi tawuce ciki dan ita bata jure hawa benen nan sabida kafafu saitafi wata bata haura sama ba.


Tadade tana kallon bayin komi daban da bayinsu dansu normal shower ne, kasa amfani da shower tayi, da kyar ta iya bude pampon shikuma ruwan sanyi ne aciki duk yanda zatai tayi takasa hakan yasa tabude wani sabon towel fari kal data gani abayin tadaura tafito tana tafiya ahankali tana kalle kalle dakin, bakin gadon taje tazauna ahankali dudda sunce zasu kaita gida gobe but hakanan taji wani sabon kuka yazomata data tuna auren da aka mata yasa take awan nan gidan dabatasan kowa ba, babu wani abu dake mata dadi aduniya, bata taba tunanin zatai aure yanzu ba ita dake ganin zabga zabgan yayunta agida basuyi aure ba, wai itane matan aure matan wani tayi kukan jin kanta na sarawa yasa ta tsagaita da kukan hakanan tareda jingina kanta da bangon gado wani kalan gyangyadi ne yafara dibanta har baccin yay nasaran kwasheta ahaka wuyanta ya bankare.



Ganin Shadaya har darabi yasa Anty Binta takashe kallon tace “zomuje mu duba Amarya saimu je mu kwanta” kashe wutan falon sukayi sukai sama, sallama sukayi jin shiru yasa Anty Binta tabude kofan ahankali zaune suka ganta daga ita sai towel babu dan kwali akanta wuyanta Ya karkace tana bacci awahale Amina tace “laaaaaa” gaban gadon Anty Amina tayi takira sunanta. “Lujain, Lujain” amman shiru dan ita tanada nauyin bacci idanba itane ta tashi ba saikai da gaske zaka iya tadata, Anty Binta tace “ko kayan bacci bata sakaba baccin ya kwasheta” Amina tace “gajiya ne da uban kukan datashi gyaramata kwanciyan kawai” gyaramata kwanciya Anty Binta tayi hakan yasa tasake sauke ijiyan zuciyan kuka Anty Binta tadan kalleta sanan taja bargo tarufa mata tareda rage gudun AC dakin sannan takashe wutan dakin sukaja mata kofa sannan suka wuce dakinka.


“Don’t forget cinta, shanta, lafiyanta, suturanta her well-being is now on you, not any of your family members ko Hajiya, I know you saisa nake fadin hakan, it doesn’t matter ko kanason auren ko bakaso anriga an daura, make sure ka kiyaye hakkokin that girl Imran, she’s in that house because of you, so kaji tsoron Allah and remember Allah na yafe kowani laifi banda hakkin wani bazanzo kafara this phase at the wrong foot her” dan gajeren tsaki yayi gama karanta messege din da Musty yatura mai ijiye wayan yayi yana kallon magungunan shi dake gabanshi kwashesu yayi yaja drawer yazuba su all this while baya sha yanzu ma bazai faraba duk maganin sa bacci hakan zai taimakamai da migraine but no kusan 12 yakai yana aiki a desktop nashi komi anatse yakeyi sannan ya kashe komi yamike yawuce gado kwanciya yayi tareda addu’a yaja bargo dudda bayajin bacci but he’s trying to fall asleep.


Wuraren 3:00 cikin bacci tace “Yunwaa” ahankali tasake cewa “yunwaaaa” jin shiru yasa dakarfi tace “Gwaggo yunwaaaaaa” jin yanda dakinta ya amsa maganan sabida yanda tai dakarfi yasa tabude idanunta rasss ganin duhu still adakin babu hasken torchlight na Gwaggo yasa ta tuna bata gidansu yau, gadon datake kai tashiga tattabawa hartakai karshen gadon bataji alamun mutum akaiba wani kalan mugun tsorone yasauka akan zuciyanta tunda ta taso tai wayau yaune rana na farko datake ganinta adaki ita kadai bata kwana da kowaba she’s always with Gwaggo ga ko’ina tsit babu ko minshari irin na Gwaggo dake fadi wani kalan tsinkewa zuciyanta yashigayi ko za’a kasheta batasan ina switch yakeba dazata danna taga haske ba balle kuma waya, tashi tayi lips dinta har rawa suke ta jingina da bangon gado tana kwalalo idanu tana bin ko’ina da kallo gani tayi kaman akwai wasu abubuwa da yawa kan carpet na dakin hakan yasa ta kara Gwalalo idanu ganin abubuwan na motsi suna kusada ita yasa tawani kwala uban ihu tsakar daren nan. “Wayyooo Gwaggooo, Gwaggo kizo akwai aljanu agidan nan wlh gasunan Gwaggo suna tahowa kusadani, wayyooo Allah na nashiga uku na bani, Aljanuuuu” tai maganan takai hannunta tadaura akan idanunta ganin kaman kwara daya yahayo kan gadon nan daidai nan aka bude kofar dakinta tareda kunna wutan dakin hakan yasa haske ya gauraye dakin, Abee ne tsaye gaban dakin sanye dawata faran jallabiya batare daya rufe boturan wuyanba da alamu da sauri yafito dan mana iya hango kwantaccen gashin kirjinshi, ganin yanda take ihu tana kiramusu Gwaggo kaman zata tadamusu da gida sama sabida ihu yasa yace “Ke!”EPISODE 1️⃣9️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Har tsakiyan kanta taji tsawan da aka daka mata dayasa lips dinta nawani irin bari tashiga bude idanunta kadan kadan tana kallon direction din da Abee yake tsaye kafin takarasa bude idanun rass sai alokacin wani kamshin turare mai bala’in dadi yadaki hancinta, dawani kalan sauri hartana neman faduwa akasa tai tsalle ta duro daga gadon tai wajen Abee daya dauke kai daga kallonta dasauri ganin abinda ke jikinta, dan nesa dashi ta tsaya tasaki kuka ahankali takai hannuwanta duka biyun kan idanunta tace “dan Allah ka kaini gida wajen Gwaggo na nan gidan akwai Aljanu gasuchan a tsakar dakin yan gajejjeru” tai maganan tana mai pointing da hannu tsakar dakin sannan tajuya jakunkunan ta guda biyu da Gwaggo ta bada akawomata tagani da kuloli guda uku na abincin da aka kawomata jiya dan zaro idanu tayi sannan gently tajuyo da kanta kaman mara gaskiya tadan kalli Abee daidai shima yazubamata nashi idanun wani kalan cika mata idanu yayi ahankali tasauke kanta kasa dasauri takai hannunta tana goge hawayen dasuka zubomata babu alamun wasa akan voice nashi yace “those things looks like Aljanu to you”? Girgizamai kai tayi ahankali tanajin muryanshi har cikin heart dinta, dan tsaki Abee yayi yajuya zai fita wani kalan fashewa da kuka tayi kaman jira take tabiyoshi da gudunta da sauri yajuyo jin tabiyoshi da gudu hakan yasa chak ta tsaya chak tasauke kanta akasa tana kuka, kallo yamata daga sama har kasa kaga idanunshi kaman zai daketa dasu yace “where do you think you are going”? Kasa magana tayi sai kukan datakeyi strictly yace “wuce ki koma cikin dakinki” ahankali kaman wacce idan tai magana da kyau zai make tace “I can’t sleep alone” watsa mata harara yayi yace “amman kin iya zuwa bayin maza alone” dago jajayen rinanun idanunta tayi takalleshi hada idanu sukayi dasauri daga ita har shi kowa ya kauda kanshi shi kanshi baisan yama akayi yayi maganan ba he’s just angry so many things acikin zuciyanshi, cikin dan murya azafafe yace “go back inside” shiga cikin dakin tayi dabaya dabaya takoma ciki tana kallonshi batare data kulle kofan ba, dan gajeren tsaki yakarayi yakai hannunshi yakama handle na kofan yajawo zai rufe karaf yaji tarike taleko da kanta ta ragowan space din dayarage ta kwawkwabe baki takalleshi idanunta sun cika da hawaye tam kaman ana ciremata rai tace “dan Allah dan Allah karka rufeni wlh tsoro nakeji, idan ka rufe ni zan mutu kaji I can’t sleep alone pleaseeeee” dan kallon idanubta yayi kadan cikin wani kalan fushi Abee yabude kofan yashiga dakin da sauri takoma baya ganin yanda yashigo kaman zai daketa, azafafe yace “inda kinsan you can’t sleep alone dabaki abinda kikayi ba, dabakije bayin maza kin rufe kanki kina kallon only God knows what ba with phone, ke bakison kwana ke kadai ni do you think I love this kaddararren auren nan da akamin dake? Do you think I want someone like you as my wife? Do you think I will ever consider you my wife? Listen and listen well? Dagayau you will sleep alone and learn how to live and survive anan you did that to yourself not me understood? Kome kika sami kanki aciki ayau ke kikama kanki, I never wanted you, I didn’t initiate this marraige, your family did, su suka miki so deal with it understood?” Gyadamai kai tayi dasauri tana hawa gado dukta daburce ta manne jikin gadon sosai ko’ina najikinta rawa yake sai gyadamai kai take kaman lizard alamun taji arayuwan nan bayan Baba sai wannan mutumin ne suka taba mata ihu da tsawa kuma sutafi tsoro yanzuma saitaji kaman tafi tsoron wannan kan Baba dan Baba kome zaiyi Gwaggo is always there to save her wannan ko babu wanda zaizo, shi kanshi Abee yanda yaga tanayi kawai saiyaji zuciyanshi ya tsinke tabashi tausayi baimasan mesa he vent his anger on her is just a mistake dako Kausar dinshi can make so why is he this bitter towards her? Did she even understand him? Why will he even waste anger nashi akan Yar yarinyar nan saikace yana fada da babba sa’anshi. Juyawa yayi yafice daga dakin dasauri tareda bangin kofan dakin kaman jira take sauka tayi daga gadon dasauri ahankali ta zauna akasa kusada kofan jitayi yunwan ma yabace dataga bala’i, sosai take kuka tanabin dakin da kallo kaman wani abu zai bayyana tagani haka takeji, maganganun dayamata sai yawo yake mata akai, for the first time bayan yay maganan sai itama taji mema yakaita tashiga bayin maza? Look abinda tama kanta yanzu? Wannan wani kalan rayuwa ne tashigo rana daya, idanunta kur har aka kira sallan farko na asuba tana matsar hawaye tananan awajen ta zauna ta kudundune kanta dan tiles ne wajen ba carpet ba ga sanyin kasa ga sanyin AC gashi daga ita sai towel wani kalan wahalallen bacci yay awon gaba da ita.



As usual 4:30 dot Abee yafito, wani ash color jallabiyane yanzu ajikinshi fuskanshi har wani haske yake na musamman sabida yawan sallan dare yana kamshi mai dadi dakin Hamza yashiga yatada shi, yashiga na Abdallah, sannan yafito yashiga yatada Kausar kafin yatada kannenshi su Anty Binta harzaiyi stairs Lujain tafadomai arai yanzu dai da gaske responsibility yakaru akanshi he can’t believe it abin namai kaman he’s dreaming, juyawa yayi kaman baiso yataka yawuce zuwa bakin kofanta hannunshi yadaga kaman baiso yayi yakai hannun kan kofa yay knocking kofar ahankali batare dayay magana ba jin shiru yasa yabude kofan kadan da fuskanta yafaracin karo dake lilo sabida yanda tai baccin awahale anan kusada kofa bayanta jingine da bango, idanunshi ne suka sauka kan hannunwanta data kankame jikinta dasu duk cikin bacci, tsigan jikinta sun tashi yirrr dazai nuna mugun sanyi takeji, almost 30sec yayi yana kallonta sannan yadaukekai shibaimasan ta yanda zai tasheta ba. “Ke” yafadi ahankali amman ko gezau batayiba kana ganin baccin kasan bata dade dayinshi ba. “Kee!” Yafadi da karfi dudda tanada nauyin bacci amman har cikin zuciyanta taji yanda yakirata agigice tafarka tamike tsaye towel dinta na neman kwancewa dawani kalan mugun sauri Abee yadauke kai tareda juyawa yace “go and pray” yaja kofan yawuce da sauri dudda uban baccin datakeji but she’s so use to salla da asuba bayi tashiga tanaso tai wanka still tarasa yanda zatayi jikinta har danko yake mata gatanan kaman kifi sabida son wanka, brush tayi kawai tayo alwala tafito tana tafiya ahankali gaban babban wardrobe na bango dake dakin taje tabude ahankali kaya tagani acike sababbi babu atampa ko daya saidai abayoyi da kayan bacci da kananun kaya sai hijabai wani milk hijab taciro tasaka tana tunanin to inane gabas aka turo kofan Kausar ce sanye da kayan bacci na riga da wando batare data shigo ba ta tsaya nan gaban kofan, gaban mirror tanuna mata tace “nan ne gabas Abee yace nazo na nuna miki” tajuya zata wuce dasauri Lujain tace “ya ake kunna shower ruwan zafi yazo”? Batare da Kausar tajuyo ta kalleta ba tace “ki murza wajen zuwa kasa” tana maganan taja kofa tawuce dan hararan kofan Lujain tayi tace “angaya miki nima inason gidan naku ne dan nama tambayeki shine zaki amsani kaman na rokeki kudi? Mai halin Ya Abida kawai” tasake hararan kofan Dadduman ta shimfida tahau kai tai salla saikuma tai shiru bazama ta iya kwatanta abinda takeji ba kaman taita ihu tana kuka takeji sabida kunci daura kanta tayi akan gadon tana tunani ga yunwa datakeji bana wasa ba yanzu shikenan barata dinga ganin Gwaggo ba da Gwaggo na nan da yanzu taci abinci, da yanzu tana mata hira, she’s missing Gwaggo kaman takira sunanta taganta anan wani sabon kuka yazo mata kawai tahau kuka anan saida tayi takoshi sannan bacci yay awon gaba da ita.


7 daidai Abee ya shigo gidan saida ya gaida Hajiya sannan yataho sama dakinshi yawuce batare daya kalli daidai da kofar dakinta ba sake wanka yayi yashirya cikin wani black suit na italian yasa black takalmi sai kamshi yake yafito rikeda wayanshi a hannu harya wuce kofan dakinta kaman wanda yatuna wani abu yadawo wannan karan bai knocking ba yabude dakin zaune yaganta kan dadduma sanye da milk hijab tadaura kanta akan gado tana bacci, daganan kofa yakirata. “Kee!” Firgigit tabude idanunta kaman taji muryan mala’ika mikewa tayi zumbur hakan yasa towel dinta yay kasa hijabin yawani kama jikinta dayasa zaka iya ganin komi dauke kai Abee yayi saikawai yajuya yafita batare dayace mata komiba.
Kokarin hawa gado tayi ta kwanta but jin fatar jikinta kaman ma danko danko yake mata yasa tacire hijabin tawuce bayi, da ruwan sanyin hakanan tai wanka dawani sabon soso da shower gel datagani abayin mai kamshin dadi sai ihu take tana sauke ajiyan zuciya sabida sanyin ruwan, daura towel tayi tafito har rawan sanyi takeyi sosai tawuce takashe AC sannan taje gaban madubi wani cream datagani awajen na QEI tadauka tabude dan shima sabone tashiga shafawa sabida sanyin ya barta gama shafa man tayi ganin taki daina jin sanyi yasa takoma bayin tacire towel din ta wurga washing machine datagani abayin tadauko wani towel din tadaura tafito, zama tayi jin sosai takejin sanyi yasa tasake mikewa tai wajen gadon tashiga gyarawa sabida tadainajin sanyin daidai tana gama gyaran ana sallama tareda bude kofan dakin hakan yasa da sauri takalli kofan da kodaddun idanunta dasunsha kuka Anty Samira ne tace “gyaran gado kikeyi Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali tace “ina kwana”? Murmushi sosai Anty Binta tayi tace “muntashi lafiya ya Kwanan sabon waje”? Shiru Lujain tamata batare dabata amsaba karban bargon hannunta Anty Binta tayi tace “kawo natayaki ninkewa naga yamiki nauyi kaman ma kin wanka ko”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, Anty Binta tace “to je saka kaya duk suna cikin wardobe atampopinki ma yau tela zatazo ta aunaki, yi maza sa kayan musauka kasa”? Gyadamata kai tayi hankalinta na kara kwantawa wannan datace su sauka kasa that means zata kaita gida kenan, wardrobe din tabude dogon rigan da hannunta yafara tabawa tadauka wani nakine amman yanada gold stone dake sparkling, dan juyawa tayi tadan kalli Anty Sam ganin hankalinta gabaki daya nakan bargon datake gyarawa akan gado yasa ta dauki cotton pant data gani awajen Babba aka sayo da kananu babban tadauka tasaka yamata cip tasaka underskirt, sannan tazare towel din ta ijiye tajuyama Anty Samira baya tadau wani white singlet tasaka daya kamata bam dan ko kadan batason tasaka bra tadauki rigan tasaka dayawani haskata da kaman dan ita akayi, dan kwalin abayan tadauka zata yafa dasauri Anty Sam data gama tana kallonta tace “noo kifara gyara gashinki” dan zaro idanu tayi ahankali tace “ban iyayi ba Gwaggo ke mini” yanda tai maganan saida Anty Binta tai murmushi ganin yarinyar nada shagwaba komi nata ashagwabe takeyi dan yamabi jikinta tace “zauna kiga” zama tayi akujeran gaban dressing Anty Binta tacire ribbon din tana kallon tsayin gashinta sannan tadauki man kitso tashafa mata tareda tsage gaban kan sannan ta tajemata ahankali tai parking gashin dayawani kwanta tai parking tsaf tana kallon fuskanta tagaban madubi tace “idanunki sun kode da yawa sa kwalli saimu sauka muyi breakfsat ana jiranmu” kwallin tadauka tasaka ahankali sai idanun sukai kaman na aljanna gyalen Anty Binta ta karba tayafa mata aka sannan tace “tashi mujeto” tashi tayi Anty Binta tai gaba tana biyeda ita abaya suka fice daga dakin sukai stairs kanta akasa, kowa na nan, Hajiya na zaune tasanya wata atampa blue mai kyau, sai Abee dake zaune kan one sitter dake facing stairs din, sai Kausar na zaune akasa wajen kafanshi rikeda littafi da byro a hannunta tana rubutu, sai Abdallah yana zaune kusada Hamza da Ibro duk suna kallon stairs din sai Sajida da Zainab da Maman Aneesarh duk suna zaune suma tareda matan Ibro ga yara akasa suna zazzaune, kallo daya tama falon da mutanen ciki tasauke kanta kasa hakanan kawai gabanta nafadi dum dum dum, ko Anty Binta ta lurada hakan ne kamo hannunta tayi suka karasa sauka kasa har zuwa gaban Hajiya tace “ga Maman mu nan gabadaya dudda jiya dakika ganta kinata kuka but itane Maman Mu Hajiya Babba dakanta” dakuwa Hajiya tama Binta tace “kinci gidanku Binta” sannan takalli Lujain da kanta ke kasa tace “Mun tashi lpy Lujain” Gyadamata kai Lujain tayi ahankali murya chan kasa tareda dan dukawa kaman yanda take gaida Baba tace “ina kwana Hajiya” murmushi Hajiya tayi tace “lafiya lau, to har yanzu boyemana fuskan akeyi ne” kara noke fuskanta tayi kasa, kusada ita Hajiya ta nuna mata tace “zoki zauna to” kasa zama tayi kusada Hajiya ahankali ta zauna akasa kaman zata fashe da kuka daidai nan Aneesarh dake wasa akasa tawani rarrafo dagudu zuwa jikinta tana kokarin magana na yara tana kallon fuskan Lujain din kaman yanda yara keyi irin taga bakuwan fuskan nan sai kowa na dakin ya tsaya yana kallonsu, ware idanu Lujain tayi for the first time dawani kalan sauri tasa hannunta tadauki Aneesarh ahankali tace “Fine babyyy” washe baki Aneesarh tayi tana dariya tanajan gyalenta ahankali gyalen abayan ya zame kasa gashinta da Anty Binta ta gyara mata yawani bayyana for the first time Lujain tawani saki murmushin dayasa dimples nata duka biyun suka lotsa ganin yanda Aneesarh keja mata gyale daidai lokacin Abee yadan kallesu.EPISODE 2️⃣0️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Breakfast aka fara kawowa cikin falon dan Hajiya tace ita barata dinning ba, Maman Aneesarh tace “Aneesarh taho kisha cerelac dinki kibar Anty Lujain tayi breakfast” sauka daga jikin Lujain Aneesarh tayi ahankali mikewa tayi kaman zataje wajen Mamanta saikuma da gudu tai wajen Abee zatahau jikinshi takasa, daukanta yayi ahankali yana kallon fuskanta ahankali yace “you don’t want to eat”? Gyadamai kai tayi da sauri tana kallon Coffee dayake sha, dan murmushi yayi yakai bakinta kurba tayi kadan jin daci yasa ta tabe baki tasauka daga jikinshi tawuce wajen Mamanta.

Lujain na zaune inda take akasa atisha yazo mata hannunta takai kan fuskanta tayi tanajan hancinta saiga nabiyu yazomata shima tayi tace “Alhamdulillah” na uku na zuwa, Hajiya tace “sannu Lujain” na hudu ne yazomata shima tayi dayasa kowa ya kalleta banda Abee dake kokarin kurban coffee shi, Hajiya tace “kin kwana da AC ne Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, hakan yasa Hajiya tace “bata farfesu da shayi tasha Binta, sannu mura keson kamata” shayi Anty Binta tahada mata mai kayan kamshi, bala’in yunwa takeji jikinta har rawa yasoma ganin shayi, Anty Binta nagamawa dasauri tadauki cup nashayin takai bakinta ta kurba wani kalan zafi dataji yasa batasan lokacin datasaki cup dinba shayin sai cinyanta wani kalan ihu ta kurma dayasa har Abee saida ya kalleta. “Wayyoooo Allah na zafi, Gwaggo” tai maganan tana kokarin kwaye doguwan rigan sama tana yarfe hannu tana kuka, Hajiya tace “daga gani bata sabashan shayi mai zafin nan ba Subhanallahi sannu ya isa daina kuka” Anty Binta ganin shirin dage rigan take yasa takai hannunta ta taba inda shayin yazuban mata tace “sannu sannu, jeki cire kayan zan biyoki da breakfsat din sama” Gyadamata kai tayi tana share hawayen daya zubomata tawuce sama da sauri tana tafiya ahankali su Sajida suka bita da harara, Anty Binta tashiga hada mata breakfsat nata a tray tace “Kausar zo dauka ki kaimata” dan turobaki tayi sannan ta tashi ahankali tazo tadauka tawuce sama daidai Abee ya mike yakalli Hajiya yace “natafi Hajiya” ahankali tace “tom Allah bada sa’a Imran” wucewa yayi yafita daga dakin suma su Hamza da Abdallah suka fice daga falon Sajida da kaman jira take su fice tace “tsakani ga Allah wlh da auren

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment