Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gwaggo awajenba hakan yasa tadauki wani dogon hijabi tadaura akan towel na jikinta tahau kan dadduma, tana sallame sallan ta tashi batare datayi azkar ba tawuce tafita daga dakin tashigo falonsu wani chocolate dake kan center table na cabry diary milk tadauka da sauri tana budewa tai wajen kofa daidai nan Gwaggo tafito daga kitchen tace “ina kuma zaki gari bai gama wayewa ba Lulu”? Batare data kalli Gwaggo ba tace “wajen Ya Samira zani” baki Gwaggo tabude zatai magana amman tuni tabude kofan tafice Gwaggo tabita tana kwalamata kira tace “bazakizo kisa kaya ba da asuban nan kina yawo daga ke sai tawul babu dan kwali akanki Lujain” ko juyowa batayi takalli kakartata ba saina kara sauri datakeyi zuwa babban flat din gidan tana tafiya kaman Kazan agric dataci takoshin nan tana tafiya da kyar tana tafiya tana ballan chocolate din hannunta tanaci, gidan dan Babba ne ba laifi kana ganin yanayin tsarin gidan kasan ba laifi gidan masu rufin asiri ne daidai gwargwado, bude kofan flat din tayi tashiga dakin tsaf tsaf sai kamshi yake babu kowa afalon direct tawuce wani daki dake corridor dataji hayaniya budewa tayi tashiga da sauri tana murmushi, yammata uku ne acikin dakin dake dauke dawani babban gado na daidai rufin asiri ga daddumai da hijabai akasa kana ganinsu hancinsu zaisa kagane sudin duka sisters ne saidai su kaf dinsu black beauties ne kuma ko kadan basu da jiki kaman ita su sirara ne yammata sosai, duk kallonta sukayi suka watsar amman ko ajikinta wani kalan murmushi tayi tamaida kofan tarufe takaraso cikin dakin tana kallonsu daya bayan daya, Babban cikinsu wacce akalla zatayi shekaru 23 ne da waya ke kunnenta tace “Baby ina zuwa zan kiraka” sannan ta katse wayan takalli wacce ta shigon tace “Lujain ba jiyan nan da daddare Baba yagama miki magana kan zama da towel dakuma rashin daura dankwali ba” dan yatsine fuska tayi kaman zatai kuka ashagwabe tace “mancewa nayi ban daura dan kwallin bafa Ya Samira” dasauri wacce takira da Ya Samira tace “to towel dinfa” dan turobaki tayi tace “wlh zafi nakeji idan nasa kaya” daya daga cikin sauran biyun matan ne taja tsaki tace “yarinya gabaki daya Gwaggo tamaidata mara saiti, ba dole kidingajin zafi idan kinsa kaya ba, jibeta kaman buhu” da normally ne da yanzu tai kuka da aka kirata da buhu but yau she’s extremely happy hakan yasa tace “wlh banda lokacin ki Ya Abida amman gobe ki tareni ki kirani buhu kiga abinda zai faru” yunkurowa Abida tayi kaman zata daketa hakan yasa da sauri Lujain din takoma baya Abida tace “maimaita abinda kikace”? Dauke kai tayi dayan sister da tundazu batai magana ba tace “Ya Abida inba so kike yau duk mutafi school da bakin ciki ba kada kitaba yarinyan nan yanzu dan wlh bamuba har Baba da Mama ransu yau saiya baci akanta kindaisan fitinan Gwaggo sarai” kaman jira Lujain din take jin ankira Gwaggo kwafa tayi tace “barta ta tabani ma tagani Ya Habiba” ganin rikici zasuyi yasa Samira tace “ni dan Allah ku kyaleta zonan kifadamin meya kawoki wajena da asussuban nan keda nasan war haka baki tashi ba” murmushi tayi ta harari Abida da Habiba tawuce wajen samira kaman maison gulma tace “ni akunnenki zan gayamiki” kunnen Ya Samira tabata magana tayi mai tsawo sannan ta tashi wani mugun kallo Samira tamata tace “chabdi wlh bazan baki ba hakanan” kaman zatai kuka tace “please Ya Samira kome kikeso zan miki Allah” shiru Samira tayi tana kallonta hakan yasa tace “wlh kuwa” murmushi Samira tayi tunawa da wani abu tace “inhar kin yarda zaki fasa asusun ki kibani duka kudin ciki zan baki wlh dama banda kudin ankon Aisha kinga nasamu” kaman zatai kuka tace “kai Ya Samiraaa duka fa kikace” hararanta Samira tayi tace “ashe baki cika crush din Mandawari ba, ni wlh idan inason wani celebrity babu abinda bazan iyayi akanshi ba, kikasan ma ko a live din dazaiyi yau yaraba ticket na zuwa kallonshi a stadium idan zai buga kwallo basaikije ba, kuma yana ganinki zaice yana sonki kinga yanda kikeda kyau ne” wani kalan mugun murmushi tayi dayasa kumatunta ya lotsa abin kaman wani machine ne awajen ya bala’in haska fuskanta, Abida dakejin firansu ne ta tsoma baki tace “Ya Samira stop deceiving this girl for your personal interest, international player irin Muhammad Mandawari kyakkyawan footballer hadadde ga kudi bazai taba cewa yanason wannan buhun yarinyar ba ko itace last woman on earth wlh” wani abune yatokarema Lujain wuya tajuya tana kallon Abida dake kallonta hararanta Abida tayi tace “yarinya abincin dazataci dukanmu nan bamu iya cinshi, tsakar dare kaman diyar aljanu dansu ke fatin abinci tsakar dare haka itama ketashi taci nata, Gwaggo kawai tabude mata ciki, tayaya ma Mandawari zai dauketa? Wlh tafi karfinshi” daga Abida har Habiba suka kwashe da dariya itakuma Samira tarike nata dariyan dan tana hango samun da zatayi, Habiba dake dariya tace “Mama ma tace babu wanda zai taba cewa yana sonta balle harma Ya aureta bakiga ba duka yan class nasu nada saurayi ita mazan ajin ko kallonta ma basayi bata burgesu everybody gets irritated with cin abincin Lujain da kibanta” juyawa Lujain tayi fuuu zata fice dasauri Samira tariketa tahararesu tace “don’t mind them yan bakin cikine Mandawari will acknowledge you one day as his die hard fan sannan zai soki harma ya aureki” sosai hawaye yacika mata idanu ahankali tace “are you sure Ya Samira bazaice nacika kiba ba” murmushi Samira tamata tace “ai kiba halitta ce kuma shi so comes from heart inhar na gaskiya ne ko kinfi kowa kiba aduniyan nan he will love you and cherish you, now smile for me muje mukarasa deal din inhar zaki kawo kudin yanzu zan baki wayan ki kalli live dinshi idan nadawo daga school na karbi wayata kin yarda” dasauri ta gyadakai murmushi Samira tayi tace “to jeki kawo kudin kafin nan nagama waya da Baby” da sauri tajuya tafita su Abida suka bita da harara sukace “wawiya kawai tama dawo ta dauke ledan chocolate din nan data ijiye mana anan dan nan ba dakin kakarta bane data maida bola ba”.EPISODE 6️⃣




Tana fita daga dakin daidai wata mata wacce kana ganinta kasan itace mahaifiyar yammatan datafito daga dakinsu sabida yanda sukai kama da mahaifiyar tasu, tsayawa tayi ahankali tace “Mama ina kwana” kallonta Mama tayi daga sama har kasa taja tsaki tawuce hakan yasa itama tawuce daidai tabude kofa zata fita daga falon taji Matar tace “duk randa aljanu zasu shigeki wlh saina bada sadakan dubu ashirin” batace komiba bude kofan dakin tayi tafita daidai lokacin wani magidancin mutum na karasowa gaban dakin sanye da jallabiya shima tareda wani babban yaro wanda bazai wuce 25yrs ba, wani mugun kallo dayama yarinyar yasa kawai jikinta yahau rawa kafinma yayi magana kaman zata fashe da kuka tace “Baba dan Allah dan Allah Baba kayakuri karka doken dan Allah” juyawa tayi zata koma dakin tsabagen rudewa saikuma tasake juyowa da sauri ta kwasa aguje tai side din kakarta mahaifinta yabita da kallo kaman zai doketa da idanu, ahankali yaron dake taredashi yace “kamata hakuri Baba please” dan ijiyan zuciya Baba yasauke saikawai yabude kofa suka shiga falon shida yaron.



Bata kara fitowa daga dakinsu ba sabida tsoron gamuwanta da Baba, saida tasake wanka dan haka take kaman kifi arana zata iya wanka sau ashirin sannan ta shirya cikin kayan makaranta, shima makarantan sabida Baba na nan ne da wlh bazataje ba, wani white long sleeve rigane daya tsaya a cinya sai kuma wani dogon gown ash dazaka daura akan farin rigan sai abun yayi kaman biri da wando dayay mata kyau sosai, zama tayi Gwaggo dakanta tashiga samata safa akafa itakuma tana kirga kudin asusunta data bude Gwaggo tace “wai Mezaki da kudin ki dakike tarawa ma salla iyye”? Turo baki tayi tace “wani abu zanyi” tabe baki Gwaggo tayi tana karasa saka mata black cover shoes nata tace “kyadaiji da rigimanki baran biyemiki da safen nan ba dan na lura neman abinda zaisa bazakije makaranta kike ba” Gwaggo tai maganan tana kawo mata wani fine black bag pack tace “ga jakan ki” karban jakan tayi tabude da sauri chocolate daban daban da aka zubamata ta kalla da biscuit da juices kala uku da goran ruwa saikuma wani dan karamin flasks na snacks sannan tadago kai takalli Gwaggo kirji Gwaggo ta dafa tace “menene kuma ni Safarau dazaki dallamin miyagun idanuwan nan naki” amugun shagwabe tace “baki samin yoghurt ba Gwaggo” kaman Gwaggo zatai kuka cikeda lallashi tace “wlh bansan yoghurt dinki sun kareba Lulu kiya kuri zansa Baban ku yasayo yau tashi muje chan palour” makema Gwaggo kafada tayi idanunta sun cikada kwalla har kyalli suke amman basu zuboba rudewa Gwaggo tayi tazauna kusada ita cikeda bala’in lallashi takai hannunta tanajan kumatunta tace “haba mana Lulu na yarinyan datafi duka yaran duniya kyau so kike ajimu, kema kinsan kome kikeso sai inda karfina yakare ko wannan ma bansan yakare bane kiyakuri kina dawowa zaki tadda yogurt naki” makema Gwaggo kafada tayi still ita bata yarda ba Gwaggo tace “to yanzu mekikeso? Ni wlh kin fitineni Lujain kin hanani sakat aduniya, zanfa tattara nakoma kauye nabarki” kaman jira take fashewa tayi da kuka sosai kaman ana yankata ta tashi fuuu tafice ko jakan bata daukaba da sauri Gwaggo tadau jakan tabita abaya tana kwalamata kira tace “Lujain zoga dubu daya saiki saya wlh wasa nake babu kauyen dazani nabarki, nima ina zan iya rayuwa babu ke kinmini nisa” kojuyowa Lujain batayiba sai kukan datake daya cika gidan gabaki daya yana eco daidai Baba yafito daga falo chak ta tsaya anan tsakar gidan kukan yamakale awuya Gwaggo takaraso dasauri tana hararan Baba tace “kaikuma meya fito dakai ina ruwanka damu ai magananmu mukeko Lulu” da sauri Lujain ta gyadama Gwaggo kai tana goge fuskanta da bayan hannu, strictly Baba na kallonta yace “collect your bag muwuce school” ahankali tamika ma Gwaggo hannu, Gwaggo tace “yauwa diyar albarka zan sayamiki kafin kidawo kinji ga jakan” karban jakan tayi ta goya Baba yafito zai gaida Gwaggo tace “jeka kaisu kadawo ai ina nan babu inda zani” girgiza kai kawai yayi yawuce Lujain tabishi haka su Samira ma dasuka fito duk sun shirya su sun fara university, suna shiga bayan motan murya kasa kasa Samira tace “ina kudin”? Mikamata kudin Lujain tayi aboye itama taja jakan Lujain tasamata wayanta da earpiece aciki tace “ai kinsan password dina” Gyadamata kai Lujain tayi tana murmushi kaman ba ita tagama kuka ba, a school dinta Baba yafara parking school ne mai kyau ba laifi ga buses awaje an jerasu sabida excursion din daza ayi sauka tayi Baba yakalleta yace “zagayo tanan” zagayowa tayida sauri ta tsaya wajen glass din motar daya sauke yana kallon fuskanta dukta tsure dan tana tsoron Baba sosai, dan jim yayi yana kallonta kaman mai tunanin wani abu saikuma yace “menene bakida shi dakike kuka?” Adan tsorace kaman mai tsoron fadi tace “yooo………ghurt Baba” murya chan kasa still yana kallonta yace “ana saidawa acikin school din naku?” Gyadamai kai tayi ahankali, yace “nawane”? Ahankali tace “500 ne Baba” dubu daya yadauka yabata yace “gashi to kisaya” wani kalan murmushi tayi daya bayyana fararen hakoranta tass irin na yara din nan tace “thank you Baba” murmushi yamata yace “excursion zaku yau ko”? Gyadamai kai tayi tana rikeda 1k din yace “ina”? Hannu tanunamai alamun batasani ba tace “amma ance wajen ceramic ne, zamuje muga yanda ake yin su flower verse, broken plate, bowl, tiles da sauransu” gyadamata kai Baba yayi yace “is a good thing makesure kinyi paying attention and learn everything kinji” gyadamai kai tayi tace “too” juyawa tayi tubur tubur zata wuce Baba yace “Lujain” dasauri tajuyo takalleshi tace “na’am Baba” ahankali yace “be careful okay” gyadamai kai tayi tajuya tawuce saida Baba Yaga shiganta school sannan yasauke ajiyan zuciya yatada motar duk cikin yaranshi yafijin tausayinta bawai sabida ita marainiya bace kadai ba sabida many things, she gets bullied a lot a school, a islamiyya, har agidama, wani zubin yanaso yarabata da Gwaggo but idan yakalla abin deep down badadan Gwaggo ba da yanzu she’s depress Gwaggo nakoya mata komi ba komi bane karta sake tai taking maganan mutane to heart and she should be confident kiba is beauty kuma haka takeyi Koka cemata me kiba da sauransu wani zubin zata iya kuka but give her one hour ta kakkabe jikinta tayi moving on gashi ko kadan batada riko her heart is as pure as white paper.EPISODE 7️⃣



Tana shiga school ana cewa sufito afara shigan bus dan 9:30 zasu bar school yan class nasu yan SS2 akace sufara tafiya bus nasu ita hartama saba batada friend shiga tayi itane sit 1 dan ita tafara biyan kudi tana zama tabude jakanta tadauko ledan biscuit tafaraci yan ajin saikaga wannan yataba wanchan anunata sai akwashe da dariya ko kallonsu batayiba dake bude jakan tayi ta leka wayan Ya Samira tareda dannawa taduba time dan 11 Mandawari zaizo live a IG, murmushi tayi maida jakan tarufe tana cigaba da cin katon biscuit dinta wata Yar class dinsu tamike tsaye a bus din bayan an gama shiryasu an koma wani bus ana shirya wasu yan ajin base on payment tace “Hey Class mate I have a story to tell u tantadaaaaa” duk kallonta akayi wasu yan mata da samari click dinsu sukace “we are listening princess” dariya tayi tace “I want to call some part of the body kugayamin uses dinsu” duk akace okay, tace “the eyes is for whattt?” Yan ajin sukai ihun “seeing” tace “the ears is for what”? Suka kara ihun “hearing” cikeda zolaya from her tone tace “and the mouth is for whatttttttt?” Yan ajin sukai ihu atare “eating” tace “for what” sukace “eatingggggg” Haba sai dariya duk Lujain najinsu hakan bai hanata cigaba da cin abinta ba, komawa princess tayi tazauna tana dariya saiga wata ta tashi da ake cema Lily tace “aga aga” dayake dudda akwai Christian a ajin but duk sunajin hausa universal language sukace “aga” tace “aga chop chop din aji” atare duka suka nuna Lujain sukace “aaaagannntaaaaaa” sai dariya tace “aga mara kawa” suka nunata sukace “aaaaagannnntaaaa” tace “aga mara aboki” sukace “aaaaagannnntaaaa” sanan tai wani ihu irin na final one din nan tace “aga mara boyfrienddddddd” duk aka nuna Lujain akace “aagannnnnnntaaaaa” kwarema Lujain tayi ba kakkautawa dasauri tashiga bude jakanta taduko ruwa da sauri tashiga sha saida tasha sosai sannan click din su princess din sukazo inda take tsabagen son ta kulasu Princess tace “ke miss chubby bakijimu bane Fatty bom bom” wani mugun kallo Lujain tamata batai wata wataba tamike tsaye tareda ajiye jakanta kan sir din dasauri Princess suka koma baya dan sun zaci dukansu zatayi ko zaunesu cikin kunanrai Lujain tace “Ohhkayyy you want me to say something ko” boldly takalli yan cikin bus din tace “aga aga” Yan makaranta fa akwai son bala’i da fitina, they live for it shine the joy and the fun that comes with being in school da sauri sukace “aga” Lujain tace “aga masu satan amsa during test and exam masuyin chokes olodon aji amman sunfi kowa iya makeup” habawa sai dariya kyakyalya bakaramin kunya princess da Lily sukaji ba, Lujain tanunata da hannu tace “idan kika kara kirana Chubby kowani stupid name saina fasa miki ciki, my name is Lujain but I prefer idan ankirani da LJ, and I am pretty, prettier than this bullies, and I am brilliant cus banayin choke, and I am beautiful I don’t need makeup kuma I have boyfriend a celebrity for that matter” tanunasu habawa sai ihu ajin ana bubbuga kujeru da kasan motan da kafa ana dariya yan class din suka fara matching ana tafi “LJ! LJ!! LJ!!! LJ!!!!” juyawa tayi takoma sit dinta dasauri ta bala’in danne kukan datakeji Gwaggo tasha gayamata kada tasake tayima yan ajinsu kuka idan sun kirata da sunaye dan zasu cigaba saisa bata sake tai kuka and bata taba nunawa wani dan ajinsu she needed them ba tana homework dinta tai karatunta da kanta dan Allah yamata brain.


Teacher dake incharge na class nasu ne tashigo tareda zama akan kujera tace “let’s settle down student remember not to touch without being permitted and not to go anyway da abace muje ba understood” duk suka amsa, juyawa tayi ta kalli Lujain da already ta tara ledojin biscuit uku agabanta tanacin na hudu zatamata magana saikuma kawai tai shiru ta gyara zamanta bus dinsu yafara tafiya.
Bini bini Lujain ke bude jakanta tana duba time awayan Ya Samira ganin har lokacin eleven baiyiba yasa tai murmushi ta juyarda kanta tana kallon hanya, sunyi tafiyan kusan 30min sannan sukakai wani dankareren babban building ita duk zamanta a Abuja bata taba zuwa wajenma bama tasan wajenba to inama take zuwa daga boko sai islamiyya da yamma sai hadda weekend, building na company yayi kyau an rubuta “IMRAN CERAMICS” security gate ne sukai directing nasu to inda zasuyi parking dan musamman aka basu special parking space dan student dole adauki caution saukowa akayi sannan one by one aka fara basu wani sticker dake dauke da rubutun visitor ajiki agaban riguna nan school nasu dake matsayin access card nasu, tanaji wasu yan ajinsu na “wow babban company na wannan, just look at how beautiful visitor’s access card namu” sai alokacin tama kalla dan ana bata mannawa kawai tayi saida teachers dinsu aka kara maimaitamusu yanda zasu behaving da banda tabe tabe sanan akace zasu iya shiga wani ajiyan zuciya tasauke dan surutun yasa bata iya duba wayanta ba kafin teacher sugani a kwace ahankali take tafiya kafin ahankali tasaka kafanta tashiga cikin katon hall don dayake nan reception wani kalan sanyi taji dayasa ta yatsine fuska ahankali tace “AC yay yawa” ihu principal nasu tayi da shigowanta kenan cikin personal car tazo tace “Assemble yourself student” assembly duk sukayi gwanin ban sha’awa murmushi principal din tayi daidai lokacin Hamza yakaraso yana sanye da suit cikeda girmamawa ya gaisa da ita sannan yace “sudan jira kadan CMD na attending ma wasu baki ne” murmushi tamai sannan takalli daliban tace “I am sure all my students here wants to meet the owner, the brain behind this company, this art, this ceramic work dakenan number one a Nigeria keji dashi, the only ceramic company dake exporting kayayyakin su su plate, verse, mugs, tiles dasauransu zuwa kasan waje, let’s know little about him and his success story right, what’s the best way to know inda daga bakinshi ba” student akace yes Ma tace “tom gashinan zuwa” sauke jakanta Lujain tayi tana yatsine fuska kawai anzo an ajiyesu waje daya su haryanzu baa nuna musu komiba ko mene zasuyi damai company oho, danna wayan tayi tacikin jaka ganin 11:05 yasa ahankali tace “Innalillahi na shiga uku” tashi tayi tashiga waige waige ganin teacher su anan baya tsaye yasa tai wajenta dasauri teacher tamata alamu da hannu menene? kaman zatai kuka tace “I want to pee zai zubo” binta da kallo teacher tayi kaman tamaketa tace “Ya za’ayi bazakiji fitsari ba babu kalan abinda bakici ba amota kaman danke kadai akai abubuwan ci aduniya” tai maganan tana cewa follow me binta tayi dasauri zuwa wajen wani security guard tace “excuse me rest room please my student wants to excuse herself” wani waje yanuna musu hakan yasa tace “Oya go” Gyadamata kai tayi ita bama tagane ina ake nunawa ba kawai tawuce abinta da sauri daga malaman har daliban aka bita da kallo wasu na danne dariya ganin yanda hankalin kowa yayi kanta yasa principal tace “attention” duk juyowa sukayi suna kallonta tacigaba da jawabi, ko kadan ita bataga bayin da akacemata ba amman ba wannan ne matsalanta ba waje take nema inda zata labe ta zauna takalli live na Mandawari wani babban corridor data gani yasa tai wajen da saurinta tashiga tafiya harta fita daga corridor taga wani bene da gudu gudu tana haki tashiga hawa benen at the same time tana cire jakanta daga baya duk tana gudu, kaga yanda take tafiya zaka dauka all this kafin agric ne da ake shirin yankawa sunason su gudu, wayan taciro da sauri tana kunna data tana makala earpiece akunne ta sannan tasa hannun tadauko ledan chocolate guda biyu atare tabare ledan ta yarda ledan akasa, jakan batare data rufeba ta sagale a hannunta tana finciko goran fanta da Gwaggo tasamata agefen dan ragaragan aljihun nan na wajen jaka, daidai tana shiga instagram tai logging into her account tana kokarin takai duka chocholate biyu dake hannunta baki ta balla tana kalle kalle ko kadan batasan inda takeba bama tasan tayaya tazo wajenba tadaisan dazu tahau staircase cigaba da sauri tayi ganin duka offices ne awajen kuma duka akulle yasa tacigaba da tafiya zuwa wani corridor data hango daidai tana shiga live din daidai tana yankan kwanan corridor din kawai karo taci da mutum fantan data bude dake hannunta ya kware ajikin mutumin zuwa kasa chocolate din hannunta yawani karye ajikin mutumin yafadi akasa tasan tafadi tasan taci karo da mutum amman still gabaki daya da fuskanta da hankalinta nakan wayan da shi kadaine abinda bai fadi daga hannunta ba sabida yanda tarike gamgam dan shiyafi mata komi mahimmaci ayanzu, ko kallan wanda tabuge batayiba kawai tabi ta gefenshi da bala’in gudu tacigaba da tafiya takara shan wani kwana data gani kawai taga wani kofa abude batai wata wataba tafada ciki ganin bayine ga bayuka kusan biyar kowanne da kofanshi inda take tsaye kuma wajajen wash hand basin ne da mirror yasa da gudunta tayi bayin farkon wajen tana budewa ta sauke marfin masan dakennan karkal ta zauna akai tareda yarda jakanta akasa tawani sauke ijiyan zuciya ta tura kofan dabaigama rufuwa har karshe ba balle tamasaka sakata tana kara tura earpiece din kunnenta da kyau tana kallon wani bakin gaye mai irin askin yan kwalo dinnan da aka kitsa yana sanye da rigan kwallo na magana yana murmushi wani farin hakorin makka na shunning abakinshi wani kalan murmushi tasaki takai wayan ta rungume kirjinta tareda lumshe ido zuciyanta na bugawa tace “I love you Mandawari” na kusan 30sec sannan tacire wayan daga kirjinta tafara replying to live dinshi I love you Mandawari from LJ, My heart beat for you, please check your DM kullum saina maka magana, emojis babu na kalan soyaya dabata dinga turawa ba tana. Cewa please if you see my comments ko sunana ne ka kira a live din nan kana ganin yanda takeyi kasan gabaki dayan brain nata na live din nan.
***
Waiwaye baya kadan….
Daidai taci karo dashi aka bude kofan wani office wani zai fito but ganin Oga tareda wata katuwan yarinya dake sanye da uniform ajikinshi dukansu a tsaye yarinyar na kallon waya kaman abu take nunamai shikuma Oga na kallon fuskanta yasa yakoma cikin office da sauri batare daya gama rufewa ba yana leke, wucewa tayi batare data dauki goran fanta daya fadi da gutsurorin chocolate nataba ta fanfala da uban gudu.


Chak Abee ya tsaya yanabin jikinshi da kallo gabaki dayan suit din dayasa yabaci har zuwa farin rigan ciki dan bai kulle boturin jacket dinba afarin rigan fanta ya zube ga chocolate din some sun manmanne a rigan kaman kashi, sai alokacin ma ya iya juyawa amman hartai kwana sai farin safan kafanta da sandals daya hango azuciyanshi dudda baisan kalan uniform na makarantan dazasu excursion ba but yasan babu any of his employee dazasu dressing like that dan haka that must be a student what on earth student keyi in this floor, kwata kwata nothing yahadasu da this floor dan dazaran yay welcoming nasu factory za’a wuce dasu dake ciki cikin building din suga yanda ake production, jikinshi yakara kallo tayaya zai sauka kasa ahaka yay addressing student, juyawa yayi ahankali cikeda takaici yabude kofan wani office daban ma’aikatan wajen duk suka mike batare daya shigaba yace “call cleaners agoge nan” atare sukace yes sir sannan yawuce yana tafiya anatse zuwa wani special corridor dakenan dawani hadadden office da aka rubuta CMD ajiki murda kofan yayi yaji akulle sai yanzu yama tuna yabar Ibro a office yacemai idan yagama yarufe kofa yakai mishi wasu files mota dan yana gama

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment