Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaninta data warware har zuwa principal office suka shiga, ganin Lujain zaune nata kallon takardan da aka bata yasa ta taho dagudu tana shafa fuskanta tana bude mata idanu tabude bakinta tana kallon da duba harshenta danta gane ko rashin lafiya take tace “Alhamdulillah babu abinda yasameki yarnan Iyyee Alhamdulillah wayyo Allah zuciyata kubani ruwa Insha” dasauri principal tabata ruwan gora budewa Gwaggo tayi ta kwankwade tass sannan ta zauna Baba batare daya kalli Lujain ba yace “gamu principal” ahankali tace “ba babanki takardan Lujain” ahankali Lujain tamikama Baba takardan fuskanta yakalla da jikinta daya baci da drinks da jakanta dahar lokacin na diddigan ruwa sannan yasa hannunshi ya amsa ya karanta yakalli principal din harzaiyi magana saikuma yatashi tareda kama hannun Lujain yace “muje” tashi principal din tayi tace “kuyakuri sir bazan iya barin yarinyar ku tacigaba da karatu anan makarantan nan ba she is a bad influence zata batamini sauran dalibai kuya kuri babu abinda zan iya” sai alokacin Baba yakalleta yace “akwai abubuwa da yawa da zaki iya na farko shine kare hakkinta jibi yanda akama y’ata wanka da drinks sabida kunga batada kani ko Yaya amakaranta kobaki koreta bama nixan cireta daga makarantan, inaso kisan abu daya, akwai Allah! Sannan zai wanke mini diyata agaban kowa muna nan zakusan you all have wronged her” yaja hannun Lujain dasauri suka fita tashi Gwaggo tayi tana kallon Mama tace “ke Maman su Samira me akace tayi ne kifadamin” chak Mama ta tsaya kaman jira take tace “yarinyan dakike mana tunkaho da ita kina fifitata kan nawa yaran video dinta dawani kato dasukaje excursion akafaninshi na yawo a yanar gizo suna fasikanci sun shiga bayi yana dugurguzanta diyarki na ihun dadi” wani kalan zaro idanu Gwaggo tayi tace “mene shairin kine dai ko” wayanta Mama taciro anan office an principal takunnama Gwaggo video tundaga lokaci da Abee ke kokarin kwance belt har zuwa lokacin daya shiga bayi ga muryan Lujain nan dako amarfi tasani tai ihu wayyooo saikuma uhmmm Uhmm uhmmm saikuma chan aka nuno Laujain tafito corridor tana gyara riganta tajuya dasauri ta tafi tunda Gwaggo take bata tabajin tashin hankali hakaba baya tayi zata sume dasauri Mama ta tarota tace “ni kada ki sumemin yace dagangan na nuna miki inason kashemai uwa mutafi” takama hannun Gwaggo tanaja suka fita awaje taga duka yaranta da Yusuf da Abdulhadi dukansu suna sanye da manyan kaya sai Yayanta sunyi jugum suna kallon Lujain da idanunta sunyi ja ganin Gwaggo tafito anriketa yasa tai wajen Gwaggo da sauri saiga hawaye, zaunawa Gwaggo tayi akasa tana zaunar da Lujain bata damu da yan makaranta ba tanuna kanta tace “Lulu tun kina cikin kwalban asibiti nake rainanki nasanki ciki da bai nasan halinki tsaf amman bansan ki da Iskanci ba kifadamin gaskiya meyamiki kike ihu” zaro idanu tayi dukta rude tace “waye? Wani ihu Gwaggo”? Wani kalan fizgota Baba yayi cikin ihu kaman zai mareta yace “ranan dakukaje excursion me mutumin nan yamiki abayi kike ihu”? Jikinta har rawa yake ganin Baba na shirin dukanta tafashe da kuka tace “wlh babu komi Baba” Baba Abdulhadi yace “to ubanme aka miki kike ihu”? Cikin kuka sosai tace “Baffa wlh naje bayi na kalli video wan nan dan kwallon Mandawari ne awaya” kusan dukansu atare sukace “a ina kika sami waya”? Cikin kuka sosai tace “wajen Ya Samira na ara bayan nabiyata da kudin asusu na” Baba yace “saime yafaru”? Cikin kuka sosai tace “ina zaune kan masai nasa earpiece a kunne kawai naga mutum yashigo yana kokarin cire wando” dukansu sukace “Meya miki kike ihu” jikinta har bari yake tana haki tace “wlh babu abinda yamin tsoro naji nadauka aljani ne saisa nadinga ihu na manne jikin kofa shine yamin ihu yace nafita nace ban iya bude kofaba shine yace na matsa yabudemin na fice yay min ball da jaka da wayan Ya Samira harta fashe na kawasa na tafi shikenan” kaman jira Mama take tace “wlh wlh karya kike ke yanzu ki kalli tsabaragen idanun Babanki da Baffan ki kina karya, kifadi gaskiya tun yaushe kika fara iskanci eh? Daman naga gabobin jikinki sai kara habbaka suke waya koyamiki? Wayake matseki? A ina kika sanshi dahar kuka hadu abayi yaushe kika dawo Yar iska mayyan maza Lujain”? Wani kalan fashewa da kuka sosai Lujain tayi tama kasa magana sabida yanda kukan yafi karfinta jin maganganun Mama, tashi Gwaggo tayi tana kakkabe jikinta takalli Baba tace “ku kaini kampanin yanzun nan” kallonta sukayi duka cikeda bala’i tace “ku kaini kampanin nan Kona tare abin hawa nakai kaina, koya mata wani abu kobai mataba bai isa tasanadin shi a batamin sunan diya ba a yanar gizo duniya tagama ganinta, wlh wlh yau sai anyita an kare” Baffa Abdulhadi yakalli Baba yace “Baba dole dama muje muganshi idan ma za’a kai kara hukuma ne asan nayi kumuje” Ahankali Baba yabude motarshi suna suka bude tasu aka shiga har akakai company nan kuka Lujain takeyi sai yanzu tagane abinda yasa su Princess suka kirata har karuwa dudda bata kallo video ba suna kaiwa company reporters dasuka gani agaban kampanin sunfi hamsin saukowa akayi Gwaggo takama hannunta suka wuce ciki ganin ana musu hoto mayafin jikinta tayaye tayafama Lujain dake kuka tarike hannunta sukai wajen shiga taresu security yayi Gwaggo da idanunta sukai jajir tace “na rantse maka da ubangiji zan tube nai dambe dakai awajen nan kace bazamu shiga ba, dan ubanka Mudi da Uwarka Safara’u idan akai kokarin batama jikanka suna bazakayi abinda yafi haka ba budemin kofa kona fasa” girgiza mata kai yayi yace “Mama Oga yace ba shiga ba fita bakiga yan jarida sun cika nan ba” cikin ihu Gwaggo tace “yo ina ruwana shi yasan Meyayi ai” jin yanda Gwaggo ke ihu Hamza da idanunshi sukai jajir yazo wajen daga ciki ganin student din makarantan nan da aka lullube da mayafi tana kuka sosai from yanda jikinta ke bari ga wayanda ke tareda ita dazai iya cewa iyayenta ne yasa ahankali yace “kushigo” bude musu kofa akayi Gwaggo taja hannun Lujain suka shiga ciki, waje yanuna musu awajen yace “ku zauna bari naje na sanar” cikin ihu Gwaggo da idanubta sun juya tace “nabaka minti biyu” stairs yayi karo yaci da Ibro da shima idanunshi sunyi jajir yana kallon su Gwaggo da yarinyan dake sanye da uniform da aka lullube da gyale ahankali Hamza yace “I think is the girls family ka kira Uncle Musty” gyadamai kai yayi yace “yama iso he’s trying to come inside” daidai lokacin wayanshi yahau ringing dasauri Hamza yace “Hajiya ko” gyadamai kai yayi ahankali, hawaye ne yakawo idanun Hamza dan he’s a very soft person yace “kana tunanin tasani” gyadamai kai yayi yace “kaima kasan that’s the only answer to yanda taketa kiranmu tun dazu clean those tears if our workers saw that kanason suyi tunanin Ya Imran zai iya aikata abin ne” girgixamai kai tayi daidai lokacin Musty na sanye da kayan sojoji da Haruna dakuma wani babban abokinsu police man su uku suka taho ganinsu yasa Musty yace “calm down you all Ya Imran din”? Ahankali Ibro yace “yana office working as if nothing is happening amman nasan deep down he’s hurting bama wanan ba Uncle Musty I believe the girl’s parent are here gasuchan” yanunasu ahankali Uncle yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un! Allahumma ajirni fi musibati” yakalli hannu da police man yace “kuje ku kutaho dasu lemme see him” yana maganan yawuce sama su Hamza suka bishi ahankali yabude kofan office din Abee, kallo daya Abee yamai yacigaba da aikin dayakeyi bazaka iya gane takamaiman reaction dake kan fuskanshi ba karasawa gaban table din Musty yayi ahankali yace “the girl’s parents are here” chack ya tsayar da typing din dayakeyi batare daya kalli Musty ba, anatse Musty yace “nace su Harun su taho dasu nan we need to speak to them and show them, but maisa baka fadamin komi ba eh Imran” dago idanunshi Abee yayi yama Musty wani kallo yace “me kake so nagaya maka takamaimai nace maka wani anonymous number sent me a text demanding 100M and this company’s document koyay releasing video tarayyana da wata da I know nothing about!”?

Knocking kofan akayi kallon Abee Mustafa yayi yace “gasunan” sanan yajuya yace “bude musu kofa Hamza” juyawa Hamza yayi ahankali yabude kofan Haruna da Police nan mai suna Abdul ne suka shigo sai Gwaggo data rike hannun Lujain gam dake lullube suka shigo tana hura hanci sai Baba dasu Baffa da Yayan Lujain sai Mama wuri harun yanuna musu kan dogon setin kujerun office din zazzamansukayi Gwaggo ta zaunar da Lujain da sheshekan kukanta kawai ketashi acikin office din itakuma Gwaggo tabi kowa na office din da kallo tace “nifa ba zama takawoni ba waye mutum dayaja sunan diyata yabaci aduniya ina mai kampanin?” Ahankali Abee da kanshi ke kasa yadago kanshi gently yazubama Gwaggo idanunshi da hakanan kawai taji magana ya makale abakinta.EPISODE 1️⃣1️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Hannunta Baba yakama cikeda damuwan dazaka iya gani kwance kan fuskanshi yace “Gwaggo dan Allah ki zauna kiyi shiru maza suyi magana, haba mana Gwaggo” Abdulhadi shima cikeda damuwan yace “dan Allah Gwaggo, dan Allah” cikeda bacinrai Gwaggo tace “aini banmasan kamilin mutun bane haka ba babba kuma, nadauka irin yaran nanne dake tashen balaga masu kudi da rawan kai amman wannan kalleshi nutsaste kamili dashi” hannunta da Baba keja alamun ta zauna yasa ta zauna kan kujeran tace “nayi shiru yanzu amman wlh idan baku karbanma jikata hakkinta ba wlh zan bude bakina ehe” ta zauna tana goge kwalla, dan murmushi Musty yayi yataho wajensu anatse yace “dudda nasan kowa hankalinsa atashi yake gaisuwan musulinci wajibi ne dan haka Assalamu Alaykum” atare dukansu su Baba suka amsa, Musty yace “nasan meke tafe daku amman dan Allah alfarma nake nema inaso kafin ku yanke hukunci kokuyi wani abu zan muku bayanin komi dakuma asalin nuna muku video CCTV camera dake nan akowani lungu da saku na company mu” gyadamishi kai su Baba sukayi alamun tom, yace “ni sunana Mustapha nine babban abokin Imran gashichan aboki nane tun muna yara yan kanana” yanuna Abee daya maida kanshi kasa dukansu suka kalli Abee, Musty yace “ga kannenshi chan Hamza da Ibrahim wayan nan kuma abokanenshi ne, Imrana nada yara hudu, biyu sun rasu tareda matarshi da akazo har gida aka kashe” ahankali su Baffa sukace “Allah musu rahama” Musty yace “sai biyu yanzu keraye, namijin nada shekaru 22, macen 21, nasan kuna mamaki maisa nake fadamuku haka inaso kusan waye Imran ne, bawai sabida Abokina bane, tunda nake bantaba ganin mutum mai kiyaye dokokin Allah kaman Imran ba tun yana kankanin shi mutum ne kamili nutsastse mai amana, abinda kuma yafaru tsakaninshi da yarku was nothing daya wuce kaddara kokuma nace samin akasi akayi wannan shine kawai abinda zance bari na kunna muku CCTV camera footage na ranan dasukazo makarantan kugani Ibrahim zokasa” zuwa Ibraheem yayi gaban babban tV dake office din yamakala flash dinshi saiga video yafara daga inda sukazo makarantan tundaga waje har zuwa ciki da lokacin datace zatai fitsari anajin maganan dudda bada kyau yake fitaba aka nuna inda ta tsaya tana juye juye dan bata gane bayin ba saitabi corridor tahau gudu tana ciro su waya da chocholate har zuwa inda ta bangaje Abee Musty yace “inaso kusaka idanunku akan wan nan mutumin” bayan ta wuce tai kwana aka nuno Abee yayi hanyar office nashi ya murda akulle sai kuma yay hanyar bayi saiga mutumin yafito, saikuma aka shiga lokacin da Lujain tashiga bayin da gudu daganan babu komi kuma sabida babu camera a bayi, saiga Abee shima yazo yashiga, Gwaggo ta gyara zama idanunta kaman zasu fito su sauka kasa, saiga mutumin yazo ya soka waya yana video jin muryan mutane yatafi yabar wajen kusan 2min da shiganshi saiga Lujain tabude kofa ta tsaya sai gashi anyo ball da jakanta da wayan ta tsugunna ta dauka ta goya ta gyara riganta tana waige waige tawuce dahar yanda mutanen nan suka mata kwatace saiga Ibrooo yazo har bayin yashiga rikeda key sannan aka nuna musu duka video Lujain a factory da yanda tai Plate har lokacin databar company su sannan ya katse.



Anatse Musty yace “abu na farko danakeso kugane kuduba lokutan da abin yafaru idan fasikanci ko wani abu sukayi dan wanan lokacin yayi yagama? Sanan akanme yana mai kampanin nan gabaki daya bawai shida wani ba bazai kaita office nashi ba inda akwai daki, bayi dakomi aciki sai nan bayin kowa bayin ma’aikatanshi Iyye? Koma bayin kowa ne zai iya sa security idan wani abu zaiyi yace kar wanda yazo banda haka kuma bayin maza ne ita meya kaita bayin maza dudda nasan yaran makaranta babu abinda waya baya sasu suyi tunda harta bugeshi batama tsaya ta kalleshi ba balle bada hakuri, abu na karshe video dakuke gani idan kunada wayanda sukasan computer zasu iya gayamuku cewa anyi editing dinshi da yanda kofan ke jijjiga da muryan karan datakeyi duka kari ne, saikuma shi wanan mutum dakukaga yay video yaturama abokina messege kan yanaso abashi miliyan dari da kampanin nan koyayi releasing video shi yana tarayya da wata shi yasan baiyi abu hakaba yay blocking kaman yanda kukaji abin nan kwatsam haka muma muka jishi kwatsam, dan Allah dudda dai babu abinda kaddarace bayasawa amman babu amfanin cewa wannan keda laifi ko wanchan keda laifi, munsan sunan diyarku yabaci haka shima nashi yabaci amman dan Allah kuyakuri, dan Allah abu baiyi dadi ba ko kadan” binsu Baba Gwaggo tayi da idanu daya bayan daya kowa jikinshi yay sanyi dan babu karya amaganan su bawai wanan ba dukansu sun kalli Abee baiyi kama da wanda zai aikata hakaba dan zai iya haifan Lujain dinma kuma itama tafadi abinda yakaita bayin tun kafinma suji bakin na mutanen nan, tsaf abinda tafadi shi suka gani a video, babu atom of lie aciki, kumama idan akace za’ayi blame yarsu ce taje bayin maza ita takai kafanta, this is just a common mistake da kowa can make ganin yanda sukai shiru babu wanda ya furta abu yasa cikin kumfan baki Gwaggo tace “ohhh barakuce komi ba”? Dasauri Baba yace “Gwaggo dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi gida kawai”. ”mtswwwwww” Gwaggo taja wani mugun tsaki ta mike tsaye batai wata wata ba ta jaye gyalenta data lullube Lujain dashi idanunta sunyi jajir fuskanta yay jaaaa sabida kuka jikinta dabare da jirwajen drinks fuskanta har kyallin dankon drinks yake tana kuka sosai tana wani kalan ajiyan zuciya tarike jikin kayanta gam da hannayen ta data dunkule kowa yabita da kallo adakin banda Abee da kanshi ke kasa, duk wani mai imani da zuciya yakalli Lujain saiyaji jikinshi yay sanyi, Gwaggo na rike da gyalen ta taka zuwa gaban table din da Abee ke zaune cikin ihu tace “kawani sauke kai kasa kaman sabon ango kalli jikana nace, dago kanta ta kalleta” ahankali Abee yadaga kanshi yadan kalli Gwaggo sannan gently yakalli direction din datake nunamai gabanshi na faduwa sauke idanunshi dasukai jaa yayi kan Lujain dake kuka sosai idanunta akasa yay shiru danji yayi zuciyanshi tai wani iri, komawa Gwaggo tayi wajen Baba ganin yana kallon Lujain din datace ta fizge paper da aka bama Lujain amakaranta tadawo ta ijiye gaban Abee tace “kaga yanda akama jikata wanka da lemu tundaga ka har kafa banda haka makarantan suka bamu takarda waisun koreta sabida fasika ce mugun iri zata bata musu sauran dalibai” fashewa Gwaggo tayi da kuka sosai daidai nan ta durkushe awajen ahankali Abee yasauke kanshi ganin yanda tsohuwar da akalla zata girmi Hajiyanshi da yan shekaru na kuka sosai agabanshi, Baba da Abdulhadi ne sukazo wajen da saurinsu zasu dagata tace “wlh kuka tabani zan daga muku nono awajen nan ku kayaleni kawai” tai maganan tana tashi takalli Abee da kanshi ke kasa sannan takalli Musty tace “kaga yarinyar nan dakake gani haka marainiya ce uwarta na nakuda kanta haifeta ta mutu agurguje akai operation aka cirota sabida wai tasha ruwan cikin wanda yamutu yarinyan nan dakuke gani saida tai kusan shekaru biyu acikin kwalban asibiti ni ke biyan komi ubanta wannan din nan dakuka gani” tanuna Baba dashima yasauke kanshi kasa tace “shi baida kudin biyan kudin kwalba duba sha biyar duk ranan duniya acirota daga kwalban wai mutafi gida, likita kuma yace ana cirota baifi tai awa ashirin da hudu ba zata mutu, mijina babansu mai kudin kauye ne daya mutu inada gado kap na saida gidaje na manya manya a binni guda hudu da shanaye na kauye haka na biya dubu sha biyar biyar na shekara biyu cur kafin acirota, nine komi na diyar nan tundaga zama a asibiti, abincinta, kayan sawanta da rainonta da komi ma, koda aka bani ita haka muka dawo gida yau lafiya gobe ciwo ko shigowa bayayi yadubata dan yanada wasu yaran lafiyayyu marasa ciwo, nikuma na nunamai zan iyama jikata mai ciwo gata tamafisu jin dadin duniya, saida yarinyar nan takai shekaru bakwai aduniya tafara makaranta” Gwaggo tashare idanu dan hawayen sinki tsayawa tace “bakuga yanzu tana shatara a SS2 ba bayan su Samira suna shekaru sha shidda sun zana jarabawan kare sakadire, amman ita har yanzu bata gamaba sabida ciwo, ni nasan wahalan danayi akan jikata nasan gumi rashin bacci rashin sukuni danasha akanta, har yau har gobe tunda tazo duniya bantaba baccin dare bantashi ba saita tadani, yau awayi gari sunanta yabaci kuce nai shiru koda akace zata mutu ban hakura akanta ba yanzu ne da lafiyanta kalau zan hakura nai shiru akanta wlh wlh Billahillazi La’ilaha Illahuwa bazata yuba ko laifinta ne ko laifinshi ne nidai nasan bakuyi fasikanci ba dan bangani alamu a jikinta ranan ina tareda ita data dawo daga makarantan ai kaima bakai kama da Babba mai lalata yaraba dan haka idan kunason zaman lpy abu dayan zan gayamaka shine ka auri jikata! Ka auri dan baran iya da raina da lafiya na inaji ina gani sunan jikata yabaci ba, tun yanzu a makarantan su kadai an mata wanka haka da koro uwa wacce aka kamata dumu dumu tana zina, ahanamini yarinya fita titi gudun kar adinga nunata wlh baran yarda ba, hanya dayace shine ka auri jikata!”



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAIJama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 1️⃣2️⃣



Kowa na dakin hatta Lujain din dake kuka sosai dashi kanshi Abee saida yadago kanshi yakalli Gwaggo jin abinda tafadi, cikin tsantsan nuna seriousness Gwaggo tace “eh haka nafadi, nace saika auri jikata! Duk abinda babba ya hango karami bazai hango ba, wannan video dakuka nunamin kokun watsashi aduniya mutane ba yarda zasuyi ba bazai wankemin jikata ba, hanya daya zai wanke jikata tastas shine ace kaidin mijinta ne da aure tsakaninku, daga masu gulma dashi usulin algugumi dan wutan jahannama daya yada video dana tabbata baku ganshi ba haryau saisuji kunya kaga ko banza yay aikin banza, shi bazai sami miliyan darin ba shibai samu kampanin ba” hannunta Baba yakama zaiyi magana Gwaggo ta fizge hannunta idanunta sunyi jajir tace “wlh wlh duk wanda yace saija dani cikinku saina tsine mishi albarka ubanme zaka gayamin lokacin dazata mutu ma baka tsaya mata ba yaune da aka kirata da fasika zaka tsaya mata? Nine komin Lujain, nine uwarta, nine ubanta, nine kakanta, kamin shiru kawai, wlh wlh saiya aureta akan wani dalili zaija sunan diyata ya baci kuma bazaiyi komi ya wanketa ba, wlh saiya aureta inba hakaba wlh wlh sai hukuma tarabamu, marainiyan yarinya na eh ku jibeta fa abin tausayi ubanta bai damu da ita ba sabida yaga batada mahaifiya, inda yau mahaifiyarta na raye Kunsan kalan tashin hankalin dazata shiga kuwa? Bayan kunsan rayuwa yakoma yanzu iskanci ado ne wajen namiji mace ce rayuwanta zai baci har abada, yanzu awannan video banda bayanshi anga fuskanshi eh? Yar yarinyar nan dai akaga fuskanta har akaga tana gyara riga, idanba aurenta yayi ba koya wanketa wazai auri Lujain iyye? Kufadamin wani namiji ne zai aureta? Wasu iyayene zasu bar dansu ya auri yarinyan da video fasikancinta ke yawo a yanar gizo? Shi yanzu bashi kwana biyu anmanta dashi itako fa? Namiji mutane barasu iya taranka ma itako Yar yarinya mace halama saidai tadaina fita danta fita tareta za’ayi amata duka a titi, yakukeso tayi? Matar ubanta kuma dama ba sonta takeba kaga gwara ka aureta naga kanada hankali kanada yara dasunma girmeta zaka rikemin ita amana koyau na mutu banda nadama dama kullum tunanina wazan aura mata da hankalina zai natsu dashi ashe kai Allah zai kawo mata amman ta wannan kaddaran” Gwaggo tafashe da kuka muryanta kawai akeji a duka office din ganin yanda take kuka kuma su Baba sun kasa mata magana gudun karta tsine musu yasa ahankali Mustafa yaje inda take tsugunnawa yayi yakamota kaman yakamo mahaifiyarshi hannu yasamata a fuska yana goge hawayen datake yace “dan Allah Gwaggo kiyakuri kidena kukan nan dan Allah sabida ni” ahankali tahadiye kukan tana kallonshi cikeda lallashi yace “Gwaggo kinga nan office neko wannan matsalan kuma matsala ce daya kamata atattauna agida kibamu address din gidanku anjima da daddare namiki alkawari dukanmu shima harda iyayenshi zamuzo sai ayi magana da kyau Gwaggo kinji Gwaggo amman yanzu kutafi, itama ku kaita gida tacire kayan nan kar wani abun yasameta maganganun nan da ake agabanta bai dace ba, kuma babu kyau yanda kike kuka agabanta, kece karfinta, kobaki hakura kitafi dan kowaba kiyi dan ita naga yanda kike sonta” juyawa Gwaggo tayi takalli Lujain dake kuka sosai har lokacin taji barata iya musuba tace “gidan mu na nan kwanan tipa a Gwarimpa idan kun shigo gida na biyar mai gate mai ruwan goro” anatse Musty yace “zamuzo anjima da daddare” tashi tayi tadauki gyalenta dake kasa taje wajen Lujain ta lullubeta dashi ta kama hannunta tadagata tace “muje Allah natare dake, nima ina tareda ke” su Baffa duk suka tashi, Musty yace “kaisu ta back door bata gaba ba sabida reporters” binsu su Ibro da Hamza sukayi dan kaisu sannan ahankali Musty yazauna tareda sauke wani ajiyan zuciya yana kallon Abee, Harun yace “wlh wlh idan aka kamo yaron nan I will make sure yay rotting at the worse Nigeria prison” Abdul yace “the guy is evil” daidai nan wayan Musty yashiga ringing ganin Hajiya ne yasa yakalli Abee da kanshi ke kasa yace “tashi muje gida Hajiya is calling” batare daya kalleshi ba yana kokarin fara typing yace “ban tashi daga aiki ba sai 4, and this is just 12:54” shiru Musty yayi yana kallonshi Allah kadai yasan yanda yake hurting right now amman bazai taba nunawa ba, ganin bakinciki Abee zai cusamai yasa yajuya yakalli su Harun yace “kumuje” saikuma yajuya afusace yadauki wayan Abee dake kan table yace “shima ka kwace idan ka isa” yawuce yafita fuuu daidai Hajiya na kara kira dauka yayi kafinma tayi magana yace “Hajiya gani nan zuwa komi yazo dasauki kada kidamu kanki hawan jininki yatashi” katse wayan yayi suna fita suka shiga mota sai gidansu Abdallah da Kausar sun dawo daga makaranta dudda sunada lectures ganin videos dake trending na babansu, Zainab data tafi daga ita har mijinta sun dawo, kofar gidansu yacika kaman anyi mutuwa dayan anguwa babu wanda baya sonshi a anguwan dukansu sun karyata guards na estate dinsu sun hana ko reporter daya ya shiga

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment