Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jallabiya ce ajikinshi fara da hula akanshi kofan Lujain ya kalla saiya karasa wajen anatse yabude kofan dago kanta tayi takalleshi suka hada idanu kafinma yamata magana ta mikeda sauri tawuce bayi dan haushin shi takeji daya hanata bin Gwaggon ta jiya dan jim yayi ya tsaya kaman mai tunanin wani abu saikuma yajawo kofan yarufe yawuce yatada su Abdallah yasauka kasa yajirasu suka fice tare zuwa masallaci.


Dayake yau asabar yadade amasallacin sai wajajen 7:00 nasafe yafito tareda Baba Liman dawasu jama’a na masallacin duk sun tsaya gaban masallaci suna magana kan Solar da Abee yasayoma masallacin daza’a fara aikin yau kaman an jefo mutun kawai wani saurayi suka gani agabansu ya tsaya yana sanye da jean da Riga bakake yasaka bakin facing cap da nose mask da bakin glasses dudda sunada yawa amman Abee yake facing, daya daga cikinsu yace “kaikuma Malam lafiya haka”? Tsugunnawa yayi agabansu ahankali tareda saka hannu yazare facing cap din kanshi, sannan yasa hannu yazaro shades din ya ijiye sanan yacire nose mask din ahankali ya ijiye kasa kafin gently yadago jajayen idanunshi dasuka kumbura suntum yakalli Abee dake kallonshi, dasauri jama’an wajen suka nunashi sukace “bakaine mutumin dayama Alhaji Imrana shairi ba ai munga hotonka a news” gyadamusu kai yayi ahankali sannan yahade hannayenshi yana kallon Abee dake kallonshi kuri saikuma kaman wanda ya haukace ya kwala uban kara cikin harshen turenci yace “mutanen estate din nan kufito dan Allah, gani nan nine nama Alhaji Imrana shairi nakuma kawo kaina da kaina” daidai lokacin Mandawari yafito daga cikin gidanshi zai tafi gudu chak ya tsaya yana kallon gaban masallacin da jama’a suka taru harda masu gadikan anguwan dakuma mutumin hakan yasa yakarasa wajen daidai Ibro shima yana karasawa wajen dan fitowanshi daga gidanshi kenan yazo zai shiga gidansu yaji muryan mutumin hakan yasa yashiga kiran Hamza, kallon duka mutanen dake kallonshi kuri yayi mutanen kuma suka cicciro wayoyinsu ana video yakalli Abee yace “dan girman Allah kayafemini wlh wlh bantaba sani hakkin wani abune mai girma ba sai bayan namuku kazafin nan kaida wannan innocent yarinyar” yay shiru dasauri Hamza yashiga kiran Uncle Abdul Police shikuma Ibro yashiga kiran Uncle Musty, cikin wani kalan yanayi na tsantsan nadama yace “tun bayan nai editing video nasaka a yanar gizo nakasa samin kwanciyan hankali dudda nai deleting amman a banza dan yarigaada ya yada duniya, bana iya bacci, banda sukuni banda natsuwa, kirjina da kaina wani kalan nauyi sukemin kaman an dauramini tankin ruwa akansu, tundaga ranan dana watsa video nan idanun nan nawa basu kara runtsawa da sunann bacci ba wlh wlh da wannan azaban gwara nakawo kaina ankaini gidan yari, nazone nafara rokonka da yarinyar gafara kafin nakai kaina dakaina police station dan Allah dan girman Allah kuyafemini, jama’a kutayani rokon gafara” yay magananan yana kallon kowa na wajen saikuma ya shiga babbaka kuka sosai kana ganinshi kasan babu peace arayuwanshi, ko’ina najikinshi rawa yake yace “wlh wlh koda wasa ba fasikanci sukayi ba nine na maida abin yazama haka da editing na computer, wlh nine nan na shirya komi nahada wlh wlh shairin shaidan ne da ruwan ido da son abin duniya yakaini na aikata abinda nayima Ogana mutumin daya bani aiki nake samu naciyar da yan uwana tasanadiyanshi shine nama haka dan Allah kuyakuri” kallon Baba Liman Abee yayi yace “Baba bari nashiga gida” gyadamai kai Baba Liman yayi hakan yasa yajuya zai wuce karaf mutumin yakama kafarshi tareda kwanciya akasa awajen flat yana kuka sosai yace “dan girman Allah ka yafeni kona samu na rufe idanuna yau ko baccin minti biyu ne nayi dan darajan Allah, wlh wlh bazan karaba shairin shaidan ne nasan nabata maka suna nabatama yarinyar suna kuyafeni” wani kalan murmushi Mandawari yayi ya gyara tsayuwa he’s enjoying the show koba komi yanzu ai zai sakin mai babe dinshi, daidai lokacin motan polisawa har guda uku suka shigo estate din suna jiniya, Abdul da Musty ne suka fito daga wani jeep na Musty, some police abayansu Abdul yace “you are under arrest for defamation of character, for threat, i advice you to keep quiet cus anything you say or do will be use against you in the court of law, kuyi arresting nashi” kara kankame kafan Abee yayi yana ihu sosai ihun da ko’ina na anguwan na amsawa mata har lekowa suke daga gidaje suna kallon abinda kefaruwa sai video ake, bambareshi akayi daga kafan Abee aka dagoshi sama Musty baiyi wata wata ba abunku da soja yabashi two sided mari at a spot yace “dan Shegiya zakaci ubanka yau” dasauri polisawan dasuka dagoshi suka sakeshi ganin Musty soja ya mareshi, wani kalan kwashemai kafafu Musty yayi yazube awajen kanshi yay wani kalan mugun buguwa zai kara kaimai duka Abee yakama hannunshi gam hakan yasa cikin fushi Musty yace “ku barni natafi dashi gad-room a barrack gobe nakawo muku shi police station wlh ko amafarki your generation to generation to more generation bazasu taba tunanin batama wani sunaba sabida yanda zan dispilaka kai kasan sunan wane kabata kasan waye Imran kuwa? Did you know how many lives Imran ya chanza including mine how dare you” azuciye Musty ya yunkura zai kara kaimai duka amman yakasa sabida yanda Abee yamai riko mai kyau, kaman jira yan anguwan suke sukace “ai wlh mumishi duka kafin atafi dashi, jungle justice in his life bazai kara tunanin yada abun kazafi ba yana batawa mutane suna babban mutum haka dakeda manyan yara” hannu Hamza yashiga gyarawa shida Ibro zasu sa hannu a lallasashi wani kallo Abee yamusu yace “ku wuce gida” ba musu duk suka juya batare da sunji dadi ba sukai gida, Abee yakalli Abdul yace “kutafi dashi Abdul nobody should touch him again” yay maganan yana kallon mutanen dake shirin dukanshi, bada go ahead Abdul yayi aka wuce dashi mota Abdul yabisu Abee yakalli Musty da ranshi ke bace yana kallonsu yace “let’s go” sannan yasakeshi, sai alokacin Musty ya iya motsi dan Abee akwai karfi, binshi Musty yayi suka wuce Mandawari yabisu da kallo wani kalan mugun kishin Abee yake kaman ba gobe duk ta yanda ya kalli Abee Abee yafishi in any way, what did he do how did he earned this much respect daga jama’a? Shi dudda yana footballer one of the best yadawo anguwan nan babu maibi takanshi saidai masu gadi ne ma ke tambayanshi for selfie, what’s so special about this man da ake sonshi sama dashi mai about 400M followers a just IG, har neman Abee yayi a social media amman yaga he’s not on any of those social media platform, wani kalan kishin Abee yake dabazai iya misiltawa ba baitaba haduwa da mutumin dayaji existence nashi poses as a threat to him ba sai Abee, yarasa sukuni, yanda Abee yake nuna baimasan dashi ba is what is killing him more, yaso bayan yama Abee maganganun nan Abee ya nemi bala’i dashi ko yasa acireshi daga community kokuma wani abu dazai bashi liver yay bura’uba dashi amman no baimasan ko yana rayeba.EPISODE 4️⃣1️⃣




Falo suka shiga a tsaye sukaga su Hajiya da Ibro da Hamza da Abdallah da Maman Aneesarh sai Kausar dan Lujain na sama tun safe data fito ta gaida Hajiya takoma waje Abee yasamu yazauna anatse yasauke wani kalan babban ijiyan zuciya dayasa har Musty saida ya kalleshi, Hajiya tace “Musty an wankesu? Yanzun nan Hamza da Ibraheem kebani labari” cikeda farin ciki Musty yace “Alhamdulillah Hajiya komi yazo karshe Abdul suntafi da yaron police station ma nasan anjima kadan zamuga broadcast” Hajiya takalli Abee dan murmushi kadan yasaki yakalli Maman Aneesarh da Kausar yace “I need my breakfast” wani kalan dadi Kausar taji rabon dataga Abee haka harta manta, zama Musty yayi kusadashi suna breakfast din tare sai kallon Abee yake idan akwai wanda yasan Abee sama dashi aduniyan nan yana ganin saidai Hajiya datake mahaifiyarshi dan tun suna yara tareda Abee suka taso kuma yasan menene azuciyan Abee yanzu haka alkawari daya zaiyi shine bazai taba bari Abee yarabu da Lujain ba Allah yamai kyautan taba sai inda karfinshi yakare yana cikin breakfast wayanshi yay kara hakan yasa yadauki wayan yakalli screen din ya amsa wayan chan yace “alright gani nan zuwa” ijiye wayan yayi Musty yace “ina zaka”? Ahankali yace “akwai some UK agent dazasu so daman yau, wai sunzo zanje nagansu zaka” girgizamai kai Musty yayi yace “bazani ba, mikewa tsaye Abee yayi yakalli Kausar yace “kawomin key motana adaki” gyadamai kai tayi tawuce sama tadauko key tasauko tabashi karba yayi yajuya Musty yabishi yace “ahaka zaka kaman wani black arab”? Gyadamai kai yayi yace “yes” haryakai mota zai shiga Musty yace “best friend” tsayawa Abee yayi yakalleshi, Musty yace “tell me what’s on ur mind” wani kalan kallo Abee yamai yace “kafi kowa sanin what’s on my mind” dasauri Musty yace “Imran menene aibun yarinyar nan? Why do you wanna leave her? Batada any matsala rabon danaga mutum this innocent kaman Lujain harna manta, Gatanan gradually she’s fitting into your family, batada matsala da su Kausar yaranka ko mahaifiyar ka, maisa zaka rabu da ita please accept Lujain as your wife” tunda yake maganan Abee ke kallonshi yace “ka isa kasani dolene”? Shiru Musty yamai yana kallonshi Abee yace “do you expect me nai accepting wanchan jaririyan yarinyar amatsayin mata for God sake Mustafa my last born ta girmeta what is that child abuse or mene”? Baki Musty yabude zaiyi magana Abee yadagamai hannu yace “ko yanzu ma dan fitan nan daya kamani ne Allah yakaimu anjima after isha’i dakaina zan kaita gidansu komi yakare” yana maganan yabita gefen Musty yabude motanshi yashiga yaja motan yabar gidan Musty yadade tsaye yana kallon gate din anatse yace “Imrana I am your best friend, kamin komi aduniyan nan, I’ve watched you suffered for good 13yrs, bazan taba bari ka koma rayuwan nan ba, bazan taba bari karabu da Lujain danasan she’s the best thing right now in your life ba dan bazaka taba samin matan dazaka samu peace kaman da ita ba” yana tsaye wajen aka bude gate Anty Binta ne tashigo da jeep dinta ganin mijinta tsaye yasa takarasa parking tafito tace “Baby ya akayi” fuskanta yakalla yace “Wifey inaso kibani honest answer not because of me tell me the truth kinason Auren Yayanki Imran da Lujain”? Wani kallon kallonshi tayi ganin how serious he is yasa anatse tace “Husby inason Auren su sabida banjin Ya Imran zai iya samin mata kaman Lujain ba, she’s fragile sweet and easy to handle gata yarinya kuma Lujain batada matsala, her whole life is just she and her grandma, I love them together, maisa kamin tambayan nan yace zai saketa ne sabida ankama yaron”? Gyadamata kai yayi anatse yace “Wifey I have a plan, but kafin nai plan kune yan uwan Imrana zan biku gabaki dayan ku one by one na tambayeku idan kuna sonshi da Lujain inhar dukanku kunaso I will do something today and I will need your support” dasauri Anty Binta tace “count me in” daidai nan Ibraheem da Hamza suka fito alamu yamusu dasuzo hakan yasa suka taho, Musty yakallesu yace “kunason zaman Imran da Lujain”? Dasauri Hamza yace “sosai ma Uncle Musty, wlh I love Lujain she’s so calm batada magana, ni kawai ina sonta sosai” Ibrahim yace “konima haka I wish Ya Imran zai sota sosai danafi kowa jin dadi but har yanzu he’s not ready to accept any woman”, murmushi Musty yamusu yace “kuwuce kutafi” wucewa sukayi shida Anty Binta ciki, a dinning yaga Kausar na kokarin kwashe plate karasawa yayi yana tayata yace “muje nakai miki kitchen Auta na” murmushi tayi tace “to second Dad” saida sukakai kitchen yana ijiye plates din batare daya kalleta ba yace “kinason zaman Abee dinki da Lujain” dasauri tadago kanta takallai folding hannunshi yayi akirji yana kallonta ahankali yace “Kausar kinason yanda Babanki baida peace of mind, you are not a small girl Kausar kema yau ko gobe zaki iya aure at any given time, why don’t you wanna understand your father that gives you everything? Inhar yaga kunason Lujain he will accept her too bakisan cewa idanma kina tunanin sabida kin girmi Lujain ne yasa baki sonta yarinya irinsu sune babanki zai iya ya tsawataar mawa kuma taji, yace tayi tayi tabari tabari but babba bazai taba iya controlling nata ba, give me ur answer Last Born kinason rayuwan Babanki da Lujain ko a’a”? Ahankali tace “da banaso Second Dad but yanzu inaso banso Abee ya auri wacce zata wahalar dashi gwara Lujain kaga tsoronshima takeji” murmushi yamata yace “Allah miki albarka” Abdallah da Maman Aneesarh duk ya tambaya ta siyasa suma sukace sunaso dakin Hajiya yashiga yasameta zaune bakin gado tana waya zama yayi akas saida takarasa wayan yakalleta yana murmushi yace “Hajiya kinason zaman Lujain da Imrana”? Murmushi Hajiya tayi tace “inaso sosai Musty, sonake ma yadawo muyi magana nasan nace I want to support him amman harga Allah banso yace zai rabu da yarinyar nan” murmushi Musty yayi yace “in sha Allah bazai rabu da ita ba Hajiya bari naje anjima kadan zan dawo” to adawo lpy, bude kofa yayi yafita afalo yaga Anty Binta zaune fita yayi hakan yasa tabiyoshi dasauri tace “ina zaka?” Dan jim yayi yace “I have a plan but it involves Docton Imran bari naje nasameshi baran dade ba” gyadamai kai tayi tareda murmushi motanshi yashige itakuma takoma cikin gida sama tawuce direct dakin Lujain tayi kwance taganta akan gado daure da towel tana rikeda hook nata na school alamun karantawa take ganinta yasa Lujain taji wani dadi ta tashi zaune tace “ina kwana Anty” murmushi Anty Binta tamata tace “wai wannan kan naki da santsi dukya warware Lujain tashi kisa kaya muje na kaiki saloon a tsefe awanke baraki kitso ba sai a gyara miki kumba” dasauri ta sauka dagakan gado tana murmushi tace “dama nagaji Anty” shiryawa tayi sharp sharp tasa dogon hijabinta sukama Hajiya sallama suka tafi saloon.EPISODE 4️⃣2️⃣



Wuraren 2 suka fito daga saloon din an gyaramata gashinta anyi stretching anyi parking sai kanshi yake an gyaramata kumbunanta, kallonta Anty Binta tayi tace “kin iyashan Popsicle”? Gyadamata kai tayi dasauri tace “eh” murmushi Anty Binta tayi tace “sweet tooth, muje nasaya miki” wani shago suka shiga tasaya mata sannan tasayama su Kausar sannan suka fito suka shiga mota suka dawo gida kusan tare itada Musty suka iso gidan parking yayi yafito daidai itama tafito haka Lujain murmushi yayi ganin Lujain yace “wifey ina kika kaima Imran mata”? Dan dariya Anty Binta tayi tace “saloon nakaita kitsonta duksun warware shine mukaje aka kawance kan gabadaya aka gyara” murmushi yayi ahankali Lujain da adan kunyace ta lallai tana sunnar dakai tace “ina yini” murmushi yayi yana kallonta yace “lafiya lau Lujain je daki zan magana da Anty taki gatanan zuwa” gyadamai kai tayi tawuce yakalli Anty Binta yamata alamu data shigo cikin mota shigowa tayi shima yashiga tace “Husby wai ina kaje I mean mekaje yu da Doctor Ya Imran”? Dan shiru yayi yace “Dr is the only person that can help us at this point yadawo kaman family” yayi dan shiru saikuma yasa hannunshi acikin aljihun gaban riganshi yaciro wani tablet kwaya daya rak yabama Anty Binta kallon kwayan maganin tayi tace “what is this”? Dan shiru Musty yayi ahankali yace “ke kanwar Imran ne bai kamata ina fadamiki sirrin yayanki ba but you are the only help danake dashi” shiru yakarayi ahankali yace “Wifey inaso Imran ya sad…..” saikuma yadanyi shiru kafin ahankali yace “I want Imran yay consummating aurenshi da Lujain!” Dawani kalan sauri Anty Binta ta kalleshi gyadamata kai yayi yace “that’s the only way dazamu iya saving this marriage inhar abu ya shiga tsakaninsu nasan bazai taba sakinta ba” yay dan shiru saikuma ahankali yace “after dogon explanation da magana Dr shi yabani wannan kwayan maganin daya tal dakike gani shima yace aure will help Imran sosai he needs a woman, he’s a full grown up middle age healthy man yana neman 14yrs ba mace kenan karyazo ya haukace” cikeda dan tsoro Anty Binta tace “to mene maganin zai sashi”? Ahankali Musty yace “I don’t know wlh exactly but nasan dai zai tadamai da sha’awa ne dabazai iya bearing ba baya neman matan banza dan haka dole yaje wajen matanshi ta sunna this is just my saying oo Dr bai fadamin takamaimen abinda maganin yake ba, but yace to avoid kar Imrana ya zargi kowa abashi maganin around 7 dan 3hrs maganin yake dauka kafin yay taking effects, kinga around magrib zaki samai a shayi dazai sha anan falo ko” gyadamai kai Anty Binta tayi saikuma tace “yaya zamuyi da mutanen gidanmu Lujain is v……..” saikuma takasa karasa maganan, dasauri Musty yace “shima is under my control duka yaran gidan nan kap hatta Maman Aneesarh kwasansu zamuyi zance zan kaisu cinema, Hajiya kadai za’a bari agidan akasa, around 9 zamu tafi idan yaso dagachan zan ce musu yau kowa agidana zai kwana dama duk basu zo sabon gidanmu ba cus banson situation dazasusan something happen tsakanin Imran da Lujain” dasauri Anty Binta ta gyadamai kai zuciyanta na bugawa hannunta yarike yace “we got this babe, I am helping my best friend and you are helping your brother, we are saving the most stubborn man dana sani aduniyan nan” atare dukansu sukai murmushi, ahankali Anty Binta tace “I wish I can have a friend like you Husby” murmushi yayi yace “I am nothing wlh wish to have a friend like your brother Imran not me” murmushi tayi tashige jikinsu tace “Allah yabamu lada and May this plan be successful” murya chan kasa yace “Ameen baby hold this magani well nasan anything 4 ko 5 zai dawo gida I will be with him har dakinshi baran bari yay any rubutu ba balle yamata saki zamuje magrib bazan bari yazauna ba zamu dawo da sumin cin abinci that’s when you will bring the tea a two cups kibashi mai magani kibani empty mara magani” gyadamai kai tayi ahankali yace “sauka muje ciki namusu announcing cinema thing din fa ticket din nan tayani kwasa agaba” kwashe ticket din tayi suka fito suna shiga falo kowa na falo banda Lujain dataje sama Musty yace “tantadaaaaa yau munada all family movie night, Ibro tell ur wife to get ready around 8:30 9 zamu tafi dukanmu Hajiya ne kawai bazataje ba nasani” hannu Hajiya tadaga tace “aikam inani ina zuwa wani kallo da idanun nan danake fama dasu” dariya akayi Kausar tace “Second Dad thank u wlh dama mun dade ba’a fita damu ba” Anty Binta tace “theater gabaki daya ya karba mana sai ashirya” sosai sukaji dadin zancen da rabon dasuyi having fun haka tun kafin kaddaran da yafada kan babansu, zama Musty yayi yace “kubani abinci wlh yunwa nikeji Hajiya”, Hajiya tace “Binta bama mijinki abinci”.



Wuraren 5 Abee yashigo gidan parking yayi yabude kofa yafito he’s so happy yau jinshi yake sakat abinda ke kanshi ya sauka maida kofan yayi yarufe yawuce ciki, afalo yasami kowa yakalli Abdallah ya wurgamai car key yace “jeka kawo abubuwan cikin mota is for you guys” gaidashi kowa yayi da kai ya amsa ya gaida Hajiya sannan yawuce sama binshi Musty yayi dasauri yana shiga cikin dakinshi shima Musty na binshi ciki yace “Ya Meeting din”? “Fine” ya amsa yana shiga cikin closet saikuma yafito yawuce cikin bathroom kwanciya kan gadonshi Musty yayi yana daddanna waya yadade cikin bathroom sannan yafito bayan yayi wanka daure da bathrobe yawuce closet nashi nan ma yadade ciki shiryawa yayi cikin jean black dawata maroon t-shirt sai kamshi yake zubawa yay wani kalan kyau dake shiga ido, Musty yanunamai abincin da aka kawo a tray yatsine fuska yayi yace “I will eat later” Musty yace “waikai me abinci yama I am sure tun safe bakaci komiba” hararanshi yayi yakalli agogon bango yace “tashi muje mosque” tashi Musty yayi suka fice tare ana magrib Musty yatasashi agaba suka dawo gida afalo suka zauna Anty Binta tawuce kitchen maida kofan kitchen din tayi tarufe tazuba musu shayi a cup sannan ta balle maganin tajefa a cup na Abee nan da nan maganin ya narke cokali tasa takara juyawa sannan tasa a tray tadauki tray tafito tana tafiya ahankali Gaban Abee taje tadauki cup nashi tadauramai akaramin coffee table dake gefenshi tace “Ya Imran ga shayin ka” murya chan kasa yace “thanks” sannan tawuce gaban Musty ta ijiyemai nashi cup din a coffee table dake gabanshi sannan tawuce tace “bari muje mu shirya” gyadamata kai yayi, Hajiya tace “kaji wai cinema zasuje Imrana, Mustafa da asaran kudi hall gabaki daya ya kama musu” dan dariya Musty yayi yace “Hajiya inada wasu kannai ko yara sama dasu ne, ba asaran kudi bane let them go out today and have fun” tabe baki Abee yayi yadauki tea shi yakai baki batare daya sa bakinshi a zancen ba, tass ya shanye tea Kausar tasauko sanye dawata doguwan Riga na abaya black tai kyau tazo gaban Abee tace “Abee kayan nan sunyi” kallonta Abee yayi ahankali yace “yes” murmushi tayi tajuya takoma sama daidai ana kiran isha’i tashi Abee yayi lokacin Ibraheem yashigo gidan shima ya shirya tsaf da matanshi da yaranshi biyu akunyace matanshi ta gaida Abee da katon cikinta haihuwa yau ko gobe amsawa yayi batare daya kalleta ba yamikama yaran hannu alamun sallama sakamai hannun sukayi sukace “Abeeeee” tareda rungumeshi daukansu yayi tareda dan murmushi yace “how are you”? Dasauri Babban Muhammad yace “Abee the coco pops u bought for us has finished” gyadamusu kai yayi yace “okay” karamin yace “Abee second Dad is taking us to cinema will you go with us too”? Girgiza musu kai yayi anatse yace “Abee has some work but I promise to go next time” murmushi yaran sukayi sukace “okay” murmushi kowa na falon yayi harda Hajiya Musty aranshi yace “I can’t wait Lujain ta haifomaka little baby Kausar tai kanwa ko kani” kaman Abee yaji abinda yace kallonshi yayi suka hada ido ya sauke yaran kasa dan suje wajen Hajiya yace “let’s go” ficewa sukayi dukansu harda su Abdallah da Hamza dasuka shirya suma duk sunyi kyau.EPISODE 4️⃣3️⃣

LAST FREE PAGE
wa.me/+2347012181461

Chat me up anan


Toh jama’a anan nakawo karshen free pages na wannan littafin nawa mai suna SAKON SO.

Idan kinason cigaba da karantawa all you have to do is pay 1k into 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK

Send evidence of payment to my telegram or WhatsApp via 07012181461.

Akwai groups guda biyu na yan 1k Episode guda biyu kullum.

Akwai group na 500 EPISODE guda daya kullum ake posting

SUNDAYS-WEDNESDAY ✍🏻

Thank you❤️❤️❤️
Don’t miss this book for anything in this world😍



Karasa tajemata gashin Anty Binta tayi tamata parking dawani pink ribbon mai kyau yanada butterfly ajiki na art, tace “yauwa gashinan gashin yadawo daidai harkin hargitse shi Lujain abinda aka gyaramiki dazu dazun nan tashi kiyi wanka kizo” tashi Lujain tayi tana murmushi sabida yanda Anty Binta ke magana, Anty Binta tafita daga dakin dawani cup tadawo nawani magani tana murmushi ta ijiye tana juyawa sabida yahuce fitowa Lujain tayi daure da towel Anty Binta tace “yi salla kizo” dadduma tahau tayi salla tana idarwa tazo wani red bubu irin masu manyan gyalen nan Anty Binta tabude sabo fil a Leda tamika mata tace gashi ki feffesa turare kisaka bari nadauko sugar nazo maganin nan ba sugar tana maganan tafice rigan Lujain tadauka taje gaban madubi feffesa turare tayi ajikinta masu dadi sosai sannan tasaka rigan batare data saka komi akasa ba daidai nan Anty Binta tashigo tsayawa tayi tana kallonta sabida yanda jan bubu rigan yamata kyau tace “wow red abu namiki kyau Lujain zokisha” zuwa tayi Anty Binta tabata magani a cup bayan tasa sugar shanyewa tayi tass tana tabe baki Anty Binta tadan buge bakin tace “ni bantaba ganin yarinya shagwababbiya irinki ba Lujain duk zama da Gwaggo ne yasa haka rainon Kaka kawai” dan dariya tayi kadan batace komiba Anty Binta tace “rikemin wayan nan zauna kijirani ina zuwa you can play game idan kinaso” karban wayan tayi tazauna bakin gado tana kokarin shiga game na candy crush.

Shigowa gidan sukayi around 8:30 Abee yakalli Musty yace “lemme go na kwanta nagaji” bai jira amsanshi ya yakalli Hajiya yace “saida safe

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment