Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abee yakawo zai bashi kaman jira Mandawari yake with so much disrespect and humiliation yajanye hannunshi yarugume hannunshi a kirji, hannunshi Abee yakalla daya kaimai su gaisa dake nan acikin thing air ahankali yaja hannunshi ya maida jikinshi yazubama Mandawari idanu, baisan mesaba jiyayi gabanshi yafadi amman daurewa yayi with so much courage yace “you took something that belongs to me Mr Imran, kuma na tabbata fada da kananun yara irinmu dazaka iya yara damu is not ur thing dan haka I come to tell you in peace ka saki babe dina daka daura lokacin da abin nan yasameku I wasn’t in Nigeria yanzu nadawo I want my woman back I want to marry her” wani kalan kallo Abee yamai saikuma yay folding hannunshi akirji yana kallonshi, Mandawari yace “yanzu ma nasameka ne namaka magana out of respect inba hakaba” anatse Abee yace “mezakayi”? Kallonshi Mandawari yayi yace “I will defame you! I will scatter everything you’ve ever stood for” dan murmushi Abee yayi iya lips nashi sannan yajuya yawuce anatse wani abu Mandawari yaji ya tsayamai awuya kaman yabishi ya chakamai wuka sai yanzu daya tsaya gaban Abee face to face kawai yaji yawani tsaneshi wani kalan mugun kishi nacinshi dan ko kadan mutumin doesn’t look old gashi he’s so handsome gashi so neat kayan dayake jikinshi tundaga kan slippers na kafanshi are designers, kamshin dayake koshi dayake takama yafi kowa using turare baikai Abee kamshi ba, wani kalan dunkule hannu yayi yadaki iska sannan yajuya yawuce gida, akan benci mai gadi yasami Olusay zaune Olusay na ganinshi yamike tsaye yace “Man nasanka to be stubborn tun muna yara, but idan kasan kazo anguwan nan ne to make trouble ni zan tattara nabarmaka gidanka, this man baida any business to do with you and yet you want to make trouble dashi akan mene ubanme yamaka eh” cikeda ihu Mandawari na tafarfasa yace “he stole my woman from me abinda Yamin kenan” cikin sauri Olusay yace “woman din dabaka taba cema kanaso ba or respond to her messages, this is not good Man, trust me this is not good at all” hannu Olusay yakai zai tabashi wani kalan bugemai hannu yayi yawuce ciki yana tafarfasa tsayawa Olusay yayi so worried Kodai yakira Mom yafada mata abinda ke faruwa ne amman yay haka Man will never forgive him, shi yasan Man always view her message dan shinema yafadamai about Lujain amman baitaba fadamai yana sonta ba saima wulakanci dakin kula yarinyar, saida wannan sex tape da news na aurenta ya yada social media shine fa tundaga ranan Mandawari yafara having sleepless night.
***


Falonsu yashiga da sallama chan kasa Musty yagani da Harun sunacin tuwo, Hajiya kadai yagaida yamusu mugun kallo yawuce sama, Hajiya tace “kudai kuna kokari da wannan abokin naku” tashi Musty yayi yace “cigaba daci Harun bari najawoshi ya sauko kasa” daidai Abee na zama gaban desk nashi Musty nashigowa ciki yace “waikai tunda kayi auren nan nakasa gane kanka” wani mugun kallo Abee yamai yace “I told you Musty, kasanni Musty banson aure let’s not even go there idan wata ne maybe I can even manage Auren na zauna not Auren little girl like this da dan karamin yaron saurayinta zai tareni this night yana threatening dina, what is all this rubbish what kind of mess kuka sani ciki haaa? At this stage some stupid small boy da aka haifa jiya jiya zaizo yatareni yanamin maganan banza can you imagine”? Yanda Abee ke magana zakasan he’s really pissed hakan yasa Musty yace “wait Imran I don’t understand me kake cewa? Waya tareka wani boyfriend kake magana”? Cikin dan ihu kadan Abee yace “her boyfriend dashine the reason behind abinda yasa taje toilet na maza mana taxauna tana kallon live video nashi Muhammad Mandawari” shiru Musty yayi yana kallon Abee dan shi dama dayashigo anguwan dazu Hamza ke fadamai sunyi neighbor wani footballer baima tsaya jin waye ba sabida Hajiya daketa kwalamai kira, one thing da Abee ya tsana to the core arayuwanshi is raini ya tsani raini da rashin kunya, dafe kanshi yayi saikuma yadago yace “how far about the tracking dasu Abdul keyi idan bazamu iyaba zan turama contact dina number a USA cus I can’t wait for all of this shit to be over narabu da yarinyar nan data shigo rayuwana tahanani kwanciyan hankali I am tired Musty I am tireddd” yay maganan yana kabar da keys na motanshi da wayanshi dake kan desk din kasa, dasauri Musty yazo yadafashi trying to calm him down yace “calm down Imran, fushinka is not good for you and kowa dake tareda kai, calm down please” dan ajiyan zuciya Abee yasauke ahankali Musty yace “what happen tell me” kaman Abee bazaiyi magana ba saikuma yafadamai komi shima Musty baci ranshi yayi yace “I don’t care koshi waye what gave him the gut dazai tare soja yanamai magana anyhow, lemme go and lock him up wlh sainai uselessing kafafuwan nan nashi na kwallo ” Musty yazo zai wuce dasauri Abee yarikeshi yace “common mu yarane dazamu biye musu, he’s just a child let him be please, is not easy karasa abinda kake so cikin dare daya to some extend I understand how bittered he’s” dasauri Musty yace “her grandmother told me baitaba kulata ba all this childish crush Lujain kemai” yatsine fuska Abee yayi yace “that’s non of my business, I’ve taken care of her, nasata a school da babu wanda zai bully nata, nayi securing waec nata and neco I am just waiting waiting for the whole thing to be over nagaji” yay maganan ahankali, murmushi Musty yamai yace “ya isa tashi muje falo muci tuwo tare” yatsine fuska Abee yayi yace “baran ci ba” Musty yace “Allah saikaci” badan yasoba yatashi yabishi suka fita falo tare, sai wajajen 11 sukabar gidan hakan yasa yarufe ko’ina yawuce sama ko dakin da Lujain keciki bai kalla ba.EPISODE 2️⃣9️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Around 1 tafarka daga bacci sabida mugun yunwan datakeji rabonta dacin abinci tun lunch dataci a school shima ba sosai ba taci, yanda Mandawari yagaya mata tacika kiba taje tarage kiba kafin takulashi yadameta tayi alkawarin zata rage kiba, barata dingacin abinci sosai ba, kulolin abincin da aka kawomata jiya da daddare takalla amman taki zuwa wajen, kife cikinta tayi ahankali tanajin yanda cikin ke sokanta amman tadaure tana lumshe idanu, ganin yaki denawa yasa ta tashi tadauki bottle water tabude tasha sosai sannan takara kwanciya tana shafa cikinta da hannunta dake cizonta cikin wani kalan murya tace “wayyooo cikina wauyooo” juyi kawai take akan gado sai wajajen 3:00 bacci yay awon gaba da ita, 4:30 Abee yafito, tada kowa yayi saida yatada Kausar yace “jeki tashi yarinyar nan” gyadamai kai Kausar tayi tawuce tafita shima Abee yafita yasauka kasa.

Bude kofan dakinta Kausar tayi takarasa gaban gadon tana mamakin yanda koda yaushe tana daure da towel bubbuga gadon tayi hakan yasa tabude idanunta ahankali Kausar dake kallonta tace “Abee yace kitashi kiyi salla” tashi tayi ahankali ta zauna itakuma Kausar tawuce tafita daga dakin, mikewa tayi ahankali tashiga bayi wanka tayo tafito tai salla sannan ta tashi tashiga saka kaya tana tunanin yau jumma’a zata huta, kayan makarantan ta tasaka batare datasa safa ko hulaba tafito sai kamshin turarukan data fesa take masu bala’in dadi, gaban dakin Kausar taje tadade tsaye sannan tabude kofan ahankali tashiga ciki Kausar dake saka dogon Riga tajuyo dasauri takalleta ta tace “mehaka kika shigo mini daki” girgiza matakai Lujain tayi saikuma ta taho cikin dakin zuwa gabanta ahankali tace “mesa kika tsaneni baki sona”? Tai maganan tana kallon fuskan Kausar hararanta Kausar tayi takarasa saka riganta tajuya tadauki dan kunne tasa ahankali Lujain tace “eh mesa” juyowa Kausar tayi dasauri tace “kinason ki sani, to sabida ke sunan Babana Abee yabaci aduniya, because of you mahaifina is suffering, bayan komi laifinki ne, kene kikazo kampanin shi amman ba’a duba hakaba sannan aka kuma kakabamai Auren ki akanshi sabida mugunta irin naku da yan gidan ku” hawaye ne yazubo daga idanun Lujain dasauri tasa hannunta ta goge takalli Kausar tace “kinsan mesa naketa son miki magana sabida ke kadai nagani agidan nan datake nan kaman matsayin yayyuna su Ya Samira, kin dauka I am happy with all this ne, kaman zan mutu nakeji, nima nagaji nagaji dakomi” saikuma tafashe da kuka wani iri Kausar taji dan tanada bala’in tausayi dauke kanta tayi tace “nidai me kikazo mini adaki mekikeso” hannunta Lujain tasa tashare hawayen fuskanta tass tace “sonake kiduba min recipes na rage kiba awayanki kibani narubuta inaso narage kiba ne” dan kallonta Kausar tayi ganin yanda take kallonta yasa Kausar tace “kiba halitta ce, haka Allah ya yiki maisa kikeson wahalar da kanki”? Girgiza kai tayi tace “nidai dan Allah kidubamini inda inada waya bazanma zo wajenki ba” bala’in tausayi tabama Kausar wayanta tadauka tashiga google tamata browsing sannan tabata wayan da memo da byro tace “write it down” zama tayi abakin gadonta tashiga kwafewa da saurinta Kausar duk tana shiryawa tana kallonta komesa takeson rage kiba oho kuma kiban yamata kyau sosai da chubby kumatunta yanzu idan tarage kiba tai muni fa oho itadai baruwanta, gama rubutawa tayi tamike tsaye tana ijiyemata wayan akan gado tai murmushi sosai dayasa Kausar ta tsareta da idanu sabida yanda dimples dinta ke lotsawa tace “thank you Kausar” sannan tawuce tafita, dakinta takoma tadauko jakanta da hijab tashiga saukowa lokacin babu kowa a falo jakan ta ijiye akan kujera sannan takalli kitchen dinsu datagani abude tawuce tashiga ciki Anty Binta datagani tsaye tana aiki yasa tai murmushi tabi kitchen din da kallo ganin yanda tahadu tace “good morning” murmushi Arty Binta tayi tace “kin tashi lpy Lujain mekikazo yi a kitchen”? Dasauri tai wajen Anty Binta paper tanuna mata tace “weight loss smoothie zan hada” kallonta Anty Binta tayi tace “kewayace miki kirage kiba so kike Gwaggon ki taganki tace bamu baki abinci” murmushi tayi batace komiba Anty Binta tace “ai shikenan fruits duka na fridge ga blender anan” dasauri tai fridge, celery tadauko, da green apple, cucumber dakuma ginger tahada tai blending Anty Binta sai kallonta take one thing datagani is tanada tsafta kaganta zaka dauka bata iya komiba amman ta iya danta yayyanka abinta tasa a blender ta blending Anty Binta dakanta tabata bottle mai kyau da straw tajuye aciki tace “Allah bada sa’a nidai banga me zaki rage ba” dan turo baki tayi tace “flat tummy da fats” dan hararanta Anty Binta tayi tai murmushi takai bittle na baki tazuko tasha taba tabe baki ko kadan baimata dadi ba amman sabida yanda takeso ta burge Mandawari rufe ido tayi ta shanye tass sannan tawanke giran da blender dasauran kwanukan wajen Anty Binta tace “debi chips naki kije dinning kici” girgiza mata kai tayi tace “a’a ni nakoshi” wani kalan kallo Anty Binta tamata tace “Lujain what’s all this kaman wacce tai wani mafarkin abu yunwa kikeso kifara hora kanki dashi sokike naje nafadama Ya Imran abinda kikeyi”? Dasauri Lujain ta girgiza kai tace “to zanci Anty please karki fadama kowa” tai maganan tana daukan plate chips kadan tadeba tasa kwai ma kadan kaman ba Lujain ba Anty Binta tace “tea fa” girgizamata kai tayi tace “idan nadawo shi zan sha” a kitchen din tazauna kan kujera taci abincin tass sannan tawanke plate ta taya Anty Binta kwaso kula tafito dasu falo Hajiya sai murmushi take tana samata albarka afalo duk akaci abinci banda Abee dabai dawobama yana gym dinshi ita tana kitchen wajen Anty Binta, Kausar ne tashigo kitchen din tace “Uncle Hamza yace kizo mutafi yau shizai kaiki school” wanke hannunta tayi tace “Bye Anty” bye Anty Binta tamata tana murmushi sanan tawuce tafita zama afalo tayi tasa safa da takalmin makaranta sannan tasaka hijab tagoya jakanta tafita itada Kausar dake daddanna wayanta motan Uncle Hamza suka shiga, motar mai kyau benz amman ba tinted bace, murmushi yama Lujain yace “Amaryan Ya Imran” sauke kanta tayi kasa bata sake cewa komiba suka fito, tsaye taga Mandawari a kofar gidanshi yauma yana sanye da wani rigan jearsay da gajeren wando, hada idanu sukayi ga mamakinta wani dan karamin murmushi yasakin mata batasan lokacin dataji wani farin ciki ya lullubeta ba, hannu yadaga mata alamun bye bakaramin mamaki tayi ba noke kanta tayi batare datamai bye ba, ita suka fara ijiyewa a school sannan yawuce yatafi da Kausar school.EPISODE 3️⃣0️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Wuraren 11 yay parking motanshi wata crazy Brabus jeep agaban school din, yadan dade aciki sannan yabude kofa ahankali yafito sanye yake da kayan kwallo farare sun mishi kyau sosai kitson kanshi ya gyara ya shafa mai sai kyalli suke, zare glasses na idanunshi yayi yakarasa zuwa wajen security dake gaban gate din suna kallonshi daya daga cikinsu zaro idanu yayi yace “ohhh my God Mandawari look guys” dasauri sauran securities din suka kara kallonshi dukansu bashi hannu sukayi dan murmushi yayi daya bayyana hakorin makkan bakinshi daya daga cikin security yace “Selfie please Mandawari” murmushi yayi yace “yeah sure” daukan hotuna biyu sukayi yace “it’s okay sauri nake” dasauri sukace “mekazo yi makarantan mu”? Dan murmushi yayi yace “wajen sister na nazo sako zan bata it’s urgent” security yace “laaa kanada sister a school din nan wacece what’s her name”? “Lujain Muhammad” daya daga cikinsu yace “wani class Kodai sabon zuwan nan da aka kawo” dudda baisani ba gyadamusu kai yayi, dayan yace “let’s go kashiga office kazauna akira maka ita” girgiza musu kai yayi yace “naah zan jirata anan jikin motana sako kawai zan bata” Babban su yace “jeka kira mishi ita yisauri” murmushi Mandawari yayi yaciro bandir na yan 1k sababbi fil yabama babban cikinsu sai murna suke suna godiya yawuce yakoma jikin motanshi ya tsaya tareda folding hannunshi akirji yana kallon gate din.


Tana zaune a aji cikinta ciwo yake sosai sabida yunwa amman takicin abinci har awurin lunch, daga bakin aji security ya tsaya yace “Lujain Muhammad yayanki na waje come with me” teacher dake koyarwa juyawa tayi takalleta tace “tashi kije” ahankali ta tashi gabanta hakanan taji yafadi to me wannan Uncle din yazo yamata yanzu, ahankali take tafiya Security nagaba tana bayanshi harsuka fita gate din ko kadan bata lurada Mandawari ba security ne yamata pointing inda yake tsaye yace “ga yayanki chan jeki karbi sakon” juyawa tayi takalli inda aka nuna mata ido da ido tayi da Mandawari wani kalan faduwa gabanta yayi ta tsaya chak tana kallonshi, dan murmushi yasakin mata hakan yasa ahankali tasaki wani kalan cute smile batare dataje wajenba dakai yamata alamu datazo gently tafara tafiya tana tahowa yabi cikinta da kallo dayaga baiyi girman dayayi jiyaba harta karaso gabanshi ta tsaya tana murmushi akunyace, tsareta yayi da idanunshi she’s breathtakingly beautiful, gawasu cat eyes manyan dayaji yana neman yasashi ya shide daurewa yayi yahadiye murmushin dayakeyi yace “har yanzu kinacin abinci dayawa ko cus you are still very fat” wani iri taji ahankali takalleshi batare datace komiba, hannunshi yasa acikin aljihun wandonshi yaciro iPhone 12 Pro max yamika mata, kallon wayan tayi dasauri saikuma takalleshi murya chan kasa tace “mezanyi dashi”? Tsareta yayi da idanu yace “I want to talk to you today ko bazaki amsa bane”? Girgizamai kai tayi ahankali batare data amsaba tace “mezance agida”? Dan daure fuska yayi yace “ke yarinya ne dakowa saiyasan nabaki waya karba kada raina yabaci inba hakaba zance nafasa auren ki” dawani kalan sauri takalli fuskanshi, gira daya yadaga mata yace “ko kindaina sona yanzu”? Wani kalan murmushi tayi ahankali akuma dan kunyace tace “inayi” murmushi yamata yace “to karba” ahankali tasa hannunta dake rawa sosai ta karba gabanta nafaduwa zuciyanta yaki natsuwa, kallon security dake kallonsu yayi yace “hide the phone and go back to your class I will call you by 7 dot na yamma bye” yajuya yashiga motanshi, gently ta tura wayan aljihun uniform nata tajuya takoma aji tana tafiya ahankali she’s super happy to see him amman kuma wani bangaren zuciyanta sai tsinkewa yake idan ta tuna she just collect phone from his hand wayama IPhone zuciyanta yaki natsuwa harsuka tashi by one na rana.


Jakanta tadauka tareda goyawa abaya tafito ahankali take tafiya tundaga mota Hamza ke kallonta, Lujain nada wani kalan kyau da idan ka daura idanunka akanta barakaso kadaina ba, batada fada baiganta dawani damuwa ba, deep down he wish Ya Imran will settle down da yarinyar yadaina kallon karantan ta zaiyi farin ciki hartazo tabude kofa baisani ba saida ahankali tace “ina yini” sannan yayi murmushi yakalleta yace “ya school kinyi karatu da kyau dai ko” murmushi tamai tareda gyadamai kai bata kara cewa komiba sundanyi nisa akan titi yace “do you need anything nasaya miki” girgizamai kai tayi tace “a’a nagode” murmushi shima Hamza yayi ganin bata sake dashi ba batare daya kara cemata komiba har sukakai gida sai kallon kofar gidansu Mandawari take she just wish inama zata ganshi, parking yayi tasauko tawuce ciki Hajiya kadaine a falo tanajan charbi ganin Lujain saida tai murmushi itama dan murmushi Lujain tayi tazo wajenta tsugunnawa tayi ahankali tace “ina yini Hajiya” shafa addu’a Hajiya tayi tace “sannu da zuwa Lujain, jeki chanza kaya kiyi wanka zansa mai aiki ta kawomiki abinci sama ya makarantan” ahankali tace “Alhamdulillah Hajiya” “sannu kinji Allah miki Albarka” ahankali tace “Ameen” tashi tayi ahankali tanadan yatsine fuska sabida yanda cikinta kemata ciwo tawuce sama dakinta tashiga dayake a gyare tsaf kayan makaranta tacire tashiga bayi wanka tayi tafito hijabi tasaka tai salla akan dadduman ta kwanta tana kallon jakan makarantan ta da wayan ke ciki gently tasaka hannunta tajawo jakan budewa tayi taciro wayan tana juyawa tana kallon daga ganin wayan sabo ne ba’a dade ana amfani dashi ba kunna wayan tayi ahankali hotonshi ne a screensaver tadade tana kallon hoton dan murmushi tayi tarasa mesa take sonshi duk idan taganshi wani kalan farinciki takeji bude wayan tayi ganin babu password tashiga gallery duka hotunan shine wanda yake buga ball da sauransu fita tayi takoma dial calls number dayane awajen da akai saving da Mandawari tadade tana kallon number kaman magic dailing number tayi yana ringing dasauri ta katse gabanta na duka uku uku kirane yashigo wayan ganin shine yasa ahankali tasa hannunta tai picking call din tareda kai wayan kunnenta tai shiru.



Daga dayan bangaren yace “baki iya gaisuwa ba”? Dan murmushi tayi ganin yanda yakeson girma murya chan kasa tace “good afternoon” shiru yayi baice komiba hakan yasa tace “hello” dan lunshe idanu yayi harcikin zuciyanshi yakejin muryanta ahankali yace “tell me everything that happen, karkimin karya kikamin karya I will hate you Lujain, so what happen daga farko zuwa karshe dahar yasa aka auramiki wannan tsohon” dan shiru tayi kaman mai tunani saita shiga bashi labarin duka abinda yafaru har zuwa yau, dan ijiyan zuciya taji yasauke ahankali yace “yataba rike miki hannu” girgixamai kai tayi tace “a’a” dasauri yace “kwana fa a ina kike kwana” ahankali tace “awani daki ni bansan inda yake zama ba” shiru yayi saikuma chan yace “kinason na aureki Lujain”? Dan lumshe idanu tayi tabude su ahankali sannan ta gyadamai kai ahankali tace “eh” murmushi yayi yace “to kicemai yasakeki basai ankamo mutumin ba I am here now kina fitowa zan aureki and make you mine mubar Nigeria” murmushi tayi sosai cute fararen hakoranta suka bayyana lumshe idanu yayi yana sauraron sautin murmushinta dan lunshe idanu yayi yabude yace “nabaki 1 week ki kashe Auren nan kifito lemme marry you, sannan kirage cin abinci look good katon cikinki yakoma flat kinada shape mai kyau amman katon cikinki yahana shape din nunawa dan haka work on yourself kinajina” gyadamai kai tayi ahankali dan murmushi yayi yace “bakice kina sona ba kodai a chat kika iya fadi” dan murmushi tayi zuciyanta namata wani kalan sanyi dan hararanta yayi kaman tana gabanshi yace “tell me now” Murya chan kasa akunyace tace “ina sonka Mandawari” dan dariya yayi datakejin dariyan daga cikin wayan yace “I am inviting you to my welcoming party gobe zan tura miki address din awaya kizo da bolt zan biya kudin kika iso makesure you look good kada kici abinci sabida cikinki yay flat” cikeda damuwa yace “please loose weight I hate mace mai kiba kinajina” yay maganan authoritatively dasauri ta gyadamai kai tace “to naji” yace “don’t eat anything again sai fruits da daddare and sleep only fruits fruits zaki dingaci yanzu kinji” gyadamai kai tayi tace “tom” ahankali yace “bye saina kira anjima da daddare”.EPISODE 3️⃣1️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Bin wayan tayi da kallo sannan ahankali ta ijiye wayan akarkashin gado tareda kife cikinta dake mata ciwo sosai sabida yunwa tunda take arayuwanta bata tabajin yunwa irin na yau ba chocholate dinta takalla dake leda lips dinta talashe tareda lumshe idanunta bacci ne ya saceta sai around 6 ta tashi kulan abinci tagani ankawo a injiyemata tashi tayi tawuce bayi alwala tayi tazo tai sallan la’asar sannan ta tashi tareda cire hijabi tana gyara towel din jikinta gaban kulan taje tabude su ahankali, biryani rice ne dayaji naman rago baja baja aciki wani kalan kugi cikinta yayi batasan lokacin data fashe da kuka ahankali ba tana kallon abincin cikinta nawani kalan murdawa dawani kalan sauri tarufe kulan tareda juyama abincin baya tadaura kanta saman gado, bude kofan dakin akayi hakan yasa ahankali tadago kanta Anty Binta ne idanunta kadai takalla tace “why did you cry Lujain menene”? Girgizamata kai tayi alamun babu komi sai kuma hawaye yazubo mata sharrr binta Anty Binta tayi da kallo ganin yanda tai zuru zuru yasa Anty Binta tace “kinyi lunch a school”? Girgixa mata kai Lujain tayi ahankali dan ita har yanzu bata iya karya hakanan ba, hakan yasa Anty Binta tabude kulan datagani adakin na abinci ganin bata tababa yasa ran Anty Binta abace tace “wai what is this behavior Lujain? Cikin gidan nan akwai wanda yamiki complain angaji da abincin dakikeci ne koko muncemiki munaso kirage kibane why will you be hurting yourself like this eh Lujain”? Wani kalan matsiyacin yunwa takeji dayasa takasa hadiye kukan, Anty Binta tadauki kulan gabaki daya takawo gabanta tareda saka mata spoon akai tace “dau abincin nan kici” girgixa mata kai tayi tana kauda kanta gefe tace “ni baran ci abinci ba” shiru Anty Binta tayi tana kallonta tace “sokike nabata dake ko Lujain” girgixa matakai Lujain tayi tana goge hawaye tace “kiyakuri Anty” tashi Anty Binta tayi tace “shikenan nima yau zan tattara nakoma gidan mijina dama sabida ke nadan zauna agidan nan sabida kisake amman tunda you are so stubborn kina neman yima kanki illa shikenan ke kadai kiyi amman zanje yanzu nafadi ma Hajiya sannan nafadama Ya Imran shima” tana maganan tamike dasauri Lujain tarike mata hannu tana kuka sosai tace “dan Allah kada kifada musu Anty” fizge hannunta Anty Binta tayi tafita daga dakin dan sosai ranta yabaci kana ganinta kasan bala’in yunwa takeji barinma ita da yawanci ita kebata abinci tasan yanda Lujain kedacin abinci all of a sudden tana neman kashe kanta, fuuuu tawuce tasauka kasa Hajiya na zaune tareda Abee da shigowanshi kenan ganinta kadai yasa Hajiya tace “lafiya ranki abace Binta” cikin fushi Anty Binta takalli Abee daya zubamata shima yana jira yaji meke faruwa tace “Ya Imran ga matanka chan na neman kashe kanta” wani kallo

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment