Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai tana numfashi da baki, kugin da cikinta yayi na yunwa yasa ta kwanta ahankali kan gadon tareda kife cikinta tajuyayar da fuskanta tana kallon mirror ta hakan yasa tajuyama kofan baya ahankali tana lumshe idanu wasu zafafan hawaye na sauko mata daga idanu sabida shegen yunwan datakeji gashi yakorota ciki, almost 5min tana kwance ahaka kaman daga sama taji kamshin turaren mai dadi nashiga hancinta dudda muran datake hakan bai hanata jin dadin turaren ba, ahankali tajuyo da kanta batare data tashi zaune ba dantaga waye yashigo dan ko kadan bataji alamun tafiya ba, Abee tagani tsaye bakin kofanta dauke da tray a hannunshi yana kallonta ba yawo ba fallasa, dawani kalan sauri takai hannunta tashare hawayen dasuke kwance kan fuskanta sannan ta yunkuro ta tashi zaune dan dafe kanta tayi tareda yatsine fuska sabida ciwonkan dataji kaman kanta zai tsinke yafadi, daukekai yayi daga kallonta batare daya shigo dakin ba yace “tashi kisa kaya” babu musu ta tashi gaban wardrobe taje tabude wani dogon rigan bacci tadauka sannan tajuya tadan saci kallonshi ganin yana tsaye inda yake har lokacin yasa ahankali tazo tawuce bathroom tamaida kofan tarufe, towel din jikinta ta cire tayi hanging sannan tasaka rigan baccin peach ne very decent ya tsaya mata iya knees dinta rigan yamata kyau sosai gadan katon tebanta daya fito daga rigan, gashin kanta dukya kara hargitsewa sabida yanda tasaka rigan dagaka, bude kofan tayi ahankali taleko cikin dakin, baya dakin amman ya ijiye mata tray abincin akan carpet, jellof rice ne da naman kaza kusan 5 akai sai tururi suke alamun yamata microwaving sai goran ruwa akan tray mara sanyi da spoon, da wani kalan sauri tafito har murmushi take ganin abincin zama tayi tadauki spoon dasaurinta zata fara ci daidainan aka sake bude kofan dakin dasauri tadaga kanta daidai tanakai rice bakinta hada ido sukayi da Abee dake rikeda kwalin magani guda biyu a hannunshi, ahankali tasauke kanta kasa tana ijiye spoon na abincin dazata kai baki tarasa mesa dazaran taganshi she use to become restless yatsunta tashiga wasa dashi batare dako motsin kirki takarayiba, karasowa cikin dakin Abee yayi har zuwa gabanta ya tsaya tareda ballo paracetamol biyu da actifed guda daya murya chan kasa kaman wanda bayason yay magana yace “take” dan kallonshi tayi ganin kallonta yake ba wasa kan fuskanshi yasa kaman wata yar yarinya tabashi hannunta, palm dinta yafara kallo sannan yasamata pills din aciki raurau tayida idanu tana kallon magungunan babu abinda ta tsana arayuwanta kaman magani, bottle water daya kawomata mara sanyi yadauka yabude yabata hannu tasa takarba shima sannan tadan kalli fuskanshi kaman mara gaskiya awani irin hankali akuma tsorace tace “in sha?” Wani mugun kallo yamata yace “no kishafa” raurau tasakeyi da idanu, sannan ahankali ta daura pills din kan cinyanta tadauki guda daya rak acikin guda ukun tana kallo sannan takalli fuskan Abee adan tsorace ganin ita yake kallo yasa dasauri ta dauke kanta takai maganin ta wurga baki taredakai ruwa ta kurba wani kalan kakarin amai tahau yi Abee dake kallonta yace “kikamin amai anan saikin lasheshi tass” yay maganan yana fizge ruwan daga hannunta ganin tana shirin zubarwa, sauran pills din yadauka daga kan cinyanta yarike a hannunshi sannan yakai ruwan bakinta ahankali yace “open your mouth” babu musu tabude bakin zuba mata ruwan yayi aciki sannan yace “raise your head” daga kanta sama tayi sannan yadan matso kusada ita faduwa gabanta yashigayi sosai amman tadaure, watsa mata pills din acikin bakin yayi dasauri tahadiye tana wani kalan tabe fuska da baki kaman taci kashi tadauki spoon tadebi rice dasauri takai bakinta tanaci hawaye yayi fall acikin idanunta, AC dakin yakalla ganin akashe yasa yakalleta har lokacin tabe fuska take irin na wanda yasha magani yace “da ruwan sanyi kike wanka”? Kaman daga sama taji tambayan, dan kallon fuskanshi tayi saikuma ta gyadamai kai ahankali kafin tadauke kanta tace “ban iya kunna ruwan zafi ba” dan shiru yayi yana kallon yanda take magana, jin baice komiba yasa tadago kanta hada ido sukayi dasauri tadauke kai, mikewa tsaye yayi yawuce bathroom nata yabude ya tsaya daganan bakin bayin yana kallon ciki bayin is very clean towels ne kusan guda 5 ta shaya ajikin hanger juyawa yayi yakalleta ganin tana zaune inda take bata tashiba yace “sainace kizo zakizo” dago kanta tayi tadan kalleshi saikuma ta taso ahankali dauke kai yayi yashiga bayin tabiyoshi ta tsaya daga nan bakin kofa nuna mata yanda zata kunna hot water yayi sannan yajuyo yace “kingane”? Gyadamai kai tayi ahankali kanta akasa ganin yana tahowa yasa tafice daga bayin dasauri takoma wajen abincinta tazauna tafaraci shikuma yafito daga bathroom din yawuce yafita daga dakin.


Tass tacinye abincin da naman tasha ruwa sannan tahau gado sai bacci.
4:30 Abee yafito cikin jallabiya yatada mutanen gidan batare daya shiga dakin Lujain ba, yawuce masallaci.
Wuraren 7 nasafe Hajiya tafito falo taxauna kan kujera daidai Kausar dake cikin kitchen tafito da kula zata ijiye kan dinning Hajiya tace “Kausar jeki cema Auntyn ki Lujain tashirya tsaf ta sauko Babanku zai kaita yasata a makaranta yau” Gyadamata kai Kausar tayi tawuce sama.EPISODE 2️⃣4️⃣




Knocking kofarta Kausar tayi jin shiru yasa tabude kofan dakin akan dadduma taganta dan yanzun nan ta tashi ganin tana salla yasa tace “Hajiya tace ki shirya kizo kasa” tana maganan tajuya tafita daga dakin.
Saida ta idar da salla tai azkar sannan ta tashi bathroom takara shiga tai wanka da ruwan zafi sosai ciwon kan datakeyi yatafi batajinshi kuma saidan hancinta dayay blocking shima kuma yaragu sosai dan tana iya numfashi da hancin yanzu bakaman jiyaba, fitowa tayi daure da towel tazo gaban wardrobe tabude tana kallon kayan wajen, wani abaya tajawo black ne gabaki dayanshi mai kyau kana ganinshi kaga saudi abaya, yauma bata saka bra ba singlet tasa da pant sannan tadaura abayan akai bayan tashafa mai, tadau gyalen abayan tadaura akan yamutsassen gashinta tabude kofa tafito ahankali tafara tafiya chak ta tsaya ganin Abee na hayowa sama idanunshi akanta hakanan jitayi gabanta na faduwa sosai, saida yazo daidai dap da ita bakinta yadan fara rawa takasa ma magana, wani kalan kallo yamata daga sama zuwa kasa sannan yace “go back inside kidauki hijab kisa” yana maganan yawuce yabarta awajen, saida taji karan ya maida kofan dakinshi yarufe sannan tajuya ahankali takoma dakinta, wardobe taje tabude tana kallon hijaban wajen wani maroon hijab tadauka tasaka yamata wani kalan kyau kaman balarabiya ne tasaka hijabin sannan tadauki takalmin da Baba yasaya mata tasaka dan babu wani takalmi adakin shima hala dan ba’asan size nata bane tafito ahankali take tafiya tazo stairs sauke kanta kasa tayi sabida yanda suka cika falon duk ana shirin yin breakfsat tunda tafara saukowa idanun Hajiya kyam akanta maroon hijabin datasaka ba karamin kyau yamata ba deep down tana addu’a Allah yasa suzo juna itada Imrana dan tanamai mugun kwadayin Yar yarinyar nan, murmushi tayi tace “Lujain an sakko” dago kanta Lujain tayi tadan kalli Hajiya wani kalan kunyan matan taji hakan yasa tamaida kanta kasa takarasa wajenta saida tazauna akasa kusada ita murya chan kasa tace “ina kwana Hajiya” murmushi tamata tace “har yanzu muran bai sakeki ba? Duk muryanki ta chanza kinsha magani kuwa”? Gyadama Hajiya kai tayi ahankali, Hajiya tace “waya baki maganin”? Dan shiru tayi dan batasan yaya zata kira sunan Abee ba hakan da Hajiya ta lura yasa tace “Imrana yabaki”? Gyadamata kai tayi ahankali, Abdallah dake saukowa kasa gaban Hajiya yazo yace “Hajiya natafi yau ina azumi bazanyi breakfast ba” yakalli Lujain da kanta ke kasa yace “good morning Anty Lujain” dago kanta Lujain tayi ahankali tadan kalli Abdallah dake kallonta yana murmushi sauke kanta kasa tayi tama rasa mezatace itane wannan babban yakira da Anty, Haiiya dake murmushi tace “Antynku Lujain badai kunya ba” murmushi yayi yace “natafi” “Allah bada sa’a Abdallah” Hajiya tafadi tana hararan Kausar datazo ta zauna gefen kujeran da Babanta ke zama rikeda plate na chips itama ta shirya makaranta hijabi kawai zata saka tafita, fitowa daga kitchen Anty Binta tayi itada Maman Aneesarh ganin Lujain yasa tai wani kalan murmushi tazo wajen suka ajiye kuloli tashafa kumatun Lujain hakan yasa tadago kanta dan murmushi tama Anty Binta tace “good morning Anty” morning Lujain bari nahada miki tea” tea tahada mata a big cup this time sannan tazuba mata chips a plate da fried egg da pepper soup, ahankali tafaracin chips din tanashan tea ahankali dan yanada zafi ba kaman wanda Gwaggo kemata ba, kamshin turaren Abee da yacika falon yasa tasan yasauko ne dan ko kadan bakajin footsteps nashi, zama yayi Anty Binta tace “Ya Imran coffee ko shayi Wanne kakeso”? “Coffee” yafadi ahankali yana duba agogon hannunshi, Hajiya dake kallonshi tace “zubamai da chips da farfesu Binta ni bantaba ganin makiyin abinci irin Imrana ba saisa gashinan Abdallah kaiya dauko” Baice komiba kawo mishi Anty Binta tayi a tray tadaura kan table dake gabanshi coffee yadauka yafara sha daidai nan Kausar tagama tamike takalli Abee shima kallonta yayi yanashan Coffee, kaman zatai kuka tace “Abee ban iya assignment dina ba” wani mugun kallo yamata yace “and u are telling me now” sauke kanta kasa tayi sabida mugun kallon dayamata ahankali tace “Abee kayakuri baran karaba” Hajiya dake jinsu tace “ke wlh fitinanniyan yarinya ce Kausar, ke kinci abincinki kin koshi saida shi yafaracin nashi shine zakimai batun assignment salon karyaci, tunda aka haifeki Babanki yadainacin abinci yakoshi” kaman zatai kuka tace “ai nace sorry ko Abee” ijiye coffee yayi ahankali yamika mata hannu alamun tabashi book din dawani kalan sauri tabude jakanta tadauko book din takawomai maths ne kan probability ne, ahankali yace “come here” kusadashi tazo cikin 2min yanunnuna mata yanda zatayi yamata solving daya yabata second question din yace tayi yagani zama tayi tafara shikuma yacigaba da breakfsat nan da nan tayi takawomai dubawa yayi yaga tayi daidai hakan yasa “now get ready, Hamza na jiranki a car” hada jakan tayi tasa hijabi tafita dagudu, saida yagama breakfast dinshi sannan yatashi yadan kalli Lujain data gama itama amman kanta akasa hakan yasa Anty Binta dake kallonsu tace “tashi kutafi Lujain” tashi Lujain tayi tadan kalli Anty Binta saikuma takalli Abee dake tsaye, juyawa Abee yayi yay kofa yace “Hajiya natafi” Hajiya tace “Allah bada sa’a bishi Lujain” binshi Lujain tayi itama tabude kofa tafito waje duk su Hajiya suka bita da kallo, wajen wata mota daban yayi bmw baka ba jeep din jiyaba budewa yayi yashiga gaba hakan yasa takarasa wajen kirjinta bugawa yake kawai to ina zasuje baya tabude ahankali zata shiga suka hada ido wani mugun kallo daya mata yasa tamaida kofan tarufe tadawo gaba tabude gently tashiga cikin motan gabanta nawani kalan fadi, motan kamshi kaman ba mota ba, ganin credentials nata a motan yasa tadan bude idanunta takalli file din datasan Gwaggo kadai ke boyemata dan awajen Gwaggo suke acikin katon akwatin bununta taboyesu, ga birth certificate dinta, primary certificate dana JSS Ce dakuma na indigen da Nin dinta duka awajen, dan juyawa tayi takalli cikin gidan to Gwaggo tazone batasani ba, bude musu gate akayi suka fice dudda motan tinted ne gani take kaman zaa ganta hakan yasa ta sauke kanta kasa, sun danyi tafiya mai nisa wani hadadden school yakaita da baida wani nisa sosai da company shi yasan mai school din sosai childhood friend nashi ne, kashe motanshi yayi a parking space yasa hannu yadauki file nata yabude kofa yafito, kasa bude kofan tafita tayi sai kallon cikin school din take da student keciki gabanta nafaduwa yanzu nan ma za’a faracemata Yar iska ne dan yanzu ko’ina ansanta hawaye ne yacika mata idanu, juyowa Abee yayi ganin bata bude kofaba har lokacin yasa yazo ta wajen bude mata kofan yayi dasauri takalleshi lips nata har rawa suke murya chan kasa tace “ni……banason school, dan Allah kada kasani, wlh banaso” tai maganan hawaye na zubomata daga idanu dasauri takai hannu tashare yana wani kalan kallonta yace “why?” Dan kallonshi tayi saikuma tasauke kanta ahankali tace “nan ma zasuce ni yar iska ce maibin maza, everybody will be looking at me ana nunani ana cewa nice a video nan” fashewa da kuka tayi yace “don’t you dare cry for me anan” dasauri tahadiye kukan tana goge fuskanta da bayan hannunta, cikin kakkausan murya yace “akwai wanda yadaukeki yakaiki sama ne when all the rest of the students na reception akasa? Akwai wayanda yakaiki bayin maza ne?” Girgixamai kai tayi wani abu na tokaremata zuciya, wani kalan dan tsaki yaja yace “kin zaci inason Auren nan da akamin dakene kokuma I fancy you one bit?” Shiru tayi yace “the way I am dealing with you dudda I don’t consider or regard you matata kema haka zaki shiga school din nan deal with anything that comes ur way and study hard” gyadamai kai tayi ahankali tanaji kaman tafashe da kuka danji tayi tabama kanta tausayi, anatse yace “futo” fitowa tayi daga motan ahankali ta matsa gefe maida kofan motan yayi yarufe sannan yakalleta yace “ke” kallonshi tayi kaman yanda shima ke kallonta, calmly yace “karki dauki Auren nan da akamin dake as anything, ke ba matata bace and bazaki taba zama dayaba, as far as Imran is concern I don’t have a wife! Dan haka do whatever you want, idan kinga wanda kikeso talk to him, mingle with your fellow students, dazaran komi settle down zan rabu dakene u will be back to your parents house cus babu abinda zanyi dake” yakarashe maganan yana tabe baki ahankali yace “kin gane”? Gyadamai kai tayi ahankali sotake tayi kuka amman yahanata gaba yayi yace “let’s go” binshi tayi tana tafiya ahankali, gaidasu masu gadi sukayi sannan suka shiga ciki ga mamakinta kusan rabi da kwatan student na makarantan turawa ne kadan daga cikinsu ne yan nigeria, sama sukaje wani babban office yabude yashiga wani babban mutum ne zaune yana ganin Abee yatashi yana bashi hannu yace “welcome Soja, ga waje ku zauna” zama duk sukayi yakalli Abee yace “itane student din”? Gyadamai kai Abee yayi yace “bani file nata” bashi Abee yayi yadudduba sannan yakira secretary nashi yabata tamai photocopy documents nata duka yabaama Abee original, agabanta tanaji Abee yabiya 5.7M school fees nata da kudin textbooks nata da kudin Waec da neco dan yace yanaso tayi a SS2 din nan idan taci shikenan, secretary aka kira ta tafi da ita changing room dan saka uniform shikuma mutumin yacigaba da magana da Abee yace “I assure you this babu wanda zaiyi bullying nata a school dina, her image will be well protected, sannan kaman yanda kamin bayani awaya last night zata dinga special lesson din 4 idan ta tashi saikazo kawuce da ita gida, and lunch dinta will be given to her, kabata one week zakaga tasake jikinta tashiga student da kyau without fear na being bullied ko kirata names, Ya guy din ankamoshi kuwa?” Daidai lokacin secretary tashigo tareda Lujain data saka kayan makaranta skirt ne dark blue da Riga sky blue long sleeve sai jacket dinshi dark blue, dakaramin farin hijab sai farin safa da black shoes, uniform din sun mata wani kalan kyau she looks chubby and sooo cute, tashi mai makarantan yayi yace “Soja muje mu kaita ajinsu tare” raurau tayida idanu tana kallon Abee daya dauke kanshi daga kanta yamike shida mutumin sukai gaba itakuma abaya wani class mai kyau SS2 suka tafi ajin duka turawa ne mutun 3 ne Nigeria sai ita yanzu ta hudu ga teacher a ajin shiga mai makarantan yayi yasa aka mata warm welcome sannan yakaita sit nata agaba tazauna ahankali tasake dagakai takalli Abee dashima kallonta yake wani kalan lankwashe kai tayi ashagwabe hawaye yacika idanunta tam har kyalli suke dawani kalan sauri Abee yabar wajen mai makarantan yasallami ajin yafito yasameshi agaban office suka karasa magana sannan yawuce yafita daga school din yashiga motanshi yawuce company shi that is just few blocks away.

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/EPISODE 2️⃣5️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/


Inner Sanctum
Zaune yake agaban wani drawer shi kadai acikin sanctum din sanye da jersey na riga green da farin wando, an rubuta Mandawari abayan rigan, farin guy ne kal dashi siriri baida kiba ko kadan, kanshi irin wannan askin nan na yan kwallo ne anyi murde murde ajikin tarin gashin da abin yay kaman kitso dan twisting ne, wayanshi ne a hannunshi yana dubawa daidai an bude kofan sanctum din an shigo wasu players ne kusan su 13 duk sun shigo ciki suna zufa kowa yay wajen zamanshi goal keeper su yace “Man! What happen is like yau bakaine a field ba is another different person, what’s happening Bro”? Wani guy ne kamanshi daya zaune kusa dashi yana kokarin cire takalmin kwallon kafanshi mai suna Olusay yace “ai Man is going through a heart break this is the second week his stalker batamai magana tamai dropping love messages ba” wani mugun kallo Mandawari yama Olusay, yan dakin dukansu kowa barin abinda yakeyi sukayi sukataho gaban Olusay dasauri sukace “yanzu Mandawari daman yanada budurwan dayakeso”? Dan dukansu are finding it unbelievable, dan dariya yayi yace “yes” wani kalan mikewa Mandawari yayi cikin fushi yace “ubanwa yace maka sonta nake” dariya Olusay yayi sosai sannan yamike tsaye tareda cire riganshi yay hanging yajuyo yakalle team members dinsu yace “wlh mugun sonta yake na rantse amman he feel mutum irinshi mai over 400M followers can not love a girl like her shida har manyan top celebrities irinsu Kim ke sonshi amman yarasa wanda zaiso sai yarinyar nan he’s even ashame to admit sonta yake barima na nuna muku page dinta kugani kuyi following nata” yakai hannunshi zai dauki wayan Mandawari wani kalan rikemai hannu yayi yana huci yace “how many time zan gayamaka kadainamin irin abin nan Abdulaziz” cikin fushi Olusay yace “how many times zan gayamaka shi so babu two ways about it idan kanason abu kanaso ne idan bakaso bakaso ne admit cewa bawata Cinderella dream girl Allah yajarabeka da so ba, normal common girl Allah yajarabeka da so Muhammad” wani kalan mugun kallo Mandawari yamai yace “and so”? Olusay yace “dan haka kadena jan aji slide into her dm and respond to all her messages and confess your feelings Bro koba hakaba guys” duka yan team nasu sukace “hakane” daya daga cikinsu mai suna Obi yace “I can’t wait to see babe din da Man keso yanda yakema mata wulakancin nan I know she must be the most beautiful girl on earth” dan tsaki Mandawari yayi yace “you guys should stay away from me and my business” yay maganan yana cire nashi rigan ya chanza kayanshi zuwa normal Riga da wando black yadauki wani big jacket yadaura akan kayan dan sanyi akeyi a Greece thank God yau zasu koma nigeria, yana gama shiryawa aka shigo akace bus nasu is ready fita duk sukayi koda sukakai bus din shida yasaba zama da Olusay yau bai zauna wajenshi ba baya yawuce yazauna abinshi Olusay baicemai komiba.



Airport suka wuce business class aka biamusu dayake shida Olusay ne zasu Nigeria sauran kowa yay garinsu, saida jirgin sannan ya kwanta wayanshi yabude yashiga chat dm din Lujain yana dubawa tun 2019 tafara turamai messages har zuwa yanzu dasuke 2022 amman baitaba amsata daidai dasau dayaba, fitowa yayi yashiga Fred dinta yana duba hotunan ta, 5 pictures ne kawai tai posting, daga wanda tasaka scchool uniform sai wanda take itada Gwaggo, sai wanda tayi ranan salla da Ya Samira, saikuma wanda tayi ita kadai tayi bala’in kyau a hotunan duka pink lips dinta ya tsare da idanu kaman tasaka pink janbaki, fitowa yayi yawuce wani blog a instagram yakara bude video ta na sex video nan da yanzu zai iya cewa yakalla yakai sau 20, saikuma ahankali yafito yashiga video da blog din still sukai posting na debunking news din cewa mutumin mijinta ne ga shaida daga wajen iyayensu, jazur idanunshi sukayi har jijiyoyin kanshi suka fito kashe wayan yayi ya runtse idanu ahankali murya chan kasa yace “you are mine Lujain! You love only me! You belong to me”…
*****


Har aka tashi daga makarantan tana aji, da kyar wuraren 1 ma tafita shima cafeteria officials nasu ne sukazo suka kirata kan tazo ta amshi lunch haka taje lafiyayyen abinci aka bata da drink harda kaza ga student awajen babu ma mai kallonta haka taci tadawo aji, malaman sai nan nan da ita suke yan ajinma namata magana itane ma bata amsasu da kyau kawai duktabi ta tsargu, 4 daidai aka gama musu special lesson din aka tashi kowa yashiga daukan jakanshi banda ita dake zaune inda take saida kowa yagama fita yarage ita kadai a ajin yasa tashiga hada books nata ajaka tamaida komi saikuma tai shiru tana kallon jakan yau kwana hudu kenan bataji muryan yan gidansu ba, bata gansu ba, koda su Baba dasu Mama dasu Ya Abida basu damu da ita ba Gwaggo fa? Yanzu Gwaggo barata nemeta ba, daman da gaske takosa takadata daga gidansu shikenan batada kowa, wannan wani kalan rayuwa ne da rana daya kawai tajefa kanta? Jitake kaman tadawo da hannun agogo baya ta chanza duka abinda yafaru ranan, babu wani abu datakejin dadinshi arayuwanta, ita batada waya, ita gidan nan babu wanda zai yarda yabata wayanshi balle takira Gwaggo ma, ita school dakomima baya mata dadi yanzu sabida batada Mama ne saisa abu haka ke damunta? Inda Mamanta na raye tasan barata wahala hakaba tunda gashi yanzu ma Gwaggo batasonta kaman Mama wasu kalan hawaye masu zafine sukazo mata tundaga yatsun kafanta kawai kife kanta tayi akan kafafunta tafashe da kuka sosai Abee yadade tsaye gaban ajin yana kallon yanda takife kanta kan kafanta tana kuka sannan yadanyi gyaran murya da sauri tadago jajayen idanunta, ganin Abee yasa dasauri tashare hawayen da bayan hannu ta mike tsaye ahankali tareda daukan jakanta ahankali ta goya sannan tafara tafiya kanta akasa ta taho gaban kofan, baice mata komiba yayi gaba hakan yasa tabishi abaya har zuwa waje, mota yashiga itama tabude gaba tashiga tazauna har lokacin idanunta jazur, harzai tada mota saikuma yajuyo yakalleta bayabo ba fallasa yace “why are you crying”? Dan juyowa tayi takalleshi yanda ya tsareta da idanu saitaji takasa mai karya lips nata har rawa suke tace “kewan yan gidanmu nake…...” Wani kukan ne yazo mata dasauri takife kanta kan jakan makarantan da akabata a school tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “babu wanda ya nemeni cikinsu da Baba da Mama, dasu Ya Samira harma Gwaggo basu nemeni ba sun kawoni gidanku I am all alone babu wanda ke sona, kowa haushina yakeji, I am so scared mutane su ganni kar adinga nunani babu abinda kemini dadi, I just wish inama zan mutu maybe namaga Mamana achan naji dadi, babu wanda ke sona har Gwaggo na” tunda tafara maganan kallonta yake tabashi tausayi sosai inda Kausar dinshi ne fa in this situation, “wayace miki Gwaggon ki bata sonki” dago kanta tayi dasauri da rinannun idanunta takalleshi dauke kanshi yayi yakunna key tareda tada motan yaja motan sukabar wajen, saida suka shiga titi ahankali tace “inda tana sona dabatamin auren nan ba ni inada wanda nakeso” dan kallonta yayi saikuma yadauke kai yakalli titi kusan 3min babu wanda yace komi acikin motan kaman daga sama yace “shi kike kallo rannan abayi”? Gyadamai kai tayi dasauri tana goge hawayen kan fuskanta da bayan hannu tace “eh sunanshi Muhammad Mandawari, ni shinakeso na aura” yana kallon hanya yace “kinfadama Babanki” gyadamai kai tayi tace “eh yasani” ahankali Abee yace “to mesa basu aura miki shi ba”? Dan rage murya tayi looking so sad tace “ai baitaba amsa messages dina a instagram bane ba” batare da Abee yakalleta ba yace “do you have phone”? Girgizamai kai

4 Comments On SAKON SO
avatar
asmee-bint-ali

4 months ago

Reply

Thanks so much

avatar
amaris-musa

4 months ago

Reply

This book is not complete and I subscribed for it

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

avatar
abasu-kala

4 months ago

Reply

Replying to amaris-musa

Pls sir due check our policy, you only subscribed for downloading access not, buying / purchasing book, we do not sell books here, and some of our books can be incomplete if you want the complete contact the author and buy from them.

Please Login or Register in order to submit comment