You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
daya bazatakai daya gidan Aurenta ba. Waye ya fada maka yaya Nazir? Aikoda Rana daya mukai Aure Sai Nakai Leemah gidanta kafin na wuce Nawa. Nazir ne yace kinmanta Kabeer Xaki Aura kuma yola Za'a kaiki,ba Lallai Na yarda baby taje yola Aranar Aurenmu ba...da Sauri feenah ta tashi tana cewa Ai bazaka Rabamu ba dan yanxu kasamu mun Amsheka, daga Haka tabarsu Zaune A wajen. Juyawa yayi yana kallon Leemah baby kawarki Akwai Rigima, Uhum bata Rigima Kaidinne Kake Sakata Rigima, Umm Na lura bakwason Laifin junanku Toh ya Soyayya ta yanzu Aranki??? Shiru tadanyi daga bisani tace tasamu waje babba Acikin Zuciyata, kallonta Nazir yayi kamar ba ita tayi mgnr ba ta wani fuske, Cikin Xuciyarshi yace Lallai Leemah irin macen danake muradin Aure ce, Afili cewa yayi Alhmdllh my baby Yanzu kinga kamin Ki koma Skul Sai Asaka mana Rana...Xaro ido tayi tace da wuri Haka? Eh mana bakiji Hausawa nacewa Abari ya wuce Shi ke kawo Rabon wani ba? Hakane but yaya Naz..but what? Nazir ya katseta da Sauri. Kabari lokacin daxa'a Saka Ranan feenah da kabeer Sai Asaka tare da namu. Kin kawo Shawara mai kyau baby Shiyasa nake kara Sonki,duk da kin barni Cikin tunaniki, kullum dake nake Kwana kuma dake nake tashi. Nima Haka yaya Nazir. Kin tabbata? Kallonshi tayi Suka hada ido ta kashe mai Ido daya tace Ummm, Ajiyar Zuciya Nazeer yayi Dan wani irin farin ciki yakeji wanda baya misaltuwa. "I love you So much my baby" Nazir ya fada yana Mata Murmushi. "love you more my baby" Leemah ta bashi Amsa kasa kasa. Xancire miki kunyar Nan Soon duk da Naga Alamar nama fara kokari Wajen cireta....dariya Leemah tayi ta tashi tace kada Su mum Su Sakko, tashi Shima yayi ya rakata Har kofar Room din Feenah yace kishirya Anjuma Nakaiki gida. Ok tace tashige Ciki.
Inno ce tsaye Kan yazeed Tana fadin Haba tsaka ka kiramun ita Naji ko tana inane. Inno nace miki wayata Bazata iya Zama A kunanki ba dan Allah kitafi ki bani waje yazeed ya fada yana nuna mata Hanyar Sama.... tsaka! tsaka! tsaka! Sau nawa nakira ka? Oho yazeed yace ke kikasan tsaka. Kwafa Inno tayi tace yaro yarone ina tausaya maka Ranar da Zaka Shigo hannuna, Xakayi nadamar yimun wannan Abun Dan Ubanka,yanzu namaka Uzuri dan nagane dalilin dayasa kakemun wannan Abun...Amma muje Zuwa ni inno jikar Saluhu da balaraba Nakusa Na dana maka tarkon da bazaka iya tsallakeshiba. Kallonta yazeed yayi yace iyaka kice idan Abba ya dawo Xaki fada mishi, Toh Sai me? Haka kace ko? Eh Haka nace mtsww kizo kitafi koma ma huta. Fatima kayimawa tsaki bani ba...muxuba ni dakai. Tashi yayi yana toshe kunanshi...daidai nan Abba yayi Sallama Cikin parlon. Suman tsaye Yazeed yayi dan yasan yau Inno Sharri Xataimishi ba kadan ba. da karfi Inno tace Ayirirerere yau Ga dana Ya dawo huta Roro. ...da fara'a Abba ya karaso kusa da ita ya gaidata amsawa tayi Cikin walwala da Sakin fuska, Abba ya kalli yazeed my Son lfy kuwa? Sannu da dawowa Abba! Yawwa Son duk kuna lfy ko? Alhmdllh Abba. Ya katsaya Haka kamar wani police? da Sauri Inno tace Nakirashi ne ya kiramun Halimatu A waya Shine yake kokarin kiranta Saikuma ka Shigo. da mamaki yazeed yake kallonta Suka hada Ido ta watsa mishi Harara, Shi kuwa cikin Ranshi yace Tabbas wannan tsohuwar Akwai Abinda ta Shirya Mun. Abba ne ya katseshi toh kakirata mana, toh Abba. Kiran Leemah yayi ta dauka ya mika ma Inno! Allo Halimatu. daga bangaren Leemah tace Na'am Inno ta. Kina inane munata jiranki Shiru Har Abbanku ya dawo. Inno Naje gidan Uncle Umar ne, yanxu gani Ahanya tare da feenah da Twins. Har Naji dadi Halimatu chanake kokin fasa Xuwa ne. Aa Inno Gani nan,me kika dafa mana? Saidai kinxo Yar nan.Toh Inno gani nan. Anshi tsaka kashe ban iyaba....Amsa yayi da Sauri yabar parlon danshi tsoro yake kada tamai Sharri wajen Abba. Mamy ce ta Sakko daga Sama Cikin Adonta, barka da dawowa Abban Leemah,yawwa barka Maman Leemah.tashi inno tayi tace bari nabarku Ku gaisa, Kuma Amadi gobe Xaka maidani inda ka daukoni, bata jira amsarshiba ta bar wajen. Yazeed na fita yaci karo da Yusuf dake Shigowa Yanzu...Aa Dr Ashe kana ciki? Ina ciki Yusuf Zomu karasa Akwai matsala fa. Karasawa bangaren yazeed Sukayi, Yusuf yace Matsalar Menene Aboki? Yusuf mamaki nake Abba ya dawo inno batace mishi komai ba, kasan Halin Inno da Rashin hakuri gani Nake Anya ba Wani Abun ta Shirya ba? Gyara Zama Yusuf Yayi yace banajin Akwai Abunda ta Shirya, Inaga kawai dan tasan Za'a Maka fada Shine tadan kauda Zancen. Shiru yazeed yayi daga bisani ya girgixa kai, Anya Kuwa yusuf? nasan Halin Inno Sarai wlh Amma mubar mgnr ni bawani tsoroma nakeji ba taje tayita fada. dariya Yusuf yayi wanda shi kadai yasan Ma'anarta yace Aikuwa Abar mgnr kawai. yawwa yazeed haryau baka samo Wacce kakesoba? bansamo ba Yusuf ni banga wacce tamunba! Kallonshi Yusuf yayi yace duk Matan dake fadin garin kaduna babu wacce tamaka? Eh Yazeed yace Atakaice danshi gabanshi ma dan faduwa yake.. Ok Yusuf ya fada Amma Kana nan kan idan kasamu yarinyar data kalle Cikin idonka tayi magana Xaka Aureta ko? daga Kafada yazeed yayi yace yes.
Atare Suka Sakko daga motar gaba daya Suka Shiga gidan. Da gudu Twins Suka karasa Ciki Suna kiran mai Kyau! Suma Shiga Su leemah Sukai ba kowa a parlon dan Haka Sukai Xamansu Anan. Nazir yace bari Naje Wajen Yazeed da Sauri Twins Sukace Suma Zasuje, fita Sukai Atare Sukai part din yazeed. Feenah tace ina mamy da Inno Suke ne? Leemah tace kya tambayeni nida mukazo tare, Kinsan Abba yadawo maybe mamy Taje mishi wlcm Sunyi missing juna kinsan, itakuma inno Inaga Wani Abun takeyi duka feenah takaima Leemah ke bakida Kunya ko? Toh Menene Ai gsky na fada, yawwa Feenah dazun baby kecemun Wai Asakamana Rana kamin nakoma Nace Nooo Saikin tashi Naki Auren. Toh waye kuma baby!? dan Rufe ido leemah tayi tace yaya Nazir mana. Tabe baki Feenat tayi tace Umm. Saiki bashi phone number dinki Kada mukoma Skul kina tunani. dariya Leemah tayi tace baki lura ba Amota ya amsa? Ina Xanlura fa kunshige gaban mota kuna Xancen love, Amma harda kukan munafurci ni feenah ina tsoro waye waye mtsww magulmata daga Ke har Shi. Inno ce ta Sakko daga Sama tana A'uzubillah wake tsaki irin na tsaka? Tashi Leemah tayi takarasa gunta tana dariya. Inno ta ya gida? Lfy Halimatu ta Shine kika fara Xuwa gidan Su Naziru baki Xomunba. Sorry Inno ba gashi yanzu Munzo tare da feenah ba. Kallon feenah Inno tayi tace Nafisatu yan makaranta... ina yini Inno? Lfy Nafisatu ya karatu? Yasu Hafsat?ya garin kuma? Ya Ummaru? Kallonta feenah tayi ta kauda kai don idan Akwai Abinda tafi tsana Shine yawan tambayoyi irin ya kaza ya kaza. daga gira Inno tayi Sama Ahhh Wlh kwarai Halinku daya da tsaka....kallonta feenah tayi tace waike kowa Saikin bata mishi Suna ne? bude baki inno tayi tace Laaa aisaiki fadamun bakyason Ina tsokanar yazeedu bawai ki rinka mun Kwana kwana ba. tsaki feenah tadanja Kadan. Inno tabe baki tayi tace Ummm gaskiyar Yusufa. Kallonta leemah tayi tace inno mai yusuf din yace miki? Zomuje daga Chan na fada miki Inno taja Hannun Leemah Suka bar Wajen. Kinsan me Yusuf ya fada mun kuwa? Aa inno fadamun! Kasa kasa tayi da murya, yace mun yazeedu da Nafeesatu Sun dade Suna Son junansu, Amma Sabida gaba dayansu Sarakan miskilanci ne yasa Suka Ki tsayawa Su Sanar da junansu, Amma yazeedu ya fada ma Yusuf yana Son Nafeesatu, kuma yazeedu Aure yakeso Sosai Sabida RANAR dana kori Kafurar yarinyar nan naje amsar kudi gunshi ya rufe kofa da Sauri ya Hanani Shiga, daga baya da idona Naga yarinyar ta fito daga bangarenshi tana Sanda, Toh ke Halimatu Kawar taki bata taba gaya miki tanason yazeedu ba? Leemah datunda Inno tafara maganar ta daskare Awajen tace, inno bata gayamun ba, Kuma inaga yusuf Wasa yake miki Feenah bazata boyemun komaiba,inno ke bakiga basa Shiriba ma da bro? Ke da alla Sakarya Yusuf yace irin tasu Soyayyar Kenan kedai Kada kifada Mata kibari muga gudun Ruwansu. Ajiyar Zuciya Leemah tayi tace Toh Inno.Amma kasan Xuciyarta Sam bata gasgata maganar ba. fitowa Sukai parlon Leemah jikinta duk yayi Sanyi So take Abunda Inno tafada yazama Gaskiya da tafi Kowa farin Cikin hakan kuwa. Su mubeen ne Suka Shigo tare da Nazir Wajen inno Suka nufa Suna dariya. Yusuf Naga ya Aje Wata mage kofar yazeed ya nufo Cikin gidan Shima. Kiran feenah Akai Awaya tace laaaa Leemah Kausar ce, bari Naje Waje na'amsa karfa kibiyoni. Toh Leemah tace Hakan ba Karamin dadi yama yusuf ba. Tana fita yace inno inaga wajen yazeed Zataje bakiji tana kada Leemah ta betaba. Ai ita Sakaryar Halimatu din nan bata yardaba inno tafada. Kallon leemah yusuf yayi yace barta inno yanxu zata yarda ai. Fitan Feenah yayi daidai da lokacin da Yazeed ya fito daga daki da Sanda A Hannu,dama ganin magen da yayi yasa yakoma ya dauko Sada dan yakoreta dan idan tana wajen bazai iya wucewaba tsoronta yake. Sandar yasaka yana dan ture magen itakuwa taki tashi. Feenah ce ta hango Abunda yake tace Kausar dan kashe kadan, bro din Feenah Kema mage mugunta Bari naje namishi ta tassss.
*Gud nyt lovers💕💕 Ina typing Ina gyangyadi duk because inasonku kamar yanda kuke Sona yasa na daure nai muku wannan*
Page....29/30
Karasawa tayi Cikin tafiyarta wacce kamar bata Son taka kasa. daidai gaban yazeed taja ta tsaya Kai Malan! dagowa yazeed yayi daga durkusan da yake ya Zuba ma kaykyawar fuskar feenah ido take gabanshi ya fadi Rasss. Itama feenah Ido ta Saka Cikin Nashi yayin da itama gabanta ke faduwa wani irin kwarjini taga yamata,jitake kamar ta juya ta koma Amma takasa motsin Arziki, daurewa tayi ta k'ara Saka idonta Cikin Nashi still takasa mgn, durkusar da kai kasa tayi tafara motse da dankaramin bakinta, Kai Anamaka Kallon mai tausayi Ashe Kai mugu ne! Yusuf ne ya karaso wajen yace Ahh feenah yazeed fa mai tausayi ne tsoronta yake Ji kawai, Amma idan kin isa ki kalli Cikin idonshi kifada mai bashida tausayi mana. kallon Yusuf Feenah tayi ta yatsina fuska tace, Kan mai Xan kasa?? Toh idan Zaki iya Kiyimana. d'aga kanta tayi tasaka idonta Cikin Na yazeed yayin data daga Dan yatsanta tana nunashi kai yazeed Sam bakada..... ai da Sauri Yusuf yabar wajen yana fadin Wlh itace matarshi. Feenah itakam mgn take mai bako iftawa bare inda inda,,,,,Kai dama duk wannan fadin Ran naka barinshi kayi domin Sam baya maka kyau, yanzu kazo kana ma mage mugunta katuna itama Hallitace kamar ka! kuma Sai Allah ya muku hisabi kan muguntar dakai mata, kana ganin kaidin kamar kafi kowa ne Toh kasan wa'inda Zaka rinka mawa mugunta,kada Abun ya kasance Har kan bayin Allah. daga Haka feenah ta bar wajen....da Sauri Su inno dasu Leemah dake lekensu Suka koma Ciki ganin ta tawo, Ashe Yusuf daya koma yace musu Suzo Suga su feenah na Soyayya, bayan Sunma Nazir bayani kuma Sunci Shima kada yamusu magana Shine Suka Leko Suna kallonsu Amma Sam basajin Abinda Suke cewa, Leemah har picture ta daukesu Dan ba karamin kyau Sukayi Ayanda Suka tsaya ba.....yazeed a inda tabarshi ya daskare pic din bakinta kawai yake kallo lokacin da take motsashi da irin yanda take nunashi da Hannu Sam babu tsoro ko fargaba Atare da ita lokacin da take maganar.....Yusuf ne ya karaso yadan bangaji kafadar yazeed firgitgit yayi yadawo Cikin Hankalinshi, Janshi Yusuf yayi Zasubar wajen Saiga feenah ta fito da Ruwa A wani Cup na plastic ta Aje gaban magen ko kallonsu bataiba ta kara komawa Ciki. daki Yusuf yaja Yazeed Kan bed Suka Zauna, yusuf Ya kalleshi ya daga mai gira yaaa tayi ko? Ajiyar Zuciya yazeed yayi ya yatsina face wace? Yusuf ne ya kalleshi yace wace kake tambayana, yarinyar nan mana. Aini koda Nace maka nasaka gasa tsakanina dakai bance maka harda yarinyar nan Ackiba, wannan yarinyar Abinda yafi hakama Zata iya, Dan dama batada kunya yazeed ya fada yana kara kauda kai. gyara Xama Yusuf yayi yace Wlh Malan baka isaba Ai Kaine Kace Mun koma wacece, Kuma Ai Wannan tacika kowani Sharadi dakace kafison mace ta kasance tana dasu. Yusuf Sharuddana Uku ne dan tayi daya Ai batai Sauran biyunba. Karya kake duka tacika yazeed. Na1. kace wacce kakeson ka Aura ta kasance mai tausayi! Agabanka yanzu ta dibo Ruwa taba mage, Kuma kana gani magen tasha Ruwan Sosai Sannan tabar wajen Kenan dama k'ishi take ji yasa tazo kofarka. Na2. Kace ta Kasance mai kuzari tahaka Xata iya kula da gidanka da kai kanka da kuma yaranka! So Ayanda feenah tamaka mgn tana Nuna maka yatsa bakinta na furta Abinda takeso ya'isa kaa gane cewa ita din Mai kuzari ce. Sai Abu na3. Kace wacce Xata iya kallon Cikin idonka tayi magana, Naga feenah tunda tafara magana bata kifta ido ba, gashi ta Sumar dakai Atsaye Sabida Xakin muryarta. Toh me kuma kakeso ka fadamun yazeed??? Numfashi yazeed ya Saukar Ahankali yace Abinda nakeso yanzu ka kyaleni Yusuf tunda kai kacika naci kabari Zanyi Shawara. "Alright" Yusuf yafada yace kasan gobe Xani Zaria ko Zaka Rakani? Allah ya kyauta na raka ka wajen Mace yazeed ya fada yayi Hanyar Cikin gida. Tashi Yusuf yayi yabi bayanshi Suka Shiga parlon Atare. Yanzu hatta Mamy da Abba Suna parlon fira kawai Suke Suna dariya. Inno Naganin yazeed Sun Shigo tafara waka....."Namiji kuchaki Ahadashi da kuchaka Kamarshi, Na miji miskilalle Ahadashi da Miskila Kamarshi" gaba daya parlon Suka Saka dariya Abba yace Inno keda waye haka? Kallon gefen idon yazeed tayi tace Amadi wakar mu muna yara na tuna kawai...tabe baki feenah tayi Aranta tace tshohuwar Nan bazata Rasa Aljanu ba bakinta Sam baya Shiru. Shima yazeed Cikin Xuciyarshi Cewa yayi ai gara dai goben tazo kitafi muhuta. Inno kamar tasan mai suke fada cikin Zuciyarsu tace Wanda ya Zageni Cikin Ranshi Allah ya hadashi da daidai Shi. dariya Suka kara kwashewa dashi. yayinda yusuf yatashi yace nidai Zan tafi Saida Safenku. Inno tace yusufa Agaida gida, Abba da mamy ma Sukamai Saida Safe. tashi Nazir Shima yayi ya Kalli Twins kutashi mutafi, tashi Sukai gaba dayansu harda feenah...Abba ne yace Nafisatu Kibari ki Kwana Anan mana.durkusar da kai tayi kasa tace toh Abba. Saida Safe Nazir yamusu, Yana kashe ma Leemah ido Sukafita da Twins dake ta rigima su Abarsu. Cemusu yayi gobe zasuzo tare da Mum, tukun Suka yarda. bayan Sunci Abinci Su Mamy Suka nufa Sama,inno ma tashi tayi tace bari naje nahada kayana tun yau. dariya Leemah tayi tace toh inno Saida Safe. Yarage parlon Saura Leemah da feenah besty tashi Muma muje mu Kwanta, tashi feenah tayi suka Haura Sama Atare. Cikin dare yazeed kasa bacci yayi daya rufe Ido pink lips din feenah yake gani Yayin da take motsa Small Mouth dinta, ga manyan idanunta lokacin da take magana wani irin Haske dasuke Kamar mai Shirin yin kuka, kara Mirginawa yayi tunowa da Yanda Kumatunta Suke lotsawa Ga Cool Voice dinta dake fita Ahankali wai Nan Ahakama bude murya tayi. Murmushi ya Saki tunowa da yanda take Nunashi da yatsa tana k'aradashi irin Alamar honing din nan. OMG yafada da karfi Cikin Ranshi kuma yace "Tabbas irin matar danakeson Aure kenan, duk Sharuddana ta Cika Su, Sannan gata da Kyau da ilimi" Noooo yafadi da karfi yayinda ya dunkule hanunshi ya buga Cikin dayan, Ni bazan Auri yarinyar Nan ba Sabida Abu daya, Abunda Naji Sunayi lastym, har Sai Nasan menene Sukayi Aranar. Sannan ma Ai Twins Sun fadamun Cewa tana da yawa kuka, ni banason mace lyk dat, don bansaniba ko Aljanu gareta, gata daji dakai, bama Hakaba Ai Sunce Aure Za'a Mata da yaron Uncle dinsu.tsaki yaja yacigaba da mirgine mirginanshi, da ker dai bacci barawo yayi gaba dashi Aranar. bangaren feenah itama kasa bacci tayi tana tunanin Anya mutum ne kuwa wannan brother din na Leemah? Shi Sam baya ganin darajar kowa, wannan Shi dama Sojane Sai ace Sun Saba da bakar Xuciya but ko yaya Nazir da yake Soja Ai baya irin haka. Kai Wannan matar dazata aureshi tashiga uku, Ni misali ko dauramun irin mazan nan Akai A kafa inajin da gudu Xan kwance Wlh. Tsaki taja tunowa da muguntar dayayi ma magen nan, take takara jin tsanar yazeed Acikin Ranta. bude Ido Leemah tayi jin karar wayarta dama ita Tuni bacci yayi gaba da'ita. ganin feenah batai bacciba Sai juyi take yasata waro ido besty baki bacciba kinaji Aka kirani har 5miscall baki peeking ba kuma yaya Nazir ne fa! gani tayi bata kalletaba yasa ta d'aka mata duka ina mgn kinyi Shiru feenah. Arazane Feenah ta tashi Xaune tace banfa jiba. daga gira Leemah tayi tasaki Murmushi lokaci daya tace da kyau,tunowa datayi lokacin da take irin haka A Skul. Menene feenah ta wurga ma leemah tambaya? Aa ba komai ki Kwanta kiyi bacci nace. Ok feenah tafada yayin da taja blanket ta rufa. Murmushi Leemah takara Saki yayin data d'aga wayarta dake famaan Ruri.....
da Sassafe Inno yau tariga kowa tashi,daret kuma kitchen tashiga Acewarta bari ta hada musu karin kumallo Yanda dasun taso Sukaci Abba ya maidata katsina. Aiko waina tayi da miyar taushe wanda yaji tantankwashe.feenah ce tafara Sakkowa jin kamshi kamshi tanufa kitchen inno ta gani ta gama hada wainar tashirya tsaff. Inno ina Kwana, Saida Aka dan kwashi lokaci tace Lfy a takaice wai itama miskilanci tafara irin na yazeed da feenah😂 tabe Baki Feenah tayi tace toh dame Xa'aci wainar? Kular data Zuba wainar inno ta dauka takai kan table saida tadawo tace, da Ruwan Lipton...tsayawa feenah tayi tana kallon Inno ganin Yanda take bata Amsa, daga bisani ta daura Ruwan Zafi a huta tana Shirin yin kunun gyada. Kasa daurewa inno tayi tace Nafisatu Ki kira hafsat tazo da iyalinta dan naga tanason waina kinga Saisu karya Anan ko? daga mata kai feenah tayi kawai.Inno takara Cewa Zaki kirata ne koni na kira ta? Kirata feenah tace A takaice, Inno ta karkada Kai Alamar mema yasa take kula wannan yar? daidai Sanda Feenah tagama hada kunun gyadar inno takara juyowa Nafisatu Mutan gidan har yanzu basu tashi ba? "Eh" feenah tace tafita da place din hanunta, kwafa Inno tayi tace Zakuyi nadama. Karfe 8 daidai duk yan gidan Suka tashi Kowa nashirin wanka. Inno taba Leemat waya takira mata Mum mahaifiyar Feenah wai suzo su Karya tayi waina.Amsan phone din Leemah tayi Sanin fitina irin ta Inno. Aikuwa ba'afi Minti 30 ba Su mum Suka karaso gabaki dayansu Har dad, Nan Akayita Murna aka wuce danyin breakfast. Fitowar Yazeed daga Wanka Kenan Yana Shirin Shafa mai yasa Kaya,tura kofarshi Akai Ahankali Aka Shiga, Innalillahi ya fadi da karfi ganin Mufeeda ce! Murmushi tayi takarasa shiga Ciki tace yadai? Kofa ya nuna mata yace tashi kifita kamin na karyaki Acikin gidan nan.Murmushi ta kara yi tace duk Abinda kace daidaine Zanfita Amma kasani Ayau Saina dandana Yanda yazeed yake! Ido yafiddo waje yace bakida hankali ne?kitashi kifita nace, kona Zaneki Cikin gidan nan kuma Naga Uban da Zai tsaya miki. dariya Mufeeda tayi Sosai tace babu wanda Zai tsaya mun kuwa Sabida Kana takama da kyau da dukiya, Amma Kasani yau Saika biyamun bukatata Zanbar gidan nan,kokuma wlh yanzu Nafita Nashiga gidanku nace Raping dina Kayi Kuma Kake guduna kaki ka aureni, kuma kasan tsaff Zasu yarda domin ran Nan kakar ka taga Sanda Nafita Inaga tarufamaka Asirine kawai. dafe kai yazeed yayi ya Zauna kan bed yana kara dayasanin Sanin mufeeda Cikin Rayuwarshi....karasowa tayi gaff dashi Honey Kayi hakuri Sonka nake da yawa Sha'awarka ta Hanani Sukuni ka daure muji dadin Juna wata kila kaima kasaba da irin haka. Runtse Ido yayi wani irin takaici yakeji Aranshi, tashi Yayi Xaidau jallabiyarshi yasa, mufeeda takara Xaunar dashi pls honey ka kulani mana...hannu takai kan kirjinshi tana Shafa gashin tana honey wanann yana burgeni, Yazeed duk jikinshi yayi Sanyi yafara fita hayyacinshi domin shidin mai Saurin Sha'awa ne. Ganin haka Mufeeda tafara zarcewa! gaba daya tafara wasa da Sasan jikinshi, Shima gaba daya yafita hayyacinshi bakinta ya kamo yasaka nashi yana kissing dinta sosai tana mayar mai da martani. dad ne yace munata cin dadi banga dana ba. da Sauri Inno tace Halan yana chan yana cika yana batsewa,dad yace yakamata Akirashi Shima yazo yayi breakfast. Mum tace Mubeen jeka kira mai kyau kace yazo. da Sauri inno tace ai tunda Nafisatu na kusa Kawai taje takirashi, kallonta Feenah tayi ta galla mata harara, dad yace Ummina kirashi mana tashi tayi tanajin Haushin inno ta nufi part din yazeed. Su yazeed an Lula gaba daya bema san awaci duniya yake ba. Knocking take iya karfinta ba'a budeba. Mufeeda da tunda aka fara taji, murmushi tayi domi burinta yacika, dama So take Wani yagansu tasan dole za'ace ya aureta ta hakane Xata cika burinta na mallakarshi. tura kofar Feenah tayi da karfi dantana ganin kamar wulakanci yayi mata.....Ido ta fiddo waje yayin da take maimaita innalillah. Mufeeda Aranta tace yawwa kanwarshi ce Afili kashe mata Ido Mufeeda tayi tana cigaba da Shafa Jikin yazeed duk dacewa da kaya Ajikinta Shikuma towel ne kawai amma ya rufe.....Saman kirjinshine kawai Abude. fita feenah tayi jiki ba kwari har wani duhu take gani tace yace yana Zuwa daga haka tayi sama Abinta. Shikuwa gogan bema San me akeba kokarin cire ma Mufeeda kaya yake tayi Sauri ta Tashi daga jikinshi, domin dama ita har ga Allah tana tsoronshi irin yanda yake juya mace baya ko gajiya. jakarta ta dauka da gyalenta tace honey Anzo Ana knocking inaganin nemanka Ake, kaje kada Akara zuwa ni natafi, Karka damu zanfita lfy. daga haka tayi Hanyar waje. tashi yayi rike da mara yashiga toilet.
Page....31
Bayan ya fito daga wanka Shiryawa yayi Cikin wata Shadda Sky blue ya feshe jikinshi da turare yayi Hanyar Cikin gida, Sai Asan nan yadamu dasanin waye yaje kiranshi daxun? D'an tsayawa yayi yana tunanin gashi kofar ba'a Rufe take ba..Toh Amma banajin wani ya ganmu domin naji Mufeeda tace knocking Akayi! Jikinshi dai yana bashi wani irin Alamu Ahaka yashiga Ciki. Zaune Suke Suna fira mum, mamy, dad nd Abba, Zuwa yayi gefensu yana gaidasu Cikin Sakin fuska duk Suka Amsa. dad yace my Son Anje kiranka kayi breakfast bakazoba kuma bayan Kace kana Xuwa. "Cikin Ranshi yace waye yace Haka Oho, bayan ko Shiga ba'ai ba" Afili cewa yayi daddy na tsaya Shiryawane. Allah ya muku Albarka. Amn yazeed yafada yace Ina Nazir? Mum ce tace yanzufa yake Nan wajen da! dad ne ya Dan tabo ta ya nuna mata Nazir da Leemah dake daga wajen parlon Suna Zaune da Alama fira mai dadi Suke. Murmushi mum tayi itama ta nuna ma Mamy dake kusa da ita...Cikin mamaki Mamy ke kallonsu take kuma Suka bata Sha'Awa dan ba karamin dacewa Sukai ba. Itama Abba ta nuna mawa Su, Shima dadi yaji har Cikin Ranshi ya kalli yazeed yace ka gansu Chan. Juyawa yayi ya kallesu Sun bala'in yin Kyau Ayanda Suke Azaune gashi Sai wani Murmushi Suke Sakar ma junansu, Cikin Ranshi yace Bakuda matsala. Inno ce ta Sakko rike da katuwar jakarta tsakiyarsu ta tsaya tana kallon Abba. Ya baka Shiryaba Amadi? Inno tafiya Zaki da gaske Mamy ta jefa mata tambaya? Tafiya Zanyi mana nagaji da Abunda Akemun Acikin gidan Nan. dad din feenah ne ya kalleta yace Inno kiyi hakuri kizauna ki fada mana me Ake Miki Sai A gyara insha Allah. Zama tayi tace ni banaso ma a gyara yau din Nan Saina bar gidan Nan. Hayaniyar inno ta juyo dasu Leemah dake Soyewarsu, tasowa Sukayi Ajere Suka nufo wajenta. Inno Ya naganki da jaka haka? Naziru yaron Albarka tafiya Zanyi Inda Ake ganin mutumcinta. Shidai Yazeed bece komaiba wayarshi kawai yake dannawa ko kallonta beyi ba. Inno Ki fadamana ko nice ke miki laifi ban Saniba Mamy ta fada cikin Sanyin Murya. Kallonta Inno tayi tace Ni Fatima bakimun komai ba kedin macen kwaraice ina Alfahari dake, kuma kaima Amadi bakaimun komaiba, laifinku daya dakuka kasa tankwarar da danku kan bakar Zuciyarshi.