Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abun. daga Kai nayi jin Ana kabbara Su feenah na hango jere kusan Su8 farin material dinkin doguwar Riga ne Ajikinsu, yayin da Suka daura dogon farin hijaf har kasa Masha Allah. Sun hasku kuwa. Tun kafin Su Xauna Naga feenah ta dafe kanta,Leemah ta tambaya besty lfy ko kanki ke ciwo? Wlh Leemah mutanen nan Sunmin yawa Anya Xan'iya tashi jifa mutane ga Hayaniya. Sorry besty Ki daure nan da 1h mun gama Insha Allah. Kada Kai feenah tayi Alamar toh. Cikin kan kanin lokaci wani malami yazo yafara bude taron da Addu'a. ya yaba kwarai da Hazakar Su feenah bangarin Boko,da islam Acewarshi be taba ganin babbar makaranta da'aka ware bangaren islam ba Sai wannan, Nan dai yagama Sanar da Abin da zeyi daga bisani ya Ambaci Leemah Amatsayin wacce Xata fara fadakarwa. fitowa Leemah tayi Anatse ta karasa tsakiyar wajen ta karbi Speaker. Nazeer na hango Sai wani Murmushi yake Ko mai yake fadi Aranshi Oho. da Sallam ta fara bayan Jama'ar wajen Sun Amsa tacigaba. (UMIRNA AN NAKIFA AMAMAKUM) " An umarceni dan na tsaya Agabanku, domin Nayi muku wani Dan jan hankali/wata yar Nasiha da Abunda naga matan Aure Sun fara mancewa ko kuma Sunakin Aikata Maganar Allah S W A da Abinda ya Aiko mazonsa Annabi Muhammad S A W dashi. Ayanzu mafi Akasirin matan Aure Sune masu Aikata babban laifi,Toh bari nafada miki yake yar'uwata kada Ki bari Azugaki kirinka dagawa ki tsaya Amatsayin da Allah ya Ajiyeki,ki Zauna dakin ki kada kifiye yawan yawo Kamar yadda Allah S.W.A. Yake Cewa (wakarna fi biyuti kunnah wala tabarrajina tabarrijal jahiliyatal Ula) MA'ANA kuzauna Adakinku kada kufiye yawan yawo irin Na Matan jahiliyya na farko. Ai wannan Abunda Allah yai mana gata yayi mana Kuma darajarmu Allah ya daukaka.domin Alokacin Jahiliyya mata ke biyan Sadaki,matan da da muke yawo tsirara wanda da birnesu Ake da Ransu,Alokacin Jahiliyya Mata Su Suke nemoma mijinsu Abinci,Alokacin Na miji yanada ikon ya Auri mace dari ko dubu,Alokacin jahiliyya mace Saita Sadu dana miji20 ko30 koma fiye da haka, har saita haihu Sannan Asamo wacce tasan kama da Sifa Sannan Atara Samarin nata Sannan adauko jaririn yana Hannu Anatafe Ana kallon Fuskar Samarin nata duk wanda yayi kama da Wannan yaron toh Shine uban Dan dashi Za'a durama Uwar yaron Aure! (MA'AZALLAH) "wannan kazanta har ina" Amma da Zuwan musulumci ya Ruguza yin hakan,yace mace yar'gata ce Kai Namiji kai Zaka nemo mata Abinci,Sutura,ilimi,lafiya da makamantansu.kuma Akace Shi Namijin Shine Zai bata Sadaki kuma Akace ta lullube jikinta ba'ayarda ta nuna tsiraicinta ba. Toh Mata kuna nufin Allah bai iyaba,Mazon Allah bai iyaba kuma musulunci bai iyaba??? Sai Ayanzu ne Wasu tsinanu, Fasikai, fajirai Zasu fitoh da mata suce Wai A inganta Rayuwarsu,Ai wannan Raini ne da wulakanci,Sai Ayanzu wasu Zasuce wai Asama ma mace kaykykyawar Rayuwa, wai duk Namiji ya Auri mace daya Kawai ta isa!😡 Toh Akwai Rayuwar data fi ta Allah da manzon Sa ne??? ko kuwa Akwai Rayuwar datafi ta musulumci? Abun bakin ciki Mu mata Shagalar tamu tayi yawa muda Akace kada mu bayyanar da adonmu ga mazajen daba namuba,Amma yanzu mata dazarar Zasuje unguwa,Zaka ga Sun dauki jan baki,jagira,hoda,eyeshadow, da dinki na Rashin mutumci mai matse jiki, Waishi Show me! ko follow me da mayafinta Akafada. ( wannan Sai a Instagram Zakaga mata da Shigar Nan kaya ya matsesu Ana juyi Ana daukar Video domin mutane Sugani Asan Ita mai kyauce) Toh Mazon Allah S A W yace( Nau'i biyu daga yan huta banga kamarsu ba! Wasu mutane ne Atare dasu Akwai bulalai kamar kunnuwan Shanu Suna dukan mutane da ita.da kuma wadansu mata da tufafinsu Amma matsairaita ne karkatattu idan Suna tafiya masu karkatar da hankulan mutane izuwa garesu,kawunansu kamar tozon Rakumi bazasu Shiga Aljannah ba,bama Zasuji kamshinta ba kuma kamshinta Ansamu ne daga tafiyar kaza Zuwa kaza.) Bama Wannan ne yafi bani haushi ba kamar yanda mata yanzu Suke illata mazajen Su,wasu Su kashe su,wasu Su konasu wai duk Dan Sabida basa Son kishiya! Toh wallahi tallahi idan muka yarda da Wannan Muna Aikata Son Ranmu muna Cikin bala'i da Musiba Mai girma. Dan haka manzon Allah S A W yace ma Sahabbanshi (kaifa bikum iza daga'imatikum Wa fasaka Shababikum) "yaya Zaku kasance idan matanku Suka rinka dagawa da Shishshigi, Samarinku Suka Zama fasikai?" Sai Sahabbai Sukace (Aya kuna Zalika ya Rasulullah?) "Shin haka Zai kasance ya Ma'Aikin Allah?" (Sai manzo yace musu fiye da haka ma Zai kasance)
Yau gashi muna gani maganar Mazon Allah S A W ta tabbata. domin gashi muna gani matanmu Na yanzu Saidai muce INNALILLAH WAINNAH ILAIHIR RAJI'UN! domin mace ce Zaka ganta ta tawo mayafi Akafada tasaka Chewingom Abaki tana tafiya tanaci Har Wani karairaya Zakaga tanayi tum barin Idan tazo majilisar maza har wani fari da ido Zakaga tanayi Wa'iyazubillah😭 kuma matar Aurece Zakaga taje gidan biki tacire dan kwali tana tikar Rawa Ita da yarta Ai wannan babbar musibace. Uwa'Uba yanzu mafi yawan Akasirin mata dabi'ar lesbian ita Suka maida Kamar Ruwan Sha! Leemah na kaiwa Nan kuka ya kwace mata, Saida tadanyi mai isarta tacigaba, da Matan kasashen waje Su Akasani da Wannan dabi'ar Amma yanz matanmu Na Hausawa Su Suke Aikata hakan musamman idan kahau Twitter Anan Suke Xuba video's dinsu idan Ka gani kai ka Rantse kace ba yaran Hausawa bane Innalillah Saidai kawai muce Allah ya gyara ya Shiryar da Xukatanmu. Daga Haka ta Ajiye Speaker ta bar wajen da dan Hawayenta. Malamar dake gabatarwa ta taso Masha Allah tubarakallah Malama Halimatu Ahmad mungode Allah yasaka da Alkairi. mata iyayenmu da yayyenmu da fatam kun gane Cewa Zafin kishi Hauka ne,domin ada mata bamuda Wani yanci Saida musulunci ya kawo mana, toh Kuma Dan Allah ya hallata ma maza Auren mace fiye da daya,muce bamu yarda ba Anya Munma kanmu adalci Anan???? Allah ya kyauta. Malamarmu ta gaba itace Kausar Hafiz malama bisimillah... domin nasan Kema bazaki Rasa Abin fadi ba.

Tasowa Kausar tayi daga inda take da'alama itama kukan tayi game da jawabin Leemah.Sallama tayi irinta addinin musulunci, gaba daya jama'ar wajen Suka Amsa. Tafara dacewa Abinda Malama Halimat Ahmad ta fada tafadi gaskiya,kuma ta kara Zaburar damu.dama ba wani Abu bane yake Rudarmu Mu Mata illah Rashin hakuri da dangana, da kwadayi dakuma Son kyalekyale na duniya. Shi yake Shagalatar damu harmu manta Xamu koma ga Ubangijimu. Wlh malama dazaki fita kiga Yanda mata Suke A hanya ke kya Rantse kice ko babu Sauran mace Acikin gida. Ayanzu Saiki Kasa gane wacece matar Auren wacece Mara Auren,domin Zaka gansu Sunci ado kuma babu lullubi Atare dasu.Toh mai tsira da Aminci Allah Su kara tabbata Agareshi yace!( mace tanada Sutura guda biyu.mijinta dakuma kabarinta) Amma Saika ga Uwa A zamanin nan tasaka yarta Agaba tana mata huduba wai don mijinta ya hanata Xuwa biki, Suna, ko Zuwa gida wankan jego😤toh wannan Hadisin Saiya tunamun da Wani babban Sahabin Manzon Allah S.A.W. yakasance Shi dakanshi yake ma yarshi Aure ya kaita gidanta,yayi Sallama da mijin nata yace ga yata Nan nakawo Maka Amana,kekuma idan kika fitoh kabarinki Za'a kaiki.Kuma tashiga ba zaka taba ganin tafito ba. Amma wannan Matan namu na Xamani dazaran Ka gansu Ahanya,kai Amarya Zasu,ko party,Ko Hinin Suna, ko kamun Ango.Wlh most especially batare da izinin mazajensu Suke fitowa ba.Toh yar'uwa mai tsira da Amincin Allah yace(duk mancen data Saba ma mijinta tsinuwar Allah da Mala'iku data mutane gaba daya ta tabbata Agareta) yar'uwa kodan wannan Abinda Allah ya fada ai kya Rage Wani Abu daga Cikin Halinki. MANZO YACE KUMA (Duk matar data mutu mijinta yana Mai yarda da ita Allah S.W.A Zai sakata Agidan Aljannah) Sannan manzo yana maiyimana gargadi Akan Kada mufita batare da izinin mazajenmu ba. ga dai Abinda yace (dukkan matar data fita daga gidan Mijinta batare da izininsa ba ta kasance tana Cikin fishin Allah S.W.A. har saita dawo ta nemi daya yafe Mata kuma ya yafe matan) Wlh wani Abu dayake Kara cimun tuwo A kwarya Shine,Saikaga maza Sun fita da dadi ba dadi Suna nema ma iyalansu Abinda Xasu ci,Kosu daura,ko suba yaransu,Amma su Rasa wanda Xasu ha'inta Sai mijin nasu,idan basu ha'inceshi ta wajen cefane ba Xasu ha'inceshi ta Wajen fita Un'guwa. Abin bakin Ciki Ayanzu Uwa Ita ke kashema yarta Aure,toh Dan Allah menene Rivar,Saikiga Andawo gida Anzauna Anajiran bazawari yazo mata,daga Anji Shiri na lokaci Saikiji anfara Xuwa Wajen boka, Wlh Malan yatace tunda Aurenta ya mutu har yanzu bata Samu Wani Mijin ba, inaganin tsohon mijinta Shi yayimata Asiri. Shikuma boka Dan iska makiyin Allah saikiga ya karkace yasata Ahanyar karyace karyace Kawai dan ya karbi Abin hanunta. Wai yaushe mata Zamuyi Hankali ne?kiduba mazanjenmu Xasu kawo mana kayan Abinci Kamar su Shinkafa,masara,wake da dai Sauran Su, Amma Saikiga mace ta iba tana boyewa wai dan kada mamarta tazo tarasa Abinda daxata bata wannan ai Sata ne Wlh.domin laifi kikaima Allah Sa'anan shi mijin Naki. Allah ya sawwake yasa mufi karfin Zukatanmu. daga haka kausar takoma ta Xauna. Wata daga Cikin daluban ta taso tayi gdy daga bisani tace Malama Khadija bisimillah.

Kallon feenah Kausar tayi Ashe Malan khady yasamu dayar? toh nimadai sai yanzu nagani Kausar.tafff bari Naji me yabata ta fada. Sallama itama khady tayima jama'ar wajen kamar Yanda taga Saura Sunyi.gaba daya taron wajen Aka Amsa.ta daura da Cewa Ni bansanma Mai Xanfada ba domin duk wa'inan malaman sunriga Sungama kwance mana Xani Akasuwa. Kallom Kausar Leemah tayi sukayi dariya,Lallai Malan Abinda yabata ta yayi daidai da yanayinta ne. Cigaba tayi Ku'inaganin bakusan Halin mazan Nan bane bawasu wanda Xa'a dauka Ayita tarairayarsu bane, da Zarar kinama Namiji ladabi da biyayya Abinda ma Xaifara Shiga tsakaninku Raini ne da wulakanci Harma yayi nufin yayi miki kishiya.kuma dakuke ta Wani fadin kar mufita kar mufita mu Zauna Adakin mazajenmu,Sukuma Mazan dasuke yawonsu Cikin gari fa? Har kuke kawo Hadisi da Aya wannan hadisan da Ayayoyin Ai bada matan wannan Xamanin Ake ba da matan Sahabbai ko Annabawa Ake. Kuma idan mace bata fita ta Neme yancinta ba yaushe Xata nema? Kullum tana daka Akulle kamar wata wardrobe waye Xai Santa? Kuduba Matan Sauran kasashe wa'inda kansu ya waye,inda Zakiga mace a Shugaban kasa ko Governor,kuma kuduba matanmu na wannan kasar Suma nan Zakiga mace a minister ko C M N,Ko Kuma Shugabar wata ma"aikatar. Amma kwa hada matan nan daku Wanda kanku yake Aduhu haryanzu baku waye ba?Ku bakusan duniya ta chanza ba kuna yawo cikin lullubi kamar wasu Munafukai😤wlh nidin nan dakuke gani n.a. tsakanina da namiji babu wata Amana domin shi ba dan goyo bane ba,ke matukar ma Naga Zaimun wata gargada sainace Ya Sakeni nikuma na bidi Wasu ga mazan Nan suna Yawo Kamar janfer a jos. Ni iya Abinda zan fada Kenan. Mai gabatarwan ce ta Amsa toh Allah ya kyauta Zan'Iya cewa kawai Anan. Malama Feenah Umar Faruk bisimillah. Yazeed da kanshi ke durkushe besan Sanda ya dago yana kallon yanayin yanda take tafiya Kamar batason taka Kasa.Subhanallah 1yr danayi kadai banga yarinyar Nan ba kalli yanda takara girma da Kyau dan tsaki yaja inama Ruwana da ita. Cikin natsuwa ta karasa Wajen..Sallama tayi Cikin Xaxxakar Muryarta Wanda ta dira Cikin kunnan yazeed! " She is So Cute nd She have a Nice Voice" Cikin Ranshi yayi maganar Amma Sai yaji Yusuf yace Allah ko? Kenan Afili Nayi maganar. Kallon Yusuf yayi yace yes kallitafa nadade inason wakokinta wayarshi ya Nuna mai Wata mace.dariya Abun yaba Yusuf Sosai yace Kawai ka Aureta. Tsaki Yazeed yaja yabar maganar. Magana feenah tafara. Haba malama Khadija Koda yake bakibani mamaki ba domin Kowa yasan Halinki da tarbiyarki. Wainan Abun da yan'uwana suka fada aiba kwance Xani a kasuwa bane, Gyara kayanka Ai baya Xama Sauke mu Raba.dakike cewa bamu San halin mazan nan ba toh kinsan duk Namijin dayake sonka baxai wulakantaka ba.domin Manzo S.A. W. Yace (duk Wanda baya kishin matarsa bazai Shiga Aljannah ba) kuma dakike maganar kishiya ai Allah bai Hana mutum ya Auri mace fiye da daya ba. Saurara kiji Abinda Allah S.W.A. ya fada Cikin Al'Qur'an *FAMKIHU MAZADA LAKUM MINAN NISA'I MASANA WA SULASA WA RUBA, FA IKIFTUM ALLAH DA'ADILU FA WAHIDATA AU MA MALAKAT AI MANUHU*! ( ku Auri Abinda yamuku dadi nadaga mata biyu biyu,ko uku uku,ko hudu hudu.idan kunsan bazakuyi Adalci Atsakaninsu ba toh ku auri guda daya kokuma Abinda hanunku ya mallaka na daga kuyangi) dan haka Malama Khadija Kinji Allah be hanasu Auren mata hudu ba,
Sadai idan bazasuyi adalci atsakaninsu ba.kuma dakike magana Akan fita har Kina cewa wai muhada kanmu da matan Annabawa kona Sahabbai! Kwarai kuwa dole mutun musulmi yayi koyi dasu, domin sudin iyayen Mumunai ne Kuma Su tsarkaka ne. Sayyidina Aliyu Allah yakara mishi yarda yace.... (babu yadda Za'ai mace tafita daga Dakin mijinta batare da wata babbar lalura ba,kuma idan ya kasance ma Xata fita tanemi Xanin baiwarta ko maiyi mata wanke wanke ta daura tayanda babu Wani namiji dazai ganta yayi Sha'awarta)Amma saikaga Matan Xamanin nan Idan Zasu fita unguwa Ansha ado Abinda batamawa mijin nata.
Kuma maganar dakike kan Sauran matan Kasashen dasuka Cigaba inda Xa'aga mata a Governor Ko wasu mukamai ai Manzon Allah yace duk jama'ar dasuka Shugabantar da mace baxasu Rabauta ba Ranar Alkiyama.kuma kince tsakaninki da namiji babu wata Amana dayayi Miki gargar Saikice yabaki takarda toh wannan Kuma Sai idan Kinyi Auren. Allah yasa mudace.daga haka takoma ta Xauna. Masha Allah jama'a suka rinka fadi yayin da Wata malama ta taso ta Rufe taron da Addu'a Su feenat Sun Samu kyauta masu yawa Dan Har kujeron maka Aka basu.daga Haka taron yatashi Cikin farin ciki. SU mammy Sun dau hanyar komawa Yayin dasu Leemah Sai Xuwa gobe.


Page...44

Washe gari tunda Safe Su feenah Suka fara Shirin barin makarantar. Haka kuma dalubai Sai Shigowa Suke Suna yaba bajinta irin tasu feenah, Kusan daidai kone Wa'inda Suke Cikin Skul din da basuzo wajen Su feenah Neman Alfarmar Su Zama kawayensu ba. Kausar da Leemah Sune masu Amsa musu wanda feenah ita dai Saidai tayimusu Murmushi,Anan ne Suka gane Ashe friends din Su3 basuda matsala da Suna masu kallon Rashin fahimta.Sundai gane Acikinsu Feenah itace marason magana wasu Suna fadi Aransu Miskila ce wasu kuma Suna ganin Tanada Class ne. Leemah duk wa'inda Suka Shigo Saita Sanar dasu bikin Kausar. da Haka drivern Su Kausar yazo inda Zai Aje Su leemah A kd Kafin ya wuce da Kausar Zaria. Mota Suka Shiga yayin da driven ya kwashe Gifts din na musamman da Aka ba Su,Dan ma Su Mamy jiya Suntafi da Wasu. Cikin mota Gaba dayansu Suke kara jin dadin irin Kayutar Xuwa Makka da Akai musu. Kausar ce tafara magana Nifa Nafison nafara Zuwa Kafin bikin Nan. dama Ai yafi my Kausar daga Chan basai muwuce Sudan dinva. Haka kuwa Leemah kin kawo Shawara mai Kyau,Amma Ina Zamu Sauka a Sudan kike gani? Hotel mana Ko kuma gidan Hajiya...wama take? Gara dai Hotel din feenah ta fada ataikace! Shikenan Hakan ma yayi yaushe Suka Shirya mana tafiyar Kausar ta tambaya? bari muga Leemah ta fada tana ciro wata takadda. Kai Ashe jibi nema tafiyar. Kai haba Kausar ta fada tana karbar takaddar.Kaai d gaske kuwa Lallai Xamusha gajiya. Kallonta feenah tayi gajiya Ake da ibada See you.dariya Kausar tayi nidai bance ba Naga Yau Xamu koma gida,jibi Muje Saudiyya Xuwa 1week muhuce Sudan,da mundawo Biki Xa'a fara Kinga Kuwa bamuda Hutu. Zubaida kawai! Feenah ta fada tana Tabe baki. Allah ya kawo wanda Zaiyi maganin wannan bakin naki.dariya Leemah tayi tace Amin. Haka Sukayita firarsu gwanin Sha'awa. Tafiyar Awa daya da Rabi yakaisu kaduna. Bari mufara Aje feenah ko.eh yafi kufara Ajeni domin wlh kun isheni daman. dariya Sukayi kausar tace iro Unguwar Dosa Zaka Ajeta ka gane gidan ko? Ahhh ai kinacewa Unguwar Dosa na gane.yawwa Kaimu Chan daga Nan gidan Hajiya fatima inda kake kai Hajiya Xaka Aje Leemah.Toh toh Toh ba damuwa Ai iro ya fada lokacin dayake parking kofar gidan Su feenat. fita tayi Kausar nafadin sai Mun hadu,Allah yakaimu feenah ta fada tayi Cikin gida. Leemah wannan Matar brother din Naki Saimun chanza ta.kinban dariya Ai Shima brother din nawa Halinshi ne Kinga vasaisu dafa kansu Suci ba. Lallai kam Su dafa kansu Amma wannan Shan kamshi haka,ke Nifa har yanzu banma yarda Suna Son junansu ita da yazeed ba,kinsan dai idan da gaske ne babu yanda Xa'ai feenah takasa fada mana. Mtsww ke Wlh Kausar din Nan kincika maida Abu baya,ke duk pictures da Video's Dana nuna miki basu gamsar ba. toh Leemah bakya ganin tunda mukazo yazeed baizo Abuja ba sai jiya,jiya dinma basu wani haduba bakiga yanda Nazir da Yusuf Suke rawar kai ba har Saida muka hadu dasu Sukaji dadi,Toh babu yanda Xa'ai Ace Feenah Na Soyayya da yazeed kuma Sukaasa haduwa Ajiyan Nan. Oh My God Kausar har yanzu baki gane boye Al'amarin suke ba basason fa Kowa ya Sanine,ke dakanki kinsan inno bata fadin maganar da ba daidai ba,kuma yusuf din daya fada mana Shima karya yayi kenan? Ke bama Wannan ba Sau Nawa Ina ganin feenah da bro Yazeed Sun kebe Suna magana idan duk wannan be isheki sheda ba pictures din Dana Nuna miki Ai sun isa. Ajiyar Zuciya Kausar ta Sauke Shikenan Amma.....katseta Leemah tayi kidai Xauna Xakisha mamaki idan kika gansu da kanki kya Rantse kice dama Chan Atare aka haifesu.dariya Kausar tayi Xanso Naga feenah an yazeed waje daya. Murmushi Leemah tayi daidai Sanda Aka karaso gidansu. Toh my Kausar Sai mun hadu pls kigaida Hajiya Sosai. Tom insha Allah my halimcy bye I will miss you. Me too bye. Daga haka tayi ciki Su Kausar Sukayi gaba.

Tana Shiga Twins Suka taso da gudu Rungumeta Sukai ur Wlcm Aunty feenah Suka fadi Atare. Thanks Cuties muje kada Ku yardani.dariya Sukai mubeena tace Aike babbace bazaki fadi ba. Waye yace babba baya faduwa Mubeena? Mai Kyau ne ya fada mana. Tsaki feenah taja tunowa datayi wa Suke kira mai Kyau, Shikenan ka dawo yanzu Zasu isheka da Xancen banza.kallonta Mubeen yayi daidai Sanda Suka Xauna kan kujera. Aunty feenah ke bakyason mai Kyau ne? Yana dariya yanzu fa,kuma yace Xaije Saudiya ko mubeena? Eh mana kuma Xai Siyo mana Aunty balarabia. Nidai kutashi ku kira mum pls. Tashi Sukayi Suka tafi da gudu.Cikin Ranta take fadin wai wani Aunty balarabia ya Xauna yana gaya musu Shirme. Mum ce ta Sakko Oyoyo My daughter,tashi feenah tayi ta Rungume mum.mumy ya gida? Lfy my daughter ya Hanya.Alhmdllh mum.kinga yanda kika kara kyau my daughter kaman ina kusa dake Lallai Leemah na kulamun dake.dariya feenah tayi Kai mum.mumy kinji jibi Zamu tafi.Kai dama da wuri Aka shirya muku tafiyar kenan? Eh wlh mum daxu naji su Kausar Suna mgn a mota. Amana addu'a.insha Allah mum.Nazir dake Shigowa yanzu Sister yaushe kika dawo? Oh yaya Nazir ka Zauna mana. dariya yayi yakarasa ya Xauna ya Leemah ta? duka Mum takai mishi Mara kunya Kawai Agabana kake Xancen budurwa. Am Sorry mumy. Yawwa mumy mun hada tafiya Zuwa Saudiyya Nida yusuf da yazeed. Kai Haba yaushe kuma? Inaganin Xuwa gobe ko jibi. Lallai kun kyauta kunga Saiku hada tafiyar dasu Feenah gaba daya.kallon feenah Nazir yayi Sister kuma tafiyan yanxu ne? Eh jibi ne Amma kuyi tafiyarku daban. matsawa yayi kusa da kunanta Sister ya haka Kibari muje tare dan Naga Leemah da Kyau. tabe Baki feenah tayi ta tashi Mum bari Naje Wanka.ok daughter kiyi Saikizo ga Abinci. Maika fadama yarinyata kasa ta tashi? Sosa Kai Nazir yayi mum bakomai.kai kasani dai Garama dad dinka yazo Afara maganar Aurenka mu huta. dariya Nazir yayi mumy tawa ni kadai. Kajika Sauran yaran nakaisu bola. Nidai bance ba mum dinmu.

Xaune Suke gaba dayansu a parlo da Sallama takarasa.Oyoyo Halimatu Oyoyo Halimatu. Karasawa tayi ta hau Cinyar Inno.kai daughter karasamun Uwar tawa Xaki? Abba Wane ni Sannuku da gida,Sweet Mamy Hy, bro Miss you. Murmushi Mamy tayi Allah ya Shiryamun ke.Amin Abba ya fada Suna dariya. Kallon yazeed inno tayi tsaka bakaga gudan jinina bane? mtww wai tsaka ni wlh Abba kaja mata kunne tafita harkata! Kaci gidanku yazeed Mamy ta fada tana nunashi da Hannu. Sunkuyar dakai yayi Sis ya Skul din? Nifa fishi Nake dakai bro Yazeed kaki kaje ka ganni Sanan yanxu Ina maka magana kayi Shiru. Sorry Sister kece daga Xuwa Kika nufi wannan tshowuwar. Ayeririri inno tayi guda yau nagane kishi irin na yazeedu dama Nadade danasanin kishina kake Cikin gidan nan Shiyasa kake Alfarma,Aurene dai kayimun tsufa Akai kasuwa.dariya duk Sukayi, banda yazeed da yaja tsaki Mtsww kinada matsala wannan tsohuwar Wlh. Tashi yake kokarin yi mai ya tuna yadawo ya Xauna.Abba jibi ne tafiyata Xamuje tare da Nazir da yusuf! Allah ya kaimu my Son. Amin Abbana,mamy bakice Komai ba. Allah yamuku Albarka Son Allah ya tsareku gaba daya.Amin Mamy ta. bro yazeed Ina Xaka ne wai??Sister Saudiya Xani Nayi muku addu'a. gyaran murya Inno tayi tana kyafta ma leemah ido. itama leemah kashema inno ido tayi Alamar ta gane. Laaaa Abba Ai muma jibi Sukace Zamu tafi. Kallonta yazeed yayi kinga idan kinje Saikiyi addu'Anki ma kawai. dariya Leemah tayi kaima ka karamun da taka ba. Tunda tafiyarku taxo daya ai saiku hada tafiyar gaba daya ko? Mamy ke tambayar Yazeed. Haka kuwa ya dace inno ta fada. Hararar inno yayi,ya kalli mamy. Kai Aa mamy tunda itama da kawayenta Zata Gara Suyi tafiyarsu ni banason Shirmen Su. da Sauri Inno tace Amadi kanajinshi fa. Murmushi Abba yayi kyaleshi tashi kaje yazeed Kowa yayi tafiyarshi daban yama fi. Tashi yazeed yayi yana fadin yawwa Abbana yasan Halin yara. Inno data Saki baki yana fita tace Amadi Bazaka daina biye yaron nan ba kenan? Inno Rabu dashi dakaina Xanje Nahada musu tafiyar. Murna Leemah tayi tace yawwa Abbana.

Kausar na karasawa gida gaisawa kawai tayi da Hajiya sai yar firar dasukai.Hajiya bari Nayi wanka yunwa nakeji Wlh.maxa yar Albarka Kiyi kixo kici Abinci.Toh mamah. Yawwa Kausar Kafin kitafi nikuwa maganin dakike Amfani dasu kinajin chanji Ajikin ki? "Sosai ma Hajiya" kinga maganin infection din nan ma Saura Kadan,Sati biyu kawai nayi Amfani dashi Naji Alamar Sauki,har Asibiti naje Sun tabbatar Mun dacewa banida Wani Ciwo Yanzu Ajikina.kai Alhmdllh Nayi matukar farin ciki Hajiya ta fada tana daga hannu Sama. Amma mamah ni haryanzu ina fargabar tarewata gidan Yusuf! Kallonta Hajiya tayi kina nufin duk Rawar kafa din nan da Yusuf keyi Akanki haryanzu babu Abinda ya shiga tsakaninku? Kausar taji nauyin maganar Amma ya zatayi mahaifiyarta ce itace wadda yazama dole tasan matsalar ta,domin daga Ubangijin daya Halliceta Sai Mazon Sa babu wani wanda yachanchanta ta girmama bayan Su Sai mahaifiyarta da Mahaifinta daga bisani Sauran mutane. Dan haka babu wani Amfani danta boye mata Sirrinta. Eh mamah babu Abinda ya shiga tsakanina dashi ina tsoron kada yakasance Nidin ba budurwa bace karashe maganar tayi da kuka. Jawota Hajiya tayi kan jikinta tana Shafa bayanta,ya'isa yata na fada miki babu Abinda Xai faru tsakaninki dashi Sai Alkairi ki kwantar da hankalinki. Inason yanxu kisanar dani gaskiya kin taba Aikata wani da Da Namiji ne? Da sauri Kausar tace Wlh Allah mamah bantaba Aikata Wani Abu dana miji ba. Indai hakane kuwa Kausar ki daina daga hankalinki Akan Wani Abu na daban. Shikenan Mamah insha Allah Na daina.Allah miki Albarka ya kareki daga Sharrin mutum da Aljani da dukkan Abu Mai cutarwa.Allah Amin Hajiyata Kausar ta fada tana kissing Hajiya A kumatu.maxa tashi kiyi Wanka.Tom Hajiya.....Namance ban fada miki ba mamah! Meke nan yata?? Jibi Xamu tafi Saudiyya. Kai masha Allah Naji dadi Allah ya tsareku.Amn Kausar ta fada tayi Ciki. Tana Shiga kiran Yusuf na Shigowa wayarta. Da murmushi ta daga.my wife I miss you Abinda Yusuf yafara fadi kenan. Miss you more Kausar ta fada kasa kasa. Meke damunki Sweetheart kaman kinyi kuka. Zaro ido tayi Kaman yana ganinta banyi ba Sweety Kawai gajiya ne. Sorry kinji.Uhum kawai Kausar tace. Albishirinki! "Goro my Honey" jibi ne tafiyarmu Saudiyya nida Yazeed da Nazeer. Wow what a Wonderful Story lyk Sweet. Ajiyar Xuciya yusuf yayi dan nace Zanyi tafiya kike murna Haka? Waye ya fada maka kawai dan inaganin Xamu tafi tare gani ga mijina Shiyasa na fada haka. Me kike fada haka? ina fada maka jibi muma Xamu tafi. Wow yusuf

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment