Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wani Abokinsu Ahmad duk dacewa Ahmad ya Rigasu Aure Dan Saida yayi Aure ya haihu ďa Namiji Sannan daddy yayi nashi Auren Saikuma Sulaiman yaya Awajen Mumy kuma Aboki Awajen daddy Shima yayi Nashi Auren. Mumy Takasance irin matan nan ne masu tattalin miji wanda Ko Zumunci basucika yiba Sabida kula da mazan su dan Haka bata zuwa ko'ina daga gidansu Sai wajen Aikinta dan Cikakkiyar barrister ce, Tana dan Zuwa YOLA wani lokacin idan daddy Zaije, ba kasafe tacika Ziyartar Maryam Matar Sulaiman ba Saidai Ita maryam din ke yawan Zuwa mata, ko Sau daya Kuma bata taba tunanin Zuwa gidan Fatima matar Ahmad ba itama Kuwa fatiman tace bazatazoba harsai mumy taje mata,,,,,kullum cikin Sa Rana take Amma ina,,,,,,,,hakan ce takasance Ayau ma tare Suke da Maryam Wacce Nazir yarada ma UMMA Tana ma mumy korafi Wlh kedai Hafsa bazaki chanza haliba kullum kina gida Kamar daddawa da Anyi magana kice daddyn Nazir na Gari Kamar dan ke kadai Akai miji, Kai Maryam kedai kullum maganar ki kenan idan ban Kula da Shiba waye Zai kula dashi beda kowa Anan garin wanda ya wuce ni da Nazir Sai wannan Cikin Nawa Uhum Toh dan Allah badole na Zamemai gata gaba da baya ba? Kizama Shi yazama ke Kawai karshen magana kenan Maryam tafada tana gyara Zamanta,,,,,,,,, Bari Nakawo miki Abinci kici Amma maganar nazama Shi yazama ni na nawa kuma Ai munzama tsoka daya mumy tafada tana bin Hanyar kitchen,,,,,,,Kayattacen Abincin da ta dafa ma daddy Aciki ta iba ma Maryam, tanaci Suna fira, Umma ce tace wai kuwa kinsan Fatima ta Haihu yau kwana hudu kenan, Kai Haba mai Aka Samu? Tahaifi diya mace, kai tubarakallah Allah ya Raya.Amin Umma tace Sannan Takara dacewa Saiki kishirya Kije Barka, Kai Maryam bakida tausayi wan nan Cikin Nawa Haihuwa ko yau ko gobe Zakice naje barka, Uhum haka kawai ma Anki Ziyara bare yanzu da Akeda Hujja mai Karfi. Kyadai ji dashi Ai Zan kirata namata barka. Allah yasa. Ni Zan tafi, haba Maryam tun Yanzu? Eh Ai nafi Mara Zumunci, ki kwantar da Hankalinki nima Zanzo. Muna jiran Ranar da babu. dahaka ta tashi Mumy taimata Rakiya.
Cikin daran Ranar Nakuda tazo ma mumy, tun tana daurewa Har takasa ta tashi daddy dake bacci cikin Rudu ya dau key din mota ya temaka mata Suka fita yasata Amota yadawo ya dau Nazir dake bacci Sai SULTANA HOSPITAL dake nan Unguwar Dosa KADUNA Mumy tasha wuya A wannan haihuwan dan saida Aka kwashi Awanni tana Abu daya daddy Zufa kawai yake yana kaiwa da komowa, daker ya'iya daukan waya ya kira Sulaiman ya Sheda mishi daga bisani ya kira Ahmad, Kusan atare Suka karaso Sulaiman da Maryam, Sai Ahmad wanda matarshi ta Haihu badaman tazo, Zuwan Su Kuma yayi daidai da fitowar wata nurses tasheda musu Anhaihu diya Mace, Atare Suka Shiga dakin Suna ma mumy Sannu yayin da daddy ya dau yarinyar, SUBHANALLAH tsarki ya tabbata ga Allah wanda da ikonshi yake Samar da Abu mai Kyau da Mara Kyau, daddy ne yafada yana nunama Ahmad (Abba) dake kusa dashi babyn, Sunyaba da kyan babyn Dan Ajin farkoce wajen Kyau. Ahakadai washe gari Aka Sallamesu Sukayi gida, Kai Alhmdullah duk dacewa Mumy bamai Son Zumunci bace mutane Sai zuwa barka Ake, Sabida kyan jariryar ke rudan wasu yarinyar tun tana jaririya da farin jininta. RANAR SUNA yan YOLA duk Sun Hallara Mutane kota'Ina kowa farin ciki yake Anci Ansha taron Suna yatshi lfy inda Yarinya taci Sunan Kakarta mahaifiyar babanta wato NAFISA Zasuna cemataa (Feenat) Haka Rayuwa tacigaba Mumy na kokari wajen faranta Ran mijinta yara kuwa Tasamu wata dattijuwa Ladi ita ke kula dasu.
Lokacin da Feenat tacika Shekaru Uku Alokacin Aka Sata makaranta nursery "iman Academy" dake Unguwar Dosa, makarntar hade take da Islamiyya, Idan Sun tashi 12am Sai suke Shiga Islamiyya 5pm driver ke daukosu lokacin Nazir yana primary6 Mamah LADI itaa ke kula da komai nasu, Feenat tana Maida Hankali yarinayace mai hazaka aduka bangare biyu, Bawanda feenah ke Kulawa Dan ita din yarinyace marason Hayaniya, Kawarta daya Halima Itama Sabida kokarinta Yasa Abotarsu tazo daya da Feenat, BAYAN WANI LOKACI Abubuwa da dama Sun faru, Feenat Sun Zana jarabawar fita daga Secondary. Ayayin da Suka kara Shakuwa da Kawarta leemah Sosai, daddy ya tura Nazir Kasar Turkey Achan yake cigaba da Karatun inda yake Karatun Soja, Alokacin Feenat ta damu kan rabuwarsu da yayanta Sabida Shakuwar dake tsakaninsu, Leemah Itama tasanar da feenat cewa brother dinta yaje karatu America yana karatu Doctor, Mumy takara Haihuwa inda ta Haifa Twins, Mace da namiji namijin yaci Sunan kakanshi daya Rasu Ibrahim Suna kiranshi (Mubeen) inda macen taci Sunan Mahaifiyar Mumy Aminatu Suna kiranta (mubeena) Anyi Shagali Sosai. Haryanzu mumy batasamu taje gidan Fatima matar Ahmad ba............Feenat basu hada iyayensu Kawanceba ita da Leemah Acewarsu Koda Zasuyi Karyar fita yawo sarinka karya dazuwa dagidajen juna tunda kowacce Agidansu Ansan irin Shakuwar da kawayen biyu Sukayi
BAYAN SHEKARU.
Wata tsaleliyar budurwace wadda Aqallah Zatai Shekaru 18 duguwace ba irin Sosai ba,farace mai matsakaitan idanu Samanshi dauke yake da dogayen gashin idanu, girarta Aciki take ta kwanta lufff, Tana da diri batada kiba Kuma ba Arame Take ba, kirjinta cike yake idan baka Zata ba Zaka Iya Cewa Wata mai yawan Shekaruce. fuskarta dauke take da dogon Hanci yayin da pink din bakinta y kasance karami, kwance take kan makeken gadon dake manne jikin ginin dakin tana danne dannen waya da Alama Chat take Ringing..... dayar wayar dake kusa da ita tafara. Hello besty daga dayan bangaren Aka amsa Hy feenat ina hanya zan zo gidanku fa, dagaske? Allah da gaske,Saikin karaso ok. Ba'afi Minti20 tsakaniba Saiga ta tashigo, turo Kofar tayi, dasauri Feenat ta Sakko Suka Rungume Juna, leemah Shine Baki gayamun Zakizoba, Sorry Kawata magana Zamuyi, Inajinki besty, Hawaye tafara Feenat yanzu Rabuwa Zamuyi, Zaro ido feenat tayi tace Akan me?muda muka Shirya yanda Rayuwarmu Zata kasance,kokinmance cewa komai namu iri dayane kinsan matsalata nasan taki,ke kikace Hatta Ranar aurenmu Rana daya zekasance, Leemah kin mance Ranar da kikacemun Mu Auri miji daya kokuma Mu Auri wa' da kani duk Dan mukasance Tare. Leemah duk kinmance yau kikemana Zancen Rabuwa. dan Allah Feenah ki kwantar da Hankalinki Ki Saurareni. INAJINKI besty Abba nane yasmamin Wata School Of Nursing A Abuja Shine yace Zai turani, Sabuwar Makarantace yanzu take tashe Akace. Hmmm Ajiyar Zuciya Feenat tayi tace Dan wan nan besty Shine kika dagamun hankli indan Wannan Zanmawa daddy magana Nima yasani Skul din Ai dani dake mai Rabamu Sai Allah.


Page....6
bayan tafiyar Leemah. fitowa tayi da niyar Samun daddy tafada mishi, mumy tasamu Zaune a parlor ga Twins gefenta bangare guda wasu takaddune birjik da Alama Akwai Abinda take nima cikinsu. tawowa tayi ta Zauna ta jingina da jikin Mumy, Mumy Sannu, yawwa my daughter Ai najiki da Halima Shine bata Shigo yau ta gaidaniba, mumy Tana cikin damuwa ne wai Acewarta yau Zamu Rabu, kinsan ma wai menene dalili?? "Aa"mumy tafada tana girgiza Kai, Mumy wai Akan Abbanta ya Sama mata Skul a Abuja,,,,,,, 😊Murmushi Mumy tayi tace Ai dole tace Za'a Rabaku tunda ganin Juna Zemuku wuya, da Sauri Feenat ta dago kanta, Mumy Zuwa nayi Nagayama daddy nima yakaini Skul din Ai, Ke dai kincika Son Rigima. daga.....koda yake aima kunfi kusa da dadyn naki mumy tafada tana daga kafada🙅 Yayin da tacigaba da dube dubenta. Feenat Maida kanta tayi kan tv dake manne jikin bango, wani American film Akeyi a Mbc Action, lokaci daya ta rintse idonta ganin Abinda turawan ke Aikatawa, mace ce Rungume jikin Wani Saurayi Sanye da wata yar riga wanda komai na jikin ta Abayyane yake, shafa jikinta yake Very Slowly, Yayin da bakinshi yake cikin nata yana tshotsa Kamar yasamu Sweet, itakuma Hannu daya tasakalo ta bayanshi tana Shafawa tanayi tana lumshe ido,,,,,,,,, take wani Abu ya Ziyarci Feenat wanda takan Dan jishi lokaci Zuwa lokaci, Kafafunta tahada ta matsesu waje daya Dan wani Abu takeji kamar yana yawo jikinta, Remote tajawo ta chanza tasha Zuwa Zee Aflam, Cikin Kasan Zuciyar ta kuwa cewa take Aure Zanyi Gaskiya tunda malan musa yagaya mana idan Kaji makamancin Haka Sha'awa ce kuma wajibine kanimi mijin Aure idan Kaji Zaka Cutu.
Sallamr dady ce ta dawo da Feenat daga tunanin da takeyi, Amsawa Sukai Yayin da mumy ta tashi tayi hugging dinshi barka da dawowa, ga bashi ba nima da Aure nayi duk lokacin da mijina yadawo Haka Zanmai maiyuwa bazanji Abun da naji dazun ba, Feenat ke fira da Zuciyar ta, Ummina yau ba magana, cikin inda inda tace Sannu da zuwa daddy, yawwa Ummina ko bakijin dadine? Jiranka take Shiyasa tayi wani kamar Mara gaskiya mumy ta fada tana ciremai takalamin kafarshi, my Kinji mai mamynki ta fada ko fira Zamuyi, daddy kaci Abinci ka huta Saina fada maka, wayaki ya Saurari Zancen Umminshi cikin Zumudi? fadamun kamin naci Abincin, Sunkuyar da Kai kasa tayi daddy dama Akwai Wata Skul Of nursing da Aka bude a Abuja Abban Su Leemah Chan Ze kaita pls daddy inason Skul din nima. Shiru nadan lokaci daga bisani daddy yace ban Amince ba, nace ban Amince ba Ita Leemah din dako iyayenta bamu Saniba Zakice komai Sai kinyi irin nata, indai nine na haifeki ban yarda ba inada burin nayimuku komai dakuke bukata Amma banda wannan, daga haka yatashi ya Haura Sama, tashi mumy tayi Zata Bishi Feenat ta Rukota mumy pls kisa baki yabarni kinfi kowa Sanin irin Shakuwata da Leemah, Mumy tun muna yara fa muke......kuka ne ya kwace mata, dafa kanta mumy tayi tace my daughter am sorry to said you kibi Umarnin mahafinki, Sabida kinfi kowa Sanin dadynki yafi kowa Son yaga kunyi karatu kunzama wani Abu, tunda kikaga bai Amince ba kiyi hakuri Kawai, daga Haka mumy ta tashi. da gudu itama feenat ta tashi ta Haura Saman daret dakinta tayi tafada kan bed tana kuka mai tsuma Zuciya, Saida taci kukanta Mai isarta tukun ta jawo phone dinta tafara dealing number Leemah, HELLO.... my besty dafatan daddy ya Amince Kinga harna Suyomana wasu kayayyakin Amfani kinsan Anko Zamu rinkayi yanda Zamu birge duk wata maijin kanta Askul din nan, Ke Kinga wani takalmi duk yanda Akai kwanan nan yafito yayi Kyau, Ke mayyar Abaya nasiyo Miki Su birjik, idan Kinga Akwai Abunda kikeso ki hanzarta gobe Kije kasuwa, Dan Wlh harna hangomu A Skul din nan, Skul dinfa ance sai Dan wane da wane Kinga yanzu Za'a kara Sanin muba yaran Kananan mutane bane. besty kinbarni inata Mgn kice wani Abu mana.
Ajiyar Zurciya feenat tayi yayinda taji Son Kawarta ta yakara dira mata A'zuciya, Cikin dashashiyar murya tace leemah daddy.......aitun kamin takarasa Leemah tace kada kice mun be Amince ba Yanayin muryanki ya nuna Hakan. Wlh Leemah yace "Aa" Itama mumy namata magana wai nabi umarnin Shi hakan Shine daidai. Innalillahi ni Yanzu Zan iya cigaba da Rayuwa batare dake bane, Ina nima Nahakura da tafiyan nan duk Skul din dazakishiga nima ita nakeso. Karki haka Leemah kamata yayi kisa Abba yazo yasamu daddy ya fahimtar tashi. Wow inasonki Feenat kin Iya hango Abu mai Kyau, Bari Anjuma Zan Samu Abba na da maganar Allah yasa idan yazo daddy ya Amince, Amin dai my Leemah Nima inasonki. Nariga na dade dasani ai kawata, besty bari nacigaba da hada mana kayanmu, kincika Zumudi. Keko Ai dole Muma Zamu Zama manyan yara, Atare Suka kwashe da dariya. Jeki karasa saimunyi waya Anjuma. ok.bye.
Tunani Kawai take Azuciyarta barkatai Shin Anya daddy ze'amince kuwa? Kodai nakira Leemah Nace tabari, Maiyuwuwa Karatuna A kaduna Shine yafi Alkairi Shiyasa daddy yaki Amincewa, Toh Amma ai karatun zaifi dadi Idan kana Tare da kawarka wacce kuke Shawara da ita tunda Ita mumy bata fiye Zama Ai fira da Itaba. Kai kada na takurama Zuciyata kan tunani bari nabari Leemah ta turo Abbanta Kawai. remote tajawo ta kunna t.v. take Abinda tagani dazun a Mbc Action ya fado mata Arai, Haka kurum taji tana Sha'awar cigaba da kallon film din, bari nagani ko basu gamaba tafada cikin Ranta tana chanza Tashar, Oh Wow basu gamaba, 😨Kai basu gama irin wannan wajenba kenan film din duk haka yake, dukufa tayi tana kallo Sosai har'inda wasu turawa Su biyu Suke fira da Harshen turanci, dukansu mata ne, dayar ke fada ma yar'uwarta irin Son da take mata, Kallmar So karara take Zayyanemata kamar irin Saurayi da budurwa din Nan, take kuma tajawo ta Suka koma Suna fuskantar juna tana cigaba da gaya mata tana Shafa fuskarta, dayar ce takara matsowa Sosai ta hade bakinsu waje daya tafara kissing dinta Sosai, Feenat lisp dinta ta kamo tafara lasa jitake kamar itace Akema hakan, turawan Nan Sun lula har takai ga Sun cirema juna kaya, Shafeshafe Kawai Suke Suna nishi, Wayyo Allah feenat tafada tana kankame jikinta, dama Ana irin haka mace da mace Toh koshine lesbian din da naji Ana fada Kai Subhanallah Ance ubangijimu Allahu yana fishi mai tsanani damasuyi irin Wannan harkan. Kashen TV tayi gaba daya tafara istigifari na kallon da tayi, bangare guda jikinta Sai Rawa yake Wani Abu takeji yana yawo A jikinta, kawai itama Sha'awan take takasance jikin namiji. turo kofar Akayi cikin Sallama, Kasa amsawa tayi Saidai yunkurin tashi da takeyi takasa, my feenah fushi kike haryanzu jifa idonki Yanda Suka kumbura Alamar kuka kikai Sosai, Mumy banjin dadi ne, Sannu daughter na kada kisa Abun Aranki Kinji, Allah yasa Hakan Shine Alkairi. Mumy jitayi Feenat bata amsaba take kuma ta lura da yanda jikin yar tata yake Bari taba jikinta tayi tace Zazzabi kike feenah, Ummm mumy. Ya Allah. Bari nakira dadynki muje Asibiti fita tayi Suka Shigo tare da daddy taba jikin yar tashi yayi yaji kamar wuta, maza Hafsa temaka mata mukaita Asibiti, Cikin kankanin lokaci Mumy tashiryata Suka nufi Asibiti dama Mubeen da mubeena LADI ke rainonsu.
Ruwa Aka Saka mata bayan bincike da doctor yayi Akanta, fitowa yayi yace daddy ya biyoshi Office. Alhji na tabbata din Kai mutum ne mai Hikima, Amma ya'Akai yarka ta Dade Abu nadamunta baka gaggauta Sama mata mafitaba, kodayake Kai namijine ba Lallai ka lura da Hakanba Amma mahaifiyarta tayi babban Sakaci. dacta meyake damun yata yimun bayani Menene matsalarta, Alhji yarka tana fama da Sha'awa me karfi wanda Ayanzu kamata yayi Asama mata Mijin Aure, ✋dakata dacta yar Tawa guda Nawa take, duka duka shekarunta 18 ne me tasani, A karatunma me tayi? dacta inaganin Akan maganar Barinta tayi karatu A Abuja dabanyi bane, Shiyasa tasaka damuwa Aranta, Amma yanzu na Amince mata taje tayi. daga Haka ya tashi Dr nakiranshi ya fahimtar dashi Amma inaaaa tuni yabar Office din, Zuwa yayi yace ma Su mumy Sutaso. Har bakin inda motarsu take dr ya biyosu daddy naganinshi yatada motar yabar wajen, Cikin mota daddy ke Sanar da mumy Abinda Dr yafada mishi........Shiru Mumy tayi nadan lokaci daga bisani tace Bana tsamanin Haka Feenat guda Nawa take, mganar jiyace tasata Zazzabi kawai. Atoh Nima Haka Nace Amma yanzu Na Amince kawai Zan Kaita makarantar, tunda Ajiya nayi Searching naga makarantar Mata Zalla ce nidama makarata da mazan nanne banaso. Aishikenan Hakan ma yafi mumy tafada. Feenat duk tanajin Abinda Suke fadi bangare daya taji dadin Amincewa da daddy yayi game da karatunta, Yayin da bangare guda kuma takejin bakin Cikin kin yarda da maganar Dr da daddy Yayi. Kamar tabude Baki tace ita tanason Auren Amma Ina bazata iyaba.

Suna isa gida ta dau wayarta ta kira Leemah tana dagawa tace besty kada kifada ma Abbab. Meyasa kikace Haka besty? Sabida daddy ya Amince, 💃💃Tsallen murna Leemah tayi tace Alhmdllh. Amma ya A'Kai ya Amince? feenat Sanar da leemah Komai tayi Abinda ya faru har kan kallon da tayi da zuwansu Asibiti da duk yanda daddy yama mumy Bayanin Abinda da Dr yace mishi bata moye Komai Acikiba, Hmmm Nifa dama Feenat nadade ina tunanin kinada Sha'awa Sosai, Sabida Na lura da Abubuwa da yawa game dake. Zan gaya Miki Wasu Abubuwa ne Amma saimun Hadu. Shikenan Saimun hadu din. Washegari daddy yaje Abuja Yayi ma Feenat komai kan karatunta zuwa kawai ya Rage mata, Sunje da Mumy kasuwa Sunyi Siyayya mai yawan gaske inda kusan Komai tare take dakko musu da Habibiyar tata Leemah. Bangaren Leemah ma Komai ya daidaita Rana daya Zasu fara zuwa Sun yanke Shawara kan cewa drivern Su feenah ne Zai kaisu domin Su tattauna game da matsalar feenah.

Page.....7
Feenah ce Sanye cikin wani material milk colour yana dauke da Ratsin Brown Ajikinshi, dinkin Riga da Siket ne yazauna tsam Ajikinta Mayafi ta daura Akai Brown colour Haka takalmi da jakarta duk Brown ne, Wani Dan Siririn Agogo ne manne A hand dinta Sai wani zobe makale da yatsanta, Kai daka ganta Kasan Akwai Hutu Atare da ita Dan fatar jikinta luwai take, bawani make-up tayima face dinta ba Amma hakan be hana kyawunta fitowaba. Mumy ce ta turo kofar tace my daughter baki gama Shiryawa bane Haruna tun tune yake jiranki A waje fa, nagama mumy kinsan nace miki Tare Zamu tafi da Leemah bata karaso bane sai yanzu, yakamata Kifitoh haka nan, "Alright" Mumy nafito. Toh daughter fadan da namiki dazun Allah yasa yashigeki Sannan kinji Abinda da dadynki ya fada miki, Allah ya bada Sa'a kikula da kanki kinji, Zuwa tayi tace thanks mumy ta yayinda kuka yakeson kwace mata, Haba feenat banace banason Yawan kukan Nan ba idan bakya Son tafiyar ne Saiki fasa, da Sauri tasaki mumy tafara Share Hawayenta,mumy Ina Twins? Suna wajen Baba Ladi jekiyi musu Sallama, Zuwa tayi tasamesu Baba Ladi namusu wasa Suna dariya, Kissing dinsu tayi A kumatu daya bayan daya taima baba ladi Sallama, kukan mubeen taji Alama Yanaso yabita tajuya ta daukeshi mubeena itama tamika Hannu, Ina Zan iya daukanku duka Baba Ladi Dan Allah daukota muje bakin gate. Suna karasawa Mumy ta Amshi mubeen daker ya yarda Feenat ta shiga mota. Suna fita ta hango motar su Leemah Haruna tsaya. Yana tsayawa Leemah tafito tashiga, Leemah tayi fes Don itama badaga baya ba wajen kyau. daret hanyar Abuja driver ya dauka.
Karyar kika Zuba ma Mamy tayarda Zamu tafi tare ko? feenat tafada tana kare mata kallo, dariya Leemah tayi tace yau Kai tsaye nafada mata tadanyi fada daga bisani kuma tayarda........ Ai gara mumy bata So maybe wani Abun ya Sameki ne but Shifa daddy Kai tsaye yake nuna bayason wani da Namiji yakulani, Kinsan Wlh Leemah Ran nan da daddy yake waya da Inna Nafisa ta yola inaji tana cemai yakamata Aimun Aure tunda Shima da ya Auri matarshi bata kai yawan Shekaruna ba, Wai Sai ce mata yayi Yana tsoron mazan yanzu ko Anyi Alkawari Za'a cigaba da karatu Sai Anshiga Su hana, cemai tayi A hada ni Aure da babban yaron Uncle dina Nazir, Amma firrrr daddy ya kauce maganar da take mai, kuma Leemah Wlh kabeer yarone mai hankali da Addine Kuma dama addini Shine babban Abu mai taka Rawar gani wajen Niman Auren miji nagari, ke bama Haka ba babban Sojane wanda Kasar Najeria take Alfahari dashi, kuma Wlh Ga Kyau idan kika ganshi Kama da dadyna yayi Sak. Gaskiya feenah daddy yayi Nisa burinshi kawai yaga Ance yau ga yarshi tazama wani Abu toh baya lura da kedin macece? daya sani gaba daya burin nashi kan yaya Nazir dinku ya daura da yafi. Idan baki manta wani hadisi da muka taba yi muna Aji Shida A islamiyya ba, "Sahihul bukari ne" "Alkam ya Ruwaito hadisin" CEWA! "Watarana sayyidina Usman yasamu Abddullah bin Mas'ud (Abu Abdrrahman) Sai yace mishi ya Abu Abdurrahman Shin na Aura maka budurwa domin ta tuna maka da yarintarka" Awata Ruwayar kuma " Shin Na Aura Maka budurwa domin ta tunatar dakai Samartakarka" kinsan me wannan Hadisi yake nufi, wannan hadisin yana Gaya mana cewa Aure Shine kwanciyar Hankali kuma Aure Shi ke Samar da natsuwa. Ke Wlh duk Matar dakiga ko mijin dakikaga Suna korafe korafe Kan Cewa basu Samun natsuwa game da iyalansu Toh ki tabbata Soyayar da Suka Kullah Kamin Suyi Aure ba Soyayyar Gaskiya bace, idanma Ansamu wanda Suka kulla Soyayar Gaskiya din Toh tabbas Basu San Yaya Ake Sarrafa taba, Soyayya ba'Ita ke Haifar da natsuwa gidan Aure ba Sarrafa Soyayyar Shine Ke Haifar da natsuwa. Misali Atambayeki me kika fi So Arayuwanki Saikice Waina, Sai Akawo miki Waina har kashi biyu, dole wacce kikaci Kikaji tafi dadi ita Zaki yaba, Sanan Kuma idan kika gama Zakiso Kiji wacece ta Sarrafa wannan wainar. Toh Haka Abun yake idan Ma'aurata Suka iya Sarrafa Soyayya Zaman takewar Aurensu Zata daure Sosai. Kuma duk mace Ko Namiji da baya Samar ma dayanshi natsuwa Shine Zakiga Aure yana tabarbarewa. Bafa natsuwa ta kwanciyar Auratayya kadai ba natsuwa Zamn auren Gaba daya nake nufi. Manzon Allah S A W yace. Idan kuka Samu NamijI mai Addini da kakkyawar dabi'a Toh ku'aurar mishi da yar'uku ANNABIN ALLAH FA Akace, wanda duk wanda yabishi yashiga Aljannah, Haka kuma duk wanda ya kaucemai Wlh Saiya Koka. feenat kinga Addi da dabi'a mai Kyau Sone manyan Abu da Suke da Muhimanci game da Aure, Allah S.W.T yana cewa da Za'a kawo mahaifiyarka San'nan Akawo mazon Allah S A W Ace kazaba Allah yace Zaka Zaba Annabi ne. Yakamata ki fahimtar da daddy yagane Aure Shine darajar diya mace, ke kojiya Saida muka kara magana da Abba yace indai inada muradin Aure tare da tsayayen Saurayi namishi magana, feenat Kinsan mazan yanzu dole Sai Kana bincike Akansu Sosai. Kingani Anbani Zabi ballatana Ke dana fuskanci Sha'Awa gareki mai karfi, ina lura dake Sometimes Idan Muna Kallo ko Wani fira yanda kikeyi, Amma mucigaba da Addu'a Allah ze kawo mana Mafita. Feenat da tunda Leemah take magana ta mayar da Hanklinta duka Kanta tace besty kedin ta dabance wlh Shiyasa banida Abokin Shawara wanda ya huce ke, Allah yabarmu tare. Haruna dake driven duk yanajinsu yaran sun burgeshi kuma yadau Alkawarin idan yadawo Saiya ma Alhji magana gameda ya Aurar da feenah. AHAKA Suka karasa Abuja Cikin Makekeyar makaranta da Akayita domin mata Zallah. Sunyi komai cikin Lokacin Kankani hostile Suka nufa Ana ganinsu Aka duba sunansu kowacce Aka bata key din dakinta domin dama Anmusu komai kamin Su karaso, key daya Suka amsa Suka dire a wani makeken daki da gado ne kato a tsakiyarshi Sai wardrobe dake gefe, dauke Dakin yake da toilet dakin dai daidai irin yanda Su feenah kesonshi. Wanka duka Sukayi Sannan Sukay Searching Unguwar domin nemo wajen Abinci dadai wasu Abubuwan.
After 2 months
Su feenah Ankara Wayewa Suna kokari Wajen karatunsu domin yanzu gabaki daya makarantar Nan Ansan da Zaman NAFISA .U. IBRAHIM (feenah) da HALIMA .A. MUHD ( leemah) kowani Malami yana Alfahiri da Su da irin kokarinsu, Sun Samu wani malami wanda Suka ware lokaci yake koyardasu bangaren Islamiyya. Wanka kuwa babu wanda Ze nunamusu bare Uwa uba Kyau da tsafta, Komai Nasu Abun birgewane, gashi basa kula kowace Mace komunji dakanta, Lokaci Zuwa lokaci Kowacce Ana Zuwa mata daga gidansu. Shakuwa mai karfi takara Shiga tsakanin kawayen Nan biyu, matsalar dasuke Samu dayace yawan Sha'awa da feenat takeyi. Akwai wani Zuwa da Su daddy Sukayi Feenat tacire kunya Ta sanar dasu Mumy Amata Aure Amma Sukace Zancen Banza tafara karatu tayaya Zata yanke, data fahimtar da mumy Abinda ke damunta Cewa tayi Tarinka Azumi da Karatun qur'an Sannan duk lokacin da taji Tarinka Shan lepton da lemon tsami. Ahaka Rayuwa taci gabanmusu, Idan Leemah tace Zata gayama Mamy domin taje ta Samu mumy sai Feenat tace bataso Kunyar Mamy takeji haka Leemah ta hakura ta Rabu da Ita. Kowacce Tana Waya da brother dinta dake Kasar waje, duk Sanda Feenat ke waya da yaya Nazir saita bashi labarin Leemah, Shimakam yaya Nazir yaji Son ganin yarinyar, itakuwa Leemat da tafara ba Yayanta labari bayama Saurarenta Yake kashe wayar. Yauma kamar kullum Sunje wani Restaurant dake cikin garin Abuja Sunacin Abinci, Wasu yanmata Suka hango Su biyu Suna nufosu Suna karasowa dayar tayimusu Sallama. Amsawa Sukayi yayin Yayin Leemah tayi musu izini Su Zauna. Zama Sukayi dayar tafara magana Ni Sunana KAUSAR HAFIZ Wannan kuma ta nuna wata dake bata Rai Kamar bataso Zuwa wajen nasuba Sunanta KHADIJA AMINU. Leemah tace "Nice" yayin da itama ta

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment