Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fadi. da Sauri Mamy ta kalleta farar daya Kuma ta tashi tabar palon Leemah na biye da ita. Subhanallah Menene ya Sameta? Kuka kawai Suke babu mai bada Amsa, Leemah bani Ruwa, toilet tashiga ta ibo Ruwan, Mamy na yayyafa mata tayi Ajiyar Zuciya ta bude ido Saikuma Hawaye Sharrr.....Hafsa lfy me yafaru Dan Allah. Wai Halima Badaku Nakeba Menene ya Sameta? Feenah ce cikin kuka tace Nice Mamy.......kece mai kika mata? Leemah ce taci mamy Wlh Sharrin Saidan ne ta kamamune........Haba Leemah kada kidaurama kanki laifin dabaki taba Aikatawa ba mana feenah tafada tana girgiza ma Leemah Kai. Ke Kausar me Tayi ma Mum din Tata? Amma Wlh Mamy ba laifinta bane nice.....kada kumaida ni mahaukaciya mana, Ina magana Wannan tana wannan menene Hakan? tashi mum tayi takama Hannun mamy tana kuka maicin Rai, "fatima ban San dame muka Ragi Nafisat ba A Rayuwa, me namata Zata Saka Mun da makamncin irin wannan? Sabida nace tayi karatu, ko mene? Fatima....muryartace ta Sarke. Hafsa kinga natsu kimun bayani me yafaru, Fatima Abinda Allah yake tsananin fushi damasu Aikatashi wai feenah Shi takeyi lesbian fa, ni Wlh gara Ace nakamata da Namiji Akan yanda naganta Ayau din nan. Rufe mata baki Mamy tayi tana maimaita "Innalillahi" kallonsu tarinka yi daya bayan daya daga bisani tace Sutashi Su fita, Tashi Sukai feenah takama Hannun mum mumy dan Allah kiyafemun, tsawa mai karfi mumy taimata, Mamy tace tashi kifita feenah. "Fita Sukay"Mamy ta juyo tana fuskatantar mum, Haba Hafsa Ai koda da Namiji kika kama feenah Ansan da bacin Rai toh Amma Zaki iya gayamun Baki taba fuskantar Feenah Nason Aure ba kokin taba? Tunani mum Tayi kadan daga bisani tace na fuskanci Hakan hasalima dakanta tasha gayamun Tanason Aure, tana yawan cemun tana Sha'awa Amma Ni da dadyn ta mundau Abun A Matsayin yarinta ne. Lallai Wlh Hafsa kunyi babban gangancin A Rayuwa, tayaya kunsan matsalarta tagaya muku Sannan Yanzu Dan kin ganta tana Aikata wani Abu kidaga Hankalinki, Ainicema yakamata Nayi mamakin Leemah Abbanta Sau Nawa Yana kiranta Akan ta fiddo da miji, yanzu kinga dagani harshi babu wanda yashiga hakkinta Amma kinga duk dahaka bamu tsiraba, ballantana ku Hafsa Wanda Hakkinta kuka Shiga kada kimanta "manzon Allah S.A.W. yace Idan kuka fuskanci yarku tafara Haila toh kada kuyarda takara Jini na biyu Agabanku kuyi mata Aure idan har Ansamu miji nagari. Cikin Saihihul Muslim" Hafsa ke Haka Akamiki? Kinkai Shekarun feenah lokacin dakikai Naki Auren? Meyasa kin fuskanci yarki tana da matsananciyar Sha'awa kika ki kimata Abinda takeso? Yau koba feenah kika fuskanci Tanada wannan Matsalarba Ai kya temaka Tunda ance matsalar ya mace ta ya mace ce, Haba Hafsa haka kikataso Anamiki A Rayuwa Wlh Na fuskanci bayan Rashin Son Zumnci kinada Sakaci Akan Rayuwar yaranki, Shin karatun boko din Nan Dolene Wai? Shi Zai kaita Aljannah kokuma Shi Za'a tambayeta A kabarinta? Sannan kisani feenah yarinya ce mai natsuwa da ilimi kema Zaki bada Shaidar Hakan, Rashin kulawarki da Rudin Shidan,Sa'anan da kawaye Nasan tabbas Sune Suka Shiga Rayuwar yarki. Kiyi hakuri Hafsa ki fahimceni bawai ina goyon bayan Abunda Suka aikata bane Amma muyi musu Uzuri, Muji ta bakinsu Nasan ba Halinsu bane wannan. Ajiyar Zuciya mum tayi tace Lallai Fatima na gamsu da maganarki kuma tabbas Gsky kika fada Mune Silar koma miye da feenah tashiga, Amma Insha Allah yanzu Na fahimci ba daidai muke Aikatawaba, Na Amince Feenah takawo mijin Aure.Alhmdllh ma da Abin yazo da Sauki tabbas munyi kuskure kuma nayi nadama. Amma Fatima kina ganin Zata bar wannan Halin? Zasubari insha Allah itama Kausar Zan neme Mahaifiyarta namata bayani Amma kafin Nan Zansamesu yanzu namusu Nasiha wata kila muyi Nasara Subar Aikata Hakan. toh Fatima ngd Insha Allah Zansamu dadynta da maganar. Babu gdy a tsakaninmu tunda duk yashafemu. Fatima kidaina Zargin Halimatu bata cikinsu bazatai Hakanba, Hafsa ba'a yabon Dan yau gaba dayansu Zan hada namusu, tashi muje parlon kada kibari Afuskanci Komai kinga Su Umma Suna Nan.
Shiga Sukayi Suka Zauna Umma tafara Zolayarsu Aminan juna yau Anhadu Shine Aka tafi tattaunawa, Murmushi Mamy tayi tace Kekam Ai Shekaru da yawa ba'a haduba, Abba yace toh Ni ko rowar ganin Nafisat din Akemun, kana ganintafa kullum, Sunachan Suna karance Karancensu. Toh Atasota mutafi Gida daddy yafada, da Sauri Mamy tace daddyn Mubeen Ai batare kukazoba zata tawo daga baya. dariya yayi yamike Hafsa taso muje, tashi mumy tayi Suka fita mamy da Abba Suka musu Rakiya, ina Nazeer ne? Ganinan daddy kutafi Zamu tawo da feenah muna fira da yazeed ne, toh Ai Shikenan fita Sukayi Su Mamy Suka koma Ciki, tsayawa Nazeer yayi yana tuno dazun kamar yaga Leemah a firgice lokacin da tashigo Palo, taban tausayi yafada Aranshi, Turo get din Akayi ya juya ganin Yusuf ne yasa yakarasa Suka Rungume juna, Kai yanaganka Anan kodama Kasan gidan Su yazeed ne? Aa Yusuf nima yau nasan gidan Nazeer ya kwashe komai yafada ma Yusuf, gaskiya Abu yayi Kyau kusanma yan'uwa Za'a kiraka kaida yazeed. Aikuwa dai. Amma Nazeer kamar kana Cikin damuwa ko? Ahha bakomai Yusuf muje. Mamy ce ta Rako Umma Yusuf ya gaishesu Suka wuce part din yazeed. Akwance Suka Sameshi Yusuf yace miskilin mutum kafi mugu iya Shege, dagowa yayi ya kalleshe ya wurga mishi Harara, Nazeer yace yadai Dr? bakomai Nazeer Yusuf din nan ne yakamata Na Chanza Shi, Kodai ni na chanza ka ba, Kasan me ya kawoni gidanku? Ciki ciki ya amsa da "Aa" Nazone Naga Kausar kawar Sister dinka Allah yasa bata tafiba. Bansaniba Banza Sa'an yara kawai, Ka ganshi Nan Nazeer kullum yara kanana yake bibiya.Murmushi Nazeer yayi yace Ai inaga da Akwai magana ne, Au kaima biye mishi Zakai? Yawuce yace Sonta yake Kuma ai irin yaran Sune irin matan dasuka dace damu. dakudai wlh Yazeed yafada Rai Abace, kai Anma Anyi kuskure da'aka baka matsayin Captain, tunda duk karfin ka din Nan Akan tunanin Auren Karamar yarinya ya tsaya. Shidai Nazeer bece komaiba. Yusuf yace Adai juri Zuwa Rafi Angon yar 30yrs.
Mumy ce ta tura dakin tashiga Zaune tagansu kowanne kuka yake Rusawa babu mai lallashin kowa. "Kubiyoni dakin Leemah mamy tafada Atakaice ta fita" feenah cikin muryar da bata fita Sosai tace Na Rokeki Kausar duk Abinda Mamy Zatace kada kice mata Leemah nacikin masu Aikata Wannan Abun, ta juya Wajen Leemah besty Dan girman Allah kada kisanar da mamy kina Aikata Wannan Abun Sabida bakida hakki Akan Hakan. Haba feenah nima Kibari Ayimun waya gaya miki banida Hakki dunbin Zunubin Dana Aikata nakaishi ina Gara Mamy tasani tun Anan gidan Duniya domin ta yafemun, idan ku kunada Hujjar Cewa iyayenku ne Sila ni mecece Hujjar? Eh duk da haka Leemah Tunda Allah ya Rufa miki Asiri kema kirufa ma Kanki ba danniba. Nayarda kutashi muje. Shiga Sukayi Suka Zazzauna Akasa. Mamy ta dago ta dubesu gaba dayansu Sannan tafara dacewa....... kunbani kunya bakuma Kanku Adalciba, Nasan kunsan Abunda kuke Aikatawa Yanada dunbin Zunubi kuma kunsan makomar mai Aikatawa Son Zuciya ne yasaku yin Hakan kokuma banzar hujjarku da batada ma'ana, Shin dan iyayenku Sunce Saikunyi karatu Kunfi karfin kuyi musu biyayya ne? Kokuma dan basu isa dakubane yasa kuka zabi kusaka musu ta wannan Hanyar? Miye Ribarku dan kun Aikata Hakan? Raguwafa kukayi kusani Rayuwarku tana Cikin babban hatsari, Halima nagode da Abinda kikaimun, feenah ce tayi Saurin dagowa Mamy kiyi hakuri Leemah bata Aikatawa, yimun Shiru banson magana kedin feenah Ai Nasan wannan ba Halinki bane haduwa da kawayen banza Shine yajawo muku, dakuma laifinmu nabarinku kuyi karatu Anesa damu. Kausar ce ta dago ta dubi Mamy kiyi hakuri Mamy nice naja Mus......naja mata, kausar labari tashiga ba Mamy har irin Halin da Feenah keshiga a School dakuma yanda khady itama ta daurata Ahanya takara dacewa Shidanne yayi Nasara Akansu, Mamy ta jinjina Al'amarin taji tausayin yaran Inda daga Sakancinsu su iyayen yara masu daura Burinsu kan dole yara Saisun Kammala Karatun boko tukun Suyi Aure. Afili cewa tayi maganar banza ai ba wannan bace Hanyar magance matsalarku. Kunsan Sharrin Aikata lesbian kowa???? "Sha'awa fitanace daga dabi'ar da Allah ya hallice mace Akanta,ta jin dadi da namiji ba mace yar'awarta ba, Cikin Aikata lesbian Akwai Rashin kunya da fitsara, Alhalin Manzon Allah (S.A.W.) yana Cewa Kunya Alherice gaba dayanta, "awata Ruwayar"kunya bata kawo Komai Sai Alkairi. "Bukari ne ya Ruwaito" Sa'annan lesbian yanada illah ta yanda Zai iya haifar da cututtukan Zamani kama daga kan H.I.V idan kana aikata hakan dame ciwon. Ana Iya Rasa budurci ta Hanyar wanda hakan Ba Karamar tozarta bace ga ya budurwa. Abu nagaba Akwai cin Amanar Allah Aciki Sabida An Aikata Abun da yai hani Akanshi. Mai Aikata lesbian takan Rayu Cikin kuncin Rayuwa Sabida Allah S.W.T. yakan dibe Ni'imarshi Akan mai Aikatawa, wanda Hakan zesa Komai na Rayuwa yaki cimaka gaba. Sannan duk wanda yake Aikata Hakan harya mutu be tuba ba yasan makomarshi" kuji tsoron Allah wanna Ranar yazama Shine Ranar Karshe na Aikata Hakan A Rayuwarku" kuka Suke Sosai daga dukkan Alamu Nasihar Mamy ta Shigesu. Hada baki Sukayi wajen fadin Mamy muntuba Insha Allah yauce Ranar karshe bazamu karaba. Rungumesu Mamy tayi tace Suyita istigfari kuma su nimi gafarar iyayensu, daga bisani takarbi number din Hajiya maman kausar. kutashi kuci Abinci kuyi Wanka. Daga haka tafita tabar dakin.

πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya Muhammad Ahmad

Page....18
A mota daddy ne ya fahimci kamar mumy bata cikin natsuwa Don firar Shi kawai yake dasu Mubeen ita bata Saka baki. Hafsa lfy dai Naga kamar kina cikin damuwa! Alhji Gaskiya ya kamata mudawo da natsuwarmu musan Abunda yadace A Rayuwa, Wani Abu ya farune Hafsat? Eh Alhaji yau feenah nagani da idona tana......kwashe komai tayi tagaya mishi har irin Jan Hankalin da mamy Tamata, daddy ya girgiza da lamarin gaba daya! daker yasamu yayi parking motan ya juyo yana fuskatar mum, Gaskiya Hafsa munyi babban Sakaci tare da kuskure, musamman ni lokacin Dr yaso ya fahimtar dani Naki yarda Sabida wani nufi nawa na daban, Amma yanzu Allah yanuna mana tun daga nan kuma nadau Alwashin Hakan Bazata kara faruwa da wani da nawa ba, yanzu me kike gani yadace muyi Akai? Alhaji ni inaga kawai Kabeer Dan wajen yaya Nazir Shi Za'a aura mata Kamar Yanda Inna Nafisa Tayi Magana kwanaki. kin kawo Shawara mai Kyau, Amma bazamu Bari takarasa karatunba tunda Shekara ya Rage ta Kammala gaba daya? Alhji ni yanzu Ina tsoro Amma Muji ta bakinta idan Zata iya, Hakane Bari Muji Toh.
Wanka Sukai Sukaci Abinci Suna kara nadamar Abunda Suke Aikatawa Nasihar mamy ta Shigesu kwarai Dan gaba dayansu yanzu komai yin Shi Suke batare da kuzariba, palon Suka dawo wajen mamy Suka Zauna, kausar tace Mamy ni nashirya Zan wuce Zaria yanzu, yawwa yata kundai Ji Abinda nace muku, yanzu idan kuka Saba Alkawari kamar kunyi butulci ne. Mamy Nasiharki ta Shigemu insha Allah kuma mun dauka, Hakan bazai kara faruwa ba, Allah ya muku Albarka, Amin Suka Amsa gaba dayansu, Mamy ta tashi ta kwaso wasu turaruka ta hada taba Kausar, gdy Sosai kausar tayi ma Mamy, bakomai yata yanzu Bari na kira Hajiyar taki Awaya don namata bayani, toh Mamy. Wannan number din Ai inada ita Cikin Contact dina number din Hajiya Sara Dubai ce! Gaba daya Suka maida Hankalinsu kan Mamy. Mamy Ai mahaifiya tace Kausar ta fada. Lallai kam Hajiya Sara Itace mahaifiyarki dole Ace Saikinga karshen boko, kawata ce Sosai a Dubai muka taba Haduwa da ita muke Zumunci Tasan halina nasan nata, kwanaki Har Zaria naje mata gaisuwan Mahaifiyarta data Rasu. Laaaa Mamy dama gidan Su Kausar kikaje gaisuwa, Chan naje Leemah. Kausar tashi Kije Zan kirata namata bayani idan takama ma har Zarian Zanzo. toh Mamy Allah yakara girma, tashi tayi Suka Rungome junansu, toh Kausar Adaiyi Shirin komawa Skul jibi,karki damu Leemah inacikin Shiri. daga haka tafita, mamy takara Zaunar dasu Leemah da feenah tamusu nasiha duk da ita Aksan Zuciyarta Tasan Leemah itama na Aikata Hakan Sundai boye mata ne. Gdy Suka kara mawa Mamy Suka haura Sama.

Kausar Nafita taci karo da Yusuf Wanda yanzu yafito daga Part din yazeed domin yashiga ciki. Kallonshi tayi ta kauda kai tana kokarin fita, Malama Kausar Sannu da gida, yawwa tace Ataikace ta fita daga harabar gidan Zuwa inda drivernta yayi parking. Binta yayi pls Kausar magana nakeson muyi, "inajinka" Shiru yayi Na dan lokaci yarasa mai Zaice mata daga bisani yace i Need ur phone number pls, kamar bazaita mgn ba Saikuma tace "why"? Kausar there are some words we have here, but Naga kina Sauri bakida tym that is why I want you to give me ur phone number Sabida muyi magana daga baya. Karban wayan tashi tayi tasaka mai number dinta tashiga driver yaja Suka huce. Juyawa yayi yakoma Cikin gidan Su yazeed yana jin dadi Aranshi. Kai dama ba tafiya kayi ba yazeed yafada yana kallonshi, Lallai yazeed Nafita na nemo Abinda nazo Dan shine kuma Nasamu,yanzu dai Zantafi. dogon tsaki yazeed yaja yace Allah yasa ba binta kayi kamata magana ba. Yazaka Misilta Abun idan Hakan nayi? Yusuf ya fada yana kashe ido daya, ya Zan misilta kuwa banda nayimaka jaje Ka Zubda girmaka gaban yarinya kara ma. Kajifa Nazeer Abinda Dan uwanka ke fada Dan Allah kayi mishi Bayanin Soyayya mana, dariya Nazeer yayi yace bazai ganeba Saiya kamu da Soyayar Jariryar yarinya wacce Zai gwammace yayi Rainonta harta girma. Tsaki yazeed yaja ya tashi yabar dakin, da karfi Yusuf yace toh Angon yar 30yrs ni Natafi Tunda nayi Nasara. dariya Sukai Shida Nazeer Suka cigaba da firarsu. Yazeed Shiga yayi yaga bakowa a parlon yasamu kujera 1sitter ya Zauna, Remote yajawo ya Chanza Channel Zuwa "ZeeAlwan " haba Malan bakaga Kallo Akeba, juyowa yayi Adan tsorace ganin mai maganar ya Saisaita kanshi yakara tamke fuska, Naga Nan ba gidanku bane dazakizo kina mana Alfahari da isa, Sakin baki tayi Cikin Ranta tace "Wai Wannan Sarkin girman kan da isa yau yake cema wani yana yi" Afili cewa tayi "idan fitsari banza ne kaza tayi mana" Alfahari ai wanda ya isane yakeyinshi, Ke Wlh ni ba Sa'anki bane yanzu zan iya takaki a gidan nan jarababban mace kawai, feenah dabata fahimce me yake nufi ba tace Ai jarabbabun dayawa Ciki harda Kai. Tashi yayi A fusace yayi Kanta. "Toh dake ta mana kadaketa nace" Mamy tafada tana karasowa Cikin parlon, Mamy bakiji Rashin kunyar da takemun bane, tayi din banza mai bakar Zuciya fita kabani waje, Tashi yayi yafita yana huce Aranshi yana Ayyana Abubuwa da dama. My daughter kiyi hakuri da Halin brother dinku, durkusar dakai feenah tayi kasa batace komaiba, Nazeer ne yashigo da Sallama Suka amsa. feenah tashi muje ko, Ahhh yazaka tafi da ita Nazeer? Mamy daddy ne yace mutawo tare Akwai maganar dazai mata, toh feenah tashi kishirya, Tashi Mamy tayi ta Haura Sama feenah tashiga dakin leemah dan ta Shirya. Fitowa tayi daga kitchen besty kinji kausar harta kusa, durkusar da kai tayi kasa ganin Nazeer, my Sister Abinci kike mana? Aa yaya Nazir, Anjuma Zanzo nakawo miki tsarabarki da kaina, toh yaya Nazeer Ngd. Never mind Sister. Feenah ta fito tasamesu Ahaka tace muje yaya Nazeer, besty tafiya kuma? Eh Leemah, Saimun hadu kigaida mum kuma kishirya ma Skul, ok my Leemah. Fita Sukai suka kama hanyar Gida. Suna Shiga daret Feenah parlon daddy ta wuce tasamesu zaune da mum, tshogunnawa tayi tafara kuka mai cin Rai, mumy Dan Allah kugafartamun Wlh bazan kara Aikata makamancin irin wannan Halin ba. Saida tayi kuka Sasai tukun mum tajawota jikinta tace "promise daughter" nayi Alkawari mumy insha Allah. mun yafe miki Ummina kiyita istigifari kinji? daddy yafada Cikin kulawa, gyada kai tayi Alamar Toh, yanzu kinada tsayayye wanda kikeso ne? Aa daddy tun kwanaki dakace bakaso nadaina tsayawa da kowa, Yanzu Ummina Zaki Cigaba da karatun ne kokuma Na hadaki da Kabeer? Shiru Tayi chan tace daddy Zan karasa karatun.Toh Allah ya miki Albarka kinga idan kika karasa dakin dawo Sai Afara maganar auranki da kabeer din. Sunkuyar da kai tayi kasa tace Amin.

Page....19/20
family din Zaune Suke gaba dayansu A makeken parlon dake Sama, firarsu kawai Suke cikin Nishadi da walwala Yayin da Mubeen da Mubeen Suka Cika wajen da Surutu, Nazeer ne yace Bari nakawo muku tsarabarku yanzu murna Suka hau yi, bayan mintina kadan ya dawo dauke da makeken Akwati ya dire a tsakiyar parlon, feenah dake kwance ta daura kanta bisa cinyar "mum" domin yanzu mum Kowacce kulawa da Uwa keba danta yanzu Shi takeyi Acewar ta tayi Hankali yanzu dole tashiga Rayuwar yaranta Tasan Menene matsalarsu musamman feenah da'Itace budurwa kuma mai Raunin Hankali da yawan Sha'awa. tashi Feenah tayi tadawo kusa da Nazeer ta Zauna, wasu back back ne Acikin Babban Akwanting wanda kowace Jaka cike take da kaya, cirowa yayi Yamika ma Mubeena da gudu tayi part dinsu wajen Baba Ladi batama tsaya naga Menene Aciki ba Lol Haka Mubeen Ana bashi Shima yabar wajen, Wasu guda biyu Nazeer yakara Cirowa ya Aje gaban "dad" da "mum" Allah yamaka Albarka Suka fadi Atare, Amin yace Yayin da ya dauko wani big back daga Akwantin ya mika ma feenah, tsalle murna tayi tayi hungging brother din nata tace "thanks So much my big yaya" Uw wlcm my Sister, mumy ce tace Lallai dayake ita yar'uwarka ce Shine nata yafi namu! dariya Sukayi daddy yace kishi kike da Ummin tawa, Ummina tashi kije ciki ki duba kada mum dinki tagani ma, (Kai daddy nima fa naso Naga ko Menene Aciki gashi kamana bukulu nida Readers lolz) da Sauri Feenah ta tashi tayi Ciki, wani back dinne Aciki mumy ta hango toh Wannan kuma Na waye? Mum dama daya Zanba Yusuf ne daya Kuma Na Leemah Kawar feenah ce Nazeer ya fada yana Sosa keya, toh bude mugani mana, kai hafsy kinada Sa ido bazai bude ba, tashi Nazeer Anjuma Saika kaimata gida ko? toh daddy yafada yabar wajen, mumy ce tace idan Zaka gidan kayima Feenah mgn kuje tare dazun mamynku ta kirani wai Feenah taje ta Kwana da Safe yazeed Zai wuce dasu Abuja, mum gobe Zasu koma School ne?? Eh mana Nazeer bakaji dazun feenah ta kara fada ba, ok Allah ya Kaimu. Amin mum tace, yazeed nabarin wajen ta fuskanci daddy, Alhaji yaron Nan Sai Rawar Kai yake Akan Halimatu Anya kuwa! Anya mene Hafsat? Sai nake Ga Kamar Akwai magana, yana bata kulawa ne Sabida feenah daddy yace, tabe baki mum tayi tace Bari naje na daura girki.
Yusuf ne ya Shigo gidan Su Leemah daret part din yazeed ya wuce, tura dakin yayi da Sallama kan tsakiyar bed ya hango Yazeed yana duba laptop da'alama wani Aikin yake, miskilin mutum Na yar 30yrs Sallaman ma bazaka iya amsawa ba ko? Yatsina fuska yazeed yayi yace waye yasan ma kashigo Malan, Oho tunani kakeyi kenan ba aiki ba, ina Ruwanka ne wai? Ruwana Ai nashanye, mtswww yazeed yaja tsaki yace waima Menene ya kawoka nan? Yusuf yace Nazone ka koyamun yanda Ake Kiran budurwa Awaya, tun 4days dasuka wuce na karba numbern ta nakasa kira. dafe Kai yazeed yayi yace Amma ka Raina ma kanka wayo Wlh, So koba wannan yarinyar Zaka kiraba bazan iya bata lokacina Akan ka ba. toh yayi inda budurwa Kace bazakace Haka ba Ai. Wani tsakin Yazeed yakara ja ya juya yacigaba da Aikinshi. Yusuf wayanshi ya ciro yashiga dialling numbern Kausar, Saida kira ta katse ba'a daga ba, cije baki yazeed yayi dan Shi haushin Yusuf yakeji yanzu baga irintaba ka kira yarinya ta Raina ka bata daga ba, ba ruwanka yusuf yace yakara dialling numbern Saida takusa tsinkewa Aka daga, HELLO! Kallon yazeed yayi Alamar ya gayamai Abinda Zaice, juyar dakai yazeed yayi be tanka ba. Hello waye ne? Am....Kausar am Yusuf, ya gida. Lfy tace kawai, Shiru nadan lokaci Yusuf yace "dama magana Zamuyi Kausar, tun Ranar damuka fara haduwa dake gidan kawarki Minal naji......bigeshi yazeed yayi Ahankali yace wawa da gaske Saika Zubda girmanka gaban yarinya karama, juyar dakai Yusuf yayi yana mai Alama da ba ruwanshi. Yacigaba Wlh Kausar tun Alokacin naji Kinzama Wani Abu Acikin Raina,pls Kausar ki karbeni Amtsayin mijin Aurenki nayarda Zan jiraki har lokacin dakika Shirya,fatana kibani waje Acikin Zuciyarki Mugudanar da Soyayya mai tsafta. Kausar daskarewa tayi daga bangarenta yayin da wani Murmushi ya Subucemata Cikin Ranta wani Nishadi take ji domin dama Mamy takira Hajiyarsu ta Sanar da Ita Halin da Kausar tashiga Sanadin kin Bata Hakkinta dasukai, Alokacin kuma Hajiyar Kausar tayi nadama kuma dayake tana karbar Shawarar Aminiyarta Mamyn Leemah Shiyasa ta Sami kausar tace ta fiddo miji Ayi mata aure, Amma duk dahaka Saita karasa Karatun ta tunda 1yr ya Rage mata. Kausar taji dadi Alokacin tayima Hajiya Alkawarin ta daina Yin lesbian har Abada kuma Zata Samo miji, toh yau Saigashi Yusuf din da tunda tafara ganinshi taji ya kwanta mata Arai Kuma yau Shine yazo mata da maganar yana Sonta, murna tarinkayi bangare guda tana tsoro kada Yasan ta taba Aikata lesbian yace baya Sonta.....Kausar kinyi Shiru ba Amsa Yusuf ya katse mata tunaninta. Shiru tayi daga bisani tace mishi Zatai Shawara, pls Kausar nabaki Zuwa Nan da gobe Kinga Zaku koma Skul, ok tace ta kashe wayar, tacigaba da tunanin Wayyo gashi naji mamyn Leemah tace budurci Shine martabar diya Mace Toh Anya nidin Virgin ce ma kuwa, Nashiga Uku Wlh lokacin khady har yatsa tana Saka Mun, gashi Ran nan A grp naji Ance Saka yatsa yana Maida mutum dis Virgin, Wayyo ni Kausar dole Yusuf Yasan Abunda na Aikata Abaya khadija ta cuceni Allah ya'isa harta So na cutar da wasu,Allah yasa Su feenah basa yarda dasaka yatsa da yanzu Suma Saisun koka,kai Innalillahi haka kausar tayita tunanin mafita. Shiko Yusuf Murna yarinkayi harda yar Rawa, Kafin ya juya dan yafada ma yazeed yanda Sukai da Kausar yaga wayam ba kowa Awajen,tabe baki yayi yafita Shidai Sai Murna yake.
Sisto kin Shirya kifito mutafi Nazeer Kema Feenah magana, Nashirya big bro Naga kafini dokin Zuwa gidan Su Leemah dinma, "Aa" Feenah Sabida dare ne, toh muje Nashirya,fitowa Sukai Suka Samu Mumy dasu mubeen tana koya musu homework dinsu, mum mun fitofa, my feenah kin Shirya komai ko? "Eh mumy Nashirya" Zomuje Akwai maganar da Zan miki tashi mum tayi feenah Nabinta Abaya Zuwa Room dinta, Zama sukai mum ta kamo Hanunta,my daughter Kinga Nasihar da mamynku tayi muku koshi kadai ya isheku, Zan kara Miki da nawa Kadan,feenah Abunda kuka Aikata Abaya inaso yazama Labari,na hadaki da girman Allah kada Ki kara aikata makamancin irin Abunda kikai Abaya, Nasan wanchen ma Sharrin Shedan ne ba Halinkin bane,Amma kinsan wajibine Dan Adam yayi yaki da Shedan A Rayuwanshi,kusan duk Abinda mutum ya Aikata na Zunubi Son Zuciya ke Angiza Shi,pls Feenah banason kara jin kin Aikata Abu makamancin wanchan badan niba Dan Allah. Sa'annan game da Sha'awa wannan wani Abu ne da yake damun duk wani baligi ko baliga mai lafiya, Inason kisani Aduk lokacin dakikaji zaki iya Samun natsuwa ta Wajen karanta aur'an,Azkar da yawan yin Azumi, Insha Allah dakin gama karatunki kin dawo Za'a fara maganar Aurenki da kabeer inhar kinasonshi kinji my daughter kimun Alkawarin bazan ji kin Aikata wani mummunan Abu ba koda Aboyene. Rungume mum feenah tayi tana kuka tace Mumy nadau maganarki Bazan kara Aikatawa ba da izinin Allah Koda Chan ma ba halina bane Sharrin Shedan ne! ( wai komai Ace Sharrin Shedan Zaku hadu dashi masu aikata Abu da gangan kuce Sharrin ShedanπŸ˜„) Allah yamiki Albarka yata, Amin mumy ta! Ki kara Maida Hankali A Skul kisamu Abunda kikaje nema, insha Allah mum. Tashi muje Toh kigaida mamyn Leemah din, toh tace Suka fito atare palon Suka dawo Nazeer har ya karasama Su Mubeena homework dinsu. Yaya Nazir muje Ko, ok Sister muje. Su Mubeen ne Suka tashi suma Zasuje, mum tace kunga Auntyn kuce ba lfy Allura Zasuje Ayi mata,duk maiso saiya bisu. Ai da Sauri Suka koma Suka Zauna feenah da Nazeer Suka fita Suna dariya.
Kai tsaye Suna Shiga gidan parlon Sama Suka haura Anan Suka tarar da Mamy da Leemah Suna fira,Sallama Sukayi da gudu Leemah ta tashi Suka Rungume juna da Feenah Suna dariya. Mamy ce ta Amsa Sallaman tana Allah ya Shiryamunku yaran nan. Mamy Sannu da gida. yawwa

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment