Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsayar dashi? Kabeer mana Feenah ta fada tana chuno baki. dariya Nazir yayi Cikin Ranshi yace wannan Sun Rainamu da yawa Suna Soyayya A boye yanzu kuma ta kawo Xancen wani daban. Afili Cewa yayi Sister kamar fa bakwason juna keda Kabeer tunda banga kuna waya ba hasalima ban taba ganin yazo wajenki ba. Tabe baki feenah tayi yaya Nazir ba Lallai Sai munyi waya dashi ba ai, Kawai Xamuyi dai Aure. kallonta Nazir yayi Sister Kenan Aurenshi kawai Zaki badon kina Sonshi ba? dafe kai feenah tayi Alamar ya isheta, yaya Nazir Cikin Zuciyata Ina Sonshi mana. Tunani Nazir yayi yasan idan ya kureta yanzu Saita mishi kuka dan haka yace Toh Shikenan Sister Allah ya Kaimu lokacin musha Biki. Amin yaya Nazir Na my besty. Murmushi Nazir yayi yace Sister Jiya din nan Sainaji dama Nida Leemah ne Mukai Aure na kosa na mallaketa Amatsayin mata. Toh yaya Nazir ba haryanzu kaki Sanar dasu mum ba maza dai wani yaje yaimaka Shigar Sauri. Kai sister kamar ya Shigar Sauri bayan Leemah ni take So? Yaya Nazeer misali wani yaje Yanzu yayima Abbanta magana yanasonta idan Abba yayi la'akari da yaron nada tarbiyya Zai iya ya Aura ma Leemah Shi, domin last time Naji yace idan bamu kawo miji Nida itaba Zai bamu Zabinshi. Tunani Nazir yadanyi Azuciyarshi gaskiyafa Feenah ke fadi yazama dole na Sanar da bukatata. Kayi Shiru yaya Nazir. Yes Sister Gaskiya kika fada, da nayi tunanin Nabari Sai kun karasa karatunne but yanzu Zan Sanar da dad kamin ya koma. Yawwa Hakan Shine daidai Feenah ta fada.daidai Sanda Suka karaso gidan Su Leemah.fita Sukayi Atare Sukashiga Ciki. Inno ce kawai Xaune A parlon tana kallon T.V. tana ganinsu Tafara Oyoyo Oyoyo Ga Naziru dan Albarka. Zama yayi kusa da ita feenah tai Shigewarta Ciki da karfi inno tace tunda wanda kikazo danshi baya parlon Ai dole kishiga Ciki bako gaisuwa. Feenah bata juyoba bare tasan me inno take fada. Juyowa inno tayi tana kallon Nazir, yaron kirki Anya Kana kokari kan maganarmu kuwa? Naga har Zasu koma makaranta basu Nuna Alamun Wani Abu tsakaninsu ba. Nazir dake Sauraron inno yace Inno ni Wlh banajin Zan'iya wani Abu Akansu, feenah dazaran kinfara mata maganar Samari Saikiga tana kokarin kare kanta, gata Abu kadan Sai kuka,Kuma Sam inno babu Soyayyar Kabeer Aran feenah, Sabida na lura batama Cika Son aimata maganarshi ba. Kawai yanzu inno mafita daya yusuf ne kuma yasan Yanda Zai Samota Naga Shi yana kokarin Shawo kan yazeed din. Nisawa Inno tayi tace Gaskiya kazama yayan banza tunda Shakkar kanwar taka kakeyi! Bahaka bane inno banason kukanta Sabida dalilai da dama. Kinga idan namata tilas Zataga Kamar nine......Mamy dake Sakkowa ita ta katse Shi take Inno tajawo wata firar tanama Nazir. Sakkowa Nazir yayi kasa Yana gaida Mamy.amsawa take Cikin Sakin fuska ya yan gidan my Son? Lfy qalau Mamy Suna gaidaki.Ina amsawa Sosai bari nakawo maka sako Ka kai mawa mum dinku. Ok Mamy Nazir ya fada.tana shigewa Nazir yace inno Leemat bata fitoba Har yanzu! Inafa Xata fito Ayi magana bayan miskilar kawarta ta sakata A gaba.inno ni ba Wannan maganarba. Toh Nazir wace maganace kuma? Sosa kai yay yace Inno Soyayya muke mai karfi nida Leemat Kuma ni inajin kunyar Sanar dasu dad. dariyar manya Inno tayi! Nifa dama nadade da ganoku kai da ita, Kawai nabarine kaima ka gama kwanakwana irin na tsaka, Amma kai Tunda kafadi Yanzu Zansan yanda Za'ai nashigar da maganarka. Inno yaushe Nazir ya wurga mata tambaya? Idan Suka dawo gida gaba daya. Inno Bakyaga Zan rasata? Kada kadamu Kana tare da inno, kaidai kacigaba daba fulawa Ruwa harta girma tayi Kyau. dariya Nazir yayi yace angama kakus daidai Sanda Yazeed ya Shigo parlon. Karasawa yayi kusa da Nazir ya zauna Suna gaisawa, inno takalleshi ya muna magana kazo kasamu Agaba tsaka? Kallonta yayi yadan ja tsaki. Kama kanka inno ta fada katon banza yanzu gashinan Yusuf yayi aure Kai bakada lokacin yi Haka Zakayita Zama da bakar Zuciya Acikin gida. Kallonta yayi yace idan ke kike bani Abinci daga yau basaiki daina ba. Dani kake magana yaro Kuma daga yau idan nace adaina baka Abinci Agidan nan ta Zauna bari kaji nafada maka. Magana yazeed ya bude baki Zaiyi Saiga mamy ta Sakko, gaisheta yayi ta Amsa Cikin kulawa. Mamy Tunda ga Nazir yazo ai Saiya kaisu Zaria din ko? Da Sauri inno ta karba wato yaxeedu Kai ba'a isa A Aikekaba ko? Kallonta yayi ya wurga mata harara, tace kama Ubanka. Mamy dake Saurarensu tace Ai kai nasaka Dan haka kai Zaka kaisu idan ban isabane Sai naji. Sunacikin Haka Su Leemah suka Sakko Cikin Shiri Sunsha kwalliya kowacce tasha kyau Abunta. tun kafin Su karoso Nazir da Leemah Suke saukar ma junansu Murmushi. Shikuwa yazeed Cikin ranshi yake magana"Subhanallah Ji yarinyar nan Yanda take kara Kyau kodan taji Ance Za'a mata Aure ne? dama naga Alama Auren take bukata matuka" Tabe baki yayi Afili ya wurga mata harara. Itama mayarmai tayi tana mgn da zuciyarta" Mutum kullum Zuciyarshi Cikin bacin Rai take kowa yake ma wannan Cin maganin Oho, kanshi gaba daya Rawa yakeyi dama Aure sukaimishi da Anhuta tunda Shidin jarababbe ne. Maganar inno ta dawo da ita kunzo kuntasamu Agaba Ana magana kun tsare junanku da ido. Sai Asannan yazeed da feenah Suka lura Ashe kallon juna Suke, lokaci daya Suka kara tamke fuska Suna hararar Juna. Shidai Nazir tuni yaja Leemat Sunyi gaba Suna Soyewarsu. Mamy ce tace yakamata kuzo kutafi fa. Feenah tace Mamy Ina drivern Ai bekaraso ba. Inno ce ta kalli yazeed tace ga driver Nan A Zaune. da Sauri yazeed ya kalli Mamy. Mamy Kinga kumaida tshowuwar nan ta tafi inda tafito kinajin Abinda take fadi salon tajamun Raini wajen yara. Murmushi Mamy tayi tace Sannu babba kayi aure kabar gidan saina daina Saka ka aikin yara. Atoh fada mishi inno tafada tana girgiza Kai.kwafa yazeed yayi yatashi idan kunga dama kuzo muje.ko motsi Feenah bataiba domin batson Raini Acewarta tayaya zaice wani idan sunga dama. Mamy ce ta kallita tace ina leemah dinne? Mamy tana waje,toh tashi kije kutafi my Feenah Allah ya tsareku. Amin mamy feenah ta fada ta tashi tayi waje. daidai Sanda yazeed ya fito daga part dinshi rike da key din mota a hannu. Yana ganinta yayi saurin karasowa jawota yayi takusa fadawa jikinshi, part dinshi ya koma da ita rike d hanunta, feenah Zaro ido kawai takeyi tsoro da fargaba Cike da xuciyarta, Cikin Ranta tana fadin Nashiga Uku mai Zaimun ko ya dauka nima irin wannan banzar budurwar tashi ce. Kan kujerar dake dakin ya Wurga ta, ya karaso gaf da ita kamar zaishige Cikin jikinta. idonta ya tsaya kallo nadan lokaci daga bisani yace ke! Saida gabanta ya fadi Sosai kuma ta kasa daga Ido ta kalleshi banlatana ta Amsa mishi. Murmushi yayi wanda shi kadai yasan ma'anarshi yace watoh karyar Rashin Kunya da fitsara dama kike, hannu ya kai kan face dinta daidai wajen idonta, kinga idon Nan naki mai kama dana mujiya duk Sanda yakara Hararata Saina saka wuka na yankeshi. Sannan yakai hannunshi Kan kunneta ya murde da karfi harsaida tayi yar kara Ashhhh, kallonta yayi yaga harta fara kwalla😢 yace duk Sanda kika karamun Rashin Kunya Agaban mutane Saina cire miki kunne Kinji na fada miki. dukda Zafin da kunnanta ke mata da kuma tsoron Yazeed da take be hanata daga Kai ta kalleshi ba, murguda baki tayi tace Allah ya'isa Kuma kaima ka dainamun Rashin kunya mana. da mamaki ya tsaya kallonta yanda take maganar duk ya shagaltar dashi musamman da idonta yake Cikin nashi ga yanda take wani yatsina face bangare guda tana dan taba kunnen ta wajen daya murde mata.jawota yayi ta fada jikinshi tuni ta tuna da yanda tagansu shida mufeeda kwanaki.marairaice fuska tayi tace Am Sorry bro Yazeed ina nufin kaima kadaina Hararata ne fa. Cikin wata kasalalliyar murya yayi magana wanda Saida Feenah taji wani Abu ya wuce mata daga kafarta zuwa saman kanta. Naji mai yasa kika murguda min baki Toh? Kayi hakuri bazan kara ba, ganin gaba daya tanason kashe mai jiki, yasa ya kai bakinshi daidai nata da Sauri ta fiddo ido waje, gashi takasa tashi. daidai kan lips dinta yasaka nashi me yakeson yayi Oho, Muryar Leemah ta katseshi jin tana besty Ina kike ne? Cizonta yayi kan lebinta yace that is my punishment, idan kika kara koba yau ba Saina miki Abunda yafi Wannan. feenah da hawaye keta Ziraro mata tace Toh.dagata yayi ya dau key din mota yaja hanunta Suka fita, daidai Sanda Mamy Ke kokarin Shigowa. kallonsu tayi tace maika kawota tamaka? da Sauri inno dake bayan Mamy tace Fatima bana gaya miki dama Suna cikiba, nafaga Sanda suka shiga har inacewa yazeed me Zaka mata,Sai ita feenah din dakanta tace waike inno ina ruwanki damu, ganin haka yasa na rabu dasu domin dama nadade dasanin Akwai Abinda Suke kullawa Cikin gidan nan. Sakin baki feenah da yazeed Sukayi suna kallon Inno da mamaki Wannan wace irin tshohuwace yazeed yafada Aranshi. Abba ne ya karaso yace lafiya baku tafi ba ku kuma? Inno tace Amadi fatima ta tsaresu dan taga Suna Soyayya tsakaninsu. da Sauri feenat ta kalli Abba tace Abba ba Soyayya muke ba Aiki ya Sakani namishi, kallon Abba yazeed yayi yace eh Abba Hakane ba Sonta nake ba. Dariya Leemah da Nazir Sukeyi ganin yanda Su feenah suka daburce. Abba ne yace toh ya isa kuzo kutafi lokaci na korewa. Toh Sukace Suka kama wajen inda motar yazeed take. Feenah faken idon mutane tayi ta jawo Yazeed gefe Saitin kunanshi tasaka bakinta kamar mai Rada tace yazeed Allah ya'isa muguntar da kaimun Sai Allah yasakamun, kaja ance inasonka me Zanyi dakai ni ko kawata Naji tana Sonka Ai Saina tausaya mata bare Ni dakai na, Allah ya Sawakemun. kaikam ka Riga da Kayi kwantai. Inno d idonta nakansu tace Amadi kalli yaran Chan kuma Sun karyatani Agabanka. Murmushi Abba yayi bece komaiba yaja mamy Sukai Ciki. Kwafa inno tayi tace dasannu Zaku gane yaran naku masoyane tunda kun Rainani gaba dayanku. Feenah nagama fada mishi tajuya tashiga mota Leemah da Nazir ne Abaya. Kallunsu tayi da mamaki, ku kuma bakwa gajiya ne Nan Kuma kuka dawo,yaya nazir ai saika fita tunda tafiya Zamuyi. Sai Asan nan Yazeed daya daskare a tsaye yazo yashiga motar yana Cin magani😊lol Feenah tashi kikoma gaba! Haba yaya Nazir Leemah takoma mana. Leemat tana kusa dani Love Zamuyi Sosai yau. Yaya Nazeer kamance Xariya wannan dusar Zai kaimu. Kallota yazeed yayi ta mirror kallon nine dusa. Harararshi tayi ta maida dubanta wajen Su leemah.Nazir yace Ainima Zarian Zani dan haka Saiki koma. Mgn feenah zatayi Nazir yace tashi kikoma nace. Batason jayayya da yayanta dan haka ta tashi takoma gaba fuska Adaure. jan motar yazeed yayi da gudu yabar Harabar gidan nasu.


Page...34

Tafiya Suke babu maima kowa magana Cikin motar Sai Leemah da Nazir dake yar firarsu kasa kasa. Yazeed tuki kawai yake Lokaci Zuwa Lokaci ya juyo ya kalli feenah dasun hada ido Su sakar ma juna Harara. gyangyadi tafara yana kallonta ta mirror yana dariya Ciki Ciki. Zuwa Lokaci kadan bacci ya dauketa. So yake ya kwantar mata da kujerar Amma besan tayaya Zai mata ba. dan haka ya Rabu da ita. Kadan kadan ya juya ya kalleta baccin kuma ya mata kyau ya fada Aranshi. Abinda ya faru dazu ya tuna lokaci daya ya lasa kasan lebenshi. Kwantowa feenah tayi kan Cinyarshi lokaci daya yaji wani Abu Zirrr ya wuce mishi Zuwa Kai. Mirror ya juya Zuwa baya ganin Leemah da Nazir Hankalinsu bema kansu fira kawai Suke yasashi jan karamin tsaki. Shi yazaiyi ya dagata domin gaba daya bejin dadin drivn din da yake. Mirginawa tayi kanta ya koma tsakiyar Cinyoyinshi yayin da face dinta ke kallon Nashi Ashhh yazeed ya fada jin Wani irin yana yi Atare dashi, idanunta yake kallo Alumshe Suke yayin da Small mouth dinta tadan turoshi Kamar mai Shirin yin mgn. Oh God ya fada domin Zuwa yanzu wani felling ya taso mishi mai karfi. Kara juyawa yayi yaja tsaki mai karfi da Sauri Leemah tace kanason wani Abu ne bro? Murmushi tayi ganin feenah Kwance kan jikinshi Hankali kwance tana bacci. Yazeed yace Kai Nazir kawani biye mata Sai Shirme take maka. Murmushi Nazir yayi yace Ai ba bacci take jiba ita. Phone ta jawo tayi Saitin face din feenah ta dauketa photo. Wow ta fada ganin yanda baccin yama Feenah Kyau. Me kikeyi Leemah? Bro Wannan Hanyar Yamun Kyau Shine na daukeshi pic. juyawa yazeed yayi Kan Feenah Ji yanda ta turo baki Acikin baccinma Rashin kunya take. Saida Sukai tafiya mai tsawo Ahaka Yazeed dai tuki kawai yake Amma Shi kadai yasan maike damun Shi. daidai wani Restaurant Nazir yace yazeed pls tsaya baby Najin yunwa. kallonshi yazeed yayi ta mirro yace baby waye mai Ciki Anan? No my Cutie nake nufi.Tabe baki yazeed yace Dan iskanci bakinci Abinci ba Leemah? Bro yazeed Kasan inada Ulser fa yanzu kamar Na mutu nakeji. Hararar ta yayi yace Mayya. bude kofar Nazir yayi yaja hannun Leemah Suka fita. Yazeed yace Nazir kanwar ka fa? da Sauri Leemah tace idan tana bacci Aka tasheta kanta Ciwo yake. Yes Hakane yanda baby ta fada maka Nazir ya fada Suna kashe ma juna ido shida leemah. magana yazeed Zai kara Nazir yaja Leemat Sukabar wajen. Juyawa yayi ya Sauke idonshi kan feenah yar Rainin wayo taji taushi tayi Kamar mage, gashi Ni duk ta Rikitani. Juyawa tayi ta Sakalo Hanunta kan wuyanshi Oh ya ilahi yazeed ya fada Zata kasheni. Karamin Bakinta ya tsura ma ido jiyake Kamar yayita Kissing dinta ko ya Samu Sauki. jikinshi tafara Shafawa tana besty bani Ruwa. Kallonta yayi yaga bacci take toh maybe mafarki take. Ahhh Shafa Jikinshi data takeyi ba Karamin kara rikitashi yayi ba. bakinshi yakai kan nata Zaiyi kiss Ahhhh No. Nace Mufeeda kesani ina Aikata Zunubi mai yasa yanzu bata Nan Nake kokarin Aikatawa. dayar Zuciyarshi ce tace mishi Toh Ai wannan ma itace tasaka tunda tun dazu take juyi Ajikinka kuma kai ba dutse bane. Yes yafada...Chan kuma yace idan ta farka ta ganni Lallai Zata kara Rainani. Amma Ai tana da Nauyin bacci Shedan din dake kusa dashi ya Rada mishi. bakinshi yakai daidai Nata Yanason ya tsotsa tsoro kuma yakeji. Ruwa Feenah takara fada Cikin bacci tana lalube lalube, bakinshi dake kan nata tafara tsotsa kamar Tasamu Sweet. Nan da nan Yazeed ya rikice yafara kissing dinta Shima. Saida Suka dau mintina Ahaka Cikin bacci Feenah taji Kamar tanashan wani Abu kuma dadinshi takeji. Jikinta taji yamata nauyi Cikinta Sai kara yake Alamar yunwa ido tafara budewa da ker, Still Abu takeji Cikin bakinta dan haka takara bude idon. Waro idanun tayi gaba daya Sabida Abin data gani. Fizge bakinta tayi ta tashi Zaune Adaburce. Sai Asan nan Yazeed ya dago da jajayen idonshi yana Kallonta yana Saukar da Numfashi Ahankali. itama kallonshi take Lokaci daya hawaye Suka Shiga Zuba A idonta. Haushin kanshi Yazeed yakeji me yasa nakasa Controlling Kaina ya fada Cikin Ranshi. Menene Haka bro Yazeed? Nafada ni ba yar'iska bace idan kanason Abunka kaje kayi meyasa ni Zaka Satoni Ka kawoni kana kissing dina kamar matarka. Allah ya'isa Kuma ni ka maidani gida,kuma Saina fada mawa Mamy, miyauna daka Sha....jawota yayi yasakin Mata Rankwashi Akai. Ni Sa'an wasan K ine? Girgiza kai take tanajin Zafin Rankwashin. Kunneta Yazeed yakama yaja kinsan me kikamun ne Sannan kirinka mun Rashin kunya. Shiyasa nace kada kizo Nan ki Zauna Amma kika nace, Ashe So kike kizo ki takura mun, Cinyata kika hau kina bacci, Sannan lokaci daya kika fara ihu kina mafarkin Aure, har rigata kika yamutsamun kalli! Karshe jawoni kikai Kikafara kissing dina kawai na kyaleki ne dan kada kitaramun Mutane domin ihun dakike sai Azata satoki Nayi. Na Rufa miki Asiri domin kina Sha'awar Aure Akan titi Amma Shine kikemun Rashin kunya.idan Naga dama Saina kira Mum yanzu Nace mata kinaso kimun fyade. ido feenah ta waro waje Kunya maganganun Shi Suka bata dauke kai tayi tana Hawaye ni bani bace Nayi Haka! Kunenta yakara ja Karya nayi kenan? Girgiza Kai Tayi Alamar Aa.yimun mgn karya nayi kenan. Aa fa banceba bro Yazeed. Toh Share Hawayen Naki Kuma kimun Shiru.toh tace yazeed duk saiyaji ba dadi yamata Abu kuma Yanzu yaci Zalinta.Sabida karta Rainani ne ya fada Cikin Ranshi. itama magana take Aranta"duk da Sha'awa Ai wannan dagaji Sharri yamun besan Nasan halinshi ba" kwafa tayi bakasha miyauna Abanza ba Zakasan Feenah ka taba. Magana kike ne? Marairaice face tayi inane Nan Toh? Siyar dake nazo yi. Amma bro Yazeed.....muryar Leemah tajiyo tana fadin besty kin tashi Kenan. Motar Suka bude Suka shiga.feenah tace Leemah,yaya Nazir ina kukaje? Abinci naci besty gama Naki mika mata ledar tayi. Amsa feenah tayi Shine kuka barni Ana...mintsilinta yazeed yayi tace "Ashhhhh" ya dai feenah da Zafi ne Abincin?eh tace Kamar yanda taga yazeed ya Nuna mata. Sorry toh.ok No problem besty.tafiyar minti Ashirin ta karasa dasu Cikin birnin Zaria kofar gidansu Kausar yazeed yayi parking Atare Leemat da Nazir Suka Sauka. Bude kofa feenah tayi zata Fita yazeed ya jawota bakinta ya bige yace parrot Common fita kiban waje.fita tayi Rike da bakinta ta Zagaya dayan Seat din da yazeed yake kanta tashigar yazeed ban yafe Abinda kaimun ba Kuma Wlh Saina Rama bashi kaci murguda baki tamai tabar wajen.kallonta Yazeed yake da mamaki Wannan yarinyar mai zan mata tabar Rainamun wayo,Hmmm kada tabari tashiga hannuna. Nazir ne ya karaso yazeed fito mana. Fita yayi fuska A daure daidai Nan mortar yusuf tayi parking fitowa yayi da mamaki Suke kallonshi, Shikuwa da murmushi ya karaso wajensu. Naje gidan Mamy inno tace kunje Zaria Shine Nima Nazo ganin Amaryaa. Tabe baki Yazeed yayi ai saikai mana jagora. Toh kumuje Amma Naga bakuzo da wuriba. Kallon Nazir Yazeed Yayi ga irinka Nan Wanda yabiyema yara yaja duk Sun Raina mutane. dariya Sukayi Suna Nan mukafi Auki Ai. Atare Suka shiga daret parlon baki Suka wuce Su Feenah Sukayi Cikin gidan.

Hajiya kadaice A parlon tana kallo da Sallama Suka karasa wajenta Suna gaidata.Cikin fara'a take Amsa gaisuwar mutanen Kaduna Shine bansan Zaku zoba? Hajiya itama Kausar bata Saniba Surprising dinta mukai.Ah lallai Zataji dadi kun kyauta kuma ya mutanin gidan? Suna lfy qalau Sunce Agaidaki.ina Amsawa drivern ya tafi ne? Leemah tace Aa hajiya bro Yazeed ya kawo mu shida yaya Nazir. Shine kuka barsu waje kuma? Suna parlon baki. Aa nan yakamata Sudawo inada manyan baki haka.Hajiya Yusuf ma yana tare dasu.Ah lallai Bari Nasa Ashigo dasu. Kutashi kushiga Ciki tana Sama. Tashi Sukai Suka haura Sama.Leemah ta tura dakin tana Amarya bata laifi.Chan karshen gado Suka hango Kausar da Sauri Suka karasa Kanta Sukai gaba dayansu.Afirgice ta tashi Atare Leemah da feenah Suka hada baki wajen fadin Surprise🙌 Wow kausar ta fada "I Really appreciate it" Rungume juna Sukai Suna dariya Saida suka dade Ahaka tukun Suka Saki juna. Kallon kausar Leemah Tayi tace kin Rame Sosai Kausar. Ai dole inata tunani Halimcy. Tunani Kuma? Eh mana Na Abinda na Aikata Abaya dakuma na Aure Uwa Uba Shekaran jiya danaje Asiviti Dr yafadamun Cewa......gaba daya yanda tafadama ma hajiya Haka tasanar dasu Leemah, Amma yanzu jiya munje Islamic Chemis da hajiya sunbani magani nama fara Amfani dashi kunji Abinda yasani tunani. Nisawa Sukai gaba dayansu feenah mai arhar hawaye har tafara kuka. Cikin kuka take cewa Ni dama Chan shiyasa Banson Saka yatsa din Nan Koda ba'a fada manava kausar kinsan Akwai hatsari, duk dacewa ba'a ma Ubangiji wayo mukuma yanzu menene tamun matsalar Oho. Ba wata matsala Insha Allah besty tunda muntuba mundaina, itama Kausar Saka yatsa ne yaja mata infection din but muyita Addu'a Insha Allah Zaki rabu dashi kuma kirinka Amfani da maganin yanda ya kamata. Amma Leemah bakiji tace tana tunanin ita dsvirgn bace? Toh Feenah shima Dr din bafa cemata yayi tazama ba, kokunto take Kuma nataba jin wasu matan Aure nafadin Mace bata Rasa budurci Sai idan Sex tayi toh yanzu tunda bashi kausar tayi ba Saiku daina damuwa kan wani Virgin Or dsvirgn. dahaka Leemah ta kwantar musu da hankali Sukabar maganar. Kausar gyaran jiki fa? Leemah Hajiya tace idan muka dawo gaba daya Sai Akai tarewan Zuwa 2weeks Sabida gyaran jikin. Yes hakan yayi Amma kinfara Shan irin Abubuwan da Akeba Amare ko? Kallonta feenah tayi besty ina kika Samo Wannan Surutun,har kikasan wa'innan Abun? Kardai ko yaya Nazir yar bariki Zai Auro. dariya sukai gaba dayansu Suna tafawa. feenah ta kalli Kausar ke yusuf fa yazo.ido t waro Kice Allah! Hajiyace ta Leko Kausar kishiryafa yusuf yazo zasu koma ne. toh Hajiya. Leemah kizo d'ana nakiranki. Rufe ido leemah tayi bata Amsaba hajiya tafita tana dariya.Lallai yaya Nazir Hajiyama yake aikowa Abun Naku ya shahara. Ba ruwanki besty Leemah ta fada tayi waje. Cikin lokuta kadan feenah ta taimaka ma Kausar tashirya Cikin wani material milk Colour dinkin Riga da Siket.kwalliya feenah ta tsantsara mata tayi Kyau kuwa sosai, Karfafa mata quiwa feenah ke karayi yayinda data Rakata har parlo. Yusuf na ganinsu ya taso. Wlcm my wife.Murmushi Kausar tamishi ta gaida Yazeed dake gefe yusuf yaja hanunta Sukabar parlon.juyawa feenah tayi zata wuce Yazeed yaja dan tsaki. Juyowa tayi da murmushi tace Ayya bro Yazeed kai kadai ko Nasha fada maka kaikam kayi kwantai, yanzu gashinan duk suntafi fira Sun barka. Kaikam Saidai kaga Ana Haka kalli Iska ta hura Ahannunta ta hurar mishi lokaci daya da wani irin kiss kashe ido daya tayi tabar wajen. Amaimakon naga Yazeed ya fusata sainaga ya lumshe ido yana murmushi. Duk Abinda tayi Kyau yake mata yafada Cikin Ranshi. Akalla Sunkai Awa biyar tukun suka kama Hanyar kaduna.bayan masu love Sunsha sun koshi. Yazeed tunda feenah ta tsokaneshi be Kara ganin taba harsuka bar garin Zaria.



Page...35

Misalin 12 Na dare Su yazeed Suka karasa garin Kaduna Dan haka yana Zuwa wanka yashiga yayi. be wani dau lokaci ba yafito yayi Shirin bacci Cikin pyjama. Kwanciya yayi da nufin yatashi da wuri domin Gobe 7:30 yakeson yafita Zuwa Office. Saida yayi kusan 1h A kwance bacci yaki daukanshi Toh meke damuna tambayar dayayima Zuciyarshi kenan. Kasa Amsamai tayi Saima tunanin Abinda ya faru dashi dazun data bijiro mishi. Lumshe ido yayi yana tuna yanda Feenah take bacci dazun Kan jikinshi. I like her ya fada lokacin daya tuna irin Abun datacemishi dazun. Ayya Nariga Dana fadamaka Kayi kwantai kaikam Saidai kaga Ana.....Rintse ido yayi ganin Abinda tamishi yake Kamar yanzu Abin ke faruwa. Me yasa Nake tunanin yarinyar Nan Haka? Kawai tana birgeni ne That is way yaba kanshi Amsa. Murmushi yayi yana lasan lips dinshi Ohmmm So Sweet mouth dinta. Bude ido yayi A'uzubillah! Shetan nason yayi wasa da Rayuwata meyasa Zanrinka tunani irin wannan bayan ni yarinyar Sam bataimun ba Asalima Haushinta Nakeji, Me ma yasani jiya ban tambayeta Akan Abinda Naji tanayi kwanaki ba? No Gara da ban tambayeta ba tunda ba matsalata bace. Cije baki yayi Amma Nayi Sake ma da yarinyar ta Rainani da yawa Zanyi magananinta wai kamarni ta kalline tacemun Nayi kwantai Mtswww yaja tsaki ya Juya baya. bangaren Yusuf Shima kwance yayi yana tuna Kausar gaba daya yakasa bacci. Wayanshi ce tafara kara kamar bazai dagaba Saikuma ya jawo ganin mai kiran Nashi yasashi mamaki dagawa yayi Hello! daga dayan bangaren Akace Bakai bacci bane Yusuf? Kai Zan tambaya yazeed kaida Kace kana Zuwa Zakai bacci, Ni baccin yaki tafiya dani, Nikam Zanma iya daurewa Kausar tagama karatun nan bata bani Hakkina ba kuwa! Wlh yazeed tunda Aka dauramun Aure da ita wata irin Sha'awa Nake fama da'ita wanda kamin dauren Auren Sam bana irin Haka. Gashi gobe Zasu koma Skul Narasa yanda Zan nunamata bukatata Sabida Na lura kamar ma tsoro Takeji, dazunfa kissing dinta Kawai Nayi Amma...... katseshi yazeed yayi Kai Malan Sai Surutu kake kamar wani Radio Ni tambayarka Kaji Nayi? Aini bani Nasaka kayi Auren jira ba, idan bukatar matarka kake nakaima Abba wayar ka fada mishi tunda Shine waliyinka, kaga Sai yasan yanda Za'aiyi Akawo maka matarka Ayau karatun ba dole Sai tayiba. Mtswww Yusuf yaja tsaki

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment