Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Afuwan boka mai Nasara. Biyomo toh kicire takalmi tafiya da bayaaaa. yanda bokan yace ma mufeeda haka tayi tabishi Xuwa Cikin yar bukkar. Munsan meke tafe dake. Wani saurayi kikeson Aure Wanda ada kikesonshi dan kudinshi, Zuciyarki ta Chanza kinasonshi yanzu b dan kudi ba, baya Sonki ko kadan Shi, dan haka kikazo A Cusa mishi Sonki Kamar yayi hauka, duk dacewa kinje wajen bokaye da dama bukatarki bata biya ba. duk dacewa mufeeda Tasaba jin irin haka wajen bokaye Hakan be hanata mamakin wannan bokan ba. duk yanda kafada Hakane boka. Wata irin dariya yayi ta marasa imani mudin munsan komai daman. Amma boka Ancemun batamun Al'amarina Akeyi Kozan Iya Sanin wake batamun? Leko Nan kiga mai batamiki tanayine domin itama takamu dason yaron. Lekawa mufeeda tayi ganin khady Cikin kokon ba karamin Razana tayi ba. Lallai zatasan koni wacece. Boka yanzu tayaya Zan Samu Shiga Zuciyar yazeed yazama nikadai yakeso kuma ya aureni?? Wannan aikinmune kin Samu, Saidai Aikin Akwai kudi da yawa. Boka kada kadamu konawa kake bukata zan baka indai bukatata Xata biya. dariyar bokaye yayi Ayauma idan kinason Auren yazeed zaki aureshi, Saidai Akwai mace daya dayakeso fiye da kowa babu wanda Zaiso Kafin ita Saidai bayanta. Yanzu Zanmiki Aiki kizama kece Abaya. Amma kada kidamu da wacce yakeso din Aurema Za'ai mata ba daman ya Aureta. Saidai duk dahaka Zakizauna da kishiya domin Ahalin yanzu Mahaifin yaron Aure Zai mishi, Saidai yaron bayason wacce Xa'a aura mishi din. da farko da mufeeda Taji yazeed Aure Xaiyi hankalinta yatashi,Amma dataji cewa bayason yarinyar Saitaji daidai. boka ba damuwa Abarshi yayi Aurenshi Amma Asan yanda Xa'ai dai Na Aureshi. Wannan ita dayace bukatarki? Ita kadaice boka. leko kigani yanxuma Aikinmu Zai fara. Lekawa mufeeda tayi Cikin kokon da boka ya nuna mata yazeed tagani kwance yana bacci tayi mamaki domin tasha ganin Acikin lokacin nan yana Sallah. kingani yanzu natura mishi Aljana, daya tashi zaifara nemanki, barima kigaaa. Yazeed taga yatashi daga kwancen dayake Rike da kanshi, Amaimakon taga yayi salati kaman yanda yasaba Saitaji yana kiran mufeeda. Wani irin Tsallen murna tayi inda taciro kudi masu yawa ta aje gaban bokan. wani kwalli yabata tarinka Shafawa duk sanda xata hadu da yazeed. Gdy tayi ta fita tabar wajen. Lokacin da mufeeda takoma baccin Su seemah Suke dan haka tashiga Shiri danzuwa gidan su yazeed.

Mamy ce da Abba Zaune A katon parlon nasu sai inno da Leemah dake gefe guda da Alama fira Inno Kema leemah. Yazeed ne yafito Sanye Cikin wata Shadda Orange Colour Sai kamshi yake kwadawa,face dinshi dauke da Murmushi yakarasa wajen iyayen Shi yana gaidasu. Cikin kulawa da nuna farin Cikin yanayin yanda sukaga dansu Ayau Suka Amsa gaisuwan. Shafa kanshi Abba yayi my Son kokaifa yau Har Kyau ka kara Sabida kasaki Ranka. Murmushi yazeed yayi nagode Abba. Allah yamaka Albarka. Amin Abba. Kallonshi Mamy tayi Sai ina haka kanata kamshi? da Sauri inno dake gefe tace Su tsaka bako gaisuwa dan Zakaje wajen balaraba? kallonta yazeed yayi ya yatsina fuska wacece balaraba kuma? matarka mana ta katsina Ai Wlh bagaka yanda kayi Kyau ba har Naji kishi ma. Mtsww ke kikasan balaraba ni kidaina batama Masoyiyata Suna. Wajenta Zaka kenan? Eh inno ko Kada naje? Aa wace ni! Ai soma nake kayi kabar gidan nan,Xanma baka sako Wajen mahaifinta. mtsww Inno kinada matsala. Kamar ubanka ko? Dariya Leemah tayi bro kabar inno zata bata maka rai kafin kaje kanuna kwalliyar. Murmushi yazeed yama Leemah Hakane sister bari naje. Waima ina Zakaje bro? Wajen mufeeda Masoyiya. ba leemah kadai ba hatta inno da Mamy Saida Suka Zaro ido. Abba dabesan wace mufeeda ba shine yayi Murmushi, my son watoh bakason zabina shine kasamo Wata koh. Abba bahaka bane daman mancewa nayi ban fada Maka Mufeeda ba. Ba damuwa son mufeeda yar gidan waye? Kafin inno tabude bakin magana Sukaji Sallama. Abba ne ya Amsa. Mufeeda ce tashigo Cikin Shigar yan bariki, tana tafiya tana karairaya. kallonta kawai Suke da mamaki. Lallai wannan da Sauran miskilancin nashi, maimakon yazo yamun wlcm ma, ga Wannan tshowuwar itama bata tafi ba Ashe!duk sainayi maganinku. Karasawa tayi ta Xauna Sannu Abba Sannu Mamy. Hy kaka, Leemah yan mata kinkara girma. babu Wanda yakulata dan duk sunyi mutuwar Xaune. Abba ne yayi karfin halin Cewa daga yarinya, wa kike nema? Sirikarkace ni Abba! Sirikata kuma?? gira ta daga mishi Alamar eh. da Sauri inno tasaki Ajiyar Zuciya Amadi ina kafurar da nake fada Maka kwanaki wadda yazeed yakawo zai Aura? Itace wannan! Nayi Zaton koya Rabu da ita Ashe kaga Yana bibiyarta. Shagwabe fuska Mufeeda tayi Honey Kaji mai kakarka take fada koh? Tasowa yazeed yayi yadawo kusa da Ita Sorry kinsan tsowuwa ce. Leemah data kufula matuka da hanzari ta taso Tayo kan mufeeda, tashi kifita Agidan Nan tunda bagidan Ubanki bane, bandama ke karyace bantaba jin inda budurwa ke bibiyar Saurayi b.Murmushi mufeeda tayi menene Aciki dan nazo gidan Uban mijina? Mayya yaushe yazeed din yafada miki cewa zai Aureki.kitashi kifita kafin jikinki yafa miki. Honey kanajin kanwarka faa? tashi yazeed yayi yana kallon Leemah. fita a parlon nan Leemah! Babu inda zani bro har sai Wannan tafita. Tsawa yazeed yabuga ma leemah fita nace kafin nakaryaki. Nifa bro babu inda Zani. daga hannu yayi Zai mareta mamy dake kallonshi tace, Wlh yazeed katabamun yarinya Saina saba maka. Mamy bakiji matar dazan aura takema Rashin kunya ba! tashi Mamy tayi taja hannun Leemah dake kuka Sukai Sama. tasowa Abba yayi yazeed Wannan daga gani ba yar gidan mutumci bace,idan Auren dazanmaka ne bakaso ka kawo wadda kakeso kamila ba wannan ba. Abba Ni ita nakeson Aure dan Allah ka Auramun ita. kallon mufeeda Abba yayi kifita kikoma gidanku Sam bakidace da Rayuwar yarona ba. Honey...da Sauri yazeed yace Nidai Abba kafadamata yaushe Xakuje nemamun Aurenta. girgiza kai Abba yayi da mamaki yau yazeed ke jayayya dashi. Juyawa yayi yahau Sama ganin haka yasa yazeed ya Rike hannun mufeeda Suka fita. Tabe baki inno tayi tana tunani Cikin Ranta, kwafa tayi daga bisani ta tashi tabar wajen
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

*I thank God for everything*πŸ‘πŸ‘

Page...62/65

Hannun Mufeeda yazeed yakama Suka fita. Ganin yana kokarin fita daga gidan yasa Mufeeda Shagwabe fuska Honey Muje part dinka mana. Akwai Abinda kikeso ne? Nooo inason Kawai Abba ya Amince Suzo gidanmu Dan muyi Aure da wuri. Wannan ba damuwa bane Mufeeda kizo nakaiki gida dare Xaiyi. Shafa Sajenshi Mufeeda tayi karka damu Xan iya Kwana Awajenka yazeed kawai kazo muje Akwai Abinda Zan fada maka. Haka kawai yazeed yaji baya iya mata gaddama dan haka yabita Xuwa part dinshi. Zama tayi kan bed dinshi tana Shakar kamshin da dakin keyi. Honey Ina matukar Sonka komai naka burgeni yake. Murmushi kawai yazeed yamata yashiga Rage kayan jikinshi. Cikin Ranta take magana inaga bawani bokan dazai iya maganin Miskilancin yazeed, kwafa tayi tunda dai yanzu kashigo hannu ai bawata matsala. Honey Mai Xakayi haka? Aiki Zanyi yafada Ataikaice. Hand back dinta ta Ajeye gefe ta dawo kusa dashi, let me help you. be bata Amsa ba ganin haka yasa takara matsawa gafff dashi hanunta takai Saman bayanshi tana Shafawa, Aikinshi kawai yake Cikin laptop betanka mata ba. Honey Anya parents dinka Zasu bari Na Aureka? Kallonta yazeed yayi nima bansani ba! Amma kanasona ko? Inasonki mana. Kasan yaya Xa'ayi kuwa? Ayi Maine? Ka Aureni ta hanya mafi Sauki! No I don't know. Ok mainene Ra'ayinka Akan kasamu dad din Feenah kasanar dashi komai inaganin he's can help you. Kallonta yazeed yayi ya lumshe ido jin ta'ambaci Sunan feenah. Yeah Hakan Zanyi dan Nima nakosa Na Aureki. Wani irin Murmushi mufeeda ta Saki wanda Ita kadai Tasan ma'anarshi. Honey kanada Kyau Sosai, Sajen nan yakara maka Kyau. Murmushi yayi mata ganin haka tafara Shafa Sajen Nashi. Wani irin Abu yakeji yana Ratsa Shi lokacin da mufeeda ta kai Hannuta tana Shafa kirjinshi. lumshe ido kawai yazeed yake lokaci daya ya jata jikinshi ya Rungume. Honey Sonka fa khady takeyi! Cikin wata irin murya ya Amsa mata wace khady?? Kawar Kausar Matar yusuf. Uhum kigaya mata Ni mijin mace daya ne. Kana nufin Matar da Abba Zai Aura maka baka Sonta? Yeah bansonta. Murmushi mufeeda Tayi Honey kayi Hakuri da Abinda nayi maka last time. Aike bakya laifi Mufeeda kedin ta daban ce. Zokaga mufeeda yanda tayi Wani tsalle jitake kamaar ta taka Rawa. Yanda tayi hungging dinshi yasa lokaci daya yaji wani irin feelings ya tashin mishi. kayan nan Sunmiki Kyau mufeeda! Oh Wow mufeeda ta fada yayin data kara bude Rigar jikinta take bra dinta ta bayyana. Ganin da yazeed yayi kusan Rabin Brest dinta waje yasa ya kama lips dinta kissing dinta yafara da wani irin Salo na daban. Zagewa Mufeeda tayi tana mayar mishi da martani da nata Salon. Knocking din door din da'ake yadawo dasu daga Duniyar da Suka lula. yazeed ne yayi karfin halin fadin Waye? dallah Malan budemun kofaaa. Jin muryan Yusuf yasa yazeed jama mufeeda blanket ya Rufeta.tashi yayi yanufi kofa. yana budewa yusuf yafara masifa tun dazun kanajin mutane kayi wani Banza ka kyale dama Nasani banzo ba ai. Sorry kawai yazeed ya'iya cema yusuf. Bani Hanya toh. Oh Shigowa Xakai? Kada nashiga kake Nufi? No! Toh miye kana Abu kamar mara gaskiya. Ware hannuwa yazeed yayi ya kauce yaba Yusuf Hanya. Shiga yusuf yayi Ciki yazeed yabi bayanshi. ganin mufeeda kan bed din yazeed ba karamin Razana yusuf yayi ba, juyawa yayi yanama yazeed kallon tambaya. bafa Abinda namata malan Kawai....katseshi Yusuf yayi kawai Romancing kayi da'ita. da Kyau.! Ina Alkawarin dakayi nacewa bazaka kara Aikata makamancin Wannan ba??? Tabe baki yazeed yayi wannan bawata matsala bace tunda Aurenta Xanyi. Ido yusuf ya fiddo waje Auren mufeeda fa Kace Zakayi? yeah Soon insha Allah. yazeed mufeeda cefa wadda duk Wata majilisar yan iska Saika Samu Sunanta Awajen. βœ‹ya'isa malan idan kanason Xaman lfy kadaina kushemun mata dan Wlh Zan'iya komai Akanta. Murmushi yusuf yayi nasan dai baka shan giya yazeed pls katashi daga baccin da kake Nacewa wannan karuwarce matarka. yusuf Wlh Xanmaka Rashin mutumci idan ka kara kiran matata karuwa. Sakin baki Yusuf yayi yana kallon yazeed da mamaki. Tashi mufeeda Tayi daga kwancen yayin data jawo blanket din ta tashi harararta Yusuf Yayi ta nuna batama San yanayi b, karasawa tayi wajen Yazeed ta rike hand dinshi bakin bed din ta zaunar dashi Sorry Honey barshi yace duk Abinda Zai fada Tunda kaidai bazaka fasa aurena ba. Haushi yabani Mufeeda. Sorry karka damu da Abinda yake fada. Murmushi yazeed yayi Ok dear.juyawa tayi takashema Yusuf dake daskare ido...Afusace yusuf ya fita yabar gidansu yazeed yayin da Zuciyarshi ke Saka mishi Abubuwa da dama. honey kabani gajiya da yawa fa. Sorry dear bansan Zan miki haka ba. Uhum kawai mufeeda ta fada tashiga Saka kayanta.Tashi ka maidani Toh. Bawani musu yazeed yasa rigarshi yadauki key Suka fita. Ko kallon Yusuf dake gefen wata bishiya Sunkuye da Kai basuyi ba Yaja motar Suka bar wajen.wata iska yusuf ya furzar daga bakinshi yashiga ya tada motarshi yabar wajen.


Mum dan Allah kubarni da wannan gyare gyaren Wlh ni banaso. Haba feenah bakiga bikin lokaci kadan ya Rage ba. Toh mum Nifa bason Wanda Za'a Auramun nake ba kuma miye amfanin gyaran? Dama badan Wani Amfani bane kawai dankiji dadin jikin ki ne. Turo baki feenah tayi ganin mum bazata saurareta ba. Mum dan Allah meyasa baza'a Bari Nasamu Wanda nakeso ba? Sabida ke kullum bakida Zabi feenah. Amma mum komai lokaci ne dakun bari Sai lokacina yazo. Bakida wayo Har yanzu feenah, wake kawo lokacin? Allah ke kawowa mumy. that is my daughter kisani yanzuma Allah ne yakawo lokacin Aurenki ba iyayenki bane Sukai son ransu. Amma mumy yola fa Za'a kaini ganinku ma Saina dade. Toh bakiji Ance Matar mutum kabarinsa ba, kawai kisama Ranki natsuwa feenah komai Zaizo miki da Sauki. Leemah wanda takeso Za'a Aura mata feenah kuma zabin inno. dariya maganar taba mum Sanin idan tayi Zata kara tunzura feenah yasa ta shanye dariyar. Leemah takawo Wanda takeso kekuwa idan Aka biye miki Haka Zakiyi ta Zama. keda yazeed Sha'aninku da wuya babu mai iyamuku dan haka Gara da inno tasamo mafita. Nidai mumy ba irin halina daya dashi ba ni banason ma Anacewa haka. Hakane yafiki saukin kai Kenan? Uhm mum nafishi. Murmushi kawai mumy tayi. Sallamar inno sukaji mumy ce ta Amsa yayin da feenah tabi inno da harara. Maraba inno Sannu d Xuwa. yawwa Hafsat ya gidan. Alhmdllh inno Bari Akawo miki Ruwa. Zama inno tayi tana kallon feenah. Nafisatu bako gaisuwa. Yatsina fuska feenah tayi mutum yana gidansu ma ba'a kyaleshi ba. dariya inno tayi Aure dai yazama dole Garama kitafi Chan yolan Ko zamu Sarara. kallon inno feenah tayi, tayi kwafa kinsan idan Naki auren Nan babu wanda Zai tilasta mun ko inno? Ke din waye Ai idan ina raye Amadi da Umar basu isa su tsallake maganata ba. tabe Baki feenah tayi tajuyar da kai. fadan Akeyi ko????? mum data fito daga kitchen ta fada. Wai Shakiyiyar yarinyar Nan har Yanzu batason Auren Nan. Inno daina biye mata tunda dai komai yazo karshe. kinsan kuwa Hafsa jiya dayan mara ta idon ya kwaso Wannan kafurar yarinyar wai ita Zai Aura! Toh inno badai mufeeda din nan ba ko? Ita Kuwa Hafsa bakiga irin kayan data Saka ba, kinga Rashin kunyar da takema Amadi Kuwa jiya? Inaganin Auren ne yazeed shima bayaso Shiyasa yakara kawo mufeeda din Ko inno? Wayema yasanin mishi Hafsa dan bakiga yanda jiya yake Nan da nan da yarinyar ba kamar Zai mata Sujadda. tashi feenah tayi fuuuu tabar parlon tana fadin duk tazo tacika mutum da Surutu, ko miye Ruwanta dan yakawo wacce yakeso Oho? Komai Saidai Ama mutum dole Shine daidai. Saiki dawo idan Son yazeed din kike kifada kada takasheki inno ta fada da karfi. Aikuwa kara fusata feenah tayi dawowa tayi parlon ni Allah ya Kyauta naso mai hali irin na yazeed bare Shi dakanshi, Kawai inafada miki ne kincika takurama mutane da Saka musu ido. Ke da Allah gudu Chan "tunkan ai daram Akai kwandi" yamutsa face feenah tayi tabar wajen dan batagane mai Inno ke Nufi ba. Allah ya Shiryamana yaran Nan. Ai duk kune kuka batasu Hafsat. Inno yaran dasuke ganin bamu basu kulawa ba Wai. Yoo yaranku ba'a iya musu musamman feenah da yazeed, kidai Cire Nazeer dan Albarka Mai natsuwa. Murmushi mum tayi kawai.yayin da inno tacigava da bata labarin yazeed da mufeeda.

Shirye Shiryen biki kawai Suke bangare biyun Nan. Ba karamin kudi Suke kashewa kan Bikin ba duk dacewa bawani farin Ciki yaran Nasu Suke Ciki ba. Leemah damuwarta bata wuce yanda Za'a rabata da feenah ba gashi bikinsu Rana daya babu yanda Za'ai ta Raka kawarta yola, bangare guda kenan. Adayan bangaren gaba daya Al'amarin brother dinta tsoro yake bata ganin yanzu bayajin maganar kowa saita mufeeda ga yanda gaba daya ya rame yadawo wani soko dashi. feenah ma damuwarta bata wuce Auren da za'a mata da Wanda bataso ba wanda hasalima batasanshi ba,bama Wannan ba Acewarta yolan daza'a kaita yafi bata mata Rai, Hakanan take Sukuku koda yaushe ba kwanciyar Hankali. Kausar ma Damuwar kawayenta data mijinta kadai ta isheta, dan ba karamin tada hankali yusuf yayi game da Halin da yazeed yashiga kan Mufeeda ba, kusan rabin dukiyarshi ya saudakar kanta,dan ma yusuf yana hana wasu Abubuwan su faru A boye. Kuma Zuwa yanzu yazeed yasanar da yusuf irin son dayakema feenah yakara dacewa dukda Nasan yanzu tamun nisa, tun farko Nayi Zurfin Ciki ban sanar da itaba, kuma nasan Koda nasanar da ita ba lallai tasoni ba. Lokacin da yazeed ke Sanar da yusuf Hakan ya matukar tausayama Abokin nashi dukda yasan miskilancin shi yaja mishi. Kowa mamakin yanda yazeed yakoma farar daya yake, Saidai gaba daya iyayen nasu Sun dau Abun kan cewa dan bayason Amai Aure da yar kauye ne ya koma Wajen mufeeda, dan haka Abba yace Su Rabu dashi Aure ba fashi duk Abinda Zaiyi yayi. Bangaren mufeeda kuwa duniya Sabuwa batada wata matsala A rayuwarta, wandaka kawai take da dukiyar yazeed Son Ranta, kullum tana manne dashi ta hana kowa ya rabe shi,lokaci Zuwa lokaci takan jaaa Ra"ayinshi da irin makircinta Su'aikata Son ransu Saidai duk da haka Yazeed betaba tunani yin Sex da mufeeda ba, Abinda take da muradi Kenan takasa Samu,gashi tana gudun takurama yazeed Asiri ya karye kamar yarda boka ya fada Cewa Aduk Sanda ta takurashi kan yamata Abu dole Asirin Xai iya karyewa,dan haka take kaffa kaffa. Tuni khady ta gano Asirce yazeed mufeeda tayi babu Hanyar da batabi dan karya asirin ba Abu yaki yuwuwa, gashi yanzu Seemah ta daina bata Shawara cewarta tagaji batada matsala da Abinda yashafesu. Lokacin da bikin Su leemah, ya rage Sati3 Alokacin yazeed ya Same dad din Feenah kan maganar Aurenshi da mufeeda Kamar yadda tabashi Shawara. Yanda yazeed yasanar da daddy haka dad ya mayar ma Abba firrrr Abba yace bazai Amince yazeed ya Auri mufeeda ba kuma bazai fasa Aura mishi balaraba ba. da ker dad din Feenah yasha kan Abba kan yabar yazeed ya Auri mufeeda yana ganin Hakan zaisa yazeed din yasamu natsuwa. Saida Abba ya lura Abin yazeed din da gaske ne tukun Aka tsayar da magana Kan Saidai yazeed ya Auri mufeeda tare da balaraba din.lokacin da Aka Sanar da yazeed cewa yayi ya Amince da Hakan. Haka Akacigaba da shirye shiryen biki duk dacewa Amaren basada kwanciyan hankali ba'a fasa yin komai ba. Yusuf ma daker yacire damuwa yashiga Shirye Shirye, inda yake hada musu party tare da Sanar da abokansu na nesa dana kusa. Kausar ma danne damuwarta tayi Suka Shiga hidima ita da Leemah na gayyatar kawaye. Feenah kuwa cewa tayi babu Abinda Zatayi A bikin dan haka batamabi takansu. Yanzu ne Kuma Hankalin Mamy yakara tashi game da Halin da yazeed yashiga. Maganar inno ce ta fado Mata Arai Ranar data ce. "Abu kamar Sihiri yaro farar daya yafita hayyacinshi mace daya yake gani da daraja" girgiza Kai Mamy tayi tabbas Akwai Abun dubawa Cikin maganar mamah dole Nasamu Hafsa Muyi maganar Nan. Shiryawa Mamy tayi tsafff dan Xuwa gidan Mum din Feenah yin Shawara.

*kunata Mun fada Readers😭😭😭Sabida Kwana biyu banyi post ba. kuyi Hakuri Nima Bahaka Raina yakeso ba, wata Akasamu ko wani yamun delete din Account dina na Facebook gaba daya, Saida Nabude Sabo. Love you all my lovers*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page....66

Mintuna kadan Suka Kai Mamy har kofar gidan Su feenah. gidan tashiga Kai tsaye babban parlon Nasu ta nufa da Sallama. Twins ne kawai A parlon Suna ganin ta Suka tashi d gudu Sukai kanta. Oyoyo Mamy Oyoyo mamy Abinda Suke fada kenan Rungumesu tayi lokacin data karasa ta Xauna kan kujera. Twins kun kara girma Shiyasa bakuzomun ba 2days koh?. Mamy gobe Zamuzo miki ai. Kacika wayo Mubeen gobe kunada Skul ba Zuwa Zakuyiba Nasani. Mamy Nidai yau Zan biki. Yawwa mubeena Kinga Saiki Kwana wajena ko? Kiga mai Kyau da Aunty leemah. Kada kai mubeena tayi Alamar eh. Ina Mumyn ku? Mum tana Sama taje daukoma Mubeen kaya. Aima gani Nazo mum dake Sakkowa ta fada. Ashe babban bakuwa Nayi! daria Mamy tayi Aikuwa keda bakya Son Zumunci Sosai ba. Kai Fatima da kenan kika Sani duka duka yaushe nabar gidan ki? Kindai Cika kare kanki. Murmushi Mumy tayi yayin data tashi, Bari Nakawo miki Abunda Zaki motsa baki. bata wani dau lokaci ba ta dawo. Sannu Hafsat. Sannu Fatima y Leemah kwana biyu batazo mana ba. Tana gida nabarta Suna fira d Inno, Halan feenah bacci take koh? umm Feenah tana Sama batajin dadi kinsan tun lokacin da'akai maganar bikinsu take faman Tunani wanda Narasa Na miye. Kenan Shiyasa yanzu take kin Zuwa gidanmu, tunanin nata be wuce Na Zaman yola da Zatai ba Hafsat! Toh tunda dai basajin magana basaisuyi hakuri ba. Inafa Zasuyi Hakuri Hafsat,kina ganin yazeed Abunda yasaka ma Zuciyarshi yanzu, tundaga lokacin Shima da'akai maganar bikinsu Narasa kanshi, Ni dama Sabida Shi nazo Nan, Hafsat gaba daya Al'amarin yazeed yanzu tsoro yake bani yaron da ada idan kika Saka mishi yatsa kikace ya Ciza bazai iyaba, Amma yanzu Shine yake ja'inja da Mahifinshi bama niba, Yanzufa Sai Abinda yarinyar nan Mufeeda tace mishi yakeyi, Ko'ina tayi yarinka binta Kaman Rakumi da Akala. Nisawa Mumyn feenah tayi Gaskiya Fatima Ina tunanin Akwai Wani Abu Akasa, idan baki mance ba Akwai Sanda yazeed yakusa dukan yarinyar Agabanmu, baya sonta wancen lokacinma daya kawota yace zai Aura ina tunanin dan Abbanshi yace ya fiddo mata ne yasa y kawota badan yana Sonta ba, Amma Gaskiya Abin nashi na wannan karon bayin kanshi bane, yakamata muyi binciki Akai. gaskiyane Hafsat Abinda inno tace kenan harta Saka wani Malamin Sunnah A Katsina ya farama yazeed din Addu'a! Tabbas Itace kuwa Mafita dan duk wanda yaji wannan Al'amarin yasan Akwai Sihiri Aciki, muma kanmu Mudage da Addu' a kawai Allah yakareshi daga Sharrinta d Sauran mutane gaba daya. Hakane Nifa Sam banason Auren nan nashi da'ita Hafsat. gaskiyane nima lokacin danaji Raina beso ba Wlh Addu'a din dai idan ba Alkairi Cikin Aurensu Allah ya Chanza Al'amarin. Amin dai domin Kwata kwata bata dace da Rayuwan yarona ba. Kinsan ma miye fatima kisaka Amishi Saukan Qur'an Ki yawaita Sadaka itama maganin masifa ce. Insha Allah Zan dage Hasfa Allah yamana maganin Abinda yafi karfinmu. Ameen ya Allah, Shima yazeed din yakamata kirinka lura da yanayin ibadarshi, kirinka Sakashi Agaba yanayin addu'oe da Azkar, Bari Nakawo miki Ruwan Zamzam kirinka Shafa mishi kuma yanasha insha Allah Za'a dace, Sannan kisamu ganyen magarya kinamishi Amfani dashi Shima yana karya Sihiri da izinin Allah. Shiyasa Shawara yake da dadi Ina Zaune kawai Nayanke Shawaran Zuwa wajenki, Allah yakara Zumunci Surukata. dariya mum tayi Amin dai, Amma kisani leemah yatace bana Surukar dake. dariya Mamy tayi Sukacigaba da firarsu ta Aminai. Bari kiga Naje na duba feenah natafi. da Wuri haka mamyn yazeed? Eh Zanje nafara lura da yazeed din ne. Hakane kuma! Ai yar taki tana Ciki Saikin Sakko. Sama Mamy ta hau ta Nufi dakin Feenah, kwance take idonta Alumshe kamar mai bacci Amma ba baccin take ba, blanket taja ta Rufe iya kafafunta. tura dakin Feenah Mamy tayi da Sallama. Kasa kasa feenah ta Amsa Sallaman still idanunta A Rufe. Karasawa Mamy tayi bakin bed din ta Xauna kallon feenah tayi ganin idon feenah Sun kumbura ya tabbatar mata dacewa kuka tayi, Ajiyar Zuciya Mamy tayi yayin datake karajin Son feenah Azuciyarta, yarinyar Na burgeta har Cikin Ranta takejin Son yarinyar. Cikin Ranta tafara magana. " me yasa yaran Nan Suka kasa fadan Abinda ke ransu? Zanso Ace feenah tazama matar yazeed domin Itace ta dace da Rayuwar Shi, me yasa Abban yazeed be hada Auren yazeed da feenah ba?, Maybe ba Alkairi bane Zuciyarta tabata Amsa" motsin da feenah Tayi ya katsemata

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment