Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya maida y lumshe yana murmushi. Bansan maiya tuna Cikin Ranshi ba ya maida fuska ya daure Sak yazeed din da yakoma. ke baki iya Sallama bane?? Cikin Ranta tace Shiyasa 2days banason haduwa dashi wlh. Ba dake Nake ba. Saida tadan bata lokaci Kafin ta dago kanta tana kallonshi. Atare Sukaji wata irin faduwar gaba atare kuma Suka maida kansu kasa. aini nayi baka Amsa ba feenah ta fada. miye yasa baki tsaya har Sainajiba? Nifa Wlh Abinda na tsana kenan tambaya da nuna isa feenah ta fada Cikin Ranta. Afili cewa tayi Nifa bansan mai Zan gaya maka ba, bro yusuf ya turoni Nan if not Kasan babu Abinda Zai kawoni wajenka,pls kacemun ga Abinda kake so Natashi natafi. tunda tacigaba da magana yake kallon bakinta yanda take motsashi idan b kallonta kake ba saika Rantse kace ba ita take maganar ba. dawo d Hankalinshi yayi kekoh! Koda yake nadade dasanin bakida kunya tun farko. Amma Xan koya miki Hankali Soon.yanxu wannan file's din Xaki iba kirinka turamun patient din dake waje One by One. Zumburo baki tayi ta'iba file's din tayi waje....kallonta yayi yasaki Murmushi komai kyau yake mata Cutie.

Haba Seemah kina ganin tun Ranar bekara nemana ba, Anya da'ace da gaske yakamu da Sona Ai da yanxu yakara nemana ko? tsaki Seemah taja Cikin Ranta Afili dariyan dole tayi Khady kincika Xumudi. Kinsanfa miskilin mutum irin yazeed komai Sai anbi Ahankali kanshi. yanxu Samu Xaki kikara Xiyartarshi daga Sanda kikaga yafara Sonki kamar ya mutu Saiki daina Xuwa wajenshi da kanshi Xakiga yadawo yana bibiyarki. haba dai Aunty Seemah? Ke wai khady Kamar ba mace ba koda yake yarinta Yasa, keni banma Ga dalilin dayasa kikeson Aurenshi ba Naga duk Abinda Ake Samu Cikin Auren kema yanzu kina Samun Shi. Hakane Seemah ni kawai Sonshi nake d Aure idan ban Aure shi ba inaganin Xan iya Samun matsala. Ashe kuwa Zaki mutu! Kallonta Khady tayi kamar ya??? da Sauri Seemah tace ina nufin Zaki mutu dan dadi dan kuwa Kamar kin aureshi kin gama. dariya khady tayi Har kinsa gabana ya fadi daxun. ai Saiki dauko Abinki ki maida dan munkusa musha biki. dariya khady tayi Shiyasa Nakesonki Seemah. Allah ko? Eh dagaske Mana. magana Seemah Zatai Mufeeda tashigo dakin. Xama tayi fuska adaure. Toh lfy kuma Mufeeda? Haba nagaji. Wlh nagaji Seemah Saikace wata bilonia ce nidin Haba ina dalili. Wai miye yafaru Mufeeda? Seemah kina ganin yawan kudin Dana kashe kan yazeed bokaye daga maicemun Aurenmu Zai kasance bayan Sati2 Sai Mai cemun yaxeed Zaizo ya Sameni da kanshi.kina ganin bokan Chan danaje wajenshi cemun yayi Aranar yazeed Zaizomun d maganar Aure yau nakoma yana gayamun wasu banxayen maganganu Haba. Lallai dole kidamu kawata, Ammafa tawani bangaren Sainaga kamar ba Abun damuwa Aciki Sabida kinriga kinsanar da yazeed Halin wacce Akace Xai Aura,kinga yanxu ba lallai ya aureta ba, Hakan Wata dama ce dazakibi kikara Zagewa dan ganin kinci Nasara. Keni Seemah Nama tambaya Ance Shida yarinyar basa wani Soyayya.Sai yanxu Nayi danasanin fada mishi Halinta tunda Abanza Nayi,gashi Ranar bakaken maganganu Nayita fada mishi Son Raina, kinga Idan bada bokaye ba ban isa nakara tunkarar Yazeed kai tsaye ba. Kallon Khady Seemah tayi ta kashemata Ido daya. Amma mufeeda Sainaga Kamar kidaina Asaran kudinki haka,kefa mace ce Yanzu kinemo kissa kirinka jefa mishi Kawai. Hmm Seemah bakigama Sanin Halin Yazeed ba Wlh,ba irin kissa da ban mishiba duk Abanza. Amma Bokan danaje wajenshi yau yace mun rushemun Al'amurana Ake, duk yanda Akai feenah din nan ce Kuma Amma Xanyi maganinta ne Ahankali. Lallai kam kidau mataki iska dai na wahalar damai kayan Kara Wlh. Kaman ya fa?? Ita feenah din Nake Nufi mana inaganin son maso wani fa takema yazeed din. Kinga kuwa ai Awahalce Zata kare. dariya Mufeeda tayi Kedai Bari Wlh Nasanma Son masu Wani din take mai Adaiyi mugani. dariya Abun yaba Seemah Sosai cikin Ranta take fadin "Wannan batasan me take ba" Afili Cewa tayi Adaiyi mugani kam. Kallon Khady Mufeeda tayi waike yaushe Xaki tafi ne?? Yatsina face khady tayi Saina Samu biyan bukatata. Tashi Seemah tayi tana dariya Zaku mutu kan Wanda besanma kuna haukar Sonshi ba. Amma idan bukata ce ai kingama biya Saidai Ko dan kedin jarabatuce.kiyi Aure Kawai Shi yafi. Aunty mufeeda bazaki gane ba mijin danakeso Ake neman Asircewa Nikuma na hana,burina kawai nakeson yacika Na Aurenshi kafin nabar garin nan. tabe baki mufeeda tayi ta tashi tabar Wajen.

Xuwa yanzu yaxeed yagama tabbatar ma kanshi Son feenah yake, matsala daya dole yacire Sonta Aranshi domin ba Sonshi take ba. Leemah tun tana tunanin mai yasa yazeed yakeson taita mishi firan Feenah har ta daina tunani. dan yanzu da xaran sun koma gida Xai xaunar da ita yace tamishi firan dasukai. ganin haka Yasa take mishi firan Feenah Hakan Kuwa yakeso Xama yake tana bashi lbr yana dariya Kamar ba yazeed mai Halin Shariya ba. Miskilancin dai yana nan domin haryanxu yaki Sanar da kowa Abinda ke Ranshi. fadanshi da feenah Sai Abinda yakaru ma. Sam ita haushi yaxeed yake bata, kusan huni Suke fada Cikin hospital din nan. Yusuf Shidai yanzu yazubama yazeed ido danyaga gudun ruwanshi,dan haka be nuna mishi cewa ya gane komai game dashi ba. Haka rayuwan take ta Cigaban musu. Leemah da Nazeer yanzu Anxama daya daurin Aure kawai Ake jira,domin yanxu basa iya Rayuwa batare da daya yaga daya ba. Mufeeda da Khady Soyayyar yazeed ba karamin Azabatar dasu take Ayanxu ba. gashi duk inda Mufeeda ta bullah Sai Taga ba chanji dan haka yanxu tadan lafaaaa Acewarta Sai bayan kwana biyu tacigaba da neman mafita. Khady Har yau takasa kara komawa wajen yazeed Acewarta kada yagane ita ba mutuniyar kirki bace gara Shi ya nemeta. Haka Seemah ke kara dulmiyar dasu kan cewa Xasu Samu Nasara, Abayan idonsu taci dariyanta ita daya. Abba da daddy Sun yanke Shawaran Saka Ranar bikin Nazir da Leemah,inda inno takafa kanbu kan sai Anhada Dana yazeed. Yanzu Abba da daddy tunanin dasuke Yi kenan yanda Xasu Shirya Abun. dan haka Suka yanke Shawaran haduwa gaba dayansu gobe a gidan Mamy you
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NadseerπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page....60

Washe gari gaba dayansu gidan Abba Suka yada Zango,inda Suka hallara babban parlon dake Kasa. Shigowar Abba da daddy kawai Suke jira. mintuna kadan tsakani Saigasu Sunshigo. gaisawa Sukayiyyi daga bisani Abba yafara Magana. Yazeed ina yusuf ne?? Abba yace Suna Hanya Shida Kausar. Madallah kafin karasowarsu Bari Naji ta bakinka. Matar danace kasamo kasamu kuwa?? durkusar dakai yazeed yayi kasa Abb.....inno dake kusa dashi tayi Saurin Kai bakinta Saitin kunnan Shi,tsaka Wannan karan kada ka Cuci kanka Xuwa yanxu Kai kanka Kasan Nafisatu kake So, Toh kafadi Gaskiya idan ba hakaba Amadi Zai Aura maka koma wacece. Maganar inno ta dake kunnan Shi, Gaskiya ta fadamun Inno. Amma yarinyar bata Sona Ai kuma! ni yanzu nace inasonta gaban mutane girmana Ai yafadi,kuma Xata kara Rainamun wayo tunda dama bata da kunya. Sannan ma....Mamy dake dayan bangarenshi Xaune ta katseshi my Son kafadi Abinda ke Ranka kada kabari Abbanka yayi fishi yamaka auren dole. Auren dole kuma?? Tambayar da yazeed yayi ma Zuciyarshi kenan! Abba Zai iya Amma gaskiya ni bazan Jama kaina Raini wajen yarinya karama ba.magana Zaima Abba yaji Sallamar yusuf da Kausar. Saida Suka gaisa gaba daya yusuf yadawo kusa da yazeed y Xauna. Abba ne yacigaba dama kai muke jira yusuf Kasancewar yakamata Ayi Komai kana Nan. Abokinka nake tambaya ko yasamo Matar danace yasamo, Kasan 6months kenan danace mishi, banda Shekara1 Dana taba bashi last time. Eh Hakane Abba Ai yanxu inaganin yasamo wacce yake So. Madallah Shine Nakesonji daga bakinshi Ai. K'asa kasa Yusuf yayi da murya kaji Abinda Abba kesonji daga bakinka, idan kaga dama kaki fadan Gaskiya Sabida miskilanci irin Naka. Kana batamana lokaci yazeed Mamynshi ta fada. Amm Abba ni bansamu wacce nakeso ba Har yanxu. kallonshi Leemah,Kausar,yusuf da Nazeer Sukayi da Alamar tambaya. Lallai Wannan bro din bazai taba Chanza hali ba Leemah ta fada Cikin Ranta. Mtsww Kaje ka kashe kanka yazeed Yusuf ya fada Cikin kufula. Yazeed kenan Soyayya ba'a mata yanga Kausar ta fada Aranta Tana murmushi. Nazir murmushi kawai yake yana kara jinjina Son girma irin Na yazeed. Inno data Cika da takaicin yazeed Afili tace dan iska kawai, kafison Abarka da kafura tana Shigomana gida Alabe tana fita a labe, toh Wlh baka isaba! Amadi kabashi balaraba yar gidan ladoo dama tun sanda yana Zuwa wajena take Sonshi. Mamy Na dariya tace Aikuwa mamah Nasan yarinyar tana Zuwa gaidani idan naje! Ita kuwa Fatima Kinga idanma yarinyace baya So Ga balaraba. Shikenan hakan Za'Ayi Abba ya fada lokacin daya maida hankalinshi kan Nazir. Captain kaidai munsan komai kuma munyi Shawaran Saka Ranar bikinku kaida Leemah Ayau. dan haka Nan da wata2 Za'ayi Aurenku insha Allah. Murmushi Nazir yayi mungode Abba, Leemah dake gefe jitake kamar ta tashi ta taka Rawa dan farin Ciki. Hada ido Sukai da Nazir Atare Suka kashema juna ido. Minstilinta Kausar tayi mazari Kawai ai kyabari Sai Ranar Auren kiyi Rawar kai haka. dariya Leemah tayi Kai Kausar kemafa haka kikai. Cigaba Abba yayi ALHJ Umar Faruk ko kanada magana dasu? gyada Kai dad yayi Aa babu Amma wacece balaraba da Za'a ba my Son? Kuma yace yana Sonta ne?? da Sauri Inno tace Ai A Katsina take Umar,ta dade tana Sonshi ba lallai Saiyace yana Sonta ba tunda beda Matar Aure,mukuma mungaji da ganinshi haka b Aure. Murmushi kawai dad yayi Allah yasa Alkairi Toh. Amin inno tace da Sauri. Kallon feenah Abba yayi My daughter kema ina Alkawarinmu dake yake?? Saida tadan bata lokaci daga bisani tafara magana, Abba Ni duk masu nemana babu Wanda Nake so, Saidai ko nan gaba. babu Wani Nan gaba Munafukan banxa, Ai Wlh Umar Akwai Wanda tun lokacin damukaje Auren Kabeer yola yanuna yana Son Nafisat, kaga tunda batada Zabi itama Amata Aure dashi Kawai. Inno ke zayyno Zancen nan. dariya dad yayi Shikenan mamah inno indai yamiki Ahadasu Kawai ba wata damuwa. Kallon dad feenah tayi tajuyar da kanta Xuwa wajen inno harara ta Wurga mata hade da kara daure fuska. Juyawa inno tayi ta nuna batamasan feenah nayi ba. Alhmdllh Abba ya fada. Tunda yazeed da feenah Sukadai Suka rage marasa jin magana ta, ni Xanyake hukunci da kaina. Wata biyu dasuka Rage Na bikin Nazir da Leemah, Aciki yazeed Shima Zaiyi Aure, dan Zuwa gobe Zani Katsina dan nema mishi Auren balaraba din. itama Feenah Alhaji Umar kashirya muje yola munemi yaron da inno tayi magana Ayi komai dan duk tare Zan Aurar dasu Arana daya. Hakan yayi daidai dad yafada Allah yakaimu da Rai da lafiya. Amin duk wajen Suka Amsa banda feenah da yazeed dasuke jin Kamar Sushake inno. kutashi kutafi ko. tashi Sukai gaba daya wajen ya Rage Abba, dad,Mamy,mumy Sai inno. Bansan mai Suke Shirin tattaunawa ba Na tashi Nabi bayan su yazeed.

Fadawa kan bed yayi lokaci daya ya Rike kanshi ya Rasa miye kemai dadi, gashi gaba daya ya Rasa Wani irin tunanima yadace yayi Ayanzu. tura dakin yusuf da Nazeer Sukai, Ciki Suka Shiga Suka Xauna. Ko kallon yazeed dake kwance basuyi ba, yusuf yafara ma Nazir magana. Gaskiya Captain ina tayaka Murna, Nan da wata2 kaima kaxama Ango tare da masoyiyarka wacce kakeso take Sonka. Murmushi Nazeer yayi kaidai Bari Dr yusuf yau dinnan jina Nake Kamar A Aljannah. Wai yau nine Akasama Ranar Aure da Leemah wacce nadade inasonta Kai Alhmdllh Wlh. Kaban dariya Captain kaidai Allah yasoka baka yaudari Xuciyarka ba, da yanxu Abba yayi maganinka irin Na feenah. Lallai yusuf aini son girmana bekai na feenah ba, duk Abinda nakeso bana Shakkar fadanshi ko A'ina ne, Sabida ni Xata kwabemawa gaba idan ma ban fada ba. Gaskiya Captain ka hadu Shiyasa Nima lokacin banyi Sanya wajen fadama Kausar inasonta ba, Alokacin har Zugani Ake wai mai Xanyi da karamar yarinya, gashi yanxu banda farin Ciki babu Abinda ke tsakaninmu. Nagani ai Dr Allah muma ya nuna mana lokacin mu. Amin Captain Amm....Wani tsaki yazeed yaja wanda yasa yusuf yin Shiru. Juyawa Sukai lfy yazeed? yusuf ya tambayeshi. ya Zaka tambayeni ko lfy bayan komai Agabanka Akayishi. Ohhh wai wannan Abun kakejama tsaki haka?? Aini banga Abun damuwa Anan ba bakada Wacce kakeso, Menene Na damuwa kuma dan Inno ta Zaba maka? Haba Yusuf wai wata balaraba fa take Cewa, Ni Wlh bana Sonta Koma mai Xa'a Mun bazan Aureta ba. Nanfa daya yazeed Kasan Abba baxai Janye magar Shiba tunda babu Wanda yace kaki Samo mata. Inada wacce Nakeso yusuf ita dince bata Sona. Hmmm yazeed tunda Agaban Abba baka iya fadin haka ba, muma ka Rabu damu tunda be Shafemu ba. Yusuf kasan banida Abokin daya wuce Kai ko? tayaya Kana ganin Xa'amun Abinda banaso kuma Kayi Shiru? Yanzune kasan baka da wanda yawuceni Yazeed? Najima tunda ka gane hakan yanxu me kakeson Nayi bayan ni bansan Sirrin Zuciyarka ba, kokuma Dan nine Sarkin Rashin kunya Sainacema Abba be kyauta ba bayan ni banida wacce Xan baka, kawai kayi hakuri Kama Abba biyayya ka Aure wacce Suke So maybe....haba yusuf inno cefa kadai Tasan yarinyar ita kadai kuma take bakin cikin Zamana Agidan nan Saikace kanta Nake Xaune. Tabe baki yusuf yayi duk Abinda babba ya hango yaro baya hangoshi koda yahau tsani. Kaga inno ta hango Wani Abun Atare da balaraba dan haka kayi hakuri Kawai. Yusuf... katseshi Yusuf yayi tunkan yace komai, Nidai ka kyaleni yazeed yanda ban isa Naji damuwarka ba, haka ban isa Nayi jayayya da Abba ba. tashi yazeed yayi yabar dakin Rai Abace. dariya yusuf da Nazeer Sukai. dan Rainin wayo Ai gara da inno ta Samo balaraban Wlh yaje yayi Auren kauye tunda girman Kai baxai Bari yafadi wacce yake soba. Murmushi Nazir yayi Shidai yazeed yanayinshi daban. Ai haka Sister dinka itama take Nazeer. Shikenan yusuf itama ai dan kauye Zasu aura mata kaga Sunja mawa kansu. dariya Sukayi Atare yayinda Suka Cigaba da firarsu kan yanda bikin Xai kasance.

Haba feenah kiyi hakuri komai idan kikaga yafaru dama Chan haka Allah yasa. Mai yuwuwa kiga Dan yola din Shine Zai Zame miki farin Ciki Agaba. Nasani Kausar Amma Ni bance inaso Asamamin mijin Aure ba, lokacin danake matukar Son nayi Auren ai basu yanke Shawaran haka ba, Sai yanxu da wannan inno din tazo komai tace Suce toh basusan lokacin wannan ya huce ba. Sorry besty inaganin wasa Suke muku babu wani Auren kauye dazasu muku. Lallai feenah kinfini Sanin Halin Abba Saikiyi tunani yana chanxa magana ko idan yayi ta Xauna. Kumafa Hakane Wlh, Amma kema feenah kin tabbatar bakida Wanda kike So? Ni Wlh Leemah banida Wani Zabi. Kingani kibari kawai ki Aurenki Kinga Rana daya Zamuyi ma kamar yanda muka tsarama Rayuwarmu. Hakane Aike da wanda kikeso Za'a miki Auren. Sorry Kema zakiso Nakin ne Soon. Tabe baki feenah tayi wai Saikace angaji dani Wai Wani dan yola, Ai wlh barima Naje Nasamu inno din Nan. Tana fita Kausar da Leemah Sukai dariya. Kinga inno ta iya jan fada daman. Aini banga laifinta ba Leemah Gara tayi maganinsu. Amma Kausar nagane da gaske feenah bata Son bro Yazeed fa, Saidai Shi gaba daya yamutu Akanta yanzu. Dama bana dade inagaya miki hakan ba, Shima yaxeed din Cikin lokacin Nan yafara Sonta, Amma dama Chan nasan yusuf ne yashirya Hakan. toh ai Kausar hadin yayi ne Sosai. gaskiya kam koni zanso ace feenah ta Auri yazeed Amma Kinga da'ace yazeed din besaka Son girma ba yafada yana Sonta da komai yazo da Sauki. Amma yanxu lokaci ya kure musu tunda ansama musu Masoya. Allah yasa Hakan Shine Alkairi toh. Amin dai Leemah. dakin inno feenah ta wuce tashiga. Yazeed tagani tsaye inno nakan bed. Kallo daya tamai ta kauda kai tana jiran inno tagama mgn. Kadaiji Abinda nace maka Wlh idan baka Amince da balaraba ba Saina fada, Ai da idona naga tokafurar tafito takalmi A hannu. Kacigaba da Rainamun wayo tsaka wannan lokacina ne na Ramawa. Rasa Abinda zaicema inno yayi. ga feenah data Shigo yanzu gaba daya hankalinshi ya kasu biyu. bangare guda na Xuciyarshi yana tunanin. ya Akayi inno taga Mufeeda ta fita daga part dinshi? Lallai daman tarani takeyi tabbas idan tafadama Abba Cewa mufeeda naxuwa wajena babu Abinda Zai hana ya yarda tunda wai har Inno ta iya daukan mufeeda pic a yar Nokia dinta. bangare guda gaba daya feenah ce tarikitar mishi da tunani ganinta kadai yasashi jin Wani yanayi. Wani irin SO nakema yarinyar Nan? Nifa banma gama yarda Cewa Sonta nakeba, ina ganin tausayinta ne Yamun yawa haka...... Feenah ce ta katseshi. Inno this is d last time dazan miki honing Kan kidaina Shiga harkata, Shi wanda yazo yacemiki yana Sona gaya miki nayi Ni inason Shi? Kawai kinaji da tsufa duk kibi Ki damu mutane. kuma Kije kisan yanda Xaki kisa Ajanye maganar aurena da Wanda bansanshiba. Kinji Nafada Miki karashe maganar feenah tayi Tana karkadama inno hannu. Tana gamawa tayi hanyar fita. Yazeed da tunda feenah tafara magana yazubamata ido gaba daya ta tafi da tunaninshi. tabe baki Inno tayi babu Wanda zesani Chanza maganata. Auren kauyene dole kiyi tunda Ummaru daga kauye yazo ya Auri Hafsat. kaikuma tsaka dallah fita kagaban Waje. Jin shiru beyi Magana ba yasa ta dago kai. ..Sakin baki tayi ganin inda yazeed yake kallo. Tohfa dama Wannan Shi ake kira suman tsaye? Hannu takai saitin idonshi tana kadawa. Firgit yazeed yayi miye haka inno? tsaka kai Zantambaya miye haka, tun dazun tafita baka saniba kayi Suman tsaye, Al'Quran kaban tsoro chanake mutuwar tsaye ma Kayi. Mtsww cemiki nayi Dan Ita Nake kallon kofa Toh? danwa kake kallo Toh? ai duk da baka juyaba Sai yanxu. Akwai Abinda nagani ne yazeed yafada lokacin dayabi Hanyar Fita. dariya inno tayi Xaka gane bakada wayo Ai go
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
YAR LESBIAN CE
πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’–
By
Nadeeya mohd Ahmad
(πŸ’–NADSEERπŸ’‹)

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

Page...61


Wata daya da Abba yasaka Bikin Leemah da Nazir. Masoyan jinsu suke kaman Sukara jawo lokacin. bayan wata Shakuwa data kara Shega tsakaninsu harda kulawa ta musamman dasuke Samu wajen iyayensu. Matsala daya ke damun Leemah yanda feenah gaba daya Ta daga Hankalinta Kan Auren kauyen daza'a mata. tun Leemah nabata hakuri har tagaji tayi Shiru. yazeed yanzu bashida Aikinyi wanda ya wuce tunani. Dan kusan yanzu Adaki yake huni, wajen Aiki baya kula kowa dukdan Sabida Auren da Abba yace Zai Mai. tun Mamy namai fada Kan yanda yadamu har tadawo tana tausaya mishi. Ganin yanda Dan nata yadawo lokaci guda. Ibadar dayakeyi ada yanxu duk yabari. Sallahr farila daker yake kawota bare Aje Ga Nafila. gaba daya Rayuwarshi ta Chanza game da Auren daza'ai mishi, bangare guda Ga wani irin Son feenah dake kara dawainiya da Zuciyarshi. Saidai bayanda Zaiyi tunda yanaji yana gani Xa'a Rabashi da Masoyiyarshi. tunanin dayake huniyi Kenan dan haka gaba daya ya hana kanshi Sukuni. feenah bangarenta hakan ne kusan huni take Adaki tana kuka, Acewarta Anya Sonta Ake Xa'a Aurar da'ita A kauye! tunda data nuna tanason Auren ba'a mata ba sai yanxu ne Zasu Auramata wanda batama Sanshi ba. Me yasa bazasu jira har Zuwa lokacin da Xata Samu wanda take So ba? Sake sakenta kenan, kullum mum Cikin lallashi take Amma kamar kara Xugata take. Ko'ina ta daina fita duk dan Ace Anfasa Auren Amma kamar kara zugasu take. dan Shirye shiryensu kawai Suke, inda Mamy tasamo musu mai gyaran jiki, duk dacewa bikin da Saura. bangaren Kausar da Yusuf Soyayya sai abinda yaci gaba dan gaba daya kulawa ta musamman Sukeba junansu. Yauma Kausar ce kwance ta daura kanta a Cinyar yusuf tana Zuba mishi Shagwaba, yusuf Sai faman lallashinta yake Kasancewar 1week kenan tana fama da Rashin lafiya. Sorry my Wife kici kadan kawai bada yawa ba! Um"um ni banason ci nakoshi Yusuf. Me yasa kikace namiki Zakici kuma? dazun Naji inaso ne yanzu kuma Na koshi. hancinta Yusuf yaja Nidai kici kadan. Shgawabe fuska tayi dama kace yau Xaka Nuna min result dina. Murmushi Yusuf yayi yes Xan nuna miki Anjuma.pls kanuna Mun yanxu Nidai. dariya ta bashi yanayin yanda tayi maganar. tashi yayi ya dako back dinshi. Wata paper yaciro yana murmushi. Albishirinki! goro Kausar ta fada Cikin kosawa. Wani kalan goro? da Sauri tace fari. dariya Yusuf yayi ya mika mata paper din. budewa tayi ta fara karantawa lokaci guda ta tashi daga kwancen da take tana kallonshi da Alamar tambaya. ido ya kashe mata "you have a 2months pregnant" koh? da Sauri Kausar ta fada Jikinshi da gaske ne Abinda nagani Yusuf?? Shafa bayanta yusuf keyi lokacin daya fara fadin yes d gaske matata takusan tazama Mum. Kara Rungumeshi tayi i Am happy hubby. Kice Alhmdllh my Wife. Alhmdllh kausar tafada. Rungumeta Yusuf yakarayi yayin da yashiga Kwararo mata addu'an Sauka lfy da Samun Zuri'a mai Albarka. Hubby kuma Sam ban san inada Ciki ba har 2months ko Amai banayi. Hancinta yusuf yaja ai Haka Akeso habibti. Amma bazan fadama Su feenah ba! Why? Surprising dinsu Xanyi Saidai kawai Suga na haihu. dariya yusuf yayi Sosai, Ai da kanshi babyn Xai tonaki idan ya girma. bazan bari yafito ba ai. dariya yusuf yayi Cikin Ranshi yace lallai haryanzu Kausar yarinya ce. Zomuje nafada miki yanda Xakiyi kada Su gane. tashi Kausar tayi tabi bayanshi Zuwa bedroom dinshi. Janta yayi kan bed ganin Abinda yake shirinyi yasa ta Shagwabe face Nifa banda lfy kasani. Jawota Yusuf yayi jikinshi Sorry. toh ka fadamun mana. Kawo kunnanki kiji oya. mika face dinta tayi Yusuf yayi Sauri kama lips dinta kissing dinta yafara Ahankali, tun tanason hanashi har Sakon yafara isarmata Dan haka tashiga tayashi.

yau tunda Asuba mufeeda tashiga Shirin fita. Dan haka tana gama Shiri ko kallon Seemh d khady dake bacci batai ba ta fita. Motar Seemah dake Harabar gidan Nasu tashiga tajaaa da gudu. tafiyar mintina30 tayi Zuwa wani kauye dake gaban kd Kafin Akai Zaria. parking motar tayi a bakin titi Inda ta tari Machin domin yakarasa da ita Cikin wani daji. Nan ma ba karamin tafiya Sukai ba. Saida Suka kusa karasawa wanda ya dauketa yafara mata magana. Hajiya Gaskiya tunda kikazo wajen bokan nan bukatarki tagama biya! Allah Ko bawan Allah? Allah kuwa Nake fada miki Hajiya duk matar Dana dauka nakawo Nan da farin Ciki take fitowa. lallai kace yau natako sa'a nima Wata kawata tamun kwatancen Nan din. Ahhh Gaskiya kawarki yar gari ce Ai yau nake fadamiki kishiyarki Zatabar gidan. Uhum bama wannan ya kawoni ba Malan. Sauka tayi, Zaka tsaya Nafito bawani dadewa zanyi ba dan kamaidani titi. Hajiya Ana jirana faaa. Zan Kara maka kudi kan yanda ka daukoni. Ahhh kaji harka jeki kizo Ina Nan. Karasawa Kausar tayi daidai yar wata bukka tana Sallama. tadan juma Awajen kafin katon wani mutum yafito bayanshi da wata mata. Daga ganin matar irin Matan manyan masu kudine marasa tsoron Allah. Wucewa matar tayi tabar wajen. Ke babu ka'idar Sallama Anan wajen.

2 Comments On YAR LESBIAN CE
avatar
kabir-2

12 months ago

Reply

Ina godiya da kasance tare daku

avatar
daiy

12 months ago

Reply

Replying to kabir-2

Aha muma muna godiya da kasancewarka a shafinmu

Please Login or Register in order to submit comment