Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu taci gaba da bokon nn don dai kam koda kuskure bata son ta sake zuwa d'akin man bare har yayi galabar sake cutar da ita.
Tana cikin hkne taji qarar bud'e gate ta tashi a hnkli ta yaye labulen windonta ta hango motar man ce ta fita ta saki labulen tana mae tunanin idan har zai barta ta koma school in ta gyara mae d'aki ,gwanda kawai tayi sauri taje ta gyra mae kafin ya dawo nn ta kalli mami dake kallon tom and jerry tace"mami muje ki rakani a d'akin yayanki sae ki kunna kallon ki a can kinji"
Ba musu mami ta tashi suka je Rynt ta gyare koina tsaf cikin en mintinan da basu fi 30 ba wacce har ta gama gyara d'akin gabanta na dukan uku uku.
Tana gamawa taja mami suka koma d'aki.
Sae bayan awa 1 da komawar su d'aki ne taji qarar bud'e gate ta tashi ta duba taga motar man ce ta kunno kai.
Byn an parker motar driver ya fito da sauri yaje ganbun baya ya bud'e ya kuma zagaya da sauri ya bud'e d'ayan,nn man da malika suka fito kowannen su d'auke da fara'a a fuskar shi man ya riqa hannun malika suka shiga gida yayinda driver ya bisu da kaya niqi niqi.

Rynt ta saki labulen ta koma ta zauna.

Har sha d'aya na dare Rynt batayi bacci ba sbd jiran ko man zai shigo idan yaga ta gyara mae d'aki amma shiru kmr shirwa ta cinye d'an tsako.
Gashi sosai take jin bacci amma tasan ko ta kwanta bazata iya yinsa ba idan ba taji, ko zai barta ta koma school ba.
Har sha biyu shiru bai zo ba, gata kwance amma fir bacci yaqi d'aukarta sae juyi take, ta kalli gefen mami da tuni tayi bacci abinta ,ta tashi zaune tare da had'e kai da guiwa sae jin tayi an bud'e qofa tayi saurin d'ago kanta yayinda hawaye ke silalowa a hnkli kan kumatun ta.
Man ne ya shigo yayi tsaye a bakin qofa yana kallonta ita kuwa sau d'aya ta kalle shi ta kauda fuska tare da share hawayenda suka zubo mata ya qarasa cikin d'akin yaje kan bedside drawern da ke kusa da Rynt ya zauna snn ya kalleta ba yabo ba fallasa yace"lafiyarki kike kuka da daren nn"
Tace"kace idan na gyara ma d'aki zaka barni na koma school ko"yace"yaushe nayi dake haka? kmr zata yi kuka tace "d'azun kmr hk fa ka nuna min"
A tunanin ki kenan amma ni ba hk bane,ya fad'i hkne tare da kallon fuskarta sae yaga nn take hawaye sun zubo mata nn yaji ta burge shi sosai sbd yanda take son karatu.
ya sauke numfashi snn yace"zan barki ki koma d'in amma fa da sharad'i"da sauri ta kalle shi tace"ina jinka gaya min"
Yace"Duk kika bar wani malami ya sake fad'awa sonki ko wlh bake ba makarantar koma nace gabad'aya bokon don ba kud'in banza nake dashi da zan kai ki karatu kije kina soyayya ba idan kuma har kince soyayya zakiyi ni kinma hutar dani kuma kin hutar da kud'ina don sallamar ki zanyi ki koma can gidan inna da taji zata iya.
Rynt ta sauke ajiyar zuciya tace" naji zan kiyaye,yace"idan ma kin kasa kiyayewa wa kanki,
Nn ya fita tayi hamdala wa ubangiji ta kashe wutar d'akin ta kwanta.

Washe gari da taje school wata qawar ta da suke shiri sosai take ce mata
"bari Rynt yanyanki yayi wlh don naji dad'in da yasa aka kori malam a shaqata daga mkrntr nn shikenan yanzu mun huta da muguntar shi"
Rynt tace"hm korar sa yasa akayi?au bai gaya miki bane? tace"um um"
Hm bari kedai naso ace rnr Friday d'in nn kinzo wlh don qaramin yaqi aka tashi yi a makarantar nn dmn en sanda fa yayanki ya kiro mishi yace a tafi dashi sae da qyar principal ta shawo kan yayanki a cewar yayi hqr kar yasa a kama shi zata sa ayi mai transfer zuwa mkrntr maza don dama ta jima da jin wasu halayen shi maras kyau da ake fad'i.
Rynt ta kalli qawar ta tace"to a bakin wa yaji cewa bana sa niqab hln?tace"gsky ban sani ba kawai dai munji hayaniyar fad'an su ne"
Qawar tace"amma yayanki yayi aure ko? Rynt tace"eh"
tace"kai amma fa ko waye matarsa tayi sa'ar miji kuma kema kinyi sa'ar yaya"
Ta6e baki kawai Rynt tayi ta jawo littafinta tana dubawa sbd haka take ko yaushe ko ba test idan dai basa komai a aji ,bazatyi strn banza ba sae dai ta jawo littanfanta tana karatu.

5:00pm
Rynt ce da mami sun dawo daga school suka sami malika da mohd zaune a falo ,malika nata zubawa man kukan shwaga6a wae ita yunwa takeje bata iya cin abincin kuku don ko warinsa bata son ji.
Tana ganin su Rynt sun shigo tace"yauwa my man kasa wnn abar ta dafa min abinci wata qil ko zan iya cin nata.
Rynt na jinta taji sa6o ma take bata dai kula su ba tayi ficewar ta ita da mami.
Shi kuwa mohd kmr ma ince tare suka shigo d'akin shida su Rynt ,
Ya kalli rynt dake qoqarin ajiye school bag yace "ke yi sauri ki cire uniform kije ki d'aurawa malika abinci"
Rynt ta ta6e baki tace"hm wae sa6o idan bazata d'aurawa kanta ba ai sae ta zauna da yunwar"
Yace"bana son raini wlh maxa ki cire uniform kije ki d'aura mata girki "
Tace"wae ya zaka ce na d'aura mata girki wane irin ma rashin tausayine ynx daga dawowata daga mkrnta"
Yace"haka zaki ce to bari kiji idan har kina son ci gaban karatunki to fa lallai sae kinyi abinda nake so wlh"
Tace"naji amma bafa zan d'aurawa qatuwar banza girki ba"
Yace"well ya rage naki idan kina son ci gaban karatun ki kije ki d'aura mata girkin idan kuma ba kya so ba dole sae kiyi zamanki.

```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```42```* and 43
Yana gama fad'ar hk ya fita.
Wani irin baqin ciki ne ya tokare Rynt a wuya da har ta sami kanta dajin qwalla sun cika mata ida bata dae bar sun zubo ba ta ajiye school bag ta cire takalmi da socks takai su inda ya dace snn ta fito downstairs ta wuce su man zaune a falo ta tafi kitchen ba tare da tako kalli gefen su ba.
Malika tace"matsiyaciya ai da na d'auka ko bazata fito ba"
Man yace"dolenta mana tunda tana son ci gaban karatun ta.
malika ta tashi tare da fad'in "bari ma naje naga wane d'an iskan abinci ne take da niyyar dafa min.

Rynt kuwa tana shiga kitchen ba abinda tayi niyyar dafawa sae indomie har ta d'aura c pot ta zuba ruwa sae ga malika ta shigo ta kalli Rynt a yatsine tace"ke matsiyaciya me kike shirin dafa min ne "Rynt tayi banza da ita ,malika tace"idan kin iya kar ki bani amsa amma wlh ina mae gaya miki kar ki kuskura ki dafa taliya ko indomie,sakwara zaki min da miyar agusi"
Still dae Rynt bata tanka ta ba har ta fita taje gurin man cikin masifa tace"wae da yrnyr indomie na samu zata dafa min don ta rainani"
Yace"wae da to me kike son ta dafa miki? Sakwara mana da miyar agusi,ya kalleta yace"amma kinsan tana da lesson 5:30 to six har yaushe ta gama,da dai kin barta kawai ta dafa miki indomie d'in, kallon sa tayi tace"ban gane ba tausayinta kake ji ne ko yaya?
Yace"ko d'aya mae lesson d'in ne bana son ta 6atawa lokaci"
Tace"to ai sae a farawa mami idan ta gama min girkina sae a mata"
Yace"ok"

Suna nn zaune cikin en mintina sae ga Rynt ta fito riqe da plate d'in indomie takai kan center table d'inda ke kusa da su ta ajiye ta kuma yi ficewarta.
malika ta bita da ido sake da baki snn ta kalli man da ya gama waya knn
tace"kaga er iska indomie d'in fa ta dafa min"
Ya tashi tare da fad'in "bari ina zuwa"
Yaje ya sami Rynt tana shirin shiga bathroom tayiwa mami wanka ,
ya dakatar da ita cikin cewa"ke zo nn "bata je ba sae kallon sa da tayi yace"me malikà tace miki ki dafa mata? tace"sanin kanka ne ban iya wnn abincin ba don ni abu biyu kawai na iya dafawa daga taliya sae iñdomie....bana son raini da kike dafawa a gidàn inna fa?
Tace"Bani ba kam sae dai ko baba hurera"
kallonta yayi kmr zai ce wani abu sae kuma ya fasa ya fita, Rynt ta ta6e baki ta bishi da ido wacce ba klr abincinda bata iya ba a gidan inna qin yine kawai tayi.
Taja hannun mami dake fad'in"wae anti meyasa anti amarya yau tace bata cin abincin kuku? Rynt tace" oho mata kedai muje ayi wanka muci abinci kafin mae lesson yazo ko"
Mami tayi murmushi dan da murmushi Rynt tayi mata mgnr,
wa enda tuni sun shigo bathroom sae ruwa Rynt ta had'a tayiwa mami wanka byn ta gama mata mami ta fita ita kuma tayi nata.

Mohd kuwa koda yaje ya snr da malika cewa Rynt bata iya wnn abincin da tasa ta ba sae masifa take ita lallai sae Rynt tazo kuku ya nuna mata yanda ake don ita kam baza taci indomie ba da qyar man ya samu ya lalla6ata har ta yarda taci indomie a cewar gobe sae Rynt ta dafa mata duk abinda take so.

Rynt tana fitowa wanka sharp sharp ta shirya suka ci abinci sae dai koda suka gama har sun shigo cikin lokacin lesson d'inta tayi saurin kwasar littafanta ta tafi ta samu kuwa har mai lesson d'in yazo yana jiranta.
Wnn karon man baizo ya fake kmr ko yaushe ba don yana can shida malikarsa a d'aki.
6:00 ake gama mata lesson d'in sae ya farawa mami ana yin magrib ake gama mata ita kuma.
But rnr Thursday ,Friday Saturday and Sunday suna samun enuf time da ake yi musu lesson bcs thursday 2:00 ake tashi friday 12:00 then asabar da lahadi islamiya ce 8am suke zuwa su dawo after 2 yayinda duk ranakun nn hud'u da qarfe hud'u lesson tearcher d'in ke zowa bashi yake barin gidan ba sae anyi magrib.

Bayan 2 dayz duk kwanan nn biyu Rynt ke dafawa malika abinci idan sun dawo daga school amma ba wani abinci bane face indomie wacce take silalawa sama sama takai ba tare da ta damu da ta nina ko bata nina ba.
Gashi kullum malika sae masifa take yiwa man ita tgji da cin indomie a kira kuku ya nunawa Rynt kallolin abinci ta riqa dafa mata,Man kuwa sae rarrashinta yake yana lala6ata sbd hk kawai yaji baya son kuku ya koyawa Rynt abinci inda dae mace ce.
Rnr dai ta matsa mai kan dole ya kira kuku suka sami Rynt a kitchen ,man ya dakatar da Rynt dake shirin d'aura indomie snn yace da malika"me kike son ta dafa miki ?
Nn ta shiga shafa cikinta a yangace snn tace"inaga yau jellop rice muke ra'ayi nida babynka amma taji busasshen kifi da manja a kuma zuba ganyen alanyafu snn ayita da yaji sosai"
Yace"shikenan abinda kk so? Tace"eh ni zanje na kwanta na huta nagaji da tsayuwar nn yace"ok"snn ta fita nn ya maida dubansa gun Rynt yace"oya ga kuku nn zai nuna miki komai yanda zakiyi".
Kallon sa kawai tayi snn ta kalli kuku shi kuma man ya nemi kujera ya zauna yana duba jarida.
Kuku yazo gaban Rynt ya had'a komai da za'a sa a jellof d'in snn ya d'ura c pot ya zuba manja a cewar idan ya d'auko zafi sae ta saka niqaqqin tattasai da albasa da tarugunda aka niqa sama sama bayan en yankakkin da ke ajiye gefe da sae jellop d'in ta d'auko dafuwa xa'a saka su.

Hanklin kuku nakan busasshen kifin da yake d'an qara gyrawa yayinda Rynt ke kallon manja har yayi mugun zafi ,ta d'auko kofin ruwa kai tsaye ta kwara cikin manjan,
baaa! belar wuta ta fito tayi sama! ai kuwa Rynt ta buga ihu da ita har kuku ba mae kama wani sae qoqarin 6ira suke su fad'i wanda tsirif ya rage Rynt ta fad'a kan jikin kuku man yayi saurin tashi ya fizgota zuwa jikin shi,
Yayinda cikin mugun 6acin rae man ya kalli rynt yace"u are very stupid! ke ba kya ganin inda zaki fad'a ne!
Ta rufe ido gam had'e da fashe mai da kuka wacce da gayya ta zuba ruwan amma tayi mugun tsorata da ganin yanda wutar ta fito a manja, dan ynz hk jikinta sae qyarma yake.
Man kuwa ganin yanda Rynt ta rufe idanunta sosai tana kuka ,ya d'auka ko manja ya shiga mata a ido nn yakai hannu zai bud'e ya hura mata idon amma taqi yarda sae tsalle take tana kuka bayan ba abinda ya shiga mata a idon pretending ne kawai don ta samu ta zillewa girkin.
Da hk ta qirqiro tari tana tayi se duk Man ya damu ya rasa yanda zai mata ya kalli kuku cikin daka mae tsawa yace"dan Allah qaton banza tashi kaje ka kashe wancan abun duk yabi ya damu mutane!
Da hnzari kuku ya tashi yaje ya kashe gas cooker,
man kuwa yaja Rynt har zuwa d'akinta wacce sae tari take ga kuma idanuwanta dake rufe still .
Bathroom ya nufa da ita ya wanke mata fuska ya ciro farin handkerchief d'insa ya share mata fuska snn ya fito da ita ya zaunar kan bed tana d'an ci gaba da tari kad'an kad'an nn yaje ya tsiyayo ruwa a glass cup ya zauna snn yace"bud'e idonki ga ruwa kisha "
Qin bud'e idon tayi sae hannu takai tana lalube sae jin tayi yakai cup d'in ruwa a bakinta tasha ruwan kad'an ta kwanta shi kuma yasa blanket ya rufa mata jikinta ya fita sae a snn Rynt ta bud'e idonta a hnkli tare da saurin yaye blanket ta tashi ta watsa da gudu bathroom sbd fitsarin da yayi mugun matsar ta.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2/4, 9:46 PM] ‪+234 703 962 5239‬: [2/4/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮
*page* *```43```*
Mohd kuwa d'akin malika ya nufa ya sameta kwance kan bed sae chat take tana qyalqyatar dry.
Ya zauna kusa da ita
ta mirgino tayi pillow da cinyoyinshi tana ci gaba da chat d'inta,ya kar6i wyr yace"wnn yrnyr fa in banda shirme ba abinda ta iya kawai kiyi hqr na nemo wata yrnyr da zàta riqà mana girki shi kuma kuku ya kama gabansa don ynz sam bana son ina ganin sa a gidan nn, da hanzari ta tashi zaune tare da fad'in"ban gane ba nifa gsky wnn abar nake son ta riqa min abinci don ma ka daina zancen d'auko wata kuma kuku meye mtslr shi, shida ma zai riqa koya mata kalolin girki.
Malika na gaya miki bazata iyaba don in banda shirme da qoqarin qona min gida ba abinda ta iya .
Tace"wae kamar ya ban gane ba?
Yace"baza ki gane bane tunda ba'a a gaban ki ta tafka shirmen ba.
Tace"to ai koma yaya ne yau da gobe zata iya"
Mtsw mohd yayi d'an guntun tsaki yace"malika bana son gardama kin sani, ki bari kawai a nemo maki wata yrny ba dole sae ita ba"
Cikin fushi ta sauka kan gadon tace"wlh gsky ni ita zata ci gaba da girka min abinci idan ba hk ba kuwa wlh sae dai a zubar da cikin nn kowa ma ya huta"
Kmr saukar guduma yaji zancen ya sauka a kunnen shi ya tashi da hanzarinsa ya qarasa gurinta ya riqo kafad'unta cikin mugun damuwa yana kallon fuskar ta yace"malika kinsan me kike fad'a kuwa ,a zubar da cikin nn fa kika ce"
Kuka ta fashe dashi snn tace"eh mana ina son cikin nn amma dole zan zubar dashi tunda baka iya d'aukar lalura ta da duk wani abu da nake so"
Rungume ta yayi yace"is ok naji zata ci gaba da yi miki girkin amma sae abinda ta iya zata girka miki kin yarda"
Ya fad'i hkne yayinda ya d'ago fuskarta yana kallonta ,ta share hawayen funafurcin dake kan fuskarta tace"to ya zanyi my man tunda babynka ya d'aura min lalurar son cin abincinta,amma kuma gsky yau bazan ci indomie ba sae dai ko fita zamuyi a siyo min gasasshiyar kaza na d'aura da hollandia milk"
Yace "to ai wnn mae sauqi ne shirya muje"
Tace"ai a shirye nake mayafi kawai zan d'auko nn taje ta ciro mayafi ta yafa suka fita.

9:00pm
Rynt ce kwance cikin tunanin anya ko za'a maida mami kuwa sbd yau suna dawowa school abinci kawae suka ci aka kai mami gida.
Tana cikin hkne taji qarar bud'e qofa tayi saurin kallon qofar don a tunaninta ko mami ce sae taga man.
A bakin qofa ya tsaya yana tmbyrta mami fa?
tace"ka manta tana gida"
Agogon hannusa kawai ya kalla ya juya zai fita Rynt tayi saurin katse shi da cewa"don Allah idan d'auko ta zakaje zan bika"
wani kallon kin raina ni ya mata snn yace"me zakije yi a gidan ?tace"zan gaida su mama ne na jima banje ba wlh"
Yace"shikenan ki same ni a waje idan kuma kin jima zaki samu bana nn"
Yana fita tayi saurin zuwa ga wardrobe ta bud'e ta nemo wata doguwar rgr atamfa ta cire riga da wandon baccin da ke jikinta ta saka ta nemo hjb ta fesa turare tasa snn ta d'auko takalmi tasa ta fita da sauri har tana hard'e qafafuwa.
Koda taje har ta samu ya tada motar shiga kawae tayi yaja suka tafi.

Suna isa gidan 6anfaren su mohd suka fara nufa ,ummar sa suka samu zaune a falo sukayi sallama sae kallon su tayi ba tare da ta amsa ba,har qasa Rynt ta durqusa tana gaida umar tashi wacce ta watsa mata muguwar harara Rynt ta tashi abinta zasu bar 6angaren da ita hr man da shima ya gaida ummar tashi bata amsa ba.
Lokacin da suke qoqarin fita ne Abba ya sauko nn downstairs Rynt na ganin shi tayi saurin durqusawa tana gaida shi, ya amsa da fara'ar sa yana fad'in"yau kune a gidan "
Tace"eh Abba"
Yace "to ya gida ya karatu tace"duk Alhmdlh"
Byn nn ne man ya gaisa da Abbanshi snn yace"mu zamu tafi Abba dama mami ce muka xo d'auka "
Nn Abba ya ciro 5k a aljihu ya bama Rynt wacce taqi kar6a har sae da qyar Abba ya samu ta kar6i kud'in tayi mai godiya snn suka fita.

Tare suka je 6angaren su saliha mami na ganin su tazo da gudu ta riqo hannun kowanen su.
Umman mami har Abbanta duk suna nn zaune a falo nn su Rynt suka gaida su man ya fita a cewar yana jiran su a waje,da yake mami a shirye take sae bin yayan nata tayi, hkn yasa itama Rynt ta tafi zata bisu umma ta kirata suka tafi d'aki.

Turarukka ne masu qamshi umma ta bata da kuma kayan kwalliya wad'anda dama a tsare suke cikin ledar su da aka yo shopping tayi niyyar bawa mami ne ta kai mata sae gashj taxo.
Rynt ta kar6i ledar tana yiwa umma godiya,,umma tace"ai inshaAllh kwanakin zan zo gidan naku"tace"to mama sae kinxo"
Har Rynt zata fita umma tace"af na manta fa rnr da mukaje visiting akwai wani saqo da saliha ta bani tace na baki har ma tace tana gaida ke,Rynt tace"Allah sarki mama bata ce dake fushi take dani ba?
um um ko d'aya kawai dai ta shiga damuwa sosai dajin kinso zowa mohd ya hana,Rynt tace"hln inna ce ta gaya mata ko"
Mama tace"eh kam don inna sae fad'a take tayi ganin har za'a tashi visiting baki zo ba,don tace mana har zaku shiga mota mohd ya same ku yace mata su su tafi wae zai kaiki daga baya"
Rynt tace"Hm hk yace mata mama"
Mama tace"to ko meyasa yayi hkn kuma sae bae kaiki d'in ba, koda yake hln mohd sae shi.
ta fad'i hkne tare da d'auko wata er qaramar leda tace"kinga saqon amma kuma ban san ya akayi ledar ta yage ba, bari na cire nasa maki a cikin ledar kynki.
Nn mama ta ciro kayan ta saka a cikin ledar turarukka da kyn kwalliyar da taba Rynt,Rynt tayi godiya tafita tana sauri don tasan man ya gama suqewa da jiranta.
koda tazo sae fira ma ta samu sunayi shida mami a cikin mota.
Tana shiga ya tashi motar suka wuce.
A maimakon yaje dasu gida sae wani babban mall ya tafi dasu.

Shida mami kawai suka shiga suka bar Rynt cikin mota.
Chocolate, biscuit,sweet n drinks ne suka siyo wato kayan mami da ake d'ibar mata tana zuwa school dasu.
Bayan su basu riqo komai ba sae ice cream .

Tun a mota mami ke shan ice cream d'inta wacce koda suka iso gida ta shanye har tayi bacci.
Da suka iso gida man ne ya d'auki mami da tayi bacci,
Rynt kuwa kyn hannunta kawai ta d'auka ta shiga cikin gida shi kuma man kuku ne yazo yana jidar kyn da suka siyo yana shigar dasu.

Rynt da shigarta d'aki ta d'auki kyn baccinta ta nufi bathroom ta saka ta fito linke da wad'an da ta cire taje ta saka a wardrobe taje ta kwanta sbd wani irin bacci da take ji .
Sae a snn man ya shigo ya shinfid'e mami yaje ya shigo da kayayyakin da suka siyo.
Yakai ledar ice cream kan bedside drawer ya ajiyewa Rynt nn idonsa ya qyalla kan ledar Rynt dake ajiye a gun.
Har zai wuce sae kuma ya tsaya yana kallon farin abinda yake hangowa ciki,
kai tsaye yakai hannu ya ciro kyakkawar sabuwar farar bra da kuma farin pant,ya cira kyn sama yana kallo yayinda Rynt ta rufe idonta cikin mugun jin kunya wacce kwata kwata bata lura da sune mamar saliha tasa a ciki ba duk a tunaninta farar vest ce saliha ta siyo ta aiko mata.
mohd ya ajiye kyn snn ya kalli Rynt da taqi yarda ta bud'e idonta yace"dama don kije ki roqo wasu kayan ne yasa kika bini"
Bata bud'e idon ba sae cewa tayi"Allah sauwaqe ni wlh roqo ba halina bane"
Yace"ok idan har baki akayi to meyasa kika kar6o byn duk tulin irin kyn nn da kk da su a cikin akwatinanki ko kuma kina nufin kaf kin murje su"
Komai qin ce masa tayi hkn yasa ya tafi sae gurin akwatinan ta ya bud'e wacce undies ke ciki ,
komai na ciki ba abinda tayi aiki dashi sae qwarorin vest da pant amma kuma se duk baiga bras ba sae wata babbar farar leda ya gani da qunshin kayanda bai san meye a ciki ba, bud'e ledar yayi ya zazzage kaf abinda ke ciki ga mamakinsa sae yaga duk brasseries d'in ne ba wacce aka ta6a, nn yaje ya jawo Rynt yazo da ita gurin akwatinan ya nuna brassieres d'in yace"uban wa kk son ya saka wad'an nn kyn da har yazun ba alamar ansa ko d'aya!
Komai bata ce masa ba asalima ko gefen akwatinn taqi yarda ta kalla sbd bra na d'aya daga cikin abinda Rynt tafi kunyar gani sosai.
Mohd kuwa tsawa ya daka mata yace "wae bada ke nake magana bane!
Kmr zatayi kuka ta kalle sa tace"to ai ni ban fara sawa ba nayi qanqanta"
Qirjin ta ya kalla tare da fad'in"what!sae kuma

Please Login or Register in order to submit comment