Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dmn naga a cikin labarinki anwar kad'ai ne d'an birni kuma kince lfy kuka rabu dashi asali ma in rashin mutnci ne ai d'an qauyen naku ya muku wato bala da yasa kuka koma daji da zama,ko kuma kin 6oye min wani abu a labarinki ne?idanuwan Rayyanat tap da qwallah take kallon saliha tace"Saliha ki daina min tambayoyi haka don Allah"
Saliha ta nisa tace "shike nn amma ga dukkan alamu ba duka kika gaya min labarinki ba"shiru Rayyanat tayi dmn tasan tabbas bata snr da saliha dalilin mutuwar Baffanta ba kawai dai tace mata ya rasu.
Tace"hm saliha ki yarda dani mana ni ban rage miki komai ba a labarina ba,kawai dai bana ra'ayin soyayya har da d'an qauyen ma dmn tunda yaya anwar ya mutu naji bazan iya soyayya da duk wani d'a namiji ba wnn alqawari ne nayiwa kaina dmn inaji idan na kula wani tmkr nayiwa yaya anwar butulce ne.
Hm Rayyanat kenan kina nufin haka zaki tabbata ba aure, d'an guntun murmushi Rayyanat tayi snn tace"To ce maki akayi rayuwar tawa tsawo ne da ita nida ma nake roqon Allah yasa rayuwata zata kai ga na cika burina" hm har akwai wani buri a gun 'ya mace da ya wuce aure? Kallonta kawai Rayyanat tayi ta kauda kanta,snn tace"inada wnn burin amma a da wato kafin yaya anwar ya mutu.
saliha tace"nidai Rayyanat al'amuranki na bani mamaki rayuwar ki idan mutum ya kalla kmr so simple n easy amma ashe in kika dake kan abu kin dake
kenan.
Ba hk bane saliha yaya anwar yana da matuqar muhimmancin da bazan iya kula kowa ba.
Cikin nuna 6acin rai saliha ta tashi tace"tunda haka kikace shikenan shi kuma yaya munir Allah ya bashi wacce ta fiki da komai ma"
Nn ta fito falo ta sami mohd zaune yana cin abinci ya tsare ta da ido kmr wani mai tuhumar ta,ta sadda kanta qasa tare da gaida shi snn tace da Ameera tashi muje gida ,nn ta tashi sukayi wa inna sallama zasu fita mohd ya kira saliha tare da zaro kud'i a aljihunsa,
saliha taxo cike da ladabi,
Ameera kuwa ta biyota cikin rawar kai ,
mohd ya dalla mata harara yace"bana son shisshiga fa ke na kira ko saliha"
kmr zata yi kuka tace"saliha"
Girgiza kansa kawai yayi had'e da d'an guntun tsaki don ko kad'an baya son hali irin na Ameera nn ya miqawa saliha two thousand a cewar suyi kud'in a daidaita tayi masa godiya suka wuce.

Bayan ya kammala cin abinci yaje d'akin inna zai mata sallama inna dake zaune tana lazimi tace"yauwa d'an albarka yanzu nake qoqarin tashi na same ka,sbd ina son zamu yi wata magana mai muhimmanci da kai,a natse man ya zauna kan gefen gadon inna yace"ina jinki inna".

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

3/1/2017

🔮```17```🔮
Muhammadu tafiya nake son zanyi a cikin satin nn zuwa qauyen mu dmn na jima rabona da zuwa shine nake son zan kai Rayyanah a can gidan ku har idan na dawo.
A natse mohd ya d'ago yana kallonta snn yace"shike nn inna amma kinyi magana dasu Abba kuwa.....Yo sae da izinin su zanyi tafiyar ne ko kuwa Rayyanah d'in ce baka son ta zauna gidan naku! Ba haka bane inna sanin dai nayi tafiyar ki idan kika yita sae wanda ya ganki,inna ta washe baki tace"ayyo ai muhammadu kasan en uwa dad'i ne dasu shiyasa nake d'an jimawa idan naje.
To inna wace rnr zaki tafi? Eh to rnr laraba nake son na tafi in Allah yaso,to Allah ya kaimu lokacin inna, Amin Amin d'an Albarka.
Tare suka fito shida inna ta nufi d'akin Rayyanat shi kuma ya fita daga gidan.

Zancen tafiyarta ne taje ta snr da Rayyanat ta fita ta bar Rayyanat cikin rashin jin dad'i da tunani sae take jin kmr kar inna tayi tafiyar nn ba don komai ba sae don sabon da tayi da inna.

Bayan kwana uku da faruwar haka cikin ikon Allah ynx munir ya fara shawo kan Rayyanat dan yanzu har tana d'an tsayi ta saurare shi.

Ko yauma tafe suke ta dawo daga islamiyya sae janta yake da fira ita dai iyakarta murmushi da kuma wasa da en yatsunta.
Har qofar gida ya rakota tana shiga gidan sae ga Muhummad ya fito zai tafi masallaci dan har an fara kirayen kirayen sllr magrib.
Cikin sakin fuska munir ya miqa masa hannu suka gaisa inda shaye da toka man ya zare hannun sa daga na munir ya wuce, munir ya bisa da murmushi dmn inda sabo ya saba da halin abokin nasa.
munir yaje ya nemi buta yayi arwala ya shiga masallaci sbd dama masallacin kusa da gidan yake .

Rayyanat kuwa tana shiga gida ta cire hijab, niqab da socks, ta jawo er akwatin ta da inna ta saya mata,ta ciro kayanta a wardrobe tana tsarawa da yake fashin sallah take shiyasa bata yi zancen sallah ba.

Komai da tasan zata buqata sae da ta zuba a ciki snn tayi zaune tana tunanin yanda zata yi rayuwa a gidan su man ,
sae roqon Allah take a ranta kan Allah yasa 6angaren su saliha zata zauna in hkne kam da sauqi.

Guraren qarfe takwas da rabi zaune suke a falo ita da inna suna cin abinci suna kallo inna tace"Rayyanah ina ce kin harhad'a kayanki dan kinsan na gaya miki sammako zanyi shiyasa ma na sallami baaba hurera tun yau, eh inna na harhad'a komai tun d'azun, tayi mgnr ne a sanyaye,inna kuwa ta washe haqora tace"to Allah miki albarka 'yannan idan kinje ki sakin jikin ki sosai don tamkar gidan ku ne kinji, Rayyanat ta gyad'a kanta wanda yayi dai dai da shigowar nasir d'auke da sallama a bakin shi,
inna ce ta amsa masa sallama, Rayyanat kuwa ta gaida shi cikin ladabi snn ta d'auki kwanon tuwonta ta shiga daga ciki.
Nasir kuwa bayan ya amsa gaisuwar Rayyanat ya gaida inna wacce ta amsa gaisuwar washe da baki snn tace"ka dai ji zancen tafiyar tamu yanda na snr da kai a waya ko, eh inna inshaAllah tunda sassafe zaki ganni,tace "amma fa ina son sae mun sauke Rayyanah a gidan naku, eh inna ai duk kin snr dani hk a waya.
To ya jikin Fatima da sauqi dai ko, wlh Alhmdlh inna taji sauqi sosai don harma tana cin abinci yanxu, to madallah Allah ya nuna mana ta sauke abinda ke cikin cikinta lafiya ,Amin amin inna.
Daga haka suka ta6a er fira ,
guraren tara da rabi snn ya wuce.

Washe gari tun da safe nasir yazo ya kwashi inna da Rayyanah suka tafi gidan nasu, inna taje kowane 6angare ta musu bankwana wacce duk 6angaren da taje tana riqe da hannun Rayyanah har saida tazo gun mota zata shiga snn ta saki hannun Rayyant tana mata sae ta dawo.
Su inna na wucewa Rayyanh ta ajiye kuka amma marar sauti,mohd dake tsaye sae kallonta yake don ya fahimci ba qaramar shagwa6a Rayyant zata yi ba.
Shida kanshi ya ja mata akwatin ta suka tafi 6angaren su,yana tafe Rayyant na bayanshi har suka tafi d'akin Ameera,sae da ya kalli Rayyanat ganin har lokacin kuka take snn ya kai hannu a hnkli ya fara qwanqwasa qofar.


Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

4/1/2017

🔮```18```🔮
Ya jima yana knocking snn aka bud'e qofar,wani mugun kallo ya watsa ma Ameera wacce ta fito cike da jin bacci sae miqa take ,tayi saurin daina miqar ganin kallonda yayanta ke mata, kmr da tsoro tace"yi haquri yaya ina bacci koda kake ta qwanqwasa min,bai ce da ita komai ba sae akwatin Rayyanat ya miqa mata tare da fad'in"ki ware mata gurin da zata saka kayanta a nn zata zauna har sae inna ta dawo.
Ba musu ta kar6i akwatin ta shigar da ita mohd kuwa ba tare da ya kalli Rynt ba yace"shiga daga ciki idan kika buqaci wani abu ki snr da ita Ameeran, daga haka ya wuce ita kuma tasa qafa zata shiga dai dai Ameera zata fito sae qunquni take ta bangaji rynt da qarfi har sae da ta nemi fad'uwa bata damu ba don dama da niya tayi snn tayi ficewarta sae d'akin hjyr su.
Ta shiga cikin kuka mai d'auke da shagwa6a tace"umma wlh ni bazan iya rayuwa da wnn yrnyr a d'aki d'aya ba, xaro ido Umma tayi tace"au wai a 6angaren nn zata zauna?eh yaya ne ya kawota wae har sae inna ta dawo daga qauye,ta qarashe mgnr cikin muryar kuka sosai snn ta d'ora da cewa"gsky umma ni d'akin masu aiki zan maida ta dn tafi cancanta a can"Umma ta nisa tace"kinsan hln yayanki ko dukan ki zai iyayi akan haka dn yafi son duk inda ya ajiye abu to yazo ya same sa a nn"uhm uhm umma dan Allah nidai ki masa magana ya sauya mata wani d'akin ai akwai d'akunan baqi ma,to shike nn zan masa magana,nn Ameera ta fita tana mai share qwallah.
Tana zuwa d'aki ta sami Rynt tsaye riqe da akwatin ta ,ta kalle ta a wulaqance snn tace" fita waje ki jira yaya zai zo ya baki wani d'akin, ba musu Rynt taja akwatin ta ta fita don sae ftr take ma a sauya mata 6angaren gabad'aya.
Ta jima tsaye a bakin qofar Ameera kuwa tuni ta shige blanket ta koma bacci.
Ganin ta gaji da tsayuwa yasa ta rage tsawonta bata jima da haka ba sae ga man ya shigo 6angaren cikin shirin sa na fita aiki yayi tsaye da mamaki yana kallonta snn yace"ke ba cewa nayi ki shiga ciki ba shine sbd qauyanci kika yiwa mutane durqushe a bakin qofa!shaye da toka ta d'ago tana kallon sa snn tace"to ai bayan na shiga wnn qanwar taka tace wai na fito zaka canza min d'aki"
Komai bai ce mata ba sae kutsa kai yayi ya shiga d'akin sae ihun Ameera taji ta fito aguje tana kuka awa wacce aka fasawa kai wanda hkn yasa iyayensu suka fito a rud'e ,
ta tafi da gudu jikin umma tana kuka Abbansu yace" lfy me yake faruwa ?Abba yaya ne ya mareni ban masa komai ba, Abba ya kalli mohd da ya fito yace"me Ameera ta maka ne wae? Abba kunfa san hln Ameera ta iya wa mutum qarya da fad'ar abinda ba'ayi ba,shine wae yau har abin ya fara kawowa kaina!nn ya matsa gab da Ameera kmr wanda zai bugota yace"yaushe nayi dake zan canza mata d'aki!dake nake magana ki bani amsa koni sa'anki ne! a razane tace"yi haquri yaya wlh qarya na mata baka yi dani haka ba.....er iska yrny wlh duk rnr da kika qara fad'ar abinda bance ba sae nayi maganinki fiye da na yau, daga haka ya wuce kmr wanda zai tashi sama.
Abba ya sauke ajiyar zuciya yace da Rynt shiga ki ajiye kayanki.
Umma kuwa taja Ameera suka tafi d'aki sae fad'a take mata tana fad'in keda nace zan masa magana me kuma ya kaiki yin haka gashi ynx kin 6arar da komai don yanzu dole ki zauna da ita d'aki d'aya ba kuwa zan nema maki alfarmar sa ba, Ameera dai sae kuka take bata ce komai ba don tasan ta riga da ta jama kanta.

Rayyanat na shiga d'akin ta nemi guri ta ajiye akwatin ta snn ta kalli agogon bangon da ke d'akin qarfe tara da rabi time d'in islamiyya ya tafi don ta makara sae dai zuwa yamma sae duk bata ji dad'i ba hkn yasa ta ciro littafanta tana mita.

Kwana Rynt hud'u a gidan kullum sae Ameera ta nemi tayi fad'a da ita amma tana basarwa duk da tana jin zafin abubuwan da take mata kuwa.
Haka kwata kwata hjy bata sakar mata fuska ko gaisuwa da qyar take amsa mata sauqinta d'aya saliha na zowa suyita fira abinsu snn duk zata je islamiyya Abba ke bata kud'in napep.
Sae dai babbar matsalarta shine abinci wanda sae da kulawar Abba ake kawo mata abinci idan bai kula ba haka zasu barta da yunwa,mohd kuwa kmr ma baya garin don tun daga rnr bata qara ganin sa ba.
Cikin shirin ta tsaf na islamiyya ta fito ta sami Abba zaune a falo ta durqusa har qasa ta gaida shi cike da ladabi ,ya amsa mata cikin sakin fuska tare da zaro dubu d'aya a aljihu zai bata ta girgiza kanta snn ta qara sadda kanta qasa tace"Abba ai kullum kud'in da kake bani sunyi yawa har ma ynx akwai canjin da zasu kaini yau da gobe, dad'i Abba yaji har ransa ba don komai ba sae don halayen Rynt dake matuqar birge shi,yace"to shike nn tashi ki tafi Allah yayi miki albarka"

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

```Na Billy giro😊```

5/1/2017

🔮```19```🔮
Cikin yanayi najin kunya tace"amin Abba ngde snn ta tashi ta fita ,Abba ya bita da kallo d'auke da murmushi a fskrsa.


6:15pm
Rynt ce tsaye tana kallon rayuwar 'ya da mahaifi mai cike da ban sha'awa rayuwar su kmr rayuwar ta da Baffanta,a kullum sae ya rako ersa safe da yamma kuma idan aka tashi zata samu yazo yana jiran er tashi, da qafa suke zowa kuma da qafa suke komawa sbd ba wani jayawa da inda yake fitowa,sak yrnyr zata iya maida kanta gida amma so irin na 'ya da mahaifi kesa kullum yake zowa d'aukar er shi,hkn ba qaramin tuna mata rayuwarta da baffanta suke yi ba,sbd itama haka Baffanta ke mata a lokacin da take primary mkrntr ba wani nisa da gidansu amma kullum baffanta sae ya rakata haka kuma duk aka tashi zata samu yazo yana jiranta su koma gida.
Baffa shine sunan da yrnyr ke kiran Abbanta dashi hkn ke dawo ma Rynt da ryuwar ta sabuwa fil,shiyasa kullum bata da aiki sae na kuka idan tana kallon rayuwar su.
Ko yanzu hawaye ne suka silalo a hnkli kan kumatunta ta kai hnnu a cikin niqab d'inta ta share hawayen yayinda take magana a ranta cewa
_"Bazan yafe maka ba ba kuma zan ta6a barin ka ba, ka yanke min farin cikin rayuwata haka nima zanyi silar yanke taka"_

"Rynt"cewar munir wanda yazo gab da ita ya tsaya har tana jiyo qamshin turaren shi, bata kalle sa ba sbd lokacin wasu hawaye ne ke faman zarya kan kumatun ta,duk
da cewa da niqabi sanye a fuskarta sae take ganin kmr zai iya hangowa idan ta kalle shi.
A hakan ta gaida shi ya amsa yana mai kallon gefen da take kallo wato 'ya da mahaifi da sukayi er nisa a tafiyar su, ya nisa tare da fad'in"dama na jima ina son nayi miki wata tamvaya Rynt, meyasa kullum sae na ganki kina kallon mutanen nn shin kin san su ne? Cikin sanyin murya tace"ko d'aya haka kawai suke bani sha'wa"
Gama fad'ar hk takai hannu zata tsaida napep yayi saurin dakatar da ita ta hnyr cewa"dan Allah Rynt yau ki barni na kaiki gida kinji"Aa wlh ka barashi kawai ngde"pls Rynt baki san yanda nakeji ba wlh sam bana son ganin kina shiga napep bayan ni inada abinda zan riqa kaiki gida"um um nidai ka barshi nagode"
daga hk ta shige napep ta barshi.

Tana isa gida ta samu sae lokacin malamin su saliha ya tashe su sbd su a cikin gida ake karantar dasu.
Sae da ta d'an gyra fuskarta sbd har lokacin kuka take,snn ta cire niqab sae kawai sukayi ido hud'u da malamin su saliha zai fita,ga mamakinta kallonta yake har sae da ta gaishe shi snn ya kauda idonsa,ta maida dubanta gun saliha wacce ta qaraso gurinta sake da fuska Rynt tace"wae ku sae yanzu aka tashe ku?eh wlh kedai makara yayi bai zo da wuri ba,Rynt tace"wae nikam meyasa Abba bazai barku ku riqa zuwa isalimiyya ba don kmr hkn zai fi..... Mtsw!Ameera da ta biyo zata wuce taja wani dogon tsaki tana mai hararar Rynt kmr idanuwanta zasu fad'o tace"to wacce ta san dai dai ai sae kije da kanki ki snr da Abban namu abinda yake dai dai tunda shi bai sani ba, banxa er qauye mai banzar rayuwa!mtsw ta koma jan wani tsaki ta wuce.
Ita dai Rynt kallonta kawai tayi saliha tace"don Allah kiyi haquri haka hln Ameera yake kowa bata gani da gashi,murmushi Rynt tayi snn tace"nikam ko kad'an banji zafi ba wlh,nn dai saliha ta qara bata haquri snn kowa ta kama gabanta.

Rynt na shiga ciki ta had'u da Abba ya fito zai tafi masallaci tayi saurin durqusawa har qasa ta gaida shi, fuskar sa wasae ya amsa mata snn yace"Rynt an dawo daga islamiya?
Can murya qasa mai d'auke da tsantsar ladabi tace"eh Abba"
yace"to Allah taimaka tashi ki shiga daga ciki kiyi sallah ki kuma sami abinda kika ci kafin dinner kinji"tace
"to Abba" snn ta tashi ta wuce shi kuma ya wuce masallaci.

Yau satin inna d'aya da zuwa qauye.
A washe garin rnr ba islamiya sbd rnr alhamis ce Rynt ta shiga cikin en aikin gidan tana taya su aiki.
Abba ne ya fito ya same ta tana goge kan dining tana ganinsa ta durqusa ta gaida shi ya amsa
Yana mai kallon yanda idanuwanta suka kumbura yace"lfy Rynt me ya sami idanuwanki? Sadda kanta qasa tayi don dai baza ta iya cemai kuka tayi ba,sae dai ta gaya mai abinda tayi bayan kukan tace"Abba kwana nayi ina karatu"
Hln kun kusa fara jarabawa ne?Aa hardar qur'ani nakeyi,
Abba ya jinjina kansa snn yace"haqiqa kinyi dabara Allah ya qara miki kaifin baseera"
cikin sanyin murya tace"amin Abba nagode"
Yace "to ya naga kina aiki saki akayi ?Aa ina taya su ne kawai,to idan dai kinji kin gaji kar ki tilasta kanki ga qarasa aikin ki komawar ki kiyi zamanki kinji.
Gyad'a masa kai tayi yayinda ya ciro wyrsa a aljihu dake faman ruri ya d'aga ya tafi,Rnyt kuwa taci gaba da nata aiki.

umma ce a d'aki ita da Ameera yayinda umma ke matsawa Ameera kan ta tashi taje ta gyarawa mohd 6angarensa sbd yau zai dawo,cikin kukan shagwa6a tace"wlh umma kinsan halin yaya duk yanda aka gyra masa guri sae yayi fad'a wae bai yi ba, au kinsan dai baya son en aiki su gyra masa d'aki ko,ko kuma ni kike son naje na gyara masa? Aa umma ga wnn yrnyr mana mai baqin son aiki tana can yanzu haka tana taya su sahura aiki, don Allah umma kice taje ta gyara masa, to shikenan naji jeki snr da ita ki kuma nuna mata 6angaren snn ki dawo.

Sosai 6angaren ya matuqar birge Rynt har ganin take kaf gidan ba inda yakai 6angaren mohd kyau .
Sae da ta gama qauyancinta snn ta gyra dak'in tsaf har bathroom ta kuma feshe d'akin da room fresh kala kala da ta samu kan dressing mirro d'insa.

Bayan tayi wanka taci abinci ta tafi 6angaren su saliha ta sami umman saliha zaune a falo saliha na cire mata qumba, ta gaishe ta cikin ladabi yayinda mamar ta amsa cikin sakin fuska har tana cewa"er halak kmr kinsan zancen ki muke ina fad'in yau dai shiru saliha bata je ba baki shigo ba, Rynt tai murmushi tace"wlh mama na d'anyi wani aiki ne"
to sannu ,zaki iya zuwa kasuwa yau kuwa saliha ce ta matsa min wae tana son ku siyo inner wears da kayan kwalliya nace ta bari na bayar a siyo muku tace ita tafi son kuje da kanku, ta gefen ido Rynt ke kallon saliha dake faman roqonta kan tace eh, dako d'an murmushinta tace"eh mama xan iya"
To shike nn kuje ku rubuto duk abinda kuke so se kuxo na baku kud'i...a'a mama ki bamu kud'i kawai in munje zamu ga abinda muke so ai, Aa saliha nafi son ku rubuta sae na baku kud'in enuf, amma fa kar a manta da er autata ita ma a siyo mata nata, "to shike nn mama ai baza mu manta ta ta ba"nn taja hannun Rynt tace "muje ko"

Bayan sun shiga ne saliha ke cewa"Rynt ni kuwa wane aiki ne kikayi da duk yawan en aikin gidan baza suyi ba sae ke?hm na gyarawa yayanku d'akinsa ne wae zai dawo....cabd'i Allah ya cece ki da masifar sa, Rynt ta zaro ido tace"me?saliha tace "ba wani abu bane fa shidai matsalar sa d'aya duk yanda aka gyara masa d'aki sae yace bai yi ba yayita masifa kuwa.
Hm ni ba masifar sa ba ma ,zagin da yake yi ne bana so don wlh na tsani a zagar min uba ,"shi kuma yanada wnn"
cewar saliha snn tace" sae dai kiyi haquri don muma wlh haka yake zagin mu in ya tashi masifar sa.
Cikin muryar kuka Rynt tace"Ai gwanda ku naku iyayen suna raye ba zafi kmr ni da basa raye"
Saliha tace "haba Rynt meye na kuka kuma
"Baffa"cewar Rynt wacce ta rungume saliha tana kuka tace"saliha wlh ina mutuwar son baffana amma an raba ni dashi zama d'aya, ba a barni da zafin ba ana kuma zagar min shi"
Saliha tace"kiyi haquri Rynt haka mutuwa take bata barin wani don wani....
_shiyasa nima Bazan bar wanda ya kashe min shi ba koshi waye_
Haka Rynt ta fad'a a ranta yayinda saliha taci gaba da cewa"shi kuma yaya dake zagin ki ai kansa ya zaga ba kowa ba"
Nn ta samu ta rarrashe ta har ta daina kuka,snn ta rubuta abinda suke so ta kaiwa mama ta basu kud'i suka tafi kasuwa.

Guraren qarfe 3 mohd ya dawo shi kad'ai ba tare da kowa ba.
6angaren sa ya nufa yana bud'e 6angaren wani qamshin dad'i ya daki hancinsa ya kuma ga komai tas tas very neat ba kmr yanda ake gyra masa d'aki ba, dmn har bathroom ya duba bai ga matsalar komai ba sae ma wani qyalli da yake ,
ya fito ya durqusa tare da d'ora d'an yatsansa akan tiles ya shafo ba wani datti,
har ransa yaji dad'in gyaran ya kuma qudiri kyauta ga wanda yayi gyaran,don yauce rnr farko da ya ta6a samun d'akin sa hundred percent .

Sae bayan qarfe hud'u su Rynt suka shigo 6angaren su Ameera wad'an da dama tuni sun dawo da kasuwa suna can 6angaren su saliha zamansu.
Mohd suka samu jingine a jikin motar sa yana waya wanda kallo d'aya zaka yi masa kasan da masoyiyar sa yake waya.
Gaida shi sukayi ya d'aga musu hannu kawai, bayan sun d'an wuce saliha ke cewa"waeh!na miki murna kin huta da bala'in sa yau"
Cikin rashin fahimta Rynt tace" ko meyasa"sbd yana waya ne da masoyiyar sa Anti malika
da yake mutuwar so,wacce baya samun suyi waya kullum sbd aikinsa da kuma yanayin karatun ta shiyasa duk rnr da yayi waya da ita tofa bazai yi masifa a rnr ba,,Rynt ta girgiza kanta tare da fad'in"hm mugun gaye ashe yana soyayya har wae ma kuka sani"
tayi mgnr ne a ranta ashe ta fito
Har Saliha ke cewa"wa! ai ba wanda ya sani koni qanwarta qawata ce sosai a school shiyasa na san komai,dmn ma akanta yayi tafiyar nn zuwa UK don tayata murnar kammala karatun ta shine ya jirata suka dawo tare wanda inshaAllah mun kusa shan biki sbd tuni ita yake jira.
"Yayi Allah taimaka" cewar Rynt kafin take cewa
_"abin tausayi malika rnr aure mijinki gawa"_

Basu jima da shiga ba mohd ya shigo ya sami Ameera na saukowa ta fito daga d'akin umma yace"ke wa ya gyra min 6angarena "cikin inna inna na jin tsoron sa tace"bani bace wlh wnn yrnyr ce Rynt"
je kiramin ita"
ta tafi sae dad'i take ji yau kam fad'an bazai qare kanta ba.

Rynt ta fito sanye da qaton hijab d'inta har qasa ,
ta same shi zaune kan dining har ya fara cin abinci.
Taje kawai tayi masa tsaye tare da kauda kanta gefe ,ya d'ago fuskar sa a hnkli yana kallonta snn yace"kece kika gyra min d'akina wae?a taqaice tace"eh"
Ya ta6e baki yace"hm abun mamaki a qauyen naku ke ke gyarawa sarkin garin

Please Login or Register in order to submit comment